Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fashe saboda tsabar shiga cikin 'bacin rai.
Hajiyar kuwa dafa ka fad'ar Husain tayi, ta ce, "Husain kada ka sake kwatan ta abun da ka aikata, badan komai ba, sai dan gudun dana sa ni amman kabi komai a sannu kaji yaro na? ".

Jin jina mata kai yayi, haka suma suka jiyo zasu bar gidan Anisah ce, ta kula da wayar Husnah da sauri ta d'auki wayar tabi bayan su, da ita.

Husain yanda taga rana haka taga dare sam bata runtsa ba, kuka kawai takeyi kanta wani irin mugun ciwo yakeyi mata kamar ya rabe biyu, idon ta kuwa duk sun kumba saboda kuka.

Zubaidah kuwa yalla'bai ya kira ta yayi mata zagin kas, kanci kuma yace, idan ta bari aka batar masa da yaran sa, kuma ta yarda wani abun ya sami Husnah sai ya kashe ta, ita da duk wani wanda take tare dashi.

Jin irin wannan furucin na yalla'bai ne ya 'kara fir gita Zubaidah dan tabbas tasan duk abunda ya fad'a zai iya aikata shi akan su ita da 'kawayen ta.

Dukan su a zaune suka kwana, kuma yace Aure ba bu fashi a tsanin su.

Husnah kuwa tana nan zaune idan kayi mata kallo d'aya ba zaka ce eh lallai Husnar nan bace, yar gayu, d'in nan ba, sai ka dad'e kana kallon ta.


Ganin har 'karfe goma da rabi yan biki nata Shirin biki babu Amaryar babu labarin tane, yasaka mutane matsawa Zubaidah akan ta dibo Husnah indai bata samu wata matsalar ba, ko ta gudu, ba.

Zubaidah jiki ba bu karfi ta matsa 'kofar Husnah ta ri'ka dokawa, Husnah na jin dukan 'kofar tasan ba kowa bace face Zubaidah, kawai Husnah ta share ta, har ta gaji da dukan 'kofar ta soma kiran, "Daughter na ki bud'e 'kofar nan fa ina son ganin farin cikin ki ne a wannan ranar da a ke da d'aurin Auren ki fa gashi ina ganin har yan zun ba ki ci abinci ba"


Share ta Husnah tayi har ta gaji dan kan ta, ta bar gurin, sai kuma hankalin ta ya 'kara tashi dan tana tsoron abun da zai je ya dawo, makulli ta nemo, cikin zafin nama ta bud'e 'kofar, turus tayi ganin yan da Husnah ta dawo kamar wata ba'kuwa a gurin ta, 'karasa wa tayi gurin Husnah ta dur'kusa a kusa da ita.


Ta ce, "haba Husy baby miye matsalar da har kika zauna ki ke wahalar da kanki a kan abun da ba wani abu ba".


Ko kallon ta Husnah batayi ba, ballema tasa ran Husnar zata amsa mata ne.

Zubaidah ta ce, "Ki tashi kiyo wanka kici abinci a zo ayi maki makeup, kin ga yau ke Amaryar ce, kuma Amarya da farin ciki aka san ta, kuma ba bu wanda ya kai ta farin ciki ".


Ganin Husnah ta yi kamar ba bu ita a gurin ne, ya saka ta tambayar,Husnah ta ce, "Husnah ina wayar ki ne , naji yalla'bai ya ce, tun jiya ya turo maki kud'in hidimar biki kuma nasan kud'in da yawa, suke dan nasan baya maki 'karamar kyauta".

Jin Zubaidah ta cika ta da surutu ne, yasaka Husnah tashi a gurin ta haye saman gado sai tayi kwanciyar ta, zuwa can Zubaidah ta tashi zata fita, Husnah ta ce, "a jiya nasan mommy kina cikin farin cikin ganin za'a kashe maki ni ki futa, to yau kuma farin cikin barin gidan kine kike yi da zanyi, ko miye ? dan ni ban fahimci komai ba har yan zun! "


Da bur cewa Zubaidah tayi ta kama soshe_soshen rashin gaskiya, ta ce, "wato Husnah ni ba wai ina son kiyi nesa dani bane, a'a kawai dai ina son naga na aurad dake lafiya hankalin ki ya kwanta, kici naira ki taka naira ki wukanta na wulakan tawa".


