Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mutunci kawai"

"Haba momy kitan
bayeta mana,garin iskancinsu tasa safiyya tayi bari,gata can a asibiti bata san inda kanta yakeba"

"Dalla rufe min baki
tayaya jalila zata sa
matar assadiq tayi bari
garin dai sha shancinta tai bari"


Dady ne yaji hayaniyar
tai yawa yasakko yake tambayar me yake faruwa,faruq ne yabashi labarin abinda
yafaru,shiru yayi yadago yakalli jalila cikin bacin rai

"Jalila me yafaru"?

"Ummm,Dady wanke wanke naimata sai kitchen din yajike,na
manta bangoge ba"

Nan yarufeta da fada sosai ran momy yabaci,suka dunguma
sukatafi asibitin sanda suka karasa assadiq yakifa kansa akan gadon da safiyya take
yanata kuka,su dady sukai sallama suka shigo,kasa dagowa yayi sai da dady yai magana sannan yadago,


"Haba sadauki sai kace bana mijiba,Allan da yabaka aishi zaibaka wani kayi hakuri kaji"

"Dady safiyya mutuwa
zatai tun da mukazo bata farkaba"

"karka kuma fada Zara
tashi"

Yaya hannatu ce takira
yayar Safiyya tafadamata,hankalinta
yatashi,taiwa ummi waya tasanar daita

sai yanzu assadiq yadago yaga jalilla wani mugun kallo yaimata,momy ma takarasa gaban gadon
taiwa safiyya sannu,

Assadiq ne yashiga tunanin hukuncin dazaiwa jalila.









*NASEEBA GAWO*✍🏻










*3
[12:44Pm,2017]


