Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

muktar bugu biyu ya daga


" Hello baby kina son soyayyar ki ta kashe muktar ko "


" Hmmm haba dear kana tuna nin zan iya rayuwa ba kai ne, kwana 2 ina tare da kewar ka banajin dadi ne shiyasa "


" ayya I am so sorry baby, yanzu ya jikin naki "


" Da sauki zaace "

" baby ina tsoran fa ciki yashiga jikin ki fa "


Mai da dubanta tayi ga hamra kana tace


" kar ka damu dear yanzu dai ya labari "


" Hmmm bari ke dai baby wlh kasa ta rikici gari yaci wuta "

" ayya ok, badamuwa zan bawa rushida ta kawo ma 200k amma dan Allah dear kafara mana tanadi kaji dan saura kiris burinmmu yacika "


" baki da damuwa baby ke de kici gaba da zube kayan aiki, wata harka zan fara matsalar sai da kudi masu nauyi ne wlh "


" Hmmm ba damuwa zan iya mallaka maka duk abinda na mallaka, yanzu zanyiwa abbana magana zai bani ko nawa nake so shima kuma Assadiq zan karba a hannun sa dan haka kar kaji komai "


" Allah sarki baby shiyasa nake masifar son ki wlh nagode, sai na jiki ki kular min da kanki "


" ok kai ma haka, ka gaida min da umma ta

" zataji baby na "


Sukai Sallama ta kashe wayar tare da fargabar yadda zasu karke da muktar kukan da hamra take ne Yadawo da ita daga tunanin da take shikuwa zaginta yake tare da kulla muguwar aniyar sa


Biki yarage saura kwana 5 kowa yana ta shiri musamman safiyya wacce bikin yazamar mata gaba da baya haisam kuwa kullum sai yazo dan shirye shiryen bikin safiyya ce ta dau nauyin gyaran amare da su turaran wuta da humra Assadiq ysbasu kudi masu yawa dan hidimar biki Muwadda kam 20k taiya bawa momy shima sai da maman ta tai da gaske ragowar tabawa muktar da kudin da ta karba gurin abban ta


Momy kam sai shiri ake tana murna yanzu zatai biki dady dai yazuba mata ido amma shima hankalin sa be yarda da haisam ba yafi son auran jalila da *Dr*almustapha

Yaya hannatu ce tazo dan shirin tafiya kafi ita da kannan momy guda biyu sai kanwar dady sai Muwadda da Assadiq ya matsawa sai taje gidan jalila zaafara yi Washe gari ayi na afifa


Sunje gidan ta ma dai dai ci mai kyau da tsari kmr ganin turawa irin ganin tsakiya gefe kuma dan karamin lambu ne katon parlo sai bedromm guda 2 da toilet ga kitchen sai dining area nan suka yaba tsaruwar gidan sukai kafin su cikin kwanciyar hankali suna cikin kafin su safiyya suka zo kawo musu abinci da kayan da aka saba bayar wa na alada sukai wasa da dariya zuka tafi Muwadda kam sai kebe baki take ta raina gidan jalila

Dady yayi kokari anmusu kaya masu kyau da tsada


Tunda Suka koma momy take tambayar hannatu


"hannatu ya gidan jalila kuwa dan nasan ba abin arziki zasuyi ba musai kaya masu tsada karshe gidan bana arziki bane "


" Gsky momy kidena haka wlh duk yar da tasa mi gidan jalila hakika ta caba "

" aa aunty hannatu meye abin burgewa agidan jalila cab "


" yauwa Muwadda ni nasan zaki fadan gsky "

Wani banzan kallo yaya hannatu ta watsawa Muwadda ta taja tsaki ta mike ta yi kitchen


Sanda Muwadda ta koma gida su jalila suna gidan gurin safiyya ta shiga lokacin safiyya tana daki afifa ce ta dubeta tace


" aunty Muwadda kun dawo ya gidan amaryar"?

