Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ko, to wlh zan dau mummuna mataki akan ki "


" Hmm yaya Assadiq kenan kwantar da hankalin ka kafin ka dau mataki ni zan dauka da kaina ina dalili, yau zanfada maka waye muktar

Hakika muktar shine wanda nake so shi ne burin raina dashi nake son yin *ZAMAN AURE* wani wawan mari Assadiq ya dauketa da shi


Nan tazube tafara gunjin kuka, tana zage zage tayi waje momy kam zubewa tayi numfashin ta na sama sama gaba daya su faruq kanta suka nufa sunai mata sannu ina bata ma san suna yi ba daukar ta sukayi sai asibiti



Muwadda kam tana fita bangaran ta ta nufa ta hada kayan ta tsaf dana hamra tayi part din safiyya lokacin tana daki tashiga sallamar ta tajiyo ta fito tana xuwa taganta tana kuka


"aa Muwadda lpy me ke faruwa "?


" aunty safiyya wlh yau angama zaman gidan nan, dan haka ga hamra nakawo miki ita ki kula da ita nasan bazaki cutar da ita ba "

" Muwadda kina da hankali kuwa yarinyar ki karama baki fa yaye ta ba "

" eh nasani nariga angama yanke hukunci wlh abinda zani da 'yar Assadiq "


Tana gama fada tai gaba tabar safiyya da sakin baki cikin dakin ta takoma ta kwantar da hamra kusa da fadila ta zubawa yaran ido kamar su daya


Wayar ta ta dauka tashiga neman layin Assadiq tanata ringing be dauka ba gajiya tayi ta ajiye wayar


Su Assadiq suna asibiti momy tana jin jiki dan jininta ya hau sosai hankalin su yagama tashi sun yiwa dady waya ya taho



Muwadda kam tana xuwa parlon gidan su tasaki ihu tana kuka cikin tashin hankali mama ta tareta


"subahanallah, Muwadda lpy me yafaru ina hamra ".

" nashiga uku mama Assadiq yaimin sharri wai bin maza nake shine yai min duka ya kwace yarsa yabawa matarsa, nashiga uku "


" cab dijan, lallai akwai dan karamin yaki wlh bari abban ki Yadawo



Abangaran afifa kuwa yau tun safe gas dinta ya kare haisam ya dauka zaiyo repilling tagaji da jiransa ga yunwa store tashiga dan dakko lemo mezata gani ba komai a ciki sai buhun shinkafar da suka farka sai taliya komai dai sai wanda suka fara amfani da su ne kawai mamaki ne yakama ta wayar ta ta dauka zata kira shi ba kudi please call me tayi masa yana gani yaki kira dan yana tare da shukura suna break fast wai dawowar sa kenan daga adamawa yan yaransu na gefensa

Gajiya afifa tayi da jiransa tasa kuka gidan ta rufe ta nufi gidan su ba kowa gidan Assadiq ta shiga ta tarar da safiyya nabawa hamra madara guri tasamu ta zauna da mamaki safiyya ta dubeta


"afifa lafiyar ki ina haisam din "?

" tun safe yafita be dawo ba shine hankalina ya tashi gashi nazo gida ba kowa ina momy "?


Kiran Assadiq ne ya shigo wayar ta da sauri tadaga

" sopy kar ki ji ni shiru muna asibiti momy ce ba lpy "


" subahanallah meyasameta Dee, wai ma meke faruwa ne "?


" pls ki jirani indawo gidan tukunna "

Kukan hamra yaji yatambayi safiyya

" sopy yanake jin Kukan hamra "?