Husnah kuwa shiru kawai tayi mata, har ta fita cikin sauri.


Husain kuwa kwance yake cikin d'akin sa, sai tsaki yake zubawa shi d'aya, zuwa can ya fita ya bar cikin d'akin sai d'akin Shaheed, shima Shaheed kwance, yake da alama tunani yake yi.

Bai ma san da zuwan Husain ba, har sai da Husain ya ce, "Shaheed kai ma waccan ban zar yarinyar ta saka ka a damuwa ko? Yan zun ka fahimci cewar mutum ba abun yar da bane ko? Yan zun ka gane cewar ita d'in babbar karuwa ce ko!?.


Wani irin kallo Shaheed yake bin sa dashi har sai da yaga ya tsaya Shaheed ya tashi tsaye ya rungume hannuwan sa, ya ce, "kai shine damuwar ka, kuma na fara fahimtar wani abun, wato kai dai kawai kace, karuwan cin ta, shine damuwar ka!?.


Husain ya ce, "eh ni kam na tsani wannan ka ruwar wallahi kuma idan na sake had'uwa da ita sai na kashe ta, kowa ma ya futa".


Jin_ jina kai Shaheed ya yi, kawai ya ce, "yan zun miye abun yi?


Husain ya ce, "abun yi kawai kada mubari a d'aura wannan Auren domin ba'a Aure ba'ayi istimna'i ba, dan za suyi Auren ne, cikin zunubi".


Shaheed wata irin dariya ce, ta zo masa, amman sai ya danne ta, amman duk da hakan sai da ya mur musa, ya ce, "a a mubar ta kawai tayi Auren ta yafi, wata kila ma ta shiryu, kaga sai ta rage wani lafin ko? ".


cikin fushi Husain ya ce, "inji uban waye ya ce mu bari a d'aura mata Aure wallahi ba bu uban da zai Aure ta ko shi uban waye a garin nan kai bama a garin nan ba duk 'kasar nan, yarinyar da ko tausayin mutane bata ji! "


Shaheed saboda dariya harda tarin karya wai dan kar Husain ya gane sa, amman a gaskiya ko shi baya goyon bayan Husnah tayi wani Aure dan ya fahimci yarinyar tana neman taimako dan akwai ayar tambaya a kai.


Shaheed ya ce, "mu nemi wata mafita mana", haka suka zazzauna Shaheed sai dariya yake 'boyewa, .


Anisah ce ta shigo cikin d'akin da gudu kamar wadda aka biyo tace, "Yaya Yusuf na kiran ka kazo ka gani wayar Husnah wallahi an zubo mata kud'i kuma, harda wayar da aka kira ta, munji cewar Auren dole ne za'ayi mat... ".


Ganin yanda Husain yake kallon tane ya saka ta kasa 'karasa maganar, tsawa ya daka mata yace, "ke dan ubanki baki da hankali ne, uban waye ya ce ki d'auko mata waya, ke nama tuno, ta ya ya a kayi ma kuka gano gidan da muke? nasan ke ce ki ke da alhakin hakan dan haka muna saura renki kuma idan kika yi muna 'karya mu karya ki a gurin nan! "


Yaya Yusuf ne ya biyo bayan ta, ganin bata dawo da wuri ba, shiru yayi shima yana sauraren ta.


Anisah ta ce, "zan fad'a maku amman Husnah saura minti sha biyar a d'aura Auren ta! ".


Ganin yanayin da take ciki kuma sun ji saura minti sha biyar, ai Husain ne a gaba gurin barin d'akin duk da suna cikin mamakin sa haka suka fita suna fita har ya tayar da motar, su Alhajin kuwa suma sun shiga cikin tasu motar dan duk abunda akeyi a kan kunnen su, mota biyu suka fita da ita.



