Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta ce " What?! Are you serious?

"Yeah! Ya bata amsa.

"Tabdijan! Cewar Ummie dan abin ya bata mamaki.

"Ba wani abun mamaki bane! Nima ji nayi hakan ya kwanta min! Anjima zanje na samu babanta nasan bazai hanani ba"

"Allah ya tabbatar da alkhairy! Dole mu fara shiri nan da wata biyu fa?

Gyada kai yayi alamar hakane. Yusuf ne ya shigo cikin suit. Sassauta tie din yayi yana ajiye jakarsa ya ce " Ya naga anata washe hakora?

Nawal ce ta zo da gudunta tana yi masa oyoyo.

Daukarta yayi yana dariya sannan ya sauketa.

" Yaya Farooq ne zaiyi aure! Ummie ta fad'a tana kallon Yusuf.

"Aure Farooq? When? Kuma wacece? Yusuf ya fad'a cike da mamakin lamarin.

"Anjima zaka rakani wajen babanta bayan sallar Ishai"

Gyada kai kawai Yusuf yayi dan har yanzu mamakin abun be barshi ba.

A nan gidan Yusuf ya yini sai bayan sallar magariba sannan shi da Yusuf din suka nufi gida wajen Mama.

A falo suka tarar dasu, Mama, Ramlah da kula Sabir.

Upstairs Farooq ya tafi danyin wanka. Yusuf kuma zama yayi kusa da Sabir yana fad'in " Gashinan yayi yawa ayi aski!

"Yanzu na gama magana! Ya ce wai gayu! Cewar Mama tana kallonsu. "Almakashi zansa na yayyanke"

Ramlah ta fada tana murmushi.

"Yau fa dan naki yayo miki sirika! "Sirika? Farooq ko kai?

"Ni kuma? A'a A'a biyu na sun isheni! Farooq dai! Yanzu ma wajen mahaifinta zamuje!

Cikin tsananin farinciki Mama ta ce " Bana son wasa fa!

"Wasa kuma? Dagaske nake fa!

"Ikon Allah! Amma gaskiya lamarin nan yayi min dadi, Allah yasa rabonsa ce! Kuma yasa jinkirin alkhairy ne"

"Amin! Suka amsa gaba daya.

Ya dade kafin ya sakko. Yasha manyan kaya yayi kyau sosai.

Murmushi dauke a kan fuskar Mama ta kalleshi ta ce " Allah ya bada sa'a"

Da Amin ya amsa yana murmushi dan yasan Faisal ya fesa musu.

Sallama sukayi wa Mama sannan suka tafi.

A kofar gidan Zayd yayi parking yana kallon Yusuf daya kashe da mamaki.

"Yes! Ummie nake so! Tun kafin ta zabi wanna Dan naka taga sabon jini gwanda na zo na fara kafa tawa gwamnatin.

Dariya Yusuf ya fashe da ita yana dukan Farooq kadai ya ce " Baka da dama wallahi! Ai baka fad'a min! Allah yasa ban fad'awa Sabir ba da anyin abun kunya!

"Da sai dai ya hakura wallahi! Cewar Farooq yana fitowa daya motor. Shi ma Yusuf fitowa yayi yana gyara rigarsa ya ce " Da anyi Baba kwabo!

Dariya Farooq yayi ba tare da yace ko mai ba ya nufi gate din gidan ya fara knocking.

Bugu biyu aka bude. Zayd ne sanye da jallabiya hannunsa rike da Hydar dake kafada dayan hannun kuma Khaleel ne.

"Wa nake gani haka? Ya fada yana kallonsu.

"Mu ne dai! Wani important abune ya taso kuma we have to be in the office right now! Cewar Yusuf yana kallonsa.

"Toh, bari muyi sallah sai muje"

Dariya Yusuf yayi ya yana daukar Khaleel ya ce " Kafi babanka kyau!

Dariya Khaleel yayi cike da jin dadi. Saukeshi yayi yana kallon Zayd ya ce " Nagodewa Allah daya bani manager kmr kai! Babu wani aiki mun dai zo wajenka be but muje muyi sallar gaba daya!

Masallacin dake dan nesa dasu suka nufa.

Sai kusan 9 suka dawo gida dan Zayd ya biya wajen me suya saboda Ummie.

Shi ya fara shiga falon yana kallon Zarah ya ce " Bakin dare mukayi samo musu abin tabawa! Ke kuma Ummie tafi da yaran nan daki"

Da toh ta amsa tana tashi tsaye ta ce " Naman fa?

"Au! Ya fada yana mika ma ta ledar hannunsa. Murmushi tayi ta karba sannan ta wuce sama tare da yaran.

Iso yayi wa su Yusuf din suka shi go, Zama sukayi a akan rug. Da sauri Zayd ya ce " Ku zauna a kujera mana!

"Nan ma is ok! Farooq ya fad'a yana dan murmushi. Shi ma Zayd murmushi yayi dan ya fara harbo jirgin.

Zarah ce ta fito hannunta rike da tray wanda ke dauke da abin tabawa.

A gabansu ta ajiye tana fa din "Ina yininku?

Yusuf ne kawai ya amsa banda Farooq. Dagowa tayi ta kallesu. Murmushi ta sakar musu sannan ta wuce sama.

Ajiyar zuciya Farooq ya sauke, shekaru 6 kenan rabon daya ganta! Tabbas idan so cuta n hakuri ma magani ne! Kuma yana fatan tarin soyayyar da yayi wa Zarah a baya ta dawo kan yarta!

"Shine abinda ya kawo mu! Kasan bazamu tsaya boye² ba.

Abinda yaji Yusuf ya fada kenan.

"Alhamdulillah! Ta bangarena babu matsala! Sai dai wajen Ummie ko mahaifinta! Amma badamuwa ka fara zuwa dan ku fahimci juna idan yaso daga baya sai kaje ka samu shi Baban nata"

"Shikenan! Bari mu tafi! Yusuf ya fada yana tashi.

"Zan iya ganinta yanzu? Cewar Farooq yana kallon Zayd.

"Badamuwa" Zayd ya amsa yana hawa stairs.

Da sauri Yusuf ya kalleshi ya ce " Me haka?

Banza Farooq yayi masa.

"Idan ka gama ka sameni a mota! Idan kuma da rabon zakayi tafiyar kafa shikenan"

Be jira cewarsa ba ya fita ya barshi a zaune.

Sam beji takunta ba kasancewar babu takalmi a kafafunta.

A dan nesa dashi ta zauna tana fad'in "Ina yini?

Dagowa yayi ya kalleta kafin ya amsa da "Lafiya lau ya makaranta?

"Lafiya lau!

Ta amsa idanunta kyar a kansa.

"SS nawa kike yanzu?

Dariya tayi kadan ta ce Level 2"

Cike da mamaki ya ce " Lvl 2? Shekaraki nawa yanzu?

Dan juya idanunta tayi kadan sannan ta ce " Shekarata 18, nayi candy ina 15yrs"

Jin jina kai Farooq yayi dan abun ya bashi mamaki.

Shuru ne ya ratsa kafin yayi breaking silence din da fad'in " Inaso na aureki! Saboda ina sonki! Kuma inaso ayi auren kafin azumi"

Shuru Ummie tayi tana jin maganar wani banbarakwai!

"Kinyi shuru?

"Toh in duk abinda Uncle Zayd ya ce mama shikenan!

Murmushi yayi kadan yana kallonta ya ce " Zan baki lokaci kiyi tunani! Ni bana son jan lokaci! Ga wayata samin contact dinki"

Karba tayi ta saka sannan ta bashi, sallama sukayi ya tafi. Ta dade tana tunanin maganganunsa.

Jikinta ne yayi sanyi tunowa da labarin da Taj ya bata a kansa!

Washe_gari

Tun 8 ta gama shirin school, tare suka fita da Zayd! Ko kadan beyi ma ta zancen Farooq ba! Itama haka har ya ajiyeta a makaranta.

A kofar in da zasuyi lecture yau taga Taj yana tsaye tana duba handout.

Karasowa tayi tana kallonsa ta ce " Hi! Yakake!

Murmushi yayi ya kalleta ya ce " Lafiya ya gida?

"Qalau! Mushiga kar ya rigamu"

Be amsa ba ya bata hanya ta shiga sannan yabi bayanta.

Lecture din 2hrs sukayi sannan suka fito. A daya daya cikin kujerun dake karkashin bishiya suka zauna.

Kallonta yayi ya ce " Yau kinyi kyau!

Dariya tayi kadan tana kallon abinda aka gama koya musu wanda tayi jotting.

Kusan 10mins da zamansu sannan ta kalleshi ta ce " Wani yazo neman aurena wajen Uncle Zayd jiya!

Da sauri ya kalleta ya ce " Aure? Waye wannan kuwa?

"Farooq! Wanna patient din daddy dinku" ......


Autar Mama ce
[3/16, 4:47 PM] Brother❤: ✨✨ *UMMIE* ✨✨

*Mallakar*
*Autar Mama*

*Wattpad @Autarmama56*

https://www.wattpad.com/1203262427?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=AutarMama56&wp_originator=AVSFFDeB1ik14hZQ%2BxxUAvT7dauoZJTfPkFRU37BGAsaR3ZA96CjlitL%2FSrBEJxd6BVS%2FLI0RJKCo1EUy1FGhDEIfmfL54HMxe11C6NGN6P%2BRqQD34QiQD90l6oj2mph

*EXQUISITE WRITER'S FORUM*

*END*

*Shafi na arba'in da d'aya*

Abaya ta saka me kyau da kuma tsada, ruwan hoda ce hakan yasa chocolate color dinta ya kara fitowa yayi kyau sosai. Turare ta fesa kadan tana kare wa kanta kallo a mudubi, ita kanta tayi wa kanta kyau ballanata ma shi!

Khaleel ne ya shigo dakin yana fad'in "Aunty Ummie, Umma ta ce kizo yana jiranki"

Da toh ta amsa tana gyara veil dinta ya zauna sosai sannan ta biyo bayan Khaleel.

Bata nufi dakin Ummanta ba, direction down stairs ta nufa.

A zaune ta ganshi kan sallayar data shinfida ya tankwashe kafafu tare da durkusar da kai yana latsa wayarsa.

Bakinta dauke da sallama ta karasa inda yake. D'ago idanuwansa yayi ya kalleta from hair to toe.

"Masha Allah! Ya fada a fili yana kallonta. Murmushi tayi tana zama a gefensa ta ce " Nasan nayi kyau ai"

Sosai ta bashi dariya, yarinyar akwai kuruciya sosai a kanta.

Bai ce komai ba sai idanu kawai da ya zuba ma ta yana kallo.

"Ina yini? Ya Mama?
Ta fad'a a sanyaye"

"Lafiya Lau, Baki tambayi sauran ba?

"Ai bansansu ba kai ya kamata ka ce akwai wasu, kaga ni kasan kowa ko?

Murmushi yayi kadan kafin ya ce " Ok! Akwai Yusuf! Shine babba sai ni! Auta! Sai Kuma matan Yusuf akwai, Ramlat itace uwargida da d'anta Sabir wanda muka hadu da daddare kwanaki! Sai dayar matar tashi Ummie itama ake ce ma ta, da yarta Nawal Amma yanzu tana da ciki, sai kuma Yan uwa na kauye watarana duk zan kaiki ki gaidasu"

"Tohm shikenan" Ta amsa tana kallonsa.

Murmushi ya sakar ma ta ya ce "Kina da kyau Masha Allah!

Jiya idanunta tayi cike da jin dadi ta ce " Nagode!

"Toh! Kamar yadda na fada miki bana son jan lokaci! Kinyi min kuma a shirye nake da aurenki! Kefa?

Kasa tayi da kanta, karo na farko a rayuwarta data ji tana nauyin fadawa mutun wani abu.

"Kinyi shuru? Ya fada yana murmushi dan ga dukkan alamu sun nuna ita min ta yarda amma yafi so ta fada da bakinta.

"Nima haka" Ta fada a sanyaye.

"Kema me?

Shuru tayi ta kasa cewa komai sai kallon yatsun hannunta da takeyi tana wani murzasu.

"Ummie Dan Allah ki fada mana"

"Na yarda! Allah ya tabbatar mana da alkhairi!

Shuru yayi yana kallonta, baya fatan ace Zayd ko Zarah ne suka ce ma ta tayarda! Yana fatan ya kasance ta yi ra'ayin hakan ne da kanta amma a hankali zai gane idan ma tana sonsa"

Jin yayi shuru yasaka ta d'ago da idanunta, idanuwansu ne suka hadu kusan minti daya suna kallon juna kafin tayi kasa da na ta tana jin kamar ta nitse kasa dan kunya.

