Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gane ki ba, kawai dai yau ki kasan ce tare dani muyi firar mu ko? ".



Yarinyar dakewa tayi dan tsawar da Husain ya doka wa Husnah, duk sun fir gita da ita.


Husnah kuwa lura da kallon da Husain ke jifan ta da shine ya saka ta fad'ar, "nikam na tsani yawan shiga cikin mutane masu yawan surutu kawai aje a fasawa mutum dodon kunne a kaisa a baro, shi mutum idan yasan iska ya kad'a to mi zai saka shi shiga gurin mutane masu natsuwa? , ke Baby zo mubar gurin nan muje cikin d'akin can muyi firar mu".



Tashi Husnah tayi, ta ja hannun Babyn suka bar gurin, ai kuwa kallon tsana kawai Husain ke jifan ta dashi gashi ta sakar masa magana Ummey ta galla masa harara, ta hana shi ya d'auki wani mataki, duk sai yaji ya 'kara tsanar Husnah.



Yaya Yusuf ya ce, "dan Allah Husain kada ka hawa kanka raini a gurin yarinyar nan, kana jifa sai da ta rama abun da kayi mata ".



Share sa Husain yayi sai cika yake yana batsewa, Shaheed ya ce, "Hajiya Auren nan fa ya fasu ba'ayi sa ba, acewar wani aboki na, amman kuma ita mahaifiyar Husnah tana kwance bata da lafiya dan yau tun safe aka kaita asibiti, hawan jinin ta ya taso, yan zun yaya ya kama ta ayi ne? "



Ummey ta ce, "Ajiye wannan maganar Shaheed bari har Daddyn ku ya dawo, nasan zaiyi magana akai cikin hanciyar hankali, kai kuma Husain nadawo kanka, ka kiyaye ni fa! , kai wai ma, tun da ka gama ginin gidan ka, ka saka komai, tun shekaru biyu da suka wuce, to yaushe ne zaka kawo mani, matar da zaka Aura dan son nakeyi naga naka jikokin ga Shaheed nan cikin satin nan zamuje mu kai kud'in hidimar bikin sa, amman kai 'katon banza, kana nan kana ta kurawa 'kannen ka, to kasani, daga yanzun zan matsawa mahaifin ka, ayi gaggawar matsa maka ka fito da matar Aure haka nan! ".



Zufa ce, take zubo wa Husain ta ko'ina, amman sai gun_guni yakeyi, zuwa can ya ce, "Ummey nifa har yanzun ban samu budurwa ba, duk yan matan yan zun basu da hankali ".



Dariya kawai suka sanya masa, Hajiyar kuwa tace, "zakayi bayani ne Husain kwanan nan".

Haka dai su yini Husnah sai 'karfe goma sha biyu tasha shayi da biredi tace shine kawai take ra'ayin ci.



Daddy na dawo wa Hajiyar ta sanar dashi halin da ake ciki, a take ya kira Husnah yace, ta shirya yau zasu je gidan su.


Zufa ce Husnah take zubo mata, sai yan zun ne ta tuno da Auren da aka shirya yi mata, to miyasa Daddy yace sai sunje gidan su cikin tsakiyar rana, ita kam taga ta kanta.


Babu yan da Husnah ta iya haka ta shirya suka nufi gidan batare da tasan dalilin zuwan nasu ba.



Suna shiga cikin gidan zuciyar Husnah kamar ta fashe saboda far gaba, suna yin parking suka fito dukan su, Husnah kuwa cikin sanyin jiki take takawa, har suka shiga cikin falon gidan suna rafka, sallama amman basu ji a anmsa masu ba, Husnah dai tana baya ita d'aya kuma tasan daman babu wanda zai iya amsawa, acikin tawagar Mommy, sannan kuma ai taga ba'kin motoci harda wanda ta sani, da wanda bata sani ba.



Zazzaune suka sami mutane maza da mata dukan su babu mai shigar mutumci, a cikin su, Husain jin yakeyi kamar ya kashe su, saboda tsabar takaicin da yakeji nasu.



