Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kukan Husnah da shashshekar kukan ta ke tashi a gurin, cikin tsawa Daddy ya sake tambayar su wanda har sai da kowa ya shiga tai tayin sa.


Husnah cike da dakewa ta soma magana tace, "Daddy zan sanar daku komai abunda ya faru a ranar kuwa shine, tun ranar dana bar gidan nan aka sanar dani cewar Husain zaiyi Aure saura kwana biyar to ina dawowa gida na rufe d'akina ban sake budewa ba sai ranar da wannan rigimar ta faru, duk da kuwa ana zuwa ana buga mani 'kofa amman bana bud'ewa, Daddy saboda wasu dalilai wanda nice nake hango su, kasan cewar bani da kowa ballema na sanar da abunda ke damuna kowa laifina yake gani, bayan naga Amarya tayi sati d'aya ne na bud'e 'kofa ta nadawo na kwanta ke nan Husain ya shigo wai Ummey tazo gidan mu har 'kofar daki na tayi ta kirana da dukan 'kofa ta naki bud'ewa, nasan darajar Ummey kuwa a gurin sa, nasan yaya yake jin Ummey maganganu dai ga sunan" haka Husnah ta labar ta masu komai bata boye, nata ko d'aya ba har zuwan Ummey da Anty Zarah har barin su gidan, tana zuwa gurin da fad'i, tayi shiru sai kuka sanban tace, "Daddy gashi nan duk wanda ya mutu shi ake yiwa 'karya idan na fad'i akasin abunda ya faru gashi nan da ransa kuma a gaban sa".



Shuru gurin yayi Daddy yace, "Husain duk Hakane gaskiyar abunda ta fad'a ko da gyara? ".

Husain ya ce, "duk gaskiya ne".

Ummey ta ce, "Husain uban waye ya sanar dakai cewar nazo gidan ku, kuma nayi ta kiran Husnah taki bud'ewa har nayi fushi na tafiya ta!? "


Cikin fushi Ummey ke wannan maganar, a take, Husain ya ce, "Ummey Allah ya huci zuciyar ki, wallahi Zee baby ce ta fad'a kuma wallahi har da kukan ta, har niyar nazo gurin ki na baki hakuri sai kuma tace ai da fushi kika fita ba zaki ko kalli inda nake ba".


Cike da takaici Ummey tace, "Husain ban ta'ba sanin cewar kai wawa ne ba sai yau, kuma ban ta'ba sanin cewar kai baka san halin makircin mata ba, sai yau, kai har wai wata zata shirya maka 'karya a kaina kuma ka d'auka? Kai a tunanin ka kishin mata ban zane? In ma banda rashin tuni irin naka da mace ta maida kai wani soko taya zan kira Husnah kira d'aya biyu ta'ki amsa mani, da har kake fad'ar tasan irin yanda nake a gurin ka kuwa? To ita Husnar ya take ne a guri na? Ko kuma taya zan zo gidan ku ba tare da na nemi kuba kai da Husnar? To yan zun zan ja maka kunne ko dai kaja kunnen matar ka akan yi muna karya ko kuma musa 'kafar wando d'aya da kai da ita aikin banza da yofi kawai! ".



Jikin Husain ne yayi mugun sanyi, dan shi kwata_kwata bai kawo tunanin halin kishi ba a gurin, yama manta da cewar itafa Husnah a gidan su take a gurin mahaifiyar sa ma.



Daddy ya ce, "to amman Husain gaskiya ka sauya tunanin ka kuma ka gyara halin ka, ace mace ce zata haddasa maku har takai ga mahaifiyar ka ta zubar da hawayen idon ta? Kai da sa ke gaskiya, sannan magana ta biyu ita ce tunda bamu isa da kuba, bamu isa ku faran ta muna rai ba, ku raba wannan Auren da muka had'a ku saboda mu kam bamuga alamar zaku iya yi muna biyayya ba, Kuma kun wulakanta mu kunci zarafin yardar da mukayi daku, a yau ne muke baku umurnin rabuwa da wannan Auren da mukayi maku kowa yaje ta zauna da za'bin ransa za'bin da bamu mukayi maku shi ba, Husnah Husain yan zun nan nake son ganin cikar wannan umarnin namu na 'karshe wanda ba zamu 'kara saka maku baki a cikin lamarin kuba, sai kowa tasa ta fitar dashi! ".


