Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ne zayi abin azo agani, dan albashi ne fa "


Jalila dai bata tanka mata haka farhana wacce jikinta yafara sanyi sakamakon jibi zaa fara biki, gashi ibraheem ya hanata fita ko ina duk partyn da xatayi yace bazai zo kuma inde da maza zatayi to kar taje, gashi bata iya yimasa musu taci burin bakinta ga yadda yakasance



Muwadda ta dawo dakinta bayan kwanakin da tayi maman ta har gida taje taiwa momy rashin mutunci bayan taramawa yarta marin da Assadiq yai mata akan afifa momy tai ta kuka tai mamakin abinda kanwar tata taimata sai kace ba yayar taba



Tunda Muwadda ta dawo Assadiq be bi takantaba yau takarbi girki ta daure taimasa girki saboda wata bukata ta dakinsa tanufa yana kwance da fadila abayansa ta kwanta sunata dariya yana ganinta ya hade rai yamike yadau yarsa zai fita hannunsa takama yadago suka hada ido wani malalacin murmushi taimasa wanda yakasa gane manufarsa๐Ÿค”








*NASEEBA GAWO*โœ๐Ÿป
[5:33Am,2017]


*ยฎ๐Ÿ’ฆ๐Ÿ’ฆ๐Ÿ’ฆTALENTED WRITTERS FORUM*๐Ÿ’ฆ๐Ÿ’ฆ๐Ÿ’ฆ


*๐Ÿ’ฆT F*๐Ÿ’ฆ






*KANNAN MIJINA*
๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘ง



*NA*

*NASEEBA I UBA*๐Ÿ’




*Rabbana atina fidduniya hassanah wafil akhirati hassanah wakinna azabar nar*๐Ÿ‘๐Ÿป


๐Ÿ’ฆ
*TALENTED WRITTERS hadin kanmmu shine alfaharinmmu*๐Ÿค๐Ÿ’ฆ




๐Ÿ’™๐Ÿ’ฆ
*Ina gaisheku TALENTED WRITTERS gsky kunaji da naseeba nagode sosai da Dedicating din da kukai min Allah yabar LOVE gaba dai gaba dai ina biye da ku sisters muje xuwa*๐Ÿ’™๐Ÿ’ฆ




๐Ÿ‡
*Ina tayaki murnar fara sabon novel dinki kawata garkuwar fulani mai suna RUBUTACCN ALAMARI Allah yasa kinfara a saa, Assadiq din sopy yana gaida hamma umar kyauta ba da kudi ba*๐Ÿค๐Ÿ‡
๐Ÿ˜ƒ๐Ÿ˜ƒ
๐Ÿ˜‚










