Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

uwar gidan nasa "


" tohm shikenan bross, sai mun hadu a gida, shegiyar yarinya ta tayar da mutane a tsaye kawai wlh gurin safeena zanje fa "



Murmushi kawai assadiq yayi ya shiga mota suka tafi bayan anmusu kwatance, isar su gidan tayi dai dai da zuwan haisam wanda yayi baki ya fita hayyscinsa kunya ce takama shi yayan sa ne suka jiyo muryar sa suka fito aguje suna


" oyoyo abbba "

Rugume su yayi yana hawaye shukura ce tafito ita ma ganin su afifa ne yasata dada hade rai assadiq ne ya gaji da kallon su yayi gyaran murya yace


" ji mana malam, yanzu kai abinda kayi ka kyauta kenan, wace irin rayuwa ce wannan ga karya ga rashin gaskiya, to mu bazamu lamunta ba dan haka kabani takardar afifa tagama zama da kai


Arazane ya dago da kansa ya zubawa afifa ido take wata soyayyar ta ta kuma mamaye shi, Shiru yayi afifa kam wani jiri ne ya debeta ta tafi luuuu zata fadi da sauri haisam ya tareta ta fada jikin sa Cikin tashin hankali assadiq ya dubeta a mota aka sata suka nufi asibiti shukura kuwa dariya tayi taja hannun yayan ta suka koma ciki



Suna zuwa asibiti aka shigar da ita ganin likita nan da nan aka fara dubata take likita yagano jininta ya hau ga karamin ciki allurai akai mata sannan aka sa mata ruwa duk assadiq ne ya biya kudin

waya yayi wa momy yafada mata hankalin ta yatashi kodimewa tayi takira faruq yazo ya kaita asibitin yace bashi kusa layin safiyya ta kira tafada mata lokacin tana tsaka da girki


"Hello, safiyya afifa aka kwantar a asibiti dan Allah inba abinda kike kizo muje, na kira faruq baya kusa "


" subahanallah, to gani nan momy "



Saddiqa ta kwallawa kira tazo dubanta tayi tace


" yauwa Saddiqa zan dan fita ne ga girki na dora ki karasa min ki kula da yaran nan, ina hamra?



"tayi bacci aunty, fadila tana gidan
momy ko?


"aa tana gidan mu,dazu bayan kinfita nasa aka kaita "


" to shikenan aunty "

Daki ta koma ta shirya ta fito sai da gyarawa hamra kwanciyar ta sannan ta fita

Sanda ta karasa gidan su assadiq momy sai sintiri take tana ganin safiyya ta nufeta suka gaisa mota suka nufa safiyya taja suka nufi asibitin


Sanda suka karasa afifa ta farka sai kuka take tana ganin momy ta dada fashewa da kuka wata harara momy ta watsawa haisam kasa yayi da kansa ya gaishe ta taki amsawa safiyya tai mata sannu da jiki


Kwanan ta uku a asibiti aka sallameta kai tsaye gidan su aka wace da ita dady ne ya kira haisam ya sa shi agaba yai taimasa fadan karyar da yayi musu da nasiha, momy kam ta tubure sai yasakar mata ya, yaki dady ne ya dakatar da ita ya dubi haisam akaro na biyu yace


"a hakika nin gaskiya ni kaina naso raba auranka da yata, to saar ka daya wannan Cikin da yake jikin ta shi zai sa nafasa ku dirina, dan haka ni yanzu zanbaka gida da jari dazaka rike iyalinka kuma zan hada ka da mutum 2 aje garinku dan ganin danginka, inafatan ka fahimta "


" na fahimta dady nagode madalla, allah yakara budi yaja kwana "


" ameen, tashi kaje nan da sati zaku tare ka kular min da afifa kaji ko kayi kuma adalci tsakanin ta da abokiyar zamanta "

" inshaallah dad"

Momy dai tarasa bakin magana afifa kuwa banda aikin kuka ba abinda take



Kamar yadda dady yafada su afifa sun tare a gidan da dady yabasu gida mai kyau sama da kasa afifa asama shukura akasa kowa kitchen din ta daban amma tsakanin ta da shukura ba sauki dan zafin kishi ne da ita gashi Allah yasa mata tsoran ta kamar me



Haka rayuwa tai ta tafiya Cikin sauyin yanayi yau da dadi gobe ba dadi safiyya kam bata da wata matsala dan yanzu tazama abar kauna ga dangin assadiq fadila ta girma sosai hamra ma haka dan har ta shiga school safiyya takan kaita gurin muwadda amma ba tare da sanin assadiq ba