Husnah kuwa har 'karfe biyu dai_dai bata ci wani abun ba, Zubaidah tayi _tayi har ta gaji ta barta tace Aure babu fashi dan biyu da rabi ne za'a d'aura Auren.


Biyu da kwata nayi Husnah ta tashi tayo wanka ta d'auko kayan ta na masu kyau da tsada ta saka ta fito sai 'kamshi take zubawa gashi taci uban takalmi masu tsayi, sai takun 'kasaita takeyi, a cikin babban falon gidan ta bayyana, ai kuwa duk koma ya tashi tsaye sake da baki harda su Zubaidah.


Wani irin farin ciki ne ya mamaye zuciyar Zubaidah, Husnah kuwa dariyar gefen baki takeyi masu.......



*Comment and share*



*A GIDANTA NA GIRMA*


*BY NANA: KHADEEJATU*

*_UMMU IHSAN_*


*SADAUKAR WA GA :- DUK KANNIN MASOYA NA NABOYE DANA BAYYANE INA SONKU SOSAI SON FISABILILLAH*


*YA ALLAH KAJIKAN MAHAIFINA KAYI MASA RAHMA KA KYAUTATA MAKWANCIN SA SHIDA YAN UWA MUSULMI BAKI `DAYA.*


*YA ALLAH KA BAIWA MAMANA LAFIYA KA BAIWA DUK KANNIN WANDA BAIDA LAFIYA NA GIDA DANA ASIBITI ALLAH KA BASHI LAFIYA AMIN YA ALLAH*




*_Bismillahir Rahmanin Rahim_*


56~60

Tana zuwa ta zauna a kusa da kujerar Zubaidah, ta sakar mata murmushi.

Daskare wa Zubaidah tayi, tana cike da mamakin wan nan ba haguwar "yar ta_ta, ai kuwa kid'a aka sauya a take Zubaidah ta tashi ita da yan tawa gar ta suna rawa da gud'a, wasu na li'ka masu kad'in kari, Husnah kuwa da ido take bin su d'aya bayan d'aya, tana yi tana duba a godon jikin bango biyu da rabi dai_dai kawai Husnah ta tashi ta badalar dasu ta fito tabi ta bayan gidan su ta faki idon mutane, kawai ta durkusa, a jikin flower, ya dauki wata, karamar, trolley din ta, kawai tabi ta bayan motar ta, tabar gidan, da gudun ta, tana isowa bakin titi, motar su Husain na zuwa saura kad'an su taka ta, Allah ne ya kyauta.


Husain da sauri ya taka burki, kamar wata guguwa haka ya fito, ya saka hannun sa, kawai ya jata, keeee... Kamar wata wadda yake gudu ta bata, duk su Hajiya da Alhajin fitowa sukayi daga cikin motar su, suka saki baki suna kallon Ikon Allah.


Shaheed kuwa da gudu ya fito ya d'auke trolley d'in Husnah suka shiga suka tayar da motaci, suka bar unguwar.


Husnah kuwa bata san ma su waye suka d'auke ta ba sai da suka iso gidan san nan hankalin ta ya dawo jikin ta, ta fara zaro ido kamar wadda tayi 'karya.


Kallon Yaya Yusuf ta soma yi, ta dawo gurin Shaheed, har zatayi magana, ke nan Husain ya ce, "dallah karuwar banza rufe, muna biki, kin fito yawon karuwan cin naki shine zaki zo kiyi wa mutane iya yin banza da yofi! ".


Husnah na ganin Husain ta ce, " karuwan ci mai dama ke yin sa, ni wallahi dama nasan kai ne da ban shiga ba'kar motar ka ba, ballema kazo, ka fad'a mani magana akan wannan kucakar motar taka".