*81*






~~~wani banzan kallo Assadiq ya watsawa muwadda ba shiri tasaki hannunsa amma bata bashi hanya ba fadila ce tadubi Assadiq tace


"papa, me aunty na tai maka? dan Allah kayi hakuri tadena, kaga fa tana bani Sweet kuma ita bata dukana kmr yadda su aunty farhana suke dukana "


Shiru yayi yaxubawa dan karamin bakinta ido irin na safiyya can yanisa yace


" shikenan Fadilaty na hakura komai ya wuce "


Ran muwadda ne yadan sosu amma sai ta dake , tashafi cikin jikinta da yafara fitowa tace

" nagode sweery, kazo muje ga abinci can nahada ma, baby fadila nagode kinji "


Tafada tana kokarin jan hannun fadila, Assadiq ne ya janyeta yace

" aa, kibar abincin ki nagode, munkoshi "

Narai narai tayi da ido kmr zatayi kuka, tausayi tabashi yabi bayan ta suka wuce part din ta ta gyara parlon tsaf, guri yasamu ya xauna dubansa tayi tace


" sweery ka karaso dining din mana "

" aa ki kawo min nan, annabin mu betaba cin abinci a kan abu madaukaki ba, haka dan bancika son hawa dining ba "

Gajiya tayi dan batason motsa jikinta, haka ta daure ta kwaso kayan abincin tare da taimakon fadila, ta zuba masa jollofe din taliya tayi sai coslow da soyayyar kaza taliyar tafara narkewa dan tadahu luguf kazar kuwa tauri tun a ido ya raina abincin, wani plate din ta dakko zata zubawa fadila, hannu Assadiq yadaga mata yadora da


"No, kibarshi zumuci tare, ya isa haka "

" ok, tafada takoma gefansa ta zauna sai faman wash takeyi ahankali ya furta

"sannu "

Yai bissimillah yafara cin abincin lomar farko da kyar ya hadiyeta yadiba yabawa fadila dubansa tayi tace

" papa "

" naam binty "

Gsky nakoshi abincin ba irin na mamma na bane, nide madara zansha"

Hmmm, muwadda kinji fa abinda yarki tace, kidamo mata madara, da Allah "


" Bani da madara, takare "


" amma baki fadanba"

"to ina naganka, amma dai shikenan, yanzu nafada maka "

Shiru yayi yadan tsakuri abincin yaci, tashi yayi zai kai fadila, dubansa muwadda tayi tace


" sweery, pls ina son magana da kai kaji "

Ok, kijirani, inje masallaci indawo , nazaci tare zamu kwana, karewa"


Goya fadila yayi ya fita zuwa part din safiyya tana kitchen tagama tuwon alkama da miyar kubewa danya tun da yadoso part din kamshi yadaki hancinsa, kitchen din yanufa tana sanye da doguwar riga ta mterial dinkin buba, a kofar kitchen din yatsaya fadila ce tace


"mamman fadilan Dee, zumunci abinci "

Da sauri safiyya ta juyo ta dubi Assadiq tace


" Dee, kanajin yarinyar nan ko,?

"Hmm, inajinta sopy, ai batai laifi ba ko?

"au tambayata kake, to ai kafini sanin amsar tambayar ka "


Ciki yakarasa bayan ya sauke fadila yadora Kansa a gadon bayanta yana shakar kamshin turaran ta ahankali ya furta


" matar Assadiq *QAMSHIN*ki daban yake, wai wane turare ne wannan "?

" Dee, dafarko dai kadagani, kaga fa hankalin yarka yana kanmmu "

" naki sopy, inbanji dumin jikinki ba fada min nawa zanji "


Ai kuwa fadila ta zuba musu ido can ta tafa hannunta tace

" la, mamma na zata goya papa na, cab wlh mamma na tanada karfi "

Sauri Assadiq yayi yajanye jikinsa daga na safiyya yanata dariya can yace

" sopyn Assadiq, tuwo kike mana, lallai zamuci dadi yau "

" aa, Dee tuwo na dady ne, sai nawa guda biyu "


" "cab kice yau akwai rikici ", yafada yana dakko kofiin fadila na madara yahada mata mika mata yayi ta karba tana sha ta mika masa tace

" karba, gaskiya bana sha, sugar bejiba "


" Kai Fadilaty, meyasa kike son wahalar dani ne, kawo inkara miki sugar "

" Dee, wlh kai kake shagwaba yarinyar nan shiyasa take ji har yanzu bata girma ba "


" to girman tayi sopy, ki kyalemu ko Fadilaty "

" eh mana papa na ni kadai "

" Ok yayi kyau fadila,
Dee ko zaka mikawa dady tuwon nan "


" me zaihana sopy, ai ba wani abu dan mata ta aiki mijinta "

" lala, rufa min asiri Dee nikam ba aikenka nayi ba "


" papa na zanbika gidan momy gurin aunty jalila "


" ok Fadilaty mutafi "

Kwandon kayan abincin ya dauka suka fita safiyya tayi tai fadila ta ajiye kofin madarar ta taki suna zuwa suka hadu da dady da faruq zasu masallaci jalila yaiwa magana tafito ta karbi abincin ta shiga da shi ciki da fadila yai alwala yabisu masallacin


Farhana naganin fadila ta kira ta

"ke dan uwarki zo nan, wai ke yar madara ko, kyaci ubanki randa kika wayi gari ba madarar "


" Hmm ai su rainon madara sukai mata, ni kuwa yayana cab bansan rainon ma me zanyi musu ba wlh ko da yake muda zamu tafi england ai sai Allah "

Cewar afifa tafada tana fari da ido jalila ce
tadubesu tace gaskiya bakwa kyautawa wlh yanxu me yakawo wanga zancan haka yakamata ace kun kaunaci yarinyar nan ko dan kasancewar ta jinin mu ko"


"aa aunty jalila yi hakuri mana, kibar mu muyi abinda muke so "


" nabarku afifa, to amma kusani zakuga abinda bakwaso anan gaba, ajuri zuwa rafi wata ran tulun zai fashe "


Karar wayar ta ne yakatseta tana dubawa taga *Dr almusty*murmushi tayi tasami guri ta zauna taja fadila jikinta tadaga kiran


