Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tace


" wlh Dee mutukar bakajeba to gida xantafi "

" sopy saboda abinda be shafeki ba xaki ce xaki tafi gida to baxanjeba ki tafin inkin tashi tafiya ki ajiye min 'yata "



" shikenan Assadiq "



Kayanta tafara hadawa a akwati tagama tsaf tamika masa fadila taja akwatin ta tanufi kofar parlo. ๐Ÿ™†๐Ÿป














*NASEEBA GAWO*โœ๐Ÿปโœ๐Ÿป
[9:32Pm, 2017]



*ยฎ๐Ÿ’ฆ๐Ÿ’ฆ๐Ÿ’ฆTALENTED WRITTERS FORUM*๐Ÿ’ฆ๐Ÿ’ฆ๐Ÿ’ฆ

*๐Ÿ’ฆT F*๐Ÿ’ฆ




*KANNAN MIJINA*
๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘ง



*NA*

*NASEEBA I UBA*๐Ÿ’





*TALENTED WRITTERS hadin kanmmu shine alfaharinmmu*๐Ÿค๐Ÿค




*Allahu akbar Allahu akbar Allahu akbar walilahil hamd*





*67*



~~~cikin sauri ya sha gabanta akwatin ya rike yaxuba mata sexy eyes dinsa dauke kanta tayi cikin sanyi ya kira sunnanta,


"Sweet sopy akan wata can daban xaki tafi kibar ni yanxu xaki iya rabuwa dani da tilon yarmu kinsan baxantaba iya rayuwa bake ba "


" Assadiq sakar min jaka nagaji yakake so inyi da raina da me xanji "

Takarashe maganar da kuka mai tsuma xuciya tausayi tabashi hannun ta yaja suka koma gefan gado suka xauna dubanta yayi yace


" sopy pls kiyi hakuri ki dena kukan haka bazan iya jure jin ki kina kuka ba yanxu me kike so inyi miki "


Shiru taimasa sai da yai ta aikin rarrashi sannan ta dago ta dubeshi tace

" in har kaga na zsuna to wlh kaje diner din bikin nan "

" shikenan inde naje hakan xai faranta miki rai "

" ummm "

" shikenan safiyya xanje amma su waye suka xo gidannan tsakanin jiya da yau "

" ba kowa"


"karya ba halinki bane saboda haka fadamin gaskiya "

" momy ce tazo "


" shikenan tashi ki taimaka min inshirya Allah ya huci zuciyarki mata ta "

Fadila ya mika mata tanata bacci kwantar da ita tayi tahada masa ruwan xafi yashiga yai wanka ta bude wardrobe ta dakko masa hadaddiyar shadda milk mai babbar riga da takalmi batozi sai silver din agogon axurfar sa mai kyau da tsada be jimaba yafito ta taimaka masa ya shirya ta fesa masa turare yafito a angonsa
Shiru yayi can yanisa yace

"Allah ya albarkaci rayuwar ki matar Assadiq nagode wa Allah da yabani mace mai hakuri da kawaici "

" Hmmm dawa zaku tafi wajen diner "?


" ke zaki kaini bazan iya tafiya ni kadai ba"

"bazan iya tukin dare ba ka kira B malik ya kaika ko achida "


" achida baya gari yaje mina ๐Ÿ˜œbut bari in kira B malik "


Wayarsa ya dauka yakira layin sa bugu daya yadaga bayan sungaisa yace yaxo gida yadauke shi yakai shi mina event center

Be jimaba ya karaso Sallama yaiwa safiyya ya fita yana fita takoma gado ta shiga rusa kuka ๐Ÿ˜ญ


_gsky auran Assadiq da Muwadda yataba xuciyar naseeba saboda ji nake kmr gaske duba da yadda safiyya takeji aranta Allah ka sauka kawa yanuwana mata radadin kishi_๐Ÿ˜ญ๐Ÿ‘๐Ÿป





Sai da tayi mai isarta sannan ta goge fuskar ta wayar ta ta dauka takira layin umminta tanata riging sai data kusa tsinkewa sannan ta daga



"Hello ummina kin manta dani ko "?


" haba safiyya ya xaai kice na manta da ke kar ki kuma fada "



" ummi kimin addua xuciyata xata fushe"

Tana gama fada takuma rushewa da kuka kyaleta tayi mai isarta sannan ta shiga rarrashinta da nasiha da shawarwari


"safiyya kiyi hakuri kinji kar ki duba ni ko yayar ki kowa da yadda Allah ya shiryamasa rayuwa kuma Allah yasan xaki iya shi yasa ya dora miki saboda haka ki daure kici jarabawar da Allah ya jarrabceki kinji ina nan inai miki addua


"to ummi nagode acewa najiba da yaya amina suxo gobe dan Allah su kwana saboda gobe xasuxo kafi "


" to shi kenan safiyya xasu xo kinji ki cigaba da addua Allah yakara hakuri "


"Ameen ummi nagode agaida baffa"

"zaiji agaida min da fadila "

" to ummina "

Sukai Sallama ta kashe wayar komawa tayi ta kwanta tai lamo tunani fal ranta




Tunda Assadiq ya fita kiran Muwadda yake shigowa da kmr bazai daga can ya daure ya daga