"Hmmm, su jalila dai anfado wlh duk girman kan yakare a dan wannan gidan ande ji kunya "


" Alhmdulillah bandamu da gida ko yawan arziki ba farin ciki nake nema da kwanciyar hankali, inshaallah sai anyi koyi da irin *ZAMAN AURENA*"



Fitowar safiyya ne yaktse maganar da Muwadda zatayi da murna safiyya ta dauki hamra tana son yar itama yarinyar tafara ganeta

"Muwadda sannunku sai yanxu "?

" eh to, nadade gidan momy ne "


" ok wlh nima kaina ke ciwo shiyasa na taho da wuri "


" Allah sarki Allah yasa wake "

" Ameen "

Tashi tayi tafita afifa ta karbi hamra ta bita jalila kam waya ta dauka suka sha hira da angonta


Washe gari aka je gidan afifa katon gida mai azabar kyau nan fa yan kafi suka gigice haisam da ksnsa ya kawo musu abinci na restueant da katan katan na lemo da ruwa sukayi suka gama ba wanda yazo da sunan dangin ango



Farhana tun ana saura kwana 5 biki taketa shiri ibraheem nadaga tafiyar Saboda kannan sa suna exam kuma tare zasu sai yau ana gobe kamu sannan suka taho da bilkisu da fatisa sai masari tun agida yace tasa nikaf da katon hijjabi kuma kar tasake taje party mutukar da maza taamsa da to amma badan ta yarda ba driver ne yakaisu suma zasu taho ana gobe daurin aure yabata kudi mai yawa tayi biki tabawa momy kuma akan idon masari



Suna daukar hanya ta dubi farhana tac


"amarya ina kudin da yaya khalil ya baki ki bamu



"kmr yaya ban fahimce ki ba zainab


"fatisa bilki kunji mu da mata

"ai wlh sai kinbamu haka ake yi dan zamu garin ku biki sai kifara wulakanta mu"


Banza tai musu saboda yadda zuciyar ta ke tashi ahaka har suka gaji sukai shiru ita ma bacci ya dauketa


Sai yamma suka isa faruq yana bakin gate suka shigo yan mata ne guda uku suka fara Fitowa sai wata da katon hijjabi da nikaf tana ta doso inda yake zaune yarasa wacece da murna ta kira sunan sa



"yaya faruq "


" naam baiwar Allah sannunku da zuwa "


Daga nikaf din tayi tana dariya da mamaki yace



" Kai farhana, na you lallai matar malam "

" su fatisa suka gaida shi ya amsa da sakin fuska ciki suka shiga nan farhana ta rungume momy dakin su tashiga su afifa na ganinta suka rungume juna suna murna


Su masari kuwa sai kebe baki suke momy da kanta takai su daki sukai wanka suka ci abinci


Farhana kam ana tare da yanuwa anata da labari sunata tsokanar ta mai ciki tana ta basu labarin *kannan mijinta* afifa ce tace


"Kai kuma kika barsu baki ci ubansu ba "


" ke aure maisa mutum yai laushi afifa ai infada miki *ZAMAN AURE* sai a hankali "


" jalila kuwa mamakin farhana ya hanata magana tashi tayi ta nufi saman dady suka gaisa yai mata ya jiki suka sha hira su zainab ma sunzo sun gaisa



Da daddare ta nufi gidan Assadiq suna kitchen shi da fadila wai alawar madara zai mata safiyya kam tana parlor tai musu banza fitowa yayi yana mata magana



"sopy dan Allah zo ki gani tayi "



" Dee nifa ban iya ba, shiyasa nace kar ka biyewa fadila "

" mamma na dan Allah ki koyawa Dee kinji "



Dariya yarinyar tabasu Sallamar farhana ce ta katse musu dariyar da suke fadila na ganinta ta kwasa aguje tai daki







*NASEEBA GAWO*
โœ๐Ÿป
[7:5Am,2017]


