Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wayar mutane kawai ".

Husnah najin su sarai har tayi niyar kashe wayar sai kuma taji bazata iya wulakanta wanda yayi maganar ba wato Shaheed barema yace, ga yayan su babba.

Husnah tace, "ok bashi wayar nasan duk ku masu hankali ne banda wani ".

Da dariya Yayan nasu yayi mata sallama, Husnah cikin farin cikin jin ya mutun ta yayi mata sallama sai ta amsa.

Yayan nasu yace, "kanwata ya kike ya bayan rabuwa? "
Husnah tace, "lafiya lau ya mai jiki dafatan dai babu wata matsala atare dashi? ".
Yayan yace, "Alhamdulillah yaji sau'ki tuni ma, amman yayi ta neman ki, gashi yace kinyi masa alkawarin ba zaki gudun masa ba".

Sai alokacin ne Husnah ta tuno da alkawarin tace, "kash wallahi na manta ne, amman isha Allah zan nemi inda yake nazo gurin sa, ka sanar dashi ina gaida shi sosai da sosai".

Yayan yace, "aa baza ayi hakan ba yanzun dai za'a kai masa wayar sai kuyi ta baki da baki kinga sai yafi farin ciki ko? ".

Husnah tace, "ok babu damuwa amman dan Allah kada ku baiwa karen gidan ku wayar nan dan kar yadame ni da haushi, kuma idan zanzo gidan nan ku tabbatar da kun d'aure sa ko kuma kubar gidan dashi".

Husain yayi saurin cewar, "idan kika kuskura kika zo gidan nan sai kinyi baya nine".

Yayan nasu yace, "haba Husain miyasa kuke wannan rigimar takune bayan ba wani sanin juna kukayi ba, amman ba'kin fad'a kamar wasu kaji".

Dariya Husnah tayi tace, " Yaya kai wa Daddy wayar muyi magana waima ina baby tane nasan yanzun ta girma sosai".

Dariya duk sukayi banda Husain, da sauri Babyn tace, "gani Anty nayi kewar ki dan Allah kizo gidan mu kuma ku dai na fada da Uncle kinji kuma yaushe ne zaki zo? "

Dariya duk sukayi Husnah tace, "to wace tambayar zan amsa maki, ina nan zuwa kinji ko? ".

Yayan nasu yace, "Shaheed kaiwa Daddy wayar suyi magana ni kuma na tsaya akan wannan mai bakar zuciyar ".

Tashi Shaheed yayi rike da wayar a hannun sa, yana yiwa Husnah firar bayan rabuwa da yanda Daddy da Hajiyar su, suka damu da rashin ganin ta, Husnah duk sai taji babu dad'i.

Baby kuwa da gudu taje ta samu su Daddy zaune suna fira harda su Anisah, kawai ta fad'a akan jikin Hajiyar tana shashsheka alamar tasha gudu har ta gaji, Hajiyar tace, "wato dai sakar cin nan naki yana nan Allah yasa Uncle dinki ya ganki kici duka".

Baby tace, "Daddy yau Uncle Shaheed yazo maka da wayar ka kuyi magana ".

Dariya duk suka sanya mata dan basu fahim ci inda zancen ta ya dosa ba, Shaheed ne ya shigo da sallamar da wayar a kunnen sa, yaciro wayar ya saka hans free yace, "Daddy suprise gashi kaji muryar waye? ".

Amsar wayar Daddy yayi, yayi sallama daga can Husnah tace, "Daddy ayi mani afuwa nayi laifi babba ".

Ai kuwa cikin farin ciki, Daddy yaji muryar da bazai taba mantawa da itaba har ya mutu yace nikam nayi fushi sai kin zo da kanki zan hakura ".

Husnah tace, " daman zan zo har gida da kaina amman Daddy Yaya akayi layin ka ba'a rufe saba akalla ansamu wattani da yawa"


Dariya Daddy yayi yace, "ina son layin ne kuma dashi nake amfani duk wasu abubuwa nawa masu muhimmanci suna a cikin sa, sai kin zo zan baki labarin miyasa ba'a rufe saba".