Cikin afifa ya tsufa yau gikin tane tana kwance tana fama shukura ta shigo dakin ta duban ta tayi ta yatsine fuska tace


"to uwar langwai wazai miki girkin da kika zo kika kwanta "



" haba maman abdul baki ganin halin danake ciki "


" eh bana gani baga makauniya ba matsalar ki ce fa ni de kitashi kimana girki kawai "


Tana gama fada tai gaba abinta kuka sosai afifa tayi ta yunkura zata tashi ta dora girkin kenan haisam ya shigo da abinci wanda yasiyo a restuarent ya mikawa shukura nata yazo suka ci shi da afifa yana ta lallabata



Nabil ne zaune shi da maman su wato yaya hannatu dubata yayi Cikin jin kunya yace

"umma dan Allah kisa baki abani auran fadilaty in ta girma "



Wata tsawa ta daka masa sannan ta dora da

" Nabil banyarda da auran zumunci ba dan wlh bazaku rabamu da junan mu ba dan haka kar na kuma ji wlh kaji dai nafada maka "

Ashraf ne ya dubi maman tasu yace

" amma mama ai...


"Dakata Ashraf bana son zancan haka kutashi kubani guri "


Fita sukayi ransu abace tsaki taja ta maida kanta ta kwantar a kujera



Anemawa faruq auran safeena ankai kudi da sa rana biki saura wata biyu yakawo ta gurin momy sun gaisa duban sa momy tayi tace



" faruq ka kaita gurin safiyya su gaisa "


" to momy daman zankaita "


Sallama tayi mata tabata turarurruka suka tafi kai tsaye gidan safiyya ya kai safeena suka gaisa take shakuwa ta kullu a tsakanin su fadila tana ganin ta ta Rugume ta tana murna assadiq ma yadawo sun gaisa ya yaba da zabin kanin nasa





Muwadda ce ta shirya tsaf tafita zuwa super market tana Cikin siyayya taga wani matashi da wata hadadiyar mata Rugume da bsby cikin sauri ta karasa gabansu dan tabbatar da abinda ta gani gaske ne, waye wannan din.












*NASEEBA GAWO*
✍🏻✍🏻
[5:54Am, 2017]