*ยฎ๐Ÿ’ฆ๐Ÿ’ฆ๐Ÿ’ฆTALENTED WRITTERS FORUM*๐Ÿ’ฆ๐Ÿ’ฆ๐Ÿ’ฆ


*๐Ÿ’ฆT F*๐Ÿ’ฆ






*KANNAN MIJINA*
๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘ง




*NA*

NASEEBA I UBA ๐Ÿ’




*Astagafirillah waatubu ilehi Astagafirillah azim*๐Ÿ‘๐Ÿป



*๐Ÿ’ฆTALENTED WRITERS hadin kanmmu shine alfaharinmmu*๐Ÿ’ฆ





๐Ÿ’™
*Ina taya Fiddausi sodangi da zara Surbajo kammala novels din su dafatan munfadaku da abinda muka karanta ameen NASEEBA na biye da ku sisters*๐Ÿ’™






*89*





Da mamaki safiyya ta karasa gurin farhana tajata zuwa kan kujera Assadiq ma karasawa yayi ya zauna suka gaisa da kulawa


"farhana saukar yaushe, ya mai gidan naki "?


" dazu yaya, lpys kalau yana gaida ka zasu zo sai ana gobe daurin aure "

" ina amsawa yaron kirki kenan, Allah yakaimu, safiyya kawo mata abinci "

" aa wlh yaya nakoshi, ya baby ina fadila banganta gidan momy ba "


Sai lokacin suka kula ba fadila a parlon Assadiq ne ya dubi safiyya yace


" sopy duba kitchen ko bata fito ba "

Dubawa tayi bata nan daki tanufa tana can kuryar gado karaswa safiyya tayi tace


" Fadila lpyr ki kika zo nan kika zauna "


" wlh mamma ko, inajin tsoran aunty farhana ne fa "


" Kai, fadila to mezata miki ta dena duka taso muje ku gaisa "


Hannunta ta riko suka fita farhana naganin fadila ta rungume ta a jikin ta


" I miss u Fadilaty "

Shiru tai mata sai daga baya ta gaida ta tare suka fita gurin Muwadda bayan ta dubi safiyya tace


" aunty zan dawo akwai hira may be anan zan kwana ma "


" tohm shikenan farhana ina maraba da ke "


Assadiq ne ya dubi safiyya yace

" sopy nagode da kulawar ki ga yanuwana Allah ya albarkaci rayuwar ki "
" Ameen Dee "




Kai tsaye farhana gurin Muwadda ta nufa tana parlor hamra sai kuka take suka shiga tana shiga ta dauki yar tafara rarrashinta Muwadda kam kallon ta kawai take yadda taga farhana ta canja tade yi kyau amma tayi sanyi sosai guri suka samu suka gaisa


" cab musulumatun farhana kece "

" kinji ki to da wace, ke kam kifiya abin haushi wlh "

Dariya tai tai mata karshe ko gaisuwar kirki basuyi ba ta tafi zata tafi da hamra ta karbi yarta



*********

Yau takama alhms yaune zaafara kamuun su jalila safiyya kam tun safe ta tafi gidan su anata shirin biki amare sunyi kyau sosai anyi kamu a gidan ya hannatu Washe gari diner tun safe haisam yadada jaddada dawa farhana kar tasake taje tanaji tana gani aka shirya aka tafi su fatisa ma sunje sai kawai tace bazata iya zuwa ba ba tajin dadi

Angwaye da amare sunyi kyau kayan su iri daya haisam yayi barin nera Dr almustapha kam sai tarai rayar jalila ya ke anci ansha su safiyya ma sunyi kyau cikin ankon su na lace faruq ma yazubar da kudi sosai haka Assadiq Muwadda kam tunda tabawa yaya hannatu hamra ta silale ta nufi gurin muktar har aka kusa tashi bata dawo ba ga yarinyar nata kuka ran Assadiq yabaci ankira wayar ta akashe haka akatashi haisam da afifa suka shiga wata lafiyayyar motarsa abokinsa yajasu suka tafi sai kissing dinta yake a mota ita kam ta narke sai zuba shagwaba take kiran shukura ne ya shigo dagawa yayi