A zabure duk suka tashi tsaye, Ummey tace, "kwarai kuwa tunda daman mune mukayi wannan had'in da zaton zaku iya yi muna biyayya, sai kash shekara d'aya da wata ukku babu alamar hakan daga dare ku dan haka mun yanke hukunci na 'karshe dole ne ku wallawale wannan had'in da mukayi maku!. "



Da sauri Husain ya dawo gaban Daddy da Ummey ya ri'ke 'kafar su su biyun ya duka yana zubar da hawaye yace, "Ummey Daddy dan Allah kada kuce haka wallahi mun anshi maganar ku kuma mu masu yi maku biyayya ne! ".


Anty Zarah ta ce, "to Husnah hankalin ki ya kwanta ko? Mutanen da basu nuna muna wani ban baci ba da yaran da suka haifa yau sune kika kasa sakawa farin ciki ko? Dariyar takaici tayi taci gaba da cewar nasha zaunar dake na sanar dake cewar ke mace ce kece ya kamata kijawo mijinki a jikin ki, kuma kece ya kamata ki koya masa sonki amman kikayi kamar wata kurma ba kya sauraren duk wata nasiha tawa, to yan zun kina nufin idan har kuka rabu da Husain zaki dawo cikin gidan iyayen sa ki zauna ne ko miye kike nufi? ".


Cikin fushi Husnah tace, "ya isa Anty Zarah haba! Komai Husain komai Husain, kuma komai laifin Husnah Husnah juya to duk naji kuma ki sani, da sani na nake kin yin abun da kike son nayi, kin ta'ba had'a mu nida shi kika tambaye mu mike faruwa a tsakanin mu, kiji laifin kowa kiyi muna fad'an tare? Sai dai kullum nice mai laifi nida bani da gata sai Allah!.


Ummey Daddy yau zakuji miye yasa nake biyewa Husain bamu zaman Aure kamar yanda kuke so, Ummey ke uwa ce ta gari kuma ni a matsayin yarki nake, shin taya kike tunanin yarki zata yarda ta zauna da mijin da yake kiran ta da sunan karuwa! ? Ummey ada can bana damuwa da wannan kalmar dan ban san mi kalmar take nufi ba, saboda *A GIDANTA NA GIRMA* ita wannan kalmar amman kasun tuwa ta daku sai na fahinci cewar mummunar kalmar ce, ada ina d'aukar shirmen mune nida shi kafin muyi Aure amman ana d'aura muna Auren yaci gaba da kira na da wannan kalmar, har zuwa yau d'in nan! ".


Kuka Husnah ta 'kara fashe wa dashi tace, "Ummey a yanda naji wani malami yana fad'ar zargin zina yana 'bata Aure dan haka nikam wallahi ba zan yarda na zauna da irin wannan mutanen b! ".




Ummey ce ta tashi ta ri'ko Husnah ta kalli Husain tace, "ashe dai Husnah tafi ka sanin gaskiya, Husain ka bani mamaki sosai dan haka, a matsayina na mahafiyar Husnah na yanke wannan alakar taku, saboda 'yata ba karuwa bace kuma zargi daman yana 'bata Aure dan haka Auren ku ya 'bace, kaje gurin Amaryar ka wadda kake so ka kawo mani takardar 'yata da kuma sanar dani saki nawa kayi mata! "


Ummey na kaiwa nan taja hannun Husnah zasu bar gurin, Anty Zarah ta ce, "Ummey dan Allah kiyi.... "


Ummey tace, "kudai yi hakuri keda kanen ki wanda baku son gaskiya kuma ku koma islamiyya".



