Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kinji "yata.
Husnah tace, "zan taro mutane ne da sukeyi ta kiran"

Yace, "ok babu damuwa kuma kada ki tafi har sai munyi sallama dake kinji ko? ".


murmushi 'kawai Husnah tayi suka fita mutane ne ta hango kusan su goma a jikin motocin biyu suna dube_dube Husnah ta d'auki wayar ta takira ai kuwa aka da d'aga hannu ta d'aga masu cikin sauri suka iso inda take a tsaye tace masu, "muje ko? ".


Bin bayan ta sukayi cikin hanzari amman kuma ita Husnah bata iya sauri ba, duk suka ka kagara su kai kawai abokin fadan Husnah yace, "dallah malama mu ki daina yi muna wannan tafiyar iskancin kawai dai Husnah tace, "malam zaka iya tafiyar ka ka tambayi wani".


Har ya taso zaiyi masifa kawai aka dakatar dashi har kofar d'akin ta kaisu tayi tsayuwar ta sai da suka shige ita kuma Husnah ta jiyo ranta a bace tayi tafiyar ta ta d'auki motar ta tayi gida.


Duk suna shiga wasu suka fashe da kuka, abokin fadan Husnah kuwa a bakin gadon ya zauna ya kama hannun mahaifin sa ya rike idon sa yayi ja sai jijiyar jikin sa ke halbawa.


Hajiyar ma ido tsakiyar kai ta matso ta kama hannun sa tace, "ya jikin naka!?".


Yace, " kada ku damu ai sai da na samu sau'ki sannan ta kiraku amman da alokacin ne kuka ga halin da nake ciki da ba zaku samu damar yin wannan maganar ba a ina kuka baro mani "yata ne? "

Kallon kallo aka somayi a tsakiyar su kowa tunanin yakeyi ina take ne?.

Yarinyar tace sai da nabi bayan ta cikin fushi ta shiga motar bata ma kalleni ba.

Asha nasan ba aikin kowa bane face Husain nasan kaine baka jituwa da mutane, Husain dan Allah kada ka bar yarinyar da ta ceci mahaifin ka ta shiga cikin wani hali, dan baka san irin taimakon da tayi maka bane da an rutsa da karin kwana da tuni na mutu kun rasa ni, gashi ko sunan ta bata sanar dani ba.


Duk kowa yaji yana bukatar ganin Husnah su zauna da ita ba kamar Hajiya.

Haka d'akin yadawi cikin jimami ga mahaifin su yadamu da zan cen yarinyar da ta cece shi, gashi babu wanda yasan sunan ta.


Husnah kuwa tana isa gidan tayi parking ta fito a falon gidan ta samu su Zubaidah kowa daga cikin su cike da damuwa sai a lokacin ne Husnah ta tuno da maganar tafiyar da zasuyi kawai Husnah ta fara matso hawayen karya ta soma din gishi ta dafe kai tace, "mommy Accident ne fa nayi gashi duk naji ciwo kuma gashi naga ranki a bace".


Ganin jini a jikin Husnah duk sai suka yarda kawai da sauri sukayo kanta Husnah sai ta 'kara narkewa.

A cikin d'akin ta Zubaidah ta rikata, ta rakata har toilet, Zubaidah na fita Husnah tayi murmushi tayo wanka ta d'auko wani bandeji da ta ta'ba ajiyewa ta nad'e gefen cikin ta dashi harda su shafa wani abu kamar jini haka tayi a kafar ta harda su dan jike bandejin alamar ruwan wanka ne ya taba gurin.


Zuwa tayi ta zauna a bakin gado tana cije baki, shi kuwa Tk duk tausayin Husnah ya kamashi, Zubaidah sai tambayar ta takeyi miye sanadiyar wannan raunin.

amman Husnah sai kukan karya takeyi masu cikin masifa Tk yace, "dan Allah ki barta har tasamu sau'ki sai muyi mata tambayar amman yan zun mu barta ta futa".


Husnah kuwa suna fita tace.........