*®💦💦💦TALENTED WRITTER'S FORUM*💦💦💦

*💦TF*💦





_**KANNAN MIJINA_**
👩‍👩‍👧




*NA*

*NASEEBA I UBA*💐






*34*



~~~Mikewa yayi,yazo
gaban jalila yazuba mata ido yace,

"Jalila kinga abibda kikaja min ko kinjawo
narasa babyna "
yana magana hawaye
na ambaliya idonsa,


"yaya pls kayi hakuri
wallahi bansan haka
zatafaru ba,kayi hakuri
I will never do it again
forgive me"

shigowar su ummin safiyya ne da yayanta
Dr almustapha ne yaka
tse masa maganar da suke da jalila,
Nan suka gaisa da su
momy sukatambayi
ya maijiki,daman dady
yadade da tafiya,
gaban gadon suka karasa tanata bacci ta
rame lokaci daya,

"sannu safiyya Allah yabaki lpy" cewar Dr
almustapha,yana kokarin dubata,

Ameen ya Allah Dr" cewar assadiq,
ahankali safiyya tafara
bude idonta,da sauri
assadiq yakarasa gaban gadon, dube dube tafarayi,can taji cikinta ya murda agigice ta fara magana

"Deeeee! zanmutu kiramin ummina wayyo Allahna"

karasawa ummi tayi
gaban gadon ta rungumeta,

"Safiyya sannu kinji gani umminki ce"

"Ummi mutuwa zanyi
ina baffana,da yayana"

"baffa yana gaidaki ga
yayanki nan"

maida dubanta tayi
ga yayan nata,tace

"yaya kayafemin mutuwa zanyi"

"yaisa safiyya waye yace zaki mutu"

Allurar bacci yaimata
akasamu tayi bacci,

tashi su ummi sukayi
zasutafi,tace amina ta
zauna daita su kwana

assadiq ne yakwantar
da kai yace,

"Ummi basai ta kwanaba zankula da ita"

"To shikenan assadiq angode Allah yakara lpy"

wani banzan kallo momy taimasa,sukai
musu sallama suka tafi,jalila ce take ta satar kallon Dr almustapha, bayan tafiyar su da kadan su
momy suka tafi suma

yaya hannatu akabari
tazauna da ita kafin assadiq yadawo,gida
yakoma yadebo mata kaya yayo mata siyayya,sanda yakoma

tafarka tana zaune yaya hannatu ce take
bata tea taki sha ,

"Yauwa assadiq zo kabata ko zata sha tun
dazu nakefama daita"

karasawa yayi gaban ta yazauna kusa da ita
yashiga rarrashinta ya
dau tea din yafara bata
dagowa tayi takalleshi
tace,

"Dee nakoshi,bazaniya shaba,cikina ciwo yake

Yaya hannatu ce tai musu sallama tatafi,
zairakata tace yabarshi yakula da safiyya,yaimata godiya

Dakansa yashiga bata shayin ta sha sai da ta shanye sannan yabata
kazar da yasiyo mata
kadan taci cikinta ta tashafa taji ba tudun dayayi,ahankali tafara
magana,

"Dee meyafaru da cikina,naji kamar babu

"Sopy kiyi hakuri Allah ne yabamu yakuma kaddaramana rashinsa

"Dee mekake nufi kana
so kace min narasa shi
kenan"

kuka tasamai nanfa yashiga aikin rarrashi

"Haba sopy kiyi shiru kidena kuka da munkoma gida zamu kuma samun wani babyn sai kinhaifa min
yaya goma"

dariya tai tadada shigewa kirjinsa yashiga rarrashinta ahaka bacci yakuma daukarta,ya gyra mata
kwanciyarta yazuba mata ido ahaka shima
bacci yadauke shi,

washegari da kansa yaimata wanka yashiryata cikin doguwar riga mara nauyi yazubamata ido
tadago ta kalleshi tace


"Dee kallo kuma,mene ne"?

"Sopy inasonka ina kaunarki,kitaimamin
duk rintsi karki kujeni
karki barni❣

"Karka damu Dee inshaallah inatare dakai"
kwanatar dani kaji"

"Aa sopy kibari kiyi break fast kafin ki kwanta yanzu faruq zai kawo abincin"

"Dee dan Allah inyakawo sai ka dagani"

"To maman baby"

"Dee baby kuma,ba munrasa cikinba"

"Zamu sami wani ai"

yaya rukayya ce ta turo kofar tashigo da katon cikinta da suhyla da babanta

hannu assadiq yabashi
suka gaisa🤝yaimasa
yamai jiki

yaya rukayya ma karasawa tayi gurin safiyya taimata sannu
assadiq ne yace zaije yadawo yaimusu sallama yafita shi da baban suhyla

suhylace takalli safiyya tace,

"Aunt cafiyya cannu,wai faduwa kikayi ko"?

"Eh suly,amma naji sauki ai"

labari Safiyya tabawa yayarta rukayya dalilin barinta,shiru tayi kana tace,

"Safiyya meyake damun *kannan mijinki*ne?

"Bansaniba aunty amma basu da kirki"

faruq ne yaturo kofar yashigo da fararsa yakaraso

"Auntyna sannu da jiki

"yauwa faruq yasu momy"

"suna gaisheki"

"ina amsawa faruq"

yagaida yaya rukayya
yabasu hakuri akan abinda yafaru sukace
bakomai yawuce suhyla tana taiwa faruq surutu aka zubawa safiyya abinci taci wanda rukayya takawo

kwananta uku a asibiti
aka sallameta kai tsaye gidan su aka wuce daita,da kyar assadiq ya yarda

sai shi kadai a gidan yana kwance a parlor daga shi sai vest sai gajeran wando ya rungume wata rigar Sopy idonsa a rufe kawai sai ganin mace yayi akujera tazuba masa ido👀









*NASEEBA GAWO*✍🏻
[6:28Am,2017]


*®💦💦💦TALENTED WRITTER'S FORUM*💦💦💦

*💦TF*💦




*_KANNAN MIJINA_*
👩‍👩‍👧




*NA*

*NASEEBA I UBA*💐



_Dedicated 2 my lovely friend_
*faeexa m usman*💦
_the typer of_ *Amuntarmu*_May God live us together sis_💙





*35*




jikinsa ne yabashi kamar anshigo,ahanka
li,yabude idonsa,da
mamaki yamike yashiga bedroom yada
kko,jallabiya yasa yafito cikin fada yafara
magana,

"ke wane irin haukane
akanki,zakishigowa
mutane gida kai tsaye"

muwaddace tanarke
fuska,tace

"yaya dan Allah kayi hakuri nayi sallama
bakajiba,dama nazo
duba aunty safiyya ne"

"Dakikazo duba Sopy
sai akace kishigomana
kai tsaye,ko kuwa bakitambayi inda safiyyan takeba,kafin
kizo"


"yaya pls kayi hakuri
kasaurareni,dama da
akwai maganar danakeso muyi"

ahargitse yafara magana,

"Muwadda! u better enter ur sence, how dare u,come 2 my home and talking rubbish 2 me,pls i beg u in the name of God live me a lone"😡


"Yaya assadiq dan Allah kasaurareni"

"kifitarmin a gida,aure
ko kije naji zan aureki
amma kisani gangar jikana zaki aura,nariga
na mallakawa sweet Sopy komai nawa"

zata kuma magana yadakatar daita,
dagudu tafita kai tsaye gidansu assadiq tawuce daman tare sukazo da mamanta tana zuwa tafada jikinta tashiga rera kuka,akidime momy tashiga tambayarta,

"yata,meyasameki keda waye"?


"momy assadiq bayasona,daga gidansa nake,ya koroni"😰

mamanta ce ta kalli momy da bacin rai afuskarta tace,


"Yay Kareema inganin
ahakura da auran nan
kawai"

"Haba aisha,kan wane
dalili,ai baabinda zaihana auran assadiq
da muwadda,ni ita nakeso"

farhanace tasa baki,
"Wallahi aunty muwadda ke mukeso
kuma kar wata mace
ta tsorataki"

"Ai momy kamata yayi
kifadawa dady kawai
yasan da maganar"
cewar afifa tana kokarin mikewa,jalila
kuwa shiru tayi ita yanzu tunda taiwa assadiq sanadin rasa cikin safiyya tashiga damuwa,gashi tadamu
da yayan safiyya,ko mehakan yake nufi?"

_To aganin naseeba dai so ne yake nukurkusar zuciyar jalila_😅

faruq ne yashigo parlorn yagaida maman muwadda,muwadda tadago takalleshi tace

"Faruq ba magana ko"

"Afuwan muwadda bankula da keba ya
kike?"

"Lpy ba lau ba"

mikewa yayi yabata amsa,da "Allah yakawo lau din"yai tafiyarsa faruq bayasan muwadda,Nan dai su momy sukacigaba da
tattaunawa.


Tun bayan fitar muwadda assadiq yashirya yafita zuwa gidan su safiyya ransa abace,yana zuwa yaimata waya gashi akofar gida lokacin Dr
almustapha,yana gida
shi yafito yashigo dashi bayan sungaisa🤝

yagaida ummi yashiga
dakin da safiyya take
tana sanye cikin atamfa ja da green,doguwar riga,anmata kitso kananu,tabazo da jelar
tayi kyau gashi ta mur
mure,ido yazubamata
yakarasa yazauna gefan katifar datake yazauna yace,

"Sweet sopy kinganki
kuwa,kebaki da damuwa ko"?

"Dee meyafaru,kaima
aibaka da damuwa gashina kayi kyau"

"Eh zaki iya cewa nayi
kyau amma bakiga yadda narameba,Sopy
bana iya bacci kinsabar min dayin komai tare dake"

"Dee ai nakusa dawowa"

janta yayi jikinsa yashiga aikamata da
sakonni,gabadaya ya gigice bakinta yashiga
tsotsa yazame dankwalin kanta,zai zuge zip dinta kenan





*NASEEBA GAWO*✍🏻
[9:00Am,2017]


*®💦💦💦TALENTED WRITTER'S FORUM*💦💦💦

*💦TF*💦




_*KANNAN MIJINA*_
👩‍👩‍👧


*NA*

*NASEEBA I UBA*💐





_Inabawa masoyana hakuri sakamakon gajartar da page 35 yayi hakan tafaru ne saboda wata tangarda dana samu_ .

*Nagode*👌🏻





*36*






