Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dan dana min a baya haka kaxalika kamallaki dukiyar danta Assadiq "

" momy me dukiyar Assadiq xataimin bayan abbana ya mallaki abinda Assadiq be mallaka ba"


"Hmmm ta yaro kyau take bata karko, Muwadda hjy kareema tai min abinda bazan manta da shi ba wato lokacin da mijinta yai kwamishina sai ta manta alaka ta daita giyar mulki ta dubeta ko kallo ban isheta ba Muwadda gashi lokacin muna tsananin bukatar taimako abban ki bashi da komai in har munsami tai mako to daga mijinta ne hjy kareema ta wahalr dani mutuka ko dan ubanmmu daya gashi mu biyu ne mata amma tun ina karama nake fuskan tar matsi daga gareta "


" Hmmm momy nafahimce ki to amma momy meye laifin Assadiq da xan mamaye dukiyar sa "


Ai in aka taba Assadiq to kmr ita aka taba tana son Assadiq"


"shi kenan mama to nifa har yanxu ina son muktar "


" kibar maganar yaron nan Muwadda kinji "

" Gsky mama bazan iya rabuwa da shi ba "


" to ba ruwana kuwa"



Iyalan alhj muhammad mai nasara ne zaune a parlon sa sai yan jiko kinsa guda uku nabil ashraf sai fadila data girma tafara rarrafe yanxu haka ma tana ta xagaye atsaka nin iyayan nata gyaran murya dady yayi bayan addua da Assadiq yayi yafara da kmr haka


"bawani abu ne yasa nataraku anan ba sai dan in shaida muku sakamakon xiyarar da malam mudassir ya kawo min jiya yanemi da muhada aura tayya tsananin daya daga cikin yanmata nan da dansa ibraheem to mun yanke shawarar hada shi da farhana in Allah ya kaimu zai zo anjima dan su dai daita atsakaninsu "


Ai farhana angama jin jawabin dady ta zunduma uban ihu sai da ta razana fadila taxo ta kankame ya hannatu tana kuka

Ita batason sa wlh yan ixala ne kuma baance a sokoto sukeba"

Dady ne yadaka mata tsawa cikin bacin rai yace

Farhana kinfara haukane da xaki fasa wannan uban ihun sai kace wacce uwarta ta mutu har kina razana fadila ko to kirubuta ki ajiye baki da miji sai ibraheem"

"Haba alhj kaifa kace bazaka taba yaiwa yayanka auran dole ba "

" yaisa haka hjy kareema kina zaton malam mudassir xai nemi abu aguna inki yaimasa shi mutukar inada iko, to kar akuma daga xancannan inba hakaba rai xai baci ku ma kuyi kokarin fito da maxajan aure "


Sai yanxu Assadiq yasa baki cikin ladabi yace


" Dady dama inason xuwa infadama tun tuni ita jalila yayan safiyya ne yake sonata"


"yayan matarka kenan "?

" shi dady Dr almustapha ba likita ne a asibitin malam aminu kano amma yanxu wani asibiti xai koma a abuja"


Momy ce take ta xabgawa Assadiq uwar harara bema san tanayiba dady ne yadubi jalila yace


"jalila abinda naji hakane"?


Cikin kunya ta kada kai


"to Alhmdulillah abinda zaai shine ka turomin shi sadauki "

" to dady "


" amma alhj saboda Allah

"dakata hjy kareema nagama magana bana son kwan gaba kwan baya, yaushe xaa kai lefan sadauki "?


" jibi xaa kai amma mata ne xasu kai ba kmr aransa nafariba da maxa suka kai ba"


"Hmmm hjy kareema kenan shikenan ai sai abinda kikace saboda nafiskanci bikin nakine Allah ya bada alkhairi, afifa kema ki fito da mijin aure kar inkuma yimiki maganar "


" to dady "


Nabil ne yace dadyn su aunty afifa nima auran xanyi kasan wa xan aura?


Fadilan uncle A"


Dariya sukasa Assadiq yace


"nabil auran Fadilaty binty sai anshirya kafadawa abbanka yafara tanadi"


"baabinda zai gagara ko nabil "?