*Comment and share*

*A GIDANTA NA GIRMA*


*BY NANA: KHADEEJATU*

*_UMMU IHSAN_*


*SADAUKAR WA GA :- DUK KANNIN MASOYA NA NABOYE DANA BAYYANE INA SONKU SOSAI SON FISABILILLAH*


*YA ALLAH KAJIKAN MAHAIFINA KAYI MASA RAHMA KA KYAUTATA MAKWANCIN SA SHIDA YAN UWA MUSULMI BAKI `DAYA.*


*Alhamdulillah Allah muna godiya a gareka daka nuna muna sallah lafiya ya Allah ka karbi ibadun mu ka yafe muna kura kuren mu amin*


*Ina yiwa kowa barka da sallah Allah ya mai_maita muna amin*


*_Bismillahir Rahmanin Rahim_*

26~30

Husnah tace, "badai bariki ba? Ai wallahi nafiku iya bariki nida nataso nasamu kaina a cikin sa, muzuba zuwa nida ku" kawai tayi kyabci da biki kaji sautin nan 'kat...

A can garin kuwa tun bayan barin su Husnah garin Marka ta shiga bokaye ita ala dole sai taga bayan su Husnah da Zarah.

Amman kuma duk inda taje sukan sanar da ita cewar ai duk rayuwar yaran ta tarwatse duk kayan dakinta sun bata a gurin bokaye,

Wannan farin cikin dashi take kwana dashi take tashi, abunda Marka bata sani ba shine "yarta indo biyar maza takeyi d'anta namiji kuwa duk unguwar kowa yasan halin sa da halin bera wato mugun 'barawo ne na agwagi da kaji da tumaki da awaki sam Marka bata san mike faruwa danata yaran ba, tana can gurin lalata rayuwar "ya"yan wasu.

Dan ita basa nuna mata halin su idan kuma wani ya yarda ya sanar da ita halin su har suka gane sa to shi kam tashi ta samesa dan wallahi idan aka fara yiwa mutum sata harda coffin gidan sa bazai tsira ba, ballema mutum yayi tuwo a gidan sa, "yarta d'ayar kuwa gulma har ta siyarwa akwai a gurin ta sam itace uwar gulma ce a unguwar, fada har na mugun abu take had'awa, amman ita ko uwar ta bata ragawa ba ballema mahaifin su, a take ne, take haddasa masu fitina, gashi Marka sam bata yarda da maganar kowa sai ta yaran ta duk abunda suka fada dai daine a gurin ta.

Baban su Husnah kuwa yau satin sa d'aya da zuwa garin su yayan sa wanda ya d'auki shekaru kusan ishirin rabon sa da garin, to a wannan lokacin ne dai yaji duk hankalin sa ya tafi gurin yan uwan sa amman kuma kash bakar wahala kawai ya shawo dan an sanar masa sunkai shekaru sha biyar rabon su da garin da suke saboda ma'akatan gwamnati ne kullum cikin sauya gurin aiki suke, gashi yanzun dai da alama sunyi ritaya, saboda tsufa sai dai yaran su, sai kuma yaji bakin cikin sa ya koma lunkuwa, ga rashin sanin inda zai samu dan uwan sa koda mutum d'aya ne, ballema ace ya samu ganin su Husnah dan yanzun yakai kusan shekaru biyar yana mafalki dasu da mahaifiyar su, yanzun ne yasamu damar fita nemo su, amman ya makara.


Gidan sa ya dawo cikin damuwa, Marka kuwa babu ruwanta da damuwar ta ballema ta tambayesa shima baiyi gigin sanar da ita inda ya tafi ba.

ita kuwa Zarah tun bayan rabuwar ta Husnah sam ts sake dawowa so silent magana bata wani damuwar ta, alokacin da goggo Amina tazo sanar dasu cewar taje gidan su Husnah ta d'auko ta, tun a gurin mutanen unguwar ta samu labarin ai itace ta aiko aka d'aukar mata Husnah, mutane na tambayar ta ya Husnah take, gidan wata 'kawar maman su Husnah taje ta bugo mata ciki tace, "ni kuwa Larai yaran nan da suka d'auki Husnah hauka ce suka zo maku da ita ko!? ".

Larai tace, "yo hauka mana ke miyasa da zaki aiko da masu d'aukar Husnah baki aiko masu hankali ba ko kuma kizo da kanki ba? ".

Anan ne Larai ta labartawa goggo duk abunda yafaru tabbas ta shiga kaduwa amman sai ta boye, haka data fito daga garin bata zarce ko ina ba sai gidan yayan su babba ta labar ta masu komai tana kuka duk idon ya kumbura, sosai hankalin kowa ya tashi a gurin shine aka yanke shawarar kada abari Zarah ra sani amman inaa sun makaro taji komai a yanzu hakama daskare take ta some.

Hankalin su ne yayi munmunan tashi wanda tun daga wannan ranar Zarah ta daina wal wala.

Sun tambayi gogg Amina akan cewar taya yaya akayi wasu suka d'auki Husnah da sunan ta?.

