Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

su yace Ku shiga ciki kuce safiyya tazo inji mijinta



"Bayan fitar Assadiq Jalila ta dubi afifa cikin fushi tace haba Afifa ya zakiyi haka meyasa zaki cewa ya Assadiq bamu ga Aunty safiyya yanzu kin hada su fada kenan kina ganin yadda ya fita a zuciye"



Afifa tayi dariya tace baza ki gane bah ya jalila ai dama fadan nakeso na hada su saboda na dau alwashin sai na ramawa ya farhana Marin da ya Assadiq yayi mata akan wannan shegiyar Matar tasa"


Tabe baki kawai farhana tayi tace haka nake so sis"



Safiyya ce ta fito fuskarta a kumbure alamar bacci yanayin da taga Assadiq neh ya bata tsoro fuskar nan tasa a hade idanuwansa sun kada sunyi ja ta qaraso gabansa jikinta a sanyaye tace Dee kayi haquri nasan yunwa ce ta koro ka ko naga duk ka canja"


Banza yayi mata yace malama shiga ki hado kayanki mu tafi gida


Shagwa6e fuska tayi tace kai Dee don Allah baa gama sunan ba fah



"Cikin harzuqa yayi magana yace zaki dakko ko inyi tafiya ta"


A sanyaye ta juya ta shiga gidan yayar tata zuciyarta cike da saqe saqe game da chanjin da ta gani gun Assadiq, dakin yayar tata ta nufa ta shaida mata yadda suka yi da mijin nata, cikin hikima mai jego ta taushe ta sannan ta hada mata abincin sunan suka fito,


Hawaye neh ya tahowa safiyya tace to yanzu yaya mutane zasuyi ta tambayar ena nake, dariya ruqayya tayi tace sai ince kun tafi cin amarci,dariya suka sa duka sukayi sallama ta fito suka shiga motar ya tashe ta da gudu a zuciye



Basu tsaya ko ena sai a gida yana yin parking,yayi zamansa harda kwantar da kujera,safiyya da taga bashida niyyar ce mata qala kuma bashida niyyar fita tasa hannu da niyyar bude murfin motar ta,ta kwashi kulolin abincinta tayi cikin gida dama kanshi air freshener motarsa na barazanar sata amai Allah Allah take ta fita taci alala da dambun suna,



Tana shiga palour ta baje ta cika cikinta da dambun shinkafa da alala tasha kunun aya ta qoshi ta tashi tayi ciki ta tsala wankanta ta fito sanye da doguwar Riga iya gwiwa pink sai gashinta data saka ta fito palour da niyyar shan ruwa, nan taga gogan nata yana cika da batsewa ko kallon inda yake bata yi ba don ta yanke shawarar qin shiga harkarsa har sai ya sakko don kansa don bata ga dalilin dazai sa ya tsiri fushi da ita, inama laifin ya gaya mata kuskurenta ta gyara ta kuma nemi yafiyarsa amma tunda ta nan ya 6illo ita ma ta iya, ruwan ta dauka tayi hanyar dakinta binta yayi da kallo ya girgiza ka tayi shigewarta tana karkada jiki


Yana ta zaune a parlour har ya gaji ga yunwa data ke kwarzabarsa gani yayi ba sarki sai Allah ya sakko ya cinye ragowar dambun da alalan data rage yana gamawa wayarsa ta fara ruri yana dubuwa yaga muwadda ke kiran nasa



Dagawa yayi fuskar sa qunshe da murmushin mugunta a zuciyarsa ya raya ya samu hanyar da zai rama wulaqanci da sopy tayi masa



Daga can 6angaren muwadda tace "hello sweery



Yace naam baby ya kike yasu mama ya qarasa zancen yana qarasawa cikin dakin safiyya ya zauna gefen gado suka cigaba da hirar su


Wani qululun baqin ciki neh ya tokarewa safiyya a qirji jin yadda Sadeeq ke wani maqale murya eta kuma tana shagwa6ewa

Tashi tayi ta fice ta buga masa qofa

Qunshe dariyarsa yayi sukayi sallama da muwadda wadda farin ciki ya cikata saboda yau daya Assadiq ya bata hankalinsa


Zama tayi a parlour ta kunna karatun alqurani cikin qira,ar sudais tana ji zuciyarta na mata sanyi

Shiryawa yayi cikin kananun kaya yayi kyau sosai ya dauki mukullin motarsa ya fito ko kallonta baiyi bah yayi ficewarsa

Yana fita kuka ya kubce mata taci kukanta ta qoshi

~~Bangaren Momy kuwa yanke shawara tayi ta dunqule wasu kudadenta ta bawa dady tace gashi nan Assadiq ya kawo yace akai masa kudin aure gidan su muwadda