" ya Assadiq "

" naam ina jinki "



" I am waiting 4 u "

" I am on the way"


Yana gama fada yakashe wayar ya mai da hankalinsa ga abokinsa yace



"Hakika abokina in banda iyaye iyaye ne wlh banga dalilin da xai sa inkara aureba "



" to ya xaai chairman dole muyi yadda suke so fatanmmu dai Allah yaraba mu dasu lpy "

" Ameen B malik "




Suna Karasawa suka tatar gurin cike da kawayan amarya sunsha anko waya yaimata yace yakaraso farhana ce ta karaso ta bude masa murfin motar harara ya watsamata yafito Muwadda ma tafito daga cikin mota cikin shigar amare tayi kyau suka jera atare hannun ta tasa cikin nata binta yayi da kallo kawai kawayanta na biye dasu suna shiga yanuwa sukai musu caa yayin da DJ yasaki wakar ango da amarya momy ta shiga yaimusu liki maman Muwadda kuwa farin ciki fal ranta su ya hannatu kuwa suna gefe ita da jalila amarya da ango suka zauna a mazauninsu akaita hotuna biki yayi biki anci ansha anyi barin nera burin Muwadda yacika anyi bikin yar gata Assadiq Ya kagara atashi hankalinsa yana kan safiyya karfe 11aka tashi ko tsayawa beyiba yatafi sai neman ango akai aka rasa yatafi


Sanda yaisa gida safiyya tayi bacci kayan jikinsa yacire yashiga wanka yana fitowa yasa kayan baccinsa yakaraso gadon yadauke fadila daga jikinta ya mai data gadonta Yadawo ya kwanta jikinsa yajata ya rungume ta yana shakar kamshin jikinta yashiga sarrafa ta cikin kwarewa da kewa sai da yagama wasa da ita sannan ya sami bacci tana jinsa tai shiru




Washe gari aka tashi da daurin aure da kanta ta shirya shi cikin farin boyel babbar riga yayi kyau da kyar yatafi daurin auran shi da abokansa Ita ma tashirya cikin atamfa super purle tai mata kyau ta shirya fadila cikin kananun kaya masu kyan gaske su najiba kuwa tun safe suka xo yaya rukayya ce tai yo girki sai data gama sannan ta xo




Karfe 10 :30 aka daura auran Assadiq da Muwadda kan sadaki 100k nan sukai ta gaisawa da jamaa dady ma yana ta gaisawa da abokansa yar walima abokansa suka hada masa




"momy ma anata fama da jamaa gidan yacika da jamaa


Gidan safiyya ma yafara cika da jamaa anata hidima tasaki ranta ana gama daurin aure Assadiq Yadawo gida kai tsaye dakin sa ya wuce yamaida kofa ya rufe kwanciya yayi yana tunanin yadda xai kwana da wata ba safiyya ba




Karfe 4 yanuwan abban Muwadda suka xo gyara dakin amarya suka shiga dakin safiyya suka gaisa suka nufi dakin Muwadda yasha kayan alatu
Tun sannan gaban safiyya yaketa faduwa


Karfe bakwai aka kawo amarya kai tsaye gidansu Assadiq aka wuce daita mumy murna kmr ta goyata akwati guda tabata shake da kaya amatsayin siyan baki



Aka kaita gidan ta sai da aka kaita dakin safiyya inbanda kamshi ba abinda yake tacaba kwalliyar ta cikin hadaddiyar shadda combination da paper cofee da yellow tasha sakar gwal nan akai musu nasiha tabata rafar yan dari biyu da kwalin cingam suka dauketa xuwa bangaranta




Yan uwan safiyya kuwa Sallama sukai mata suka tafi tayi jugum ta rungume fadila


Assadiq kuwa yana daki akulle yakashe wayarsa.

















*NASEEBA GAWO*โœ๐Ÿป
[5:45Am,2017]



*ยฎ๐Ÿ’ฆ๐Ÿ’ฆ๐Ÿ’ฆTALENTED WRITTERS FORUM*๐Ÿ’ฆ๐Ÿ’ฆ๐Ÿ’ฆ

*๐Ÿ’ฆT F*๐Ÿ’ฆ




*KANNAN MIJINA*
๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘ง




*NA*

*NASEEBA I UBA*๐Ÿ’





*TALENTED WRITTERS hadin kanmmu shine alfaharinmmu*๐Ÿค๐Ÿค



*Allahu akbar Allahu akbar Allahu akbar walilahil hamd*





*sako zuwa ga wasu daga cikin marubuta hakika banji dadin yadda wata marubuciya taxage ta faffadi maganganu game da masoya littafinta ba ni aganina kaunace yasa suke bibiya be kamata ace kiyi amfani da wannan damar kifadamus maganganu marasa dadin jiba dan Allah mu gyara, shawara ce ๐Ÿ‘Œ๐Ÿปgyara kayanka baya taba xama sauke muraba*๐Ÿ™…๐Ÿป

*Ina yinku masoya online writters farin cikin ku shine burin naseeba*๐Ÿ’™







*69*




