Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hannatu rufemin baki,mekikeso kice min,kinason kice kina goyan bayan assadiq yaauro wata ba muwaddaba?"

Nandai momy taitafada karshe dai hannatu hakuri tabata tashaida mata zasuyi maganar da assadiq inyadawo,


Da yamma Kowa yadawo suna falo dukkansu sunata hirarsu gwanin shaawa su ashiraf sai tsalle suke akan faruq,duk da halin fadansa, yana son yara,

Dadyne yashigo da gudu yaran suka je suka rungumeshi,cikin doki yake tambayar su

"Abokan dady,saukar yaushe"

"Dazu abbanmmu yakawo mu,dady banje school bafa yau,bani da lpy"cewar nabil,

.faruq ne yai caraf,yace

"Baka da lpy kake tsalle a Kaina"

Dariya sukayi dukansu,zama yayi dadyn suka gaisa da yayan nasa,mussamman hannatu dayaji dadin ganinta,anan yakebasu labarin yadda sukayi da mahaifin safiyya,

Nan momy tai tsalle ta dire,bata yardaba

"Hmm hajiya kareema kenan kamar kinmantani koh,to ai ba laifi kiyi,babbar rigarsa yakade yaja hannun jikokin sa yai sama,nanfa faruq da hannatu sukaitabawa momy baki

"To ku yanzu mezancewa aisha,kunaso ince mata kafasa auran muwadda?to ni baruwana da auranka inko bazakajanye ba,to,sai dai kahadsu biyun kaura,dukkansu sun razana dazancan momyn tasu banda farhana da afifa,


"Shikenan momy naamince,amma zanfara auran safiyya tunda ita muwadda bata karasa makarantar ta ba"

"Duk yadda kayi dai dai ne,zanje da Karina infadawa Aisha yadda mukayi"


Hannatu ce tai musu sallama tatafi da kyar nabil ya yarda yabita shi dai kwana zaiyi gurin aunt jalila,


Faruq ne yakoma daki yasha hirar sa da rabin ransa,karshe yace tarufe idonta yai musu adduar bacci kasancewar dare yayi.









*NASEEBA GAWO*✍🏻

💦 *TF*💦
[1:48 pm,2017.]