Dady ya kar6a ya jinjina abin a ransa amma yace Allah ya bada alheri,yace to zanyiwa su Yaya da Alhaji salihi sai suje sukai

A 6angaren Assadiq kuwa bai dawo ba sai taran dare

Safiyya tun tana jiransa har ta gaji tayi bacci bata ga dawowar sa ba



_Tirkashi fans yau kunji rigimar data danno tsakanin sopy da Assadiq๐Ÿค”nidai naseeba nace fadan nasu ma na love neh_







*NASEEBA GAWO*โœ๐Ÿป
[8:55Pm,2017]

*ยฎ๐Ÿ’ฆ๐Ÿ’ฆ๐Ÿ’ฆTALENTED WRITTERS FORUM*๐Ÿ’ฆ๐Ÿ’ฆ๐Ÿ’ฆ

*๐Ÿ’ฆTF*๐Ÿ’ฆ




_**KANNAN MIJINA_**
๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘ง



*NA*

*NASEEBA I UBA*๐Ÿ’



```Ina gaisheku masoyana ina kaunarku kmr yadda kuke kaunar littafina mai taken ```

*kannan mijina*

```karku manta da bazarku nake kwaso shoki```๐Ÿคฆ๐Ÿปโ€โ™€๐Ÿ’ƒ๐Ÿป





_Wannan shafin nakune_*Talented writters forum*๐Ÿ’ฆ

_inban mantaba hadin kanmmu shine alfaharinmmu_๐Ÿ’™







*42*



~~~Assadiq bedawo ba,sai after 10 lokacin
safiyya tadade da yin bacci dakin yanufa,safiyya ya gani tacire rigar daxu tasanya have vest da da dan karamin skin tied,tayi rub da ciki gashinta yabazu akan filo,tayi masa kyau gashi tayi kiba gwanin shaawa,wata irin soyayyar tace tafizgeshi,tare da shaawarta,ahankali ya karasa gabanta yaxubamata kyawawan idonsa, a hankali,yafara shafa gashin kanta mai taushi da baki,yashiga
Shafa mata jiki ,acikin
Bacci taji kamar ana shafa mata jiki mirginawa tayi tadada
rungumo shi,sakamakon kamshin turaren da ya bugi hancinta,mamaki ne ,yacika assadiq
Yaushe Safiyya tai kiba haka mararta yashafa yaji tadan daga,kissing dinta ya farayi a hankali ta bude ido ganinta tayi
ajikin assadiq tahade rai tace

"Ya haka mekuma nayi
maka,zaka zo kana tabani"

takarashe maganar tana kokarin tashi tare da turo masa baki,

Shi sai yagama kamar da gangan tai wannan shigar riko kugunta yayi,takuma fado jikinsa,kana yace,

"Sopy mijinki ne fa,guduna kike"


"Mezanmaka ni nazaci kana da wata matar,to
Kaje nabar mata kai,haka akeyi ni banyi fushi dakaiba sai kaine zakayi,menayi maka"

Tafada tana hawaye tare da shigewa kirjinsa turaransa ne yaimata dadi,
dariya ce taso kubce masa sopynsa tana tsiwa kuma sai dada shigewa jikinsa take,

Fuskarta yadago yaxuba mata kyawa wan idonsa yace,

"Sopy assadiq kikewa tsiwa, dan kinga nadamu dake,shine zaki tsiro min da halin da banakiba,har zanzo karbar hakkina kiyi min haka kina son in karbi hakkina ta karfi kenan to zaniya yahau kiciniyar danneta kuka tasamasa tace

"Dee dan Allah katsaya kaimin bayanin laifin danaimaka da har kake kokarin yimin fyade"

"Au hakama zakice ko
to ni bazantaba yimiki fyadeba Allah yatsreni kije kirike kayanki banaso"

Yafada yana kokarin janyeta daga cikinsa

Fita yayi yakoma dakinsa ya kwanta ransa naimasa suya,

Kuka safiyya take wiwi,ahaka bacci barawo yadauketa

Assadiq kuwa juyi kawai yake yakasa bacci tunanin sopynsa yacikamasa zuciya,ga
Shi yana tsananin bukatarta a wannan lokacin,tunani yayi ko de a gidan suna ne akasami wata mara tsoran Allah ta zuga masa mata ahaka bacci yadaukeshi,


Washegari da wuri yashrya yafita,kai tsaye gidansu ya wuce,a dining area yasami momy da kannan sa suna break fast,karasawa yayi gabanta yagaidata,
Kannansa ma suka gaisheshi,yaja kujera ya zauna momy ce tadubeshi tace,

"Aa assadiq ya haka zaka baro gidanka kazo kacimana abinci,matarka fa"

Shiru yayi kana yace