Kawai Ummey tayi tafiyar ta da Husnah na jikin ta.


Husain da ido yake bin Ummey har ta 'bace wa ganin sa, jiyowa yayi ya bud'e baki daker zaiyi magana da Daddy, Daddy ya ce, "kada kace dani komai malam dan haka hukunci yayi kyau ina goyon batan gaskiya na godewa Allah daya sa Husnah tafika ilimin addini ni kunga tafiya ta".



Daddy tashi yayi yabar gurin Yaya Yusuf kuwa cewa yayi, "Zarah kinga abunda nake fad'a maki kirika bin cike ki daina ganin laifin Husnah ki bin ciki Husain amman kika rufe idon ki dan haka yan zun wa gari ya waya? ".



Shima tafiyar sa yayi, Shaheed kuwa cewa yayi, nikam kunya ta kani ya tashi yayi tafiyar sa haka su Anisah suka bar gurin aka bar Husain da Anty Zarah kowa ya kasa furta kalma daya.




*Comment and share*



*A GIDANTA NA GIRMA*




*BY NANA: KHADEEJATU*

*_UMMU IHSAN_*


*SADAUKAR WA GA :- DUK KANNIN MASOYA NA NABOYE DANA BAYYANE INA SONKU SOSAI SON FISABILILLAH*


*YA ALLAH KAJIKAN BABA NA DA MAMA NA KAYI MASU RAHMA KA KYAUTATA MAKWANCIN SU KA SANYA SU A ALJANNAR KA TA FIRDAUSI BIGAIRI HISAB SU DA YAN UWA MUSULMI BAKI `DAYA.*

*AMIN YA ALLAH*


*To Alhdulillah Allah ya nufeni da dawowa gashi zamuci gaba daga inda muka tsaya*



*_Bismillahir Rahmanin Rahim_*

106~110
Anty Zarah ta dawo a kusa da Husain tayi 'kasa da muryar ta ta ce, "Husain shin da gaske ne kuwa abunda Husnah ta fad'a a yan zun? ".


'kasa yayi da kansa yana kallon Anty Zarah ya ce, "Anty Z kun yarki nakeji a yanzun tabbas ban kyautata maki ba, koda ace basu Daddy ne suka had'a wannan Auren ba, ai zanyi duba da irin yanda kike nuna mani soyayya da kulawa kamar wanda muka fito ciki d'aya, tabbas kuwa ni na zaman to butulu, wanda ya kasa saka farin ciki a cikin zuciyar ki, domin kuwa tun kafin ki yarda da Auren Yaya Yusuf nasan irin soyayyar da kike yiwa 'kanwar ki, kuma nine wanda yayi maki alkawarin nemo maki ita duk inda take tare da alkawarin bata kulawa ta musamman, amman kash! sai gashi na swaba wannan alkawarin nabi son zuciya ta, gashi Husnah zaman hakuri takeyi dani amman ke kullum cikin ganin laifin ta kikeyi a kaina, Anty Zarah ba zan boye maki ba ina jin haushin kaina da jin zafin kaina dan gane da kin faran ta maki Anty Zarah kiyi hakuri bazan iya zama guri d'aya dake ba a matsayin da nake ciki ba yan zun! ".




Tashi yayi da sauri yabar gidan, Anty Zarah kuwa dafe kai kawai tayi ta kasa attaka komai.


A can cikin d'akin Ummey kuwa lallashin Husnah takeyi tare da jaddada mata cewar zata amsar mata takardar ta sai ta Auri duk wanda take so, amman fa sai taga ta saki ranta ta cire damuwa a tattare da ita.


Husnah dai kwanciyar ta kawai tayi, har sai da Ummey taga tayi bacci san nan ta sauka saman gadon ta fara zarya cikin d'akin ta maida hannuwan ta a baya ta soma zuwa gurin madubi ta dawo bakin 'kofa, tana ta aikin tunani.