Wannan shine damuwar ta itama dan har yan zun bata san ko su waye ba.

Zarah kam ta zama wata irin mace miskila ta karshe idan kaji tana magana tofa abun babba ne, haka rayuwar ta ta dawo kullum tana d'auke da photon su ita da Husnah da maman ku gashi kullum tana mafalkin Husnah na miko mata hannu akan ta janyo ta a jikin ta amman kuma sunyi nesa da junan su sosai.

A haka har kannen mahaifin su ya had'a Zarah da dan gidan ogan sa aure tunda duk wanda ya fito da sunan zai Aure ts, takan sanar da mutum cewar sai ranar da taga Husnah ko zata iya Aure ada sun saka mata ido amman kuma daga baya suka sauya shawara, badan Zarah tana son Auren ba aka had'a ta da dan gidan ogan su baffah Isah, kuma shima yana ganin Zarah yace tayi masa amman sai kannen sa ya ganta idan yace tayi tofa lallai ne ita yake so.

Aikuwa kannen nasa ma baya 'kasar amman sai da yadawo yazo ganin Zarah, cikin ikon Allah a take yaji Zarah ta kwanta masa shi dai kawai ayi Auren da sauri ma, ita kuwa Zarah ta sanar dashi yayi hakuri amman sai ya dawo yana lallashin ta har suka sabu da juna ita da kannen nasa sam baya narin tayi zaune ita d'aya, sosai suke kula da ita dan sun san damuwar ta kuma mijin nata ya kwashe photon da yake saka ta damuwa tayi neman sa har ta gaji, wannan shawarar kannen sa ne.

Haka dai rayuwar Zarah take tafiya har Allah ya bata haihuwar ya mace mijin kuwa ya saka mata sunan Husnah a gaskiya ba Zarah ba har su baffah sunji dad'in wannan karamchin, kuma aikin kannen mijin Zarah ne.

Mundawo asibity tun suna sa ran Husnah ta dawo har suka cire tsammani ita kuwa Hajiyar har gurin ma'aikatan hospital din taje neman Husnah amman bata sameta ba, dole suka hakura har aka sallame su.


Husain kuwa dad'in rashin ganin Husnah yayi, ta wani ban garen zuciyar sa, ta wani ban garen kuwa yaji haushin rashin ganin ta kodan da mahaifin sa da kuma rashin kunyar da tayi masa dan yadau alkawarin idan ya samu damar sake ganin ta sai ta yabawa aya za'kin ta.


Husnah kuwa kwananta tara ta samu sau'ki a cewar ta, kuma babu wanda ya gano cewar karya takeyi.

Zaune take tana buga game a wayar ta Zubaidah ce ta shigo ita da wasu maza suna rungume da juna, kallo d'aya Husnah tayi masu ta tashi zata bar gurin ta dawo cikin d'akin ta, mutanen d'aya yace, "ke ''yar mu zoki nemo mani abunda zanci dan mun kwaso yuwa da gajiya ga zafin rana".

Yana gama fad'ar haka ya fad'a akan kujerar da Husnah ta tashi.

Baki Husnah ta turo gaba ta juyo tana fad'ar, "a gaskiya gidan bamu dafa komai ba, kuma ni bance a dafa wani abun ba saboda a iya sani na mommy bata cin abinci idan ta dawo gida wannan shine 'ka idan ta, kaga kuwa ba zaku samu damar cin komai ba".

Cike da masifa abokin tafiyar su yasoma fad'ar, "ke haka katuwar mace da ke gaki da sura son kowa amman ace baki iya dafa abinci ba, a gaskiya kinyi asara babba".

Cike da tsanar mutanen Husnah tace, "yo kai miye naka ne a ciki tunda ba akan ka nake zaune ba,da har zaka wani damu da rashin iya abinci na, ai dai bamuda wata alaka da kai malam dan haka ka shafa mani lafi.... Kafin Husnah ta 'karasa lafiya tuni an wanke ta da mugun mari wanda a cikin sakan biyar ta tuno da irin sa, a lokacin da Zubaidah ta mareta irin wannan kuma a gaban saurayin ta har ta saka mata sharudda masu tsauri yau shine aka mai_maita.

Zubaidah cikin hasala har jikin ta na mazari tace, "Husnah kanki d'aya kuwa? Kin san waye shi kuwa a garin nan? Rashin kunyar da na haneki ashe dai tana nan ko,? Babbar magana Husnah kin kusa d'ebo ruwan dafa kanki, tunda har zaki iya yiwa senator rashin kunya kuma a gidan nan babu mai rabaki dashi".

