Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

duka, shifa duka da kike gani baya gyara sai kangarar wa "



" shikenan Dee xan kiyaye "


" yauwa sopyn Assadiq yafada yana janta jikin sa ahankali ta kira sunan sa




"Dee, dazu munyi waya da farhana, nan tabashi labarin yadda sukayi da farhana murmushi yayi kana ya dubeta yace



"sopy kenan, to ke kintaba ganin wani yashiga hurumin gidan wani to in kira ibraheem ince masa me, baa haka tayi hakuri tabi umarnin mijinta kawai "



" Amma Dee....


Kan takarasa ya toshe bakinta dana sa bayadda ta iya haka takyaleshi yashiga sarrafa ta yadda yake so



Abangaran farhana kuwa har tasaba da dawainiyar *kannan mijinta* yanzu haka zaune take a parlor tana kallo masari ce tafito da wani plate cd a hannunta kai tsaye gurin tv ta nufa tasa, cikin bacin rai farhana ta

Dubeta tace, "ke, masari kike ko wa?, wani irin iskanci kenan ina kallo zaki zo ki sa min wani abun daban"



"Hmmm, amarya kenan, A baki bata ba masari suna na ko kice zee, inbanda abinki wayaki waazi ke mufa baa cika kallo a gidan nan ba gwanda ma ki sani "

Cikin zafin nama farhana takaiwa masari mari da azama fatisa ta rike hannuta mamaki ne yacika farhana ta kwace hannunta nan sukai mata tatas daki ta shige tai ta kuka ranar ko girki batai ba

Ibraheem yana shigowa su fatisa suka sa kuka wai farhana ta xagi malam, ransa ne yabaci cikin sauri ya nufi dakin tana kwance a gado yafara mata masifa



"farhana me yakai ki zagin mahaifin mu, akan wane dalili "


" ibraheem wlh karya suke min ta yaya zan zagi mahaifin ku bari kaji fa yadda akai........



"yimin shiru farhana baki da abinda zaki cemin karya ba halin mmu bace dan haka kijira hukuncin da zai biyo baya dan ina sonki bashi zai baki damar cin mutuncin yan uwana ba "


Yanagama fada yafita kai tsaye part din hajiyar sa ya nufa muryar fatisa yaji tana fadawa hajiya abinda farhana tayi gaban sa ne yafadi saboda yasan zafin hajiyar tasu intaji be san matakin da zata dauka ba


Haisam ne zaune acikin mota afifa na gefansa taci kwalliya sunata tsara bikin su wayar sa tana hannunta kiran shukura ya shigo kallon sa tayi tace


"Darling shukura fa?

"Dan Allah manta da ita kanwa tace, bazai wuce zancan biki zatai min ba kinsan tunda bikin nan yakarato bata da aiki sai tsare tsare "

" Allah sarki ai daka daga "


" manta da ita muci gaba da hirar mu, yauwa dady fa yace da anyi bikin mmu zamu wuce england "

" Kai amma naji dadi sosai Allah ya kaimu

"Ameen tawan "


Jalila ce zaune tana karatun wani littafi wayar ta fara ringing tana dubawa taga *Doktar*nan tadaga suka gaisa tambayarta yayi

" habibty me kike shiryawa game da bikin mmu "


" Gsky sai kazo tukunna "

" to shikenan ba damuwa, amma fa maganar gaskiya ni ba me kudi bane "


" Haba dokar dan Allah nifa bandamu da kudi ba kai nake so "



Dariya yayi sukai Sallama ta kashe wayar, yau tun safe Muwadda ta tashi da nakuda tun da aka fadawa momy takasa zaune takasa tsaye asibiti aka kaita sai ihu take hankalin Assadiq ne yatashi haka mamanta har yamma bata haihu ba dole Assadiq yasa hannu zaai mata cs




*NASEEBA GAWO*
✍🏻
[5:55Am,2017]