Zubaidah ce kwance sai fifita akeyi mata, Husnah na d'aga idon ta, kawai ta hango Zubaidah a kwance duk ta rame tayi ba'ki kamar ba Mommy yar gayun nan ba.


Da gudu Husnah tayi kanta tana kiran "mommy! Mommy!! Miya sameki ne, na shiga ukku na ni Husnah mike shirin faruwa dani ne Mommy please kada kiyi Mano haka, bani son ki mutu kibar ni, please mommy kiyi hakuri na tuba, nadawo gareki! ".



Kawai Husnah ta fashe da kuka sai tattaba jikin Zubaidah takeyi da yayi mugun zafi, bud'e ido Zubaidah tayi a hankali idon ta ya sauka akan Husnah da take ta zubar da hawaye duk ta rud'e.


Tashi zaune Zubaidah tayi da ket, ta ce, "Husnah kin bani mamaki Husnah yan zun nice zaki tonawa asiri, kin san kuwa irin halin da na shiga Husnah akan rashin ki a kusa dani!?, Husnah nayi zaton kamar yanda kika furta cewar kina son farin ciki na, fiye da naki, bazaki 'ki abun da nake so ba, kin fi kowa sanin bana bu'katar na ganki a cikin damuwa ballema a ce yau nice zan zabawa 'yata mugun miji, Husnah kiyi tu nani idan har kika fasa Auren nan yaya zanyi da kayan mutane ne Husnah!?.



Su Daddy da Hajiya dasu Shaheed mamakin irin halin mahaifiyar Husnah sukeyi, wato ita ba ciwon rashin ganin Husnah takeyi ba, aa ciwon rashin samun biyan bu'katar ta, takeyi, amman Allah tir da iyaye masu irin wannan hali, haka suke ta sa'kawa, a ran su.



Zubaidah ta ce, "Husnah hawan jini gare ni, zuciya ta, ta kumbura, dubi tarin yawan maganin da aka bani, bayan allurai, wanda ban san ada din su ba" maganin ta nunawa Husnah.



Husnah ta ce, "mommy kiyi hakuri banza 'kara yin nesa dake ba, amman kuma ki sa ni bazan ta'ba Auren kowa ba, ke bama wannan mutanen ba, kowa bana bu'katar Aura a halin da ake ciki, sannan kuma ki sa ni, zan iya kula da lafiyar ki, fiye da tawa lafiyar amman kuma wannan bu'katar taki bata da ma sau'ki ko gurbi a zuciya ta"



Wata uwar zabura Zubaidah tayi ta tashi tsaye cikin masifa har dasu rufe ido, jikin ta, sai rawa yakeyi, ta ce, "Husnah!!" Da 'karfin gaske wanda sai da Husnah ta zubura ta tashi tsaye cikin rawar jiki da kad'uwa.



Zubaidah taci gaba da fad'ar, "Husnah ni zaki zubawa 'kasa a ido to wallahi baki isa ba, sai dai idan yau aka d'aura maki Aure da wannan yalla'bain ki fad'i 'kasa ki mutu, kuma Auren ku kamar anyi sa an gama ne".



Cikin fushi da nu na rashin tsoro Husnah ta ce, "to Mommy kamar yanda kika damu akan cewar sai kin Aura masa ni to ke mi zai hanaki ki Aure san, mana, ko wani ya hana ki!?.



Ba Zubaidah hatta Ummey da Daddy dasu Yaya Yusuf da Shaheed dasu Husain dasu, da mutanen dake gurin baki d'aya, sai da suka zaro ido suna kallon ta, cike da mamaki, Anisah harda murza ido.


Zubaidah kuwa, murza idon ta takeyi tana fad'ar, "Husnah? Kin san abun da kike fad'a kuwa, anya ma kanki d'aya kuwa, kodai kin samu tabuwar hankali ne!.



Cike da kaduwa Zubaidah ke maganar.

