Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

naki ina tsafin da kike takama da shi?, wanda mutuwar maman mu bata zame maki ishara ba, mahaifin mu da kika mai dashi jela, yan zun nasan kin 'karasa kashe shi ko? Him to Allah ya shiryi masu irin halin ki".


Juyawa kawai baffah yace, "Marka ina kane na ko dai kin kashe sa ne?"


Wani mutum ne yace, "ai malam ya dad'e baya tare da Marka yayi Auren sa mai gari ne ya bashi kanwar sa wadda yake ri'ko kuma makotan sa sun bashi gidan da yake zaune harda sana'ar sai da magi an bud'e masa kuzo muje gidan sa, ita wannan tar ta kwana biyar bata magana, kuma ido d'aya ne ke da ita, kuma warin nan dake tashi a jikin ta, bamu san na miye ba, yaran ta kuwa ta riga da ta gama da rayuwar su, dan sun raba jaha da mahaifin su, sun za'bi uwar su".


Kaico kowa keyi da wannan rayuwar, tafiya sukayi gidan da baban su Husnah yake, da sallama su baffah suka shiga ita kuma Husnah kin shiga cikin gidan tayi duk sun d'auka Husnah tana tare dasu.



Cike da matu'kar mamaki Baban Husnah yake kallon su baffah da sauri ya zo inda yake ya ri'ke sa ya fashe da kuka, haka gurin ya d'auki kuka, sai da baffah yayi magana akayi shiru, baffah yace, mun sameku lafiya? "


Gaishe gaishe akayi wanda bayan an gama gaisawa, baffah yace, to ga ya'yan ka Zarah da Husnah, da sauri Zarah tace, ya'yan sa suna can tare da Marka mu ba ya'yan sa ba ne muda yake duka bayan mutuwar mahaifiyar mu, ma bai sauya ba sai karuwa, dan haka nikam".



Baban su Husnah tashi yayi ya durkusa, a gaban Zarah zai fara magana da sauri Zarah ta tashi ta fad'a jikin sa tana kuka, Daddy ya ce Husain ina matar ka take ne? "


Da sauri ya tashi ya ce, "him Daddy kadai san halin Husnah bari na shigo da ita ".


Baban Husnah yace, "indai Husnah ce bazata shigo ba saboda Husnah tun tana 'karamar ta bata shiri dani, kuma idan tace ba zatayi abu ba tofa lallai ne bazata yisa ba, amman ni zan sameta da kaina ".


Haka suka fita 'kofar gidan basu gan taba har hankalin Husain ya tashi Baban yace, indai Husnah kada ka damu zo muje, su Daddy ma biyo su sukayi cike da alhinin, rashin ganin Husnah, tshon gidan su ya shiga tare dasu da Daddy, d'akin su Husnah ne ya gani a bud'e yace, "Husnah kiyiwa Allah ki ajiye komai kibar ni na shigo cikin d'akin nan, wanda rabon da na shige sa tun kafin mutuwar mahaifiyar ku".


Anty Zarah ce ta shiga cikin d'akin da gudu, Husnah ce ta isko ri'ke da sarka da yan kunnen da maman su take so sai har take sheda masu irin son da take yiwa yan kunnen, ai kuwa Anty Zarah da sauri itama ta d'auki kayan ta fashe da kuka kamar yan zun ne mutuwar mahaifiyar tasu, Daddy dake tsaye a waje duk mu shiga ciki ganin halin da suke ciki ne ya baiwa Yaya Yusuf da su Husain tausayin su, gurin su suka 'karasa Baban su Husnah ya matsa shima ya anshi kayan yace, "tunda ba addu'a zakuyi mata ba, ku kawo kayan na zubar" da sauri suka share hawayen idon su Husnah tace, bayan kayi farin cikin mutuwar mama na kwana d'aya akayi jimamin rashin ta, a gidan nan amman kuma, kuka ci gaba da jin dad'in ku, kuci abinci mu kuwa mu zauna da yunwa, kokon da mune muke damashi amman mune ake baiwa wanda kudaje suka bi wanda yayi datti dan dai kawai lokacin mutuwar tamu ba yi bane, shine yan zun kake cewa zaka rabamu da abu mai muhimmanci a rayuwar mu, baka zama damu baka sauraren mu, naira biyar taka baka bamu, zagi da duka ne tsakanin mu da kai, haba dai".



