Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

*GIDANTA NA GIRMA*


*BY NANA: KHADEEJATU*

_*UMMU IHSAN*_


*SADAUKAR WA GA:- DUKKANIN MASOYA NA NA BOYE DANA BAYYANE INA SONKU SOSAI SON FISABILILLAH*


*YA ALLAH KAJIKAN MAHAIFINA KAYI MASA RAHMA KA KYAUTATA MAKWANCIN SA SHIDA YAN UWA MUSULMI BAKI `DAYA.*


_*Bismillahir Rahmanin Rahim*_

1~5

"Wayyo Allah Mamar mu kin tafi kin barmu cikin kuncin rayuwa wallahi sai na bikii... "

Kawai bata 'karasa ba ta shed'e ko motsi babu, duk ilahir mutanen gidan gaisuwar nan akayo kan ta, ruwa aka fara zuba mata amman bata motsa ba.

Rudewa yayar ta tayi, da gudu tafita kofar gidan tana ihu, mazan dake kofar gidan sukayo kanta da gudu, tambayar sukeyi miye yake faruwa amman ta kasa magana sai cikin gidan take muna masu, ai kuwa basuyi kasa a gwiwa ba suka shiga cikin gidan da gudun su.


Hankalin su ne yayi mugun tashi ganin abunda ke faruwa, wani dattijo ne wanda daga gani kasan shine mahaifin su, dan sunyi matukar kammani dashi, ya duk kusa a kusa da yariyar wadda bazata wuce shekara Tara ba, ya duka ya d'auke ta idon sa cike da hawaye amman kuma hawayen ya'ki barin su, su zubo masa 'kofar gidan ya nufa da ita, wani mutume ne ya d'auke su a mota harda yayar tata, sai asibity.


Taimakon gaggawa aka bata, su kuma duk suna waje a tsaye sai jeka dawo sukeyi.

Doctor ne ya fito yace, "ga wannan takardar a nemo wannan maganin da sauri".


Mutunen ne ya amsa ai kuwa sai gashi da magani da ruwa ya kai aka ansa, cikin ikon Allah, sai gashi ta falka da kuka.

Allurar bacci yayi mata, ya fito, hannu ya baiwa mutanen yace, "ta falka amman nayi mata allurar bacci, saboda haka insha Allah data falka zata dawo cikin hayyacin ta".

Sai doctor yace, "amman dan Allah miye ya firgita ta haka gashi zuciyar ta tafara kumbura dan gab take da kamuwa da ciwon zuciya mai tsananin gaske ".

Sharce hawayen sa dattijon yayi, yace, "ai dole Husnah ta fir gita tayi kamar zata hauka ce, mutuwar uwa ai babban rashi ne, koda ciwo ballema mutuwar cotsom d'aya".


Shi kamshi doctor ya tsorata sosai a take yaji tausayin yarinyar ya 'kara kama sa, Addu'a yayi masu tare da ta'aziyya.

Godiya sukayi masa, ya wuce su.

Zaman sukayi na d'an wani lokacin kafin dattijon ya tashi yazo gurin yar sa d'aya yace mata, "Zara ku sanya hakuri da juriya a cikin zuciyar ku ki zauna da yar uwar ki, lallashe ta, ki sanar da ita, mahaifiyar ku Addu'a take bu'kata ba kuka ba, zan je gurin ansar gaisuwar ne.

Gyad`a masa kai takeyi hawaye na zubar mata a ido.

Tafiya sukayi su biyu ita kuma ta zauna har sai da nurse tazo ta kirata sannan ta shiga cikin d'akin, gin cire yarinyar take a jikin gadon da Karin ruwa jone a hannun ta.

Kujera taja ta zauna a kusa da ita tana kallon ta, tausayin kansu ne ya'kara kama ta.

Tace, "Husnah muyi wa Mamar mu Addu'a ba kuka ba, nasani Mama duk da koda tana a raye bata iya hana a cutar damu kuma, duk azabtar war da akeyi muna tare da ita akeyi muna shi, uwa_uwa ce bare ma uwar da ta koyar damu hakuri da dan gana, ko kin manta da cewar, kullum sai tayi muna nasahar mu d'auki kaddara mai kyau ko marar kyau?, Husnah kin ga gashi doctor yace, kin kusa kamuwa da ciwon zuciya dan Allah ki rufa mani asiri kin san nice kawai zan shiga cikin wani halin idan kika samu wata matsalar".