" wlh kuwa ummata"


Dady dai murmushi kawai yake ya mai da dubansa ga hannatu yace

Dukkan ku baku da kara, hannatu kar ki tafi ki tabbata kinga xuwan ibraheem"


"to dady "

Kowa tashi yayi suka fita ran momy abace musamma da dady yayarda auran jalila da yayan safiyya.





Safiyya ce xaune adaki tana gyarawa fadila wardrobe Assadiq yai Sallama yashigo da fadila a hannusa tana ganin safiyya tafara kokarin sakkowa tana ta kiran


"mamma"

"lala ki kafara iya sunan mamanki kafin nawa ko nagode Fadilaty "


" wlh Dee wani sain kafiya ban dariya to bani nasha wahalr nakuda ba


"au hakama xakice to bani nai..........

"kayi me fadi mana "

". adai bar maganar "


Dariya tayi ya tashi ya janyo akwatinan da ya xo dasu binsa kawai take da kallo agabanta ya ajiye su cikin sanyi yakira sunnanta

" Sweet sopy ina dada baki hakuri bisa kaddarar data samemu na karin auran da xanyi bansan da wane yare xan fahimtar da ke ba, sai dai ince kiyi hakuri kiyi hakuri safiyya "


" Dee nafahimceka ni dai yanxu abu daya nake so daga gareka "


" ina inki sopy "


" kabarni inkoma makaranta kaji "


" Angama madam kuma daga yau xanfara koya miki mota kinga sai ki dinga tafiya dakanki, ga kayan fadar kishiya nan ki duba in daakwai abinda babu sai kifadamin "


" ni da kabarsu ma nagode "


Takarashe xancan tana rushewa da kuka fadila ta mika masa tabar dakin binta yayi da kallo ya mike yabi bayanta a parlo ya sameta nan yajata jikinsa yafara aikin rarrashi da salon soyayyarsa ya mantar da ita yajata sukai daki suka kwanta cikin dare safiyya ta tashi tayo alwala tafara salloli data idar tashiga kwararo adduoi tana fadawa Allah damuwarta dafatan Allah yakareta daga sharrin mai sharri yakuma bawa mijinta ikon yin adalci tashafa anan bacci yai gaba daita data tashi da safe sai taji ranta yai sanyi da irin abinda takeji jiya da azumi ta tashi a ranar




Yau aka kai kayan lefan Muwadda kaya na alfarma momy tahada kmr yadda tafada mata ne suka kai aka sa biki sati biyu su farhana sunata murna nan suka fara shirin biki yaya hannatu ce taje gidan safiyya tai ta bata hakuri da ban baki kimar matar ta nunku a idonta.



Safiyya ce tashirya taje gidan yayar ta rukayya tafada mata auran Assadiq shiru tayi can tanisa tace


"hakika safiyya Allah ya jarabceki agidan aure amma kiyi hakuri xakici riba nan gaba"

"shikenan yaya nagode, amma ina fargaba wlh "

Nan tai tabata shawarwari yadda xata dada kula da mijinta suhyla ce take tafaman shara ala dole ta girma sai masifa takewa kaninta yana dawo mata da shara baya cikin fushi tace


" aunty safiyya kiwa musadiq magana "



" lallai suly angirma andena cewa cafiyya "



Da daddare Assadiq yaxo ya dauketa suka tafi wani katafaran shago yakaita ta xabi kayan gado da kujeru musu kyau da tsada tai masa Godiya suka biya kudin suka tafi gida washe gari aka fitar da tsofafun kayanta aka xuba mata sababbi komai purle da fari.