Husnah cikin damuwa tace, "zan zo ranar friday Daddy ".
Daddy yace, "to kice Insha Allah nikuma Insha Allah nida iyalai na munayi maki barka da zuwa tun kafin kizo, ke zaki zo da kanki ne ko na aiko a d'auko kine".

Shiru Husnah tayi zuwa can tace, "aa zanzo da kaina ne idan nazo sai a dawo dani ".

Sallama sukayi suka kashe wayar da sauri Hajiyar tace, "tabbas koda baku bamu labari ba mun san cewar addu'ar mu ta 'karbu ne tun daga ganin farin cikin Alhaji dasu Shaheed dan haka yau sadaka zamuyi kuma Allah ya kawo ta lafiya ".

Cikin farin ciki kowa yace, "amin "

Ranar yini yan gidan sukayi cikin farin ciki ganin iyayen su sun samu abunda suka dad'e suna nema.

Husnah kuwa ajiye wayar tayi ta mayar da ita inda ta ajiye ta, kwanta wa tayi tana tunanin wannan bayin Allah, da Allah ya had'a ta dasu.

Zubaidah kuwa tuni tabar garin tayi gurin shashan cinta a can ta hud'u da wasu yan fafa kawai ta mike 'kafa taci gaba da abunda takeyi amman tana kiran "yarta taji wane abun takeyi.

Yau friday gidan su Husain tashi sukayi sunata shirye shiryen tarbon bakuwar su Husnah , Husain kuwa sai hura hanci yakeyi kamar wani namijin zaki, sai cika yake yana batsewa shi ala dole kada bakuwar taga damar sa ta raina sa.

Kowa da abundant yakeyi ma tarbon Husnah.
Husnah kuwa sai karfe sha d'aya ta tashi tayo wanka tayi dan make up d'in ta, gurin saka kaya ne ta rasa wanne zata saka duk kayan sunyi mata 'kanana babu kayan mutumci, ai kuwa tunda Husnah take yaune kai ta taba takaicin rashin kayan mutumci a gareta, kawai ta fashe da kuka, tana kukan ne duk tabi kayan ta kaf ta saka tana cirewa, duk basuyi ba, kawai ta d'auko doguwar rigar ta ta sallah da hijab d'in ta saka ta goge fuskar ta, ta kalli madubi tace, "wannan shigar da ita zani gashi duk kayan sun tsufa ni yaya zanyi ne wai ni Husnah, kawai tayi zaman yan bori dir shan a 'kasa tayi tagumi.

Tace, "nima fasa zuwa bari nakira wayar na sanar masu" kawai Husnah ta tashi ta d'auko wayar ta kunna to kuma wayar babu gurin kira baka ganin number ma kawai ta ajiye wayar.

Kamar daman jira akeyi ta bude wayar kira ya shigo tana d'aga wa tayi sallama cikin sanyin murya aka amsa mata, aka ce, Anisah ce kanwar Yaya Shaheed muna ta jiran ki gashi har biyu tayi bamu jiki ba Daddy da Hajiyar mu duk sun damu suna cewa Allah yasa kada ki shuka su".

Jikin Husnah ne yayi sanyi tace amso sorry kice masu yanzun zan fito amman kurika kirana kana yi mani kwatancen hanyar yanda zan gane"

Cikin farin ciki kowa yace, to ranki ya dad'e" dariya Husnah tayi tace, ashe duk kuna jin abunda na fad'a to gani nan zuwa" tayi shiru sai ta tuno da maganar Daddy ranar yace tace, Insha Allah, kawai tace, "Insha Allah".

Suka ce, " to Allah ya kawo ki lafiya " tace "amin"
Husnah kuwa ta ajiye wayar, tace, "haka nan zan tafi sai dai suyi mani dariya ".