~~~Ahannunsa safiyya ta rike tashiga girgizamasa kai alamar aa,

"Sopy kibarni mana,
nayi kewarki nayi kewar tattausar fatar
Jikinki"

"Dee kayi hakuri kaga
baa gida mukeba,karfa
wani yashigo"

Kan yabata amsa anyi
Sallama abakin kofar
dakin shiru aukayi yai
Sauri yagyaramata
rigarta ya dai daita nutsuwarsa,yamatsa
gefe,sannan safiyya tace ashigo,Najiba ce
dauke da katon tray anjera kuloli akai takawowa assadiq

"Yaya assadiq ga abinci"

"Yauwa Najiba kamar
Kinsan yunwa nakeji,
Kun daukemin mata ko

"Yaya ai takusa komawa tunda taji sauki muma munfiso
takoma tafiya sa mutum aiki" tafada tana dariya

"Aa badole tasaki aikiba ita dabata da lpy,kicigaba da kular min daita zanbiyaki"

"Angama oga"
Gaba dayansu sukai dariya tafita mai da dubansa yayi ga Sopy
ta matso tabude kulolin tuwon semovita ne da miyar danyar kubewa yaji naman kaji da manshanu ankullashi kamar kullin alala tasa
Masa kulli biyu taturamasa gabansa


"Sopy ni zanci da kaina gaskiya kibani dakanki"

"Dee wani lokacin kafiya rikici"

"Eh naji"

Nan tadinga bashi da hannunta yanata zuba
Santi sai da yaci kulli uku yakusa cinye wa safiyya tasamasa abaki yahada da hannunta yaciza yarkara tayi yasa hannunsa yatoshemata baki da shagwaba tace


"Dee cizona fa kayi kuma Allah sai narama

Dariya yasa yace

"To kirama ummi tajiyo muna kokawa incemata hakkinki kikeso"

"Lala Dee au bayan nataho kuma sharri ka koya"

Nan dai sukasha hirarsu daga karshe yaimusu sallama da zunmar washegari zaizo yadau matarsa,
Najiba yakira yabata siyayyar da yayomata


Kai tsaye gidansu ya wuce lokacin su muwadda suntafi jalila
tanaji ya shigo ta gudu
Yasami guri yazauna yagaida momynsu tahade rai tace


Assadiq daga ina kake
?

"momy naje naduba jikin safiyya ne"

"Wato kai baka dawata magana sai ta safiyya ko,me kayiwa muwadda dazu?"