*NASEEBA GAWO*โœ๐Ÿป
[5:44Am,2017]




*ยฎ๐Ÿ’ฆ๐Ÿ’ฆ๐Ÿ’ฆTALENTED WRITTERS FORUM*๐Ÿ’ฆ๐Ÿ’ฆ๐Ÿ’ฆ


*๐Ÿ’ฆT F*๐Ÿ’ฆ




*KANNAN MIJINA*
๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘ง




*NA*

*NASEEBA I UBA*๐Ÿ’






*TALENTED WRITTERS ๐Ÿ’ฆhadin kanmmu shine alfaharinmmu*๐Ÿค๐Ÿค




*Allahu akbar Allahu akbar Allahu akbar walilahil hamd*




*sakon gaisuwa gareki xainab Abdullahi blouse uwa ga Fadilaty binty wannan shafin nakine ke kadai*๐Ÿ˜





*65*





~~~Shirye shirye ya kankama ta ko wane bangare amma banda ango Assadiq momy kuwa ji take yanxu ne xatai biki haka su farhana anata shiri anfir fitar da anko safiyya kuwa ganin abun take kmr almara gashi kullum gidan ta cike yake da masu aiki anata fenti andada gyara bangaran da Muwadda xata xauna gaba daya atakure take Assadiq ne Yadawo da wuri daga office tana can kuryar daki fadila na gefenta tanata wasa ahankali yatura kofar dakin yashiga idonta ta rufe saboda yadda takejin xafinsa ko san ganinsa batayi da hanzari fadila ta mike ta nufi gunsa

"papa papa "

" oyoyo Fadilaty inye yaushe aka fara tsaiwa "

Safiyya tana jinsa taimasa shiru guri yasamu ya xauna kusa da ita ahankali yafara kiran sunnanta yana shafa lallausar gashin kanta


" sopy, sopy nasan ba bacci kike ba pls ki bude idonki"

Tafiyar tsutsa yafara mata akafar ta ba shiri ta bude idonta tashi tayi ta zsuna ya xuba mata ido taimasa kyau wata guntuwar riga ce ajikinta ta zubo da gashinta baya


"matar Assadiq kina rikita mijinki fa kullum kyau kike karawa kmr budurwa meye sirrin "

" Dee sannu da xuwa ya office "

" lpy kalau ina tambayar ki kinyi shiru "

" mexance maka to"

Maida dubanta tayi ga fadila tace

"shine kika hana ni bacci ko fadila ke bakiyi ba ni baki barni nayiba"

"wai haka Fadilaty kin hana mamma bacci "

Gwalanto tafara yaimasa ala dole magana xata fara

" sopy bani abinci inci innagama mufita kifara koyan motar ko "


" To Dee ammafa cous cous nadafa bansan xaka dawo yanxuba gashi basonsa kake ba "

" Badamuwa kawo min kadan kinxubawa masu aikin can ko "

" eh"

Fita tayi taje ta dakko masa abincin fadila tana ganinta da kuloli tafara murna ajiyewa tayi tashiga zuba masa a plate ta tura masa gabansa kallon ta ya tsaya yi yace


"sopy kinfara gajiya dani ko acikin sauyin da kike min har da horan cin abinci da kaina pls safiyya kar kimin haka ki taimaka kici gaba da kula dani kinji "


" Haba Dee yanxu wane canji kagani daga gareni me andena yima amma dai shikenan inshaallah xan nunka abinda nake akan da shi kenan "


" shikenan matar Assadiq nagode Allah yai miki albarka "


" Ameen"

Basu saniba fadila tasa hannu tana ta ci sai yanxu suka ankare safiyya tasa tissue ta goge mata hannun ta da bakinta kuka tasa danme xaa matsar da abincin safiyya tadau cokali tafara bawa Assadiq abincin inta bashi sai tabawa fadila ahaka suka koshi dubansa tayi tace


"Dee inason yaye fadila tunda takama abinci komai ci take "


" safiyya tun yanxu da dai kibarta ta dan kara sha kmr xaifi "


" Dee wlh taisa kaga kuma ga makaranta xankoma gwanda a yayeta tun yanxu "

