Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zo dashi ya had'a tea ya kawo farfesun kayan ciki ya bud'e kaza biyu da hollondia dash exectic da dai sauran su, da kayan marmari iri daban_daban.


Koda Husnah ta fito ko kallon sa batayi ba, ta soma neman hijab dan gyale ne tazo dashi, har ta gaji bata samu ba, gurin Husain ta dawo tace, "to ai sai ka kaini gidan Ummey na nemo hijab nayi sallah ".


Kyaleta yayi ya tashi kawai ya bud'e waydrop kawai ya d'auko hijab d'aya ya bata, ta ansa ya shimfida mata sallaya, ta tayar da sallah, kallon ta kawai yakeyi, har ta 'karasa ta cire hijab d'in tazo zata kwanta yace, "malama baki gama ba, kizo ki ci abinci kafin ki kwanta "


Kwanciyar ta tayi tace, "nifa wallahi idan mutum ya dameni, sai dai yaji haushin abunda zanyi dan nifa idan ina fushi da mutane da yawa kowa haushin sa nake ji".


Shima kuwa yace, "indai nine dik abunda kika yi kanki bada ni ba saboda ni na riga da na saba da halayen mutane iri daban_daban musamman ma naki ".


Shiru yaji koda ya duba har tayi bacci.

Shi kam cin abincin sa yayi yana gamawa ya tashi ya fita, sai da Asubahi ya zo ya tayar da ita da ket ta tashi, tayi sallah ta koma sai 'karfe goma da rabi dai_dai ta tashi.


Akwati ne dozin ta gani pink a gefen gadon ta, kawai ta tashi tayo wanka tazo ta bud'e babban atamfa ce duk an dinka su, riga da siket da riga da zani fisis tsaki kawai Husnah tayi ta bud'e wani, les ne da materials DUK an d'inka sa ta ajiye ta janyo kusan na takwas riga da wando ta gani irin_iri kawai Husnah ta d'auko tace, "haba yan zun dai naji magana "


Saka kayan tayi ta rufe akwatin ta janyo wani akwatin na hud'u takalmi ta gani sai da ta za'ba ta darje ta saka taje gaban madubi ta gyara gashin kanta ta d'aure da ribom ta feshe jikin ta da turare tayi tafiyar 'kofar ta bud'e sannu a hankali taji ta bud'e ta sauke ajiyar zuciya kawai ta fito ta zaga ko ina, falo ta fito tv ta gani a kunne a kallon boll tsaki kawai tayi ta nufi gurin ta d'auki remote d'in ta dawo akan kujera ta sauya tasha ta dawo bollywood, Indian series akeyi tayi zaune tana kallo, kawai taji an anshe remote din kofa da duba Husain ne zaune a 'kasa yana kallon ta yace, "wallahi kin raina ni da yawa yarinyar nan nifa bana son raini".



Husnah ta ce, "Allah ko? Wai ma nikam miye ya zaunar dakai cikin sashe nane? bayan ga naku sashen can, kwaya d'aya "


Kallon kin ma raina mani da wayau yake yi mata yace, "wallahi kin ma ci uban rainin wayau wato dai ke kullum da abunda kike tsarawa ko? To bari anjima a kawo mani Amarya ta ki gani, wallahi sai kin nemeni kin rasa ina can ina shan soyayya ta da Amarya ta".


Ta'be baki Husnah tayi tace, "oh ! dai wannan uwar guzumar matar mace mai kama da irin 'kattan nan da suka tashi kashe ka a gidan mu"


Tsaki yayi ya tashi tsaye yace, "ga abincin ki nan da Ummey ta aiko maki dashi ni kinga tafiya ta, keda gani na sai ranar da muka fito shakatawa nida Amarya ta".


Husnah kuwa tace "ayi dai mu gani in tusa na hura wuta".


Dariya yayi ya fita Husnah kuwa tea kawai tasha, tayi kwanciyar ta, haka Husnah ta yinini ita d'aya daga kallo sai sallah sai bacci.