~~~mamaki ne yakama su suka shiga tambayar kansu me Muwadda take nufi kenan basu da wannan amsar cikin isa tadubesu tace


"afifa kina haukane da zakixo ki canja min tasha ina cikin kallo ko kuma kawai iskanci ne to wlh tallahi kar ki kuma yimin irin wannan dan bazan jure ba "


" Haba aunty Muwadda be kamata ace kina fada akan dan wannan dalilin ba "


" au farhana wannan iskancin datai min shine dan, ok yayi kyau Allah yabata Saa tayi gagarimi tagani "

Waje suka samu suka xauna suka gaidata taamsa a takaice ta maida hankalinta ga tv can farhana tace


" aunty na ina kaxar amarcin abamu mudan taba "

" Hmmm farhana kenan ai kaxar amarci layi ce dan haka sai kujira tazo kanku "

" kai aunty Muwadda dan Allah ki bamu, to shi kenan dafa mana ko indomie ce kinji "


" kut wacece xatai muku girkin wai ni, Hmmm ku tunda kuka sanni kuntaba ganina nayi girki to bari kuji girkina yana wuyanku dan kuwa ko xaku dinga yimin wlh "


" angama auntyn mmu, yanxu dai bari mudafa indomie "


" ku ta shafa fitsararru kawai "


Takoma ta kwanta kitchen din suka shiga ya hadu komai blue da fari suka kunna gas suka hau dafa indomie da kwai basu dadeba suka kammala suka juyota a plates suka dakko lemo suka fito tana xaune ta dora kafa daya kan daya ta dube su tace


" guda nawa kuka dafa "?

" guda uku ce aunty "


" Hmmm sai kubani inci inrage muku ai "

" kixo dai muci tare ko "

" saboda raini xanci abinci da ku dalla malamai kubani "

Bashiri suka mika mata taci rabi tabasu rabi suka karba suka ci abinda taje musu suka maida plate din kitchen suka dawo suka xauna dubansa tayi tace

" inafatan kun gyara min kitchen din "


" Eh angyara "


Sallamar kawar tace takatse mata maganar da xatayi ita da kanwar muktar suka xo ta tashi ta rungume su tana murna ta shiga kitchen ta dakko musu kaxar da suka ci da daddare da lemo ta hado musu da katuwar fresh milk ta kawo musu su afifa suna xaune suna kallon ikon Allah ta dubi kawar tata tace


"kawata bisimilla rushuda ya muktar da umma "?