*®💦💦💦TALENTED WRITTERS FORUM*💦💦💦


*💦T F*💦





*KANNAN MIJINA*
👩‍👩‍👧


*NA*
NASEEBA I UBA💐




*Allahumma salli ala sayyadina muhammad wassalim*📿


💦
*TALENTED WRITTERS hadin kanmmu shine alfaharin mu*💦




*2nd 2the last*👈🏻




*98*



~~~Cikin rawar murya muwadda takira sunan muktar basarwa yayi, yayi kamar be ji ta ba sai maryam matar sa ta tabo shi sannan ya dago da kansa ya kalleta fuskar sa ya hade sannan yace


"oh, muwadda ya kike ya maigidan naki"


"muktar wacece wannan, yanzu kai kana ganin kai min adalci kenan kaci amanata ka cutar da zuciya ta, mukatar...... "


" dakata dan allah kar ki tara mana jamaa, wannan da kike ganinta mata ta ce, sunanan ta maryam ga babyn mmu nan, shaheed, so dan haka ki saurara min ki rabu dani ki manta da kin taba sanin wani muktar a duniya kin gane ko "

" Allah ya isa tsakani na dakai wlh bazan taba yafemaka ba mugu azzalumi, kuma wlh sai ka biyani dukiyata "


Maryam ce ta kosa da jin kalaman muwadda jikin muktar ta matsa ta ce


" sweet *mk* pls mu tafi mana wai meye alakar ka da ita ne nifa banason kana hurda da mata "


Takarashe maganar Cikin shagwaba dubanta yayi yace


" ayya kar ki damu matar *mk* baki da fargaba akaina ai ko zanyi hurda da mata to bazanyi da mahaukata ba, so that muwuce kawai "



Tafiyar su suka yi suka bar muwadda atsaye kuka ne ya kwace mata tayi iya yinta ko siyayyar batayi ba ta fito abakin kofa ta hadu da su safiyya sunzo shoping kamar ance ta kalli can sai ga assadiq ya sakale hannunsa Cikin na sopy sun taso yaransu agaba gwanin shaawa sunci kayan su iri daya doguwar riga ta swiss lace sunyi kyau tsayawa tayi tana kallon su safiyya ce ta kula da ita cikin murna tafara mata magana assadiq kuwa gaisawa kawai sukayi ya shige ciki fadila ce ta gaisheta ya yin da hamra ta nufi gurin papan ta ko kallon ta batayi ba sai da safiyya ta kira sunan ta sannan ta dawo

"Hamrah baki ganin maman ki ko, bazaki gaisheta ba "


" ni ba itace mama na ba, kece mamana "


Shiru sukayi muwadda kam kamar tace wayyo Allah saboda takaici safiyya ce ta ja hannun yarinyar ta hada dana muwadda tace


" Hamrah, itama mamanki ce kar ki kuma cewa ba mamanki bace kinji ko, ba kyau ko kina son Allah ya kona ki a wuta "?


Kai ta girgiza alamar aa," yauwa yata to ki dena kinji "


Kiran wayar assadiq ne ya shigo dubawa safiyya tayi taga shine Cikin sauri ta daga


" Hello, Dee "

" wai safiyya me kike har yanzu baki taho ba, meye haka ne ko ance miki bani da aikin yi ne yanzu da zaki tsaya kina bata min lokaci in amfasa siyayyar sai ki fada min "


Yana gama fadar haka ya kashe wayar safiyya ce ta maida dubanta ga muwadda tace


" kiyi hakuri muwadda bari mu wuce sai munyi waya "


Rungume Hamrah tayi ajikinta sai kuma tafara zubar da kwalla safiyya taja hannun Hamrah suka shiga ciki


Sanda suka shiga assadiq yacika yai fam a hankali ta kira sunanan sa


" Dee I am so sorry"


Banza yayi mata itama basarwa tayi ta shiga daukar abinda tazo siya suka gama suka biya kudin suka fito a mota safiyya take taiwa assadiq magana yayi mata magana yayi Shiru fadila ce ta kira sunan sa


"papa, mamma na fa tana ta maka magana baka amsaba, dan Allah ka amsa "


" ki rabu da ita fadilaty ina jinta, mun bata ne "


" gsky banyarda ba nide, mamma na ki bashi hakuri kinji "


Shiru safiyya tai musu karshe ma tashiga danne danne a wayar ta, Hamrah ce ta ce


" papa"

"naam kalaty"


Wai mamma ba ita tahaifeni ba, wai aunty ce mamma na "


Kallon safiyya yayi ya tsareta ta da ido dauke kanta tayi can ya nisa yace


" aa bahaka bane, wa yafada miki haka "


" papa auntyn ce fa tafada dazu "


" to aa sopy ce maman ki kinji ko kar na kuma ji "



Safiyya ce ta dubeshi har zatayi magana sai kuma tayi Shiru ahaka suka karaso gidan su safiyya yana yin parking fadila ta bude murfin motar ta fito ta nufi Cikin gida Hamrah ma binta tayi safiyya ma kama murfin motar tayi zata fita ya dafe hannun ta ido yakafe ta dashi ita dinmma shi take kallo fuskar ta yashafa sannan yace


"sopy fushi ko, kina fushi da assadiq ko saboda nai miki fada, shikenan sopy kiyi hakuri "


" ni haka nace maka"


"to yane, inbahaka ba, shikenan dai yanzu kishiga ciki kifadawa ummi zan shigo mugaisa but ki kawar da fushin da ya kwanta a kyakkyawar fuskar nan taki kinji "

Yakarasa maganar yana kashe mata ido tare da langabar da kai dariya tayi tace


" wlh Dee halinka sai kai wanda besan halinka ba ya wahala "