"momy mezanmata wani abun tace nayimata"

"Bansaniba assadiq to ka saurareni kaji da kyau inaso kaje kasami dadynku kaimasa zancan muwadda kuma ka nuna masa Kaine kakeso kadai jini ko"

"Naji momy"

"yaushe zata dawo matar taka?"

"gobe"

"ba laifi,katashi kaje kaci abinci"

"Nakoshi momy"

farhana ce tafito tasami guri tazauna tadubi yayannata race

"yaya aunty muwadda tace wai ka kirata"


wani mugun kallo yaimata yatashi yatafi
murmushi kawai momy tayi

yana komawa gida yai wanka yahau gado yadau wayarsa yakira sopynsa suka sha hira
sunacikin hirar tyi bacci addua yaimata yakashe wayar yana kashewa kiran muwadda yashigo tsaki yayi ya kashe wayar ya kwanta.



washegari tun safe aka
kirawo mai kunshi tazo taiwa ssfiyy ana cikikin kunshin yaya rukayya tazo takawowa safiyya magun gunan gyaran jik, ummi tai taimata nasiha mai ratsa jiki,tare da nunamata girman hakuri kan Rukayya ta koma tace

"Rukayya inkuma ganin kafarki agidannan inbaso kike kihaihu a hanyaba"

"Dariya sukayi gaba dayansu,Da magariba assadiq yazo yadau mtarsa Baffa yaimusu nasiha sosai yayanta yabata 20k tatafi tana kuka,assadiq ne yadubeta yace,.

"Haba amaryar assadiq meye na kuka
muda zamusami baby
adaran nan"

shiru taimasa ahaka suka karasa yanata rawar jiki,aranar assadiq yayi kwanan farinciki dan sopy takoma masa kamar amarya,washegari dakansa yashiga kitchen yahada break fast yatasheta sukai wanka suka shirya cikin wata shadda sky blue iri daya sunyi kyau sukasha hotuna🤳🏻suka koma parlor sukai break da kamar bazai fitaba dady yaimasa waya yazo zasu unnguwa haka tafita badan yasoba,ya kalli Safiyya yace,

"sweet Sopy,ki kular min dakanki"

"To Dee kaima haka"


yaja motarsa yafita,be jima da fitaba sai ga afifa tarako muwadda
kallonsu safiyya tatsaya yi tace

"Sannunku,,kushigo mana"

"Aa bazama zamuyiba
yayafa"

"yafita,yasu momy afifa?"

"Tana gaisheki,tanai miki yajiki,ai mu yanzu tsoran shigowa muke
kar muje mukuma zubar da ciki"

kantabasu amsa assadiq yashigo muwadda ce tamaida dubanta gareshi takalli kayan jikinsa takalli na safiyya .










*NASEEBA I UBA*✍🏻
[10:22Pm,2017]



*®💦💦💦TALENTED WRITTER'S FORUM*💦💦💦

*💦TF*💦




**_KANNAN MIJINA_**
👩‍👩‍👧



*NA*

*NASEEBA I UBA*💐




_Ina gaisheki Kawata ina miki sannu bisa zazzabin da kikayi 2days Allah ya kara sauki yasa kaffara Ameen_
*Sadiya smart*