" itace Dee "

Shiru yayi ya kashe wayar afifa ce ta tambayeta meke faruwa gaya mata tayi sai tasa kuka safiyya ce tai ta rarrashinta ta shiga kitchen ta dakko mata abinci nan tashiga ci sai da ta cinye tas sannan ta karbi wayar safiyya ta kira haisam tafada masa tana gidansu Hankalinsa ne yatashi ba shiri ya biyota



Su jalila sun zo kano hutu sai da suka huta sannan suka nufi gidan su safiyya su gaida su baffa ya rukayya ma tazo haka amarya amina sukai Sallama suka shiga suhyla tana ganin jalila ta rungume ta tana murna suka gaisa da su cikin mutunci ummi kuwa tarasa inda zata sa jalila dan farin ciki suka shiga suka gaisa da baffa yasa musu albarka nan yatafi ya barta ta wuni najiba kuwa sai hira take mata sai dare yazo ya dauketa suka tafi tabawa ummi kudi najiba kuwa turaruruka ta bata


Cikin dare farhana na jikin ibraheem taji wani irin ciwon mara da baya agigice tafarka tasamasa kuka kukanta yaji ya tashi ganinta yayi tana juyi ba shiri yaje ya fadawa hajiyar sa cikin sauri ta taso kan suzo ta galabaita suka dauketa suka kaita asibiti su fatisa sai dariya suke mata zata haifi bakwaini.


Farhana kam tasha wahala abin mamaki kuwa bakwaini ta haifa na miji nan aka kaishi nursery ita kuma aka kaita dakin hutu






*NASEEBA GAWO*

✍🏻
[9:16Pm, 2017]




*®💦💦💦TALENTED WRITTERS FORUM*💦💦💦


*💦T F*💦




*KANNAN MIJINA*
👩‍👩‍👧



*NA*


NASEEBA I UBA 💐






*Astagafirillah waatubu ilehi Astagafirillah azim*👏🏻



💦
*TALENTED WRITTERS hadin kanmmu shine alfaharinmmu*💦






*kawata faeeexa usman ina kika shiga ne kwana 2 bana jin ki dafatan dai lpy kike* 👌🏻