Sai da safe Husnah na kwance a falo tana bacci, Husain ya shigo kallon ta yayi yace, "dube ta kamar ta kwarai ".


Ina kanta yake, yake dokawa, bud'e idon ta tayi, tana ganin Husain kawai sai ta tashi zaune tace lafiya? Husain yace, "malama ki tashi muje ki bud'e mani sashe na muyi magana da ku ".


Kamar ba zata tashi ba, kawai sai ta tashi tana zuwa d'akin ta ta d'auko makulin ta bashi tayi kwanciyar ta, shi kuma ya fita, har magriba bai ga Husnah ba, har akayi isha 'i har 'karfe goma da rabi kawai Husain ya sameta zaune ta buga uban tagumi, yana kallon ta yace, "mikike tunani ne kuma tun d'azun nake neman ki baki zoba tun safe har zuwa wannan lokacin ".


Budar bakin Husnah keda wuya, tace, masa "ina waya ta"


Ko kallon ta baiyi ba ya tashi tsaye yace, "tashi muje ke nake jira".


Kin tashi tayi har ya gaji da jiran ta ya tafi.


Satin Husnah ukku a gidan Husain Amman kullum cikin fad'a suke, Husain yayi_yayi akan Husnah tazo suyi magana da ita da Amaryar sa amman ta 'ki zuwa, yauma kamar kullum Husnah ce zaune tana yankan farce, Husain ya shigo kawai ya kara mata waya a kunne.


Ummey ce tace, "Husnah ya kike ya na ba'kun ta?" shiru Husnah tayi, Ummey ta ce, "Husnah ki dai na fushi dani akwai dalilin da yasa kowa bai nemeki ba, saboda muna fatan ki daure ki zauna zaman Auren ki kamar yanda nima na nake zaune da nawa igiyar Auren, Husnah dan Allah kiyi hakuri kiyi biyayyar Aure, kuma na baki umarnin kije inda yake neman ki, zai had'a kanku ne keda matar sa, Husnah indai kin yarda da cewar nice maman ki ba Maman mijin ki ba tashi ki tafi".


Tashi kawai Husnah tayi ba tare da tayi magana ba, shima tashi tsaye yayi yace, nsgode Ummey, suka kashe wayar.


Tunda Husnah ta tashi ya shiga gaba tabi bayan sa, sai yau Husnah ta , ta'ba zuwa bakin 'kofar tun farkon zuwan ta gidan, d'akin na tsakiyar ya bud'e suka shiga a kwance suka same Mardiyya tana charting da wayar ta, Husain ne yayi sallama, Husnah kuwa kallon yanayi da tsarin gurin kawai takeyi.


A kan kujera ta zauna ta d'ora 'kafa d'aya akan d'aya, Husain ya zauna bayan ya zauna ne yayi salatin Annabi muhammad Sallalahu alaihi wasallam, sannan yayi godiya ga Allah da ya nuna masu wannan ranar sannan yace da Husnah, "Husnah dake zan fara domin ke uwar gida duk da kasan cewar Mardiyya tana gaban ki nesa ba kusa ba, to ina son ku zauna lafiya ku fahimci junan ku bana son fad'a bana son raini ya shiga tsakanin ku"



Mardiyya nadawo kanki kada ki ga cewar kin girmi Husnah yasa ki raina ta, aa ban yarda ba, itace gaba dake a gidan nan bana son ki raina ta bana son fad'a kuyi zaman ku na lafiya, Mardiyya zan koma jan hankalin ki, Husnah 'karamar yarinya ce, amman bata d'aukar raini da wulakanci idan kika zauna da Husnah zakiji dad'in zama da ita, amman idan aka samu sa'banin haka to wallahi, zan koma gefe ne nayi kallon ku, nidai a iya sani na, Husnah bata da daukar magana komai abun mutum indai ba shine ya tsokane ta ba, to babu ruwan ta da mutum,


Husnah kada kiga kamar ina yabon kine a gaban ta aa iya gaskiya ta nake fad'a , ke kuma Mardiyya kada kiga kamar ina goyon bayan Husnah ne aa iya gaskiya ta nake fad'a nasan halin ta fiye da tunanin mai tunani nasan abunda zata iya aikata wa ko miye ".