~Talented group admin~💦








*37*







~~~Kallonsu yayi a wulakance yadada tamke fuska yace,

"Uban me yakawoku gidana"


"Ummm yaya dama aunty muwadda narako"


"Tayimana me"?

Sopy ce tariko hannunsa tace,


"Haba Dee meyasa haka,yakamata kasaurareta"


"Kibarta sweet sopy,metakeso inmatane"?

Hannun matarsa yaja suka shige daki sukabar su atsaye afiface tadubi muwadda tace,

"Aunty muwadda zo mutafi kuma wallahi zatasani munafuka kawai"

Fita sukayi suka tafi gida,safiyya kuwa suna shiga daki tafizge hannunta daga na assadiq tace,


"Dee Meye tsakaninka da yarinyar nan yau sai kafadamin tsakaninku"

Jikinsa yajata yakurawa kyakkyawar fuskarta ido yace,

"Sopy banason bacin ranki,farincikinki shine
Nawa,shiyasa naki fadamiki tsakanina da muwadda"


"Dee kafadamin mana"


"Sopy muwadda itace yarinyar da momy takeso inaura"

"Deee yaushe😳nashiga uku"


Dada rungumeta yayi yashiga shafamata bayanta ahankali cikin kwantar da murya yashiga rarrashinta da banbaki kuka take kamar ranta zaifita,

"Sopy kiyi shiru banason muwadda kenake so,kice zabina,Sopy kice rayuwata kukanki yana
kona min rai"

"Dee shikenan zamurabu ko,kadena sona,nashiga uku"


"Sopy yaisa,kinason inyi kuka ko kinason
Jefani cikin damuwa
Ko"


"Aa Dee"

"To kiyi shiru ai bayanzu zaai auranba
Kinji"

Nan dai yaita rarrashinta haryasamu takwantar da hankalinta.


Momy ce zaune akusa
da maigidanta tana bashi labarin auran da
Assadiq zaikara yai shiru can yanisa yace

"Yanzu hajiya Kareema
bazaki bar maganar yarinyar nan ba ko"?

"Aa Alhj nima bayadda
banyi da assadiq yabar maganar auran nanba yaki"

"Balaifi zamuyi maganar da shi dudu du yaushe yai auran"

"Kaima kafada Alhj to yayan yanzune insukaso abu to saifa sunyi hankalinsu zai kwanta"

"Allah yashirya"

"Ameen"

Shigowar faruq ce takatsemusu hirar da sallama yashiga suka
Amsa masa karasawa
yayi gaban dady yamika masa hannu,

"Dady barka da dare"

"Yauwa umarul faruq,dafatan kanacigaba da shirin tafiya"?


"Eh dady namagama
Shirina kawai inajiran
lokacine,to amma dady duk bayan shekara daya zandinga zuwa ganinku"

Sai yanxu momy tasa baki,"Aa kabari kagama gabadaya kazo"

"Momy dagaske dai ashe bakyasona,dady
Kaji abinda momyna
tafada"

Dariya sukayi saboda yadda yayi maganar

"Faruq tanasonka mana"

"Ka kyaleshi Alhj ai shiyasan laifin dayakemin"

Nan dai sukacigaba da hirarsu karshe yai musu sallama yasakko jalila yatarar zaune tasa littafi agaba tazuba uban tagumi yadubeta yace,

"Alhudada sarkin karatu lpy dai ko"?

Glass din fuskarta ta cire tagoge hawayan fuskarta tace,

"Yaya faruq dan Allah karakani gidan yaya assadiq indada bashi hakuri,wallahi kunyarsa nakeji"

"Jalila kenan sanda kikaimusu sanadin rasa babynsu ni narakaki,bansan kinjeba danhaka ke kadai zaki yanzunmma"

Yanagama fada yai gaba,yabarta anan

°°°°°°°°°°°°°°
Yau ne ranar da faruq zaitafi Dubai kowa yashirya dan rakiya yashiga yiwa Safiyya sallama ya tarar daita a kitchen tana karasa masa danbun kaza tagama tajuyemasa tahada masa da kilishi
tamika masa kinkarba yayi yace,


"Cab bazakirakaniba"

"Mezaihanani raka karamin maigida,yanxu zanje inshirya"

"Yauwa,ai gwanda aunty dan Allah kicigaba da hakuri da yarannan watarana zasu dena"

"Haba faruq badamuwa nagode da kokarinka gareni,Allah yabar zumunci yakaika lpy,yabada abinda akatafi nema"

"Ameen aunty nagode"

Yasakai yafita,daki takoma tatar da assadiq dukunkune a bargo karasawa tayi tayaye bargon tafara magana,

"Dee katashi mushrya
faruq zaitafi"

Wani irin hucine yafito
daga bargon,agigice tataba jikinsa,taji zafi

"Dee meyasameka,meke damunka"?

"Sopy rufeni sanyi nakeji kaina kamar zaifado"

Kuka tasa tarungumeshi ajikinta
tarasa mezatayimasa,bude idonsa yayi dayakada yai jazur yace

"Sopy kukanki baabinda zaikaramin sai ciwo dan Allah kiyi shiru,wash yafada yanadafe kansa,

Karar wayarsa ne yakatseshi safiyya ce
tadauka faruq ne tadauka tafara magana kuka yakwacemata,

"Faruq assadiq bashi da lpy"

Betambayi meyasameshiba yakaraso gidan abakin kofa yatsaya Safiyya tasa hijjabi tace yashigo shiga yayi yakarasa gabansa yai
Masa sannu yayi yayi dashi sutafi asibiti yaki
Yace karyafadawa su momy yana kwance sukai sallama yatafi😰
Safiyya tarakashi bakin gate tadawo wayarta ta dauka tashiga neman layin yayanta Dr almustapha bugu biyu
yadauka,tana kuka tafara magana,

"Yaya assadiq bashi da lpy kataimaka kazo kadubashi kar yamutu"

"Meyasameshi,kedaga
Ciwo sai mutuwa ko,ganinan"

Dakin takoma tajiko tawul tazo taciremasa
Jallabiyar jikinsa tashiga dannamasa jikinsa tana hawaye ahantkali yabude idonsa yazubamata ido kai yagirgizamata alamar tadena yakakama hannunta ya sumbata,


Dady ne yatambayi faruq ina assadiq, yakefadamasa bashi da lpy,tafiya sukayi basu dawoba sai da jirginsu yatashi✈


Assadiq ne kwance a cinyar Safiyya tanata shafa sumar kansa yaruntsi idonsa wayarta tai ringing tandagawa taga yayantane zamekan assadiq tayi tadora akan filo,taje tashigo dashi sanye yake cikin kananun kaya masu tsananin kyau idonsa sanye da farin glass,duk inda akeneman dan gayun namiji akasami almustapha angama kallonta yayi yace,

"Ina assadiq din safiyya,ke badama mutum yayi ciwo saikice mutuwa zaiyi ko"

Dariya tayi tace yaxauna tashiga tatarar dashi azaune yadafe kai takarasa tarike hannunnasa tace

"Dee sannu kataso ga yaya almustapha yazo dubaka"

"Sopy bazan iya tashiba kaina kamar yatsage,kice yashigo"

Tashi tayi taje tace yashigo shiga yayi yaimasa sannu yafara dubashi atake yagano malaria ce dakuma damuwa yarubuta masa magani yaimasa allurar bacci yana shirin tafiyane sai gasu jalila sundawo sukabiyo duba assadiq

Tunda jalila taganshi tadada gigicewa ido tazubamasa harsai da yajiyo yakallesu yace


"Yanmata sannunku ,ya maijiki"

Suka amsa da yauwa jalila ce ta dora da

"Mai jiki aikai zamutambaya Dr"

"Hakane"

"Eh mana"


Yaimusu sallama yatafi nanfa dadi Yakama jalila,su afifa kuwa haushi tabasu,suka shiga suka duba yayannasu yanata bacci sukafito sulaimata sallama sukatafi tayi tayi su zauna sukaki gurin mijinta takoma tazuba masa ido yanata bacci tashige jikinsa ta kwanta tare da sakarmasa kiss a lebansa.

Su farhana kuwa sauna zuwa gida momy tace ya suka dawo da wuri,afifa tace

"Munce zamu zauna shine tace mutafi kar mu dami mijinta"

Itawa din"?

"Momy matarsa mana".










*NASEEBA GAWO*✍🏻
[4:31PM,2017]


*®💦💦💦TALENTED WRITTER'S FORUM*💦💦💦

*💦TF*💦



_*KANNAN MIJINA*_
👩‍👩‍👧



*NA*

*NASEEBA I UBA*💐



_Dedicated 2 my lovely family_*Alhj uba gawo* 😍 _U are in my mind brothers & sisters_💔






*39*