*92*




~~~zaman asibiti ne yakama farhana yayar ibraheem ce tazo daga katsina take zaune da ita gida ya koma nasu masari ibraheem da Kansa yaiwa Assadiq waya yafada masa haihuwar yai murna nan yake fada masa rashin lpyr momy yace kar ya fadawa farhana



Ankwantar da momy saboda yadda jininta ya hau yaya hannatu ce tazo hankalin ta ne yatashi yadda taga yadda momy take shan jiki Assadiq ne yajata gefe yabata labarin abinda muwadda tayi dubansa tayi tace


"Hmmm nasan a rina wai ansaci zanin mahaukaciya, to yanzu wane mataki ka dauka kenan "

" ai yaya ina ganin yazama dole inrabu da muwadda atsarin rayuwata babu sakin mace saboda illar dake cikin hakan "


" to yazakai gwanda kasaketa taje tayi *ZAMAN AURE* da wanda take so mara mutunci kawai, kuma wlh bazaka bata hamra ba "


" aa yaya bazan raba ta da yarta ba "

" Assadiq kenan, Allah ya kyauta kawai "

" Ameen, bari inje in dawo


" ok badamuwa sai kadawo "



Fita yayi ita kuma ta koma ciki faruq yayi tagumi yana kallon momyn tana ta bacci saboda allurar daakai mata


Sanda Assadiq yakarasa gidan sa su afifa sun fito ita da haisam zasu tafi asibiti duba momy da sauri ta karasa gurin sa


" yaya Assadiq ya jikin momyn "?


" da sauki afifa yaushe kika zo?

"dazu "

Haisam ne yabashi hannu suka gaisa yai masa ya mai jiki tare da tambayar sa number dakin da aka kwantar da momy yafada masa Sallama sukayi suka tafi ciki yakarasa hamra na bayan safiyya tayi bacci sai fadila kwance a kujera tana kallo ya shiga da gudu fadila tazo ta rungume shi


"oyoyo papa"

"Fadilaty kina lpy, ya school "

" Lpy lau, papa naje gurin aunty bata nan ta tafi ta bar hamra na taiwa mamma na kuka, dan Allah papa akaita gurin ta "

Shiru yayi ya maida dubansa ga safiyya wacce ta zubawa fuskar mijin nata ido yadan fada fuskar sa ba wal wala can yanisa yace


" sopy muwadda fa "?

" Dee wai me ke faruwa ne?

"tambayar ki nayi ko, ina muwadda?

"Bata nan tazo tana kuka ta kawo min hamra wai inkula da ita, tabar min "


" Good haka tace, ba laifi sopy ga hamra nan ni Assadiq nabaki ita ki zame mata uwa halak malak"

Yana gama fada yasaki hannun fadila ya nufin dakin sa

Kanta ne ya daure tabishi dakin yana zaune gefan gado dafe da Kansa kusa da shi tasamu ta zauna ahankali ta kira sunan sa


"Dee dan Allah kasanar dani abinda yake faruwa "

Dago da Kansa yayi ya dubeta idon sa yakada yai jazur

Labarin abinda yafaru yayi, hankalin ta ya tashi kuka tasa masa cikin shash shekar kuka tafara magana


" Dee dan Allah kayi hakuri kar ka saki Muwadda kar ka raba uwa da yarta "

" Dakata safiyya, inbazaki rike min yarinyar nan ba insani karfa ki manta inada masu rike min ita amma banfada miki maganar nan ba dan ki sa bakin ki ciki ba aa nafada miki ne kawai dan kin isa infada miki kin gane ko, dan haka abar zancan, kitashi ki dafawa momy abinci kar ki sa gishiri "


" shikenan Dee, nagode ubangiji Allah yataya ni riko, ya jikin momy "

" da sauki inkingama kishirya muje ki duba ta "


" to "


Fita tayi ta nufi kitchen ta dora fatan wake da farfesun hanta ta kammala ta soya wainar kwai ruwan dumi ya hada yaiwa yaran wanka itama ta shiga tayi tafito wasu riga da wando tasawa yaran iri daya purple da fari sunyi kyau hamra sai kallon Assadiq take tana daga hannu ya dauketa fadila ce tace


"papa, ko de anbarwa mamma na hamra "


" Kai Fadilaty, anbar mata, shikenan hankalin ki ya kwanta

sopy kiyi sauri ki shirya bari inje in sa kaya "

" tohm "

Be jima ba ya fito suka dau abincin momy a kuloli masu kyau suka shiga mota suka tafi ahanya yake fada mata haihuwar farhana