Shike nan sai kuma rabon kwana zaku iya za'ba wa kanku yanda kuke so.


Husnah dai iya kacin ta bin su da ido, Mardiyya kuwa sai cika take tana batsewa sai hura hanci takeyi tana gun guni, Husain ya ce, ku nake saurare".

Mardiyya ta ce, "wane rabon kwana kuma bayan wanda kayi kwana biyu_biyu to amman nifa gaskiya Husnar nan kada tace zata takani yanda take so, dan bazan d'auka ba, kuma ni wallahi ba bu wanda ya isa Ina tare da miji na yazo ya tsare ni da ido.


Husnah kuwa murmushi tayi tace, "ka gama ko dan zan koma ne naci gaba da abunda nakeyi, bana son sai na tashi a dawo dani".


Husain yace, "zaki iya tafiya".


Tun daga wannan ranar Husain da Husnah basu 'kara had'uwa ba har sai ranar da Ummey suka zo da su Anty Zarah, Husain na zaune da Mardiyya su Anisah kuwa suna tare da Husnah suna labarin su, Husnah ta ce, "yauwa Daddy Ummey zan dawo wannan d'akin da zama na gaji da zama wan can sashen".


Husain da Mardiyya cike suke da mamakin Husnah wadda ko kallon inda suke batayi ba.


Daddy yayi dariya yace, to ai daman makulin nakine kuma suna hannun ki, ki dawo warki kiyi zaman ki"


Husnah ta ce, "Daddy ya ari makulin bai dawo mani dashi ba".


Daddy yace, "ka dawo mata da makulli ta yanzun nan".


Bata makullin yayi, ba tare da yace uffan ba, Husnah kuwa murmushi tayi, haka suka yini sai dare suka bar gidan, Husnah kuwa rufe d'akin tayi ta rufe 'kofar shiga sashen ta, ta bud'e sashen Husain ta shiga, sai da ta za'bi d'akin da take so ta zauna.


Husain kuwa tattara komai nasa yayi yabar mata sashen, har Auren su ya kai wata hud'u tsakanin Husnah da Husain babu wani ci gaba Mardiyya kuwa hankalin ta kwance Husain ya zama nata, sunje ganin gida yafi biyar kuma su Anisah na zuwa gidan.



Yauma kamar kullum Husnah ce zaune tana kallo ga baki d'aya hankalin ta ya tafi akan film din bata ma ji shigowar su ba, sai daga baya ta lura da mutane zazzaune, Husnah yi tayi kamar bata gan suba, Husain ne ya shigo dai dai lokacin Mardiyya da abokan ta na fad'ar, "Husnah wallahi sai munyi maki d'an banzan duka a gidan nan, babu uban da zai iya kwatar ki a hannun mu, kuma Husnah ki sani sai kin bar wannan gidan da kike mulki a cikin sa".



Murmushi Husnah tayi ta ce, "Husnah taje koyon sallama kuma yiwa Husnah duka a dai dai wannan lokacin tamkar yin kisan kaine a gaban kotu".


Su shidda harda Mardiyya sunyo kanta ke nan Husain ya daka masu wata uwar tsawa ya sai ya d'aure su, har Mardiyar sai ta bar masa gida.


Duk a razane suke kallon Husain cike da mamaki Mardiyya cikin rawar murya tace, masa, "yaushe ne ka dawo?".


Ba tare da ya bata amsa ba kawai ya fita zuru_zuru sukayi, Husnah kuwa dariyar ta kawai takeyi tace, "indan Husain ne baku san halin sa ba, kema Mardiyya idan na fahimce ki to har yan zun baki san waye mijin ki ba, zaune ne kawai kike dashi har na tsayin wata hud'u zuwa biyar amman nikam halin Husain sai dai na bada labarin sa, da zakiyi mani biyayya da baki sha wahala ba gurin karantar halin sa ba, gashi dai yan zun zaki d'an dani station kiji dad'in ki Mardiyya matar Husain ".



Kuka Mardiyya ta saki yan sanda ne mata suka shigo suka tasa 'keyar su a gaba suka bar gidan dasu.


Shima fita yayi Husnah kuwa kamar bata gurin.


Su Mardiyya sun sha matu'kar wahala a gurin yan sanda kuma Husain ya'ki zuwa belin su har sai da iyayen su suka je da kansu, Husain bai sake waiwayar Mardiyya ba, kuma baya d'aukar wayar ta, sai da iyayen ta suka je suka sanar dasu Daddy, ai kuwa Daddy yayi fad'a sosai da kansa yaje gidan ya d'auki Mardiyya da iyayen ta, sukaje gidan sosai Daddy ya tsare Husnah da Husain yayi ta zagin su, ta inda yake shiga ba tanan yake fita ba, ranar duk hankalin su ya tashi, kuma Daddy yace, Mardiyya ciki ne da ita wata hud'u idan kuka yarda cikin nan ya sami wata matsalar to sai kunyi na damar sani na a matsayin mahaifin ku! ".


Tashi yayi ta fita ba tare da ya saurari d'aya daga cikin su ba.


Iyayen Mardiyya kuwa Daddy ya burge su sai kuma suka dawo jin nauyin sa.


Mardiyya kuwa cike take da mamakin irin yanda akayi Daddy yayi wa su Husain da Husnah haka bayan tasan irin son da yakeyi masu.


Husnah kuwa murmushi tayi tace, "yau mun taro Daddy amman ni kam yau na tsani kaina ace Daddy yau nice na ta'bo sa ".


Husain kuwa cewa yayi "hankalin ki ya kwanta, Mardiyya yau kin bar mani tarihi a rayuwa ta, kizo ki zauna kiyi yanda kike so bazan 'kara cewa dake komai ba".


Shiru kawai Mardiyya tayi, tana kallon yanayin su, Husnah tashi tsaye tayi tace, "idan kina da bu'katar wani abun koda na cin mutumci nane zaki iya yi mani magana " kawai ta shige warta cikin d'akin ta.


Haka suka bar ta cikin falon a zaune, tun daga wannan lokacin Mardiyya ta dawo sashen ta, bata sake zuwa gurin da zasu had'u da Husnah ba, Husain kuwa ya kanzo ya tambaye ta abunda take bu'kata ya kawo mata amman babu wani sakin fuska kuma har yan zun da ake maganar sati biyu da faruwar wannan abun Daddy baya d'aga wayar Husain kuma ko gidan yaje Daddy baya kula sa.


Sai da akayi sati biyar Daddy ha'kura ya fara kula su, Mardiyya ce zaune tana kallo Husnah kuwa tana sanye da 'kanan kayan ta sai 'kamshi ke tashi kam badai 'kamshi ba, Husain kuwa fitowa yayi da kayan motsa jikin sa, yana zuwa kujerar da Husnah take zaune ya zauna akai, Husnah kuwa tashi, zaune tayi tace, "malam lafiyar ka kuwa? Zaka zo ka zauna mani akai na? ".


Kyaleta Husain yayi, Mardiyya tayi dariya ta ce, "ni kuwa tun ban fahimci miye kuke ciki ba, har nazo na fahimci komai ace watan ku bakwai da Aure amman kullum cikin fad'a kuke, ya kamata ku zauna lafiya ".


Husnah da Husain kuwa kamar basa gurin kawai Husnah ta tashi tsaye zata shiga cikin d'akin ta, ke nan sukaji saukar halbi tare da ihun Mardiyya, ai kuwa da gudu sukayo kanta sai jini ya fara zubar mata a gefen ciki, Husain da Husnah rud'ewa sukayi suna kiran Sunan ta, amman inah mutane ne kawai suka dirar masu, sanye da fuska ba'ka, da bindigogin su a hannun su, kawai suka ta'ka Bindigar su akan Husain da Husnah wadda ga baki d'aya suka shiga cikin tsananin tashin hankalin ganin yanda jikin Mardiyya ke jijjiga ga jini na zubar mata.