Fita tayi tabarshi yana dariya kallon ta yake yana dada godewa Allah da yabashi safiyya amatsayin mata tana shiga suhyla ta Rungume ta dan suma sunzo nan suka gaisa da yaya rukayya yaya amina ma tazo ummin su dadi yacika ta ganin yayan nata sun zo tafadamata assadiq zai shigo suka gaisa yabada siyayyar dasuka yi musu aka shigo da ita nan yai musu sallama ya tafi hirar su suke Cikin so da kauna wayar safiyya ce ta hau ruri tana dubawa taga sunan momy dagawa tayi suka gaisa sannan ta dora da


"Safiyya dama zancan hado lefan faruq ne dake zaa je dan haka assadiq zakai ki ai miki pasport daga dubai zaku wuce saudi kuyi umara "


" to shikenan momy allah ya kaimu amma yanzu bana gida muna gidan mmu sai mundawo "

" to shikenan badamuwa bani ummin naku mu gaisa "


Wayar ta mikawa ummi suka gaisa Cikin mutunci momy taitaiwa ummin safiyya godiya da ban hakuri bisa abubuwan dasuka faru abaya tace bakomai ai anzama daya sukai sallama ta kashe wayar


" cab mahakurci mawadaci safy momy ce me kiranki a waya lallai komai na da lokaci "


Cewar yaya rukayya yaya amina ce ta ce gaskiya safiyya kinyi hakuri ina zan iya abinda kikayi Allah nagode maka da bani da *kannan miji*

" to yanzu bagashi komai ya wuceba "

Cewar ummi nan tai taiwa yaran nata nasiha, sai yamma Dr almustapha ya kawo jalila su safiyya sukai ta murnar ganin su, nan suka gaisa jalila ta gaida ummi Cikin girmamawa Dr almustapha ne ya dubi najiba yace


" najiba ga amanar matata nan ki kular min da ita kimata me ma kikace habibty"


Dariya jalila tayi tace, "najiba danwake"


Dariya ummi tayi safiyya ce ta dubi najiba tace


"najiba kowa ke yake bawa amanar matar sa, haka fa da Dee yakeyi "


" ai sun san ba wasa badai kula ba, dan haka bari ma natashi indorawa aunty jalila dan wake "


Dariya sukayi dubansu jalila taja hamra jikinta tanai mata wasa sai da magariba baffa ya shigo suka gaisa da yayan nasa kowacce ta tafi gidan ta


Afifa ciki ya tsufa da kyar take iya aiki tana daki yanuwan shukura sukazo suncika gidan da hayaniya da shewa sun dameta amma ba yadda zata yi haka ta hakura ta kulle kofar ta ta danne kunnanta da pillow sai yamma suka tafi cikin dare tana jikin haisam tana bacci kamar an tsira mata allura tafarka agigice



"wayyo Allah na haisam zan mutu katashi mutuwa zanyi "


Agigice haisam yafarka yarasa yadda zaiyi shukura yaje yataso tanajinsa tai masa Shiru hakura yayi ya koma yana zuwa tana sakin wani nishi mai karfi sai jin kukan baby yayi murna ce takama shi ganin Afifa ta haifa masa baby girl waya ya dauka ya kira momy nan tai ta murna dady ma haka ya taimaka mata ta gyara jikinta da sassafe yaya hannatu taje gidan Afifa nan aka shiga hidimar suna farhana tazo tayi kyau da kiba ga danta gwanin shaawa tunda assadiq yaga aman ya dauke shi ya rungume saboda yadda dan ya shiga ransa safiyya ce tamiko hannu zata daukeshi assadiq yace



"aa sopy kema ki haifo naki babyn kide ki ko shikenan aure zanyi amaryar ta haifo min mai sunan dady



"Dee banaso "


" to kiyi zuciya ki haihu "


Su farhana dai dariya suke musu jalila ma ciki ya tsufa faruq ne ya shigo nan sukai masa caa suna tsokanar sa ango ango dariya yayi yace



" wlh kar kuga kunyi aure ubanku zakuci "



" aa faruq ya da zagi kuma, karfa ka auro yar mutane kazo kana zaginta fa "



" haba dai yaya assadiq ina ni ina zagin feena cab allah ya sawake "



" ameen angon safeena "


Cewar safiyya tafada tana karbar aman ahannun assadiq




Ranar suna baby taci sunan babar haisam wato khadija ansha taro yanuwan sa sunzo yankauye dasu kawai kallon su Afifa take



Su safiyya sun kammala shirin su tsaf dan tafiya dubai da saudi anbar su fadila a gidan momy safiyya taso akai hamra gurin muwadda assadiq yaki yadda tunda suka je safiyya takwanta rashin lafiya komai sai assadiq yaimata haka tai ta fama asibiti yakaita ana gwada ta aka gano tana da ciki na wata 2 watan su daya suka dawo



Wani alhjn birni ne ya zo neman auran muwadda fafur ki tayi saboda yadda taganshi











*NASEEBA GAWO*
👌🏻
[5:29Am,2017]




*®💦💦💦TALENTED WRITTERS FORUM*💦💦💦

*💦T F*💦





*KANNAN MIJINA*
👩‍👩‍👧



*NA*

NASEEBA I UBA 💐





*Alhmdulillahil Alhmdulillahil tammat bi hamdillah wa shukurullah mashaallah la kuwata illa billah*👏🏻



💦
*TALENTED WRITTERS hadin kanmmu shine alfaharin*💦





*hakika burina yacika a yau ssabar 7/october 2017 bazan iya musulta farin cikina ba na kammala kannan mijina ba sai dai in kuma cewa alhmdulillah abinda muka karanta Allah ya sa mu amfana wanda nai kuskure Allah ka yafeni*😍👏🏻






*🔚100🔚*



💙
*Dedicated 2 all kannan mijina fans all over the world*💙