Post da key kawai ta d'auka ta fito ke nan suka hud'u da Zubaidah suna shigowa, burki taja, amman ta dake cikin sauri Zubaidah ta fito cikin motar ta 'karasa inda Husnah take tanayi mata kallon sama da 'kasa da mamaki cike da fuskar ta.

Murmushi Husnah tayi ta matsa inda Zubaidah take ta rungume ta, tayi mata rada a kunne, saboda ganin yanda abokan sha shancin ta maza da mata suke kallon ta tace, "mommy shigar ustazai ke nan nasamu labarin sa baya kula macce mai shiga irin tawa, sai ta ustazai kuma ko ustazai masu kamun kai, dan gidan mansir ne, haji mansir naira da kwabo dan sa wanda shine kawai ya gaji dukiyar sa,

matar Aure yake nema ta kwarai bayan ya gama lalata rayuwar wasu, shine naje nabiya kud'i aka bani wannan kayan da yanda zanyi shigar da kuma yanada zanyi masa magana batare da gane wace ce niba".

Wata irin ajiyar zuciya Zubaidah ta saki, Husnah kuwa murmushi kawai tayi, Husnah tace, "naso sanar dake da bakya nan amman sai na fasa saboda ban 'karasa iyawa ba yanzun ma zanje gurin koyon salon yanda zanyi masa makirci ne da iyayen 'karya".

Zubaidah ta dawo da kanta saitin kunnen Husnah tace, "na jin jina maki amman zanyi shiru saboda wannan shegun zasu iya watsa maganar har zancen ya watse kin ga suyi muna ba'kin ciki, sai kin dawo ".

Rabuwa sukayi Husnah ta bude motar ta shiga ta bata wuta, su kuwa "yan gulma duk sun so san miye Husnah ta sanar da Zubaidah amman kai tace masu, "ta samu ustaz ne irin na yan bari".

Ta rufe wa kowa baki.

Husnah kuwa tana tafe hankalin ta kwance, aka kira wayar ta sanar masu inda take, aikuwa tun daga wannan lokacin ne, suke waya a tsanin su, har tazo inda suke ta kwa tan ta mata, wata motar ce, dake gefen titi ta gani, mai motar ne ya fito yayi mata hannu tana zuwa gurin itama tayi parking 'karasowa inda take yayi yace, "kanwata muje nayi maki jagora, ni ina gaba ke kina biye".

Dariya Husnah tayi tace, "ok Yayan mu muje kawai ".

Haka suka jero shi bakar mota ita kuma ash har suka 'karaso wata unguwa mai manyan gidaje, a take Husnah taga ashe dai unguwar su kauye ce, bata gama tunani ba suka gangara wani titi hannun hagun su, kayataccin gidajen da Husnah ta gani ne suka so bata tsoro, batama 'kara sa rud'ewa ba sai da suka doshi wani 'katon gida wanda yafi ko wane gidan tsaruwa da had'uwa a unguwar, a take aka bud'e masu get suka shiga ciki get ukku ne a gurin duk babu na rainawa a ciki koda sukayi parking a wata rumfar alfarma a take Husnah ta fara raina suturar dake jikin ta ita ganin takeyi duk batayi kyau ba kuma ita ganin suturar dake jikin ta duk yawa ce, gashi zafi takeji duk rigar da hijab din sun takura mata.



Kwan kwasa mata kofar akayi sai alokacin ne ta tuno da ita ake jira, fitowa Husnah tayi, ai kuwa tayi tozali da Hajiya wadda tana ganin Husnah sai taji duk son duniya tanayi mata shi, kamar ta goya ta , rungume Husnah tayi tace, " 'yata ina yi maki barka da zuwa nagode wa Allah da ya sake sada mu dake zo muje" hannun Husnah taja ta hana kowa yayi mata magana ko ya rungume ta.

Husnah dai anzama ba kyauya sam idon ta na kallon tsarin gidan, ga kuma kaunar Hajiyar da taji ya darsu a zuciyar ta.