" mashaallah, Allah yaraya yabata lpy amma Dee waye zai zauna da ita ".

" aa wa kuwa zai zauna da ita wannan wace irin magana kike "

Yafada yana gyara mudubin gaban motar sa


" eh gaskiya gwanda atura yar dattijuwa ta zauna da ita ko adawo da ita gida "


" Hmmm sopy kenan, shikenan zaa samo wacce zata "




Karasawa yayi cikin asibitin yayi parking din motar sa suka fito daukar hamra yayi safiyya kuma ta dauki kwandon kuloli fadila na gaba da faruq suka hadu yana ganinsu ya dauki fadila tare da sakar mata kiss ya gaida safiyya dakin da momy take suka shiga tana xaune yaya hannatu na da afifa na gefenta safiyya ce takarasa gaban gadon tai mata sannu


"momy ya jiki "


" Da sauki safiyya, nagode kinji Allah yai miki albarka "


Kallon kallo aka shiga Assadiq kuwa mamaki ne yakama shi aransa yake fadin


*_ikon Allah momy ce ke sawa safiyya albarka lallai mai hakuri yakan dafa dutse har yasha romansa_*



Momy ce taka tse masa zancan zucin da yake ta hanyar maganar da take masa


"Assadiq wane mataki ka dauka akan shedaniyar yarinyar nan, kuma ya naga hamra atare daku "


" momy hukunci yana hannun ki tunda dama ke kika aura min ita "


" Gsky ne Assadiq, to sakin ta zakai yau din nan ba sai gobe ba "



" kar ki soma hjy kareema akan wane dalili zakice yasaki matar sa to ni nace aa "



Gaba dayansu suka juya dan ganin me magana dady ne


Fadila ce taje ta rungume shi karaso wa yayi ciki gaba dayan su suka tsuguna suka gai da shi yaamsa momy ce tace


" Haba alhj basu fada maka abinda yarinyar nan tayi bane "


" basu fadan ba, yanxu ke bata lafiyar ki ake ba, dan haka abar duk wata magana sai anje gida "


Jalila ce tashigo ita da Dr almustapha kai tsaye gurin momy ta nufa hannun ta takama tashiga yimata sannu



Dr almustapha ne ya tsuguna ya gaida dady yabawa su Assadiq hannu suka gaisa karasawa yayi yaiwa momy sannu da jiki taamsa a mutunce

Haisam kam yana waje cikin mota yakira afifa a waya tazo

Shiga tayi tasame shi duban ta yayi yace


"baby abinda yakamata ayi shine ki zauna ki kwana da momy "

" aa dear yaya hannatu ce fa zata kwana tare da ita "


" eh duk da haka kema ki kwana "

Badan taso ba taamsa da to Sallama yayi mata yatafi sai bayan ya tafi ta tuna ba kudi a hannun ta ciki ta koma lokacin su jalila na shirn tafiya da kyar dady yabarta ta kwana su safiyya ma suka tafi sai lokacin momy ta iya cin abincin safiyya



Haisam na zuwa gida ya kwashe kayan lefan afifa ya kulle gidan ya nufi gidan shukura tunda yau girkinta ne



Assadiq ne kwance yayi rub da ciki safiyya ta shigo sanye da rigar bacci fara kal gefansa tasamu ta kwanta mirginowa yayi ya jata jikinsa hade da sakarwa wuyanta kiss ahankali yafara jan rigar tata bireziyar ta yacire mata ya wurgar ahankali yace


Bana hanaki kwana da wannan abar ba "


Cikin shagwaba tafara magana


" Dee, nide gsky kamayar min da abata



"to ai banaki bane abun dan haka abar min su haka "


Kan tabashi amsa ya hade bakinsa ta nata




Tun da Muwadda ta je gida take kiran layin muktar akashe shiru tayi tashiga tuna nin lpy ya kashe wayar sa







*NASEEBA GAWO*
✍🏻
[9:07Pm,2017]



*®💦💦💦TALENTED WRITTERS FORUM*💦💦💦


*💦TF*💦




*KANNAN MIJINA*
👩‍👩‍👧



*NA*

NASEEBA I UBA💐




*Assatagafirillah waatubu ilehi Assatagafirillah azim*👏🏻



*💦TALENTED WRITTERS hadin kanmmu shine alfaharin mu*💦






*masoyan KANNAN MIJINA ina gaida ku kyauta dan Allah masu son kannan mijina daga farko kuyi hakuri na kusa gamawa document yana nan tafe*👌🏻






*93*