*®💦💦💦TALENTED WRITER'S FORUM*💦💦💦

*💦TF*💦


**_KANNAN MIJINA**_

👩‍👩‍👧


*NA*

*NASEEBA I UBA*💐



_ Ina mika godiya ta mussamman ga masoyan kannan mijina novel
*Nagode*


*9*


~~~ Baffa ne,zaune shi da matarsa,suna taba hira,saiga dansu Dr almustapha ya shigo,

Gaida iyayannasa yayi,
Sai yadora da,

"Baffa ance jiya anzo neman auran safiyya,gashi ko yaron bamu saniba"

"Hakane,mustapha,ai abunda mahaifin yaron yayi,ni naji dadi dakansa yazo yanemawa dansa izinin zuwa zance gurin safiyya"

"Hakane"
Cewar ummi ai shine dai dai dama,dazu ma tace zaizo da yamma yagaida mu"

"To ba laifi yayi kyau,zanyi kokari indawo da wuri,inshaallah ,yakamata kaima almustapha kasamo mata,kai aure,zaman haka bashi da amfani"

"Baffa zanyi inshaallahu,nafiso inkammala gini nane,tukunna"

"Eh hakanmma yana da kyau,Allah yabada nasara"

Ameen baffa,bari inzo inkaika,kasuwar"

"Aikinka fa,ko babu?"

"Da akwai,baffa amma sai dare,yau inada call ne"

"To balaifi,Kenyan inkatafi acan zaka kwana?"

"Eh,baffa"

Fita sukayi ummi tai musu fatan dawowa lpy.

Basu dade da fitaba,rukayya tashigo,

"Assalamu alaikum"

Waalaiki salam,aa rukayya sannu da zuwa"

"Yauwa ummi,ina kwana"

"Lpy lau,yajikin naki?"

" da sauki,yanzuma daga asibiti nake,nacewa yusif yasaukeni a nan"

"Allah sarki"

"Ummi,nagaji ga yunwa"

"To mezakici?"

"Yimin danwake"

"To"

Tashi tayi tadoramata danwaken sunataba hirarsu,anan take bata labarin saurayin Rukayya,tai farin ciki sosai,

"Ummi suna ina ne gidan shiru"

"Zainab tatafi,B U K.
Najiba tana makaranta,kasancewarta yar secondary, safiyya kuma naiketa gidan aunty bara ita da suhyla"

"Ummi yazancan makarantar Safiyya?"

"Jamb zata canja tunda bata samu taciba"

Daki rukayya,takoma tadan kwanta,su Safiyya ne sukadawo,suhyla tana ganin takalmin ummanta,tashige dakin,


"Ummata! Ummata!"

Afirgice rukayya ta tashi dan har tafara bacci abinka da mai ciki,nan tafara mata Dada,

"Suhyla kina haukane?",meye haka,zaki fado kainane?"

"Aa,umma kiyi hakuri,na dena"

"Karma ki dena,kicigaba da shashanci"

"umma ina abbana?"

"ya wuce kasuwa,yana gaidaki"

Safiyyace tashigo da sallama,dauke da plate din danwake,nan suka gaisa da yayar tata taimata yajiki,taajiye mata danwaken agabanta,
tsokanar ta farayi.



"Safi amarya 2 be"

"Kai yaya rukayya"

Danwaken tabude zata fara ci,taga har da dafaffan kwai,

"Kai ummi data sani bata dafamin kwaiba,banaci,karni yakemin"

"Mu zamuci ko suly"?

"Aa,wlh aunty safiyya bazanciba,tunda ummata bata ci"


Dariya tabasu dukkansu,ana haka su zainab sukadawo,nan suka hadu sunata hira gwanin shaawa.

°°°°°°°°°°°°°°
Abangaren assadiq tun a office yake Allah Allah yamma tayi yaje gidansu safiyya,wayar sa yadakko,yaddana lambar abokinsa,


"Hello"acida man"

"Chairman,barka da rana"

"Yauwa,acida,zanshigo anjima zaka rakani gidan su mutuniyar"

"Muwadda?"

"Bansaniba mara mutunci"

Dariya yayi kana yadora da,

"Wlh bana gari naje mina,amma why not kakira dan shuwa"

"Wai Ebet"

"Eh"

"Ok,sallama sukayi,

Yafara neman layin abokinnasu wato,Abdullahi dan shuwa.Ebet

"Hello,Ebet,kana gida ne anjima,zanzo ,karakani uguwa"

"Eh chairman ina gida,

"Kashirya anjima zanzo karakani,gidan surukaina,ammafa kasanya manyan kaya"

"Dariya yabashi,"dagirman kujerarka,chairman "
Sukai sallama.

Assadiq yana barin office, gida yawuce yashirya cikin dakakkiyar shadda multi colour yasanya hula kalar kayan,sai kamshi yake ,yafice daga gidan,be yarda sunhadu da momy ba.

Yana isa gidan abokin nasa yaimasa waya yafito,sutafi kiyayi yace lallai sai ya shigo sungaisa da matarsa,dole yafito daga mota,yarufe yashiga ciki,sallama yayi,tana zaune ta katon cikinta,agaba,fara tas daita daka ganta kaga shuwa,

"Amarya ya gida?"

"Lpy,ya kake?"

"Lpy lau aran angonki zakibani"

Dariya tayi,tace"gashi nan"

Godiya yayimata yazaro kudi yabata taimasa godiya

"Shukuran"
Mijinnata ne yamatsa kusa daita yakira sunata

"Khadimalla bari inraka shi indawo kinji bejira amsartabawa ya sumbaci cikin jikinta yafita.
















*NASEEBA I GAWO*✍🏻
[6:01Am,2017.]



*®💦💦💦TALENTED WRITTER'S FORUM*💦💦💦

💦 *TF*💦


**_KANNAN MIJINA**_

👩‍👩‍👧



*NA*


*NASEEBA. I UBA*💐



*10*





~~~Su assadiq suna fita,yatsaya a wani babban mall,yayiwa safiyya siyayya,ciki kuwa har da wayar hannu mai tsadar gaske,suna isa kofar gidansu,yakirata awaya yashaida mata karasowar su,lokacin duk suna zaune har da yayansu,Dr almustapha,fadamusu tayi,atake yayannasu yafita yaahigo dasu,


"Salamualaikum"

Nan yabasu hannu suka gaisa,ni suna na
Almustapha kabeer,"

"Nikuma assadiq Muhammad mai nasara,wannan aboki nane,abbdullahi(Ebet)"

"Mashaallahu bisimillah ku shigo"

Nan suka sa kai suka shiga aka saukesu afalon baffa,suka gaisa,da kowa,agirmame,baffa ma yashigo,suka gaisheshi,kasancewar yadan fita,bayan yadawo daga kasuwa,nan kowa,yafita,yabarsu,
Sai suhyla tanata musu surutu,

Safiyyace tashigo cikin wani material mai fulawowi,green da orange,tunda ta shigo ya zuba mata,ido yana dada yabawa da zabin da yayi ,

"Inayinin ku"

lafiya lau amarya ta"

Kunya yabata,tagaida ebet yaamsa cikin sakin fuska,nan assadiq yagabatar mata da abokinnasa,ya kuma shaida mata,acida yana gaidata"

Nan dai abokin yaimata sallama yabasu guri su za ta,

"Safiyya naga Dr almustapha a ina yake aiki?"

"Aminu kano"

"Wacece mai kama da ke,nazacifa kece"

Aa autarmu ce najiba"

Kaga daga yaya almustapha,sai yaya rukayya,sai yaya zainab,sai ni,sai najiba"

"Ok yaya rukayya itace maman suhyla?"


"Eh"

Assadiq yana so yaga safiyya tana magana tana motsa dankaramin bakinta,

Nan dai suka taba hira karshe yai mata sallama yafito,yaiwa su ummi ma yafita, sabiu yagani zai shiga gidan yabashi kayan dayakawo mata ya kai ciki,yaja motarsa sukatafi,ahanya ebet yake yaba zabin abokinnasa.


°°°°°°°°°°°°°°°

Farhana ce kwance kancinyar momy suna kallon dubai 1,can ta dago takalli momyn tasu

"Momy yakamata ki kira aunt aisha kifadamata halin daake ciki"


"Yi shirunki farhana gobe insha allahu zanje da kaina muyi maganar"

"Yauwa momy,zanbiki ma,wlh tunkafin inga yarinyar da ya assadiq zai aura naji na tsaneta"

"Nima raina be kwanta da itaba farhana"



Faruq ne yashigo yana ganin farhana a cinyar momy yafara mata halinnasa na fada,


"Ke meye haka, dalla dagata

Baki ta turo gaba,tatashi,

"Faruq ina ruwanka daita ne"?
Meyasa baka san zaman lpy ne dan Allah,

Tasowa yayi yakwantar da farhana kancinyar momy,

Kwanta farhana Allah ya huci zuciyar momy na,nidai gyara nake"


Assadiq ne yashigo falon da sallama,

"Momyna sannu da gida"

"Yauwa assadiq,daga ina haka?"

Naje gidan ebet ne"

"Allah sarki ya matar tasa,tahaihu koh?"

"Aa ta kusa dai"

Faruq ne ya kalli yayan nasa yace ,

"Wow bross gaskiya kayi kyau,ko de ..... .,

Dariya yayi yace,

I will talk 2 u later"

"Ok"


Washe gari da yamma momy suka je gidan yar urwata aisha,nan take shaida mata abinda yafaru shiru tayi kana ta nisa tace ,

"Yaya ai shikenan bakomai ,amma assadiq yabatawa muwadda lokaci,gaskiya

"Haba aisha ai aure ba fashi sai anyi"

"Aa yaya muwadda bazata iya zama da kishiyaba"

Da kyar dai taamince zata aurawa assadiq muwadda,shi gogan mma besan wainar daake toyawaba.momy ta umarci muwadda data dinga kiransa suna gaisawa.









*NASEEBA GAWO*✍🏻
*®💦💦💦TALENTED WRITTER'S FORUM*💦💦💦

*💦TF*💦



**_KANNAN MIJINA_**
👩‍👩‍👧



*NA*

*NASEEBA I UBA*💐




*11*

Shakuwa,mai karfi ce ta kullu tsakanin asaadiq da safiyya,yakaita gidan yayarsa hannatu sungaisa,tayaba da zabin kanin nata,a lokacin su jalila suna gidanta,safiyya ta tsorata da irin kallon da kannan assadiq sukai mata,bata kawo komaiba,

°°°°°°°°°
Ayau alhaji muhammad mai nasara,yaje nemawa dansa auran safiyya,shida yayansa,alhaji munir mai nasara,sunkai kudin aure,dubu100k tare da sanya rana,anyi komai cikin mutunci,


Assadiq ne kwance a luntsunme men gadonsa,yakira layin safiyya,


"Hello"

"Matar assadiq"

"Au har nazama matarka?"

"Kwarai kuwa,me yarage,shafa fatiha"

"Haka dai kace,ya momy,da su afifa?"

"Suna lpy,suna gaidaki"

"Safiyya"

"Naam A B"

Wace irin kulawa zakibani inmunyi aure"

"Hmm AB kenan sai munyi auran tukunna ko?"