Husnah kuwa ido tsakiyar kai tace, "kwarai kuwa Mommy ina cikin hayyaci na, akan miye zaki takurawa rayuwa ta, bayan kema ba Auren nan kikayi ba, ni kuma kice, dole sai kin yi mani Auren dole, akan miye akan wace hujjar!?.


Saukar wani wawan mari taji a kuncin ta wanda sai da jin ta suka d'auke duka, sai da tayi kusan sakwan talatin sannan jin ta ya dawo, hankalin ta ya dawo jikin ta, ta d'aga ido kawai, idon ta ya sauka akan Husain wanda yake ta huci kamar wani kumurcin zaki.


Yaya Yusuf ya ce, "nagode Husain kayi mani dai_dai ai nine nayi niyar ai kata hakan ka rigani, Husnah danan baki da kunya har hakan, dan baki da mutumci, mahaifiyar taki, kike fad'a wa irin wannan maganar!?.



Daddy cikin matsanan cin fushi ya ce, "Husnah ta ba haka take ba, Husnah ta bata yiwa kowa rashin kunya ballema ace tayiwa mahaifiyar ta, dan haka kuzo mu juya, idan na samu Husnah ta, zuwa gaba, zan tarbi abuta, amman nikam wannan ba tawa bace, ku tafi muje".



Dukan su juyawa sukayi, da gudu Husnah tabi bayan su tana fad'ar, Daddy dan Allah kada ku tafi ku barni, kada kuyi fushi dani, akan abun da baku sani, ba, amman ina sun sa kai kawai bar cikin falon gidan.



Dariya mutanen gurin suka sanya harda tafawa, Zubaidah kuwa rawa ta fara takawa, Husnah kallon su kawai takeyi cike da mamaki ga fuskar ta, kumbura, saboda ta maru iya mari, har shatin yatsun Husain sai da ya fito, a fuskar ta,.


Dariya Zubaidah tayi ta ce, "yaro_yaro ne Husnah ke a da a tunanin ki, kina nufin cewar zan saka maki ido ne ina kallon ki, haba Husnah ai ko wa ya riga ka bacci sai ya riga ka tashi, Husnah na lura kina son kiyi wasa da nine amman kuma ki sa ni nice uwar ki baki da wata uwa a duniya bayan ni, kuma Husnah na riga da na gano cewar kin samu wasu mutanen ne shi yasa kike son gudu na, amman Husnah yan zun nayi maki na babba da yaro".

Zubaidah ta ci gaba da fad'ar "Husnah baki da wani za'bin sai na Auren yalla'bai kuma babu uban da zai hanaki Auren sa indai ina a duniyar nan, shi yasa nayi maki na yan duniya irin mu, goggagin yan bariki, kinga gashi sun tafi sun barni dake, yan zun baki da gurin zuwa ko? ".

Hahhhh suka sanya dariya dukan su.

Magana suka jiyo daga can bayan su, Hajiya ta ce, "Husnah daman nasan akwai wata a 'kasa dan ba halin ki bane wukanta babba, amman nayi mamakin haka, dan haka ne ni naji A zuciya ta ban yarda da wannan shirin Mommyn ta ki ba, muka dawo domin yi maki tambaya, Husnah mike faruwa ne".



Kukan farin ciki Husnah ta fashe dashi ta ce, "Ummey daman nasan ku da fahim ta nadan bakwa yanke hukunci cikin fushi amman yanzun zakuji komai, amman Daddy sai kace ka yarda dana fad'a zan fad'a".


Matsowa Daddy ya yi, ya ri'ko hannun Husnah yace, "ki fad'a 'yata na yarda da ke ".


Murmushi Husnah tayi ta ce, "Mommy zan sanar da kowa dake gurin nan abun da bakiyi zaton nasani ba a taki wautar amman".


Dariyar yan bariki Zubaidah tayi ta ce, "to fad'a mana waye ya hane ki iya? ".


Murmushi Husnah tayi ta ce, "Daddy Ummey Yaya Yusuf da Shaheed Anisah Suhailah da duk wani wanda yake gurin nan, ku saurara da kyau kuji harda ke Mommy ".


Duk gurin sukayi shiru suka zuba wa Husnah ido .

Husnah tayi murmushi ta ce, " *A GIDANTA NA GIRMA!! * ".


Ga baki d'aya gurin suka had'a baki tare da zaro ido wake da doka 'kirji gurin fad'ar, " *A GIDANTA NA GIRMA!!?*


*(NIMA DAI NACE A GIDANTA NA GIRMA!!?)*

to kufa masoya?


*Comment and share*



*A GIDANTA NA GIRMA*


*BY NANA: KHADEEJATU*

*_UMMU IHSAN_*


*SADAUKAR WA GA :- DUK KANNIN MASOYA NA NABOYE DANA BAYYANE INA SONKU SOSAI SON FISABILILLAH*


*YA ALLAH KAJIKAN MAHAIFINA KAYI MASA RAHMA KA KYAUTATA MAKWANCIN SA SHIDA YAN UWA MUSULMI BAKI `DAYA.*


*YA ALLAH KA BAIWA MAMANA LAFIYA KA BAIWA DUK KANNIN WANDA BAIDA LAFIYA NA GIDA DANA ASIBITI ALLAH KA BASHI LAFIYA AMIN YA ALLAH*




*_Bismillahir Rahmanin Rahim_*

66~70

Husnah tayi murmushi tace, "Tabbas *A GIDANTA NA GIRMA!!* nasan zakuyi mamakin jin wannan maganar saga baki na, kwarai kuwa, mommy nasan zakiyi mamakin a ina naji wannan maganar toba a bakin kowa naji ba, kina gani na kamar 'kuruciya tayi mani na damuna, to abun ba haka yake ba"



Mommy ina kiran ki da wannan su nan ne saboda ina son ki sani cewa ni yar halak ce ban ta'ba man tawa da cewar ke ce kika fitar dani daga cikin wahala ba, a lokacin ina cikin shan wahalar kishiyar uwa, dan haka ina son ki sani cewar, Husnah tasan komai tun daga mutuwar mama na, har zuwa wannan ranar, "



Wata irin zufa ce, ke kwararo wa Zubaidah sai jikin ta da yake rawa, kamar mazari, abokan Zubaidah kuwa hannuwan su, suke tafawa cike da mamaki da zallar wautar Zubaidah suke gani.


Daddy da su Hajiya kuwa cike suke da al'ajabi


Husnah ta ci gaba da fad'ar, "tabbas ina yar shekara tara zuwa goma ne, kuka je kuka bada kud'i aka baku ni, kamar yanda naga tsabar rashin gaskiya a tattare da tafiyar da kukayo dani, na sauya motoci da barin taku motar a cikin jeji, da yanda kika baiwa abokiyar ki kud'in da ta taimaka maki kuka d'auko ni, tun daga ranar kika baro garin dani, ban sake ganin ta da ido na ba, kuma kema ko zan cen ta bakya yi"




Mommy idan baki man tada wata rana ba, ranar da kika tasa ni a gaba kina bani labarin rayuwar ki, da yanda kike son na zama ba, tun a ranar nake tausayin rayuwa ta da taki rayuwar, Mommy ba zan sanar da kowa abun da kika sanar dani, daga cikin rayuwar kiba, domin yin hakan kamar ba tona wa kaina asiri ne, ko nace na sokawa ciki na wuka ne.


Amman idan ke ce kika sanar da wani labarin da kika bani, to bani da damuwa.


Mommy Husnar dai ce wadda kika zaba wa dadiro tun tana 'karamar ta, ita ce ta girma ta kori dadiron Mommy kin san waye kuwa?".


Ganin Zubaidah na zubar da zufane yasaka Husnah fad'ar, "nasan zaki sha mamaki idan na sanar dake cewar nice, na had'a Tk da iyayen sa harda matar sa, kuma gashi ya shiryu, amman na nuna maki naji zafin abun".


