Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gyarawa Assadiq ne Yadawo kai tsaye dakin safiyya yanufa yana shiga yai gun fadila tafarka tanata kalle kalle da sauri Ya dauketa jiyayi jikinta zazzabi da sauri ya shiga kwadawa safiyya kira

A parlon sukai kacibus cikin kidima ya tambayata

"safiyya meyasami Fadilaty naji jikinta xafi "

" sannu da xuwa Dee"

"yauwa inajinki"

"tunda aka kawo ta daga gidan momy take kuka in antaba hannuta xata sa kuka"

"safiyya karfa yarinyar nan faduwa tayi "

Shiru taimasa hannun ya taba ai kuwa sai kuka, shiru yayi can yace

" samata kaya mutafi asibiti"

Kaya ta samata masu dumi tafesheta da turare kuka take ta faman yi kallon ta yayi

"sopy bata tasha kafin mutafi"

"Dee taki sha da kyar ma nasamu tasha daxu"

"kide bata mugani"

bata ta kuma yi kin karba tayi karbarta yayi suka fita safiyya ce ta rufe kofa a mota tasamesu karbarta tayi yajasu suka nufi asibiti likita yadubata ya tabbatar musu faduwa tayi Assadiq ne ya maida dubansa ga safiyya yace

"safiyya ya akai tafadi"

"Dee bansaniba nima haka aka kawota"

Magani aka rubuta musu suka je suka siya suka koma gida dakansa yabata maganin yarungumeta take tai bacci yayan safiyya ne yaimata waya yana waje Assadiq tafadawa yamikamata fadila yafita yashigo da shi da cewa yayi baxai shigo ba xance yazo gurin jalila dariya Assadiq yayi yace

"Dr ai gwanda kashigo mu gaisa"

Shiga yayi suka gaisa safiyya ma ta gaidashi yakarbi fadila jiyayi jikinta xafi yadubi safiyya yace

"safy yanaji jikinta da fever anbata magani"

"Eh ya yanxu muka dawo daga asibiti"

"ok"

Maida dubansa yayi ga Assadiq yace

"Assadiq naxo da kokon bara ta dafatan zaabani auran jalila"

"Aa me xai hana Dr amma naji dadi sosai Allah ya tabbatar da alkhairi"

Suka amsa da ameen safiyya taje ta kawo masa lemo yadan sha kadan yafita xuwa bakin gate waya yaimata baajimaba ta karaso tacaba kwalliya tayi kyau nan suka sha hirarsu suka kulla alkawarin aure yaimata Sallama yatafi yabata kudi da kyar ta Karba yaiwa su safiyya ma Sallama ciki jalila ta koma suka gaisa da safiyya ta bata hakuri akan faduwar da fadila tayi karaf akunnan Assadiq take ransa yabaci kai tsaye gidansu yanufa yana xuwa yasamesu a Parlo marin farhana yayi nan ta fasa ihu da sauri momy tafito tana xuwa ta daga Assadiq yanata faman masifa nan ta daka masa tsawa ta rufe shi da fada take tsanar safiyya ta nunku aran farhana cikin fushi yabar gidan kai tsaye gidansa yawuce yasami jalila nacin abinci fadila ya dauka yai dakansa jalila nagamawa taiwa safiyya Sallama ta tafi kayan abincin safiyya ta dauka takai masa daki cikin bacin rai taganshi da kyar tasamu yaci abincin sukai salla sukai shirn bacci can cikin dare xaxxabi ya rufe safiyya saboda yadda fadila taki shan nono yaciko yadameta gashi kwana fadila tayi tana kuka Assadiq Hankalinsa yakasu biyu sai gefin asuba yasamu fadila tai bacci.