A babban falon gidan suka yada zango kowa ka kalli fuskar sa zaka fahimci yaji dad'in ganin Husnah a kusa da Daddy Hajiyar ta ajiye Husnah, hannun Husnah Daddy ya rike guda biyu, yana murmushi yace, "your welcome my doughter Allah alhamdulillah da kasa ke nuna mani wannan baiwar taka, sannu da kokari kinji 'yata yau kin cika mani alkawarin da kikayi mani".


A take idon Husnah ya cika da hawayen farin ciki tace, "nima naji dad'in shigowa ta a cikin ku, dan Allah Daddy nima nazama 'yarka man! ".


Murmushi kowa yakeyi Anisah tace, " 'yar uwata kada kidamu yanzun haka kina cikin yan uwanki maza da mata, idan kun gama ganawa da yan iyayen ki, ki nemu a wan can d'akin suka nuna mata da hannun su".


Murmushi Husnah tayi mata ta gyada mata kai dukan su suka tashi suka basu guri mazan dama tuni sun bar gurin.


Wani irin farin ciki ne Husnah take cikin sa wanda batama san irin saba, duk sai ta saki jikin ta suna fira da Daddy da Hajiya sai kusan la'asar Daddy yace, "'yata har yanzun baki sanar da Hajiya sunan ki ba amman ki bari a dawo sallah sai ki sanar damu duka ".


Dariya Husnah tayi ita da Hajiyar, Hajiyar tace, tashi ki samesu inda suka sanar dake tashi Husnah tayi ta nufi inda suka sanar da ita, tana zuwa a bakin kofar taji suna fad'ar.....




*Comment and share*





*A GIDANTA NA GIRMA*


*BY NANA: KHADEEJATU*

*_UMMU IHSAN_*


*SADAUKAR WA GA :- DUK KANNIN MASOYA NA NABOYE DANA BAYYANE INA SONKU SOSAI SON FISABILILLAH*


*YA ALLAH KAJIKAN MAHAIFINA KAYI MASA RAHMA KA KYAUTATA MAKWANCIN SA SHIDA YAN UWA MUSULMI BAKI `DAYA.*


*YA ALLAH KA BAIWA MAMA NA LAFIYA DA DUK KANNIN WANDA BASU DA LAFIYA NA GIDA DANA ASIBITI ALFARMAR ANNABI MUHAMMAD SALLALLAHU ALAIHI WA SALLAM AMIN*


*_Bismillahir Rahmanin Rahim_*

36~40


Kawai Husnah taji suna fadar "a gaskiya wannan kam duk inda ta fito balarabiya ce ta asali wallahi"


Ni kuwa wallahi Suhailat tafiyar ta kawai nake kallo cikin cikin 'kasaita da yanga nifa wallahi da zata koyar dani dana more wallahi.


Kawai suka sanya dariya.


Husnah kuwa tana a bakin kofar d'akin tana sauraren duk abunda suke fad'a akan ta, kawai ta soma duba shigar ta da 'kafar ta itafa ba taga wani abun burge waba a tattare da ita ba, kawai ta mere baki, ta tura 'kofar ta shiga, ai kuwa da gudu suka zo suka tarye ta, suna yi mata sannu da zuwa.


Da murmushi Husnah take biyar su d'aya bayan d'aya, a bakin gadon suka yada zango .


Anisah tace, "a gaskiya munyi farin ciki da zuwan ki gidan nan dan Allah wata rana kizo kiyi muna kod one week ne! "

Dariyar da Husnah bata shirya bace ta kubce mata, ai kuwa duk suka tsare ta da ido sai da tayi dariyar ta mai isar ta, tace, "yo ku banda abun ku miye na han zari haka bayan duka_duka yau ne na fara zuwa, ai ina ganin kamar yan zun ku ne zaku zo gidan mu ko? ".



Da sauri Anisah tace, "ai ko yan zun zamu iya biyar ki har gidan muyi maki wata koda biyu ne zuwa ukku ".