"Batajin dadine shiyasa"

"Allah yabata lpy"

Yaamsa da ameen yadau cup ya. hada tea afifa taxuba masa farfesun hanta da koda sai wainar kwai,

Yaja gabansa zaifara ci kenan momy tace

"Mabawa dadynku kudi akai maka gidansu muwadda sai kafadi wata nawa zaasa"

A raxane yadire cup din da yadauka yakai bakinsa,har yana kwarewa,yace

"Momy da wuri haka kuma ai bekamata kibada kudinkiba"

"To da kake cewa da wuri kai da sai yaushe kenan koko kafisan kaita zama da matarka dataki ta haihu,wancan cikin tace farhana ce to yanxu meyahanata haihuwa,dan haka kafadi lokacin dazaai bikin"

"Shikenan momy ai komai yana hannunki,sai yadda kikace"

Yafada yana kokarin tashi yafita,murmushin jin dadi tayi tace to madallah,dariyar mugunta farhana tayi suka tafa da afifa sannan tace

"Gaskiya momy yanxu xamuyi biki"

Farhana kuwa cewa tayi ,"ai ni momy gidanma zankoma"

"Nima burina kenan ku koma can da zama aware muku daki"

Ihun murna suka sa,jalila kuwa shiru taimusu saboda ita yanxu batason abinda akewa safiyya,sai dai miskilancinta yahana taja safiyyan a jikinta.


Safiyya kuwa tunda tai sallar asuba dakyar takoma gado ta kwanta,zazzabi mai xafine yarufeta,ga yunwa tanata kiran layin assadiq unforwad taki shiga,layin farhana takira sai da takusa tsinkewa tadaga

"Hello"

Dakyar Safiyya taamsa wayar tace tataimaka tazo dakyar taamsa can saigata tazo lokacin bacci yafara daukar Safiyya taxo saitin kanta tafara magana da karfi adan
Firgice tafarka tace

"Yauwa kanwata dan Allah taliya xaidafamin jollof da manja da attaruhu wlh banajin dadi"

"Allah yasawake amma dazakina kiranmmu da *kannan mijinki*kamar xaifi,

Daakwai komai a kitchen din"

"Da akwai"

Fita tayi tashiga kitchen din tadoramata girkin maimakon. Manja da attaruhu,sai tasamata mankuli da tattasai da kifi,tai kaca kaca da kitchen din ta hautsina parlorn har dasu ledar maggi tagama takai mata,lokacin xaxxabi yaci karfinta tajuya tai tafiyarta sai da tadanji dama dama sannan tatashi da kyar tabude abincin sabanin abinda tafadamata tagani ga karnin kifi ai fa nan tashiga amai abin tausayi

Assadiq yana dawowa yaga parlor kaca kaca,ga kitchen a bude tukunya a bakin kofa

Da bacin rai yadoshi dakin Sopy.

[1:03,PM2017]


*ยฎ๐Ÿ’ฆ๐Ÿ’ฆ๐Ÿ’ฆTALENTED WRITTERS FORUM*๐Ÿ’ฆ๐Ÿ’ฆ๐Ÿ’ฆ

*๐Ÿ’ฆTF*๐Ÿ’ฆ


_**KANNAN MIJINA_**
๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘ง



*NA*

*NASEEBA I UBA*๐Ÿ’




_Nagode da kulawar ku gareni fans nasami sauki_*Allah yakaramana lpy Ameen*๐Ÿ‘๐Ÿป





_Dedicated 2 my family_*Alhj uba takarda gawo*๐Ÿ’˜





*43*



~~Tura kofar yayi ransa abace fuskarsa ba walwala,yashigadakin
Mezai gani safiyya ce kwance gefe kuma amai tayi duk tabata dakin,dahanxari yakarasa gabanta yana jijigata,

"Sopy sopy meke damunki"

"Dee mutuwa zanyi,daure min cikina,pls"

hankalinsa ne yatashi yarasa ma mexai fara
Bargon data rufa dashi ya yaye,abin mamaki bakomai jikinta,jiyayi
Wani abu yatsargamasa Dakar
ta yayi,yakaita toilet yahada ruwa mai dumi yaimata wanka yagasa mata jikinta yabarta cikin barb yafito yafara gyara dakin yakwashe gurin aman,ya gyara gadon tare da canja bed sheet din,yafesa air freeshner,sannan yakoma,ya dakkota,akan gado ya direta,ya bude wardrobe yadakko mata yar fingilar riga iya gwiwa lemon green
yasamata yadaure mata gashinta,da farin ribbon, yadakko turare,xaifesa mata,takarba sanshanawa tayi tai sauri ta mikamasa tace,