*NASEEBA GAWO*✍🏻
[9:38Pm,2017]


*®💦💦💦TALENTED WRITTERS FORUM*💦💦💦

*💦T F*💦




*KANNAN MIJINA*
👩‍👩‍👧




*NA*

*NASEEBA I UBA*💐



*TALENTED WRITTERS kuna kamshi ana binku da humra cewar kamshin TALENTED*🤣

*Hadin kanmmu shine alfaharinmmu*🤝🤝




*masoyana ina godiya da adduoinku gareni nagode sosai da kulawar ku gareni Allah yabar kauna ina sonku Fadilaty binty na gaidaku kyauta*👌🏻😘






*61*







~~~Bayan kwana biyu fadila tasami sauki haka safiyya ma amma ta rage kaita gidan su Assadiq yarinyar tayi wayo ta girma ga kyau gwanin shaawa yau Assadiq ya shirya dan tafiya kasar dubai tun safe safiyya ta tashi tai masa danbun kaxa da yawa tadibarwa momy tabayar aka kaimata daki ta koma ta tatar da Assadiq na hada jakarsa ta kaya cikin shagwaba ta dubeshi tace


"Dee baxaka bari in xo in hadama kayan ba"

"I am so sorry Sweet sopy naga kina aiki ne shi yasa"

"Dee gsky xamuyi kewarka da yawa ni baxantaba iya bacci ba inba a faffadan kirjinkaba"

Tafada tana shigewa kirjinsa bazato tafara rera kuka kidimewa Assadiq yayi dada matseta yayi a kirjinsa yafara kissing dinta mayar masa tafara yi cikin kwarewa xip din rigarta ya xuge nan ya dada gigice wa akan gado suka xube Assadiq yagama ki dimewa nan suka shiga farantawa junansu sun barje kmr sababbin aure basa taba gjy da junansu domin safiyya jaruma ce tana jure bukatar mijinta shiyasa yake dada sonta sai da komai ya lafa sannan ta hada musu ruwa sukai wanka nan ma sai da suka kuma shan soyayyar su kukan fadila ne yasa Assadiq saurin daura towel yafito ya xo yadauketa yana daukarta tafara yimasa dariya shima dariyar yaimata yafara mata wasa safiyya ce tafito itama daure da towel ta dubeshi tace

"Dee kawota aimata wanka"


"papanta ne xai mata ko Fadilaty binty"

Kmr taji shi tai dariya


"Dee karfa kasamata yaji a ido tom"


"lallai ma sopy bari kiga yadda uba xai wanke yarsa"


Ban dakin yanufa ya hada ruwan xafinsa ya tsoma fadila ya shiga yimata wanka tana tai masa dariya ahaka ya kammalamata tsaf yanadota a towel dinta yana fitowa ya tarar safiyya ta shirya tsaf cikin wata ash din atamfa riga da siket rigar ta kamata ido kawai Assadiq ya xuba mata yace


"matar Assadiq kinyi kyau anyawa kuwa bafasa tafiyar nan xanyiba"

Lala Dee baruwana kace xaka sa faruq dan karamin hauka"

"to yaxanyi nariga nafadamasa ina tafe amma xanyi kewar fadilaty "

Dariya kawai safiyya tayi yashiga shafa mai ya Shirya cikin brwon din shadda safiyya ta shirya fadila cikin wasu riga da siket pink tasamata safa tagyarata tsaf kuka tafara Assadiq ne yadubi safiyya yace


" sopy kular min daita mana"

"Dee rigar ce ta matseni narasa yadda xanyi inbata tasha"


"cab ashe kuwa xan yaga rigar"

"pls xugemin zip din kaji"


Zuge mata yayi ya kuwa xuba mata ido tashiga shayar da fadila suka bashi shaawa can ya nisa yace


"Sweet sopy nima xansha"

Yafada yana kashemata ido ido taxaro tace

"Dee ka girma fa


dariya yayi yakarasa shryawa fadila ce tai ta kallon sa daukar ta yayi safiyya tai musu hoto aka gama yamikawa safiyya ita taki xuwa dariya sukasa yace

"Fadilaty binty ta gane papanta bari intafi da ita gidan momy daga nan xanje ingaida baffa tunda sai dare jirginmmu xai tashi "