Dafe kunci Husnah tayi, kawai ta fashe da kuka kamar ranta zai fita, saboda takaici.

Daga can bayan su, suka jiyo muryar Tk yana fad'ar, "tabbas Zubaidah dan bariki baida amana da alkhawari tunda har zaki iya cin amanata ki d'auki budurwa ta ki baiwa wani bayan kin san tawa ce, kuma harda su dukan ta, dan kinga bana kusa daku to anyi walkiya na gano ki ".

Kawai yazo har inda suke yasa hannun sa ya janye Husnah suka fita suka bar falon motar sa ya saka ta, ya figi motar sai wata park ya ajiye ta, ita dai Husnah har yanzun kukan takeyi dan yanzu kam ta mallaki hankalin kanta tasan tozarci.



Kallon Husnah yakeyi ya saka hannun sa a aljihun rigar za, ya zaro wani dan akwati, ya bud'e ya d'auko zobe mai kyau ya kama hannun Husnah zai saka mata, da sauri Husnah tace, "wato kai burin ka ya cika ko? Ina cikin wannan halin ne zaka saka mani zobe bayan nasan cikin farin ciki ake saka zobe".


Murmushi ya sakar mata wanda Husnah takejin kamar ta bushe da dariya saboda bai iyaba kamar wanda ya mere baki cikin fushi.


Yace mata, "kiyi hakuri Baby daman dan na faran ta maki raine yasaka ni zan saka maki zoben badan wani abu ba".


Kauda kai Husnah tayi tace, "kaina ciwo yakeyi kamar ya rabe biyu ka maidani gida in kwanta ko zai daina".


Cikin rawar jikin da tsoro yace, "ashha tashi na kaiki hospital a duba mani ke".


Tashi Husnah tayi suka nufi hospital sosai aka duba ta aka bata magani, ya d'auke ya kaita super market tayo siyayya, tace masa ita bata son komai, ai kuwa da kansa ya shiga ya kwaso mata kayan ma'kulashe gurare ya kaita yayo mata siyayya haka suka dawo gida shi be shiga ciki ba ita ce kawai ta shiga ciki da sauri Zubaidah tace, "ina fatan kin faran ta masa rai ko? Dan nasan halin Tk idan yayi fushi sai yaji macce a jikin sa, yake sauka".



Husnah bata ce da ita komai ba tunda har yanzun wannan mazan su biyu suna nan zaune a kusa da ita.


D'akin ta kawai ta wuce, masu aikin gidan ne suka soma shigo da kayan da Tk ya siyo wa Husnah, da sauri Zubaidah ta fara dubawa kayane masu yawa kamar bai san zafin kud'i ba, magani taci karo dashi cikin farin ciki Zubaidah tace, "wow Husnah an girma lallai dole Tk yayo maki uwar tsaraba tunda ya mallaki komai naki Husnah, a gaskiya bariki tayi tunda gashi Husnah abun bai sauya mata ba, har bayan barin budurcin ta a gareta".



Mutanen yace, "ai kuwa da zaki bani ita nima da nayi mata tawa bajin tar tunda ita sabuwa ce ni ina so".


Da sauri Zubaidah ta rufe masa baki tace, "Husnah bazata taba yarda ko inuwa d'aya ku had'a da ita ba, saboda ita bata kula kowa sai Tk koshi ba sosai take kulasa ba, barikin Husnah ya zarta tunanin mai tunani ku dai mu chanza zance kawai ".



Husnah kuwa ta fito ke nan zata d'auki maganin ta saboda kanta ya matsa mata tajiyo duk abunda su Zubaidah suke fad'a kawai sai ta koma taci gaba da kukan ta, a haka Zubaidah ta sameta, aikuwa da ringa lallaba ta, taje bayi ta had'a mata ruwan zafi ta rakata har bayin ta fito wai ta gasa jikin ta.



Husnah kuwa murmushi tayi wanda yafi kuka ciwo, haka tayi wanka, ta fito ta samu Zubaidah ta kawo mata ruwan tea, kin sha tayi maganin dai tasha ta koma ta kwanta.


Tun daga wannan ranar Husnah ra sake zama wata irin shu'uma sam bata fira da Zubaidah kuma koda Zubaidah ta tambayi miye matsala takan ce mata akwai abunda ta hango gurin Tk shine take son amsa kuma abun mugun tsada ne dashi yace baya iya mallaka wa kowa abun nan kuma ita bata son yasan tana son abun dan yace zai iya rabuwa da kowa akan abun ".