Kawai aka saita kan Husain suka halba, jin kake darammmmmmmmmm.......




*Comment and share*


_Kada ku manta yau biyu ne... _



*A GIDANTA NA GIRMA*



*BY NANA: KHADEEJATU*

*_UMMU IHSAN_*


*SADAUKAR WA GA :- DUK KANNIN MASOYA NA NABOYE DANA BAYYANE INA SONKU SOSAI SON FISABILILLAH*


*YA ALLAH KAJIKAN MAHAIFINA KAYI MASA RAHMA KA KYAUTATA MAKWANCIN SA SHIDA YAN UWA MUSULMI BAKI `DAYA.*


*YA ALLAH KA BAIWA MAMANA LAFIYA KA BAIWA DUK KANNIN WANDA BAIDA LAFIYA NA GIDA DANA ASIBITI ALLAH KA BASHI LAFIYA AMIN YA ALLAH*
*Godiya da jin jina a gareka masu comment da sharhi mai 'kara mani 'karfin gwiwa, kuyi hakuri kwana biyu ban samu amsa maku Comment din ku ba, amman na duba ina godiya sosai*

*Djamila Ali*
*NafseyAbraham*
*Mommy na*
*Halimatus sadiya*
*Maman nana*
*My takwara*
*Maman hafsa*
*Sarah*
*Maman Muhammad*

Da sauran mutanen gidan group din *A GIDANTA NA GIRMA*


*_Bismillahir Rahmanin Rahim_*

86~90


"kawai kaji saukar alburushin bindiga saitin Husain darammmm, Husnah kuwa fad'uwa tazo zatayi 'kasa cikin zafin nama Husain ya taro ta yana ihun kiran sunan ta, "Husnah! Husnah!! Husnah!!!, miyasa kika aikata irin haka a gare ni bayan kin fi kowa sanin bana son abu koda kwayar zaira ne na cutarwa ya sameki, dan Allah kada ki mutu kibar ni, nine nafi da cewa dana kare lafiyar ki, ba keba, Husnah dan Allah kada kiyi mani haka, idan babu ke atare dani bana iya rayuwa Husnah! ".

Husain kuka yakeyi harda hawayen sa yana gir giza Husnah wadda aka zo halbin Husain a kan sa, tayi saurin ture sa gefe saboda ita ce kawai ta lura da lokacin da za'ayi halbin kawai aka halbe ta a ka fad'ar ta, wanda yayi halbin kuwa cikin hanzari ya cire fuskar da yasaka, yana zarar ido, sauran ma duk suka cire abun, sukayo kansa suna fad'ar, " lallai jaga ka jawo wa kamka matsala waye yace maka ance ko rauni mubar ta tayi, bayan kasan da cewar aikata hakan a gareta tamkar rasa taka rayuwar ce".


Cikin tsananin tsoro yace yan zun ku ba zaku iya taimako na ba ne?.

Duk suka had'a baki gurin fad'ar, "to zamu iya taimakon ka Amman sai ka kashe wannan mutanen cewa da Husain wanda ya soma baiwa Husnah taimako gaggawa, suna juyowa a kan Husain suka ga yana 'ko'karin cire mata bulet din da yar askar dake hannun sa kawai suka zuba masa, ido.

Da gudu ya tashi ya shiga cikin d'akin Husnah yaje ya watse lokar kayan Husnah ya d'auko akwatin sa na taimakon gaggawa, ya dawo a rud'e shifa har yama manta da wata Mardiyya kan Husnah ya yo su kuwa duk suna tsaye suna kallon sa, cikin ikon Allah yayi kokari ya cire mata bulet din ya saka mata magani ya wanke gurin ga jini duk yayi kaca_kaca dashi har a fuskar sa, sannan ya gyara mata gurin ya saka cotton fa plaster yana gawa ya kama Husnah ya rungume wadda ko motsin batayi.

