Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dafe goshin ta tayi fa hannun ta, su Anisah sai kukan ya 'karu daman kukan rashin ganin Husnah sukeyi.


Daddy yace, "ya Allah kaine mai iko akan komai ya Allah ka tona asirin wanda suka sace mani yara, ya Allah ka tsare mani yara na a duk inda suka tsinci kansu".


Kowa yace, "amin"


Neman duniya anyi wa su Husain Amman kuma labari, gidajen tv radio jaridu da mujjalu duk neman su ake ta internet, kasuwan ni asibitoci da dai sauran su amman kuma babu wani labari, Anty Zarah kuwa ta dawo kurma tun lokacin da taji labarin harda Husain an sace sa a asibiti sai ta dawo baci ba sha ba magana sai an matsa mata, su Shaheed da matar sa sun dawo gida, Mardiyya kuwa har yan zun tana asibiti gashi har anyi sati d'aya.



Kowa ya rame yayi d'an wuya saboda babu kwanciyar hankali.

Ko ina ka zaga gari da wajen gari neman su Husnah da Husain akeyi.


Gidan Daddy ya dawo gidan ku rame kullum cikin sadaka da salloli da addu' oi suke.


Kowa yayi zurfi cikin tunanin shin ina su Husain da Husnah suka shiga ne? Su waye suka sace su? Miye dalilin sace sun? kuma wane laifin ne suka aikata har hakan? .....



*Comment and share*




*A GIDANTA NA GIRMA*



*BY NANA: KHADEEJATU*

*_UMMU IHSAN_*


*SADAUKAR WA GA :- DUK KANNIN MASOYA NA NABOYE DANA BAYYANE INA SONKU SOSAI SON FISABILILLAH*


*YA ALLAH KAJIKAN MAHAIFINA KAYI MASA RAHMA KA KYAUTATA MAKWANCIN SA SHIDA YAN UWA MUSULMI BAKI `DAYA.*


*YA ALLAH KA BAIWA MAMANA LAFIYA KA BAIWA DUK KANNIN WANDA BAIDA LAFIYA NA GIDA DANA ASIBITI ALLAH KA BASHI LAFIYA AMIN YA ALLAH*




*_Bismillahir Rahmanin Rahim_*


91_95

Kawai Yaya Yusuf ya tashi tsaye da sauri ya ce, "Shaheed akwai gagarumar matsala sai yan zun na tuno da maganar da Zubaidah tayi akan Husnah cewar ta d'auki burika masu tarin yawa akan Husnah, haka kawai rana tsaka, tace zata guje mata? To wallahi sai ta tabbar mata da cewar ita tsohuwar yar bariki ce dan bata isa ta kunya tar da ita ba a cikin taron mutane ba, wanda basu san cewar 'karya takeyi masu ba akan cewar itace ta haifi Husnah da cikin ta, duk mutane sun yarda sai yanzun rana tsakiya ta zo ta yi mata wanan tonon asiri?"


A take Shaheed ya ce, "tabbas kuwa babu ko shakka itace ta aikata hakan domin daga ganin Zubaidah komai zata iya aikata wa akan cikar burin ta".


Daddy ya ce, "Tabbas ko shakka babu sai yanzun ne ma na tuno da cewar Husnah na cikin tarko, a baya mun d'auka abun ya wuce ashe ba haka bane, a gaskiya mun tabka babban kuskure, tunda muka bari Husnah tayi nesa da mu! "


Ummey ta nisa tace, "humm to Alhaji ai ba sakacin mu bane saboda Husnah koda tana cikin gidan nan zasu iya zuwa su aikata abunda suka aikata yan zun tunda makamai ne dasu, ba haka suke ba".



Kowa ya ce, "hakane kam gaskiya yan zun ta wace hanyar ne zamu bullowa wannan al'arin ne? ".