Baban yace, "Husnah ki fad'i duk abunda yazo bakin ki nasan duk na aika ta shi amman dan Allah kiyi hakuri bada son raina na aikata maku hakan ba kuma kullum cikin kukan rashin matata nakeyi mace ta kwarai mai afuwa shin miya sa Husnah ba zaki gado da ita ba ne? ".


Da sauri Husnah taje ta fad'a jikin sa tana kuka wanda kowa ya tausaya masu.


Haka dai su Husnah suka yafi mahaifin su shima ya yafe masu, matar sa kamar itace ta haife su, da zasu tafi kamar kar su rabu.



Koda suka koma garin su akayi bikin su Anisah aka kaisu gidajen su lafiya su Husnah kwana biyu suka dawo gidan su ba tare da sun sanar da dawowa war suba, sukayi mugun gani, dan Zee ce ta kwarto kwance a saman kujerar falo, zigidir haihuwar uwar su.


Wani irin tsanar su Husain yaji a take ya d'auko wayar cabur yaci uban su ya saki Zee a gurin kuma yace ko tsinke bazata d'auka ba, a haka tabar gidan.


Cikin kunci yake da ket Husnah ta samu ya sauka, tun daga wannan ranar ne suka dawo da soyayar su, watan Husnah d'aya da dawowa ta fara ciwo, sukaje asibiti aka sheda masu cikin Husnah boye, wa yayi yan zun ne ya fito watan sa hud'u, murna da farin ciki gurin su ba a magana, koda aka sanar dasu Ummey sunyi farin ciki sosai tare da fatan Allah ya raba lafiya.


Bayan wasu watanni Husnah ce ke lebour, Husain duk ya rud'e kamar ba Doctor ba indai akan Husnah ne, mancewa ma yakeyi da cewar shi likitane.


Nurse, ce ta fito tayi masu albishir da an samu baby boy, farin ciki harda sujada Husain yayi, da take lafiya ta haihu aka sallamesu suka dawo gida Ummey Zubaidah anyi Aure anyi hakali da ita ake Komai su Anisah kuwa ba 'acewa komai.

Su Baban Husnah da matar sa sun zo anan ne matar Baban Husnah wadda suke kira da mama tace, "wai kun san kuwa a ranar da kuka baro garin a ranar ne Marka ta haukace tabi daji, a she yaran nan nata "ya'yan bokan tane yazo ya kwashe yaran tare da sanar da ita cewar ai tunda ta bari su Husnah suka zo garin ita kuwa sai bar garin kuma bada yaran sa ba, kuma fa a gaban kowa hakan ta faru, kowa Allah waddai da masu irin halin ta suke yi"

Ai kuwa Husnah da Zarah suka ce Allah ya 'kara karemu da son zuciya"

Atake kowa ya amsa da amin.


Anyi biki lafiya Husnah kam an samu gudumawa a gurin yan uwa da abokan arziki, biki yayi biki, sai sam barka anyi taro lafiya an watse lafiya an samu Hanif

Su Baban Husnah sun koma garin su tare da sha tara na arziki.

Zubaidah ma tazo tayi barka ta zauna har akayi biki, mijin ta ya zo ya d'auke ta suka wuce.



kwanan su sitting aka maida Husnah d'akin ta, suna kwance sun saka Hanif a tsakiyar su, Husain yace har dai na tuno da Husnah lokacin da kike cewa, suka had'a baki gurin fad'ar *A GIDANTA NA GIRMA* .


*TO ALHAMDULILLAH NA GODEWA ALLAH DA YABANI IKON KAMMALA WANNAN LITTAFIN WANDA YA D'AUKI DOGON LOKACI BAN 'KARASA SABA SABODA RASHIN LAFIYAR MAHAIFIYAR FIYATA HAR ZUWA RASUWAR TA YA ALLAH KAJIKAN TA RAHMA KASA ALJANNA CE MAKOMAR TA ITA DA MAHAIFINA DA DUK KANNIN MUSULMI BAKI D'AYA* AMIN


INA GODIYA DA HA'DIN KAN DA KUKA BANI MASOYA NA ALLAH YABAR 'KAUNA. AMIN



*COMMENT AND SHARE*


Sai mun had'u a wani sabon novel d'ina mai suna...


*UMMU IHSAN CE*

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment