Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

♥
♥ ❤
♥♥❤
*~K'AREENATEEY~*
(K'AWATA)


https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/


*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*




*~We are bearer's of so golden pen🖊~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*

*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*







*written*✍

*by*

*Deeja one love*


*JAKADIYAR GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION👸*



*~Dedicated~*

*_To*_


*~Aisha yunus(eesha lurv)~*

Bismillahir rahmanir raheem


*YA ALLAHU*


[al-Bukhari]
On the authority of Abu Hurayrah (may Allah be pleased with him), who said that the Messenger of Allah (peace be upon him) said: When Allah decreed the Creation He pledged Himself by writing in His book which is laid down with Him: My mercy prevails over my wrath. It was related by Muslim.


[Quran 35:13]
He merges the night into the day, and He merges the day into the night. And He has subjected the sun and the moon, each runs its course for a term appointed. Such is Allah your Lord; His is the kingdom. And those, whom you invoke or call upon instead of Him, own not even a Qitmîr (the thin membrane over the date­stone).


_1_

Sauri nake domin na karasa gida dan yau garin da rana gashi azumi nake,jikin na kuwa har diga yake da zufa.



Get na kwankwasa aka bude mata,cikin girmamawa na gaishe da mai gadin sannan na wuce ciki.



Gidane mai part-part da yawa,kusan guda hudu,biyu dake gefe Wanda daya yana kallon daya,daga gaban gidan kuwa,wani hadadden part ne Dan madaidaici.


Wannan karamin part din na kalla,takalma na gani a kofar part din wanda hakan yana nuni da babana yana gari kenan,part din nan guda hudu na biyu na kwankwasa.



Kanwata hafeeza ita tazo ta bude mini,cikin natsuwa na shiga da sallama,,ummi dake kitchen ta amsa mini,da sauri na karasa kitchen din,ganin ummi tana girki,raina ya bace.



Daki naje na ajiye jaka ta sannan na dawo kitchen din har ta gama dafa doyar,amsa nayi na daka mata sakwarar,ina gamawa ana kiran sallar magrib,don haka na fara hada kunun aya.




Dabino naci sannan na wuce dakin mu domin yin sallah,babu kowa sai dai dakin tsaf yake ko'ina a gyare,bathroom na shiga nayo alwala na fito,Ina idar da sallah nayi azkar sannan na fito.



A falo na sami ummi tayi wanka ta canza kaya nasan saboda yau ita take da girki ne kuma abban mu na gari,cikin natsuwa nace mata"ummi zanje in gaishe da Abba nayi mishi sannu da zuwa",amsawa tayi da "a dawo lafiya,amma kiyi sauri domin kinga baki ci komai ba",ina tafiya na amsa da to.




Cikin natsuwa na isa part din mahaifina,har lokacin akwai takalma a kofar falon shi,sallama nayi sai da ya amsa sannan na nemi izni na shiga.



Yana zaune a kan abin sallah,littattafai ne gasu nan da yawa a gaban shi,sai mutane guda biyu wanda duka daliban shi ne,kusa dashi naje na zauna.



Matso dani jikin shi yayi yace"mama na ya azumi,ance Dani kinyi azumi",daga kai nayi alamar eh kafin nace"nayi Abba kasan na saba da hakan",girgiza kai kawai yayi.



Na dade a wajen shi sannan na fito domin na tafi,a bakin get na hadu da rufaida tana ta faman sauri,dafa ta nayi cikin sauri ta juyo,a hankali tace"Abba ance ya dawo",cikeda takaici nace"haba rufaida meya sa kike hakane tun safe da kika fita sai yanzu kika dawo fa",harara ta galla mini tace"dalla rufe mini baki,ina ruwan ki dani matsa ni ki bani waje",bangaje ni tayi ta wuce.



Da idanu na bita ina mamakin hali irin na wasu daga cikin yan gidan mu.



Koda na koma na samu ummi tana kallon aljazeera,zama nayi sannan nace"ummi sannu da hutawa",cikin farin ciki tace"yauwa sannu yar albarka,jeki ki dauko abinci kizo kici kada ki zauna da yunwa",cikin natsuwa na mike naje kitchen na dauko abincin.





Sai da naci na koshi sannan na tashi,wanka kawai nayi na daura alwala sannan nayi sallah,doguwar riga nasa banyi wata kwalliya a fuska ta ba amma duk da haka rigar tayi mini kyau,hijab har kasa na zumbula sannan na fito,nasan yau aji zai cika domin Abba yana gari.



Kamar yadda na zata haka kuwa ya faru domin bangaren,hajiya a cike yake,waje na samu na zauna,tun daga kan kanne na na fara koyar dasu sai goma da rabi sannan a ka tashi.


Hannun kanne na na rike muka tafi bangaren mu,yanzu mama tana kwance ne a three seater,sai da safe muka yi mata sannan kowa ya wuce dakin shi.



Mu uku muke kwana a dakin mu,sai da nayi alwala sannan suma kannen nawa suka yi,shafa'i nayi sannan na kwanta.


*ASALIN MU*
Alhaji mukhtar mai atamfa, yana da mata guda d'aya wacce wato juwairiyya ita ta haifi yara guda biyar hudu maza daya mace.



Alhaji datti shine babba,wanda yake gidan da yake kusa da namu, yana da yara da mata guda biyu, mutum ne mai sauk'in hali,da kaifin tunani, sai dai fa kaifi d'aya ne.



Sai abubakar wanda yake bi mishi,shi kuma allah yasa mutum ne mai zafi da saurin fushi, sai dai kuma yana wa d'an uwan shi biyayya.



Sai habeebu,shi kam bai d'auki duniyar da zafi ba,yana da wasa da dariya sosai, sai dai akwai zafi idan aka tab'o shi.



Sai mahaifina mahmoud shi kam be ma cika magana ba, yana da zurfin ciki sosai da hakuri da juriya.


Sai autar su kareema macece mai kirki da kyawun hali, duk yan gidan mu suna son zuwa wajen ta hutu.


Alhaji datti(baban gida) yana fama da ciwon idanu hakan yasa abubuwa suke faruwa bashi da masaniyar duka.



Alhaji abubakar(abba) kasuwancin shi yake yi acan k'asar dubai, haka yafi zama a kano inda mafi yawan shagunan sa suke.


Alhaji habeebu(baba)shi kam duk abinda aka gaya mishi hawa kai yake ya zauna especially matan shi gashi kuma still bashi da zafi sosai.



Alhaji mahmoud(baba malam) shi kam yawon wa'azin shi yafi mishi tarbiyat yaran shi.

Sunana juwairiyya mahmoud mukhtar mahaifi na malam mahmoud mukhtar babban malami ne da ake ji dashi a kasa nigeria da ma makwabtan kasashe.



Ni juwairiyya,sai kanina abdul azeez,shi yake bina,daga shi sai fateema wacce muke kira da hafeeza domin itama sunan maman mahaifiya na aka saka mata,daga ita sai abdul malik,bayan shi sai autan mu abdulhafeez.



A duk kannena mun fi shakuwa da kanina Wanda yake bina,duk wannan fadan na sako mu ba muyi shi ba,duk abin da yake damuna nakan gaya mishi,haka shima yakan gaya mini nashi matsalolin kuma mukan bawa juna shawara.

Amarya itace muke kira da aunty,ita kam bata cika damuwa da shiga harkar gidan ba,koda yaushe bangaren ta a kulle yake,yaran ta biyu,abdul jabbar da abdul jalal.yar katsina ce ita.

Yawan tafiye-tafiye wa'azi da baban mu yake yi ya fara taba tarbiyar yaran shi,duk da hakan ma wai iyayen mu mata sukan sa ido akan mu.




Akwai kyakkyawar alaka tsakanin yan wannan dakin da wannan dakin hakan ya Dan rage lalacewar tarbiyar tamu, sai dai fa akan taba fada especially akan 'ya'ya.



Kadan daga yayan baban mu ne suka fita zakka ciki kuwa harda ni,domin kowa a gidan ya tashi kwatancen abin arziki to Dani akeyi,yawan ibada ta yasa mahaifina yafi sona a kaf yaran shi,haka ma mama na,Dan ita bata wannan kawaicin na yan fari.




Muna zaune tare da wan mahaifina,alhj abubakar da matar shi maryam,yana da yara guda uku, yaya khaleed shine babba sai yaya khaleel,sai khairiyya.



Duk gidan kowa yasan irin shirin da muke da yaya khaleed,haka kuma kowa yasan rashin shirin da muke da yaya khaleel.



Akwai ma'aikata akwai yan kasuwa a cikin yaran gidan mu,yaya khaleed yana daya daga cikin yan kasuwar gidan mu,domin ko a makaranta business admin ya karanta.



Duk yaran gidan mu mata basa wuce secondry ake aurar dasu,ni kuma gaskiya ina da burin cigaba da karatu.

Sai gidan dake kallon namu, nan mahaifiyar baban mu take, sai yayyin babanmu guda biyu,suma dai kusan yadda gidan namu hake haka suke har ma sai namu gidan ya dan fi nasu tarbiya.


Yaya khaleel kuwa shida yaya abdul samad(na biyu a yaran umma)kuwa su dama suna can makarantar sojoji,dake kaduna don tun suna kanana suke burin zama sojoji.



Tafiyar su ya karawa yaran gidan mu rashin ji damin dama sune masu zafin.



Yanzu haka mu biyar muke,ss3,ni da rufaida sai khairiyya,aliyu da ameer.



Nida rufaida dama bamu cika shiri ba kasancewar halin mu ya bambanta,ita tana da fada ni kuma inada kafiya,da khairiyya muka fi shiri sosai.

~Wannan shine ainihin labarina.~




***** *****



Washe gari da wuri na tashi na shirya domin muna zuwa lesson don mina daf da yin jamb,atmafa me ruwan hoda da ratsin lemon green na saka,hijba ruwan hoda na saka har kasa sannan na dauko nikab na daura.




Sallama na yiwa ummi sannan na fita,bangaren hajiya na fara zuwa na gaisheta sannan na shiga dakin su rufaida,ta rigada ta shirya abaya ta saka baka,hijab fari ta saka,a tare muka fito muka yiwa hajiya sallama.



A bakin get muka taradda aliyu da ameer,kallon su nayi nace"ku jira ni na Kira khairiyya",ameer kawai ya amsa da to,cikin sauri na nufi bangaren su.



Karo muka kusa yi dashi,cikin sauri na ja da baya,kallon juna mukayi muna murmushi,a hankali na gaishe da shi,fuska sake yace"lafiya lau kanwata".





Tare muka jero muna tafe muna fira cikin nishadi,a bakin get muka tarar dasu ina kallon rufaida tana galla mini harara.


Suna gaba muna baya har muka fito bakin titi,kallo na yayi yace"beauty bari na koma daga nan,kiyi karatu da yawa domin ina so ki zama cikakkiyar likita".



"Insha Allah kada ka damu yaya zan yi karatun da sai kayi alfahari dani", murmushi yayi yace "yauwa yar kanwata".

Ajiyar zuciya kawai nayi kafin nayi murmushi nace"allah na gode maka daka bani yaya wanda yake ji dani",dariya mukayi duka kafin na juya mu ka tsallaka titin.




Sai da muka bacewa ganin shi sannan rufaida ta harare ni tace"ke kam wallahi akwai banza,mai zai sa ki wani janyo mana yaya khaleed kin San kuma gyale nake son yafa wa",murmushi kawai nayi.



Mota muka tare muka hau,dai dai layin radio aka sauke mu anan ta tsaya ta canja hijab din zuwa gyale,dagama legacy daya daga makarantun da suke tashe a sabon gari kenan da kewaye.




na maida hankali sosai da sosai akan karatun da mukeyi kuma alhamdulillahi na fahimta Dan ba yabon kai ba nasan ina da kwakwalwa, Dan duk kwakwalwar da aka bude ta da alqur'ani da farko to bata dakikanci.





Ko bayan mun tashi sai da na siyi pure water,muna tafe duk inda muka gifta fadi ake ga *'ya'yan malam*.




Kamar yadda muka shiga haka muka fito mu biyar, ameer yace"to nidai zan shiga sabon gari Dan haka sai anjima",Dan haushi ko kallon shi ban yi ba.




Mun tsaya a bakin titi rufaida ta tare me keke napep tace mana"kai ni zan wuce idan kunje gida kuce na tafi gaishe da wata friend dina wacce muke class daya".




Cike da jin haushi nace"wallahi baki isa muyi karya ba,Dan haka duk Wanda ya tambaye ni cewa zan yi nima bansan inda kika tafi ba".



Harara ta tayi kafin ta kalli khairiyya tace"kinji sis idan kinje ki gayi yadda na fada miki",daga kai tayi Wanda hakan ba karamin bata mini rai yayi ba.




Ko kallo na bata kuma yi ba ta shige keken,a dai dai kofar doka aliyu shima ya sauka,Dan shi bema ce mana komai ba.




Muna sauka,nace"wallahi khairiyya wannan hali na yaran gidan mu na bani haushi,amma wanda nafi ganin laifin shi shine baban mu,domin yafi bawa wa'azi mahimmanci fiye damu yaran shi",khairiyya tayi murmushi kawai.




Sai da muka kusa gida sannan tace"hakane juwairiyya sai dai ki sani aikin shi aikin allah ne",harararta nayi nace"mu kuma yaran shi sai akace ya barmu mu lalace,kada ki manta uba makiyayi ne akan yaran daya haifa kuma sai allah ya tambaye shi akan abinda yake kiwatawa,da yake malami sai akace ya gyara gidan wasu,shi kuma gidan shi ya bari ya lalace?".



Murmushi tayi tace"hmm juwairiyya kenan Amma kada ki manta baba bema San me yake faruwa ba".



Numfasawa nayi nace"khairiyya ba saboda baya zama bane yasa be san me yake faruwa ba?",haka dai har muka karasa gida firar da muke kenan.


Kamar yadda na zata hakan ne ya faru domin baba dai baya gida,to dama a ya kwana biyu a gida a sati yayi kwana biyu,Allah ya kyauta!.





Kusan duka mazan gidan basa nan,matan ma sai kadan ,domin wasu duk sun tafi makaranta.





Da sallama na shiga bangaren mu,ban sami kowa ba a falo,hakan ya bani tabbacin ummi tana barci.



Wanka kawai nayi,wata shadda na saka,ruwan hoda doguwar riga ce wacce tana da aiki a jiki,ta zauna das a jikina.



Kitchen na shiga na fara kokarin dafa mana lunch,nasan kanne na sun kusa dawowa,kuma abdul'azeez bashi da juriyar yunwa.




Jalop din shinkafa da wake ta manja na girka,ina gamawa na hada mana zobo,sannan na wanke kayan Dana yi amfani dashi.



Dama an riga da anyi kiran sallar azahar Dan haka ina gamawa na wuce daki,sai da nayi wanka sannan na dauro alwala,riga da siket na material na saka.



Cikin nutsuwa bayan na idar da sallah na nufi dakin ummi,a kwance na same ta tana ta barci,filo na Dan bubbuga tana bude ido nayi murmushi nace"ummi lokacin sallah fa yayi".



Mika tayi sannan ta shige bayi,cikin nutsuwa na gyara gadon data kwanta,sannan na fita daga dakin.









♥ ❤
♥♥❤
*~K'AREENATEEY~*
(K'AWATA)



*~GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATON~💫💫💫*

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/

*~❄we beare's of soon golden we writer's assiduously percieven No pain so magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Out worlds for it cause u np pain~*





*written *✍
-by-
*Deeja one love*

~Dedicated~

To


*~Aisha yunus(eesher lurv)~*


Wattpad 13deeja

Deeja1love.blogspot. com

An k'arbo daga abu huraira Allah ya k'ara masa yarda yace:Manzon Allah (SAW) ya hana aske wani yanki na kai a bar wani b'arin.


*YA AR-RAHMAN*


_2_



Ina zaune a daki kanne na suka dawo daga makaranta,abdul'azeez ya shigo da sallama, amsawa nayi, gefen gado ya zauna sannan yace"sweet ya dai naga kamar wani abu na damun ki", girgiza kai nayi nace"babu komai, kaje kitchen abincin ku yana nan", bece komai ba ya mike ya fita.




Ana sallar la'asar na shirya domin tafiya makarantar islamiya, dogon hijab na saka har kasa sannan na fita,a bakin get na tarar da yaya khaleed yana jiran fitowa ta, murmushi yayi mini nima na maida mishi, jerawa mukayi muna tafe muna fira kamar yadda muka saba.




Can bakin fita layin mu muka hangi abdulhafiz da ameer da kayan kwallo daga ganin alamu kwallon zasu tafi,yadda yaya khaleed bece komai ba haka nima ban ce komai ba.




Muna shiga makarantar na wuce nawa ajin shi kuma ya wuce office domin makarantar ta abba ce haka yaya khaleed ya bawa shugabantar makarantar kasancewar be cika zama ba.





Ina shiga ajin daliban ciki suka fara girmamani duk da akwai wa'inda muke sa'a daya kai harda wa'inda suka girmeni sai dai fa a shekaru kawai amma a karatu duk na fisu, karatu mukayi cikin girmama juna har lokacin tashi yayi.




Sai dana jira ya kammala abinda yake yi sannan muka taho,muna zuwa kofar gida mita nayin parking, rufaida ce ta fito daga ciki da alamu bata ma lura damu ba.




Saurayin dake ciki ne ya rike hannun ta yana murmushi,itama murmushin tayi mishi,dago kan da zata yi suka hada ido da yaya khaleed, ganin irin kallon da muke mata ne yasa duk ta tsargu.




Cikin daburcewa ta janye hannun ta, ta fara tafiya har ta shiga get yaya khaleed ya kwala mata kira jikin ta ya hau rawa, karasawa kusa da ita mukayi, kallon tuhuma yayi mata kafin yace"ki sani duk abinda kika yi a wannan lokacin kanki kike yi mawa, sannan duk abinda kikayi watarana zaki yi dana sani dan haka kiji tsoron Allah a duk inda kike", kallo ma yayi have"muje ko", wucewa mukayi muka barta a tsaye jiki a sanyaye.



Mun zana jamb din mu alhamdulillahi ya fto kuma munci baba data Dan duk rashin jin yaran gidan mu akwai kwakwalwa fa.



Yanzu haka yau muke graduating daga secondary, dan mun gama wa'ec da neco, yanzu zaman jiran result muke.




Ina zaune ina yanke farce, khairiyya da rufaida sukayi sallama suka yi, murmushi nayi nace"sannun ku da zuwa ku karaso kunji,zama suka yi khairiyya ta harareni tace"ke wallahi baki da mutunci ko leke wato saboda yanzu babu makaranta ko", maraicece fuska nayi nace"yi hakuri wallahi ba haka bane kinsan abubuwa sun yi mini yawa ne".



Dariya suka yi suka tafa kafin khairiyya tace"aifa kiji sai kace wata yar kasuwa", dariya muka yi gaba daya. Nan dai muka cigaba da fira har yamma tayi.



Rufaida tace"ni wallahi zaman gidan nan yau ya ishe ni jira nake kawan my guy yazo mu fice", babu wanda yace komai a cikin mu.




Khairiyya ta rike hannun na tace"tashi muje ki raka mu", har na bude baki zanyi magana sai na fasa(ashe rabon wahala ke kirana).



Kasancewar cikin gidane yasa na zura karamin hijab na hafeeza muka fice, ko ummi ban gayawa ba.



Muna tafe muna fira da shewa, daga gefen parking lot na hango yaya khaleed da alama mota zai shiga, kwala mishi kira nayi ya juyo,kallon su rufaida nayi nace"to nidai na tsaya anan bari naje wajen yaya khaleed.



Ban tsaya jin me zasu ce ba na juya da gudu na nufi wajen shi,rike murfin motar yayi yace "kanwa ta rigima wai yaushe kika zama hakane? ", jingina da motar dake kusa dani nayi ina murmushi.



Jinjina kai yayi yace"ya akayi to? ", dariya nayi kasa-kasa nace"kai yaya meye dan nazo wajen ka, ina zuwa haka? ".



Shiru yayi kafin yace"abba ne ya kira ni yace naje na dauko shi yana airport? ", da mamaki nace"au dama baya kasar", daga mini kai kawai yayi, murmushi nayi nace"inzo muje", kallo na yayi kasa da sama yace"a hakan zaki je to ba sunana saratu ba, kin gama tafiya ta", ya fada yana shiga motar.




Dariya nayi domin nasan dama haka zai ce, daga mishi hannu nayi har ya juya zai fita ya leko yace"kanwata wuce gida", noke kafada nayi ina bubbuga kafa a kasa nace"ni ni sai naga fitar ka", murmushi kawai yayi ya karasa ficewa.



Kamar jira na cikin motar yake ya fita ya budo kofar da karfi wanda hakan yasa murfin ya ture ni na fadi kasa, na kuwa bugu a kwankwaso na.



Tsayawa kawai nayi ina mamakin me karfin halin nan, yafi minti biyar a ciki har na cire ran ganin ko waye ya sako kafar shi guda daya,a hankali cike da kuzari ya karasa fitowa.



Tunda naga takalmin sojoji jikina ya dauki rawa, amma duk da haka sai da na bishi da kallo, namiji ne kakkarfa, wanda gaba daya jikin shi a murde yake, wandon jikin shi na sojoji ne sai farar riga, kanshi facing cap din sojojin ne kunnen shi sanye yake da head phone,babu laifi yanada haske amma kuma ba irin sosai din nan ba.



Ina tsugune gaba na na cigaba da dukan tara-tara, tsawa ya daka mini wanda yasa gaba daya na rude, hawaye ya fara zuba daga idanu na, hannu daya yasa ya dago ni.




Kallo yake bina dashi ranshi a matukar bace,runtse idanu nayi,magana yake a nutse yace"ba zaki bude idanun ki ba sai na karya ki a wajen", sanin hali yasa nayi saurin budewa.



Cikin daga murya yace"ki dafa mini wani abu mara nauyi ki kai mini daki na daga nan ki tsaya ki gyara, saura naga ba yarda nake so ba",yana sakina na kwasa a guje nayi part din mu.



Da kanina abdul'azeez muka hadu, jiki na har bari yake yi wajen wuce wa, hannuna ya riko yana fadin"sweet meya faru? ",waje kawai nake nuna wa ina ajiyar zuciya, ganin bazan yi magana bane yasa ya ja ni muka shiga cikin daki.



Gefen gado ya zaunar dani, sannan ya fita minti biyu ya dawo hannun shi rike da cup, miko mini yayi, amsa nayi na shanye ruwan ciki tas, sai da ya ajiye kofin sannan ya dawo ya zauna.



Jiki a sanyaye yace"su yaya abdus-samad sun dawo ko? ", daga mishi kai nayi,ajiyar zuciya yayi yace"ai nasan wannan mara mutuncin shi kadai zai tsorata mini yar uwa,ban tanka ba haka ban dena ajiyar zuciyar ba.




Shiru ya biyo baya tsayin minti goma, a hankali na sami relief, ina dagowa muka hada ido da abdul'azeez murmushi muka yiwa juna kafin yace"kai sweet kin cika tsoro".



Fadin haka yasa na tuna da ya sani aiki, ai a sittin na mike jiki na ya dau rawa, allah sarki dan uwana dandanan hankalin shi ya tashi,yana tambaya ta meya faru? ",hawaye na goge nace"sweet wallahi yau yaya khaleel duka zai yi mini aiki fa ya sani", dogon tsaki yaja ya juya zai fita.



Yadda na lura abdul'azeez haushin yaya khaleel yake yi domin yanda yake mini, hannun shi na rike nace"na shiga uku sweet wallahi abinci yasa ni nayi mishi?",tabe baki yayi yace"kije ummi ta gama ai sai ki diba mishi", daga haka ya fita.




Cikin sauri nayi hanyar kitchen, allah kuwa ya taimake ni ta gama din ta, babu kowa a kitchen din dan haka na dauki cooler na deba na jera komai a basket na fita da sauri.




Shi kuwa bangaren shi, haushin yadda yarinyar ta sashi sai ya sake wanka yake ji, domin yadda ta dinga bubbuga kafa tana wani shagwaba, lumshe idanu

1 Comments On KAREENATEEY
avatar
hauwa-8-2

1 year ago

Reply

Mashaa Allah

Please Login or Register in order to submit comment