" Lpy kalau aunt Muwadda suna gaisheki "

Ina amsawa"

Rushida ce tamai da dubanta ga su farhana tace


"afifa kuxo muci mana "

Caraf Muwadda tayi tace" kirabu dasu yanzu suma sukaci nasu ku de kuci "


Mamaki tabasu sukai mata shiru safiyya ce tai Sallama tashigo cikin mutunci suka amsa banda su farhana abinci ta kawo musu Muwadda tace


" farhana ko afifa ku karbeta mana kun tsaya kuna kallon ta, aunty sannu da aiki "


" yauwa sannunku "

" ina fadila "

Dee yakaita gidan momy"

Tana gama fadar haka tafita tana yaba haduwar dakin Muwadda aranta take mamakin yadda su farhana sukewa Muwadda biyayya safiyya na fita Muwadda ta maida dubanta garesu tace

Afifa dakko mana plates a kitchen "


" kai aunty Muwadda wlh nagaji "


" oh ni xan dakko ko me dallacan jeki dakko mana banza kawai "


Tashi tayi ta dakko ta kawo tace farhana taxuba musu xubawa tayi tamikawa kowa taxuba nata da na afifa
Suka kammala tace su kwashe Kwanikan su wanke ba musu suka wanke Kwanikan suka gyara kitchen din tsaf cewa tayi su gyara parlon taja su rushida suka koma bedroom farhana ce ta dau mayafinta tai tafiyarta afifa ce ta gyara parlon takunna turaran wuta dakin tashiga ta taga tabaje musu kayan lefan ta suna xabar atamfofi da kayan kwalliya Muwadda ce ta dubeta tace

"yadai menene?


"aunty Muwadda mungama xan je gida "


" farhana fa?


"ta tafi tun dazu "


" au batai aikin ba, lallai yayi mata kyau "

Janbaki tabata da hoda sai jagira da body spray tace tagaida gida fita tayi tana mamakin halin Muwadda tana xuwa gida ta tatar da su farhana a parlo kayan ta zazzage a kasa momy ce ta dubeta tace

" afifa wannan kayan fa Saa tace abawa "


" Hmmm nawa ne aunty Muwadda tabani "


" kai kai dan wannan kayan tabaki cab "

Cewar jalila tana kokarin sauke fadila daga bayanta momy ce taamshe xancan tace


" to ina lefi abinda xaa rabawa dangi shiyasa nasa aka xuba mata su da yawa "


" kunga kayan data ke hadawa kawarta da yar kanwar abbansu da yawa wlh "


" bayason korafi afifa ku xauna lpy da Muwadda kunga dai burinmmu yacika "

Sai yanxu farhana tasa baki ta dubi momy tace

" amma fa wlh mutukar xata dinga sa mu aiki wlh bazamu zauna lpy ba "


" to meye dan tasaku aikin ba yayanku bace "

Jalila dai dariya kawai take kunshewa ta dau fadila tafita dan kaita gida


Da yamma Assadiq ya dawo gida kai tsaye dakin safiyya yafara shiga tana kitchen ta xaunar da fadila a kujera tana ta cin biskit yashiga tana ganinsa ta tashi ta rungume shi

Oyoyo papa "


Oyoyo Fadilaty binty"

Safiyya ko juyowa batai ba tai masa sannu da xuwa rungume ta yayi ta bayanta ahankali yace


I miss u Sweet sopy "

" Hmmm Dee kenan kai da kake da sabuwar amarya pls cika ni inkarasa aikina "


" sopy Assadiq yayi laifi ko "?

Kunnansa yakama yace

" natuba matar Assadiq ayi hakuri nadena "

Dariya tayi kuma rungume ta yayi yafara kokarin zura hannunsa a rigar ta rike hannunsa tayi ta girgixa masa kai alamar yabari hakura yayi ya sakar mata kiss yafita da fadila bangaran Muwadda yanufa tana xaune tana kallo tacaba kwalliya cikin english wears

Cikin sauri takarasa ta rungume shi

"welcome honey I miss u "

Thanx Muwadda I miss u too"

Hannu ta mika da niyar karbar fadila taki yarda
Assadiq ne yace

"Muwadda bari inje Inyi wanka "

" aa nide tare xamu tafi gsky honey "


" ok muje "

Fita sukayi yafara kai fadila gurin safiyya da kyar ta yarda tana ta kuka

" papa "