Shaheed ya ce, "Daddy kamar yanda nayi bin cike a wan can lokacin har na gano gidan da Husnah take to ko a yan zun hakan ce zata sake faruwa kudai kawai ku taya ni addu'a Allah yasa mu gano su cikin 'koshin lafiya ".


Shiru kowa ya yi suna nazarin wannan maganar ta Shaheed kafin Anisah ta ce, "Yaya Shaheed kai d'aya wannan aikin ba zaiyi dad'in yi ba, amman ni kuma zan shiga cikin aikin kodan, halaccin da Husnah tayi muna, duk yan da bata shiri da Yaya Husain Daddy ne kawai ya bata umarnin Auren sa, amman ko kukan tozarta maganar Daddy batayi ba, uwa uba ceton da tayi muna na ceto rayuwar Daddy, dan haka nima saboda Husnah zanyi wannan aikin a ma daina maganar Husain ace dan yana d'an uwa na ne".


kallon ta kowa yakeyi, Daddy ya ce, "a a Anisah kiyi zaman ki, sai dai ko Yusuf ya taimaka wa Shaheed d'in ".


Kuka Anisah ta sanya masu ai kuwa dole suka amince mata tare da addu'ar fatan nasara, Yaya Yusuf kuwa nasa shirin yakeyi Anty Zarah kuwa iya kacin ta dasu ido.


Haka su Anisah suka fito tayi shigar ta, ta dau wanka sai 'kamshi takeyi ga jaka ta rataya, mota suka shiga su biyu Shaheed ne ke tu'ki sun sha addu'a sosai kafin su fita daga cikin gidan har suka bar gidan ana yi masu addu'a.


Hanyar gidan su Zubaidah suka nufa a nesa da gidan sukayi parking a gefen titi, Shaheed ne ya fito yana duba mota ya bud'e gaban motar yana duddubawa, motoci da mashin sai wuce su sukeyi, Anisah ce ta fito ta rataya gyalen ta a kafad'a, sai gilas da ta saka a idon ta, no respect ta fito tazo a kusa da Shaheed ta dafa motar tace, "bro ina fatan ka lura da wata mota a bayan mu can nesa kad'an damu a anyi parking d'in ta da alama mu ake bibiya dan tun d'azun na lura da ita".



Shaheed ya ce, "a ankare nake shi yasa nayi parking a dai_dai nan gurin na ga ko sune suke bibiyar mu".


Murmushi Anisah tayi tace, "Yaya Shaheed ashe dai kana da target, amman ba wannan ba, yau nayi maka kama da Husnah kuwa? ".


Tayi fari da ido, Shaheed ya bushe da dariya ya ce, "kai Anisah kin cire mani kewar yar kanwata 'yar gayu, kefa sai da mata ta ta ce sai na ri'ka barin ta, tana d'auko karatun gayu gurin Husnah, nine na hane ta, saboda nafi son sai sun dai na mugun halin su, tukuna mutane kamar wanda ba mutane ba, kamar dutse, ace mata da miji suyi wata bakwai amman babu wata sha'kuwa sai ta 'boye wadda sai mai hankali ne kawai zai iya gano cewar suna mugun son junan su da ga ba'kin kishin da sukeyi wa junan su amman shirme ya hana su gane komai ".


Dariya duk sukayi Anisah ta bud'e baki zatayi magana ke nan, sukaji ance, "sannun dan Allah ko zan iya taimakon ku kuwa?".


Da sauri suka jiyo suna kallon mai maganar, magidan cine kimanin d'an shekara arba'in da biyar, ba wani fari bane fes kuma ba ba'ki bane ba, wankan tarwad'a ne , daga ganin sa kasan cikin futu yake ba cikin wahala ba, duk cikin yan sakwanni suka 'kare masa kallo.


Duk sai suka sha mur suka daina dariya, Anisah tace, "malam babu wata sallama zaka wani ce zaka taimakon mu, to mun gode masu taimakon mu sunje koyon sallama ".