"Dee bawannan xakasaminba"

Karba yayi batare da yaimata maganaba dayan yadakko,yamika
mata tasanshana ta daga masa kai alamar ya samata,karba yayi
yasamata,yaja hannunta,yakaita parlor, yazaunar da ita kan kujera yakunna mata kallo,kitchen ya koma,yadakko mata tufa da abarba yasako a plate yakawo mata agabanta yadire mata,yakoma kitchen
din yafara gyarawa,kallon kofar kitchen din tayi,tana mamakin halin assadiq dama haka yake da fushi,tufa tadauka tafara ci,
Sai da yagyara kitchen
din tsaf ya wanke kwanikan tambayar kansa yake wa yayai Girki a kitchen bashi da wannan amsar dan bazai kula Safiyya ba,

Yana gamawa yadawo
Parlor,ya gyara tsaf kallonta yayi yaga tana lumshe ido,taimasa kyau kamar baby,yakoma bedroom yashiga toilet yai wanka,yashirya cikin riga arm lace green,da farin 3quater yafesa turaran da Safiyya takeso,yafito parlorn ganinta yayi tayi bacci da tufa ahannunta,girgiza kai yayi,yakarasa gurinta ya zare tufar,yasami kusa daita yazauna,yadora kanta
Acinyarsa,yashiga yimusu pics tanata baccin,yagama yaxubawa kijinta ido,yana bukatar safiyya amma yadau alwashin hadiye shaawarsa,kissing dinta yayi ya maida hankalinsa ga tv ahaka shima bacci yaigaba da shi.




Yau su Alhj salihi da yayan Alhj Muhammad mai nasara suka kai kudin auran muwadda murna gurin momy da maman muwadda,
abangaran assadiq kwa besan ankaiba,

Yau tunsafe ummin Safiyya take tunanin yartata,cewa tayi da yayarta Amina taje tagano mata lpyr ta shiryawa tayi tazo akulle taga gidan tanata bugu a rufe,takira wayarta no answer shawara data shiga gidansu assadiq ta tambaya,karasawa tayi tashiga gidan mai gadin ta tambaya masu gidan suna nan
Yaamsa da eh,

Shiga tayi farhana ta tarar a parlor suka gaisa kamar bata ganetaba,ta tambayar ta tayi su safiyya sauna nan,
Shiru tai can tacemata

"Basanan suntafi gidan su kishiyar safiyya,yau mafa aka kaimasa,kudin auransa.

Shiru Amina tayi bata fahimci zancan datakemataba,tashi tayi taimata sallama tatafi.











*NASEEBA. GAWO*โœ๐Ÿป
[6:00PM,2017]



*ยฎ๐Ÿ’ฆ๐Ÿ’ฆ๐Ÿ’ฆTALENTED WRITTERS FORUM*๐Ÿ’ฆ๐Ÿ’ฆ๐Ÿ’ฆ

*๐Ÿ’ฆTF*๐Ÿ’ฆ




_**KANNAN MIJINA_**
๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘ง



*NA*

*NASEEBA I UBA*๐Ÿ’




_Inabawa masoyana hakuri sakamakon kadan da page 43 yayi hakan yafaru ne sakamakon wata yar Marsala_ *Nagode*๐Ÿ‘Œ๐Ÿป





*44*




~~safiyya ce tabude idonta taganta akan cinyar assadiq daga kanta tayi ta zuba masa ido,ahankali tashafi sajen fuskarsa
Cikin bacci yaji anashafa masa fuska idinsa yabude,ya kalleta murmushi taimasa,yadauke kansa gefe,yajanyeta daga jikinsa,yana kokarin tashi wayarsa tai ringing momy yagani ajikin screen dagawa yayi

Momyna ina yini"

"Lpy lau kazo inason ganinka"

"To gani nan momy"

Janyeta yayi yatashi,ahankali ta kira sunansa

"Dee,
Jiyowa yayi yazuba
Mata kyawawan idon
sa,idonta ne yakawo
Kwallah yawuce yatafi

Yana fita suka hadu da
Yaya amina suka gaisa,take cemasa tazo basa nan yace suna ciki bainda sukaje tawuce shima yakarasa gida .

Sanda yashiga momy
tana kitchen tanaiwa dady tuwon alkama gaisheta yayi yaja kujerar dining din kitchen yazauna yace

Momy sannu da aiki,
tuwon akemana ne"?

"yauwa assadiq zakaci
Kenan"?

"Zamuci momy Damian sopy bazata iya yimana girkiba"

"Saboda me"?

"Momy sopy batajin dadi kwana 2"