Safiyya ce ta rungume ta yarinyar tabata tausayi da dane Assadiq bazai rabu da fadila ba amma gashi saboda yayi amarya sai rawar kafa yake


Suna shiga dakinsa Muwadda ta dubeshi tace

" honey inxo intayaka wankan "

Aa nagode baby"

Bandaki yashiga yai wanka yagama yafito daure da towel yakaraso gabanta yace

"baby baki fito min da kayan da zansaba "

" honey ai bansan wanda xaka sa ba "

" ok yayi kyau "

Jallabiya ya dakko fara tas yasa yasami gefenta ya xauna amma hankalinsa yana gun safiyya tashi yayi yafita kacibus sukayi da ita xata kawo musu abinci fadila na biye da ita Assadiq ne xai dauketa tamake kafada tayi fushi surar ta yayi suka sa dariya shi da safiyya ahaka suka shiga Muwadda tana ganinsu taraina kanta yadda taga safiyya ta caba kwalliya cikin dandatse tsan lace dinta taiwa fadila ma kwalliya gashi sun shigo suna dariya kayan abincin taajiye cikin yauki tacewa safiyya

"sannu da aiki aunty "

" yauwa amaryar Assadiq "

Wani kallo Assadiq yaimata tai dariya kasa kasa taxuba musu abincin a plate daya suka fara ci Assadiq yana ta santi yanai taiwa safiyya hira ga fadila tanata tsalle a jikinsa du haushi yahanata cin abincin bayan sungama yace su shirya suje sugai sa da dady yadubi Muwadda yace



"Muwadda kitai makawa sopy ku fitar da Kwanikan daga nan ki canja kaya "


Bata amsaba ta kwashe Kwanikan haduwar dakin safiyya yabata mamaki kitchen dinmma ya tsaru dakinta ta koma ta dora abaya tafito abakin kofar Assadiq suka hadu suka rankaya suka tafi

Parlon ba kowa sai jalila da hanzari ta karaso ta taresu fadila na ganinta tafara murna momy naganin Muwadda ta Washe baki ita kuwa haushi ma momyn tabata.






07037732029 ๐Ÿ‘ˆ๐Ÿป




*NASEEBA GAWO*โœ๐Ÿป
[4:41Pm,2017]



*ยฎ๐Ÿ’ฆ๐Ÿ’ฆ๐Ÿ’ฆTALENTED WRITTERS FORUM*๐Ÿ’ฆ๐Ÿ’ฆ๐Ÿ’ฆ


*๐Ÿ’ฆT F*๐Ÿ’ฆ





*KANNAN MIJINA*
๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘ง



*NA*


*NASEEBA I UBA*๐Ÿ’






*TALENTED WRITTERS hadin kanmmu shine alfaharinmmu*๐Ÿค๐Ÿค



*Allahu akbar Allahu akbar Allahu akbar walilahil hamd*




*sakon fatan alkhairi ga daukacin musulman duniya musamman alhazan mmu ina rokon Allah yabasu arfa mai sauki yakarbi ibadunsu damu baki daya ubangiji yabamu alkhairin wadannan gwala gwalan ranaku Dafatan xamuyi shagulgulan babbar salla lpy AamEEN*๐Ÿ‘๐Ÿป


*littafin KANNAN MIJINA daga wannan page din yatafi hutun salla babba Allah yasa ayi lpy agama lpy*๐Ÿ’•