*®💦💦TALENTED WRITTERS FORUM*💦💦💦


*💦T F*💦





*KANNAN MIJINA*
👩‍👩‍👧


*NA*

NASEEBA I UBA💐






*ya hayyu ya kayyumu bi rahamatika astagisu aslihil shaani kullahu wala takilni ila nafsi darfati ainin* 👏🏻





💦
*TALENTED WRITTERS hadin kanmmu shine alfaharinmmu*💦





*🎈Hip hip hurry*🎈

*💙2day is a worndafull day 4 u suhyla mustapha khalid whish u plenty years a head*💙


*Happy birthday 2 my dear suly*😘








*86*





~~~Dab da zaa shigar da Muwadda dakin tiyata ne Allah ya sauke ta lpy ta haifo yarta mace amma tasha jiki sosai murna gurin Assadiq baa magana haka momy sai murna take anhaifa mata takwara maman Muwadda kuwa hankalinta yana kan yarta ita so tayi ta haifo namiji sai gashi hakan bata samu ba aka kintsa mejego da baby kai tsaye dakin hutu aka kaita kan kace kwabo asibiti ya cika ya hannatu ma tazo tare da nabil da ashraf yaran sun zama manya Muwadda kuwa hankalinta yana kan babyn ta sai da magariba safiyya ta zo dauke da abinci fadila tana ganin baby ta karasa sai murna take aunty ta sai baby safiyya ta gaida su momy tare da yimusu barka mai da dubanta tayi ga Muwadda


"sannu Muwadda, ya jiki"

"Alhmdulillah, aunty da sauki "

" mashaallah, Allah yaraya baby "

" Ameen nagode "


Safiyya ce ta ja ya hannatu suka fita waje, domin tattaunawa akan matsalar farhana


" ya hannatu, dan Allah ayi wani abu game da matsalar farhana "


" maman fadila kenan ke har kin manta iskancin da yaran nan sukai miki, to me zaai mata kowa ai da haka yasaba rayuwar aure saboda haka ki kyaleta ta dan dana"


"haka ne yaya amma.......


"safiyya mubar maganar farhana mushiga wata "


" shikenan yaya "




Kwanan muwadda 2 a asibiti aka sallamota mamanta taso tafiya da ita gida Assadiq yaki yarda dole suka hakura aka kaita gidan momy daki guda aka bata nan dinma dole akai masa afifa sai murna take ansami takwarar momy shiru kawai take musu amma ita sunan mamanta zaasamata kullum safiyya zata shigo ta ga baby sannan ta wuce school momy zata kulata ba yabo ba fallasa


Faruq ne zaune a parlo bayan Yadawo daga kai fadila jalila ya kwallawa kira da sauri tafito


"yaya faruq gani "


" alhuda huda, karatun ake yi ne "?


" yaya faruq alhuda huda kuma nazama "


" sunan da yadace da ke kenan, yauwa jeki dakko min babyn nan inganta "


" to, yaya "


Tana shiga ta tatar da Muwadda na bata nono, karasawa tayi kan gadon ta dubeta tace


" aunty Muwadda ya faruq ne yace abada baby zai ganta "


Shiru tai mata sai can ta nisa tace


" to, yanzu zanrabata da nono ne ko kuma yazaai?


"kmr yaya, kawai kibada ita shine zaki tsaya kinaimin dogon turanci "


" inya matsu ya shigo mana yaganta, ko kuwa zai gwada min iko irin na *kannan miji* ne"


"me abin iko anan daga ki bada baby sai kice wani zaagwada miki iko to angwada ikon yar ke kika haifeta ke kadai ne "


" oho miki jalila, amma wlh ba inda zaaje min da baby "