Husnah dake kallon Ummey sai duk taji ta bata tausayi, lallai Ummey takai Uwa har Uwa duk inda Uwa take Ummey takai can, haka Husnah tayi ta nata nazarin har tayi baccin gaskiya.



Daddy ne da Ummey suke tattauna akan wannan lamarin, Daddy ya ce, "Hajiya ada naso ace Husnah a cikin mu ta rayu amman gashi Husain ya 'bata Auren nasu, ni na rasa ina tunanin Husain ya tafi ina gudun zuciyar sa suka tafi shin wai ma ina irin yanda yake yiwa Zarah alkawarin zai kular mata da amanar Husnah suke anya ma kuwa Husain kan sa d'aya kuwa? ".



Ummey tace, "toh! Alhaji nifa wallahi Husain na kasa gane mike damun Husain ace kullum cikin kiran matar ka da karuwa kake, taya ma idan wata ce zata zauna da kai har ku kai irin wannan tsayin lokacin? "


Suna cikin maganar ne Yaya Yusuf ya shigo cikin damuwa yace, "Daddy dan Allah kuyi hakuri tabbas nasan Husain bai kyauta amman ni nasan abunda, zan iya yin wani abu akai dan Allah Daddy kudai na maganar saki a tsakanin su, wallahi bana kaunar jin irin wannan maganar dan Allah Daddy Ummey ku janye ta kawai ku dai bani dama, kunji? "



Shiru sukayi Daddy ya ce, "Husain son Husnah ne baya yi, ba komai ba".


Ummey tace, "aa wallahi yana son ta sai dai bai san da hakan ba, har sai ranar daya tayi nesa dashi, irin nisan da zai iya zaman to masa, ga 'koshi ga kwanan yunwa".


Dariya duk sukayi suka kitse maganar su, anan, Yaya Yusuf ya je ya duba Husnah wadda suke zaune dasu Anisah suna labari ita kuwa sai anzo gurin dariya take yin dariya amman bata saka masu baki ba a cikin labarin su ba.



Tana ganin Yaya Yusuf ta saki fuskar ta tace, "Yaya Yusuf ina yini ina yara na, wallahi nayi kewar su ba kamar Baby na, amman babu komai itama yar tawa ta gujeni".



Dariya Yaya Yusuf yayi yace, "lafiya lau Alhamdulillah Husnah ya jikin naki dafatar dai babu wata matsala? ".


Husnah gyada masa kai, sannan yace, "masha Allah, yauwa to ke Husnah tunda baby taki zuwa gurin ki ke ki shirya ki kai mata ziyar bazata gashi kuwa yau juma'a da wuri suka dawo school kuma taje anyo mata kitso nasan yan zun dai tana gida".



Mare masa baki Husnah tayi ta ce, "bazan je gidan ku ba, idan taso zata zo idan kuma bata zoba kanta dan gobe nake son zuwa gidan Mommy nayo mata wata d'aya ko sati ukku".


Ba Yaya Yusuf ba, hatta su Anisah sai da suka zaro ido suna kallon ta, cike da mamaki.


Da ket Yaya Yusuf ya saita kansa ya ce, "haba dai ina ma laifin kije kiyi mata kwana biyu ki dawo? "


Dariya Husnah tayi ta ce, "Yaya Yusuf da gaske na keyi fa wata d'aya ko sati ukku zan yo".



Anisah ce ta kasa daurewa tace, "kice dai zaki kwashe kayan ki ki koma gidan ta ko? ".


Shiru Husnah tayi tana nazari zuwa can Husnah tace, ", toh Yaya Yusuf ni wallahi kadaici nake son yi ko kuma nayi tafiya wani gurin inda babu kowa".


Shiru yayi yana kallon ta zuwa can yayi masu sallama yayi tafiyar sa ba tare da ya bata amsa ba.


Suhailah tace, "Anty Husnah mi zai hana kije gidan Yaya Shaheed tunda kuna shiri dashi da matar sa, ki dan kwana biyu ina ga kamar zaki d'an futa a can ".