" Dee pls in shrya mutafi tare "


" Aa"

Fita yayi ya nufi gidansu yasamu momy tana cin danbun kaxar da safiyya ta ai kamata ya mikamata fadila ta karbeta suka gaisa duban dan nata tayi tace

"badai tafiyar ta zoba "


" aa momy sai dare xan je gidansu Muwadda ne "


" kai amma ka kyauta Assadiq Allah yaima albarka "


" Ameen momy na, dady fa "?


" ya fita wani bako yayi daga sokoto suka xo shi da dansa babban dan ixala ne a can a unguwa uku suka sauka "


" ok ko malam mudassir ne "


" tabbas shine "


" momy bari inje sai na dawo"


"to, Assadiq Allah ya kiyaye"


Yana mike wa fadila ta fara kuka juyawa yayi yace


"Haba Fadilaty binty momy kuma xakiwa kiwa"

"tafara wayo ai", cewar momy jalila ce ta dauketa akai Saa ta hakura yasa kai yafita gidan su safiyya yafara xuwa ya gaida iyayenta yace najiba tazo ta taya safiyya kwana xaiyi tafiya ummi tace

"najiba bata nan Assadiq taje rano gidan kanwar baffansu "

Yaamsa da to yabata kudi takarba da kyar yaimata Sallama yatafi gidan ya hannatu ya nufa taita murna su nabil suka kankameshi yana tambayarsa



uncle A ina Mata ta"?


" tana nan kalau nabil "


Assadiq ashe dubai xaka yau she ne tafiyar"


"yaya anjima ne "


" xaka hado lefan amma "


" aa gsky "

" ok Allah ya kiyaye agaida faruq "


Xaiji"


Ta bada kilishi da yawa akaimasa yaxaro kudi yabata taimasa godiya sukai Sallama yatafi

Be xame ko inaba sai gidan su Muwadda yai Sallama yashiga tana kwance a cinyar mamanta cikin shiga ta kananun kaya da sauri ta tashi ya gaida mamanta murna fal ransu tasa aka kawo masa lemo ta tashi tabasu guri suka gaisa suka dan taba hira yafada mata tafiya xaiyi tace


"kasiyo min kit din kayan kwalliya kaji sweery "


Hmmm ok"


Ya tashi xai tafi mama tafito sukai Sallama ya xaro kudi yabata a bakin gate yahadu da abban Muwadda suka gaisa yaja motarsa yatafi


Yana xuwa gida wanka yayi yaci abinci yafara shiri fadila kmr tasan tafiya xai yi ta makale masa achida yai wa waya yaxo ya kaishi airport baajimaba yakaraso nan fa suka kule adaki shi da safiyya suka rungume juna safiyya sai kuka yadagota yana sharemata hawaye yabar mata kudi masu yawa yace su farhana xasu xo sutayata kwana gabanta ne yafadi suka fito xuwa gurin mota achida ya karbi fadila suka gaisa da safiyya ya mikawa Assadiq ita yadaga ta sama Fadilaty binty papa xai yi missing dinki yabawa safiyya ita suka ja motarsu suka tafi yana daga musu hannun safiyya tana ta share hawaye haka fadila kuka


Gidansa ya tsaya yaimusu Sallama yaiwa dady ma yarabawa kannansa kudi da masu aikin momy yafadawa su farhana suje su dinga taya safiyya kwana sunajin haka suka fara murna xasu sami damar musgunawa safiyya



Karfe tara jirginsu Assadiq ya tashi ✈












*NASEEBA GAWO*✍🏻
. [6:42Am, 2017]


*®💦💦💦TALENTED WRITTERS FORUM*💦💦💦

*💦T F*💦





*KANNAN MIJINA*
👩‍👩‍👧



*NA*


*NASEEBA I UBA*💐




*Allahu akbar Allahu akbar Allahu akbar walilahil hamd Allah yakabamu alkhairin da yake cikin wannan gwala gwalan ranaku ameen*👏🏻👏🏻






*TALENTED WRITTERS hadin kanmmu shine alfaharinmmu*🤝🤝


*Ina rokon Allah yakara miki lpy kawata faeex talented kina raina naseeba talented na miki sannu Allah yasa kaffarane ameen*😘





*62*