~~~ Kai nake saurare
Sadauki"gabansa ne yashiga faduwa yayinda kalaman momynsa yashiga yawo a kwakwalwarsa,
Ahankali yabude baki
Yace,

"Eh dady ni nakesonta"

"To amma sadauki yaushe kayi auran,to shikenan dai ba laifi
zamuje neman auranta

"To dady nagode Allah yaja kwana"

"Ameen sadauki,Allah Yakima albarka,ka gaidamin da yartawa,
Ka rarrasheta kaji ko"

"To dady nagode"

Yaimasa sallama yasakko yana sauka yahadu da momy kallonsa tayi tace,

"Ya kukayi da dadyn naku"

Nan yabata labarin yadda sukayi murmushi tayi tasa masa albarka yaimata
Sallama yatafi,su farhana najin yadda sukayi suka hau ihun murna,waya sukaiwa muwadda sukaimata albishir,murna tayi tare da kulla aniyarsu ita da mahaifiyarta.


Assadiq yana fita gidan yayarsa ya nufa waya yaiwa safiyya kartaji shiru yaje gidan yaya hannatu,taamsa da agaidata,

Yanazuwa yatarar daita a parlor yaranta tanata wasa sunaganinsa suka taso aguje
"Uncle A oyoyo"

Rungumesu yayi yakarasa gurin yayartasa yagaidata,

"Assadiq lpyr ka meke damunka"?

Shiru yayi idonsa yakada yai jaa mai aikinta takira tazo taja yaran zuwa dakinsu,

Tamaida kallonta gareshi tace,

"Assadiq gayamin damuwarka"

"Yaya,momyce"

Sai kuma yaishiru,dakyar dai yaiyabata labarin abinda yafaru,tai shiru can tanisa tace

"Baabinda zance maka assadiq sai dai inbaka hakuri kayiwa momy biyayya assadiq nayi iya yina infahimtar da momy amma taki fahimtata"

"Yaya yazanyi da safiyya,mexance mata"?

"Karka damu zatafahimceka kaji amma karka fadamata yanxu"

Yaamsa da to,yaimata
Sallama yatafi,

Safiyyace zaune tanata jiran assadiq bedawo ba,sai ga afifa
tashigo, da ledar rake
Ahanunta,tagaida Safiyya tasami guri tazauna tadau remote tacanja tashar data tarar tana kalla,batacemata kalaba tadakko rakenta,tafara sha takalli safiyya tace,

"Aunt Safiyya ga rake "

"Aa nagode afifa,amma Dan Allah karki bata gurin"

"Kinjiki sai kace karamar yarinya"

Taja bakinta tai shiru tacigaba da kallonta
Wayartace tahau ringing tashiga daki tadauka,yayarta ce amina,takefadamata yaya Rukayya ta haihu taita murna,takira yayartasu taimata murna tafadamata zata zo da safe,sukai sallama tafito mezata gani afifa tabatamata parlor da bawan rake,tai tafiyarta gurin tazubawa I do tadakko tsintsiya kenan assadiq yashigo,gurin yakalla yace,

"Sopy ya haka,waye yashamana rake a parlor"

"Dee afiface"

Tsintsiyar yakarba a hannunta yashare gurin yagama yashiga toilet yai wanka gaba daya sopynsa tausayi takebashi,suka fito parlor sukaci abinci tafadamasa haihuwar yayarta,yaimurna,yashafi cikinta,yace

"Saura ke,Sopy"

"Dee,tsoro nakeji"

"Sopy yau zanbaki baby kishirya"

"Deee wlh banso"

Washegari suka shirya zasu je gidan yaya rukayya biyawa sukayi gidansu assadiq zasu gaida momy suka shiga bakowa a parlor
Yace Safiyya tazauna yakira momy zama tayi bedade da shigaba farhana tafito daga kitchen da cup din zobo a hannunta tana zuwa dai dai gaban Safiyya cup din yasubuce yazube a jikinta yabata mata kayanta,hakan yayi dai dai da fitowar assadiq.



Ayi hakuri da dan wannan👌🏻







*NASEEBA GAWO*✍🏻
[8:6Am,2017]