" shikenan sopy amma kibari sai bayan biki ko kuma banyarda akai min ita ko inaba "


" ni da akaita gurin ummi "


" Hmmm sopy kina son hana Assadiq nutsuwa kenan, hada min ruwan wanka"


"tashi tayi ta fita dakinsa ta koma tahada masa ruwan wanka yana nan inda tabar shi fadila nata wasa ajikinsa tadubeshi tace

"Dee nahada ma kawota kaje kayi "


" kishirya kema ki dibi kayan da xaki kai dinki mubiya mukai "

" Ok"

Yasa kai yafita Kwanikan tafara debewa takai kitchen fadila na bayanta ta goyata ta wanke Kwanikan ta gyara kitchen din daki ta koma ta gyara inda fadila ta xubar da abinci tagama tafesa air freshner tahada ruwan wanka taiwa fadila tafito ta xaunar daita itama ta shiga tayo wankan kan tafito fadila ta dafa gado ta mike ta dakko mai tayi wasa dashi tabata gurin da jikinta safiyya tana fitowa taga aika aikar datai mata cikin sauri takarasa ta karbe man dan haushi sai da tadaketa ai kuwa tafashe da kuka Assadiq yana dakinsa yajiyo kukanta ya shirya riga kawai xai xura yaji kukan tilon yartasa yaajiye rigar yafito dakin yanufa yana shiga yaganta kaca kaca da mai yadubi safiyya yace

"sopy me yasameta haka "?


" wlh sabagar fadila sai ita Dee kaduba fa kaga yadda tai wasa da mai "

" to kukan me take "?

" Dukanta nayi daga mata wanka sai ta tsiri wasan mai shikenan bazata barni in hutaba "


" yaisa haka safiyya gaskiya kar ki kuma dokar min ya nawa fadila take da xaki daketa "


" Allah yabaka hakuri "

" Ameen "yafada yana kokarin daukar ta bandaki yashiga yakuma yimata wanka da ruwan dumi safiyya tana kallon sa aranta tace

_in tayi mura ai tazo tahanaka bacci mai ya Allah intayi ba dai dai ba sai na daketa_

Ashe afili tayi maganar karaf akunnan sa


" shikenan safiyya ki daketa kar ki fasa bani kayanta insamata "


Wasu riga da wando ta mika masa jajaye wandon dan gajere iya kaurinta yake xuwa rigar mai hannun vest da farin rubutu agaban anrubuta

*my parents my every thing*


Yakarba yakamata yasamata farar safa da jan takalmi akaxo gyaran gashi yakasa cikin fushi yacewa safiyya

"kibar abinda kike kigyaramata kai "

Yana gama fada yafita gida uku taraba mata gashinta tasa jan ribon a gefe da gefe tasamata fari abaya ta shafa mata powder da turare tayi kyau yarinyar gashi dai ba fara bace amma kalar ta mai kyau ๐Ÿ˜˜


Dawo wa yayi dakin tana ganinsa tata fi ta rungume shi daukar yayi ya cillata sama yace


"wow binty kinyi kyau"


Maida dubansa yayi ga safiyya yace


"inkingama shiryawa kisamemu a mota, kar ki manta da kayan dinkin "


" Dee pls kayi hakuri kaji "


" shikenan sopy ya wuce "


Yasa kai yafita gurin maaikatan ya nufa sunata aikinsu suka gaisa ya dudduba aikin suna taiwa fadila wasa yarinyar badai farin jiniba yai musu Sallama ya nufi mota yana shiga kiran Muwadda yashigo dagawa yayi


" Hello sweery "

" Muwadda kina lpy ya shirye shirye "

" Alhmdulillah sweery yakamata kasami lokaci kazo kaji "


" xanxo Muwadda kijirani gobe "

" sweery yaufa "

" yau ba lokaci Muwadda "

" shikenan sweery ina fadila "

Lpy kalau gata tana jinki"


"agaida min da ita "


" ok ki gaida mama "