"Hello, zankiraki "kawai yace ya kashe wayar yana dada shigewa jikin ta


Sanda Muwadda ta koma gurin dinner antashi kai tsaye gida ta wuce ta tatar da hamra nata bacci a gurin safiyya Assadiq na zaune a kujera ahankali ta shiga ko kallon ta be ba tasa hannu ta dauketa tare da yiwa safiyya Godiya satar kallon sa tayi taga ya hade rai yana tunanin matakin da zai dauka akanta


Washegari aka shurya aka tafi dinner din da haisam ya shirya jalila taje amma ba Dr su safiyya ma ranar sukayi ta yaya amina duk budirina daake banda farhana saboda *kannan mijinta* sunhanata sakat dabasu tazo da baabinda zai hanata zuwa dinner din daakeyi gashi su ibraheem sunzo har da su jaafar ibraheem ne yazo ya dauketa suka tafi mamakin su saboda yadda yayi kewar ta sai dare Yadawo da ita bayan sunsha soyayyar su


Washegari aka daura aure sdakin afifa 200k na jalila 50k akai yini da yamma aka fara shirin kai amare dady yai musu nasiha mai ratsa jiki aka debesu jalila taraka afifa gidanta mai balain girma da kyau sannan aka kai jalila sai da aka fara kaita gidan su safiyya lokacin antafi kai amina sannan aka kaita gidan ta mai kyau

Kowa ya watse aka bar amare a gidansu
Assadiq kuwa fushi yake sosai da Muwadda ko kulata baya yi washegarin gama biki ibraheem yace su farhana su shirya su tafi momy tace yabar ta takara hutawa da kyar yabar ta suka wuce dasu masari momy tai musu alhr haka ma dady


Amare anyi kwanan farin ciki kmr ko wacce amarya babu abinda babu a gidan afifa komai baja baja haisam da Kansa yaimata komai

Haka jalila hakika tayi dace da miji na gari ba karya a lamarinsa sai da taje gidan sa sannan ta fahimci lallai tayi saar miji


Kwanan farhana 5 sannan ta koma bayan tabawa safiyya labarin yanayin *ZAMAN AURANTA* tabata shawarwari tare da yimata alhr


Kwanan su jalila 5 akano suka wuce abuja bayan sunje gidan su da gidan su Dr ummi sai nan nan take da ita sunje gidan afifa ma



Abangaran afifa kuwa anata shan soyayya kullum tambayar haisam take yaushe zasu wuce england sai yace bayanzu ba


Yau da sassafe suna bacci taji wani mahaukacin bugu a firgice ta tashi taje bakin gate tana tambayar waye "

" bude ki gani "


Aranta take nanata kalmar bude ki gani, to waye wannan?






*NASEEBA GAWO*
โœ๐Ÿป
[5:57Am, 2017]



*ยฎ๐Ÿ’ฆ๐Ÿ’ฆ๐Ÿ’ฆTALENTED WRITTERS FORUM*๐Ÿ’ฆ๐Ÿ’ฆ๐Ÿ’ฆ


*๐Ÿ’ฆT F*๐Ÿ’ฆ




*KANNAN MIJINA*

๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘ง




*NA*

NASEEBA I UBA๐Ÿ’