Mutanen ne sukayi ido a tsanin su, Husain ba tare da sanin saba suka daka masa bindiga a kan sa, a take jin sa da ganin sa suka d'auke sai jini, kawai ya fad'i 'kasa a some, su kuwa d'aukar Husnah sukayi suka tafi da ita.

Kiran wayar Husain Yaya Yusuf yakeyi wanda suke a zazzaune kusa da Daddy wanda dukan su sun rasa mike faruwa ne, dasu suka rasa natsuwar su, duka Anty Zarah kuwa da fad'uwar gaba ta kwana sai wani irin zazzabi da ya rufe ta, Yaya Yusuf shima ya rasa miye yasaka baya cikin natsuwar sa, dole ne ya d'auko su Anty Zarah suka dawo gida gurin su Ummey, abun mamaki duk gidan haka suka tashi cikin wannan halin, Shaheed ne ya shigo ido tsakiyar kai ya ce, "Daddy nayi mummunan mafalki akan su Husnah da Husain kuma gashi ina ta kiran wayar su su duka ba'a d'aga wa".

Ummey tace, "ni kaina nayi ta kiran wayar Husnah da Husain harda Mardiyya amman ba bu wanda ya d'aga daga cikin su, na rasa a ina suka shiga ne duk da wayar Husnah tana hannun Husain ya'ki bata Amman idan an kira yana bata tayi wayar ya tafi da wayar, Husain duk abun sa kira d'aya zai biyo ka yaji abunda ke faruwa, nikam dai hankali na ya kasa kwanciya".


Daddy yace, "ba wannan ba ku tashi muje gidan mu ga abunda ke faruwa indai ba suna can ba suna aikata halin su, yara kamar masu zuciyar dutse kuyi wata bakwai a gida d'aya amman hali bai sauya ba".

Babu mai wani 'karfi a cikin su haka suka nufi motocin su guda biyu suka shiga suka d'auki hanyar gidan su Husnah, tun a bakin get suka fara shiga far gaba saboda ganin get d'in a bud'e , tsayawa sukayi Daddy ya kira police, ai kuwa babu wani 'bata lokaci suka iso saboda sun san indai Daddy ne ya kira su kira mai mahimmaci ne, kuma harda CID ya kira duk suka iso, jami'an tsaron sune a gaba su Daddy na biye dasu, masu gadin gidan ne kwance jikin jini ai kuwa a take kowa ya saka salati Anisah kuwa tuni ta fad'i gurin a some, d'aukar ta Shaheed ya yi ya kaita gefen flower, ya kwantar ya ce, "Suhailah ku tsaya a tare da ita", gyada masa kai kawai sukeyi suna kuka.


Haka get din na biyu babu kowa a gurin, cikin d'akin tsakiyar suka shiga wanda shine a bud'e kuma da alama akwai abunda ya faru saboda hanyar da bulet ya shiga, aikuwa atake suka 'kara shiga cikin rud'ewa, suna shiga ciki falon duk sukayi mutuwar tsaye jami'an ne kawai suka 'karasa gurin da sauri ai kuwa kiran motar asibiti sukayi kan kace kwabo har sun iso, su Yaya Yusuf da Shaheed da Zarah da Ummey kaka kawai sukeyi dan su kan yanda suka ga jini yana zuba a kan Husain sun san jinin sa ya 'kare yama mutu, haka suka ga yanda Mardiyya ta zama lallai kam duk an kashe su, kowa ya rud'e harda jami'an tsaron.


Saboda tsabar rud'ewa duk sun manta da Husnah har sai da wani CID ya ce, "su biyu ne kawai a gidan ko akwai cikon na ukku? "

Ummey ta ce, "Husnah? ".

Atake hankalin kowa ya dawo to ina ita Husnar take ne?.