Safiyya ce ta karaso cikin wani wani lace na alfarma blue rigar have gwon tayi kyau ta bude kofar motar ta bude tashiga kamshin turaran ta ne yabigi hancinsa ya dubeta yace sopy wane turare kika sawa kayanki


" Dee gaffas nayiwa kayan "


" meye kaffas sopy "?

" Dee bafa wani abu bane akan wani dan abu nakaba zaka sa kayan sai kasa turaran wuta akasa hayakin zai dinga ratsa kayan "


" au shine baaiwa Fadilaty ko "


Dariya tayi yajasu suka fita tun daga nan tamaida hankali taga yadda yake tuki




Farhana ce kwance anatafama daita ta tashi ta shirya ibraheem yaxo da kyar tatashi wanka tayi tashirya cikin wasu english wears riga da sikert ta shafa powder ta feshe jikinta da turare dankara min mayafi tayafa tafita yana sit room sanye cikin shadda fara kal da hula ash fari ne amma ba tas ba da dan madai dai cin gemu ahabarsa Sallama tayi tashiga tunda ya kalleta sau daya yadauke idonsa saboda yadda ta matse jikinta shiru sukayi can yanisa yace

"Amm malama farhana idan badamuwa ko xakije kicanja koda mayafi ne

"ko me naji kina yayi "

" wato ainihin be kamata kina irin wannan shigar ba duba ga yadda shigar taki tayi ba dai dai ba "

Banxa taimasa nan yaitai mata waazi damunta yayi ta kira afifa awaya ta kawo mata mayafi baajimaba ta kawo mata ta gaida shi tafita yafawa tayi ya dubeta yace

" mashaallah kinga yanxu kinfi kyau "


Nan yagabatar da kansa gareta yakuma jadda da irin son dayake mata gaba daya haushi yabata tai masa banza ya karbi wayar ta yasa number sa yakira yai saving din tata tashi yayi yaimata Sallama yatafi yana fita ta rushe da kuka sai da tayi mai isarta sannan ta koma ciki tundaga ranar ya tsiri yimata waya wataran ta kula shi wataran tai masa banza



Yau almustapha yaxo amsa kiran dady suka gaisa cikin mutunci take dady ya yaba da hankalinsa yakuma ce ya turo magabatansa yai masa Godiya yatafi jalila yakira ya fadawa yadda sukayi da dady tai murna



Yana zuwa gida yasami baffa yafada masa zancan auransa da jalila yai murna yakuma tabbatar masa xai tura baffan ninsa ummi dai bata ce komaiba amma tana ganin momy bazata so wannan auran ba mai da dubansa yayi ga ummin tasu yace


"ummi na yanaji kinyi shiru "


" Allah ya sanya albarka mustapha "


" Ameen "


Washe gari Assadiq yaje gidan su Muwadda nan fa tashiga lissafa masa partyn da xatayi shiru yai sai data gama sannan ya dubeta yace

" Muwadda duk najiki amma fa kisani baxan iya xuwa wadannan events ba "


" Haba sweery meyasa "


" raayina kenan dan haka kifadi nawa kike bukata kawai inbaki "


" kabar kudinka "


" ok"


Yai mata Sallama yatafi binsa tayi da kallo tasaki wani murmushi.










*NASEEBA GAWO*โœ๐Ÿป
[5:28Am 2017]



*ยฎ๐Ÿ’ฆ๐Ÿ’ฆ๐Ÿ’ฆTALENTED WRITTERS FORUM*๐Ÿ’ฆ๐Ÿ’ฆ๐Ÿ’ฆ

*๐Ÿ’ฆT F*๐Ÿ’ฆ




*KANNAN MIJINA*
๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘ฉโ€๐Ÿ‘ง




*NA*

*NASEEBA I UBA*๐Ÿ’



*TALENTED WRITTERS hadin kanmmu shine alfaharinmmu*๐Ÿค๐Ÿค



*Allahu akbar Allahu akbar Allahu akbar walilahil hamd*



*Dedicated 2 billy ladan fans group thanx 4 ur suport*๐Ÿ’™



๐Ÿ”›๐Ÿ”๐Ÿ‘ˆ




*66*