*Allahumma salli ala sayyadina muhammad wasallim*๐Ÿ‘๐Ÿป





*๐Ÿ’ฆTALENTED WRITTERS hadin kanmmu shine alfaharinmmu*๐Ÿ’ฆ








*90*





~~~haisam ne ya farka yaga bega afifa ba parlo yafito yana kiranta da muryar bacci yaji shiru sai yaji kmr tana kokarin bude kofar gate da sauri ya bude kofar parlon yafita ya kira sunnanta


"baby, lpy zaki bude kofa "?


" yauwa dear zo ka bude tun dazu ake bugu nagaza bude kofar "


Daga murya yayi yatambayi," waye "?


" KB ne "


Hantar cikin sa ce ta kadada amma sai ya dake ya dubi afifa yace


" amm baby koma ciki inbude masa bana son dan iskan nan yagane min ke "


" dear shi din waye to "

Tai magana cikin shagwagaba kmr zatai kuka

" kar ki damu wani yaro nane a kasuwa, ki shiga ciki ki jirani zanzo in dora mana break "


Ok, dear pls kar ka dade kaji"


Tana gama fada ta shige ciki sai da yaga shigar ta sannan ya bude kofar ido hudu sukai da kb sai cin magani yake dubansa yayi yafara magana


"KB, yaakayi ne dafatan lpy "


" kut amma gsky ka raina min hankali tambaya ta ma kake lpy, ya mukayi da kai? kasa na debi kudin mutane na ranta ma har yanxu baka biya ba, kuma saboda rainin wayo ka wani tambayeni lpy"


"ho KB, to inbanda abinka yaushe akai daren bare gari ya waye ko sati fa baayi da auran nan ba kar ka damu zanbiyaka"


"wlh dana Sani ban dau kudin mutane nabaka ba, yanzu gashi kana kokarin Sani cikin matsala "


" Haba KB xanbaka, nan da ranar assbar ma zanzo da kaina "


" shikenan sai najika

Ya lallaba shi yatafi ya maida kofar ya rufe Hankalinsa yai masifar tashi musamman da yatuna mutanan da suke binsa bashi ahankali ya furta *AURAN BASHI* dai daita nutsuwar sa yayi ya koma ciki afifa tana kwance tana kallo be bari sun hada ido ba ya nufi kitchen binsa tayi ta rungume shi ta baya


"dear yatafi "

" yatafi baby, wai sunji ni shiru banfito kasuwa ba, nace amarya ce ta rike ne "

Dariya tayi ta taimaka masa suka hada break




Abangaran Muwadda kuwa tagaji da shariyar da Assadiq ke mata ya dena bata ko kwandalar sa ga muktar yamatsa mata kudi yake so shiryawa tayi ta nufi gidan su

Sanda taje maman ta tana kitchen ita da mai aikin ta sallma tayi kai tsaye kitchen din ta nufa dauke da hamra

"mama sannu da aiki "


" aa Muwadda daga ina haka?


Tafada tana kokarin karbar hamra tanai mata wasa


"daga gida mama "


" aunty ina yini "


Ina gajiya saude"

Fita sukayi suka barwa saude aikin suka koma parlo suka zauna Muwadda ce ta dubi maman ta tace


"gsky mama nagaji da gidan nan wlh, yanxufa papan hamra kawata kwata baya kulani kuma ba abinda nai masa "


" Hmmm, Muwadda ina zargin kishiyar ki fa "

" aa mama bata da laifi wlh, kawai wulakanci ne itama momyn yanzu ba sona take ba ni dai wlh nagaji "


" ta yaro kyau take bata karko, Muwadda ki nutsu ki bari musami cikar burinmmu mana "


" Kai kai mama, nima fa ina da nawa burin fa "


" ki adana naki kifara cika min nawa "

Shiru tayi karshe ta kwallawa saude kira da sauri ta zo ta tsuguna


" gani aunty "

" naganki saude, da Allah ki dau hamra ki goyata ki kular min da 'ya fa "

" to aunty "


" mama bari inje indawo bazan dade ba, ina son ganin abba na ma "


" ai kuwa baya gari ina kuma zaki Muwadda "?

" nai masa waya yanzu zandawo "

Tasa kai tafita kai tsaye motar ta tanufa tashiga gurin da suka saba haduwa da muktar ta nufa yana nan yana jiranta tayi parking ta fito kusa dashi ta zauna



" dear yi hakuri kasha jira "

" jira ai yakusa karewa baby yakamata ki rabu da mijin nan naki ki zo muyi auran mu "


" kar kadamu dear saura kiris ni kaina nagaji da zama dashi ada ina masifar son Assadiq amma tunda na hadu da kai gabadaya naji bana son sa kai nake so muktar "


" Hmmm nima ina sonki baby, sai dai muktar ba kudi "

" kar kaka damu muktar zan tattare duk wata sarka tawa kai har da mota ta asiyar inbaka kudin kaja jari muktar "

" wow, Allah baby "


" kafi karfin haka dear "