~~~Safiyya na shiga daki ta kira umminta bayan sungaisa take tambayarta fadila tace


lpy kalau ummi, ummi Assadiq ne yaitafiya shine kannan sa xasu sutayani kwana wlh ummi fargaba nake nasan baxamu wanye lpy ba "


" eh daxu yaxo safiyya da cewa yayi najiba tazo ta kwana to ta tafi rano gidan innarku amma abinda nakeso da ke shine kiyi kokarin kyauta ta musu kinji ki dauke kai kiyi ta hakuri safiyya wataran sai labari "


" to, ummina nagode agaida baffa da ya amina xanxo cikin satin nan ma"


"xasuji keda mijinki baya gari ina xaki fita"

"kai ummi ai xanmasa waya ai "

" To Allah yakawoki "

" Ameen ummina "


Sukai Sallama ta kashe wayar waya taiwa jalila sutaho dan Allah hakuri tabata cewar bata da lpy amma gasu farhana nan tai mata sannu baajimaba suka xo cikin faraa safiyya ta taresu sai cika suke suna batsewa farhana ce tamika hannu xata dau fadila tasa kuka dunguremata kai tayi tace

"au ni xakiyiwa kiwa lalle to bari kiji yarinya ni uwar ki ce dolen ki kuma"

"aa to fadamata ya farhana kinsan fa su yaya sunfison dangin uwarsu alhalin dangin uba sune suka fi karfi "

Cewar afifa kenan safiyya dai yarta ta dauke xatai daki farhana tadubeta tace

" Aa aunty safiyya yunwa fa mukeji"


"Gsky bani da abinci sai dai danbun kaxa da yagot inxakuci in kawo muku "


" to muda mukejin yunwa ina mu ina cin wani danbun kaxa da yagot kayan kwadayi, gsky kimana girki "


" yi hakuri mana farhana ai kitchen din ba bakonku bane xaku iya shiga ku dafa "


Tai tafiyarta daki tafara shirin bacci tashi sukayi suka dora indomie sukai kaca kaca da kitchen din har da fasamata cups suka juyo ta parlo suka dawo suka ci kadan suka barta anan dakin suka shiga sukai wanka lokacin safiyya tayi bacci rungume da fadila afifa ce tace


"ya farhana a ina xamu kwanta mu dan wannan gadon yaimana kadan "


" au afifa xamu kwana akasa ne ai wlh tashinta xamuyi "

Aikuwa tashinta sukayi wai dole sai tabar musu gadon ido kawai ta xuba musu ta dau yarta ta fita ba kunya suka kwanta dakin Assadiq takoma ta kwanta kewar mijinta tadawo mata karatun kuraani ta kunna take bacci ya dauketa

Bata farka ba sai asuba ta tashi tai salla tayi axkhar fadila ce tafarka goyata tayi tanufi kitchen kaca kaca taga sun mata da shi tarasama taina xata fara cikin kankanin lokaci ta gyara komai ta dora musu break daya da kwai tayi sai farfesun kifi ta dafa tea ta kammala tajera a dining tafito ta gyara parlon takunna turaran wuta dakin Assadiq takoma tagyara tai wanka taiwa fadila taje dakinta tadebo musu kaya har lokacin bacci sukeyi ta tashesu sukai mata banza tafiyarta tayi ta shirya tsaf tashirya fadila ruwan tea tafito tasha takoma daki suka koma bacci su afifa basu farkaba sai wajen 10 wanka sukayi sukai salla wardrobe din safiyya suka bude suka dau sababbin atamfofinta suka sa sukai kwalliya parlo suka fito xama sukayi sukai break fast suka barmata doya guda uku miyar kuwa du suka shanye tashi sukayi suka kunna kallo safiyya ce tafito dan yin break mexata gani kayanta ne a jikin su sababbi ma sharewa tayi tadubesu tace


"kuntashi lpy "

" mungode Allah, ina sarkin kiwa "

" bacci take dafatan kun karya "

" ummm mun karya "


Karasawa tayi da xummar karya wa ba komai sai ragowa haushi ne yakamata tace


" ya baku cinyeba "


" munkoshi ne "


Kwanikan ta kwashe takai kitchen kunun gyada tadama tasha haka suka kadai jikinsu suka tafi



Abangaran Assadiq kuwa yasauka a dubai faruq ne yaxo daukar Assadiq shi da abokinsa fahad yana ganin Assadiq ya rungume shi yana murna tambayar sa yayi

" yaya Assadiq ina yata fadila "


" lafiyar ta kalau faruq, duk suna gaidaka"