Hawaye sukeyi, babu mai lallashin su, sai mutanen dake gurin da yaran suka cika zuciyar su da tausayi, duk rashin tausayi irin na nurse amman sunji tausayin yaran.

Daket Husnah tace, "Aunty Zarah shike nan Mama ta tafi ta barmu ko? Kuma sai da nace mata, kada ta tafi ta barmu gashi kuma Baban mu baya son mu, baya kulamu".

Rufe mata baki Zarah tayi tace, "haba Husnah kada kice haka kiyi shirun ki kawai Baban mu yana son mu".

Da sauri Husnah tace, "shine ya kawo mu nan ya gudu ya barmu ko? Kuma kice yana son mu, ko ya bar maki kud'in da, zaki siya muna abinci ne, nifa Mamar mu kawai zanbi".

Kuka Aunty Zarah takeyi sosai, ganin hakane yasaka Husnah kuka itama sai tayi shiru da masifar ta.

Tun 'karfe goma na safe suke asibityn nan har la'asar babu wani abunda ya shigo hannun su, ganin sun gala baita ne yasaka wata matar dake kusa dasu ta basu abinci da ruwa.

Godiya sukayi mata, Zarah ce, take baiwa Husnah abincin a baki har sai da takoshi, sannan itama tace shinkafar jalof.

Har dare babu Baban su babu labarin sa kuma babu wanda ya leko su, mutane sai ala waddai da irin wannan halin sukeyi.

Mutanen gurin kowa basu abinci yakeyi da kayan mar mari iri daban_daban.

Da safe 'karfe takwas da rabi, doctor ya duba Husnah yace, "zan sallame ta a yanzun dan Allah ku kula da maganin ta dan gab take da kamuwa da ciwon zuciya mai tsanani, amman idan an kula da damuwar ta da maganin ta Insha Allah komai zai zama dai dai kuma naga harda Olsar ke gareta dan Allah ku kula kunji ko? ".


Gyad'a masa kai Zarah takeyi tace, "mun gode sosai".

Sallama ya basu Husnah fad'ar takeyi, "Anty Zarah muyi zaman mu anan inda babu wanda yake takura muna kuma muna samun abinci mai yawa muna ci ko? ".

Gir giza mata kai tayi tace mata, "dole ne mu koma gida mu zauna kawai dai musaka hakuri a lamarin mu".

Wayau tayi mata, suka bar asibityn tare da wasu kud'in da wasu mutane suka basu, da murna Husnah ta anshi kud'in tana godiya tare da farin ciki, suna fita Husnah ta kwance zanen ta, ta nade kud'in ta kullesu a habar zanen ta, ita dai Zarah kallon ta kawai takeyi abun hawa suka hau suka sauka unguwar su.

Mutane sai gaisuwa sukeyi masu, a take kuma mutuwar mahaifiyar su ta dawo masu sabuwa.

'kofar gidan su babu kowa duk mutane sun watse cikin gidan suka shiga wanda suke jin kamar kada su shiga cikin gidan.

Addu'a d'auke a bakin su suka shiga cikin gidan sallama sukayi aka kyalesu ga mutane zazzaune kamar itace basu amsa Sallama.

Baban sune zaune yana cin tuwo ya kallesu kallo d'aya, ya watsar, kawai cikin masifa wata mata tace, "to gan talali harda mutuwar uwar baisa kun natsu ba, sai da kukaje yawon karuwan cin, ai dama nasani tun jiya kuka baro asibityn sai yanzun kuka ga damar dawowa gidan nan ko!? ".


Fashewa sukayi da kuka kamar ransu zai fita.

Tace, "kukayi banza dani ko bada ku nake ba ne? "

Cikin rawar baki Zarah tace, "kiyi hakuri Goggo wallahi daga asibity muka fito" cikin kuka take maganar.

Tsawa ta daka masu tace, "kai..! Kada ku maida mu mahaukata ko kuma makafi mana! Dubi yanda kukayi mul mul abunku dubi yanda kuka dawo kamar ba masu jinya ba, anya ma kuwa kunji ciwon mutuwar uwar ku kuwa? ".

Kukan makirci ta fashe dashi tanayi tana fad'ar, "Allah na tuba yaran nan zasu sakani bakin mutane bayan mutuwar uwar su, shine zasu fara biyar maza duka yau kwana d'aya da mutuwar uwar su, wai nikam yaya zanyi da y'ay'an Allah bani? ".

Kukan takeyi tana fyace majina da habar zanen ta.

Cikin 'bacin rai da masifa Baban ya jefo su da kwanon da yake cin tuwon sa yana fad'ar, "wallahi 'karya kukeyi ku saka ni kuka, tun kuna yaran ku, wato abun da uwar ku ta koyar daku ke nan ko? ".

Da gudu suka shige cikin d'akin su suka rufe jikin su sai rawa yakeyi dan sun san yan zun nan za a had'a masu jini da majina.

A bakin gado suka zauna sai rusa kuka sukeyi Zarah ce ta goge hawayen ta kwantadda Husnah akan kafafun ta, tana lallashi, dukan 'kofar yakeyi kamar zai 'karya ta yana fad'ar, "kuzo ku bud'e 'kofar nan kafin na balla ta na shigo ciki".

`Kin bud`ewa, sukayi har sai da ya gaji yayi tafiyar sa.

Basu fito ba sai bayan magrib suka bud'e sukayo alwala suka dawo d'akin sukayi sallah, suna zaune har 'karfe goma na dare babu abunda suka saka a bakin su, dabara ce ta fad'o masu, suka lallaba suka d'auki kwano, sukaje suka siyo tuwo suka dawo cikin ikon Allah babu wanda ya gansu.


Tuwon sukaci, Zarah ta baiwa Husnah maganin ta suka kwanta.

Sai kukan kewar mahaifiyar su sukeyi a haka bacci 'barawo ya sace su.

Tun da asuba suka tashi, sukayi sallah sannan suka fita tsakar gida zaunar da Husnah Zarah tayi, ai kuwa a take tafara wanke_wanke da share_share sannan ta d'ora ruwan dafuwar kuko.

Suna tafasa kawai ta dama kokon ta ajiye masu suka dawo cikin d'akin su.

Fitowa uwar ikon tayi zata fara masifa sai hamma takeyi daga gani ko sallah batayi ba, gashi koda take ta zabga hamma babu Addu'a, abun da yabata mamaki shine duk aikin da take son taci masu mutumci idan basuyi ba, sunyi har sun gama, dube_dube ta somayi ko zataga wata matsalar ta daban amman bata gani ba.

Tsaki tayi ta wuce ta d'auki buta, ta shiga cikin bayi ta fito ta wanke baki ta debi kokon tasha, ta zabga sugar sai da tayi biyu da robar koko san nan ta tashi ta fara `dauraye jikin ta ta shiga cikin d'akin ta sanyo hijab ta d'auko charbi ta shiga d'akin Baban su Husnah, ta gaishe shi sannan ta fito ta zuba masa kokon, ta kai masa, yaran ta ne suka fito su ukku mace biyu na miji d'aya babu sallah babu salati, kawai suka wanke baki suka zubo kokon suka 'koshi ragin da sukayi ne aka zuba wa su Zarah aka kira su suka zo suka d'auka, da sanyin sa suka sha.

Misalin 'karfe sha d'aya gidan ya cika da ba'ki na ban mamaki.

A take jikin su Goggo ya d'auki mazari sai ta samu guri d'aya tayi zaune ta rafka uban tagumi.

Su Husnah kuwa farin ciki ne ya kamasu a take taje gurin mutanen ta shige cikin su.

Bayan duk sun zazzauna ne, wani dattijo wanda yadara Baban su Husnah tsufa kadan kuma gashi kamar su d'aya, yace......



*Comment and share*

_*Yin comment din ku da sharhin ku shine zai bani damar ci gaba da wannan labarin kuma shine zai bani tabbacin cewar kuna son labarin*_


*A GIDAN TA NA GIRMA*



*BY NANA: KHADEEJATU*

_*UMMU IHSAN*_


*SADAUKAR WA GA:- DUKKANIN MASOYA NA NA BOYE DANA BAYYANE INA SONKU SOSAI SON FISABILILLAH*


*YA ALLAH KAJIKAN MAHAIFINA KAYI MASA RAHMA KA KYAUTATA MAKWANCIN SA SHIDA YAN UWA MUSULMI BAKI `DAYA.*


_*Alhamdulillah Allah ya dawo dani lafiya na samu sau'kin jiki na ina godiya a gare ku masu kirana kuji ya na 'kara ji da jiki na Alhamdulillah Nasamu sau'ki sosai nagode da kulawar ku a kaina*_



_*Bismillahir Rahmanin Rahim*_

6~10

Mutumen yace, "Allah ya jikan ki Hinde mutuniyar kirki a gaskiya anyi babban rashi a gaskiya mutuwar Hinde tabar gurbi mai wuyar cikewa ya Allah kayi mata rahma"

Ya madaida kallon sa gurin Baban su Zahra yace, "zan dauki Zahra na had'ata da sauran yarana har zuwa lokacin Auren ta, Amina kuma tace itace zata dauki Husnah".

Da kuru ruwa da har gowa delu tazo a gaban mutamen tana fad'ar, "dan Allah kada ku rabani da yarana wallahi ina son su zanyi masu ri'ko na amana da gaskiya" hawaye kawai take zubar wa tayi kwance ta rike 'kafar dattijon tana kuka.

Kallon ta kowa yakeyi Zarah da Husnah kuwa sakin baki sukayi suna kallon salon makirci irin na marka.

Girgiza kansa dattijon yayi yace, "nasani zaki iya ri'kesu a gurin ki bawai bazaki iya bane malka, ko dan ganin mahaifin su Amman gaskiya kiyi hakuri kuma ba yanzun zan dau'ke suba sai angama ansar gaisuwa duk da naga kamar angama ansar gaisuwar ace kwana d'aya har anwatse kamar daman an matsu mutum ya mutu? ".

Babu wanda yace uffan daga cikin su Malka da Baban su Husnah.

Yan uwan girgiza kansu kawai sukayi suna jin zafin wannan mugun halin na mutanen gidan nan, Malka kuwa tunda taji abunda wannan dattijon ya fada sai ta tashi zaune na matso hawaye dan yaji tausayin ta, amman ya dauke idon sa yana kallon su Zarah yana 'kara tausaya masu.

Addu'a sukayi suka tashi tsaye dattijon yace, "Sa'idu kaji dai hukun cin dana yanke a matsayina na yayan ka kuma koda wasa kada naji kada nagani, Allah ya jikan ta da rahma Allah ya baku hakurin jure rashin ta".

Kallon sa ya maida akan Zarah da Husnah yace, "to muntafi sai mun dawo ku kara hakuri kuma kuyita yiwa mahaifiyar ku addu'a kunji ko? Domin addu'ar ku tana isa a gareta ".

Gyada masu kai sukayi.

Rakiyar su, sukayi sai da suka ga tafiyar su suka dawo gida suka tarad da Malka ta balbale Baban su da fada tana fad'ar, "ai wannan tozarci ne wallahi dan mutum yana gaba dakai shine har yake da ikon zar tar da hukunci akanka da iyalan ka? Abu sai kace wanda ya haifeka ako dai koda wanda ya haifeka ne banyi zaton zaka kasa ce masa komai ba, wallahi malam ka bani kunya wallahi, yaran ka matane fa kasan irin abunda ya tsara a ransa kuwa a kansu ? nifa ban ma yarda da wannan salon nasa ba".

Tashi mahaifin su Husnah yayi ya fita yabar mata gidan, dan ya kasa musawa Yayan nasa dan ko iya hada ido dashi bayayi ballema har takai ga yayi musu dashi.

Da ido tabisa ta ri'ke ha'ba tace, "ikon Allah wato dai malam indai a kan zancen Yayan san nan ne bazai iya attaka komai ba, haka kawai mutum ya shanye kowa a cikin dan ginsa dan yafisu kud'i wallahi indai nice Malka sai na hana yaran nan jin dad'in rayuwar su".

Kallon ta kawai su Husnah keyi kuma itama tana kallon su amman ta'ki daina fad'ar abunda take fad'a a gaban idon su.


Bokiti kawai suka d'auka suka fita d'ebo ruwa, koda suka kawo masifar takeyi bata daina ba yaranta ne zaune sun d'aura kafa d'aya a kan d'aya suna zaman kashe wando.

Ajiye ruwan sukayi suka hada kayan wanke_wanke Zarah ke wankawa Husnah na d'auraya, suna gamawa suka d'aura girki sukayi alwala suka nufi daki Malka cikin masifar ta tace, "munafukan banza uban waye kuke nunawa cewar ku musulmai ne , ita kanta uwar taku a lokacin karuwa ce sai da aka 'ka'kabawa Malam ita sannan ta daina a cewar ta amman bafa barin tayi ba, ina kallon yanda take fita zuwa yawon karuwan cin ta, asirin tane kawai bai tonu ba har ta mutu, kunga ke nan ku kan ku ba kuda ya'kinin cewar ku masu tsalki ne ko masu kazanta ne?".


Wannan maganar kam ta shigesu musam man ma Zarah wadda take yar shekara sha biyar hawaye kawai ke zubo mata tana sharewa har suka gama sallar.

Husnah tace, "Anty ki daina yiwa muguwar nan kuka wallahi idan nayi kud'i sai na rama muguntar da takeyi muna da zagin mahaifiyar mu harda su kazafi wallahi bamu yafe ba, ko kuma itama nayi mata Addu'a ta mutu kowa ma yafuta".

Murmushi Zarah tayi tare da shafa fuskar kanwata, sai kuma ta tuno da itama Husnar an kusa rabasu, kawai ta sake sakin sabon kuka tana fad'ar, "mutuwa mai tonon asiri yau gashi rashin uwa zai saka a raba mu nida 'Kanwata ya Allah ka bamu hakuri ya Allah kabamu kariyar ka a duk inda muka tsinci kanmu ya Allah kada ka baiwa wani azzalumi cin nasara a kanmu ya Allah kasani yan zun bamuda wanda zai kwabemu idan muka aikata ba dai_dai ba,ya Allah ka d'ora marayun ka a kan dai_dai ya Allah kada kabarmu da dubarar mu!".

Cikin kuka Husnah ke cewa,"amin ya Allah Anty ai kema ba mutuwa zakiyi ba kibarni ko? kamar yanda Mamar mu ta tafi tabar mu ".

Kiran da akayi masu ne ya sakasu fita ni'kan gari suka kai sai kuma cefane, Husnah ce ke 'kul 'kule Zarah kuma ita ke girkin.

Haka rayuwar su ke tafiya har akayi sati ukku da rasuwar mahaifiyar su .

Du'ke Zarah take tana yiwa Malka da yaran ta wanki Husnah na zuwa d'ebo mata ruwa duk sun gaji, Baban nasu na zaune yana sauraren Radio yaran Malka ukku Ashiru da Nafi da indo suna zaune suna cin abinci dan basuda aiki sai wannan.

Malka kuwa ta kasa ta tsare tana iya bakin 'karfin ta tana zabga bala'i, "wai wankin 'keta ne Zarah keyi masu bata murza kayan sufita".

Sallamar da akayi aka shigo ne ya hanata ci gaba da masifar su Alhaji Audu ne wato Yayan malam Sa'idu shida wasu yan uwan sa harda mata a cikin su sun kai dai su biyar.

Kallon su Zarah sukeyi da suketa zufa ga gajiyar wanki ga zafin rana ga yunwa, girgiza kan su sukeyi tare da kallon yaran Malka dake cin abinci a kusa da dan uwan su.

'Kara sowa sukayi cikin gidan Malka duk ta tsure karyar ta ta 'kare yau sai tayi mutuwar zaune dan batayi zaton cewar maganar daukar su Zarah tana nan ba dan har ta manta da wannan zan cen.

Alhaji Audu ya kalli d'an uwan sa yace, "anyi walkiya mun gano komai Zarah had'o kayan ki mu tafi Amina kuma zata zo ta d'auki Husnah zuwa gobe".

Wani kukan ne ya kama su Zarah da Husnah ai kuwa sunci kuka da ket aka raba su aka tafi da Zarah.

Husnah sai ta dawo abar tausayi yanzun kam ta zama marainiya ga rashin uwa ga rashin Yayar ta kuma abun takaici babu mai janyo ta jikin sa yayi lallashin ta.

Gabaki d'aya gidan zama yayi shiru saboda Malka yan zun han kalin ta yayi mugun tashi saboda taga alamar fa yaran nan za suyi gaba fa ita kuma ta d'auki alwashin wula'kan ta rayuwar su sai sun zama abun kwatance.

Baban kuwa kamar baya gurin haka ya zama.

Da dare Husnah batada abunda zataci abinci dole ta kwanta bacci ya kasa 'daukar ta gashi tsoro takeji babu mahaifiyar su babu Anty Zarah, sai yanzun takara yarda da cewar itama fa tafi kowa maraici kaka kawai takeyi ta dun kule guri daya, har bacci ya d'auke ta baccin wahala.

Run sanyi aka kwalaya mata, a take jikin ta ya d'auki mazari da rawar sanyi.

Malka ce a tsaye sai cika take tana batsewa ri'ke take da bokitin ta a hannun ta tana harar Husnah tace, "uwar kice zata fito ramin tazo ta hura wuta ta d'ora Abinci tayi mani shara da wanke_wanke Iye? "

Girgiza mata kai kawai Husnah keyi, sai rawar sanyi takeyi Malka tace, "tsohuwar munafuka karuwa lalatacciya shegiya maza jeki kifara yi mani aiki tun kafin na kasheki da hannu na! ".

Ai kuwa da gudu Husnah tabar d'akin taje ta had'o kayan wanke_wanke ta ajiye ta d'auki tsintsiya ta soma shara tana kuka ga iska na bugowa ga sanyi na shiga cikin jikin ta, tana 'karasa sharar cikin rashin kwarewa ta d'auki bokiti taje ta d'ebo mata ruwan sai da ta cika komai tafara kiciniyar d'ora girki gashi bata iya ba, ko itacen bata iya had'awa ba, Malka kuwa duk abunda takeyi akan idon tane, kuma tayi kamar bata ganta ba, ganin har tara tayi ne yasa kata zuwa gurin tasa hannu ta turata ta fad'i 'kasa, hannun ta ya daki dotsen murhun taji zafi sosai, da sauri ta tashi ta bata guri tayi gurin wanke_wanke tana gamawa taje tayo alwala ta shiga cikin d'akin nasu ta cire kayan jikin ta wanda ya soma bushe wa a jikin ta, ta tsane ruwan dake kwance a tsakiyar d'akin san nan tayi sallar asubahi.

Har wucewar sha d'aya sannan aka kirata Malka tace, "dan uwar ki jeki ga ragin koko can 'kuda nabi ki d'auka kisha dan kawai naji ance babu kyau horo da yunwa dana haneki kokon nan.

Allah sarki cikin rawar jiki da sauri Husnah ta d'auki kokon duk yayi 'kasa saboda iska gashi duk yayi kakka'bi abun dai zar tausayi haka ta zauna ta shanye kokon har tana sarkewa, harda sud'e kofin sai da Malka tace mata, "shegiya kada ki fasa mani kofi jeki kwaso sauran kayan ki wanke mani su kuma akwai kayan da Zarah bata 'karasa wankewa ba jiya yanzun ki 'karasa wanke su, dan uwarki dan baki sha kokon banza ba".

Babu digon tausayi haka ta kwaso mata kayan nasu harda su zanen gado wanda akayiwa fitsarin kwance.

Har Husnah ta d'uka zata fara wan kewa aka doko 'kofar gidan aka shigo ko sallama babu da ido kowa yake biyar su Baban ne ya fito daga cikin d'akin sa cike da mamaki yake kallon su, haka Malka da yaran ta duk sun saki baki da hanci suna kallon 'kofar gidan.

Kallon kallo akeyi tsakanin Malka da Malam da yaran gidan Husnah kuwa kallo d'aya tayiwa gurin ta d'auke kan ta ta soma jika kayan dan kayan sunfi 'karfin

Please Login or Register in order to submit comment