"Allah yasawake sai kuje asibiti ai,daman kiranka nayi infadi maka ankai kudin auran nan,ansa rana wata 7"

Shiru yayi yarasa mexaice karshe kitchen din yabari,yahau saman
dady.yana shiga yatsuguna gaban dady
yagaisheshi,yamika masa furar datake gabansa

"Sadauki lpy dai ko,ko da matsala ne"?

"Aa dady bakomai,kawai dai yanayin rayuwa ne sai
ahankali"

"Sadauki ita rayuwa taka ke gani hakuri akeyi kaji dan haka dukkan abinda yatasoma kanutsu ka fuskanceshi kaji ko"?

"To dady nagode Allah yakara girma"

Ameen sadauki,ya matar taka"?

"Lpyt kalau dady"

"Dakar mata furar nan ka kaimata kayi katafi

Tashi yayi yaimasa sallama yasauka.




Amina nashiga tatarar da safiyya nata hawaye da sauri takarasa gabanta tadafa kafadarta tace,

"Safiyya meke damunki" kike kuka"?

Farhana tace bakwanan,kuma gashi
Nazo natarar kina kuka"?

Hawayen fuskarta ta goge,tadubi yayartata
tace,

Yaya Amina banajin dadi kwana 2 narasa mekemin dadi"

Takasa fadawa yayarta sirrinta domin
tasan *mijinta sirrintane*

Itama amina godiya taiwa Allah da yaruwarta batasan zancan kai kudin assadiq ba ta numfasa tace,

"Ysnxu safiyya dan baki da lpy sai kina yin
Kuka,har yanxu baki dena kukaba dan baki da lpy,bazaki girma ba
ko"


"Shikenan ya amina nadena,yasu ummi da baffa,?"

"Lpys kalau suna gaidaki"

Nan dai suka sha hirarsu tadada kwantar
Mata da hankali batabar gidanba sai data tabbatar ta saki ranta,sannan tabar gidan,


Tashi tayi takuma yin wanka sakamakon zafin da takeji, tanacikin wankan assadiq yashigo da kulolin abinci ahannunsa,yaduba bedroom bata ciki karar zubar ruwa yaji a toilet yasami gefan gado yaxauna,ya zubawa kofar toilet din ido,bejima,da zamaba tafito daga ita sai towel da dankarami akanta tana tsane gashinta,tataho da baya da baya,tana yanwake wakenta bata saniba tai karo da kafar assadiq kansa tafada,takwalla kara,

Garin yunkurin tatashi
towel din jikinta yakwance,da hanxari assadiq ya kuma janyota jikinsa,ahankali yace,

Shiiiiii
Shiru tai taruntse idonta kasa jurewa assadiq yayi da fushin da yake yashiga sarrafa safiyya,jikinsa har rawa yake batason abinda yakemata,tunowa da fadan dasukayine yasa

ta hakura tabarshi yai yadda ransa yakeso daita daga karshe takasa jurewa tasamasa kuka,rarrashinta yashi
ga,yi da kyar yasamu
tai shiru,sai da komai
yalafa sannan yakalleta tayi lamo ajikinsa,yace

"Sweet sopy kinmin laifi amma bakiiya bani hakuriba ko"

Ashagwabe tace Dee,wlh bansan laifin danai makaba"

Nan suka warware matsalolinsu suka shirya masoyan asali kenan๐Ÿ’™

wanka sukayi suka shirya cikin kananun kaya rigunan ja anrubuta lovers da farin rubutu,sukasa bakin jeans sunyi kyau sosai,parlor suka koma sukaci tuwon da yataho musu dashi,sunaci suna tsokanar juna wayarsa
ce tahau kara safiyya ce tadaga batre da tasan wayeba,

"Muwadda ce tace bawa mijina wayar,mana

Wayar tamikamasa tacire hannuta daga cikin abincin takoma kan kujera ta kwanta.




















*NASEEBA GAWO*โœ๐Ÿป
[5:57PM,2017]


*ยฎ๐Ÿ’ฆ๐Ÿ’ฆ๐Ÿ’ฆTALENTED WRITTERS FORUM*๐Ÿ’ฆ๐Ÿ’ฆ๐Ÿ’ฆ

*๐Ÿ’ฆTF*๐Ÿ’ฆ




_**KANNAN MIJINA_**
๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘ง



*NA*

*NASEEBA I UBA*๐Ÿ’




_Inaiwa daya daga cikin *talented writers forum*jaje bisa ga abinda yasameta wato_*maman fareeda*_mai littafin danmaliki mai ruwan nairori_ Allah yakara lpy sis Ameen๐Ÿ‘๐Ÿป










*45*