Fahad ya gaida Assadiq suka rankaya suka tafi hotel din dasukai masa buking suna isa faruq ya karbi wayar Assadiq yafara ganin hotunan fadila yaga takara girma tun daga ranar faruq ya tattaro kayan sa daga school Yadawo gurin Assadiq da xama

Assadiq ya kira safiyya yafadamata yasauka cewa yayi takarawa fadila wayar magana yafara yimata


"Hello Fadilaty binty ya kike ya kewar papa haka dai yai taimata magana karshe sukai Sallama

Haka dai safiyya tai tafama da su farhana


Yau shiryawa tayi ta tafi gidan su Assadiq kwai tasiya takai musu tasaiwa dady turare masu tsada dady yai farin ciki sosai da ganinsu momy kuwa ba yabo ba fallasa su farhana ne suka bata kayan dasuka sa nata tace su barshi tabar musu can xuwa anjima ya hannatu ma tazo gidan gwanin shaawa momy tarasa inda xata sa jikokinta ya hannatu takarbi fadila ta rungume ta nabil yanata murna yaga matarsa nan suka yini da yamma tai musu Sallama takoma gida ta aikowa dasu nabil kayan wasa nan su momy suka fara tattaunawa kan bikin Muwadda



Yau satin Assadiq biyu a dubai tun safe safiyya take shirin tarbar sa tanata girki girke Assadiq kuwa da kyar faruq yabar shi suka rabu cikin kewar juna yace da yagama karatunsa nan da shekara daya xai taho



Safiyya ta gyara ko ina tayi kunshi da kitso ta gyarawa fadila kai da ribons masu kyau kitchen ta koma tana xuwa taga farhana ta saukemata girki ta dora nata girkin wai danbu xata yi gashi jirgin su Assadiq ya sauka.












*NASEEBA GAWO*✍🏻
[6:26Am,2017]


*®💦💦💦TALENTED WRITTERS FORUM*💦💦💦

*💦T F*💦






*KANNAN MIJINA*
👩‍👩‍👧




*NA*

*NASEEBA I UBA*💐





*Allahu akbar Allahu akbar Allahu akbar walilahil hamd*



*TALENTED WRITTERS hadin kanmmu shine alfaharinmmu*🤝🤝



*wannan shafin nakine kanwata umyma inai miki fafan alkhairi Allah yakaiku lpy yabaku arfa mai sauki baxan iya misilta irin kewar dazanyi ba sai dai fatan Allah yabani juriya*😰💕