Kallon Anisah yake cike da mamakin tsiwar ta, Shaheed kuwa ya ce, "a'a mun gode ai har mun gyara yan zun zamu wuce, mun gode da kulawa".


Murmushi mutanen yayi ya ce, "kuyi hakuri Assalamu Alaikum ya baiwa Shaheed hannu, Kallon_kallo aka shiga yi tsakanin Shaheed da Anisah, zuwa can Shaheed ya bashi hannu suka gaisa, bayan sun saki hannun juna ne, mutanen ya ce, "idan ba zaku damu ba, sai naga kamar ba saurayi da budurwa ba, kuma ba mata da miji ba, kamar dai Yaya da 'kanwar sa".


Cike da tsabar mamaki suke kallon sa, Shaheed ya ce, "to kodai munyi maka wani laifin ne da har ya saka kake 'kare muna kallo? ".


Gir giza masu kai yayi yana murmushi, Anisah tace, "to malam ba dai gayyatar ka mukayi ba, inma saurayin da budurwa ne ko mata da miji ko 'kanwa da Yaya miye naka a ciki? Nifa bana son rainin hankali irin na mutanen zamani".


Murmushi ya sake yi, yace, "da alama sai naga kamar ke ce wadda zan Aura bayan rashin tawa masoyiyar wadda nake mugun 'kauna anshi waya ta saka mani number ki" wayar sace ya mi'kowa Anisah gashi wayar haddiyar gaske da ita.


D'auke kai Anisah tayi daga baya kuma ta jiyo tayi murmushin takaici tace, "oh! Ada ka d'auka bani da masoya ko ya nufin ka, ko ka d'auka cewar ni irin matan nan ne makwad'aita? to indan wannan kallon kakeyi mani ka sauya, kuma sai anjima malam!"


Ba mutanen ba hatta Shaheed sai da yayi dariya saboda yanda Anisah ta zage sai masifa takeyi daga maganar arziki.


Mutanen yace, "da alama zakuje gidan Zubaidah neman Husnah ne ko? "


Yayi maganar yana murmushi yana kallon yanayin fuskar su, Shaheed ya ce, "kamar ya kuma waye kai!? ".


Anisah tace, "da alama wannan shine dalilin da yasa kake ta bibiyar mu tun lokacin da muka fito daga gida, to waye kai? ".


Murmushi yayi yace, "zan taya ku neman Husnah amman kuma kafin nan, sunan da nasan wata kila kun san shi a gurin Husnah shine, Tk idan har kun ta'ba jin wannan Sunan a gurin Husnah to nine Tk ".


Dukan su mutuwar tsaye sukayi, Shaheed ya ce, "kana nufin kaine wanda ya d'auki nauyin Husnah tun lokacin da aka zo da ita a garin nan? ".


Dariya Tk yayi yace, "sosai ma kuwa kuma ni kaina Husnah tayi mani nata taimakon domin ita ce sanadiyar shiriya, nagano hakan ne tun lokacin da nayi bin ciken wanda ya aikata hakan a gareni domin na kyautata masa".


Anisah kam yanzun tayi shiru bata sake cewa dasu uffan ba.


Shaheed ya ce, "amman taya kasan muna neman Husnah ne? ".

Tk ya ce, "saboda nasan irin son da kukeyi mata, tun kafin ta Auri Husain d'an uwan ku".


Anisah tace, "amman kuma duk da kasan da cewar Husnah matar Yaya Husain ce, to Yaya akayi kake bibiyar rayuwar mu? "


Murmushi yayi yace, "saboda Husnah ta zamo mani 'kanwata, tajini ne saboda nasan bata da kowa, kuma nasan halin Zubaidah zata iya aikata komai akan rashin Husnah a tare da ita saboda Husnah ita ce jarin Zubaidah, dan Zubaidah ta d'auki dogon buri akan Husnah, tun lokacin naso na d'auke ta na ceci rayuwar ta, amman kuma sai kuka zo kuka fini 'karfin a gurin Husnah, ni kuwa saboda yanda naga kuna bata kulawa sai na ji dad'i na zuba wa rayuwar gidan ku ido ".