Mommy nice dai Husnah taki, na kori Tk a rayuwa ta, kuma kamar yanda kika hanani kula kowa a rayuwa ta, kika zabar mani rayuwar kad'aici to nima na za'bi na kori duk wanda kike son na kasan ce dashi domin duk abunda na aikata kece silah,kin koyar dani rashin ganin darajar kowa da girma ma kowa, da wulakanta kowa, amman ni bana son aikata hakan domin nasan da cewar a kwai ranar da zan nisan ce ki".




Mommy ko anan kawai na tsaya na rufe babin da kike gani na ko ince kowa yake gani, na a matsayin yar da kika haifa, to kowa ya shaida Mommy ba ita ce, ta haife ni ba, *A GIDANTA NA GIRMA* kawai "



Zubaidah cikin masifa ta ce, "Husnah yan zun duk kina nufin da wayon ki amman kuma baki ta'ba nuna mani ko da wasa ba, cewar kin san komai ba? Husnah daman kece kika kori Tk wanda yake taimakon rayuwar ki, tun kina cikin datti har kika zama mutum, shine ki ka basar,? Shin Husnah daman kin shirya tona mani asiri ne ko miye!?.



Dariya Husnah tayi ta ce, "Mommy ke nan duk abunda kika ji na ambata babu 'karya ko d'aya a cikin ".


Zubaidah ta ce, "Husnah idan har Tk ya bar maki abunda ya baki, to shi wannan ina yi maki albishir da cewar duk abunda ya kashe maki koda tsinke ne sai kin biya shi abun sa, kuma daga yau babu ni babu ke na koreki daga cikin gidan nan kuma nima badan duk hidimar kiba tun lokacin da nazo dake, Tk yake yinta ba da nace, sai kin biya ni abuna amman ina kin tsira Tk ne gatan ki yariya, kuma ki biya yalla'bai kafin ki bar cikin gidan nan kuma, kada na sake ganin 'kafar ki a gidan nan ".



Dariya Husnah tayi ta ce, "mommy ai ni har yan zun ba zan dai na kiran ki da wannan su nan ba, amman ki sani ko kwabo na wannan kazamin mutumen banci ba, ga kud'in sa, bari yan zun zanyi maki transfer na kud'in nasa, Anisah bani wayar ".


Anisah cikin kwarin gwiwa Husnah tayi mata transfer na kud'in da Alhajin ya turo mata, matar da wayar take hannun ta ta ce, "miliyan d'aya ta shigo, jama'a ku duba, ansar wayar mutane ke tayi suna gani, cike da mamaki, sannan Husnah ta ce Mommy na gode da ri'kon da kikayi mani bana bu'katar kayan cikin d'akin can naki nabar maki zan d'auki sauran ajiya ta, "



Hayewa d'akin Husnah tayi ta d'auko tsofafin kayan ta, tace, "Mommy na barki lafiya yanda nake wa kaina fatan shiriya, kema ina yi maki fatan shiriya".



Kawai Husnah tasa kai batayi wa kowa magana ba, tabar falon tayi waje gurin motar ta, ta nufa ta bud'e, zata shiga ciki Anisah ta tabiyo bayan ta, tace, Husnah kina nufin ba gidan mu zaki koma ba, tafiyar ki zakiyi, to ina zaki shiga ne a cikin duniyar nan?.


Husnah kuwa ta ce, "Anisah zan shiga duniya ne, kin san duniya fad'i gare ta".


Anisah tace, "subhanallah Husnah kina nufin kudurin ki na zaman hotel yana nan kina nufin zakiyi zaman kan ki ne!?.


Husnah kuwa shiru kawai tayi, Husain kuwa cikin takaici ya janye Anisah da karfin, ta dawo gefe kawai yazo ya kama hannun Husnah ya murde, ya anshe makullin motar ya rufe, ya yi cikin gidan ya ce da Zubaidah, "ga makullin motar ku nan ku 'kara da ita".