~~~Alhj namadi dariya yake wa muwadda musamman yadda ya ganta yar gayu ita kuwa dada tsuke fuska tayi ahaka ta karaso gurinsa taja ta tsaya dubanta yayi yace


"ranki ya dade gimbiyar mata jarumar mata sarauniyar mata mata a gidan Alhj namadi in Allah.......


"Heee, dakata haba malam meye haka, ya kuma haka, wacce irin magana kake son furta min, nashiga uku "


" Allah sarki baby kiyi hakuri so da kauna ce ta kawo ni gurin ki kuma auran ki zanyi "



Shigowar abbanta ne yasa ta tayi Shiru karasowa yayi dan shiga parlorn sa da sauri Alhj namadi ya tsuguna ya gaida abbanta muwadda kam ciki ta shige

Abba ne ya dube shi yace," sannu ko, meye manufarka akan yata"


"Auranta zanyi alhj"


"mashaallah, zanso jin taeihinka "


" to badamuwa, ni sunana Alhj namadi ni dan kasuwa ne a kasuwar kwarai ina da mata 2 da yaya shida ina zaune a sharada "


" to yayi, ba laifi, abinda nake so da kai shine ka turo magabatan ka dan ku ba yara ba ne ina fatan ka fahimta "



" nafahim ta Alhj na kuma gode sosai inshaallah cikin satin nan zan turo "


" yauwa, allah ya kaimu "


Sukai sallama ya shiga ciki alhj namadi ya shiga motar sa ya tafi cike da farin ciki samun nasarar auran karamar yarinya



Tunda da abban muwadda ya shaida mata ya bawa Alhj namadi auran ta take kuka gashi yanzu son assadiq take kamar hauka maman ta ce tazage tai ta masifa yai mata kaca kaca dataji fadan yai yawa taja bakinta tai shiru



Abangaran safiyya kuwa tana kwance tana fama da laulayi ga final exam ta taho yau yini tayi tana amai ga assadiq ya fita tana kwance a daki taji Shigowar sa, sanda ya shigo parlorn su fadila suna zaune da saddiqa fadila na koyawa hamra homework suna ganin sa suka tashi suka rungume shi duban su yayi yace


"fadilaty binty, ina mamma, ko jikin nata ne "?


" A papa, gsky akai ta asibiti mamma na fa tana jin jiki "


" Ayya, zan kaita inshaallah, hamra ya jikin mamma "


" Ba sauki papa, yau fa amai tai tayi "


Dariya suka yi saboda sun saba da shirman hamra gabuwa ce da kaganta kaga yar fari tashi yayi ya shiga dakin safiyya tana gado a kwance gaban gadon ya karasa ya zauna jikin sa yajata ya zuba mata ido ita kuwa lumshe ido tayi saboda dadin turaran sa dataji a hankali ya kira sunanta


"sweet sopy ya jikin ki fadilaty tace kina ta amai hakane "


" Dee, dama bansami Cikin nan ba da yanzu ina nan ina harkoki na ko"


"haba sopy akan me zakice haka ni da nakeso ki haifa min yaya dozin "



" Dee so kake inmutu ko, ka gaji dani ko kaduba fa kaga yadda nake shan wahala kuma kace sai nayi dozin , ni yanzu ya zanyi da Exam din da zamu fara "


" haba sopy ta yaya assadiq zai so ki mutu ai tare zamu mutu baki san bazan iya rayuwa bake ba, maganar exam kuwa inshaallah zaki iya kinji, yanzu mezaki ci akawo miki "?