Tk yaci gaba da fad'ar, "sace Husnah da Husain kuwa a gari naji da jaridu da gidan redio, sai na fara bibiyar rayuwar ku saboda nasan ba zaku iya yin shiru ba, sai kun aikata wani abun shine yasaka nake bibiyar ku"


Ajiyar zuciya suka sauke baki d'aya, Shaheed ya ce, "to yan zun ta yaya ne zamu samu shiga gidan Zubaidah neman Husnah da Husain? "



Tk ya ce, "Zubaidah tana gidan ta, yanzun haka kuma nasan ba ita d'aya take ba, kawai ku zo mu tafi tare, nasan idan a tare muke ba zaku sha wata wahalar shiga cikin gidan ba".


Haka kuwa akayi Shaheed da Tk sune gidan gaba, Anisah kuwa tana can baya bakin ta cike da addu'a.


Suna isa 'kofar gidan Zubaidah masu gadin gidan ne suka zo koda suka duba Tk suka gani a take suka sara masa harda su kirari, kud'i ya d'auko batare da ya duba ko nawa bane ya basu, cikin farin ciki suka amsa sai godiya da murna da farin ciki addu'a kawai suke zuba masa, bud'e masu 'kofar akayi suka shiga cikin gidan, suna yin parking suka fito suka shiga cikin falon gidan kamar yanda Tk ya fad'a hakan ta faru kuwa, domin Zubaidah ce zaune ta rabka uban tagimi ga mutane maza da mata cike da falon kowa da abunda yake aikata wa.


Zubaidah na ganin Tk tawani irin tashi tsaye ta daki kirji ta ce, "Tk...! Daman kana sane da gidan nan baka manta dashi ba?, kodai wani abun ne ya kawo ka, idan ma Husnah ce kazo nema, tofa lallai ne nida kai muhad'a 'karfin mu guri d'aya muje gidan da suka d'auke ta mu yankar masu sammaci domin kuwa naga sanawar sace tan da akayi har cikin gidan ta! ".



Kallon_kallo aka shiga yi tsakanin mutum ukku Tk Shaheed Anisah, mutanen cikin falon kuwa kallon su kawai suke duk sun bar abunda sukeyi sun dawo da hankalin su akan su Tk.



Shaheed kuwa ya ce, "kada ki rainawa mutane da wayau malama ko kin manta cewar Husnah ta ce, *A GIDANTA NA GIRMA* ba wai tana nufin cewar ke ce mahaifiyar ta ba, kuma idan ma ke ce kika saka aka sace Husnah da mijin ta Husain to kisani kin d'ebo ruwan dafa kanki! ".


Da sauri Zubaidah tace, "eh lallai muna fukai tunda kun rabani da 'yata kun siyar da ita ai dole ne kuzo ku zargeni dan kada duniya ta zageku".


Anisah tace, "wannan maganar da kikayi ita ce take bamu tabbacin cewar kina da sa hannu gurin sace Husnah da mijin Husain saboda tsabar ba'kin cikin da kike ciki na Husnah ta juya maki baya".


Zubaidah tace, "ke kuwa uban waye ya saka bakin ki a cikin wannan maganar da dake ake yin ta ba? ".


Anisah ta ce, "da dan kada na zageki wata rana na Husnah taji labarin hakan ba, ta d'an 'bata rai da kuwa kinga aiki da cikawa sai dai kash farin cikin Husnah shine namu farin cikin shi yasa zan iya d'aga maki 'kafa, da sai kin gane babban cin Husnah da Anisah!,


Sannan kuma ki sani Husnah 'yar dangi ce gaba da baya, kodan kinga kunje gidan su kun sato ta, kike ganin kamar bata da kowa,? to idan ma haka kike tunani abun ba haka yake ba,