"Ummie kin yarda na je wajen mahaifinki da maganar auren ki?

A hankali ta ce " Na yarda"

"Toh Masha Allah! Naji dadi Allah ya tabbatar mana da alkhairi"

Da amin ta amsa tana dam dagowa kadan ta kara da fad'in " Abinci fa?

Zaro Ido yayi yana danyi kasa da murya ya ce "Waye yace miki ana cin abinci gidan surukai?

Turo baki tayi dan yau idan beci abinci nan ba dariya Ummanta zatayi ma ta har da tsokana ma.

"Nifa sai kaci" Ta karashe maganar tana tashi ta bude kula ta fara serving dinsa, sosai ta cika plate din sannan ta dauko bowl ta zuba masa farfesun kayan cikin da tayi shima sai da ta cika sannan ta zuba natural pineapple and coconut juice da tayi masa a Kofi tana ajiye a gabansa ta ce Bismillah!

"Sai dai muci tare"

"Aunty karki manta ki rage min"

Ta jiyo muryar Khaleel daga sama. Wani k'ululun bakin ciki ne ya tsaya ma ta a wuya data sani bata ce bazata bashi ba da ace Farooq din bako ne sosai da ya gama kunyatata amma yanzu ma ai ya kunyatata! Ni kuwa nace siblings duniya ne lol....

"Alhaji Khaleel na magana fa! Cewar Farooq yana murmushi dan ya lura da yanayinta.

"Uhm" Ta fada tana dan kallon up stairs ko zata hamgoshi amma Bata ganshi ba tasan Ummanta ta korashi daki.

Spoon ya saka guda biyu yana kallonta ya ce " Bismillah"

Ba musu ta dau spoon d'aya suka fara ci yana yi yana kallonta.

Sai da suka gama ci sannan ta ya kalleta ya ce " Umma ta iya girki"

"Toh ni na dafa! Ta fada tana dan kumbura fuska.

" Ban yarda ba!

Turbune fuska tayi tana Neman saka masa kuka, "Sorry mana wasa nake!

Shuru tayi taki cewa komai tana kallonsa

"Ummie! A bikin mu fa babu wani dinner ko ma ince babu event ko d'aya! Daga daurin aure sai walima da nasan Zarah zatayi but bayanshi bana son komai"

"Shikenan, Allah ya tabbatar mana da alkhairi!

Da amin ya amsa sannan ya tashi Yana fad'in " Goma ta wuce abari na gudu gida, yau kin cika min ciki dayawa"

Murmushi kawai tayi kafin itama ta tashi tsaye.

"Sai da safe ko?

Ya fada yana kallonta. "Toh Amma muje na rakaka bakin kofa"

Be ma ta musu ba, har kofar falo ta rakoshi sannan ta dawo cikin tayi kaye² na kaya sannan ta nufi dakinta bayan tayi wa su Zarah sai da safe daga bakin kofa.

Tana komawa daki ta tarar da kiran Taj yafi Goma. Cike da mamaki ta yi redialing number tana karawa a kunne.

Katsewa yayi ba jimawa ya kirata.

Dauka tayi tana fad'in " Ya jikin? Naga kiranka dayawa har gabana ya fad'i"

Murmushi yayi me sauti kafin ya ce " Bakomai dama na kiraki ne na fada miki jibi insha Allah zan tafi UK tare da Daddy! Gobe zamu tafi Lagos daga chan zamu wuce"

"UK? Ban gane ba! Me zakayi a UK Tajuddeen?

Shuru yayi dan ya manta rabon da ta kirashi da asalin sunansa.

"Kayi shuru?

"Ah Ummie Bakomai a cahn zan cigaba da karatu na! Ina miki fatan alkhairi Allah ya tabbatar da farinciki a cikin rayuwarki ta yanzu da wadda ma zaki shiga a gaba"

"Taj! Wai dagaske kake?

"Eh mana!

Ya bata amsa.
"All of the sudden? Taj ko dai wani abu ya faru?

"Bakomai UMMIE I just want peace of mind! Amma karki damu zan dinga zuwa lokaci zuwa lokaci insha Allah"

Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta ce " Shikenan Taj, amma banji dadi ba"

"Karki damu kinji?
"Toh Allah ya bada sa'a"

Da amin ya amsa yana katse wayar.

A sanyaye ta ajiye wayar dan taba ji dadi ba ko kadan.

Washe gari bayan da dawo daga makaranta ta na daki a kwance dan ta gaji sosai, Zarah ce ta shigo daki tana kallonta ta ce " Waye kuma yake nemanki a waje? Nifa bana son kule² kin amincewa Farooq amma kina kuma jajibo wasu?

A kasalance ta kalli Ummanta ta ce " Bansan me waye ba fa kuma bance kowa yazo ba"

"Sai ki tashi kije ki fada masa Dan ba'a Neman aure cikin Neman aure tun da shi Farooq din yaje ya samu Mahaifinki tun dazu kuma kinsan abun kamar na gida ne ba dadewa za'ayi ba ko?

Tashi Ummie tayi da zuciyarta ta sanar ma ta da cewa Saleh ne!

Hijabi kawai ta saka sannan ta fita. Yau ko mashin din bezo dashi ba. Fuskarta dauke da murmushi ta karasa tana fad'in "Malam Saleh yau Ina mashin din?

"Yana wajen gyara! Ya fada yana kallonta cike da mamaki ganin ta saki fuska.

"Kar ka wani damu kaji! Ai rufawa juna asiri ne! Bakomai wallahi ya wuce badai nason Iyayena su sqn Kaine ka aikata hakan kawai zan kai musu kai ne a matsayin wanda nake so, Kuma yanzu Uncle Zayd be barina na fara hira ba ka dinga zuwa makarantar mu kawai muna haduwa"

Cikin mamaki kawai yake kallonta dan beyi tsammanin hakan daga gareta ba.

"Shashahsha! Ta fada a ranta tana kallonsa.

"UMMIE! Dagaske kike?

Ya fada cike da tsantsar mamaki.

"Eh! Fatan zaka rike alkhawari?

Hawaye yaji ya taru a idanunsa.

Gogega yayi yana fad'in "Nagode UMMIE! Nagode! Amma inaso naa fada miki wata magana idan ba damuwa!

"Inaji! Ta fada yana kallonsa.

"I..Ina da lungs cancer! Shuru tayi tana kallonsa.

"Yes, sakamakon shan taba dana dinga yi! Kuma Ina stage 2 please Ummie inaso ya zamana ba yaudarata zakiyi ba!

"Lallai ma wannan Salen! Wato ya aureta ya mutu ya mayar da ita karamar bazawara? Ko ma dai ita zata rigashi mutuwa bazata taba aurensa ba! Kawai zata rabu dashi yaje yaji da cutarsa ta fasa wahalar dashi ta barwa Allah shi zai saka ma ta!

Ajiyar zuciya ta sauke tana fad'in "Kayi hakuri! I was testing you Kuma ka fad'i! Ni an kusa aurena kaje Allah ya baka ta gari!

Bata jira cewarsa ba ta juya ta barshi a wajen.

"Tabbas yana me dana sanin abinda ya aikatawa UMMIE! Ba mamaki da be aikata hakan ba zata iya yarda ta aureshi! Amma son zuciya ya kaishi ya baroshi!....

*Dan karshen Saleh ya kasance haka be zama lallai naka ya kasance haka ba, ba mamaki naka yafi nashi tsananin muni! San zuciya bacin ta! Zina babban laifi ce! Mu guji aikatata! Tana janyo abubuwa dayawa! Allah datar damu Amin*

*Bayan kwana biyu (Na hausawa😂😂)*

Shirin biki aka fara dan har an saka rana 2months.

Both bangaren amarya da ango! A cikin wata ukun da sukayi da Farooq ta jiku da soyayyarsa sosai haka Shima a nashi bangaren, soyayyarsa gwanin birgewa tayi da zuba masa kuruciya! Hankalin Zarah ya kwanta sosai dan Mama da kanta tazo taga Ummie har gida Kuma da alama za'a zauna lafiya.

Biki saura wata d'aya Zarah ta tura Ummie meduguri wajen me gyaran jiki, Zainab ce ta hada su da ita kuma anyi ma ta bayanin halin da Ummie ta tsinci kanta saboda tana bukatar gyara yadda ya kamata.

Kusan kullum suna cikin vd call ita da Omar dinta.

Yau kwananta 15 a meduguri, tayi bala'in canzawa ta kara wani kyau da sheki sai khamshi takeyi! Me gyaran jikin bata bari ta fito daga daki! Kuma ko da wasa ta haneta ta fadawa mijinta wani abu ya taba faruwa da ita kamar yadda Zainab da Zarah suka ja ma ta kunne!

12pm

Ummie na zaune tana cin naman da me gyaran jikin ta bata wayarta ta fara ruri.
*OMAR❤️✨* Shine sunan dake yawo a screen din wayar.

Murmushi tayi ta dauka tana fad'in "Hello Habibi!

"Hy! Abar kaunata Ina meduguri fa!

Zaro Ido tayi ta ce " Me?

"Yes! Ina ma kofar gidan da kike! Aunty Zee ce ta kawo ni! Tare muke ai!

Ajiye bowl din hannunta tayi tana fitowa cikin sanda. Bata ga kowa a falon ba, da sauri ta fice tana isa bakin kofar gidan.

"UMMIE! Taji muryar matar ta kirata da karfi!

Runtse Ido tayi alamar kash.

Fitowa matar tayi tana kallonta ko takalmi bata saka ba!

"La'ilah! UMMIE?

"Aunty please! Cewar Ummie tana bude kofar gidan.

Aikuwa Farooq ne da Aunty Zainab.

Zaro Ido tayi cike da mamaki tana kallonsu.

Ji tayi an rufeta da hijabi.

"Muje ciki! Taji muryar me gyaran jikin ta fada tana janyota. Bata da choice haka nan ta bita suka koma daki.

Kallon Aunty Zee yayi ya ce " Kinganta kuwa?

"Ai ba makauniya bace ni! Muje ko kwana bazamuyi ba duk dare sai mun koma gida"

"Bakomai! Ya fada yana shiga sannan Aunty Zee.

Me gyaran jikin ce ta fito tana musu iso zuwa cikin falon.

Gaisawa sukayi ta kawo kusu ruwa tana fad'in "Ashe so kuke ku bata min aiki na kuka zo!

Ta karashe maganar cikin zolaya. "Kinga mijin na ta shi ya takura min!

Zainab ta fada tana nuna Farooq.

"Aikuwa haka zai koma be ganta ba danni haka tsarina yake!

Narai² yayi da idanunsa Yana kallon matar ya ce "Just two minutes please!

"Addition of Money! Ta fada tana dariya. "Na yarda! Ya amsa da sauri.

Kiran Ummie tayi, dama jira take da sauri ta fito tana kallonsu.

"Karaso mana! Cewar Zainab. Karasowa tayi ta zauna kusa dashi tana kifta masa Ido tare da daga masa gira daya.

Taba Baki Aunty Zee tayi dan tun da take bata ganin amarya mara kunya irin Ummie ba.

Waje me gyaran jikin ta basu.

Haka ma Aunty Zee Dan tana sonyi sallar azahar.

"Toh yaya? Ya kewata? Ta fada tana kallonsa.


"Kinga yadda kika koma?

Ya fada idanunsa a kanta. Dariya tayi tana fad'in " Tukunna ma! Ya maganar lefan?

"Ba kinki bada size din ba! Shikenan babu ke Babu bra ai!

Turo Baki tayi ta ce " Toh Ummana ta ce ansaka! Ta fada min yau kwana uku da kaiwa, nagode Allah ya kara budi!

Ta fada tana yin kasa da kanta. Hannunta taji ya riko, da sauri ta kalleshi a hankali ya fara murzawa! Kwacewa tayi tana fad'in " So kake Aunty ta fito ta ganka ko?

Dariya yayi ya ce " Ok sorry! Bari na je nayi sallah"

Da toh ta amsa tana kallonsa har ya fice tana jin zuciyarta na kara narkuwa tare da tarin kaunarsa.

Be dawo ya tarar da ita a falo ba, daga cikin daki sukayi sallama sannan suka tafi tana ji kamar ta kamoshi.

Kwanaki na ta sudewa, lokaci na karatowa biki saura kwana biyu yau! Kuma yau da yamma Ummie ta dawo gida tayi wani kyau na bugawa a jarida shafin farko😜

Farooq yafi kwana 10 be ganta ba haka suke ta hakuri Dan vd call ma yanzu Babu saboda Zarah ta karbi wayarta! Ta kagu ayi auren dan kullum Ummin Bata da zance sai na Farooq!