*70*





~~~~cikin ranar jiki momy takaraso ta rungume Muwadda guri safiyya tasamu ta zauna gefenta Assadiq yazauna momy a kujera mai cin xaman mutum uku momy da Muwadda suka xauna safiyya ce taxamo daga kan kujera tace


"momy barka da dare "

" yauwa yagida"

"Alhmdulillah momy"


Ran Assadiq ne ya sosu da irin yadda momy taamsa wa safiyya shima ya gaisheta ya tashi ya hau saman dady yabarsu
Muwadda ce ta maida dubanta ga momy tace

"momy na ina yini "


" Lpy kalau 'yata, dafatan ba wata matsala ko "

" eh momy "

" yauwa duk wanda yabata miki rai kimin waya kafada min kinji ko "

" to momy na, su afifa fa?

"suna dakinsu basu san kinxo ba "

Kwalla musu kira tayi suka amsa can sai gasu nan sun fito safiyya tana xaune ita da jalila suke hirarsu suna fitowa suka ga su Muwadda da murnar su suka rungume ta


" oyoyo ga amaryarmu ga amaryarmu "

Dariya ta sakar musu tare da rungume su ajikinta tace


" yanmatan kanne na kuna lpy ko dayake ma nayi fushi wlh, wai momy yarannan suka tafi daxu ko Sallama nahada musu kayan kwalliya suka ki tsayawa su karba "

" amma baku kyauta ba farhana ku da yayarku xaku tafi bakuyi mata Sallama ba "


" kai momy

"yimin shiru afifa banyarda wani yasabawa Muwadda ba daman inason jadda da miki ke safiyya kiji tsoran Allah kixauna da abokiyar xaman ki lpy ban yarda ki cutar min da 'ya ba inba haka ba xanbaki mamaki"


"to momy inshaallah xan kiyaye "

Wani irin tafasa xuciyar safiyya takeyi saboda yadda momy take nuna mata kiyayya jalila ce tace


" amma momy ai bekamata kiyiwa aunty safiyya fada ita kadai ba sai kihada da ita aunty Muwadda ki musu "


" jalila ni kike fadawa haka saboda rashin kunya oho saboda kin likewa yayanta shine xaki sa min baki ina magana ko, yayi miki kyau "


" momy kiyi hakuri amma na kula jalila bata farin ciki da aurena ashe kanwar saurayinta take tayawa kishi "

" haba aunty Muwadda ai mu muna sonki kuma muna yinki "

Cewar afifa safiyya sai tarasa ma me xatace fadila ce fara kuka ta karbeta a hannu jalila tafara bata nono momy ce ta dubeta tace

" wai sai yaushe xaku yaye yarinyar nan abinda bata xuwa ba kuma abinda bataci amma kinki yaye ta haba "

" ke kuwa momy ba yar so bace yaushe xaa rabata da nono "

Cewar farhana kenan takarashe maganar tana kokarin daga wayar ibraheem cikin bacin rai Assadiq ne yasakko daga saman dady yadubi safiyya yace

" sopy kuxo muje kugaisa da dady"

Muryar sa fadila taji tasaki nono tafara kiransa

"papa"

"Fadilaty binty kindena fushin dani "


Daukar ta yayi yahau saman su safiyya suka bi bayansa da Sallama suka shiga cikin sakin fuska dadyn yaamsa sallamar su guri suka samu suka xauna safiyya ce tafara gaida shi

" dady barka da dare "

" yauwa 'yata kuna nan kalau ya matar tawa sarkin hada hada tazo tai tai min yaran da bana ganewa "


" Lpy kalau dady ai wai dole sai tayi magana "

" mashaallah"

"ina yini dady "

"Muwadda kina lpy ya bakunta"

"Alhmdulillah "

" naji dadin xuwanku badan komai ba sai dan intunasar daku xaman tare musamman ma kai sadauki kaine shugaba ka kula kabawa ko wacce hakkinta in matanka sun hada kai sun xauna lpy to daga gareka ne in aka samu matsala to daga gareka ne sadauki ku kuma

Kuhada kanku ku xauna lpy banda tashin hankali musamman ke Muwadda kace karama dole sai kin girmama safiyya dan gaba take da ke haka kema safiyya kibata hakkinta na kanwarki kunji Allah yaimuku albarka yabaku xaman lpy "

Suka amsa da ameen kimar dattijon tanunku a idon safiyya fadila ce ta dau huular dadyn tasa masa suka sa dariya dady yace


" lallai fadila ana auran da dady to ke da momy ba ruwana "

" dady ai kaimata tsufa dama "