" Hello, *Doktar*"

"naam habibty, kina lpy "

" Lpy kalau, ya aiki ya ummina "?

" aiki gashina nan yaimin katanga da mata ta ummi kuma tana kano "

" Hmmm, *doktar*kenan, yaushe zaka baro abujan?

"ummm, wajen jibi zandawo dan namatsu inyi tozali da kyak kyawar fuskar mata ta "
" shikenan Allah yakawo min kai lpy, ga fadila ku gaisa "

" Hello uncle *Dr*, ina yini, ina umminku "?


" Lpy kalau aku, ina surutu?

"nadena sai dan kadan fa nakeyi yanzu "

" to yayi kyau ki ce ina gaida maman ki "

" to uncle zan fadamata, ina allura, kazo kaiwa su aunty farhana tunda basa sona "

" shiiii, fadila kar ki kuma cewa wani bayason ki kinji ko "


" uncle *Dr*"

"naam fadila "

" dukana fa sukeyi "

Zasu dena kinji ko, kibawa aunty wayar"


Jalila ce ta karbi wayar suka taba hira karshe sukai Sallama ta kashe wayar su farhana kuwa tunda tafara wayar suka bar mata wajen dan sun raina auran jalila gani sukeyi ba wani abu zata tsinta ba


Dady ne ya shigo da zaratan yayan sa abayansa lokacin momy tana zauna a kujera fadila na kwance a cinyar ta, Assadiq yaji dadin hakan aransa yake tunanin momy tafara kaunar fadilan sa karasawa sukai suka zauna fadila ta taso ta rungume faruq shima rungume ta yayi yana fadin


"fine girl, kwana 2, ina mamma "


" Lpy kalau uncle, ga tuwo can na kawo maka ai zaka ci "

" bana cin tuwo fine girl amma zanci naki "

" Kai, uncle bani ce nayi ba fa, mamma na ce tayi "


Assadiq ne yadubesu yace Fadilaty tuwo fa na dady ne da zakiyiwa uncle kyautar sa"


"Rabu daita sadauki, ai andena bata rancan kudina "


Sakin faruq tayi ta tafi gurin da dady yake zaune ta rike kunnuwanta tace


" kayi hakuri dady tuwon ka ne "


Gaba daya suka sa dariya Assadiq ne yagaida momy, jalila ta dakko plate ta zuba wa dady tuwon safiyya suma suka zuba sai sa mata albarka yake, haushi ne yakama momy aranta take fadin ina ma Muwadda ce tayo girkin nan



Assadiq be koma gida ba sai wajen 10 suna ta tsara bikin farhana, lokacin safiyya har tafara bacci suka shiga
Fadila ce tafada jikinta atsorace ta farka, tsawa ta daka mata

"wai dan wace irin yarinya ce ke fadila, bakya abu da nutsuwa ko, wlh jikinki, zai fara gaya miki"

"mamma na kiyi hakuri nadena "

" ai banaso ki dena kici gaba, Dee sannu da xuwa, ya su momy"


"yauwa sopy, lpy kalau, amma naji kamar kina cin alwashin dokar min ya ko to kar ki fara"


" Haba Dee yanzu baka ga me tayi min ba "

" nade fada miki "


Hannun fadila yaja suka nufi bandaki yai mata wanka ya sa mata kayan bacci masu kyau ya kaita kan gado ya kwantar da ita tare da yimata addua safiyya ce tashigo dakin ko kallansa batayi ba tasa kayan bacci ta kwanta sai da fadila tai bacci sannan Yadawo gefan safiyya ya shiga balle mata maballin rigar ta ahankali yashafi kirjinta ya ce


"Sweet sopy kidena kwana da bra zata hanaki bacci mai dadi"

"sai gashi kuma ni inaso, ya kenan "


" to banyarda ba sopy "

"yafada yana kokarin kai bakinsa ga kirjinta ture shi tayi tare da rufe kirjinta ahankali yace


" kar ki kuma rufe min ai banaki bane ke kadai, kuma ai mallaki na ne, sai da yagama jagwal gwaleta sannan yagyra mata rigar ta

Yasakar mata kiss sannan yaja musu kofa part dinsa yanufa yai wanka sannan yanufi part din Muwadda tana zaune da wata yar bingilar riga ajikinta wacce ta fito da cikinta tana ta shan agwalima gefanta yazauna ta kwanto da kanta aciyarsa tace


"sweery kadade, meyasa "?


" muna tare da su dady ne "

Yafada yana shafar cikin jikinta, dan dago da kanta tayi tace


" sweery yakamata bani kudi infara yo siyayyar baby "

" ok, yanzu dai zanbaku kudin hidimar biki "

Shiru taimasa saboda bikin baya gabanta



Biki yazo anata hidima haisam yazo ya kawo wa afifa kaya a akwati da kudi saboda hidimar bikin farhana


Dr almustapha ma yazo yaiwa jalila kyautar kudi yabawa momy ma gudun mawa

Farhana ce take ta faman shirin zuwa kunshi ita da kawayanta yan gayu kuma yan karya kiran ibraheem ya shigo wayar ta tana dagawa kawai tasaki kuka tare dayin cilli da wayar.





*NASEEBA GAWO*โœ๐Ÿป
[3:46pm,2017]



*ยฎ๐Ÿ’ฆ๐Ÿ’ฆ๐Ÿ’ฆTALENTED WRITTERS FORUM*๐Ÿ’ฆ๐Ÿ’ฆ๐Ÿ’ฆ



*๐Ÿ’ฆT F*๐Ÿ’ฆ



*KANNAN MIJINA*
๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘ง




*NA*

*NASEEBA I UBA*๐Ÿ’




*mashaallahu la kuwata illa billahil azim*๐Ÿ‘๐Ÿป



๐Ÿ’ฆ*TALENTED WRITTERS hadin kanmmu shine alfaharinmmu*๐Ÿค๐Ÿ’ฆ





๐Ÿ’™
*wannan shafin naka ne yaron kirki hakika yau rana ce ta* *musamman a gareni da kai kanka ummin ka tana tayaka murnar cika shekara 5 dakayi* *ayau 16 september ubangiji Allah ya albarkaci rayuwar ka yasa kazama abin alfahari ga alummar* *musulmi Allah yasa kaza memin hasken idaniya ta Ameen Allah sarki Assadiq kenan tun kana karami kakewa ummin ka waka*๐Ÿ’™


*_sannu gimbiyar mata ummi sarauniyar mata_*๐Ÿ’ƒ๐Ÿป


๐ŸŽˆ
*HAPPY BIRTHDAY Assadiq muazu yusif๐ŸŽˆ*๐ŸŽ‚๐ŸŽ‚
๐ŸŽ‚







*83*