Kawai ya fito Husnah sai harar sa take ko kallon inda take baiyi ba kowa ya shiga cikin mota banda Husnah, har sun ta tar da mota Husain ya fito ya je ya janyo hannu Husnah tana tirjewa kawai ya jefa ta, a cikin motar shima ya shiga, Shaheed ya tayar da motar, suna dariya 'kasa_'kasa.


gidan su suka dosa Husnah sai hura hanci takeyi tana gun guni, maganar dai bata fito fili ba, ballema aji abun da take fad'a, matsawa tayi can nesa dashi tana kallon window, har suka iso gidan.


suna yin parking Husnah tace, "Yaya Yusuf nifa ba zan iya zama a gidan kowa ba, zan nemi sunan garin mu ne na koma, gida zaifi".


Dariya suka saka Yaya Yusuf ya ce, "Husnah zo kiji wani labari, daga ni sai ke".

Husnah dai kamar kada taje, sai kuma ta fito tayo gurin Yaya Yusuf suka jera suna tafiya, Yaya Yusuf ya ce, "Husnah kada kiyi gan_gan cin tafiya yan zun domin kin san halin Mommy ki baza barki ba, domin ba zatayi maki ri'kon banza ba, sai ta d'auki fansar tona mata asiri da kikayi a gaban idon mutane, kika karyata ta, gashi tayi karya baki san adadin mutanen da tayiwa 'karya ba, a kan ki ba".


Ajiyar zuciya Husnah ta sauke ta shiga nazari, zuwa can ta ce, "tabbas nasan halin Mommy da wannan azzaluman mutanen da wannan mugun mutanen zasu d'auki mummunar fansa a kai na, babu inda zani ina gidan nan, amman wallahi kayiwa wan can mugun magana ya daina shiga har yata".



Dariyar cin nasara Yaya Yusuf yayi, ya ce, "yauwa kanwata ta kaina".

Haka suka shiga cikin falon gidan suka zazzauna Shaheed ya ce, "Husnah dan Allah ki zauna damu ina son ayi biki na tare da ke ".


Dariya Husnah tayi ta ce, "na yarda za'ayi bikin ka dani Amman ba zan zauna ayi na ta zuru ba".


Husain ya ce, "kam uban can ke wasa nake dake ne? ".


Hajiya sunji dad'in yan da Husnah ta saki jikin da su, ta ce, "to kayi Auren mana sai a daina tsokanar ka".


Tashi Husain yayi yabar gurin.

tun daga wannan lokacin ne Husnah ta zama yar gidan sam Husnah ta dawo kamar ba ita ba, babu mai yi mata kallon da shi bane, kuma sam Husnah ta murje hankalin ta ya kwanta, sallah da karatun sallah da ambaton Allah shine suke koyar da ita, kowa tausayin Husnah yakeji musam man ma da sukaji cewar mahaifiyar ta rasu, kulawa sosai suke bata ".


Ankai komai na bikin Shaheed Auren ma sati ukku aka saka, ai kuwa shirin biki kawai akeyi, Husnah sune kirjin biki, Husain ne ya shigo cikin gidan cikin uzuri ya sanar da Ummey da Daddy cewar matar da zai Aura iyayen ta, sun ce ya turo a had'a bikin sa dana Shaheed ".


Kallon_kallo aka shiga yi tsakanin Daddy da Ummey, babu yanda suka iya, suka amsa masa, aka tura gidan su yarinyar aka bashi ita, aka maida bikin satin ukku daman saura kwana shidda.


A ranar da aka sanar da su Anisah dasu Shaheed Auren Husain ne ya saka aka d'aga Auren duk sai suka bata fuska, Husnah kuma tsalle ta doka, cikin farin ciki tace ashe dai su mugu ana da budurwa Allah yasa a dawo da Auren a gobe ma, na dai na ganin mutum kullum ".


Duk sai suka bita da ido jin sukeyi kamar su make ta, Shaheed ya ce, "dan Allah Husnah tashi ki koma cikin d'aki kina nufin ke farin ciki kike yi da wannan Auren ai wallahi kin bani kunya".