Ajiyar zuciya Husnah ta saki ta ce, "ok to idan Shaheed din yazo zan bisa gidan nasan tun kun za'bi hakan kuna ganin kamar idan naje gidan Mommy yar gidan jiya za'a dawo ".


Dariya kawai sukeyi mata har dare da Shaheed yazo Husnah ta sanar dashi zata je gidan sa gobe da safe tayi masu kwana biyu, dariya yayi yace, "sai dai ki tashi mu tafi yan zun saboda daman muna kewar ki tunda ba gurin kowa kike zuwa ba".


Dariya Ummey tayi da yake ta san da maganar tafiya kuma farin ciki da jin gidan Shaheed din zata je ".


Tashi Husnah tayi suka je gidan Shaheed matar sa na ganin Husnah ta rungume ta cike da farin ciki, taja hannun Husnah suka zauna sai fira, sai gurin sha biyu suka kwanta.



Da safe ma tare suka had'a breakfast sosai Husnah taji dad'in zuwa gidan, satin Husnah d'aya tace zata dawo gida ai kuwa suka hana harda su 'boyewa Husnah trolley d'in ta, da ket dai Husnah ta zauna d'in.


Husain ne ya shigo cikin gidan ya gaida Ummey da Daddy su Anisah suka gaida shi ya amsa yayi zaune yana kalle_kale ya kalli wan can ya kalli kofofin d'akin duka shiru_shiru, zuwa can ya maida hankalin sa gurin Ummey, ya fara sosa kai yace, "Ummey".


Kallon sa Ummey tayi d'aure da fuskar ta, tace lafiya kuwa? ".

Shiru yayi yana kallon Ummey yayi kamar tausayi ya 'bata fuskar sa, yace, Ummey yunwa nake ji ko zaku sam mani abinci? ".


Kallon sa Ummey tayi tace, "babu shi ina abincin gidan ka, kuma ina yan aikin ku ina matar ka?.


Shiru yayi kamar yayi kuka, Daddy yace, "abinci ya 'kare mun cinye amman ga 'kannen ka nan suje su dafa maka koda Indomie ce".


Safiya ce ta tashi zataje ta dafo masa yace, "ki barshi kawai".


Kallon Ummey, Ummey tace sai ki dawo ki zauna tunda ya fasa ko? ".


Zama tayi, shi kuma a gidan ya yini sallah ce kawai yake fita yayi, kuma da ya gama sallar yake dawowa sai 'karfe goma da rabi ya koma gidan sa, tun daga wannan ranar kullum sai ya zo Ummey da Daddy kuwa da Yaya Yusuf da Shaheed duk suna kallace dashi.


Sai da Husnah tayi sati ukku ranar ta saka masu rigimar dawowa gida dole suka kawo ta gida.


Har dare suka koma gidan su A ranar kuwa Husain bai zo ba, da safe tun bakwai Husain yake zaune a cikin falon gidan nan yaci abincin safiya, Husnah sai 'karfe tara ta fito sanye take da riga da wando rigar iya cibi wando kuma ya kama ta sosai iya kwabrin 'kafar ta kanta kuma anyi mata kalaba ta, tana tafe hankalin ta a kwance, tazo ta wuce sa ta kawai tayi hanyar kitchen ta shige ta fara soya wainar fulawa.



Husain a hasale kishi ya rufe sa idon sa ya rufe ya ce, "kan uban can uban waye ya saka yarinyar can zuwa wani gurin ba tare da izini na ba, kuma dan tsabar wulanci ku dubi irin shigar da takeyi wato dan ta ga nayi shiru shine har take wulanci son ranta har tazo ta ra'bani ta wuce, ba tare da ta ko kalli inda nake ba, wallahi sai nayi maganin wannan rashin kunyar taki! ".