~~~Ahankali farhana take bin yanmatan nan da ido su dinmma ita suke kallo tare da karewa dakinta kallo bayansu kuma wasu samari ne guda biyu dauke da akwatina shigowa sukai suka zube akwatin a parlon


Gaisheta sukayi taamsa a wulakance basu kulaba daya a cikin suce ta dubi farhana tace,

"amaryar ya khalil bakya magana ne, ai de kya bamu dama mu gabatar da kanmmu ko duk da de da sannu zamu saba tunda zamu zauna a muhalli daya "

Wata farar yarinya ce tafada, shiru farhana tai musu can tanisa tace

" bandamu da sanin ko kudin suwaye ba,amma badamuwa ina sauraran ku "

Gaba dayansu mamaki kalamanta yabasu sukai mata shiru can yarinyar da tafara magana ta kuma yin Caraf tace,

" amaryar mu kenan, to dafari de, ni suna na fareeda, wannan kuma
fatisa ga faixa ga bilkisu sai kanwar hajiyar mu zainab masari"

"ok sannun ku, ko ya kuke?

Wacce aka kira da masari ce tabata amsa

"kamar yadda kike, haka muke"


Ibraheem ne yai Sallama ya shigo suka amsa kannan nasa ne suka shiga yi masa sannu da xuwa ya amsa da kulawa, farhana kam ko kallon sa batai ba yasami gefenta ya zauna ya dubeta da kulawa yace

"farhana ya baki kawo musu komai ba?