" Dee banason cin komai komai wari yake min, turaran ka kawai nake son shaka "


Hmmm sopy kenan sarka mai rikicin gan gan, turare na kike so bani ba ko"



"Dee to ai kaine mai rikicin gan gan daga cewa ina son qamshin turaran ka sai ka juya min magana "

" shikenan dai yanzu me zansamu sweet sixteen"



"Dee tun yau she natashi daga sweet 16 kuma "



" wa yafada miki haka ai bakya tsufa a gurin assadiq, yanzu dai abani agajin gaggawa dan dab nake da shiga wani hali "



Shiru tayi kamar bataji shi ba ta runtse idonta saboda yadda take tsoron haduwar ta da shi baya saurara mata amma bayadda zatayi haka ta daure tabashi hakkinsa amma tasha kuka saboda yadda ta jigata be san ma tanayi ba sai da komai yalafa sannan yaga yadda take kuka dariya yayi ya dada jan ta jikin sa yana shafa gashin kanta yace,



"sopy waye yasa min ke kuka bayan baby na yana wahalar min dake "



Hararar sa tayi tare da turo baki tace



" bayan assadiq ne ya kasa yimim afuwa bisa halin danake ciki "



Dariya tabashi sosai tashi yayi ya shiga toilet ya hada musu ruwan dumi yazo ya kama hannunta suka nufi toilet dan yin wanka




Kwanan su jalila 6 da komawa abuja Dr yana kitchen yana girki ita kuma tana parlor tana kallo taji marar ta da bayan ta sun daure ga wani azababban ciwo kara tasaki wacce ta gigita Dr yafito da sauri cikin tashin hankali ganinta yayi a durkushe nan yakama ta ya shiga yi mata sannu gumi akwai takeyi ba shiri ya dauketa ya kaita asibitin da yake aiki cikin Kan kanin lokaci aka shigar da ita dakin haihuwa da taimakon sa dana abokan aikinsa jalila ta haifo danta namiji fari tas dashi ko gyara dan baayiba Dr ya dau dan ya rungume shi har da kwallar farin ciki jalila kam tana kwance saboda yadda ta sha fama nan aka kimtsa mai jego da baby aka kaisu dakin hutu

Waya yayi wa ummin sa yafadamata haihuwar. murna tayi tace lallai yakawo ta kano gobe yaamsa da to sukai sallama. Nan yaita kiran wayar yan uwan sa yana fada musu

Washe gari da sassafe suka shirya sai kano tun da suka dau hanya take bacci tana rungume da baby hankalin Dr yarabu gida 2 yana Kan tukin da yake yi yana Kan matar sa da babyn su ahaka suka karasa kano kai tsaye gidan su yakaita momy tai ta murna nan aka shiga hidima su safiyya sunzo ganin baby najiba kuwa kullum sai tazo momy tai ta tsokanar ta sai tai ta dariya


Ranar suna yaro yaci sunan baffa suna kiransa da fahad nan momy taci gaba da kula da maijego



Bikin faruq yazo ankai lefe na alfarma baki yarage saura kwana 2 anata shirye shirye


Ranar alhmis safiyya ta hada masa dinner ita tayi komai anci ansha ango da amarya sunyi kyau *kannan mijin*safeena da safiyya sai jansu suke da wasa yaya hannatu sai dariya take musu akai lafiya aka gama lafiya ranar daurin aure assadiq da faruq sunci shadda iri daya sunyi kyau haka nabil da ashraf sunyi kyau sunsa shadda iri daya da su fadila gwanin shaawa

Andaura auran faruq da safeena akan sadaki 100k


Da yamma aka kawo amarya gidan ta kusa da na assadiq bayan ankawo ta ganin su assadiq


Amarya suna zaune lpy da safiyya da *kannan mijinta* faruq bayajin kunyar makalewa matar sa ko agaban waye suyi tamasa tsiya




Muwadda ta tare a gidan Alhj mai kudi gidan mata 2 ita ta uku gidan balai dan matan akwai kishi ga yayan nasa basu da mutunci shikuma kulle ne dashi baa fita haka dai take zaune abin tausayi




Safiyya ta haifi danta namiji kykkyawa murna gurin assadiq da su fadila baa magana safeena ce kullum take shiga gidan safiyya take tayata aikin gida ranar suna yaro yaci sunan dady wato muhammad suna kiransa da *little* fadila kam tana kiran sa da

*didi* tun tana fada safiyya tana hanata har ta hakura ta kyaleta



*BAYAN SHEKARA*
*3*




DUK wata nasara da mace take fatan samu a gidan aure safiyya tasamu domin ahalin yanzu safiyya tazama hanshakiyar mace ga kudi ga ilimi dan anbata kwamishinan ilimi suna zaune cikin kwanciyar hankali da mijinta




Fadila ce zaune tana duba wasu takardu nabil ya shigo Cikin shiga ta alfarma tana ganinsa gabanta yafadi saboda yadda ya matsa mata da maganar aure karasowa

Please Login or Register in order to submit comment