Baki ta mur gud'a masa, Husain cikin fushi ya juyo zai mareta, Yaya Yusuf da Shaheed suka tare sa, ita kuwa sake da baki take kallon sa, kwan_kwasa 'kofar motar akayi Shaheed ya bud'e daman 'kofar da Husnah take zaune ne, fita daga cikin motar tayi, tana had'a ido dasu Alhaji da Hajiyar sai ta du'kar da idon ta 'kasa ta kasa ko da dogon motsi, kafeta da ido sukayi, ganin yanda jikin ta, ya soma rawa ne, Hajiyar ta sauke ajiyar zuciya ta kamo, hannun Husnah suka tafi, Alhajin na biye dasu, har cikin falon suka zaunar da ita akan kujera, suma suka zazzauna.



Suhailah ce, ta kawo wa Husnah ruwa mai sanyi a cofi, su Husain ma shigowa sukayi duk suka zazzauna, ruwan Husnah tasha ta fara sauke ajiyar zuciya gurin yayi tsit kamar babu kowa sai fankar dake aiki.



Alhajin ne ya yi gyaran murya ya ce, "ada naso mubi komai a sannu a hankali amman na rasa mi yasa kwatsam wasu abubuwa suke faru, shin Husnah mike faruwa ne, kuma da kika gudo, ina zaki tafi ne?.


Shiru Husnah tayi sai kawai ta saki kuka kamar ranta zai fi, shiru sukayi suna kallon ta, Husain ya ce, inafa zata tafi bayan sana'ar ta, ta karuwan ci! ".


Cikin fushi, Daddy yace, "Husain!! " tare da daka masa tsawa, "kayi wa mutane shiru waye ya ce maka wasa muka zauna yi a gurin nan?.


Shiru Husain yayi bai sake magana ba, Hajiyar tace, mubar ta har ta dawo cikin hayyacin ta, muyi magana da ita, cikin kwanciyar hankali ".


Alhajin ya ce, "ok babu komai Anisah ku shiga da ita cikin d'akin ku, kuma ku barta sai ta futa, kada wanda ya dameta, oya tashi Husnah ku tafi ".


Ri'ka hannun Husnah sukayi suka bar gurin da ita, bayan su Husnah sun bar gurin ne, Alhaji yace, "Husain ya kama ta ka iya bakin ka, ka daina ai banta yarinyar nan, kasan irin yanda nake son ta, dan haka na gar_gad'e ka akan ta kaji ko? ".


Gyada kai Husain yayi ya tashi yabar gurin.

Yaya Yusuf ya ce, "dan Allah Daddy nikam ina jin kamar Husnah jini nace, bana kaunar na ganta cikin damuwa, wallahi idan naga yanda take zubar da hawaye sai naga kamar zan tuno wani abun, amman kuma na rasa miye?".


Daddy ya ce, "Yusuf kada ka damu muci gaba, da biyar komai a sannu Insha Allah komai zai dai_dai ta, sai dai nikam a tsanin Husain da Husnah na rasa miye Allah shine mafi sani, amman ni bana son ganin suna samun sa'bani"



Hajiya ta ce, "ni wallahi idan na kalle su har wani abun yake dar suwa a raina amman ina tunda ina ganin yan zun da Auren wani a kan ta ".



Shaheed ya ce, "Insha Allah babu Auren kowa a kan ta amman mubi komai a sannu ".


Haka dai su Alhajin sukayi ta tattaunawa akai.


Husnah kuwa bata dai na kuka ba, sai taga su Anisah duk sun fara taya ta kukan kawai sai ta bar nata kukan, ta dawo tana kallon su".


Wayar ta ce tayi ringing sai kawai Husnah ta shiga cikin mamakin ya ya akayi wayar ta, tazo nan gidan, dariya Anisah tayi tace, "wayar ki tun jiya take hannu na, amman na rasa taya zan maida maki wayar ki a gurin ki ba, shi yasa na ajiye ta a guri na".



'karfe ukku da rabi nayi, Husnah ta anshi wayar ta, ta soma dan na wayar tana shafar wayar, suna labarin su, suna saka Husnah dariya, dan burin su Suhailah su saka Husnah cikin farin cikin.



A can gidan su Zubaidah kuwa, suna ta chashe war su, ba bu ji ba bu gani, wasu dai sun ga fitar Husnah amman basu kawo komai a ran su ba, har sai da aka kira wayar Zubaidah, tana fita cikin mutane ta d'aga wayar tace, "hello yallabai an d'aura Auren kuwa? ".