Dariya sukeyi dukan su suna cikin dariyar ne Shaheed ya shigo hannun sa ri'ke dana Baby yace, "kai amman fa kun iya wayau wallahi shine zaku wani d'auke ta ku dawo cikin d'akin ku kuyi ta fira da dariya to ku taso muje falo muci abinci"


Tashi sukayi suka fita daga cikin d'akin suna dariya a falo suka yada zango inda babban yayan su Husain yake zaune a kusa da 'kafar Hajiya shi kuwa Husain kwance yake akan kujerar da Alhajin yake zaune kansa a saman cinyar Alhajin yana duba husnul muslim hankalin sa ga baki d'aya yana a kan littafin, Husnah kuwa bata ma kula da waye a gurin ba, asalima Baby ta d'auke mata hankali shi kuwa kamar ance d'aga idon ka, ai kuwa Husnah ce yaga zata ratsa ta kusa da kujerar da suke shida Alhaji alamu sun nuna a kusa da Yayan nasa zata zauna, kawai yayi sauri ya tashi tsaye ya yayi kamar zai bar falon yasa hannun sa d'aya ya ture ta, kawai sai ganin Husnah sukayi inda Husain ya tashi a zaune kamar kace ar'''' ta gudu duk tsoro ya kamata da mamakin taya akayi hakan ta faru?.



Husain kuwa kujerar nesa dasu ya dawo ya zauna kamar bai san abunda ya faru ba sai murmushi yakeyi ya daura littafin sa akan fuskar sa.


Duka mutanen cikin d'akin sukayo akan Husnah Alhajin kuwa ashe shine ya tare Husnah da hannun sa saboda duk abunda akeyi akan idon sane wannan ne ya hana Husnah faduwa kwance.


Sannu kowa yakeyi mata da Allah tsare gaba, gir giza kai kawai Alhajin yayi, Yayan su Husain kuwa cewa yayi, "haba Husain kowa yana jimamin fad'uwar ba'kuwar mu amman kai ko a jikin ka? haba Husain gaskiya baka kyautawa! "


yi yayi kamar badashi ake ba Hajiya tace, "Husain ka gyara halin ka sai naga kamar da gayya ka ture yar mutane dan Allah yanda tazo gidan mu lafiya ka barba ta koma gidan su lafiya! ".


Da sauri Husnah ta mai do da idon ta gurin Husain cikin zuciyar ta tace, "ashe dai inada shedun gani da ido him! Ba Husain kake ba ko husaina kake sai na rama dan naga ruwan marasa kunya ne da kai amman mu zuba ido baka san wace ce Husnah ba".


Alhajin ne ya katsewa Husnah tunanin ta yace, "yata tashi kici abinci rabu da wannan mai zafin ran ".


Hannun Husnah suka ri'ko suka je gurin da aka ajiye masu abinci Husnah ta zauna kowa ya zazzauna Hajiyar tace, "kai kuma sai ankira ka ko? "

Tasowa Husain yayi ya zauna akan carpet nesa da Husnah Alhaji yace, "Husain ka dawo nan a kusa dani ".


Gurin da Alhajin ya nuna masa ne ba Husain ba har Husnah Anisah dasu Shaheed sai da suka zaro ido ganin gurin da Husnah take zaune ne babu wata tazara mai yawa a tsakiyar su, Baby kuwa da murna tace, "yo sauri Uncle na tare maka gurin ka kada wani yazo ya zauna maka gurin ka".


Ganin kallon da Alhajin da Hajiyar sukeyi masa ne yasaka Husain badan yaso ba yazo ya zauna a kusa da Husnah har da taka mata hannu aikuwa da sauri ta janyo hannun tace, "wash! Allah hannu na! " ta soma yarfa hannun.


Babu wanda yaji abunda Husnah ta fad'a saboda kowa yasan Husnah da sanyin murya amman kowa yaga abunda ya faru kuwa babu wanda yace dasu uffan.


Yana zama Husnah ta dan 'kara matsawa a nesa dashi amman duk da haka ba wani nesa da juna suke ba saboda gurin kowa ya zauna an zagaye abincin.