Zubaidah ta kasa gane inda zancen Husnah ya dosa amman tasan ko miye yanada muhimmanci sosai a rayuwa tunda Husnah taso hakan.


Zubaidah tace, "Husnah kada ki d'auki abunda ya fi karfin ki kada ki yarda ki rabu da Tk batare da kin anshi abu mai mahimmaci a garesa ba tunda kinga yanzun ya anshi budurcin ki, sai kinyi da gaske dan kinaga tun ranar bai sake zuwa ba ko waya na kira sa baya d'aga wa daga karshe ma bana samun sa, yau kusan wata d'aya ke nan ".




Murmushi Husnah tayi tana 'kara kallon Zubaidah tace, "mommy daman haka ne idan namijin bariki ya gama da maccen bariki sai ya juya mata baya, sai dai ya nemi wata, ko ita ta nemi wani? "


Zubaidah tace, "itafa bariki haka take kamar wainar fulawa take lallaba ta akeyi, saboda idan mutum ya tafi da garaje zata lalace masa ne".


Dariya Husnah tayi tace, "hum mommy na yarda da hakan nima zan afka sosai a cikin ta, saboda ina son ganin farin cikin ki mommy ".




Da sauri Zubaidah ta rungume Husnah harda hawayen farin ciki Husnah zata cika mata burin ta, zuwa can Husnah tace, "amman bazan iya kula raga jabul ba dan inada aji nafi karfin irin wanda kike kulawa saboda haka koda wani yayi maki magana kice masa ya nemeni da kansa dan nice dai_dai da zancen"



Sosai Zubaidah ke jin dad'in wannan maganar ta Husnah, Husnah tayi mata sallama taje ta kwanta, ta kama dariya harda rike ciki tace wayyo Allah biriki ashe dai Zubaidah mommy baki iya duniyan cin ba har nafiki iyawa nida na taso na sameki kinayi, shi kuma Tk taya zaki nemesa ki samu bayan nayi masa nasa tuggun na had'a sa da iyayen sa harda matar sa, kinga kuwa Husnah tafi mommy iya bariki".


Husain dan Allah number da yarinyar nan ta kiraka ita zaka bamu.


Da sauri Husain yace, "ya salaam kama tuno mani yaya ida zamu sameta ba karya ta, tunda tayi mani rashin kunya".



Kai nifa ba masifar ka na nema ba ka duba yanda mahaifan mu suka damu da rashin ganin ta ko godiya muyi mata".



Bin ciken wayar ya soma yi amman babu wata bakuwar number, shima yayan nasa ya ansa ya duba a hankali bai samu ba, duk sai sukayi shiru suka ajiye wayar suna nazarin yaya akayi number ta fita ne, tunda basa goge kiran da akayi masu?.



Husain yace, "Anisah eh lallai Anisah babu ko shakka itace ke yawan d'aukar wayar mutum tayi waya idan baya kusa".


Ai kuwa da sauri suka nufi cikin falon suna kwala kiran, "Anisah! Anisah!! Ai kuwa da kaduwa ta taso tazo gurin su ta durkusa, jikin ta na rawa, Husain cikin 'bacin Rai yace, "uban waye yasaka ki d'auki waya ta alokacin da muke jinyar Daddy!? ".



Kuka Anisah ta fashe dashi jikin ta na rawa tace, "wallahi waya ta ce ban gani ba shine naga wayar ka na charge na d'auka na kira tawa, sai nagano ta, to ina gudun ka gani kayi fad'a sai na goge kiran da nayi nagoge harda kiran wasu numbobi da basuda suna Allah banyi zaton zaka gane ba amman dan Allah kayi hakuri ".




wani uban shuri yayi da ita wanda sai da tayi mul mula ukku zuwa hud'u harda fitsari sai da ta saki bata sani ba, belt kawai ya ciro yayi ta lafta mata, da ket aka samu aka anshe ta, ita kuwa Hajiyar da Alhajin duk sai daga baya suka bada hakuri, yayan kuwa cewa yakeyi, "'kara mata munafukar banza"


Sauran mutanen gurin duk suka sha jinin jikin su, Baby kuwa kuka takeyi da gudu tazo ta rungume Husain wanda ya saki belt din saboda ita"


D'aukar ta yayi suka fita daga cikin gidan sukayi gurin yawo tun daga wannan ranar Husain bai sake wani farin ciki ba, shidai wannan yarinyar kawai yake son gani suyi fad'an masifa da ita.