~~~~Assadiq yana tafiya Muwadda ta kira number momy bugu biyu ta daga


"Hello 'yata "


" Naam momy Ina yini"

"Lpy kalau ya maman taki ya shirye shirye "?

" Lpy kalau momy "

" Badai matsala ko "?

" eh to dama Assadiq ne yazo daxu nafada masa events din da xanyi da kuma kudin danake bukata shine yahau ni da fada kuma wai ba inda xaije "


Tana gama fada ta rushe da kuka akidime momy tafara magana


" yaisa yata share hawayanki kinji ai ni na haife shi bashi ya haifi kansa ba saboda haka kar ki kuma asarar hawayanki kinji kuma maganar kudi da kansa xai xo ya kawo miki"


"to momy nagode Allah yakara girma "


" Ameen Muwadda ki gaida mama kinji "


" zataji momy "




Sukai Sallama ta kashe wayar tana dariyar mugunta

Assadiq kuwa yana barin gidan su Muwadda kai tsaye gidan su ya wuce a parlo ya tatar da momy tana waya da faruq tun da yashiga take hararar sa tagama wayar ta dubeshi tace


" sannu Assadiq wato har yanxu baxaka Maida hankali kan auran Muwadda ba ko kudin da ake bawa amarya kai kafurje baxaka bata ko har ikirari kake wai baxaka halacci bikin ba to kar kaje kaga yadda xansaba maka kuma wlh kaje da kanka ka kaimata kudin nan kaji dai nafadama "


Tana gama fada ta mike tabar gurin kansa yadafe yarasa ma mexai ce shi dai yasan bahaka sukai da Muwadda ba to amma me momy take nufi jalila yakira tana kitchen tafito da glass dinta manne a fuskar ta guri tasamu ta xauna


" ya Assadiq gani "


" jalila Muwadda ta bugowa momy waya ne "?

" eh yaya sunyi waya amma bansan me tacewa momyn ba but naji tana bata hakuri "


" shikenan badamuwa, dady fa?

"dady be shigoba"


"ok, jeki bari in wuce kicewa momy natafi "


" to "


Fita yayi ransa a mutukar bace yana xuwa gida kai tsaye dakin sa ya wave kayan jikin sa ya cire yafada toilet ruwan sanyi yasakarwa kansa saboda yadda yakejin xyciyar sa na zafi ya dade yana wanka sannan ya fito yashirya cikin 3quater da riga armlace ko mai be shafaba ya kwanta bsyan ya kashe kwan fitila

Safiyya kuwa tana dakinta tana lallaba fadila tai bacci dayake ba baccin xatai ba sai tabar safiyya da baccin nan ta tsiri wasa ta tabo wannan ta taba wancan sai da ta hautsina dakin sannan ta dawo jikin safiyya ta kwanta bacci yai gaba daita

Safiyya bata farkaba sai wajen 10 taga aikin da fadila tai mata murmushi kawai tayi aranta tace


_yarinya sai kirinkin tsiya adaketa babanta ya hau sababbi Allah yashiryi fadila_


Mai da dubanta tayi ga agogon dayake manne a jikin bango mai dauke da hoton fadila taga karfe 10 mamaki tayi to ina Assadiq yau be dawo da wuri ba wayarsa takira tanata ringing baadauka ba dakin ta gyara tamaida fadila cikin gadon ta tai mata addua tashiga wanka bata jimaba ta fito tashirya cikin wata rigar bacci lemon green iya gwiwa tafeshe jikinta da turare ta gyara gashinta hula tasa fara kal parlon tafito ta ga baya nan kai tsaye dakin tanufa sai taga kwai akashe sai kuma tajiyo kmr nishin Assadiq tsorata tayi tafara addua kwan ta kunna Assadiq ta hango kwance cikin bargo da sauri ta karasa ta hau gadon ta yaye bargon jitayi jikinsa da mugun xafi cikin sauri takira sunansa


"Dee, Dee meyasameka nashiga uku"


"sopy rufe ni sanyi nakeji xaxxabi ne ajikina "


" sannu kasha magani "?

" Aa baxan iya shaba kawo bakin shayi kadan "


Fita tayi ta dafa masa tahado masa da abinci takawo da kyar ta taimaka masa ya tashi yajingina da pillow ya karbi shayin yafara sha da kyar yasha rabi abincin tafara bashi yadan ci shima dan ta matsa masa ta bashi magani yasha dubanta yayi yace


" sopy ina Fadilaty binty "?


"tayi bacci, Dee meyafaru kadawo bansaniba kuma kayi wanka da ruwan sanyi ko?