Ahankali motar tashigo gurin nacikin motar sai waige waige yake yana neman abokin sa dasukayi alkawarin haduwa a gurin karaf idanunsa ya sauka akan muwadda da muktar suna ta hira cikin mamaki Assadiq ya kuma kallon su sai dariya suke take yagane saurayin shine wanda yataba ganinsa da ita a asibiti Kansa ne yasara take ya juya yabar gurin sai waya yaiwa abokin nasa bazai sami damar zuwa ba yayi hakuri


Ko office be koma ba yanufi gida

Sukuwa basu ma kula da shi ba sai da suka sha hirar su sannan suka bar gurin da niyar zata kawo masa sarkokin ta da motar ta yasiyar



Sanda Assadiq yakoma gida safiyya ta dawo daga school kai tsaye bangaran sa ya nufa asaman gadonsa ya kwanta jin Shigowar mota ne safiyya yasa safiyya ta leka mamakin ganin Assadiq ya dawo a wannan lokacin ne yasa ta nufar dakinsa sanye take da doguwar riga purple ta material tasaki gashin kanta baya tayi kyau
Ahankali ta turo kofar parlon baya parlon daki ta nufa nan ta hango shi kwance akan gadon dafe da Kansa da sauri takarasa gabansa

"Dee, lafiyar ka, naga kadawo yanzu "?


" ummm"

Kawai yace mata ya juya ya kwanta shiru tayi tana nazarin sa lumhe idon sa yayi kmr mai bacci gjy tayi da zama tace


Dee, bari inje in dakko fadila a school "

" sai kindawo dan Allah kar ki dade "


Shiru taimasa bata ce komaiba ta fita tana fita yaji wasu hawaye masu xafi suna bin kuncin sa tunda ya auri muwdda be huta ba




Abangaran farhana kuwa cikin ta ya fito da kyar take iya yin aiki su fatisa basu fasa yimata rashin mutunci ba tun tana tanka musu har tadena yau tun safe tana kwance su suke aikin gidan ibraheem ya fita tana daki sai jin karar fashewar abu tayi tass suna ta dariya ahankali ta taso ta fito show glass dinta suka fasa gaba daya rasa me xatace tayi tabisu da kallo can tanisa tace


"Haba zainab garin yaya dan Allah kukai min haka?


"yi hakuri bamu kula ba "


" ku makafi ne da zakice baku kulaba "


" eh to wataran mukan taba makanta "

Cewar fatisa tasaki taja ta koma ciki bata kuma fitowa ba sukuma basu share ba har ibraheem ya dawo ya tatar da gurin ahaka suna parlor ya tambayesu

" wa yafasa abun nan "


" wlh ya khalil aunty farhana ce ta biyo fatisa zata mareta tafasa abinta da kanta "


" akan me zata mareta "

" haka kawai "


Dakin ya nufa tana kwance sunnanta ya kira da karfi


" farhana me fatisa tai miki xaki mareta har kika fasa abinki kuma kika kasa kwashe wa "


" haka suka ce maka to shikenan suje dan kansu tajuya taci gaba da kwciyar ta sai kuma hawaye fita yayi ya gyara gurin sai kuma tausayin matar tasa yakamashi


Jalila kam bata da wata matsala da mijinta kullum suna faranta ran junansu duk sati sai yakira dady sun gaisa ga aiken abin arziki da yake wa momy ita abun ma mamaki yake bata wani lokacin ma jalila bata san yayi ba yasa momata islamiyya tana xuwa kafin afara admission ta dawo kano tafara B u k yanzu haka fita zaiyi zuwa aiki sai shagwaba take yana ta yimata dariya



"Haba matar doctor bazan dade ba zandawo kinji bana son inganki cikin damuwa "


" *Doktar* nide bana son yanmatan abuja su kalle min miji wlh "

" to yanzu bani nikaf insaka shikenan "


Dariya sukayi ya sakar mata kiss yafita ciki takoma tana murmushi hade da gode wa Allah


Muwadda tahada komai takaiwa muktar ya karba harda motar ta faruq ne yaxo wuce wa yaganta itama shi take kallo take tsoro ya kamata dauke Kansa yayi muktar kuma yimata Sallama da niyar zasu yi waya

Kai tsaye faruq gidan Assadiq ya nufa dan sanar da shi abinda yagani






*NASEEBA GAWO*
โœ๐Ÿป
[6:00Am, 2017]


*ยฎ๐Ÿ’ฆ๐Ÿ’ฆ๐Ÿ’ฆTALENTED WRITTERS FORUM*๐Ÿ’ฆ๐Ÿ’ฆ๐Ÿ’ฆ


*๐Ÿ’ฆT F*๐Ÿ’ฆ





*KANNAN MIJINA*
๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘ง


*NA*

NASEEBA I UBA๐Ÿ’






*Alhmdulillah ala kulli halin*๐Ÿ‘๐Ÿป





*๐Ÿ’ฆTALENTED WRITTERS hadin kanmmu shine alfaharinmmu*๐Ÿ’ฆ





*๐Ÿ’ฆDedicated 2 kannan mijina group*๐Ÿ’ฆ









*91*





~~~sanda faruq yaje gidan Assadiq baya nan sai safiyya ya tarar tana koyawa fadila home work tana ganinsa ta taso a guje ta rungume shi


"uncle oyoyo, yaushe xaki kaini gidan su yaya nabil "

" can kike son zuwa "

" eh wlh "

" to zankai ki amma kwana zakiyi "


" Kai kai, mamma kinji wai kwana zanyi gsky aa "


" ai kuwa sai kin kwana, faruq ya aiki "?

" wlh angode ma Allah aunty, yaya Assadiq fa "


" yana gidan momy, tun dazu "

Fita yayi ya nufi gidan su Muwadda kam hankalin ta yagama tashi da yadda faruq yaganta da muktar tana dakin ta tayi shiru amma wani bangaran na zuciyar ta farin ciki take Allah yasa yazama silar rabuwar ta da Assadiq kenan



Assadiq yana zaune gaban momy yana fada mata abinda muwadda take yi, faruq yashigo guri yasamu ya xauna bayan ya mikawa yayan nasa hannu sun gaisa


"yaya ashe kana nan naje gidan ka banganka ba "



" ina nan faruq Allah yasa lpy?

"eh to, lpy ba lpy ba "


Nan yabashi labarin abinda yagani ransa Yakuma baci

Momy ce tanisa tace

" wai wacce irin yarinyar ce wannan, wlh fitinar Muwadda ta isheni fa "

Waya ta dauka tashiga neman layin ta sai da ta Kusa tsinkewa sannan ta dauka


" Muwadda inkina gida kizo ina son ganin ki "


" gani nan "

Sai da ta jima sannan ta shigo guri tasamu ta zauna sai harare harare take momy ce ta dubeta tace


" ke Muwadda waye yaron da aka ganki da shi "


" wane yaron fa momy "?


" bansaniba tambatayata ma kike "

Assadiq ne yadago ya kalleta bayan ya watsa mata wani kallo


" ke bama son raini waye muktar "?

" aa haba papan hamra so nawa zanfada maka matsayin muktar a gurina "

" ke yazaki rainawa mutane hankali ne da wa naganki dazu ko bake bace "



" to kai kuma meye naka malam ina ruwanka kabari muyi magana da mijina "


" Gsky nifa momy nagaji wlh shi kenan badama kayi muaamula da mutum sai ace dan me akan me?


"Muwadda momyn kike fadawa haka saboda baki da mutunci

Please Login or Register in order to submit comment