"ni bansan kitchen din ba "


" Hmm ko, ok zan nuna miki kafin nan zan gabatar miki da yan uwa na, nan ya kuma yimata bayani game da su ya dora da


"farhana, zamu zauna tare da fatisa da zainab anan bangaran na mu saboda haka ku zauna lpy, ki dauke su kamar kannan ki banasan ki dauke su amatsayin *kannan mijinki*"


Wani kallo tai masa, amma fargaba ce fal ranta, saboda yadda taga zagada zagadan yanmata nan ace tare zasu zauna, ahankali ta furta

"Allah ya bani ikon zama lpy "


" Ameen, ke bilkisu shigar musu da kayan su dakin su, ku kuma ku tashi kushiga kitchen ku dora mana girki "

Yana gama fada yaja matar sa sukai daki tashi sukayi suka shiga kitchen suka fara girki


Farhana kuwa, suna shiga daki tafara kuka, ita bazata iya zama da *kannan mijin ta*ba, tun ibraheem yana rarrashinta har yagaji ya fara yimata fada karshe yabar mata dakin



Sanda su fatisa suka kammala girkin su farhana tana daki suka ci suka koshi, ko takanta basu bi ba su bilkisu sukai tafiyar su

Ibraheem be shigo ba sai bayan sallar ishai lokacin su masari ne kawai a parlon sukai masa sannu da xuwa suka koma dakinsu zama yayi yana jiran farhana shiru bata fito ba gajiya yayi ya nufi dakin tana xaune ta idar da salla dubanta yayi yace

"farhana tashi muyi salla ko"

"ni bana salla "


" Hmmm baki san waye ibraheem ba farhana, to bari nadan baki kadan daga cikin halayena, bana son karya haka kazalika bana son raini, ya inzo in tatar da ke kina salla amma saboda wulakance kice ba kya salla "


" to naji ina salla, karabu dani bazan iya ba, fakat "



Sai da yaimata da gaske sannan ta tashi sukai salla rakaa biyu dafa kanta yayi yaimata addua sannan ya dakko ledojin da yashigo dasu guda biyu ya dau daya yafita da ita dakin su zainab ya nufa ya kwankwasa budewa sukayi ya mika musu ledar kazar tuna ni tashiga yi me ibraheem ya fita yi shigowar sa ce ta katse mata tuna nin data ke nan ya zauna suka ci kazar tambayarta yayi


"farhana kinci abinci amma?


"banciba "

" meyasa?

Shiru taimasa ahaka suka kammala cin kazar tashi tayi tashiga toilet tai wanka tana fitowa shima yashiga yayi, kan yafito ta haye gado ta kwanta tunanin gida tafara sai kuma kuka ahaka ya hau gadon ya jata jikinsa, da kyar farhana ta yarda da ibraheem komai ya kwana tasha azaba da kyar tasamu bacci


Washegari da asuba ibraheem ya tasheta taimaka mata yayi tayi wanka har ta koma ta kwanta ya dubeta yace


"farhana be kamata ki kwanta ba, kitashi ki shiga kitchen ki hada mana break fast, kinga su fatisa zasu makaranta "


" a gaskiya ni bazan iya ba.....



"dakata farhana ki daure ki tashi bana son yarannan su makara "



Tashi tayi tafita zuwa kitchen tana zuwa taga wasu cups dinta afashe ga Kwanikan da sukai girki duk abace haka ta daure ta dafa tea ta soya dankali ta kammala takai parlon ta zubawa su zainab nasu ta barshi a kitchen ta koma daki ta kwanta


Karfe 8 su fatisa suka fito daga dakinsu a lokacin ibraheem da farhana suna parlon suna break, karasawa sukayi suka gaisa da yayan su, fatisa ce kawai tagaida farhana ta amsa a sanyaye zainab ce ta dubeta tace


"amarya break dinmmu fa?


"yana kitchen mana "


Tashi tayi tashiga kitchen ta dakko musu flaks din tea da dankali ta dawo fatisa ce ta bude dankali ta gani mai da dubanta tayi ga zainab tace


"yaya zainab kinmanta bana cin dankali"

"to ya zakiyi amarya shi tayi "

Ibraheem ne ya dubesu yace


Wai me kuke fada ne?


" yaya khalil bana cin dankali, nafison indomie "



Maida dubansa yayi ga farhana yace


" farhana daure ki dafa mata indomie "


Dagowa tayi ta zuba masa ido tarasa ma me xatace ce,

Bayadda ta iya haka ta tashi ta dafa mata indomie tana yi tana hawaye


Bayan ta kammala ta shirya cikin wata atamfa green da ja tayi kyau ibraheem ne yadubeta


" kisa hijjabinki kizo muje ki gaida su hajiya

Kallonsa tayi tana jinjina sa hijjab, haka ta dakko hijjab din tasa suka nufi bangaran su hajiyar ibraheem kannan sa ne maza zaune a kujera nan farhana tagaida hajiya taamsa da kulawa nan tashiga yimata nasiha

Kannan sa ne suka dubi farhana suka ce



"amarya kwanan abincin mmu yana gurinki "


" dariya ibraheem yayi yace

"jafar kenan, to ai badamuwa ko farhana "

Shiru farhana tayi tadan zauna jim sannan ta koma part dinta tana shiga taga parlon kaca kaca kamshi tajiyo a kitchen
Ahankali ta shiga kitchen din bilkisu tagani tana soya doya shiru taimata tanufi dakinta tana shiga tafashe da kuka wayar ta ta dauka tashiga neman layin momy







*NASEEBA GAWO*โœ๐Ÿป
[5:56Am, 2017]


*ยฎ๐Ÿ’ฆ๐Ÿ’ฆ๐Ÿ’ฆTALENTED WRITTERS FORUM*๐Ÿ’ฆ๐Ÿ’ฆ๐Ÿ’ฆ

*๐Ÿ’ฆT F*๐Ÿ’ฆ






*KANNAN MIJINA*
ํ ฝํฑฉโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘ง




*NA*

*NASEEBA I UBA ๐Ÿ’







*Allahumma ya mukallabil kulubi sabbit kalbi ala dinika AMEEN*๐Ÿ‘๐Ÿป




๐Ÿ’ฆ
*TALENTED WRITTERS hadin kanmmu shine alfaharinmmu*๐Ÿ’ฆ






๐Ÿ’™
*wannan shafin nakine sumayya sumy Allah yaraya mana nana khadija ya albarkaci rayuwar ta ameen*๐Ÿ’™





๐Ÿ’˜
*sakon gaisuwa gareku mutanan nijar maradi zindar da mali sakon ku ya iskeni dafatan duk kuna lpy ina gaisheku da babbar murya Allah yabar kauna AMEEN*๐Ÿ’˜








*85*





~~~Mamaki ne yakama safiyya, tare da tambayar kanta me zaisa farhana ta kira ta tana kuka cikin kidima tafara tambayarta


Hello, farhana lpy kike kuka "?


" aunty safiyya, wlh nagaji, bazan iya ba *kannan mijina* basu da tausayi bare afuwa kullum agurina suke tarewa banda guda biyu da muke tare da su ga maza kullum ni ke basu abinci, wlh nagaji momy tace zaa kawo min mai aiki ibraheem ya ce be yardda ba "


" aa subahanallah, to abinda nake so da ke farhana, kayi hakuri ita rayuwa da kike ganin ta hakuri ake musamman rayuwar aure kinji ko, yanzu me kike so ayi "


" aunty so nake ki fadawa ya Assadiq ko zaiyiwa ibraheem magana akawo mai aikin dan Allah "


" to shi kenan farhana zan fada masa inshaallah, amma fa kikara hakuri "


" tohm shikenan, ina fadila bata mu gaisa "


Safiyya tana mikawa fadila wayar ta gudu bayan yaya rukayya ta buya ita bazata gaisa da ita ba sai da safiyya tai da gaske sannan ta karbi wayar, farhana nata magana tai mata shiru hakura tayi ta kashe wayar


Safiyya ce ta mai da dubanta ga yan uwanta tabasu labarin yadda sukayi da farhana, najiba ce tai Caraf tace


"Hmm dadina da gobe saurin zuwa, har anyi daren gari kuma ya waye, kijifa ummi wai yaya safiyya take bawa labarin *kannan mijinta* wlh bata ma da kunya "


" aa to ba rayuwar kenan ba, najiba shiyasa kayi da kyau ko dan gaba "

Cewar ummi, amina ce ta dora da

" ni ba abinda yafi bani haushi ma wai abata fadila su gaisa, yarinyar da ta dau karan tsana ta dora mawa "


" to ni de zanyi iya bakin kokari na wajen ganin ankai mata mai aikin "


" Allah ya nufe ki safy "

Cewar yayar su rukayya, sallsmar yayan su ce ta katse musu hirar nan suka gaisa da shi suka zauna hira gwanin shaawa ummin su dadi yakamata ganin yaran nata cikin walwala da nishadi sai dare Assadiq yazo daukar safiyya ya shiga suka gaisa da
Su baffa yai musu
Alhr suka tafi tun a hanya fadila tabawa Assadiq labari


"papa, kasan me?

"aa Fadilaty sai kin fada "


" Dazu aunty farhana tai wa mamma na waya
Wai abani mugaisa
Nikuwa naki mata magana "



Safiyya ce ta daka mata tsawa ta dora da," wlh fadila akan
banzan surutun ki ko wataran sai na zane miki jikin ki "


" amm sopy, kullum kina ikirarin dokar min 'ya wlh kinji na rantse kar ki fara zaki ga mugun bacin rai na, kinji dai nafada miki "


" Haba dan Allah Dee.........


"yaisa bana son mai maita magana baya ya juya yakalli fadila da take tsaye abayan kujerar sa yace


"binty, kinajina "


" A, papa"


"Good, kar inkuma ji kince anbaki farhana awaya ku gaisa kin ki, itama auntyn ki ce kinji ko "


" To papa na, nadena bazan kuma "

" dakyau Fadilaty binty "


Safiyya kam shiru taimasa, ahaka suka karasa gida suna shiga ta balle murfin motar ta nufi part dinta, sai da yarufe kofa sannan ya budewa fadila kofar motar ta fito ya riko hannunta suka nufi part din Muwadda tana daki sai rushida a parlon tana cin abinci, da sauri tai masa sannu da zuwa ya
amsa a takaice saboda shi dai yarin
yar, bata kwanta masa ba, kai tsaye dakin Muwadda yanufa tana kwance agado tana waya da muktar tana ganinsa ta katse wayar dubansa tayi
Shi din ma ita yake kallo, kan gadon ya karasa ya dubeta yace


"ya jikin naki "?


" Da sauki sweery, sai ciwon baya kadan kadan haka "


" Allah yasawake, yaushe zaki koma asibiti "?

" sati na sama inkuma na haihu ne ma shikenan "


" haka muke fata Allah yaraba lpy "


" Ameen sweery, fine girl ba magana ko "


" to ai kema baki yiwa uncle dina magana ba shiyasa nima nai miki shiru "

" Kai fadila lamarin ki yana da ban mamaki, tashi muje ki kwanta,Muwadda sai da safe ki kular min da baby "


" ok sweery, baka da damuwa, sai da safe "


Yasa kai yafita dama so take yayi yafita tace gaba da wayar ta



Kai tsaye part din safiyya yanufa fitowar ta kenan daga wanka yashiga dauke kanta tayi sai da ta shirya sannan ta dubi fadila tace


" kiwuce muje inmiki wanka "


" kibar shi zanmata, kije ki dafa min lipton "


Bata amsaba ta fita shikuma yashiga toilet din yaiwa fadila wanka yasa mata kayan bacci wasu farar riga da gajeran wando ja yasa mata turare dubanta yayi yace

" saura kuma me?


Kunan sa takama tarada masa magana murmushi
Yayi ya ja hannunta suka fita kai tsaye kitchen suka nufa safiyya tana kallon su taci gaba da abinda take cup ya dauka ya dama mata madara yabata suka koma parlo tasha tana gama sha tai bacci safiyya ce takawo masa lipton din data dafa masa ta zuba masa a cup mika masa tayi yadauke Kansa dole tashiga bashi yana sha can ya dubeta yace



"matar Assadiq, fushi ko??

"Dee to ai kai dinne wlh kafiya sangarta yarinyar nan "



" to ai kece kullum baki da zance sai na

Please Login or Register in order to submit comment