Daga can d'aya ban garen, yalla'bai d'in yace, "a a an kusa dai akwai wan da muke jira, manyan ba'kin mu, ina fatan dai Amaryar tawa, tana kusa, dan yau ina son jin muryar ta, ki bani ita muyi magana naji wannan zazza 'kar muryar ta ta, kamar yanda nasaba jin ta idan kuna waya da ita, yau nima nad'an d'ana mana kafin tazo gida na, ta zama ni d'aya zan ri'ka jin muryar ta".


Dariya Zubaidah tayi ta ce, "to ranka ya dad'e bari na kira maka ita, na bata wayar ".


Da wayar a hannun ta ta nufi cikin gidan bata ga Husnah gurin da ta bat taba, ta nufi d'akin Husnah nan ma babu labarin Husnah, haka tayi ta zaga gidan kamar da wasa abu ya zama gaske gidan kowa ya shiga cikin tashin hankalin neman Husnah wasu suce, sun ga fitar ta, wasu kuma suce basu ga kowa ba, ai kuwa gidan biki ya zama jaje da neman inda Husnah ta shiga.



Shi kuwa yalla'bai d'in ya ce, "wallahi sai an nemo ta kuma wallahi kar wadda ta yarda tabar gidan namiji ne ko mace".


Zubaidah ku ka kawai takeyi kukan gaskiya takeyi bana wasa ba, test message ne ya shigo a cikin wayar ta, ai kuwa cikin rawar jiki ta duba kawai ta tashi tsaye ta kurma uban ihu ta fad'i 'kasa babu rai a tattare da ita.



To mike nan Zubaidah ko ta mutu ko tana raye!

Shin wane sa'kon ne ya firgita Zubaidah har haka?


Kudai ci gaba da bin Ummu IHSAN dan wal_wale maku wannan 'kullin



*Comment and share*

*Ummu Ihsan ce*๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน
8/25/21, 7:20 PM - Ummu Ihsan ce ๐ŸŒนโœ๏ฟฝ?: ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ

*ยฐโ€ขยฐA GIDANTA NA GIRMAยฐโ€ข๏ฟฝ?*

๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ


*BY NANA: KHADEEJATU*

*_UMMU IHSAN_*


*SADAUKAR WA GA :- DUK KANNIN MASOYA NA NABOYE DANA BAYYANE INA SONKU SOSAI SON FISABILILLAH*


*YA ALLAH KAJIKAN MAHAIFINA KAYI MASA RAHMA KA KYAUTATA MAKWANCIN SA SHIDA YAN UWA MUSULMI BAKI `DAYA.*


*YA ALLAH KA BAIWA MAMANA LAFIYA KA BAIWA DUK KANNIN WANDA BAIDA LAFIYA NA GIDA DANA ASIBITI ALLAH KA BASHI LAFIYA AMIN YA ALLAH*

*Hahhhh wayyo ciki na wallahi duk kun bani dariya masoya, ita mommy Zubaidah kukeyi wannan mugun fatan? .*

*Kai Djamila idan nice na turowa mommy Zubaidah sa'ko ai sai na sanar da ita inda kuka 'boye mata "ya.*


Ina godiya sosai da Comment din ku da sharhin ku masoya.


*Nafsy a gaskiya shar hinki na sakani farin ciki ina godiya sosai*

*Kamar irin kowa da kowa duk ina godiya sosai da addu'ar ku*

My takwara jin jina da ban girma a gareki*



*A GIDANTA NA GIRMA*



*_Bismillahir Rahmanin Rahim_*

61~65
Duk kan nin mutanen dake gurin sai sukayo a kan Zubaidah suna fad'ar, "Zuby! Zuby!! Zuby!! " suna gir giza ta amman inaa ko motsi Zubaidah batayi ba.