"Banyarda ba gaskiya sai kinfada min"

"Naki,wayon"

"To ni bari infada miki irin kulawar da zanbaki kinga ni zandiga baki abinci abaki,inmiki tausa,ke har wanka dakaina zanmiki"

Dariya yabata dif takashe wayar tana dariya,



Almustapha ne suke tattaunawa da baffansa kan auran safiyya,

"Wato,mustapha naso ace,yaron nan khalifa yadawo daga tafiyar nan da yayi,da sai ahada auran safiyya dana zainab"

"Eh wallahi baffa,amma tunda bekamalla karatunsa ba dole ajira shi ai,inyadawo ayi"

"Haka zaai,mustapha,sonake afara siyayyar kayan daki ko?"

"Eh baffaa hakane,ai inshaallahu baabinda zai gagara,zanyi iya yina danganin baaji kunyaba"

"Allah ya nufa mustapha,yanuna mana lokacin"

"Ameen baffa"


°°°°°°°°°°°°°°
Alhaji Muhammad mai nasara ne,zaune tare da iyalinsa,suna tattaunawa kan bikin assadiq,

"Wato, hajiya kareema sonake ayi bikin da bazaaji kunyaba,saboda haka ina ganin zanbaki kudi kuje dubai kuhado lefe,sannan gidan nan nakusa damu angama sai kazauna aciki"

"Dady pls dani zaaje"

"Kinji afifa,dawata magana,to dani zaa"

"Yaisa haka farhana"

"Ai alhaji ina ganin basai anje dubaiba, anan ma hada lefe zaai"

"Hmm hajiya Kareema kenan,nafahinci bakyason auran nan,to ba laifi,abinda zaai kai faruq kaje gidan yayarku hannatu kace tazo ina nemanta"

"To,dady"

"Inyaso ita
sai suje dasu jalila"

Sai yanxu assadiq yasa baki,

Dady na nagode madalla allah yaja kwana,yakara girma,

"Ameen sadauki"

Assadiq beji dadin abinda momynsa tayi masaba,amma bayyada zaiyi yaji ya gani,



A haka lokaci yaja,su hannatu suntafi dubai siyayyar kayan lefe,datasu siyayar,momy cetaiwa hannatu waya lallai asiyowa muwadda kayan fitar biki,bayadda taiya haka tashiga yiwa muwadda siyayya .



Muwadda ce zaune a garden din gidansu tana ta kiran layin assadiq tana ta ringing bai dagaba,sai daga baya yadaga,

"Hello,ya assadiq,ina yini"

"Muwadda,kina lpy,ya mama?"

"Lpy lau,ya assadiq sometimes innakiraka,baka amsawa,meyasa?"

"Am,kingane ne,muwadda wani lokacin ina aikine,bancika amsa wayaba"

"To,shikenan,yanzu yaushe zakazo"

"Muwadda kenan da inzanzo ke kike sani"?

"Aa"

"To kizuba ido,duksanda nasami time,zanzo"

zatakara magana yakatse wayar,ransa a bace,safiyya ya kira suka sha soyayarsu,karshe yace tafadawa ummi nan da sati 2 zaakawo lefe,gabanta ne yafadi,data tuno kannan assadiq.


su yaya hannatu,sundawo,tayo kaya masu yawa da kyau,momy taga kaya nan tasa yartata a gaba da fada,

"Hannatu wannan uban kayanfa,kina da hankali Kuwa?"

"Haba momy yanzu ba girman mubane,ace assadiq yakai wadannan kayan"

"Rufe min baki,hannatu,ai nafahimci inda kika sa gaba"

Afiface tasa baki,

"Wlh momy tun acan,naceewa yaya,kayan sunyi yawa"

Azafafe yayar tasu tadauke,kanwar tata da mari,

"Afifa har kinyi girman da muna magana,kisa baki,to kici gaba"

Tundaga wannan lokacin afifa tadada tsanar safiyya.









*NASEEBA GAWO*✍🏻
[11;29 pm,2017.]



*💦💦💦TALENTED WRITER'S FORUM*💦💦💦


*💦TF*💦



_**KANNAN MIJINA_**
👩‍👩‍👧



*NA*


*NASEEBA I UBA*💐


_godiya tamussamman gareku mosayana nagode Allah yabar kauna_
_ina maraba da duk wanda yaga gyara acikin labarina ko a rubutuna,kofa abude take dan karbar gyara daga gareku masoyana_

*NAGODE*👌🏻






*12*


Safiya nagama waya da assadiq,takira zainab tafadamata dan tafadawa umminsu,tanagama fadamata tafita tasami ummin tasu a kitchen,

"Ummi sannu da aiki"

"Yauwa zainab,bani kulolin can

"To ummi,yauwa wai nan da sati biyu su assadiq zasu kawo lefe"

"Oh!ni nafisa abun yazo,to Allah yakaimu"

"Ameen ummi,yazu meyakamata ashirya?"

"To sai dai ayiwa Rukayya waya,aji meyakamata ayi ko?"

"Hakane ummi"

"Yauwa Allah ya kaimu yasa ayi damu"

"Ameen ummi"



Assadiq ne sukaje gidan yayarsu shida faruq dan tattaunawa akan bikin,nan take basu labarin yadda sukai da momy da afifa,faruq be yai kwafa,kana yace,

"Wlh yaya shiyasa banason shiga sabgar yarannan basu da kunya"

"Kabarsu faruq zasuci ubansu,wlh"

"Yaya pls Mubar zancan nan,nida shawarar danayake itace,mezaihana su dandy sukai lefan nan,ko kuwa?"


"Yayi daidai,bross gwanda mukai wlh

"Au faruq har da kai?"

"A yaya hardani zaa"

"To shikenan assadiq yayi,but u should talk 2 dady "

"OK yaya I will"

Su nabil me suka shigo falon da gudu,

"Uncle faruq oyoyo"

"Uncle A,ina dady?"

"Lpys kalau my boy"

Nan dai sukaitai masa sharrrinmansu,yaraba musu alawa,karshe sukaiwa yayartasu sallama sukatafi,



Hajiya kareemace zaune ita da maigidan nata,tana yanka masa fruit, assadiq yai sallama yashigo,nan yagaidar da iyayensa,

"Dady barka da dare"

"Yauwa sadauki"

"Momy na sannu da gida"

Sannu,assadiq"


"Dady dama wata shawara ce nazo daita"

"Inajinka sadauki"

"Dady me zaihana kasa su baba salhi da abba munir sukai kayan lefan na"

"Tunaninmmu yazama daya sadauki,haka zaai zan musu magana inshaallahu"

Momy tanjinsu bata tofaba,

"Hajiya kareema bakice komaiba"

"To mezance alhaji,ai tunda assadiq yagama shawara da yaruwarsa hannatu aishikenan kuma"

Dariya yayi yadubi dannasa,

"Sadauki tashi katafi Allah yabada alhr"

Tashi yayi yafita yaimusu sai da safe,

Nanfa dady yarufe momy da fada,daga karshe yaimata nasiha,dole ta hakura ta karbi safiyya a matsayin surukar fari,

Su farhana kuwa sun ci burin wulakanta safiyya,da muzguna mata,





A yau aka kai kayan lefan safiyya kamar yadda assadiq yaso mazane suka kai akwaati saiti 2 cike da
Kaya na afarama ,ansa biki wata guda,sunsallamesu da kayan arziki,da tukwaicin 100k Dr almustapha yabayar,

Hakika lefan Safiyya yaja hankula anata turuwar zuwa kallo,mussamman kawayanta.......








*NASEEBA GAWO*✍🏻
*[2:09pm,2017]*




*®💦💦💦TALENTED WRITTER'S FORUM*💦💦💦


*💦TF*💦


**_KANNAN MIJINA_**
👩‍👩‍👧



*NA*


*NASEEBA I UBA*💐



*13*




~~~Tunda aka Kai lefen Assadeeq ya kasa zaune ya kasa tsaye farin ciki ya mamaye zuciyarsa yanzu haka ma tunanin gimbiyar tashi yake a karshe ya yanke shawarar kiranta bugu biyu ta dauka cikin salon muryarta mai kashe masa jiki tace
"Assalamu Alaika"

Cikin wata kasalalliyar ya kishingida a jikin kujerar office en nashi ya amsa mata da
"waalaikissalam Amaryar Sadeeq ya kike? Yasu umma da kowa

"Tace lafiyar su kalou ya aiki"

"Yace Alhamdulillah ya ake ciki hope kinga kayan nan kuma ena fatan komi yayi miki idan akwai abinda bai miki bah ki sanar dani kinji babyn Sadeeq.

Tayi murmushi hade da rufe fuskarta da tafikan hannunta kamar yana ganinta cike da kunya tace komi yayi min Allah ya saka da alkhairi Allah ya maida abinda aka 6atar.

"Yace Ameen baby nah Allah ya nuna mana lokacin da zaa kawo min ke dakina😀"

"Tace Hmmnn 🙈

"Yace kinga malama nifa bana son hmmnn en nan kice Ameen kawai kina so kina kaiwa kasuwa kinga dan saurayi kin rikice ya karashen zancen yana fashewa da dariya don yasan halin kayarsa baza ta tanka masa ba

"Tayi murmushi tace to malam na dena cewa hmmnn en tunda baka so"

"Yace yawwa my dear 😘 yace me zan samu neh yana mai Shafa cikinsa

"Tace name fah?"

"Yace naci mana yunwa nakeji na gaji jiya duk ban huta ba wallahi

"Tace to ae dole ka gaji ka tashi daga office en nan haka kaje gida kaci abincin Momy kaji uncle A nima na dana tasu Nabil.

"Yace toh Aunty S yace toh byee luv you"

"Tace ok 👌byeeee "

Yace ki amsa min mana

Ta rufe fuskarta tace luv you too❤

"Assadeeq ya miqe ya tattare files en gaban shi ya kullo office en ya fito yana qwalawa sectary en shi kira yace mishi ni na tashi duk wanda yazo kace na tashi ya shiga office en Abdullahi yace Achida man👨 ya meye labari neh yace normal mutumina wai kana nufin har ka tashi.

"Yace wallahi yunwa nakeji kuma kasan inba girkin sweet mother naci bah bana ganewa ya fada yana ficewa"

"Achida ya daga murya yace kuma nan da few days zaka fara cin na gimbiya safiyya bah"

"Assadeeq yace Dan iska kawae ya wuce parking space ya bude motar shi Fara qirar Ferrari"

"kae tsaye gida ya wuce bai samu kowa a palour bah ya kwalawa Saa kira ta amsa yace hada min abinci yunwa nake ji"
Bayan ta kawo mishi abincin yace ena Momy tace Sun fita dasu jalila,faruq neh ya shigo palourn yace ah bros ka shigo kenan yace wallahi cikina neh ya kira ciroma nadawo kawai zama yayi kusa dashi ya dauki cokalin yafara cin abincin gaban shi suna dan ta6a hira can bros ya nisa yace bros me Kake ganin zamu shirya neh na bikin nan saboda ena so muyi gagarumin bikin da baa ta6a yi bah

"Assadeeq ya numfasa yace faruq ae duk wani shiri yana wurinku nidai dan tayi neh"

"Sallamar su Momy ce ta katse musu hirar suka amsa suna mata sannu da shigowa Emmatan neh suka qaraso hannunsu riqe da ledoji manya gaba dayan su suka xube a kan kujeru suna wash-wash Sadeeq ya dubesu yace ragwaye kawae kamar kun dakko dala Afifah ce tayi magana cike da shagwa6a tace wallahi yaya mun gaji yace toh sannunku emmatan momy suka amsa da yawwa faruq neh yaja wani dogon tsaki yace rufe mana baki malama kona makeki suka yi masa shiru saboda sanin halinsa.

"Momy ce ta kira Saa tazo tace ki kwashe kayan nan ki kaisu sama tace Momy sannun da shigowa ya hanya tace lafiya lau ta kwashi kayan tayi sama

"Assadeeq yace Momy nah kin gaji naji kinyi shiru"

"Tace wallahi kuwa toh ya zamuyi abu yana ta matsowa ai banga ta zama tunda Ina shirin aurar dakai"

"Murmushi yayi kawai ya sunkuyar da Kai"


"Momy ce ta numfasa tace amma fa duk da haka karka manta da sharadi nah"

"Gabansa neh ya yanke ya fadi cikin zuciyarsa yace dama momy bata bar wannan maganar bah wanna fah shine ga _ga qoshi ga kwanan yunwa_😬❗.








*NASEEBA GAWO*✍🏻


*💦TF*💦
[6:14Am,2017.]



*💦💦💦TALENTED WRITTER'S FORUM*💦💦💦

💦*TF*💦



_**KANNAN MIJINA_**

👩‍👩‍👧


*NA*

*NASEEBA I UBA*💐



_> Gaisuwa ta mussamman ga yaruwata,Aunt umma aymana_
_da irin shawarwarin dakikebani Allah yabar zumunci_

*Ameen*👏🏻





*14*




~~~~ Biki yarage saura sati daya,shirye shirye sunyi nisa,safiyya ce zaune kusa da umminsu,tanai mata nasiha da shawarwari yadda zata zauna da mijinta lpy da *kannan mijinta*kuka tasawa ummin tata,musamman data tuna da *kannan mijinnata*
ummi taimata nasiha mai ratsa zuciya,

"Safiyya kiyi hakuri rayuwar aure kinji shi aure da kike gani bakomai cikinsa face hakuri,haka dai taitaiwa,diyarta ta.

Abangaren angwaye kuwa,shirye shirye yai nisa,sun tsara zasu gudanar da kamu,da dinner,sai walimar daurin aure,ita dai safiyya bata da tacewa duk yadda assadiq yafadamata,binsa take da to,domin jikinta yagama yin sanyi,


Abangaran su safiyya kuwa,yayanta yayi rawar gani dan yayi mata,kayan daki na alfarma,baffa ma yaimata nasa,gaskiya iyayan safiyya sunyi mata kaya nafitar kunya,yau ne akafara rabon iv card,amma yaya rukayya tahana safiyya zuwa,saboda takaita gurin hajiya aunt gyaran jiki,


A gidan su assadiq ma shiri ake banawasaba,dady yadada gyara gidan,yacanjawa momy kayan daki,dai dai da maaikatan gidan sunsan zaai bikin dangata,domin dady sai da yaimusu kayan biki suma,


Assadiq ne yaje gidan yayarsa hannatu dancigaba da shirye shirye,wasu kaya ta dakko masu tsananin kyau. Da tsada,

"Ango ga wadannan kayan ka kaiwa Safiyya tasa ranar dinner,kaima kasaka kadar su"

"Angama yayata da girmar kujerar ki"

Dariya yabata," yaushe zasuzo,kafi?"

"Tace jibi ne"

"To badamuwa zanyi kokari inzo da wuri,dan ataresu"

"To yaya"

Sallama yayi mata yatafi gidansu safiyya,tunda ya hagota,yaji wani irin so da kaunarta acikin zuciyarsa,

Sallama tai masa,be iya amsawa ba,yaja hannuta,suka koma cikin mota,

"Baby kinganki kuwa,kinajin kamshin da yake tashi a jikinki kuwa"
Shiru tai masa saboda ta tsorata da yanayin assadiq yau,tafiskanci fitina yakeji,

"AB,pls kabari banaso"
Kwaikwayarta yayi da salon muryarta,

"Ni inaso,baby,kibarni inshaki kamshin tattausar jikinki"

Rugumota yayi jikinsa atake yasauke wata nannayar ajiyar zuciya,ita kuwa safiyya jikintane ya hau rawa,ahankali tazame jikinta,

"Baby guduna kike ko?",badamuwa,ai saura kiris,tafin hannunta tasa ta rufe fuakarta,

"Ka kayan dinner inji yaya"

"Nagode uncle A,ayimin godiya"

"Sannu,nizanmiki godiyar ma,bari inkirata dai kiyi mata da bakinki"

"Aa bazaniya ba"

"Aikuwa sai kinyi"

"Dan Allah kabari,wallahi kunya nakeji"

"Shikenan zanbari amma sai kinmin alkawarin abu daya"

"Nayarda"

"Tunkafin kiji abun har kinyarda,lalle matar assadiq bata da wayo"

Kanta ankara yamanne bakinsa anata yanata tsotsa kamar alawa,

Kuka tasamasa,dakyar yacikata,idonsa yakada yayi ja,murfin motar takama zata fita,yai saurin riko hannunta ya kafeta idanusa,yashafa lifiyayar sumar kansa


"Sweet baby kiyi hakuri bazan kumaba"kunnuwansa yakama,

Murmushi tayi,batace komaiba,

"Oya share hawayenki amarya bata kuka,ko kinaso ummi taga kinyi kuka?"
Kai ta girgiza masa,ta sharen fuskarta,taimasa sallama tashiga gida,yadade betafiba,yana maida numdashi, daga baya yaja motars yatafi.



Tundaga wannan rana,Safiyya taki yarda suhadu da assadiq,faruq ya turo yakaisu kunshi da salon,

"Auntina barka da fitowa,ya shirye shirye"?

"Yauwa sannu faruq,angode ma Allah ya momy?"

"Tana gaida surukarta"
Murmushi tayi yajasu sukatafi,tunda sukatafi yake tsokanar najiba,



Gidan su safiyya yafara cika da yanbiki,mussamman yanuwan baffa,da suke a katsina,


Su yaya rukayya ne sukatafi kafi ita da yanuwan umminsu,sunyaba da gidan safiyya sosai,katon gida mai dauke da part 2,suna cikinn jeran ne su afifa,suka shigo suna yatsine fuska,kanwar ummi ce kallesu,

"Kukumafa?

"yayan albarka"


Farhanace tabata amsa

*kannan mijinta*


Tirkashi,muje zuwa..
.
*[9:54 AM,2017.]*




*®💦💦💦TALENTED WRITTER'S FORUM💦💦💦*



*💦TF💦*



**_KANNAN MIJINA**_

👩‍👩‍👧

*NA*

*NASEEBA I UBA*💐




_Ina miqa godiya gami da jinjina👍🏻 gareki qanwata abar alfahari nah UMAIMAH_💋❤😍


*15*



~~~Gaba dayansu suka yi saroro, Ruqayya ce ta dubesu tace toh sannunku

"A ciki suka amsa da yawwa suka ja guri suka zauna suna kallon yadda suke gudanar da jeren nasu,Afifah ta dubi hajir cousin en su da suka xo dg kaduna er qanwa daddy ,tace tace don Allah Hajir dubi gida har gida amma ba wasu kayan azo a gani"

"Farhana ce tayi caraf tace nima dae abinda na gani kenan duk yadda ya Assadeeq ya gama kashe kudinsa akan gidan nan amma bah Furnitures en kirki ta qarasa zancen ta yatsina fuska"


"Ruqayya ce ta yunquro ta miqe da kyar da niyyar yi musu magana da hanzari Aunty Asma'u ta dakatar da eta suka cigaba da aikin gaban su kowa cikinsu na mamakin hali irin na *kannan mijin*safiyya kowa da abinda yake saqawa a ransa

"sallamar wata mace doguwa fara tas neh ya katse musu zancen zucin da kowanne yake yi a ransa fuskarta dauke da murmushi da kaganta kasan yayar emmatan dake zaune ce saboda kamar dasuka yi bayan ta kuma yan aiki neh hannu su riqe kuloli da Tray wanda aka nade shi da foil paper sannan kuma ga yara maza su kuma sun dakko kwalin ruwa da lemo tayi magana cikin bada izini ,tace ku ajiye anan suka ajiye suka fice,ta fadada murmushinta tana mai qarasowa cikin parlour,tace sannunku da aiki suka amsa da yawwa nan suka gaggaisa ta gabatar musu da kanta A matsayin yayar Angon"


"Ruqayya ma ta gabatar mata da kanta da kuma Aunty Asma,u,da Aunty zahriyya a matsayin qannen ummin su sae kuma Gwaggo saude qanwar baffan su da kuma yakumbo bilki matsayin matar wan baffan su Wanda suke kira da (baffa babba)"

"Ya Hannatu ce ta dago ta dubi su farhana tace ku dama kuna nan neh?"

"Suka amsa da Eh, nan suka shiga gaishe ta, hajir tace ya Hannah ena su nabil"


"Tace suna gidan Momy hajir, tace ae jiya da mukayi waya da Momy Take cemin kun iso

"Hajir tace eh wlh amma nida ya beelal muka zo mamy sai xuwa yau xata qaraso"

"Tace toh Allah ya kawota lafiya"

"Gaba daya palourn suka Amsa da Ameen"

"Nan su Aunty zahriyya suka zuba abinci suka ci sukayi sallah suka cigaba da aikinsu

"Nan ya hannatu tayi musu sallama ta dubi emmatan,tace ku taso malam sule yana jiran mu nace masa zai kaimu kunshi kar lokaci ya qure sukayi sallama suka fice Suka shiga gida hannatu tace Momy kinga dakin amarya kuwa mashallah sunyi qoqari"

"Momy ba tace komai sai baki data ta6e"



******
Farfajiyar gidan Ruqayya neh cike da emmata da Manya dangin amarya dana ango gefe km DJ breka ya Saki waqar (shimfidar fuska) bayan dangin ango sun Kama amarya, qawayenta neh suka cigaba da cashewa can sai na hango 💦Talented writters sun shigo filin rawar da kumaYan Naseeba Gawo fans ✍🏻suna cewa muma bazaa barmu a baya bah💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻




"Washegari ta kama ranar dinner tun misalin karfe hudu su safiyya suka tafi wurin Make up dake ribado Road Achida neh ya saukesu ya leqa shagon yace Aunty faty ga amaryan mu nan ki mata Make Up en da zamu kasa ganeta


"make up artist din ce ta dago tace baka da damuwa sir da yake qanwa ce wurin wani abokin su,nan su safiyya Suka gaisa da aunty Faty, tafara aikinta wajen qalqale fuskar safiyya da cancada Mata ado na ban mamaki nan da nan sai gashi ta Chanja dama abinka da mai kyau wayarta dake hannun qawarta wato Sadeeya Smart ce ta fara qara ta taso ta miqawa safiyya, tana dubawa taga ba kowa ke kiran illa angon nata a ranta tace to meye kuma dan rigima ta kara wayar a kunnenta tana mai yimasa sallama,ya amsa yace an kusa gamawa, tace eh, yace ena fatan baki manta da kayan dana kawo miki na wurin ya hannatu ba koh?,Tace ban manta bah,yace toh

Please Login or Register in order to submit comment