Cewar Assadiq suka kuma yin dariya ran Muwadda ne yabaci yadda ta kula dady nason safiyya sai ta kosa su tashi su tafi Assadiq ne yace

"dady bari muwuce"

"to ba laifi sadauki madalla gashi kabawa ko wacce dubu goma goma "

" Dady angode amma kabawa yayanka ayi tuya anmanta da albasa ni baka bani ba "

" Allah ystsareni dabawa ma gidanci kudina, kuje sai da safe "

Dariya Assadiq yayi suka fita suna sakkowa momy tabawa Muwadda wasu turaruruka masu tsada aleda safiyya ce tamikawa momyn wasu mayafe a wata yar jaka masu shegen kyau karba momyn tayi tace

" ke bakya gjy da hidima to angode fadila sai da safe sarkin kirinki Muwadda kigaida gida kinji "


" gida xaiji momy na nagode "

Assadiq yaimata Sallama shima bayan yabata kudi jalila ce tarakasu tadan jera da safiyya tana ta bata hakuri Muwadda kuwa sai nanewa Assadiq take ita ga me miji

Suna komawa gida kowacce tai bangaranta Assadiq kuwa bayan safiyya yabi da fadila a hannun sa tana shiga daki tiolet tashiga tahada ruwan xafi tafito hannu tasa xata dauki fadila yarike hannun nata ido yaxuba mata take yafahimci bacin rai afuskar ta cikin kwantar da murya yace

"matar Assadiq meyabata miki ranki haka na kula tunda muka taho baki magana ba "

Pls kabarni bacci nakeji bani ita wanka xanmata mu kwanta"

"barshi ni xanmata wankan ai bake kike mata wankan dare ba "

Matsawa tayi bata kula shi ba tafara kokarin cire nata kayan ta daura towel ta bude wardrobe din fadila ta dakko mata kayan bacci Assadiq kuwa tiolet din yashiga yaiwa dadilansa wanka yafito yana fitowa safiyya tai shigewar gaba daya Hankalinsa na kanta adaddafe yashirya fadila ya kwantar daita ban dakin yabi safiyya tana cikin wanke fuska taji shigowar sa cikin fushi tace

"waye ne?

Shiru yayi dauraye fuskar ta tayi taganshi dada daure fuska tayi tace

"Lpy dai ko dama baka gamaba na shigo sai infita "

" Karasawa yayi gab da ita ya hada bakin sa danata yafara tsotsa kuka tasa masa shi kuwa bemasan tanayi ba saboda yadda yai kewar ta karfi tasa ta tureshi ta daura towel dinta tafito kan gado ta hau tai ta kuka biyota yayi ya tsuguna gabanta cikin da kushashshiyar murya yakira sunnanta


Sweet sopy dan Allah kifadamin damuwarki in nine wlh baxan kumaba kiyi hakuri pls wlh sopy duk abinda kika ga inayi kafin hali nake na matsu in dawo gareki mata ta "

" ni ba abinda kai min kawai katafi kabarni kana shiga hakkin matarka "

" shikenan sopy xantafi amma kibarni inji dumin jikin ki pls "

Kan tayi magana ya rungume ta atare suka saki wata ajiyar xuciya xamewa tayi ta kwanta ta rungume fadila ba yadda ya iya sumbatar fadila yayi ya tashi kwan fitila yaja musu kofar yafita


Yana zuwa dakinsa wanka yayi yasa kayan bacci yakoma kan gadonsa ya kwanta tuna nin safiyya fal ransa jiyayi Muwadda shiru tashi yayi yabita dakinta kofar yatura yashiga bata parlo bedroom din yashiga hangota yayi can kuryar gadon cikin wata bingilar rigar bacci tanata shashshekar kuka da sauri yakarasa kan gadon yakira sunan ta

"baby kuka kuma meyafaru haka "?

Shiru taimasa tacigaba da kukanta yai ta magana damunta yayi ta tashi xaune tace


" pls katafi kabarni haka ka koma gurin matarka "

Kansa ne yadau xafi yarasa dame zaiji jikinsa yajata yafara rarrashinta tayi shiru yayi yai daita ta taso su koma dakinsa taki yahakhra ya kwanta adakinnata ahankali yafara aikamata da sakonni tanajin hannunsa ajikinta ta suka daga gadon takoma kasa ta kwanta biyo ta yayi ta kuma guduwa yarasa yadda xaiyi da ita haushi ne yakama shi yaja mata kofar yafita xuwa dakinsa asaman gadonsa ya kwanta yarasa meyake masa dadi.











*NASEEBA GAWO*โœ๐Ÿป
[6:8Am,2017]


*ยฎ๐Ÿ’ฆ๐Ÿ’ฆ๐Ÿ’ฆTALENTED WRITTERS FORUM*๐Ÿ’ฆ๐Ÿ’ฆ๐Ÿ’ฆ

*๐Ÿ’ฆT F*๐Ÿ’ฆ




*KANNAN MIJINA*


Please Login or Register in order to submit comment