Tashi yayi fiiii ya nufi kitchen d'in ai kuwa kafin ya 'karasa Ummey ta dakatar dashi tace, "wallahi kada ka yarda kaje kitchen d'in nan saboda kai ba komai bane a gurin ta! ".



Husain yaja burki ya jiyo yana kallon Ummey duk jijiyar jikin sa ta tashi, Ummey tace, "Husnah! Husnah!! Husnah!!! Sauri Husnah ta fito da wainar fulawa a hannun ta ta zubo tace, "Ummey gani kwad'ayi na tsaya yi, fa kinga abunda na soyo saboda tsabar kwad'ayi".


Ummey tace, idan kika 'karasa zakuje gidan Alhaji Isma'il dan yaran sa sun dawo daga dubai dan Allah ki daure ayi wannan hidimar bikin tar bon su dake".


Husnah ta ce, "yeeee Ummey daman ina son fita wallahi kuma naji dad'in wannan maganar taki.... Idon ta ne ya sauka akan Husain wanda ya kafe ta da ido, d'aure fuska tayi tace, "Ummey zan shiga ciki".


Wuce Ummey tayi ta shige cikin d'akin su Anisah da sauri ta ajiye wainar fulawar ta haye saman gado ta dafe kirji tana sauke ajiyar zuciya kamar wadda tayi tsere da kura, duk ido suka zuba mata sai da ta dawo dai_dai sannan ta lura da kallon da sukeyi mata, Anisah tace, "lafiyar ki kuwa? ".


Share zancen tayi kawai ta sauka ta d'auki wainar ta, ta soma ci suma duk suka shiga sahun ta, Anisah tace da alama kin had'u da twin d'in ki ko? ".


Shareta Husnah tayi, Suhailah da Safiya suka saka dariya, Husnah ta share su.


Koda suka gama Husnah kin fita tayi, harkar su tayi, suka ta yi mata shegan taka ta'ki kulasu tashi sukayi suka shirya harda Husnah sukayi anko suka saka doguwar riga sukayi rolling suka fito Ummey sukayi wa sallama suka fita Husain kuwa yana ganin sun fita ya faki idon Ummey yabi bayan su suna zuwa zasu shiga ke nan ya saka hannun sa ya janye Husnah ya ri'ke ta da karfin gaske tana ta son ta kubce ya kiya, yace, "zaku iya tafiya kuma wallahi duk kuka sanar da Ummey sai naci uban ku dukan ku".


Babu yan da suka iya shiga motar sukayi suka ja suka wuce, Husnah kuwa duk haushi ya kama ta janta yayi ya shigar da ita cikin motar sa da sauri ya rufe da sauri tazo zata fito yayi saurin shiga yaja motar da 'karfi Husnah kuwa tace, wallahi duk abun mutum nafi karfin sa, kuma ba zan zauna dakai ba, kuma ko yan zun da ka sato ni, nafi karfin ka, dan ko 'kafar samarin da nake taraiyya dasu baka kai ba".



Cike da zafin kishi Husain yaja motar sa ya bata wuta, wani irin horn ya danna wanda sai da mutane suka rud'e harda Husnah sai da ta tsorata da sauri ta rufe kunnen ta, masu gadin gidan ne suka bud'e 'kofar a tsorace, yaja ya fita da gudun sa, dai_dai fitowa Ummey da Daddy, cike da mamakin wannan uban horn d'in da ya doka, tambayar masu aikin tayi mi ya same sa, suka ce, matar sa ya d'auka suka fita.


Kallon_kallo su Ummey suke yiwa junan su Daddy yace, "kin dai yarda da zan na ko? "


Ummey ta ri'ke baki, tace, "ai dole na yarda wannan maganar kunyar yaron, ai naso ya 'kara horuwa ka dubi yanda ya dawo kamar wani sakarai yana neman inda take ya kasa magana dan yasan babu wanda zai bashi amsa, kuma fa harda ciwo yayi, mutanen da harda korar yan aikin sa yayi saboda ya gano cewar sune suka kira ni akan ana rigima shida Husnah ".


Dariya Daddy yayi yace, "to Allah dai ya kaisu lafiya duk inda zasu amman wannan uban gudun haka? Nifa yarinyar tausayin ta nakeji wallahi"



Hanya suka d'auka suka nufi wani uban gida hadden gaske horn yayi da sauri aka bud'e masu 'kofar gidan da 'karfin sa ya shiga gidan ya taka burki ji kake kiiiiii...., har 'kura na tashi,


Ko kallon inda Husnah take bai kalla ba, bud'e 'kofar motar yayi yafita ya dawo ya bud'e wa Husnah 'kofar inda take ai kuwa ta d'auke nata kan tace, "babu inda zani nikam kama mai dani gida wallahi" .


Ai kuwa kowa ya tattare hannun rigar sa ya dawo dai_dai jikin motar ya d'auke ta, ya d'ora a ka fad'ar sa ya rufe motar da 'kafar sa, ai kuwa tayi ta wutsil wutsil da 'kafar ta da hannu ta, shi kuwa ya share ta yaje ya bud'e 'kofar gidan ya shiga da ita yana zuwa akan kujera ya dire ta, ai kuwa ta kwasa da gudu, shi kuwa yayi saurin rufe d'akin da remote d'in dake hannun sa tana zuwa tayi_tayi ta bud'e ya'ki bud'e wa dole ta hakura tayi zaune a gurin ta fashe da kuka.



Shigewar sa yayi ya barta a gurin tun 'karfe biyu har la'asar, sallah take son yi ta rasa yaya zatayi gashi har taji tashin motar sa, koda tashi tsaye taje jikin window shine ya fita cike da mamakin sa, tace, "mugu wallahi sai nabar wannan gidan, neman ruwan alwala, tayi ta kuwa sami fanfo tayi alwala, tazo tayi sallah har akayi isha'i bai dawo ba, tsoro ne ya kamata, da sauri ta nemi wani d'akin da tagani kusa da inda ya nufa gashi kanta ciwo yakeyi, gado ta gani aikuwa ta rufe d'akin tazo tayi kwanciyar ta gashi bata da waya a hannun ta sai ta 'kara jin wani sabon kukan a haka bacci ya d'auke ta.


Can cikin bacci taji ana ta'ba ta ai kuwa a fir gice ta tashi zaune tana zarar ido mutum ta gani, ai kuwa ta fasa uban ihu da sauri ya rufe mata baki yace," ke nine fa matsoraciya kawai".



Janye hannun sa tayi, ta matsa nesa dashi, dariya yayi yace,"kiji da zazzabin dake damun ki yarinya kafin nima na d'ora maki wani sabon ciwon dan naga alamar ba wani 'karfi ne dake ba kamar yan da kike cika baki, wai har ni kike kwatan tawa da 'kadan garun bariki wallahi yau sai kin gane da ban_ban ci".


Tashi yayi ya dawo ya ajiye mata ledodi, yace Amarya ga kajin amarci nan da ango yake kawowa ranar farkon Auren su, ga kuma abinci nan nasan kina jin yunwa kuma ga magani nan nasan kina jin zazzabi".



Tashi tsaye Husnah tayi tace, "wannan duk mafalki ne kakeyi dan haka tun wuri ka cire wannan maganar da ranka ni nafi karfin irin wannan shirmen naka, kuma ka sani nida kai sama tayi wa yaro nisa".



Dariya yayi yace, "malama bisimillah ko ki kwantar da hankalin ki ko kuma ki tada hankalin ki labari ba zai chanza ba".



Kallon sa Husnah takeyi cike da mamakin sa yau ya dawo mata sam ba Husain din da ta sani ba, har ma ta fara tsoron sa, lokaci d'aya,

fita d'akin yayi ai kuwa da sauri taje ta rufe 'kofar ta dawo abinci taci taje tayo wanka ta dawo tana neman kayan da zata saka bata

Please Login or Register in order to submit comment