Bari in sanar dake abun da baki sani ba, yan zun haka Baffan nin Husnah da goggo nin ta harda wadda kukayi 'karyar ta aiko ku, to duk muna tare dasu uwa uba ma, Yayar Husnah wato wadda ki kaji Husnah na kira da Anty Zarah, dukan su,


idan ma har kin musan ta hakan, zaki iya bin cike ki gano gaskiyar, lamari dan haka ki ma dai na ala'kan ta Husnah da wannan kazan tacciyar rayuwar, Husnah yar halak ce mai cikakken hankali, addu'ar mahaifiyar tace ke tattare da ita shi yasa kike ganin bata yin irin abunda kike yi, dan haka malama tun kina da sauran dama, kije ki nemi yafiyar iyayen ki, da yafiyar Allah ki kasan ce, cikin tuba, kuma tuba ta gaskiya, ba tuban mazuru da kaza a bakin sa ba,

San nan kuma magana ta 'karshen da zanyi maki, shine ki fito muna da "yan uwan mu, ko zaki ga dai_dai a rayuwar ki, ta duniya da lahira, ni kinji abun da kawai zan iya sanar dake! ".


Ba Zubaidah ba hatta Shaheed Tk da mutanen dake gurin cike suke da mamakin 'karamar yarinya wadda bata wuce tsaran Husnah ba, ace itace ke irin wannan maganar ta masu hankali.


Tk ya ce, "to malama Zubaidah kamar dai yanda kikaji Mata ta ta fad'a to haka abun yake ki tuba ki nemi yafiyar iyayen ki ki ajiye duk wasu alfasha da kike ina mai tabbar maki da cewar wallahi sai kinji dad'in sabuwar rayuwa, kuma Husnah da Husain idan kin san inda suke, ki sanar damu, idan kuma wani abun kike da bukata ko nawa ne to kiyi bayani kin sani ni mai iya baki ko nawa ne".


Zubaidah tun lokacin da Anisah ta fara magana jikin ta yayi sanyi kuma ta yarda da cewar baffan nin Husnah suna nan da ran su harda antyn Husnah, to abun mamaki ma wai ace 'karamar yarinya ce keyi mata irin wannan kalaman masu shiga jiki, uwa uba ma Tk wanda yayi masifar bata mamaki.


Anisah ta ce, "kai dubi mutum haka kawai zaka wani kira na da matar ka?, matar ka na gidan ka ka baro ehey".



Shaheed ne yayi murmushin da bai shirya ba, ya ce, "Anisah dawa sa fa yake yi maki ".


Murgud'a baki tayi Tk ya ce, "aboki da gaske na keyi ta bari na aika da kaud'in Auren ta, tace, "ba zata Aure nin ba".


Anisah ta ce, "Allah ya sawa'ke nikam na Aure ka, ina da wanda nake so kuma shine za'bi na, ba wani can ba daga had'uwa rana d'aya ".


Maganar Zubaidah ce ta katsewa Tk han zari, tace, "eh kam nasan da batan Husnah da mijin ta, amman babu hannu na a ciki, ada nayi farin cikin faruwar hakan, amman kuma yau, naji haushin faruwar hakan, nasan wanda ya sace Husnah da mijin ta, ku shirya makaman ya'ki dashi domin kuwa shi gagara ne ya gagari mutane da dama, har jami'an tsaro sun kasa iya wa dashi dan haka kodai muyi masu addu'ar fitowa lafiya daga gurin sa, ko kuma mu ja masu damu kanmu da yan uwan mu shiga cikin hatsari, domin mutum ne mai matu'kar hatsarin gaske".



wata daga cikin 'kawayen Zubaidah ta ce dasu, "kuma dai yi hakuri domin yan zun nan daga cikin mu an samu in formers din sa sun sanar dashi cewar ana shirya yanda za'ayi a zo gurin sa a ya'ke sa cikin su kuwa harda Zubaidah, ga sa'kon da aka turowa muna nan cewar muma yan zun haka muna cikin hatsarin gaske ".



ga baki d'aya gurin ya d'auki shiru, Anisah ta nisa tace, "koma dak waye shida Allah ne mun bar mutum da Allah, ya Allah duk wanda ya sanar da wannan azzalumin mutun abunda ke faruwa, Allah ka had'a shi da mugun ji da mugun gani, koda fushin wannan azzalumin mutumen ne! ".