*Hajiya 2 bee*🕋





*63*





~~~cikin bacin rai tadubeta tace

"farhana meye haka xaki saukemin girki bayan gas dinna ba daya bane"?

"to ai gani nayi daya barin ba ya ci sosai ni kuma sauri nake baki xanyi "


Wani baxan kallo safiyya ta watsa mata ta sauke ta maida nata girkin ta dora mata a daya barin rashin kunya tafara yimata tai mata banza karshe ko danbun bata kula ba tai tafiyar ta safiyya kuwa ta kammala aikin ta tsaf ta jera a dining takarasa mata danbun ta juye a kula taiwa jalila waya ta turo mata Saa data xo tabata takai mata.


Karfe 3:00 achida Yadawo Assadiq gida cikin sauri ya shiga parlon yana tozali da safiyya ya ware hannusa cikin farin ciki tafada jikinsa ya rungume ta yana shakar kamshin turaranta cikin kewar juna yace

"Sweet sopy ina Fadilaty binty "


" ta gaji da jiran papa tayi bacci"


Sakinta yayi ya nufi dakin tana cikin gadonta tana bacci daukanta yayi ya rungumeta cikin farin ciki ya kira sunnanta


"Fadilaty binty wake up ur papa was return"


Mika yaimata ai kuwa ta bude idonta ta kuramasa ido kuwa sai kuma tai dariya mai da dubansa yayi ga safiyya yace


"sopy mekike bawa Fadilaty ta girma ga wayo "


" Dee ba komai, amma ina ganin ankusa fara bata abinci"

"banyarda ba abata nono kawai "


" Dee wlh yanxu baya isarta "

" shike nan sopy "

Sai yanxu ya tuna yabar abokinsa a waje fita yayi da fadila a hannun sa acikin mota yasame shi yana ta danna wayarsa ya dubeshi yace


" afuwan abokina nabarka kasan in ina gaban sopy manta komai nake"


"Gskyr magana abokina aure xanyi saboda nima inhuta inhade jikina guri daya"

Ya karashe xancan yana karbar fadila a hannun Assadiq

Dariya Assadiq yai taimasa sai da yayi mai isarsa sannan yace


"abokina kaji maxa waya fadama xaman goranci abu ne mai dadi"


"chairman mubar maganar wasa pls kabani afifa in aura "


" Dagaske kake achida nasan sharrin ka fa "

" I am serious chairman "

" ok xamuyi maganar da momy, yanxu dai taso mushiga ciki kaci abinci "

" wlh kmr kasan yunwa ce fal cikina dama hajiya bata nan"

"to gauro, bude min but inkwashe tsarabar mata ta data binty"


"chairman kenan nima ankusa xama baba"

Yafada yana kokarin fita daga motar taimaka masa yayi suka shigar da wasu akwatuna musu kyau har guda shida sai wasu guda biyu daban

Safiyya ce tafito sanye da mayafi suka gaisa da achida ta zuba musu abinci fadila ta karba ta koma daki nan suka fara cin abinci dukkansu sunji dadin abincin achida kuwa sai zuba santi yake suka kammala ya mike dan tafiya turaruruka Assadiq yabashi yaiwa safiyya Sallama yatafi ciki Assadiq ya koma safiyya xata hada masa Ruwan wanka kenan yajata jikinsa dubansa tayi tace

"Dee wanka fa?


"Bashi xanfara ba sopy ke nake bukata baki san daurewa kawai nake ba"

Kunya yabata ta sinne kanta a kirjinsa rada yaimata a kunne tasa dariya ta shige daki da gudu binta yayi a ciki ya cimmata ya kankameta a gado suka zube yashiga sarrafa ta cikin kwarewa

_nikam dakin sopy na koma na kula da Fadilaty_🤣



Sai da komai yalafa sukai wanka kmr yadda suka saba yashirya cikin kananun kaya yayi kyau kmr saurayi ya kwashi tsarabar su momy yafita bayan yabawa safiyya tata nan yabarta tanata duba kayan dana fadila akwati guda da tarkacan kayan wasa

Yana fita kai tsaye gidansu ya wuce abakin gate suka gaisa da malam sule mai gadi yaimasa sannu da xuwa ya wuce ciki a parlo yasami momy afifa na matsa mata kafa Sallama yai musu yasami guri ya xauna dadi ya cika momy ya gaida ta taamsa da kulawa ta tambayar tayi faruq

"lpy kalau momy yana gaida ki "

" ina amsawa, ina yar rigima tunda katafi sau daya aka kawota "

Lpy kalau take momy

Yafito da tsarabar su yabasu lesina ne musu kyau kyau da takalma sukai masa Godiya maida dubansa yayi ga momy yace


" momy daman abokina ne yakeson afifa da aure shine nace yajira infara tuntubar ki tukunna"

"waye kenan"?

"Abdullahi ne momy "

" to ai gata nan inta amince shikenan ai yana da kirki "

" Gsky momy banason sa ina da wanda nakeso wlh "


" afifa ki dubi kwayar idona kice bakya son abokina "