Mere baki Husnah tayi tace, ni wallahi dama nasan yanda za'ayi da anfara yin nasa bikin ma, kowa ya futa".



Dafe kai Shaheed ya yi, ya ce, "Husnah dan Allah ki..

Daddy ne yayi saurin cewar Shaheed kabar zan cen kawai, Allah ya tabbatar da alkhari.


Duk suka ce, "amin "


Tun da Husnah taje gurin kwanciya, bacci ya ce, bai san idon ta ba, ta rasa miye ya hana ta bacci, jure_juye kawai takeyi.

Da ta gaji da kwanciya kawai sai ta d'auko wayar ta, ta kunna ta rasa, mi zata kalla, kawai Husnah ta rasa ita fa, yau mike damun tane, haka har asuba tayi, tana yin sallah, ta kwanta sai bacci, koda ta tashi bata da wata wal wala cikin damuwa take haka ta yini kowa dai yana mamakin miye ya sami Husnah? .


haka Husnah ta dawo suku ku, har satin bikin duk wanda ya tambaye ta, mike damun ta, takan ce, Mommy take son gani, sai dai suyi ta lallashin ta, ana biki saura kwana biyu Husnah na zaune a baran dar gidan tana game da wayar ta, Husain da abokan sa, suka shigo sukayi parking, duk suka fito, Husain yana wai wayowa, kawai ya hango Husnah zaune tana wasa da wayar ta, harara ya ballama, duk da yasan Husnah bata gan sa ba.


Cikin sauri yace da abokan sa kuje can ga key din d'akina ku tafi ina zuwa, duk basu lura da abunda yake nufi ba, har suka wuce, amman abokin sa d'aya murmushi kawai yayi ya gir giza kai.


Sai da Husain yaga wucewar su, yayo inda Husnah take zaune hankalin ta, yana a kan wayar ta, da alama tana jin dad'in wannan game d'in, Husain na zuwa ya wafce wayar, ya duba game ne ya gani tana buga wa, ya maida wayar a cikin aljihun rigar sa, Husnah kuwa da bata san da zuwan Husain ba, yana wafce wayar ta tashi tsaye da sauri, zatayi magana taga Husain ne, kawai ta d'auke kai, Husain ya ce, "ki tashi ki baiwa mutane guri domin ina tare da bi'ki na, muna da bukatar gurin ki koma cikin gida ".


Husnah kuwa ta ce, "malam nifa wallahi bana son takura kaje kaji da abunda yake gaban ka, ni game shine a gaba na, kaji ko? Waima dan Allah ba zaku sauya gurin da zakuyi taron ku ba ne? ".


Husain ya ce, "malama ki dai kama gaban ki kawai, kiyi cikin gida, kuma ma Amarya ta tace, "kuzo gurin denier din da zai ayi yau da dare, ki sanar da "yan uwan ki".


Mere baki Husnah tayi tace, "wallahi ba bu inda zani indai har zata su zasu je ba zan hana su ba amman nikam ba zani ba".


Cikin jin haushi Husain ya ce, "dallah mallama, kada Allah yasa kije, kuma kafin na kirga biyar kin bar gurin nan ".


Tafiyar ta kawai tayi, abokin Husain kuwa tace, "malam wayar ta fa? ".


Galla masa harara Husain yayi ya juya suka koma gurin abokan su.


Husnah na shiga cikin d'akin su tayi kwanciyar ta, kawai ta fashe da kuka sai da tayi kukan ta mai isar ta, sannan tayi bacci.


Koda su Anisah suka dawo bacci takeyi gashi tare suke da maman Baby tunda basu ta'ba had'uwa ba, ganin tana bacci dole suka bar ta, suka sanar da Anty tasu,ita kuma ta koma gida saboda shirye_shiryen bikin Husain ita ce, komai.


Husnah sai marece ta falka, anan ne take sanar dasu sa'kon Husain wanda har had'uwa sunyi dashi amman

Please Login or Register in order to submit comment