Wani guy ne ya yi dabarar d'ebo ruwa ya yayyafa mata a take ta saki ajiyar zuciya, da 'karfi, ta kurma uban ihu, ta tashi tsaye tana dube_dube, ta ce, "na shiga ukku ni Zubaidah Husnah ta gudu ya ya zanyi da rayuwa ta ne? Gashi Husnah harda su turo mani sa'ko wai ita tabar ni, ni a daura Auren dani! "

Yaya zanyi da rayuwa ne ni Zubaidah Husnah ta tona mani asiri a idon duniya, Husnah yan zun ne na kejin takai cin rashin hankalin da nayi, na yarda da fitowar ki, bayan nasan nayi, nayi ki tashi kiyi hakuri ki shirya tun waye war gari, amman kika 'ki yarda, sai yanzun ne, daga baya kika nuna mani kin fini iya bariki nida na haifeki da ciki na, amman kizo ki fini, kwarewa a gurin bariki, na d'auki alwashin duk inda kika shiga sai na gano ki!

"Zubaidah" ke nan take magana a cikin fushi da nuna 'bacin rai, su kuwa mutanen dake gurin, duk sunyi zuru_zuru suna kallon ta, wayar tace, ta d'auki 'kara, bata ko duba mai kiran ba, ta d'auka ta saka hans free, kawai sukaji, muryar yallabai yana fad'ar, "Zuby kin raina mani da wayau dake da "yar ki da 'kawayen na baki to, kusani, dukan ku wanda yake cikin gidan da yar ki, da ke kanki, zanyi maganin ku, kuma ku saurari sharri na d'aya bayan d'aya kuma duk wani abu nawa wanda ki ku san cewar nawa ne, ni na baku ku dawo mani dashi, daga nan zuwa gobe, kuma kad'in da na turawa Husnah ko naira, ban yarda ba, ace ta 'bata, kuma kusani ba iya nan na tsaya ba, sai kunyi nadamar sa ni na a rayuwar ku, kuma na koreku aiki ga baki d'aya ".


Tunda suka fara sauraren wayar, har aka gama wasu na kuka hawaye sha re_sha re a idon su, wasu kuma hannun su, suka d'aura a kai, dan kowa yasan waye yake magana kuma sun san zai aikata duk abunda ta fad'a, ba bu fashi.

Tsine wa Husnah kawai sukeyi tare da Zubaidah tunda kowa sakacin Zubaidah yake gani, kowa ya manta da nasa laifin.

Husnah kuwa hankalin ta, kwance, yake, har tama manta, da cewar ta baro fitina a gidan su.

Tun lokacin da Husnah tazo gidan har dare bata fito cikin falon gidan ba, haka Husain, duk abun da Husnah take bu'katar sa, a take ake kawo mata shi, Husnah ta zama kamar wata yar gidan.

Hankalin Husnah a kwance ta shari baccin ta, tun 'karfe tara na dare take bacci sai 'karfe goma na safe ta falka, su Anisah mamakin irin wannan baccin na Husnah sukeyi, amman ita hankali kwance take yin abin ta.

Husnah na falkawa, ta shiga toilet, tun suna hakurin jiran ta, har sai da Suhailat, ta nufi bikin 'kafar bayin ta soma, kiran, "wallahi ki fito haka nan dubi mutum kamar wadda bacci ya d'auka a ciki"

Husnah dake cikin bayin ta ce, "ke malama, son kikeyi na fito a ji jikina, na tsamin d'aud'a, haka kawai, kawai dai ki barni, idan na gama son rai na, sai na fito, zaki saka, ni na fito ban wanke wani gurin ba, ko na fito, wani gurin bai ma san anyi wasar ruwa ba".

Ai kuwa ga baki d'aya suka, had'a baki gurin fad'ar, "Allahu akbar jaa muje muslima".

Ai kuwa sai ganin Husnah sukayi ta fito d'aure da towel a jikin ta, sai dariya takeyi, kamar wata hauka sabon kamu harda hawayen ta, dan dariya.