" raina ne abace safiyya shine nai wanka da ruwan sanyi "

" Haba Dee dan ranka yabaci sai kasawa jikinka ruwan sanyi bayan kasan illar da yakewa jikinka "

" bazan kumaba sopy, dakko Fadilaty mu kwana anan "

" ok"


Fita tayi ta dakko ta tadawo karbar ta yayi ya kwantar da ita kusa da shi ya juya ya rungume matarsa take yaji damuwarsa ta gushe lallai ya yarda safiyya itace rayuwarsa a haka bacci ya dauke shi cikin dare safiyya tazame jikinta ta tashi tayo alwala tazura hijjabinta ta fara sallolin nafila


Washe gari Assadiq yashirya yaje gidan yaya hannatu yafada mata yadda sukayi da momy haushi ne yakamata ta dube shi tace


"wlh Assadiq bana son abinda momy takeyi nifa hankalina har yanxu be kwanta da auran Muwadda ba "

" wlh kuwa yaya bani da matsala da mata ta banasan abinda xai bani ciwon kai to nafahimci yarinyar tana da damuwa "


" bakomai Allah ya tabbatar da alkhairi, yanxu kaje ka kaimata kudin karbarta da halinta "


" Gsky yaya baxanje ba amma abokina B malik yana gari innaje office xanbashi kudin yakai mata "

" shikenan Assadiq yanxu yaushe xaa fara bikin "

" oho musu, nifa bansan komai ba nasan dai ranar lahadi daurin aure "


" oh ni hannatu wannan wane irin ango kenan "


" ai nagama biki yaya tunda na auri Sweet sopy "

" Assadiq mijin sopy, ina 'yata fadila?

"Lpy kalau sai sabga tunda tafara tafiya shikenan aka banu bata xama "


" ai dama, yakamata a yayeta tunda safiyya xata koma makaranta "


" ni tausayinta nakeji wlh kawai acireta daga nono "

" au to abarta Assadiq kar ka bari ayayeta yarinya ta girma to me yarage "

" zaai yaya ina su ashraf "?

" suna school "

Sallama yai mata yatafi yana xuwa office yabawa B malik kudi musu yauwa yakaiwa Muwadda bayan yaimasa kwatance
Haka yabawa safiyya itama tayi hidimar biki




Yau takama laraba yau aka fara bikin Muwadda da Assadiq yau kamu tun safe su farhana suke shiri gidan su Muwadda suka tafi ita da afifa jalila kuwa kin binsu tayi

Muwadda kuwa tana gurin salon ita da kawarta naeema da kanwar saurayin ta rushida muktar dinne yakaisu a motar ta

_to Muwadda basu rabu da muktar ba kenan_๐Ÿค”


Suka gama yamaida su gida nan akafara shirin tafiya kamu su farhana sun rasa wacece rushida tambayar Muwadda sukayi tace yar kanwar abban ta ce

Amarya anfito ansha kyau gashin nan yaci atach wayarta ta dauka tashiga neman layin Assadiq akashe gurin mamanta tanufa kmr xatai kuka tace

"mama inata kiran layin Assadiq akashe "

" bari inkira ya kareema

"bugu biyu ta daga nan ta tambayeta ina Assadiq ya shiga momy tace bari ta nemi wayarsa neman duniya baasami Assadiq ba haka akai kamu ba ango kmr yadda aka tsara sai da aka kusa tashi Sannan Dr almustapha yakawo jalila abin yabatawa Muwadda rai


Ana gama kamu momy tanufi gidan Assadiq tana xuwa ta tatarar da safiyya a kitchen fadila tanata ta wasanta Sallama tayi tasami guri ta zauna safiyya taji kmr muryar momy tana fitowa taganta takarasa tai mata sannu da xuwa taamsa a takaici dubanta tayi tace


"bawani abune yakawo ni ba xuwa nayi infada miki kifita a idona in rufe kin hana Assadiq sakat kibarshi yai biki kmr yadda yai naki nasan makircin ki ne yahana shi xuwa kamu to wlh kishiga hankalinki kuma bake ba Muwadda kinji dai nafada miki "

" wlh momy rabona da Assadiq tun safe inata kiran wayarsa akashe "


" ke tashafa nade fada miki "

Tana gama fada tai gaba ko fadila bata kulaba idonta yarufe safiyya tai kuka kmr ranta xai fita karatun kurani ta kunna take tasami saukin damuwarta



Washe gari diner Assadiq ya furje bazashi sai da safiyya tai da gaske

Please Login or Register in order to submit comment