Fita tayi tasameshi zaune inda tabar shi dubanta yayi yace


" jalila ina babyn?


Nan tabashi labarin yadda sukayi da Muwadda shiru yayi can yanisa yace



"lallai yarinyar nan rashin mutuncinta ya isa, dan ta haifi ya shine zata ninka rashin mutunci, tabar 'yarta nafasa ganin yar "


Momy ce tafito daga dakinta ta dubi faruq tace


" to, sarkin rikici me yafaru kake sababbi "


" momy ni da mara mutuncin yarinyar nan ne mana "

" safiyya ko?


"safiyya kuma, aunty safiyya zankira da mara mutunci, wa ccan de "

Nan yabata labarin abinda tai masa yanzu, shiru tayi ta tashi dakin Muwadda ta nufa tana rungume da babyn dubanta tayi

tace," Muwadda meyasa kike haka ne?

"momy me nayi kuma?

"ya faruq zai aiko abashi baby yagani kice aa akan wane dalili "?


" Haba momy, shi faruq din wa yafi da bazai yaganta ba zai wani aiko "


" yaisa yanzu dai ki kawo ta akaita gurin alhaji yaganta ko shima bazaki bada akaita ba "


" aa akaita mana "


Daukar ta momy tayi tafita faruq tafara mikawa kin karbar ta yayi ya leka yaganta a hannun momy


" gata nan kuwa kamar su daya da uwarta, Allah yasaba hali "


" Ameen ya faruq "

Cewar jalila tafada tana gyra xaman glass din fuskar ta momy de dariya tayi ta wuce saman dady

Kiran farhana ne yashigo wayar afifa wacce tashigo parlon yanzu


" Hello, aunty farhana ya kike ya ibraheem "

" Lpy kalau afifa, Hmmm ustaz zakice "

" aa kice da matar malam nake magana "


" ke de bari afifa ai abin baa cewa komai, ya aunty muwadda da baby "?


" Lpy kalau, ashe kinji haihuwar "


" naji kinsan kusan kullum sai ustaz sunyi waya da yaya Assadiq to shi yafa da masa "


" ok, ya *kannan mijinki* kuwa?


"yan iska de zakice shegu, kinga ki turo min pics din baby ingani kafin muzo suna "


" tohm shikenan aunty farhana "


Sallama sukayi ta kashe wayar take ta tura mata pics din



Sanda momy takewa dady baby yana toilet sai da tajira shi yafito sannan ta bashi yar yaganta yasa mata albarka tare da mata addua dagowa yayi ya dubi momy yace


" ita kuma wannan ya sunnanta "?


" Hmm alhj kenan ai takwara ce "

" to ba laifi Allah yaraya, ina sarkin surutu kwana 2 bata zo karbar kudin alawa ba "


" Fadila ta shiga makaranta shi yasa take wuyar gani



Ina ruwan fadila "

Karamar sarka ya dakko ta gwal yabawa baby, sai dai bata kai girman ta fadila ba


Momy tai masa godiya ta sakko lokacin maman Muwadda tazo suna daki ita da yar
tata suna shirye shiryen suna momy ta turo kofar tashigo

Nan suka gaisa da yar uwar tata ta bada sarkar da dady yabawa baby sukai godiya haka momy ta hado kayan barka wai ai takwarar ta ce dole taimata Muwadda ce tadago ta dubeta tace



"momy takwarar ki kuma, gaskiya sunan mama zaasamata "


" Muwadda kiri kiri kike cewa sunan mahaifiyar ki zaasa miki, baki ji kunyata ba "


" aa mama kijifa ingama shan wahalar sannan sunan ma sai anzaba min, gsky nide...........