Kallon ta, kawai suka tsaya suna yi, Anisah ta kasa hakuri ta ce, "Anty Husnah lafiyar ki kuwa wan nan dariyar haka? "

Husnah ta ce, "ku dan jira na gama shirya wa, zan baku amsa d'aya bayan d'aya".

mai da hankalin su sukayi gurin Husnah suna kallon yanda take shirya wa komai cikin tsari kuma hankali kwance, trolley d'in ta, ta d'auko ta bud'e ta, mugun mamaki sukeyi ganin yanda duk kayan Husnah suke 'kananan kaya, babu atamfa ko d'aya a cikin kayan, ita kuwa hankalin ta a kwance ta saka riga da wando, rigar pink da kwalliyar yellow, sai wando, jeans blue, ta gyara gashin kanta, ta saka ribom pink da yellow, mai kawai ta shafa, da yar powder ta, sai turare kusan biyar sannan taje ta d'auki hijab ta saka, ta d'auki sallaya, ta shimfida ta, tayar da sallar Asubah.

Duk suka rungume hannun su, suna kallon Husnah har ta kammala, bayan ta idar ta dad'e a zaune kafin ta, tashi, tayo gurin su, cikin murmushi Husnah ta ce, dasu, "antashi lafiya ya gidan? ".

A tare suka amsa mata da, "Lafiya lau Alhamdulillah dafatan kin tashi lafiya ".

Dariya kawai Husnah tayi bata amsa masu ba, suna dai ta bin Husnah da, ido ganin irin yanda kayan suka kama mata jiki, suna cikin kallon Husnah, kawai Husnah ta ce, dasu, "to muje kuci abinci ko? Dan nikam sai 'karfe sha biyu nake karyawa".

Duk suka zaro mata ido, suna fad'ar "wane irin sha biyu? Mukam tun 'karfe tara munci abinci, ki dai chanza shawara, kije kici abinci kuma ku gaisa dasu Ummey".

Husnah tace, muje kawai mu gaisa amman abinci ba yanzun ba".

Haka suka kama hanya, amman su kunyar shigar da Husnah tayi sukeyi, amman kuma, abun mamaki Husnah harda takalmin ta, masu uban tsini ta saka, kuma hankalin ta, kwance take tafiyar ta.

A falo suka sami su Hajiyar Husnah Kawai ta 'karasa gurin Hajiyar ta rungume ta, cikin so da kauna, Husnah tace, "ina kaunar ki Ummey, barka da safiya da fatan kin tashi lafiya ? ".

ajiyar zuciya Hajiyar tayi, cikin tausayin Husnah wadda tun fitowar su, Hajiyar ta kafe su da ido, ita ma ta rungume ta, ta ce, "lafiya lau Alhamdulillah Husnah da fatan kin tashi lafiya, ya ba'kun ta, ya kika kwana ina fatan dai su Anisah basu takura maki ba? ".

Dariya Husnah tayi ta ce, " a a ba suyi mani komai ba, sai tattalina, dai_dai da shigowar su Husain da Shaheed da Yaya Yusuf da Baby, ai kuwa Babyn tayo kan Husnah da gudun ta, ta rungume Husnah, itama Husnah cikin jin dad'in ganin Babyn kawai ta saki Ummey ta rungume Babyn suka sanya dariya, su Shaheed sakin baki sukayi suna kallon Ikon Allah.


Husain kuwa cikin zafin zuciya ya ce, "kee! Uban waye ya baki damar da zaki ri'ka yiwa mutane wannan muguwar shigar, ta karuwai, ko an fad'a maki nan ma gidan karuwan ne!?.


Ba Husnah ba, hatta Ummy da duk wani wanda yake gurin yaji ciwon wannan maganar da Husain yayi wa, Husnah wadda suka fahimci cewar ita bata da laifi, saboda abun da ta taso ta ga an koyar dai ta , to shine itama take amfani dashi, amman sun d'auki alkawarin taimakon ta, su maida ita tamkar yar gidan kowa.


Ko kallon inda yake Husnah batayi ba, kawai taci gaba da, fad'ar "Baby nayi kewar ki, tun da nazo gidan nan ban

Please Login or Register in order to submit comment