A take jami'an suka ba zama bincike amman basu gano Husnah ba, wani jami'i ne ya ce, "kudubo nan da alama sun d'auke ta sun tafi da ita saboda kayan aikin da akayi amfani dasu kuma ku dubi jikin yaron ku, ku gani yayi mata aiki ne dan ga bulet din da ya cire mata nan, amman kuma suka bugesa suka d'auke ta bayan ya gama yi mata aikin gurin".

Faduwa Anty Zarah tayi a jikin Yaya Yusuf wanda idon sa yayi jaa saboda tsananin tashin hankalin da suke cikin sa, d'aukar ta yayi suma su Husain aka d'auke su aka saka su, Ambulance su ukku aka nufi asibiti dasu, gidan kuwa bin cike aka shiga yi ansamu bulet biyu, da dai wasu abubuwan da jami'an tsaro ke nema.


Taimakon gaggawa aka basu, tuni Anty Zarah ta falka, amman kuka kawai takeyi sai lallashin ta akeyi, da dai likita yaga zata jawo wa kanta wata matsalar musamman cikin dake jikin ta, kawai sukeyi mata, allurar bacci.


Husain ma ya dawo hayyacin sa cikin sa'a sai dai kuma anyi masa allurar bacci shima, ita kuwa Mardiyya anyi asarar cikin dake jikin ta dan ya mutu cs ma sukayi mata suka cire d'an itama da ket aka samu ta samu kanta.


Su Daddy da Ummey da Yaya Yusuf da Shaheed tunanin sukeyi taya akayi hakan ta faru ne, waye yayi masu wannan d'an yen aikin? Sun rasa gane wa, jami'an tsaron kuwa CID sune suke tsare da Husain.


Can cikin dare Husain ya falka, cike da tsoro a zabure ya falka yana fad'ar mi miye mukayi maku ne? Husnah dan Allah kada ki mutu kibar ni, su Yaya Yusuf da CID nan su biyu sukayo kansa suna kallon sa, likita ne ya shigo da sauri saboda kiran da akayi masa, yana zuwa ya fara duba Husain, ya ce, dashi "ka kwantar da hankalin ka, kabi komai a sannu gudun bugawar zuciyar ka, am kana jin wani abun ne? Ko kuwa zakayi wata lalurar ne? ".


Kallon su Husain yakeyi kamar wasu ba'kin halitta, zuwa can idon sa ya sauka akan Yaya Yusuf, Husain ya ce, "Yaya Yusuf sun kashe su ko!?.


Gir giza masa kai yayi yace, "basu kashe kowa ba, duk suna a raye, amman kuma su waye su? ".


Husain yace, "Yaya Yusuf ina ji a jiki na Husnah tana cikin wani hali dan Allah ka sanar dani tana ina ne? ".

Yaya Yusuf ne zaiyi magana CID yace, ko zaka tashi kasha ruwan tea ne sai kayi sallah ko aboki na? ".


Tunawa da bayi sallah ba shine ya saka Husain tashi suka raka shi har bayin yana tafe yana d'in girsa, jin yakeyi kamar kansa zai rabe biyu saboda tsabar buguwa.



Tunda suka zai iya yin komai da kansa sai suka fito suka baro sa ya 'karasa.


Zaune suke suna jiran Husain ya fito amman shiru, har kusan minti talatin kawai CID nan yace zaman yayi yawa ka dubu sa mana".


Yaya Yusuf ne ya shiga ya dubu Husain amman babu Husain babu labarin sa si wani gurin, da yaga an fasa an shigo ko an fit, ai kuwa Yaya Yusuf ya kwatsa uban ihu sai ga bayi ya cika da jami'an tsaro da mutane, dur kushewa 'kasa yayi ya dafe kai ys rasa miye ma zai iya aikata wa a halin yan zun.


Jami'an tsaron kuwa cikin tsananin tashin hankalin suka rufe asibitin babu shiga babu fita.


Koda aka sanar dasu Daddy kuwa kasa cewa komai sukayi sai salati.

Ummey kuwa

Please Login or Register in order to submit comment