Tun daga chan akayi wa Ummie kunshinta da gyaran gashi! Ko a gida bata fitowa.

Har jere an gama yi ma ta komai a gidanta bungalow me kyau da tsari dan ba babba ne sosai Two brothers sun iya tsarin gida da kawatashi😜

Yan uwan Ummie sai San barka ake tayi ma ta, tare da fatan zaman lafiya, tun kafin ayi jere Farooq ya turo ma ta da vd din gidan komai a choice dinta akayishi.

Ko irin sanyi da jikin amarya yake idan biki ya matso jikin Ummie beyi ba! Me gyaran jiki ta gama kwantar ma ta da hankali Kuma ta tabbatar ma ta da mijinta bazai gane ba sannan duk daren dadewa karta fada masa! Allah ya rufata mata asiri karta ce zata tonawa kanta.

Ana gobe daurin aure Rahama tazo, sosai Ummie tayi mamaki da ta ce ma ta kwana zatayi ai mijin ya barta dan shima zai tafi kasar waje kuma tana laulayin ciki bazata iya binshi ba.

Da daddaren ranar Ummie da Rahama na kwance suna dan taba hira Zarah ta shigo tana fad'in " Ummie Aunty Zee na kiranki!

Da toh Ummie ta amsa tana fita daga dakin.

"Rahama sannu! Laulayi da wahala! Ga wannan kisa a baki saboda Tara yawu zakiji yawun baya taruwa"

Da toh Rahama ta amsa tana karbar gautar da Zarah ta bata.

Kadan ta gutsura ta saka a baki sannan Zarah ta fita.

Kaya Aunty Zee ta bata tana fad'in " Sa'adah ce ta aiko dasu! Wannan gold necklace din Kuma babanki ne ya aiko dashi su zaki saka gobe da safe Wanda Zayd ya baki Kuma idan za'a kaiki gidan miji sannan Ihsan tana ta nemanki tun da babanku ya sauketa maybe tana dakin Zarah ki duba!

Karbar kayan Ummie tayi tana kallon Gold necklace din shigen wadda Uncle Zayd dinta ya bata. Zama tayi kusa da Zainab tana fad'in "Aunty Zee ban taba tunanin Abbana zai Soni haka ba!

"Kinga bana son shirme bana ce ki manta da rayuwar baya ba? Kinsan dai Aunty tana nan idan taji kina zancen abubuwa da suka faru zaki ci ubanki!


Murmushi tayi tana tashi ta fita.

Karamar wayarta ta dauko bayan ta shiga daki takira Shehu, sun dade suna waya harda Aunty Sa'adah sannan sukayi sallama.

Tana son kiran Omar Amma Ummanta tace A'a karta kuskura ta kirashi.

Rahama har tayi bacci.

Daukar wayarta tayi ta kira lambar Taj ta kasar waje, bugu uku ya dauka.

"Taj nice! Ya kake? Ya kwana biyu?

"Lafiya Lau UMMIE ya biki?

"Alhmdll! Ta amsa tana murmushi! Addu'a yayi ma ta sosai sannan sukayi sallama.

Washe_gari

Karfe 11 na safe aka daura auren Farooq da Ummie a kan sadaki naira 200k, daurin auren d'aya tara daruruwan mutane.

Ummie tayi kyau cikin lace din da Sa'adah ta ba ta.

Light make up akayi ma ta. Ansha hotuna kafin amarya ta fito.

Tun da ya dora idanunsa a kanta ya kasa daukewa.

Tana dagowa ta hangoshi, kashe masa Ido tayi tana dariya.

Yusuf na kallonsu! Sam Ummie bata jin kunyarsu har wani kashe masa Ido take!
Ya fada a fili Yana kallon Farooq.

Sai wajen karfe 1 sannan suka koma gida aka cigaba da gudanar da shagalin bikin.

Karfe 6 saura aka shirya Ummie cikin lafaya me kyau da tsada zuwa gidanta na aure.

Tasha fada sosai da nasiha. Ko digon hawaye batayi ba. Ummanta na gama yi ma ta fada

Please Login or Register in order to submit comment