Zazzare ido aka farayi a gurin, a take wasu daga cikin gurin suka fara tashi suna fita daga gidan, cikin mutum sha bakwai sai da aka bar mutum biyar har gami da Zubaidah.


Su Shaheed kuwa mamakin irin kalaman Anisah sukeyi a ina ta samo su.

Anisah kuwa dariya tayi tace, "bro wannan aikin Husnah ne ita ce malamar mu nida Suhailah da Safiya, dan na fahimci kana cike da mamaki na".


Ajiyar zuciya Shaheed ya sauke Zubaidah kuwa cewa tayi, "tuni na fahimci hakan daga gareki, yan zun ku tashi ku bar gidan nan, zan sameku a gidan ku zan zo da wasu bayane na wannan mutanen sannan sai kunyi hakuri dan zan dad'e ban zo ba, kudai kuci gaba da yi masu addu'a ".


Amsa mata sukayi badan sun yarda da ita ba, suka koma gida suka sanar da kowa abunda ya faru har had'uwar su da Tk, su Daddy sun jin jina al'amarin, haka sukaci gaba da addu'a.


A can wani gurin kuwa?


Husnah na ce kwance jikin ta da bandeji kwance take akan wata jibgegiyar kujera mai kamar gado kuma ba gado bane sai laushi, ga sanyin A/c na ratsa ta tako ina gurin sai 'kamshi ke tashi.

Motsawa ta soma yi ta saka hannun ta, ta dafe hannun ta, ta bud'e idon ta ta soma biyar ko ina da ido tashi zaune tayi a zabure, ganin gurin da take kwance a halin yan zun sai ta shiga cikin mummunan tashin hankalin saboda tsin tar kanta tayi a 'kasar da tasu ba, duk irin had'uwar gidan su sai taga ba komai bane, sauka tayi a 'kasa d'akin duk glass ne ta ko ina, hankalin Husnah ya kai matu'kar tashi, jin zugin da hannun ta yakeyi ne ya saka Husnah duba hannun a take ta tuno abunda ya faru kawai ta dur'kusa 'kasa ta fashe da kuka ".



Husain kuwa bud'e idon sa ke da wuya ya soma ganin hazo_hazo jiri_jiri duhu_duhu fankar dake li'ke a sama ita ce ke juyawa, shi kuwa jin yakeyi kansa na juyawa dafe goshin sa yayi kansa na yi masa mugun ciwo kan nasa nad'e yake da bandeji, tashi zaune yayi gurin da ya tsinci kansa ne ya 'kara d'aure masa kai dube_dube ya farayi d'akin glass ne kuma inda yake zaune carfet ne tsanwa mai ruwan ciyayi, mamaki ne fal ransa, dafe kan nasa yayi da hannun sa duka biyun.


Wata 'yar 'kara ce ya jiyo daga bayan sa kawai ya d'ago kansa a hankali ya juyo, mutane ne su biyu murtu'ke da fuska jibga_jibga dasu babu alamar tausayi ko nan da can, suna 'karasowa kawai suka saka hannuwan su suka tallabe Husain wanda yake ta kokarin su sauke shi 'kasa amman ina ko sauraren sa basuyi ba , sukayi waje dashi, gashi sunyi masa ri'kon bawa da maigida basu ajiye sa ko ina ba har sai da suka shiga wani katafaren hadden falo ma girman gaske, a gaban wani mutum ne suka sauke sa da 'karfin gaske har sai da yace wash!.


Husnah kuwa tana cikin kukan ta, wata tsohowa ce ta ce, "yata taso muje kiga wani abu".