~~~gajiya tayi da neman layin wayar muktar taajiye wayar, muktar kuwa sai da yagama hade kan kudin muwadda sannan ya kunna wayar sa layin wayar ta yakira
Bugu biyu tadauka


"Hello baby ya kike kinji ni shiru ko "


" Hmmm, wlh sweery hankakina har ya tashi, Allah yasa lpy "


" wlh baby, ina can ina fafutikar hada kuda dan nan ni de kiyi kokari ya sakeki musamu mucika burin mu "

" baka da damuwa sweery ai wlh bazan koma ba nifa da kai kadai zan iya *ZAMAN AURE*"


"to shikenan baby sai najiki, to ina kika bar babyn taki "?


Diriri cewa tayi cikin rawar baki tace


" Dear baby kuma, wacce kenan ban fahimce ka ba "

" oh, rushida tace min anbaki yar kishiyar ki ko "


" Hmmm, dear kana tunanin zan dauki yar wani bayan naki haihuwa "

" gsky ne kuma baby, to shikenan dai sai kinji ni, zankira ki anjima "

" ok dear, love u "

" love u too "


Sallama sukayi ta kashe wayar komawa tayi ta kwanta tana tunanin hamra ahankali aka turo kofar dakin aka shigo saude ce ta tsuguna tace


" aunty abba na kiranki "

" naji jeki gani nan zuwa "


hijjabinta tasa tafita yana zaune a parlor mama na gefansa tayi Sallama tashiga guri tasamu ta zauna dubanta yayi yace

" muwadda meyafaru kuma ina hamra?


"Dady nagaji assadiq kashe ni zaiyi wlh ga sharri da yaimin wai bin maza nake"


Tana gama fadar haka ta rushe da kuka ransa ne yabaci mama zatai magana ya daga mata hannu wayar sa ya dakko ya shiga neman layin assadiq


Kwanan momy 2 aka sallamota su assadiq suna tare da ita sun zagayeta fadila na gefanta Dady ma ya shigo dakin dubata wayar assadiq ce tafara ringing dakko wa yayi yaduba abban muwadda ya gani ajikin screen dauka yayi


"salamu alaikum, abba barka da yamma "


" dakata malam ka bude kunanka da kyau ka saurareni, ka kawo min takardar sakin muwadda nabaka nan da awa daya "


Yana gama fada ya kashe wayar mai da dubansa yayi ga su dady su dinma shi suke kalla nan yabasu labarin yadda sukayi da abban muwadda faruq ne yazaro biro da takarda yamikawa assadiq


" bross dont wait, pls divorce her "


" to dama me xai jira faruq ai wlh sai ya saketa "


" hannatu meyasa haka ne eye, ku zaku yanke hukunci ko me"


"dady kayi hakuri "


" sadauki wane laifi matarka ta aikata ma ka ina son jin me yahada ka da ita "


Momy ce ta kwashe komai tafada masa shiru yayi can ya nisa yace


" sadauki tashi muje gidan su matarka bana son zancan banza akan me zai saki matar sa "


" amma alhj........

"Hajiya kareema dakata du Allah "


Fita yayi assadiq ya bi baysnsa fadila ce tai zunbur ta mike tace

" papa zanbika dan Allah katafi dani "


Dawowa yayi ya tsuguna agabanta tare da hada hannunsa danata yace


" binty ki zauna da su umman nabil ga uncle dinki nan zai kaiki shop rite kinji "

" papa amma har da hamra ko "


" har da ita mana fadilaty "

" to shikenan, sai ka dawo papa "


Kissing dinta yayi ya fita gurin faruq ta koma ta zauna sunan sa ta kira


" uncle, kaji abinda papa na yace ko "

" naji fine girl dole inkai ki "


Momy ce ta dubi yaya hannatu tace


" hannatu kiramin farhana awaya inji lafiyar su "


" to, momy, wai wa zai je ya zauna da ita ne, nide wlh zanje da kaina in dakko ta "


" kafin kije dakko ta, ki fara kiramin ita nide "

Wayar ta ta dauka ta kira layin farhana bugu biyu ta dauka


Suka gaisa da yaya hannatu tai mata ya jiki tare da tambayar lafiyar baby mikawa momy wayar tayi


" Hello, farhana ya jiki ya baby dafatan ba wata matsala ko "

Farhana najin muryar momy tasa kuka kwantar mata da hankali ta shiga yi da kyar tayi shiru


" haba farhana kar ki damu zamu zo kinji kuma gobe maijidda zata zo, ta zauna da ke "


" shikenan momy nagode agaida dady

Sukai Sallama takashe wayar tattaunawa Suka ci gaba da yi akan farhana




Sanda su assadiq Suka je gidan su muwadda abban ta na sitt room Sallama sukayi Suka shiga Suka gaisa dady ne yafara magana


"alhj, banji dadin abinda yafaru ba ko kadan amma du Allah ayi hakuri adawo da yarinya dakin ta "


" au alhj muhammad ba takardar muwadda kuka kawo min ba, to ni kam yata tagama zama da yaron nan tunda be duba *zumunci* ba "


Dady yakada yaraya amma abban muwadda ya kafe sai ansaketa ran assadiq ne yabaci yafurta


Abban ni assadiq na saki muwadda saki daya"


"ba da baki nake son ji ba ga biro da takarda rubuta ga bani "

Karba yayi ya rubuta yana gamawa ya mike yafita






*NASEEBA GAWO*
✍🏻
[12:11pm, 2017]


*®💦💦💦TALENTED WRITTERS FORUM*💦💦💦


*💦T F*💦






*KANNAN MIJINA*
👩‍👩‍👧



*NA*

NASEEBA I UBA💐






*Allahumma inna nasalika afiyan walafiyati fidduniya walakhairati AMEEN*👏🏻




*💦TALENTED WRITTERS hadin kanmmu shine alfaharin*💦






*alhmdulillah kamar yau ne kanwata ta tafi tabarni cikin ikon Allah gashi ta dawo umymaty ukuty inai miki sannu da zuwa dafatan kindawo lpy Allah yakarbi ibada sis WELCOME BACK SWEERY*💃🏻💃🏻💃🏻




*94*






~~~Ran dady ne yabaci hannu ya mikawa abban muwadda suka gaisa ya fita a cikin mota ya tarar da assadiq ya kifa kansa a sitiyarin a mota be ce masa kala ba assadiq yaja motar suka tafi



Safiyya tana zaune a parlo tana bawa hamra firiso cream assadiq ya shigo kan 3siter yasamu ya kwanta dafe da kansa mikewa tayi tadawo kusa da shi bayan taajiye hamra ahankali ta kira sunan sa


"Dee me yasameka dafatan ba ciwon kan nan bane"


Dan karamin tsaki yaja bayan ya bude idonsa ya dora su akanta take yafara samun saukin damuwar sa ahankali yadubeta yace


"sopy kaina kamar yafashe haka nake ji pls kawo min liptone kadan "


Mika masa hamra tayi ta nufi kitchen ta dafa masa liptone ta kawo masa tashi yayi ya karba yafara sha yana bawa hamra Safiyya kam ta zuba masu ido dago da kansa yayi ya kalleta yasakar mata murmushi itama murmushin ta mayar sa


" sopy, ina fidilaty?

"tana gidan momy, yauwa Dee muwadda shiru dan Allah kaje kadawo da ita


"Safiyya Safiyya Safiyya! sau nawa na kira sunan ki "


" sau uku Dee "


" Good kar ki sake yimin maganar muwadda bana so kinji dai nafada miki ko "

" naji, kayi hakuri bazan sake ba inshallah "

" tashi ki hada min ruwan wanka "


Tashi tayi tashiga bedroom ta nufi toolet ta tara masa ruwan wanka



Afifa ce zaune tana kallo haisam ya fita sai jin bugu tayi tashi tayi tanufi bakin gate din tambaya tafara yi


" waye ne?

"bude kigani mana "

" kai kamar yaya, bangane ba "


" zaki gane ne to kb ne, yana nan ne "?


" bansaniba, banza kaje ka koyi yadda ake tambaya sakarai kawai "

" kut ni kike fadawa haka wlh zaki sani aikin banza auran naki da akayi da kudin bashi banzar mace kawai "


Shiru taimasa yai ta zage zage amma hankalinta yagama tashi tana mamakin lamarin haisam yafara bata tsoro ciki ta koma ta dau wayar ta tafara kiran layin haisam tana ta ringing be dauka ba

Ajiye wayar tayi tanufi bedroom dinta akwatinta ta jawo tafara budewa abin mamaki ba rabin kayanta duk ankwawhe tambayar kanta tashiga yi ina kayanta shiru tayi tafara tunanin meke shirin faruwa da ita ne wayar tace tafara ringing mika hannu tayi ta dakko akan bed side sunan jalila ta gani da sauri ta daga wayar


"Hello, yaya jalila "

" Afifa gani a kofar gida zo ki bude min"


Zabura tayi tafita zuwa bude mata tana ganin ta ta rungumeta tana murna ciki suka shiga suka sami guri suka zauna kallon Afifa kawai jalila take murmushi afifa tayi tace


"yaya jalila lpy naga kina kallo na "

" Hmm afifa, lafiyar ki kuwa kamar fa baki da nutsuwa"


Kuka tasaka mata sai da tayi mai isar ta sannan tayi shiru ta dora da


"yaya jalila, wlh nafara tsorata da halin haisam gaba daya yacanja duk bayan kwana 2 sai yace yayi tafiya ga shi dazu wani yaro yazo wai auran bashi haisam yayi nifa nafara jin tsoro gashi ya dena bani kudi


"haba Afifa me kike son fada min ki nutsu haba may be yana can yanai muku shirin tafiya england "


" kai yaya jalila anya kuwa "


" kinga tashi ki dora mana girki "

" cab wlh bani da gas "


" to yazaai kenan afifa, amma bari naiwa Doktar waya ya turo min wanda yake zuwa yakai aimin refiling "


" yauwa dan wlh haisam bazai kai ba wai risho fa zai siyo min, yauwa yaushe zamuje gidan farhana "


" eh ni wajen jibi da nake son muje ko "


" to Allah ya kai mu "


Yaron ne yazo yadau gas din afifa akai refiling aka kawo ta dora girki suka ci suka sha hira da yamma Dr almustapha yazo ya dauke ta yabawa afifa 10k tai ta murna suka tafi



Momy tana kwance fadila tana matsa mata kafa tadago ta dubeta tace


" *kakus* kinsan me?

"aa fadila sai kin fada "

" aunty fa tabar mana hamra, mamana ce take mata wanka "


Kan tabata amsa Safiyya ta shigo sallama tayi tasami guri ta zauna ta gaida momy taamsa cikin sakin fuska dubanta tayi tace


" Safiyya sannu da kokari kinji Allah yai miki albarka yabaki ikon rike hamra da amana kuma ina baki hakurin qbubuwan da suka faru abaya kinji "


" ameen momy nagode bakomai "


Yanzu zansa akawo miki mai aiki ta taimaka miki da rainon hamra ko tunda kina zuwa makaranta"


"to shikenan momy nagode, ga faten wake "


" yauwa yata nakuwa gode fadila dakko plate azuba mana ko"


"yauwa momy wa zai je ya zauna da farhana "


" antura maman su ta tafi tun jiya amma su jalila ma zasu "


" ok thom shikenan momy "

Nan suka zauna suna taba hira Safiyya dai mamaki ne yakamata yadda momy take mata



Muktar kam yahade kan dukiyar muwadda ya bar garin text yaimata ya tura mata tana zaune tana cin abinci amma hankalinta yana garin Muktar da yarta hamra wayar ta tai kara alamar shigowar text







*NASEEBA GAWO*

✍🏻
[6:14Am,2017]


*®💦💦💦TALENTED WRITTERS FORUM*💦💦💦


*💦TF*💦




*KANNAN MIJINA*
👩‍👩‍👧



*NA*

NASEEBA I UBA💐



*1st october*🇳🇬
*alhmdulillah 2 day it is wonderful day the day that nigeria get her independed oh freedom

Please Login or Register in order to submit comment