*®💦💦💦TALENTED WRITTER'S FORUM*💦💦💦

*💦TF*💦



_**KANNAN MIJINA_**
👩‍👩‍👧


*NA*

*NASEEBA I UBA*💐





*40*



~~~ Yana karasawa yadauke farhana da mari,zaikaramata momy tadaka masa tsawa,

"Assadiq kana haukane zakasa min yarinya agaba kana marinta,akan wane dalili"?


"Momy kidubafa kiga abinda taiwa sopy"

"To zataimata da gangan ne,karka kuma dokar min yaya zakazama faruq ko"

Safiyya tana zaune tarasa ma mezatace
tagaida momy taamsa
Adakile,assadiq ne yadubeta yace tataso sutafi,farhana kuwa tana jikin momy tana guraheken kuka,afifa ce tafito daga daki tadubi momy tace,

"Momy meyasami ya farhana"

"Wai saboda tazuba wa matarsa lemo ajiki
shine yamareta"

"Cab,yi shirunki yaya farhana Allah sai na rama miki"

Momy tanajinsu batai kokarin hanasuba,su assadiq suna fita kai tsaye gida suka koma
yacirewa Safiyya kayan da farhana tabatamata,yahadamata ruwan dumi tashiga tayo wanka tana cikin wankan kuka ya kwace mata,shash shekar kukanta assadiq yaji ya tura kofar toilet din,azaune yasameta acikin barb tahada kai da gwiwa karasawa yayi gabanta yadago da kanta idonsa yazuba mata masu narkar mata da zuciya
Ahankali yakira sunanta,

"Sweet sopy,kuka fa?,pls kiyi hakuri kiyi shiru,nasan baa kyauta mikiba,amma kibarni da ita sai ranta yabaci,kitaimakamin inyiwa momy biyayya"


"Dee,kannanka basa sona,menayi musu?"

Dee nagaji bazan iyaba pls kamai dani gurin ummina"

"Sopy yazaki fadi haka
Kina tunanin zaniya rabuwa da kene"?,karki kuma fada"

Zata kuma magana kenan ya toshe bakinta danasa,assadiq kenan yasan salon mantar da matarsa damuwa,dakansa yaimata wankan suka fito yabude wardrobe dinta yadakko mata atamfa super orange da adon fulawowi yellow,dinkin have gawon,da zani,tashirya tsaf,tayi kyau hartafi shigarta ta farko,shima
Yadakko yadi light orange yasa mai tsada kana iya hango farar vest dinsa,kallonta yayi ya sumbaci goshinta yace,

"Sweet sopy kinyi kyau"

"Kaima kayi kyau Dee"

Sukagama shirunsu suka fito,aharabar gidan suka tsaya sukasha pics🤳🏻

Sukagama suka shiga mota suka tafi,tunda suka hau titi yake dada rarrashinta a daidai wani babban kanti suka tsaya anrubuta
Baby dream,dagowa tayi takalleshi,tace


"Dee yahaka mekuma zamuyi anan?


"Eh,zanfara tarin kayan baby ne"

Dariya tayi sukafito suka shiga ciki,kayan baby assadiq yashiga diba,fal sopy tana kallonsa,yagama yabiya kudin suka fito sukatafi,ido taxuba masa yayi murmushi tare da lakucemata hanci yace,


"Yade,ku mukoma gidane"?

"Dee muyi me a gida kuma"

"Aa nasani ko dankinji nace zanfara tarin kayan baby,kice mukoma kozamu samu yau"


"Lala,Dee,sharri ko,to aini banaso finkarfina kawai kakeyi"

"Kedai kigode Allah kinsami jarumin miji"

Dariya sukayi ahaka suka karasa gidan rukayya,tashiga da murnarta nan fa Suhyla ta rungumeta tana murnar ganinta

"Matsa suly ni baby zan dauka"

Kuka tasa wai aunty Safiyya bata Santa,tajata jikinta tana rarrashinta,rukayya ce tadubeta tace


"Safy ina assadiq din"?

"La,yana waje yaya"

"Dan hauka kikabarshi a waje,kije kishigo da shi"


Tashi tayi taje tasameshi a mota yana waya da faruq tajira yagama tace

"Dee afuwan nabarka ko"?

"Bakomai sopy,ai ina nan ina kallon yanmata"

Duka takaimasa ya goce,yarike hannun aikuwa tacijeshi,yasaki
Yar kara,gaba daya janbakinta yagogu a hannunsa,

"Dee kaga ko,kasa nagoge janbakina,Allah sai kabiyani"


"To badanni akasaba,to na goge abina"

Suka gama shiriritarsu
Suka jero gwanin shaawa,yagaida da yaya rukayya tare dayimata barka,Suhyla takarasa gabansa tace

"Uncle A kaga babynmmu

"Nagani Suhyla,ai dashi zamu tafi"

"Aa uncle A kuma kusiyo naku"

Akai dariya yamike zai tafi yabawa maijego 10k
Yabawa Safiyya kayan baby tabata,yaimusu sallama yatafi,
Safiyya tabawa yayarta rashin kirkin da *kannan mijinta*sukemata tadada bata hakuri tare da kwantar mata da hankali,


Abangaran muwadda kuwa shiri take tayi dan zuwa gurin assadiq taci wasu kananun kaya tayafa yalolan mayafi tafito tadau motarta tafita wayarta tadauka tashiga Neman Layin assadiq sai data kusa tsinkewa sannan yadauka,shiru yayi tafara magana,

"Sweery kana gida"

"Kamar ya ina gida wace irin tambaya kenan"

"Inason ganinka ne"

"Ina office"

"OK

Bekawo zata iya zuwa office dinsuba kawai sai jin bugu yayi yayi tunanin Achida ne,kansa a dunkufe,yace a shigo,har yafara magana,abokina yaakayine,shiru yaji anyi yadago da kansa,
da mamaki yaga muwadda tsaye tazuba masa ido dakaraji yafara magana

"Muwadda baki da hankaline meyakawoki office dina"

"Sweery kayi hakuri san ganinka nake,ko kasan jiya. baniya yin bacciba"

"Bansaniba kuma banason insani,so that get out 4rm office"

"Sweery
Kanta takarasa yabuga tebirinsa da karfi yanunamata hanyar fita,yanayin fuskarsa ta kalla taji tsoro tafita,kaitsaye gidansu assadiq tawuce,tanazuwa tafadawa momy abinda assadiq yaimata,nan momy tashiga aikin fada yayanta tanata zugata

Yau ake sunan yayar safyya rukayya tuncikin dare safiyya takefama daciwon kai taki fadawa assadiq ahaka tashirya yakaita daman taaikawa su farhana suzo suje,sukace bazasuba .assadiq yakula da yanayinta,

"Sweet sopy are u ok"

"Yap,Dee"

"OK ki kularmin da kanki"

Taamsa tashige yaja motarsa yatafi anfara shagalin suna ciwon ciki ya matsawa sopy,dakin Rukayya tashige ta kwanta nan da nan bacci yadauketa

Jalila ce tamatsawa kannanta sai sunje sunan yayar Safiyya da kyar suka yarda sukaje sanda sukaje Safiyya tanata bacci zaatasheta jalila tace akyaleta yayar Safiyya amina takawo musu kayan suna taimusu karbar mutunci nan jalia take tambayarta Dr almustapha,tace yana nan.sukaci suka koshi dazasu tafi aka basu kayan daaka raba sukatafi

Suna zuwa gida suka tarar da assadiq a gidan afifa ce take tambayar sa yabasuga aunt safiyyaba kallonta yai da mamaki yashiga kiran
Layin Safiyya tanata ringing bata dagaba.









*NASEEBA GAWO*✍🏻
*[9:49AM,2017]*




*®💦💦💦TALENTED WRITTE'S FORUM💦💦💦*



*💦TF💦*







**_KANNAN MIJINA**_
👩‍👩‍👧






*NA*


*NASEEBA I UBA*💐




*41*






~~~Yanke shawara yayi kawae ya miqe cikin fushi ya nufi gidan ruqayya yana isa kofar gidan ya qara gwada wayarta yanzu ma dai kamar dazu tana ta ringing amma bata daga ba wasu yara yaga sun fito daga gidan sunan ya kira

Please Login or Register in order to submit comment