Yayi kyau afifa nagode "

"abar maganar Assadiq tunda bata sopy, anhada lefan Muwadda sati mai xuwa zaa kai befi asa sati hudu ba"

"Allah yakaimu momy "

" Ameen bari a dakko ma kayan kagani "

" aa basai naganiba momy, bari inje mugaisa da dady "


Mikewa yayi yanufi dakin dady yana kashin gide da kayan fruits agsbansa da Sallama yashiga yasami guri yazauna hade da tankwashe kafarsa ya gaida shi cikin girmamawa hannu ya mika masa kmr kullum ya noke yace


" sadauki andawo lpy ya kabaro faruqu "

" lpy kalau dady yana gaida ku "


Muna amsawa ina kabar matar tawa"

"bacci take shiyasa bamu taho tare ba "


" to madalla momyn ku tafada min cewar nan da sati biyu xaa kai lefan Muwadda ko "

" eh dady yanxu nima tafada min "

" to Allah yabada alkhairi sadauki kazama jarumi a gidanka kaji "

Ameen inshaallah dady, nagode"


Ya bashi turaruruka masu kyau da tsada yai masa Godiya Sallama yaimasa ya tashi yatafi




°°°°°°°°°°°°°°°



Yau tun safe aketa aikin girke girke a gidan su Assadiq saboda bakin da dady xaiyi malam mudassir ne xai kawo wa dady xiyara 12 dai dai suka iso da murna dady yataresu a sit room ya saukesu nan suka gaisa cikin girmamawa matashin dansa ya gaida dady momy tashigo suka gaisa su farhana ne suka dau kayan abincin suka tafi kai musu da Sallama suka shiga jalila ce tafara shiga sai afifa farhana ce karshe tunda tashiga matashin saurayin yake kallon ta suka tsuguna suka gaisa da malam mudassir ya amsa da sakin fuska dady ne ya dubesu yace


Baku gaisar da yayan ku ba "

Gaida shi sukayi suka hada ido da farhana take gabanta yafadi murmushi ya sakar mata suka tashi suka fita suna fita malam mudassir ya dubi dady yace


" alhj muhammad mexaihana abawa ibraheem auran daya daga cikin yanmata nan kaga dangantakar mu tadada kulluwa addua ibraheem ya ke aransa Allah yasa abashi ta ukun nan dady ne yadubi abokanansa yace


"amma naji dadi sosai ina ganin sai ahada shi da farhana "

" wacce ce farhana "?


" tabayan mai doguwar riga "

" to Alhmdulillah naji dadi sosai Allah yatabbatar da alkhairi

"Ameen "

Inshaallah kafin mutafi xaai komai agama"

Nan suka cigaba da tattaunawa karshe sukai masa Sallama suka tafi amma ibraheem yaso yakuma toxali da farhana.











*_readers meye raayinku game da wannan novel din na KANNAN MIJINA_*


*Ina sauraranku ta wannan number 07037732029*👈🏻












*NASEEBA GAWO*✍🏻
[6:04Am,2017]



*®💦💦💦TALENTED WRITTERS FORUM*💦💦💦

*💦T F*💦





*KANNAN MIJINA*
👩‍👩‍👧




*NA*

*NASEEBA I UBA*💐





*TALENTED💦 💦WRITTERS hadin kanmmu shine alfaharinmmu*🤝🤝





*Allahu akbar Allahu akbar Allahu akbar walilahil hamd*



*masoyana naji raayinku raayoyinku game da wannan novel din na KANNAN MIJINA nagode sosai kuma inshaallah xakujini da raayoyinku farin cikin ku shine nawa kune ni da bazarku nake rawa*🤝



*kuna raina kawayan kwarai*💙

*Nana Fiddausi umar*
*zainab maigalura*
*Najaatu gusau*
*Reeda boss*

*sirinmmu make up & novel group*

*Duk ina gaida ku kyauta*👌🏻






*64*





Abangaran su Muwadda shirin biki suke bana wasa ba yanxu haka ma zaune suka a parlo suna tsara yadda bikin xai kasance Muwadda ce ta dubi abbanta tace

"abbana amma dani xaaje siyayyar kayan ko"?

"Muwadda da alhj rufai zanbawa sautu tunda yana can kasar dama"


"To abba pls kacanja min motata kaji "

" Haba Muwadda me xai hanani canja miki mota ni de fatana ki xauna lpy kinji kar inji kar ingani "


" to abbana inshaallah "

Mai da dubansa yayi ga hjy aisha yace

" hjy yaushe suka ce xasu kawo lefan "

" jibi ne alhj "

" to mashaallah sai ai min list din abinda xaa bukata in nadawo sai Abani "

Yafada yana kokarin fita taamsa da to tare da yaimasa adawo lpy mai da dubanta tayi ga diyar ta ta tace


" Muwadda ki bude kannanki da kyau kiji abinda xanfada miki "

" to mama na ina jiki "

" kin san munfar auranki da Assadiq "?

" Aa "

" Tohm bari kiji, sonake ke kishiga jikin hjy kareema sosai ki tarwatsa farin cikin ta ki kunsa mata bakin cikin da ta

Please Login or Register in order to submit comment