"yi shirunki Muwadda, haba yaya kareema kibar yarinyar nan tazabi sunan da take so asawa yar nan mana "


" shikenan aisha nabari asa mata wanda take so din Allah yaraya mana baby "



" Ameen yaya "






Farhana ce taje gaida hajiyar su ibraheem tana shiga tasami guri ta zauna tagaida ta taamsa a takaice can tanisa tace


" farhana naji abinda kikayi mungode madsllah to amma bari kiji daga yau kar ki sake kunna mana kallo a gidan nan, kuma kullum kar ki bari karatu ya wuce ki kidinga fitowa da zarar kingama aiki, ki zauna lpy da kannan ki kidena kallon su a matsayin *kannan mijinki* dafatan kin fahimce ni banason musami matsala da ke farhana "


" wlh hajiya yanzun ma bani da laifi sune suka fara takalata musamman zainab tafi yimin wulakanci "


Nide banason maimaita magana, ke bilkisu tashi ki rakata ta gaida malam"


Tashi sukayi suka fita zuwa bangarsnsa yana parlon sa da tulin littattafai a gabansa suka tsuguna suka gai dashi ya amsa da sakin fuska yadora da



"yata kina lpy dafatan dai ba matsala "


" ba komai malam, andawo lpy "

" Lpy kalau, anfada miki ana karatu da asuba ko?


"eh anfada min "


" to madalla, Allah yai muku albarka "


" Ameen "

Tashi sukayi suka fita bilkisu yakira taamsa


" bilkisu ki turo min jaafar da malam karami "


" to "



Suna fitowa farhana tai bangaran ta su fatisa ne a parlon sun baje littattafai suna karatu parlon kaca kaca ga shi sun bude mata showglass dubansu tayi tace



" zainab ya kuka bar min showglass a bude "


" eh kamshi muke ahaka ko munyi lefi "


" oh tambaya ta kike to bansaniba "


Dariya suka sa mata suka ci gaba da abinda suke shiru tai musu ta nufi kitchen ta dora girki, tagama ta zubawa kowa nasa ta dauke na ibraheem inbahaka jaafar da yagani zai dauka tayi magana ibraheem ya rufeta da fada



Karfe 8 ibraheem ya dawo gidan tayi wanka tacaba adonta cikin kananun kaya tayi kyau yana shigowa yai tozali da ita rungume ta yayi tare da sakar mata kiss


"mashaallah, matar ustaz kinyi kyau "


" nagode ustaz dina, muje kayi wanka kazo kaci abinci "


Daki suka shiga yayi wanka yasa jallabiya duk abinda sukayi akan idon su fatisa ne masari ce mai kwaikwayar farhana suka tuntsire da dariya


Parlon suka fito tazuba masa abinci yafara ci dubansa tayi tace


" ustaz jibi sunan aunty Muwadda dan Allah zanje "

" aa farhana gaskiya ki hakura kinga bikin su jalila ya kusa sai kuje tare da su bilkisu "


" Dan Allah ustaz "

" dakata farhana banason magiya dan haka mubar zancan haka "

Fitowar su fatisa ne yasa ta koma cikin dakinta tasa kuka sukuwa zaman su suka yi suka taba hirar su da yayan nasu


Ahankali ya tura kofar dakin yashiga tana xaune tana cin farfesun kajin da momy tai mata kan gadon yanufa yasa hannu ya dau babyn
Ahankali ya furta,

"uwata ta kaina, Allah yaraya ki "


" sweery wane suna kenan "?


" wace irin tambaya ce wannan "


" eh munyi magana da momy tace sunan mama na zaasa "