~~~ Kashe wayar yayi yakoma kusa daita yashiga aikin rarrashi da kyar yashawo kanta ta sakko suka ja abincincinsu suka fara ci dakansa yakebata abincin suka ci suka koshi tadubeshi tace,


"Dee gaskiya momy taiya girki,dama xandinga samun tuwonnan kullum"

"Zanfadamata sopy sai adinga yimiki"

"Nagode Dee"

Tashi tayi zata kwashe kwanikan yadakatar daita dakansa yakwashe yakai kitchen binshi tayi da kallon kauna a haka yadawo yatarar ta zubawa kofar kitchen din ido kallonta yayi yace,

"Yade,matar assadiq ko mukoma ne"

"Dee ina"?

Dariya yayi yabata amsa da inawa"

Nibansan inawaba"

"Kinga tashi mushirya inkaiki asibiti dan atabbatar min da zargin danake,sopy yanayinki kamar mai ciki"

"Dee bawani ciki,malaria ce"

"To malaria, naji tashi mushirya muje"

Daki suka shiga sopy tadakko bakar abaya tasa,mai adon stones silver, assadiq kuwa dakayan jikinsa yafita,suka jera suka fita xuwa gurin mota,yabudemata tashiga,shima yazaga mazaunin driver yazauna,harzai tada motar tadubeshi ashagwabe tace,

"Dee,pls bari indakko furar da dady yabayar ka kawomin kaji"

"Dacan meyahanaki sha,kawai kinason batamin lokacine inmundawo kyasha"

Dauke kanta tayi bata kuma maganaba,yasa hancin motarsa,yafice
Tunda suka tafi hanya
Yakemata hira,taimasa
Shiru,can yajiyo yadubeta,yakira sunanta da wata irin murya,

"Sweet sopy meyafaru kinajina inata magana"

Shiru takuma yimasa ahankali yalalibi hannunta yahada cikinnasa ya matsa,kara tasaka tajiyo da fuskarta mezai gani hawaye take,gefan titi yasamu yai parking ya jiyo yafuskanceta yace,

"Matar assadiq kukafa,meyasameki,
Meye dalilin xubar hawayenki Sopy"

Rushewa tai da kuka,nan hankalinsa yatashi,da shashsheka tace,

"Bayan kaine kahanani dakko furata"

Dariyama abun yabashi yace shikenan dalilin kukan sopy"tissue yazaro yashiga goge mata hawayanta yace

"Karki kuma zubar da hawayanki akan wata fura,mufara zuwa insai miki,wata,shagwababbiya kawai,yafafada yana lakacemata hanci,

Shagon daake saida fura yanufa,yasiyamata roba biyar yamikamata
"Gashi ai tasha,kar a kuma yiwa assadiq kuka"

Karba tayi tana dariya
tabude,roba daya tafara sha tace,

"10q my handsome Dee"

Asibiti suka karasa kai tsaye, office din likita suka shiga,aka shiga duba safiyya atake likita yagano safiyya nadauke da ciki na 3 assadiq murna baa magana,yarubuta musu magani suka taho,tun ahanya yake tsokanarta da mai ciki, dariya kawai taimasa,

gidansu assadiq suka wuce,lokacin duk suna parlor suna kallon arewa 24,sukai sallama suka shigo,guri safiyya tasamu tazauna,tagaida momy
taamsa da sakin fuska
Sai abun yabawa Safiyya mamaki,jalila ce tagaisheta,taamsa,
tashi tayi ta kawo mata lemon kwa kwa,abun yabawa su farhana haushi ko kallon inda safiyya take basuyiba,sai itace
taimusu magana ba kunya suka amsa,assadiq ya kallesu kawai,momy ce tadubi dannata tace

"Assadiq inafatan kaje gidan su muwadda"

"Momy banjeba,amma
amma zanje"

"Yakamata kam"

Shiru safiyya tayi tarasa gane me momy take nufi amma tabarwa ranta,assadiq ne yace sopy tashi mutafi,sallama sukaiwa momy sukatafi,


***************

Haka rayuwa tacigaba datafiyarwa safiyya yanxu cikinta nada wata 7 ,yafito tadada kyau,**kannan mijinta*
*Readers kuyi hakuri da gibin daaka samu*๐Ÿ‘๐Ÿป


_cigaban_*45*


*kannan mijinta*
basu fasa mata rashin kunya ba yanxu iskancin dasukemata kullum a gidanta suke yini subata mata gida sutafi subarta da gyaran gida batace musu kala,yanxu hakama tana kwance tagaji kwana 2 assadiq baya barinta tana isashshan bacci ga jikinta yanadada nauyi,kallon take bacci yadauketa kawai sai jin hayaniyar mutane tayi a parlorn ga karar TV daaka kure,farkawa tayi adan tsorace afiface da kawayenta su uku,binsu tayi da kallo,tanadaga kwance ga wani ciwon kai da yamatsamata,ahankali
tadubeta tace

"Haba afifa yazaku ahigo min gida kuna hayaniya wai baku kula da halin danake cikiba"


"Hmmm sannu mai gida tayaya zamukula kekuwa ga makafi,kedai har abada bazaa rabekiba to ki kwantar da hankalinki munkusa dena xuwanniki daki,amma bazaki hana mu zuwa gidan yayanmmuba"

Daya daga cikin kawayen ce mai suna
Basma tace

"To ma inbanda abinki aunt safiyya meye naki na magana nagafa gidan danuwansu ne,duk tsiya kan yasameki su yafara samu ko"?

"Ke dakata banason iskanci kinji ko,rufe min baki ke kuma a wa"?
Dalla kufitar min daga gida"

Fita sukayi afifa tagama harar ta sannan tawuce suna fita tadafe kanta takoma ta kwanta.


Suna fita kai tsaye gida afifa tanufa tacewa momy safiyya ce ta korota,takuma mareta a lokacin assadiq yana zaune momy tanaimasa bayani kan auransa da muwadda,sai yarasama mexaice yasan karya takewa matarsa amma beisa ya karyataba yanxu momy tahau shi da fada,ai kuwa nan tahau balai danme zataiwa yarta haka dan suna
*kannan mijinta* ai bekamata tanai musu hakaba,amma bakomai tacigaba lokacintane wata rana ko da kudi akace taiyi bazatayiba mai da dubanta tayi ga assadiq

"Kafadamata maganar auranka da muwadda"


"Aa"

"To sai yaushe kenan kana tsoran fadamata ne ko me,to ni xanfadamata da kaina"


"Momy pls kiyi hakuri xanfadamata kinga yanayin datake ciki baason abinda zai dagamata hankali"

"Hmmm yayi kyau assadiq, nan da sati 2 su hannatu zasu dubai hado lefe,nayi waya da faruq yafara siyan wasu kayan kan su karaso"

"Allah ya kaimu"

Yatashi yafita ransa ba dadi gidansa yanufa yatarar da safiya kwance tadafe kanta da sassarafa yakarasa gabanta yakira sunanta,

"Sopy sopy,meyasameki"

"Dee kaina ciwo yake"

Magani yadakko yabata tasha yaragemata kayan jikinta cikinta yakalla yaga yadada girma ga babyn sai motsawa yake ahankali,tanashan maganin tadan sami afuwa soyayi yafadamata auransa da muwadda amma yanafargabar abinda zaifaru. Rungumeta yayi yashiga bata hakuri akan abinda afifa taimata kuka tasamasa nan hankalinsa yadada tashi.


*kai wadannan kannan miji*๐Ÿคฆ๐Ÿปโ€โ™€
















*NASEEBA GAWO*โœ๐Ÿป
[10:37Am,2017]


*ยฎ๐Ÿ’ฆ๐Ÿ’ฆ๐Ÿ’ฆTALENTED WRITTERS FORUM*๐Ÿ’ฆ๐Ÿ’ฆ๐Ÿ’ฆ

*๐Ÿ’ฆTF*๐Ÿ’ฆ






_**KANNAN MIJINA_**
๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘ง




*NA*

*NASEEBA I UBA*๐Ÿ’.







_Har yanzu inamaraba da masu yimin gyara gameda rubutuna ko kuma labarina burina bewuce fadakarwa ba tare da isar da sakon gyara a zamantakewarnu da yanuwanmmu_
```zaaiya samuna ta wannan number``` ~07037732029~ ```Taku``` *Naseeba ismail uba*๐Ÿ’









*46*






~~~yunkurawa tayi tatashi da kyar yamike da hanzari zai riketa dakatar dashi tayi tahanyar dagamasa hannu tajanye jikinta ahankali taketakawa takoma daki ta kwanta
Kukane yaci karfinta tadau wayarta tashiga neman layin yayarta rukayya,

Biyota yayi dakin yazauna kusa daita wayar hannunta yakarba yanadubawa yaga yayarta take kira katse Kiran yayi,yaajiye wayar yakamo hannunta yahada danasa ahankali ya kira sunanta,


"Sweet sopy,yakamata kisaurareni kikuma fahimceni,wlh bani da yadda xanyi akan abinda yake faruwa kisa a ranki bawanda yaisa yashiga tsakani na dake"