Husnah aka fara zubawa sai daga baya aka zubawa kowa Husnah zata d'auki plate d'in ta ta soma ci Husain ya riga ta ya d'auke.


Murmushin gefen baki Husnah tayi ta gir_giza kanta ta jin_jina kai ta janyo nasa plate din ta soma ci.


Yayan zaiyi magana da sauri Alhajin da Hajiyar suka dora hannun su akan bakin su ai kuwa kowa yayi shiru kamar babu wanda yaga abunda yake faruwa a gurin.


Husnah kawai ta tashi tsaye kamar wadda ta tuno wani abun ai kuwa ta samu sa'ar taka wa Husain yatsun 'kafar sa da wannan uban takalmin nata kuma harda mur zawa ai kuwa Husain da yaji wata uwar azaba kawai ya saki plate din hannun sa ya runtse ido zuwa can Husnah ta bar gurin tana dariyar 'keta 'kasa_'kasa Husain da sauri ya tashi yaja 'kafar sa yana d'in girsa 'kafar sa har ya iso inda kujera ya fad'a ya ri'ke 'kafar sa, ai kuwa 'kafar har tayi wani uban jaa kuma ta fara kumbura, Husnah dake tsaye a bayan sa ta dawo kusa dashi ta faki idon kowa tace masa, "kai dai ka daina ja dani baka san wace_ce Husnah ba Husnah bata d'aukar wulakanci a gurin kowa sai dai idan ita Husnar ce taso dan haka yaro sai ka ki yayi babbar Anty a gurin ka! ".


Ta nuna masa yatsa tayi tafiyar ta.


Zafin da Husain yakeji ne ya daina ji yadawo kallon karamar yarinyar a cewar sa, wadda yake ganin kamar Baby dan bai yarda ta kai shekara goma ba to koda ta kai shekara goma to shi ginin ta yakeyi kamar jiya_jiya ne aka yaye ta.


Husnah kuwa da farin ciki ta koma cikin d'akin su Anisah tayi zaman ta, daman ita ba gwanar cin abinci bane shi yasa tayo masu wayau tabar gurin.


Su Hajiya kuwa duk abunda akeyi akan idon sune sai dariya sukeyi Anisah harda hawaye da dafe ciki saboda dariya Samha tace, "Allah nagode maka yau gashi ina kallon Yaya Husain na biye wa yara tunda duk wata mace a duniya indai bata kai sa'an su Hajiya ba to yarinya ce a gurin sa".



Yayan yace, "aikuwa ashe dana kubsa muna gurin kallon drama kai Allah na gode maka yau gurin Maman Baby zani na bata kyakykyawan labarin akan Husain".


Kawai ya tashi yana dariya yabar gidan haka kowa ya dawo cikin babban falon ya zauna Husain kuma tuni yabar gurin.


Husnah kuwa ganin kiran Zubaidah tayi bata d'aga ba sai da tayi kira ukku ana hud'u ne ta d'aga ta kara wayar a kunnen ta, tace, "mommy ya ya ne? ".


Acan ban garen Zubaidah tace, "ki dawo gida haka nan idan har kin samu ganin sa, dan yanzu zan bar 'kasar nan tafiyar gaggawa ce ta sameni".


Husnah tayi ajiyar zuciya dai_dai shigowar su Anisah tace, "duka duka yaushe ne kika dawo kuma yanzun kice zaki koma mommy kifa duba kad'aici ya dameni gaskiya amman kijira ni nadawo muyi magana dake! ".


Cikin damuwa Husnah ta kashe wayar ta tashi zaune taga duk su Anisah sun baje ta da ido Husnah ta 'ka_'karo murmushi tace, "to wani satin ma zan dawo indai mommy bata tafi dani ba".


Dariya kawai sukayi amman Anisah ta fahimci Husnah kamar ita d'aya ake bari a gidan kawai dai ita ma shiru tayi da bakin ta.


Husnah kuwa kayan ta ta d'auka tace dasu , "mu tafi ko?".