" to ni banyarda ba ke yakamata ki sa mata suna ko ni, dan haka sunan momy zansa "


Yana gama fada ya ajiye babyn yafita kai tsaye dakin momy ya nufa tana xaune ita da yaya hannatu suna tattaunawa kan taron sunan da zaai
yai Sallama ya shiga ya gaida su duban yayar tasu yayi yace

" yaya saukar yaushe?


"tun dazu nazo Assadiq "


Momy ce tadubeshi tace

" Assadiq wane suna zaa sa wa babyn?

" momy nida sunanki zaa sawa yarinyar nan "


" Hmmm Assadiq Muwadda taki wai sunan maman ta zaa sa mata"

"eh yanxuma haka tace ni dai nace aa "


" aa bakomai asa mata ai dani da aisha abu daya ne bakomai "


" amma momy...



"ya isa hannatu abar maganar haka "





Assadiq rai bace ya koma gida safiyya na kitchen taji shigowar sa guri yasamu ya xauna ya nata kada kafa fitowa tayi tasameshi


" Dee lafiya kuwa?

" bakomai bani ruwan sanyi insha "


Kawo masa tayi yasha ya kwanta bata matsa masa taci gaba da aikin ta sai da tagama ta shirya taje kaiwa Muwadda kayan barka fal tai ta godiya nan take fadamata sunan mama aka sa tai mata Allah yaraya ta dawo gida a parlon ta tatar da su shi da fadila suna cin abinci tasami guri ta zauna suka ci tare da kyar tasamu ya dena fushin da yake,


Ranar suna yarinya aka sa mata aisha afifa tace sai adinga ce mata humyra
Cikin yatsine fuska Muwadda tace


"aa bawani humyra *hamra*zaa kirata "


Bayadda suka iya haka suka hakura ansha suna ankashe kudi safiyya kam a gidanta tayi nata taron da yanuwanta taro yatashi lpy dan Muwadda kin sakarwa su afifa tayi kawayanta ne akan komai



.muktar ne zaune a dakinsa Yana ta gwada layin Muwadda yaki shiga tsaki yaja ya cillar da wayar gashi rushida bata nan ballantana yaji labarin halin da Muwadda take ciki abokinsa ne yai Sallama ya shigo


"abokina lpy dai ko, kai da zanga ka kana murna budurwar ka ta haihu sai Inganka a hargitse "


" nazifi meyasa wani lokacin kafiya soki burutsu ne wacece budurwa ta "

" Muwadda mana "

" karya kake nazifi "


" wlh abokina ba wasa nake ba "

" kut ashe kuwa akwai balai, amma shegiyar yarinyar nan bata fadan ba "

" wa kenan "?

" rushida mana ai kuwa sai taci ubanta "
Can kuma me ya tuna yasaki wani malalacin murmushi




*NASEEBA GAWO*

✍🏻
[6:21Am,2017]



*®💦💦TALENTED WRITTERS FORUM*💦💦💦


*💦T F*💦





*KANNAN MIJINA*
👩‍👩‍👧



*NA*

NASEEBA I UBA💐




*Alhmdulillah Alhmdulillah hakika Allah kaine abin godiya ayau muka shiga sabuwar shekarar musulunci alkhairin da yake cikin ta Allah kasada mu da shi sharrin da ke ciki Allah ka nisanta mu da ga shi Allah ka albarkaci rayuwar mu kacika kowa burinsa na alkhairi ka karemu daga sharrin mai sharri AMEEN*👏🏻


*Allahumma salli ala sayyadina muhammad wasallim*📿



*wannan shafin nakine sadnaf💅🏻 ina 💞tayaki murnar kammala novel din ki DAGA TAIMAKO🙆🏻 a gaskiya kin nishadantar kin waazantar Allah yakara basira yasa kifi haka naseeba💐 na biye da ke*




*87*