Yau kimanin wata bakwai ke nan rabon su da ganin dariyar Husain duk dashi ba ma'abuci fira bane, baya wani dariya a matsayin sa na Doctor Husain, zaune yake shi d'aya da wowar sa daga gurin aiki ke nan yayan sa ne ya samesa a gurin yayi zurfi cikin tunani kannen sa Shaheed Yana biye dashi rike da hannun Baby da jakar school din ta a hannun ta.


Zama sukayi a gefen sa suka saka shi a tsakiyar su Baby kuwa saman jikin sa haye tace, "uncle yauwa maganar da nace idan ka dawo zan fad'a maka ko? "


Sai alokacin ne ya dawo hayyacin sa, ya gaida yayan sa, Shaheed kuwa da Baby suka gaida shi sukayi masa ya aiki.

Ya amsa masu, Baby tace "Uncle kana jina ko? "


Shafa kanta yayi yace, "ina jikin yarinya ta".


Sai da tayi gyaran murya tace, "Uncle kace kowa ya barin nayi magana"


Dariya duk sukayi mata dukan su hardai yanda take gyaran murya.

Tace, "Uncle wayar granny tana hannun anty? Anty wadda takai granny asibity? Kuma wayar tanayi amman iyakar wayar ta kawo haske bata komai duk tarar ratse".


Wani irin farin ciki ne ya ziyar cesu da sauri Shaheed ya soma kira kafin kowa ya kira, sunyi kira ya kai sau goma babu amsa zuwa can Husain ya kira da wayar sa kamar almara wayar ta shiga duk suka saki baki suna kallon sa ga farin ciki ya baibaye su.



Husnah kuwa tana fitowa daga cikin falon kawai ta wuce gurin way drop zata d'auki maganin ta saboda yau cikin ta ne ke ciwo wayar bawan Allah nan ne tayi tozali da ita kawai ta tuno da abunda ya faru a ranar shine ta kunna wayar ta 'kara bin cikawa ta gani ko zata samu number wani daga cikin iyalen sa, kawai wayar kamar abun jira ta soma ringing, cike da mamaki Husnah take kallon wayar.


Sai da akayi kira biyar ta d'aga tace......




*Comment and share*


*A GIDANTA NA GIRMA*


*BY NANA: KHADEEJATU*

*_UMMU IHSAN_*


*SADAUKAR WA GA :- DUK KANNIN MASOYA NA NABOYE DANA BAYYANE INA SONKU SOSAI SON FISABILILLAH*


*YA ALLAH KAJIKAN MAHAIFINA KAYI MASA RAHMA KA KYAUTATA MAKWANCIN SA SHIDA YAN UWA MUSULMI BAKI `DAYA.*


*Alhamdulillah Allah muna godiya a gareka daka nuna muna sallah lafiya ya Allah ka karbi ibadun mu ka yafe muna kura kuren mu amin*


*Ina yiwa kowa barka da sallah Allah ya mai_maita muna amin*


*_Bismillahir Rahmanin Rahim_*

31~35


Husnah tace, "wannan daga ji bakauye ne na karshe tunda daga bud'e waya har kayi kira biyar ba 'a daga ba ai kasan mutum yana wani aikin ne".

Husain cikin fushi yace, "to barauniya ai sai ki dawowa mutane da wayar su tunda ba gadon ta gareki ba, shine kika wani za'kewa kina yiwa mutane fad'a kamar wanda kika haifa".

Dariya Husnah tayi tace, "good job lallai ashe dai ta tabbata ina magana da mahaukaci ne to ka iya bakin ka ko kuma na yanke halshen ka".

Husain yace, "nikuma sai yanzun ne nagane cewar babbar karya nake fad'a da ita, to kisani sai na yanke kafar ki kuma sai na zubar maki da hakori duka inga ta inda karya zatayi magana da kuma cizon mutane! ".

Husnah tace, "ja jiki kanzo bani da ruwan ji'ka ka, ballema kayi ban kama".

Husain yayi dariyar keta yace, "muzuba mugani ni dake kuma sai kin dawo da wayar da kika sace".

Shaheed ne yayi saurin amsar wayar yace, "sorry yar uwata dan Allah ku dai na irin haka, ni suna na Shaheed munyi ta neman ki bamu sameki ba sai yau ga yayan mu babba kuyi magana dan Allah kiyi ha'kuri ki saurare mu"

Husain yace, "miye na wani bata ha'kuri kawai kace mata ta dawo da

Please Login or Register in order to submit comment