Jerawa sukayi suka nufi cikin falon Husnah tace, "Am Daddy Mommy zan koma gida kiran gaggawa akeyi mani ".


Badan sun soba haka kowa ya raka Husnah harda su Shaheed, wani abu ne Daddy ya bata cikin leda ba'ka Haka mommy ma ta bata gashi Husnah bata san miye ba Shaheed kuwa tasa motar ya shiga ya bata wuta, ya tafi.


Husnah taji dad'in wannan karamchin haka tayi masu godiya ta shiga motar ta ta nufi gida tare da kewar su Anisah.



A parking space, ne ta ajiye motar ta ta fito kid'a ne kawai ke tashi, tsaki Husnah tayi ta d'auki kayan da aka bata ta shiga cikin falon duk ga maza da mata yan bariki wasu na rawa wasu kallon batsa wasu kuma run gume da juna, harda Zubaidah a cikin su babu wani mai shigar arziki a cikin su.


Husnah kuwa bata bi takan kowa ba ta shige cikin d'akin ta, cike da takaici.


Zubaidah ce ta shigo ita da wasu kawayen ta cikin takaici Husnah ta d'aure fuskar ta tace, "mommy kada ma kiyi mani wata tambayar har sai wannan mutanen sun bar mani cikin d'aki! "



Sanin halin Husnah ne yasaka duk sukayi tsaki suka bar cikin d'akin, ita kuwa Zubaidah tace, "ba zanyi magana da gani sai ke ba, kizo da abunda kika samu ki same a falo".

Kawai Zubaidah ta bar cikin d'akin cikin fushi.


Tashi Husnah tayi, ta d'auki kayan ta nufi falon idon kowa akan ta kujera ta samu inda Zubaidah take a zaune ta zauna akan hannun kujerar ta bata kayan.


Ansa Zubaidah tayi ta baiwa wata mata dake gefen kujerar ta ita kuwa cikin izzah da isa take bude ledar, wani kwali ne taci karo dashi ta bude, ai kuwa wani dan akwati ne ta gani mai mugun kyau ai kuwa da sauri matar ta daka tsalle ta rungume Zubaidah tace sweety lallai yarinyar nan da gaske take ba 'karya ba kamar yan da wasu daga cikin mu suka fad'a ba".


Baiwa Zubaidah akwatin tayi aikuwa ita kanta Zubaidah sai da tayi ihu tace, "yauwa Husnah kin kyauta a gaskiya naji dad'in wannan fitar taki ki aje mani ita har zuwa sati ukku masu zuwa babbar rana a gurina ke nan "

D'aya ledar kuwa ana bude wa turare ne masu kyau masu tsada ga kamshin gaske, har kala biyar, ba karamar murna sukeyi ba.


Husnah kuwa bar masu kayan tayi ta koma cikin d'akin ta.



Zubaidah kuwa cewa tayi, "ina fatan duk kun gama yi muna oder ankon namu da kayan amare da kayan diener dana kamu bana son asamu matsala koda ta gurin launin colour ne "



Ihu suka sanya, ita kuwa Husnah da tazo zata d'auki wayar ta, kawai ta jiyo firar da suke yi da ihu cewa takeyi, "biki kuma? Kayan amare kamu kuma!? Nifa abun da mamaki dan ba'a taba bikin da mommy tace zata ba ko zatayi anko duk kuwa da irin alakar ta da mutum, to kodai mommyn ce zatayi Aure? ".



kai inaa!!..........

Assalamu Alaikum yan uwa ga wanda bai san da maganar da nayi ba ta bada gudumuwa ta a gurin koyon sana'oi ba to wasu sun sani sune ma suka bada shawarar na ri'ka sakawa a 'karshen page d'ina dan wanda ba group dina yake ba shima ya koya.


_*Abubuwan da zan ri'ka sakowa kuwa sune--:>*_

*koyon decoration koyon girki koyon kayan mata koyon

Please Login or Register in order to submit comment