Husnah na ganin wannan matar kawai ta tsare ta da ido dan ganin takeyi kamar mafalki takeyi, hannun Husnah ta kama ganin Husnar ta zama status da ita, cikin falon akayo da ita inda aka ajiye Husain a nan aka ajiye ta, a gaban wani mutum wanda bai d'aga fuskar sa ba amman mutanen daga ganin sa kasan babu imani a tattare dashi.



Sun dad'e da zama babu um ba um_um, Husnah bata san da akwai mutane a gurin ba illah mutanen da tagani an ajiye ta a gaban sa sai kirjin ta ke dukan uku_uku.


Husain kuwa tun isowar Husnah ya maida hankalin sa akan ta, har ta zauna yanda take kallon mutanen ne yasaka shi maida hankalin sa, a can gurin.


Mutanen ne ya cire malfar da ya rufe fuskar sa da ita yana kallon su ya kalli Husnah ya kalli Husain, idon mutumen jawur dasu gashi ba'k'ki 'kirin dashi kamar bayan tukunya.



Wata irin dariyar keta ce ya bushe da ita ba bu dad'in sauraren ta hahhhhh, yace, "Husnah yau gaki ga mijin ki wanda baki da wani mijin bayan sa, nine yalla'bai d'in da kikaji zuby na fad'a nine wanda na tashi Auren ki, a ranar kika gudu, gidan su saurayin ki wannan kika 'bata mani suna a gurin abokan hulda ta" ya nuna gurin da Husain yake da hannun sa.


Gurin da yayi mata isharar ne ta maida hankalin ta, waye zata gani inba Husain ba, suna had'a ido dashi take suka d'auke idon su suka mayar akan mutanen.


Mutanen yace ya naga kunyi kamar baku san junan ku ba? Bayan nasan tunda ku ka zauna a guri d'aya har tsayin wattani bakwai ai nasan kun murji anarci da kyau tunda gashi har yan zun baku tashi haihuwa ba, nida naso na ganki da ciki, sannan na d'auke ki tare da mijin na saka a ciro mani dan a gaban idon ku, na saka wu'ka ta na yanka jin jirin nasha jinin sa, nasa a kaiku kichin a gaban idon ku a dafa mani naman nacinye duka, akan idon ku, amman kash! Hakan bai samu ba, to yan zun zan yi maku hukun ci irin wanda ya dace, kai goga! Ka saita Bindigar nan ka kawo mani ita a nan! ".


Da sauri wanda aka kira da goga ya cika aiki, ya kawo bindigogi guda biyu, ya ansa ya saita su ya halbi yaran sa guda biyu a hannun, ji kake darammm_darammm, su kuwa cewa sukayi washi, suka dafe gurin, sai jini ke zuba ido yayi kamar an watsa masu barkono.


Husnah da Husain duk sai da suka zabura, mutanen da yaran sa cike da d'akin suka bushe da dariya harda doka 'kafa.


Sai da sukayi dariyar su mai isar su, sannan mutanen yasha mur ya had'e rai yace, "Husnah keda wannan munafukin ku ri'ka kowa ya halbi dan uwan sa, gurin da yake so"


Mika masu Bindigar yayi yana d'aure da fuska, kin amsar Bindigar sukayi, kawai ya ce, "to ni zan halbe ku da kaina ta inda naga yafi burgeni ".


Mur yasha, ya saita Husnah a goshin ta, ya saita Bindigar d'aya a saiti da zuciyar Husain ya gyara zai halba da sauri suka anshi Bindigar suka tashi tsaye suna ri'ke da bindigogin a hannun su, tsawa ya daka masu wadda sai da Husnah ta zabura kamar zata fad'i 'kasa, daket ta saita kan ta, tayi tsaye, tsawar ya 'kara daka masu ya anso wata Bindigar zai halbesu, kawai sukayi saurin sai ta junan su da bindigogin Husain

Please Login or Register in order to submit comment