Hawayen fuskarta ta goge,tace


"Dee nagaji da jin kalamanka kullum karatu daya kakemin nazaci sama kake dasu farhana,meyasa amatsayinka na babba baxaka tsawatarmusuba"


"Sopy darajar momy sukeci banason abibda xanjayo momy taifushi dani kitaimaka min wajen yimata biyayya
Pls"

"Naji but yau inason kafadan gaskiya make tsakaninka da muwadda ,Dee karkaboyemin komai koda hakan yana nufin mutuwata"

Shiru yayi yadada damke tafin hannunta cikinnasa tare da xubamasa kyawawan
Idonsa,yace



"Safiyya kiyi hakuri daabinda xanfadamiki amma kisani bani da hannu cikin lamarin kuma baason raina zanaikata hakanba,umarni ne na momyna"

Nan yabata labarin auransa da muwadda tundaga farko har karshe,ido yazubamata yana karantar yanayinta,
Shiru tayi tarasa ma mexatace jitayi dancikinta yahautsina yajuya kara ta kwalla tafara murkususu,hankalin assadiq yai masifar tashi,a gigice yadauketa yakaita asibiti yaya hannatu yaiwa waya yafadamata hankali atashe ta barwa mai aikinta su nabil tanufo asibitin assadiq ta tarar yanatafaman zirga zirga hankalinsa tashe,tambayarsa tayi

"Meyafaru da safiyyan daman watan haihuwar Yakama ne"


Girgiza kai kawai yayi saboda yadda hankalinsa yatashi,likitane yafito yace yabiyoshi office binsa yayi yasami kujera ya zauna likita yagama rubuce rubucansa yadago dafuskarsa mai dauke da farin glass yace,


"A gaskiya yarinyar tanada damuwa gsky damuwarta zata iya haifarmata da matsala
Yakamata abata kulawa ko dan babyn dayake cikinta"

"To shikenan doctor nagode inshaallah zaakiyaye "
yarubuta mata magunguguna yai masa sallama yafita,

Dakin daaka kwantar da safiyya yanufa yaya hannatu ce zaune kusa daita yakarasa gaban gadon yazauna yashafi cikin jikinta tanata bacci numfashi take a hankali,yadubi yayarsa yace,

"Yaya narasa yadda zanyi da maganar aurannan banaso banason abinda zai jawowa Safiyya damuwa,ga iskancin yarannan"

"Assadiq wai meyakawo safiyya ta
shiga cikin wannan halin"

"Nan yabata labarin abinda yafaru nanta rufeshi da fada danme zaifadamata zancan auransa da muwadda,yai shiru kansa yaixafi yarasa dame xaiji,safiyya ce tamotsa tabude idonta tadorasu kan assadiq suka hada ido yasakarmata murmushi,dauke kanta
tayi takalli yaya hannutu tace ya hannatu zansha ruwa

Assadiq ne yadakko ruwan zaibata tadauke kanta,yayi yai tasha taki yaya hannatu ce takarba tabata tasha,bayan tagama sha,tace yaya dan Allah kikaini gurin ummina,bazaniya zamaba,tagama fadar haka tasa kuka,nan hankalin assadiq yatashi,

"Kiyi shiru safiyya kiyi zamanki adakinki kinji

Karkibari shaidan yashiga zuciyarki,mijinki yanatare da ke,nima kenake so ba muwaddaba"

I do safiyya tazubamata can tace yaya kiramin ita,

To zankira miki ita,kiran ummi akai bayan sungaisa da yaya hannatu takefadamata rashin
lpyyr Safiyya hankalin
Ummi yatashi,tabawa Safiyya wayar suka gaisa tace ta kwantar da hankalinta zasuzo anjima,sukai sallama

Ran yaya hannatu ne yabaci tace bari taje gidan,safiyyace tariketa tace

"Dan Allah yaya karki tafi kibarni"

"Safiyya ga mijinki zai zauna dake yanzu zandawo"


Shiru tayi taxame jikinta takwanta tare da runtse idonta batason ganin assadiq a halin yanxu.


Kai tsaye yaya hannatu gidansu tawuce tanazuwa tafara zazagawa kannanta balai momy ce tafito daga kitchen tadubi hannatu tace,

"To uwar fada daga Ina
Kike,daga xuwa sai ki hau yara da fada shiyasa fa basazuwa gidanki wlh"

"Momy bakisan Safiyya tana asibitiba
Kuma ciwonta nada nasaba da yaniskan yarannan.

Ran momy ne yabaci.










*NASEEBA GAWO*โœ๐Ÿป




K
[7:49Pm,2017]


*ยฎ๐Ÿ’ฆ๐Ÿ’ฆ๐Ÿ’ฆTALENTED WRITTERS

Please Login or Register in order to submit comment