~~~sallamar rushida ce ta katsewa muktar tunanin da yake cikin sauri yafito daga dakinsa tare da yimata wani mugun kallo yadora


"ke, dan uwarki zo nan shegiya mai suffar munafukai "


" aa haba yaya muktar me nai maka daga dawo wa ta "

" uwarki kikaimin tunda tambayata ma kike, dama Muwadda ciki ne da ita har ta haihu, saboda ke manafuka ce baki taba fadamin ba "


" Hmmm yaya muktar kenan to meye alakar ka da cikinta, tabbas nasani itace tace kar inbari kaji "


" yayi kyau, to naji amma abinda nake so dake shine kar ki fada mata nasan ta haihu mutafi a bansaniba daga nan zuwa sanda burina zai cika "

" yaya buri kuma, wani irin buri kenan "?


" to yar jarida ke de kiyi yadda nace, kema zaki shana wlh "

Tohm shikenan yaya na, kuma fa munyi waya da ita bata fadan ta haihu ba"

"to ba munafuka bace, kibarni da ita zan koyamata hankali "

" yaya muktar umma fa "?

" tafita aiki "


" ok bari inshiga ciki in huta sai inje gidan nata "






Muwadda sunyi arbain ansha fama dan kullum cikin rashin mutunci take momy kam ta kosa ta koma gidanta yau tun safe take shirin komawa gidanta Assadiq ne yai Sallama ya shigo

Guri yasamu ya xauna ya dubeta bayan ya dau hamra dubansa tayi tace

Papan hamra dama tun dazu kai nake jira "

" ina jinki, ya kwanan baby ta "

" afuwan ina kwana "

" Hmmm lpy "


" dama ina son zuwa gida ne in kwana 2 saboda arbain din da nayi "

" aa ba kwana 2 zakiyi ba shekara biyu zakiyi, to ban yarda ba ki shirya in saukeki ki yini zuwa dare zanzo in dauke ku "


" gaskiya sweery ni dai.....


"dakata muwadda nariga nagama magana inkin yarda ki shirya in baki yarda ba ki hakura ina parlo ina jiranki "


Daukar hamra yayi ya fita parlon su faruq suna zaune suna break fast yasami guri ya zauna momy ce ta dube shi tace


" Assadiq Muwadda tace maka zata gida ta kwana 2 ko "

" tafada min momy nace aa "

" yauwa yaya kar ka barta wlh saboda shiririta kawai sai ta wani tafi gida ta kwana "

" faruq me yashafeka da zakasa mana baki, ina ruwanka "

" Allah ya baki hakuri momy na, sai na dawo "

Yafada yana kokarin tashi bayan ya kurbi tea yaajiye kofin hannunsa yafita


Fitowar Muwadda ne yakatse musu zancan da sukeyi tacaba ado tayi kyau sosai tasami gefan Assadiq ta zauna momy ce ta dubeta tace

" Muwadda kin shiryo, saa takai miki break fast ko "


" takai min amma banci ba in naje gida naci acan "


" to ai shikenan, Allah ya kiyaye hanya "

" aunty Muwadda pls inzo inraka ki "

" bangyyace ki ba afifa dan haka kisha zamanki "

Karbar hamra tayi a hannun Assadiq tai waje Sallama yaiwa momy ya rufa mata baya suka nufi gurin mota suka shiga yajasu suka tafi



Abangaran haisam kuwa burinsa ya cika yagama shirin sa tsaf yaje gidan su abokinsa yanemi alfarmar zaa kawo amaryar sa nan amatsayin su na iyayen sa suka amsa da bakomai ai shima dansu ne tunda abokin dansu ne

Shukura kam yau takai bango jiransa take ya dawo ya fita ysbarsu ba abincin kirki cikin ikon Allah sai gashi yashigo tana parlon su dan madaidaici

"Shukura uwar gidan haisam uwar gida ran gida "


" banfahimce ka haisam baka taba yimin irin wannan kirarin ba ko meye hakan yake nufi "

" to shikenan bazan kodaki ba sai yazama laifi, Allah to ya huci zuciyarki mata ta, kawo min abinci "


" ba abinci zankawo maka kasuwar dawano zankawo ma "

" to, yadabakar bagana kuma, me yayi xafi shukaran haisam "


" kafini sani ai, tunda kasa kafa kafita baka sake bi takanmmu ba sai yanzu zaka kwaso yanmatan kafafunka kazo kace abinci "


" shikenan ya isa tawan, yanzu bari infita indawo "


" Kai kasani kuma "

Fita yayi yanufi kasuwa acikin kudin bikin sa ya diba yaimata siyayyar kayan abinci yakaimata tai ta murna tadora musu girki suka ci dubanta yayi yace

" Shukura zanyi tafiya zuwa adamawa a kalla zanyi sati uku "


" tare zamu tafi amma ko "?

" aa, kibari inje indawo tukunna "

" shikenan haisam Allah yakaimu "

" Ameen, ina su hafiz "?

" suna gidan mu "




Safiyya ce kwance a jikin Assadiq suna hira cikin so da kauna can tadago
dakanta ta dubeshi bayan ta shafi sajen fuskar sa

" Dee kasan me?

"sai kin fada sopy "

" wlh hankalina be kwanta da saurayin nan na afifa ba "

" Hmmm, to ai ita taji tagani ko, dan haka sai akyale ta "


Hayaniyar fadila suka jiyo tai saurin barin jikinsa rike ta yayi tsam ajikinsa dagowa tayi tace

" Dee bakaji fadila zata shigo ba sai tazo taganni a jikin ka ko "

" and so what "

" to badaniba, gaskiya "
.
Da gudu ta shigo parlon tana xuwa ta fada kan Assadiq

" oyoyo papa, inata jiranka kazo ka daukeni a school baka zo, na dena kula ka "

" ho, Fadilaty bakisan uzurin da ya rike ni ba, yanzu wa ya dakko ki "

" uncle dina "

" to bashi kenan ba, wuce kije kicire unifoam dinki "

" Kai wlh ban iya ba mamma "

" zo incire miki binty "

" yauwa papa na gurin hamra zani aunty ta goya min ita"

"kide yar da ita, wa zai baki yarsa "

Safiyya tafada tana kokarin tashi bayanta fadila tabi suka nufi daki


Abangaran farhana kuwa tun dare take fama da zazzabi da amai hankalin ibraheem ya tashi da sassafe suka shirya Suka nufi asibiti sai da tasa katon hijjab da nikaf sannan suka fita gwajin farko aka gano tana da ciki na wata 2 murna gurin ibraheem baa magana suka dawo gida suna zuwa ta kwanta be jimaba yai shirin fita kasuwa dubanta yayi yace


"farhana in kinji dadin jikinki ki dafa abinci kinga su fatisa sunkusa dawo wa daga makaranta "

Da mamaki tadago ta zuba masa ido, tarasa ma me xatace masa shiru kawai taimasa yasa kai yafita



Yau aka kawo kayan lefan afifa kaya bana wasa ba akwati saiti 2 shake da kaya momy sai murna take afifa tayi goshi

Washe gari aka kawo na jalila saitin akwati daya kayanta masu kyau da tsada nan afifa tai ta dariya aka sa biki sati uku

Bangaran gidan su safiyya ma ankawo na yaya amina da angonta khalifa shirye shirye kawai ake


Muwadda ce zaune ita da Assadiq kiran muktar yashigo wayar ta Assadiq ne yadau wayar yana dubawa yaga sunan *muktar*






*NASEEBA GAWO*
✍🏻
[8:57Pm,2017]



*®💦💦💦TALENTED WRITTERS FORUM*💦💦💦


*💦T F*💦





*KANNAN MIJINA*
👩‍👩‍👧



*NA*


NASEEBA I UBA💐





*Allahumma la sahala illa ma jaaltuhu sahala waanta tajalu haznah iza shi itu sahala*👏🏻





*💦TALENTED WRITTERS hadin kanmmu shine alfaharinmmu*💦






*Ina taya kiyaya group murnar karuwa da muka samu na babies hauwa munir da suwaiba sale bala mai salla Allah yaraya mana kiyaya🎓 2009 munzama mamas😂Allah ka sauki mama aliya sani shehu mai hula lpy ameen*







*88*




~~~cikin tuhuma yake kallon ta dakewa tayi ta karbi wayar kan ta daga kiran ya katse cikin shakewar murya yace

"Muwadda waye muktar "?


" Oh yayan rushida ne fa, kuma nafada maka alakar mu tun tuni "


" Muwadda yaakayi bansan su ba ne "?


" eh bazaka san su ba gsky, ba a garin nan suka fara zama ba "


Shiru yaimata badan ya yarda da ita ba yagama shirinsa ya fita zuwa office

Yana fita ta kira layin

Please Login or Register in order to submit comment