Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bai sanar dasu ba, sai Husnah ya sanar, cikin farin ciki suka ce da ita, "Husnah mu d'auki wanka muje"


'kawai Husnah ta sha mur da fuskar ta, ta ce, "sai kun dawo dama bikin Shaheed ne dana je ni kam".


Dama sun san hakan ce zata faru, dole suka shirya suka nufi gurin denier din amman Husain na ganin basu zo da Husnah ba, ta ce, "maza suce shine yace ta zo kuma zuwan dole ne".


Wayar Ummey suka kira dan sunyi ta kiran wayar Husnah tayi ringing babu amsa, Ummey ce ta kaiwa Husnah wayar tace, gashi inji Anisah, halan ina taki wayar ne Husnah? "


Husnah ta ce, "Ummey ba wan can mugun bane ya anshe mani waya ba, bayan kuma game nake bugawa abu na, amman saboda tsabar mugun ta, sai da ya anshe mani waya ".


Jin jina kai Ummey ta yi, ita fa mamaki Husnah da Husain suke bata a ce kullum mutane basa zama lafiya gashi duk sun ce, ba ruwan su da juna, Ummey ta ce, "him! Allah dai ya shirye ku, anshi wayar an sake kira".

Husnah na amsar wayar ta saka hans free, ai kuwa Husain ne yake magana yace, " ke ban ce kuzo tare dasu gurin denier nan ba, wallahi kiyi maza ki shirya kizo kuma ki san motar da zaki shigo , aboki na yana nan gurin mai gadi yana jiran fitowar ki, saura kuma kiyi wan nan shegiyar shigar taki, kuma kada ki yarda kiyi magana dashi, ke dama kowa a gurin dan zan saka maki ido ne, saboda bana son kiyi abunda zai zubar da kimar gidan mu, tunda kowa yasan da cewar ke kanwata ce, kuma wallahi ki kula da kyau! ".



Husnah kuwa ta buga uban tsaki ta ce, "to sannu uban Husnah ai dole ka saka ni aiki kuma kazo kana yi mani masifa, irin kai baban nan wanda bai d'aukar raini, to ba zan je d'in ba, ka jira idan ka dawo kayi mani dukan mutuwa, kaji baban Husnah".


Ummey kuwa tun tana daurewa tana hana dariyar ta, fito wa fili har sai da dariyar ta fito fili, ta ce, "kai kuwa Husain ai lallashin ta zaka yi ba masifa ba, dan Husnah har tayi shirin bacci kaga kuwa bazan takurawa rayuwar "yata ba, a kan bikin ka, kuyi bikin ku kawai ita kam Husnah baccin ta kawai zatayi".



Husain ya ce, "Ummey ki daina biye mata kice kawai tazo kinga duk gidan mu kowa yana gurin ban da ita, kinga idan tazo bikin zaifi yin armashi".


Husnah kwanciyar ta tayi tace, "Ummey sai da safe ni kam ".


Kashe wayar Husain yayi, Ummey kuwa tace, "Husnah da gaske ba zaki je ba? Idan har zaki iya zuwa kije mana tare da Auta, da wasu yan uwa mana dan gasu can zasu tafi ".



Husnah ta ce, "Ummey nifa ba zani wani bikin nan ba, inda dai bikin Shaheed ne dana je".

Ummey gir giza kai tayi ta tashi ta fita.


Husnah kuwa kamar wadda aka tsun kula, ta tashi ta shirya tayi shigar doguwar riga purple mai adon stone, rigar nada ratsin ba'ki da pinki, sai dan kwalin rigar dama kan Husnah a kwance yake ta gyara gashin sai she'ki yakeyi, kawai ta banka turare sai 'kamshi ke tashi a bakin kujerar madubi ta zauna ta dayi light makeup, har ta tashi zata d'auki takalmin ta dawo ta zaun, ta fara bata, fuska tace, "wannan ma shegen bikin zanyi wa kwalliya? Bari dai naje naga shegiyar amaryar wadda ba yarinya ba, ni wallahi na tsani shegiyar amaryar nan, shi kuma sai shegen rawar 'kafa yakeyi akan ta, bari dai mugani da ido na".


Tsani Husnah tayi ta d'auki uban takalmin ta masu mugun tsini ta saka kawai ta fito hannun ta ri'ke da dan kwalin, tana fita Ummey tayi murmushi ta ce, "daman nasan za'a ri na, wai an sace zanen mahaukaciya, Husnar ce, ko Husain d'in ".


Husnah na zuwa gurin Ummey ta 'kwabe fuska tace, "Ummey gani na fito amman fa ba zan dad'e ba".


Ummey tayi murmushi ta ce, " to ku tashi ku tafi, Tara nan ta fito ".


Mutanen da Ummey tayi wa magana sai kallon Husnah sukeyi, ba kamar yanda ta fito kamar ba, bahaushiya ba, sai da Ummey ta anshi dan kwalin tayi mata rolling dashi, san nan suka ga ashe dai ita balarabiya ce, fita sukayi, sai kuma suka dawo kallon takun 'kasaitar da ta keyi, tana wani karai raya, sai uban tsinin takalmin ta, ita kuwa Husnah bata tasu ma takeyi ba, tafe take jin takeyi kamar kar taje gurin amman zuciyar ta, na son gane mata, abunda ke faruwa.


Matar dire ban gidan nasu ta shiga tare da mutanen wasu kuma suka hau motar abokin Husain wanda yake jiran Husnah, kuma yaga Husnah ta gan sa amman tayi fuska ta hau motar gidan su, gir giza kai kawai yayi, yace, "Husnar Husain halin ku sai ku".


Motocin na tashi, basu tsaye ko ina ba sai gurin da ake dinner din Husnah kuwa zaman ta tayi a cikin motar, kowa ya fita har direban amman ban da Husnah, kallon gurin kawai takeyi, mamakin cikar gurin takey, yan mata take kallo masu fira, wasu kuma na dance wa, su Anisah ta hango zaune sun takure guri d'aya ga Yaya Yusuf zaune a tare dasu, sai Kallon_kallo akeyi a tsakanin Anisah da Suhailah, suna 'bata fuska.



Husnah saboda tsabar dariya motar ta fito sai dariya takeyi, dan tasan su Anisah sun tsara yanda zasu baje da rawa a gurin amman an takura su, gurin kawai Husnah ta dosa, babu ruwan ta da kowa amman idon maza da mata duk akan ta.


Wasu jin sukeyi kamar suyi mata magana, har mamaki ta ina ta fito anya mutum ko aljan, ita kam Husnah na zuwa gurin su Anisah ta saka hannun ta, ta daki Anisah sai da Anisah ta zabura, tana ganin Husnah ce kawai itama ta tashi ta zago gurin Husnar ai kuwa Husnah na ganin hakan tayi saurin cewa, "Yaya Yusuf kace mata kada ta daki baiwar Allah ".


Dariya yayi yace, "Allah dai ya shirye ku, to ku zana anan gaba na, dan ba zan barku ba ku d'aya kuyi, ta gogayya da samarin banza ba".


Zama sukayi suka saka shi a tsakiyar su, sai suka soma yiwa Husnah dariya tunda tace ba zata zoba gashi anyi mata dole d'aure fuska Husnah tayi tace wallahi ra'ayi nane dai".



Husain kuwa tun zuwan Husnah ya sauke ajiyar zuciya dan idon sa na akan ta, kuma zuwan ta yake jira, har Amaryar taso ta fahimci wani abun.


Ganin irin shigar da Husnah tayi, gashi idon kowa a kanta, kawai sai yaji mugun haushi.


Husnah kuwa kallon 'kasan ido tayi wa gurin dasu Husain suke tayi kallon tsab Husnah tayi wa Amaryar, wata dariya ce Husnah ta sanya wadda sai da su Anisah suka ce, lafiya dai Husnah wannan dariyar fa wallahi daga gani kin ga 'keta, dan nuna muna mu ma mu gani, wallahi Yaya Yusuf ya tsayar damu, gashi an soma wa'azin tun d'azu".


Husnah kuwa tashi tsaye tayi zata bar gurin saboda dariya, Yaya Yusuf da Shaheed da isowar sa gurin ke nan, kawai yanye hannun Husnah ya zaunar, shima ya zauna ya ce, "Husnah ku kula da kyau kuji wallahi kin san akwai masu bibiyar ki, dan haka kada kiyi nesa da yan gidan ku".



Zama Husnah tayi ta natsu, amman bata dai na dariya ba, har su Shaheed sakin baki sukayi suna kallon ta.


Yau Husnah mamaki kawai take basu, zuwa can Husnah tace, "Yaya Yusuf dan Allah ka barmu muyi rawa ko sau d'aya ne mu taya dan uwan mu farin cikin wannan za'ben da yayi a gaskiya Amaryar ta had'u iya had'uwa"



Tun da Husnah ta fad'i hakan sai kowa ya gane mi take yiwa dariya, su Shaheed kuwa suma dariyar suka sanya harda tafawa.



Wasu samari ne masu ji da kyau da nera suka zo gurin da su Husnah suke sukayi, sallama kawai Husnah dasu Anisah sukayi shiru suka d'auke kai gefe.


Hannu suka baiwa su Shaheed bayan sun gaisa, suka ce am dan Allah ko zaku iya bamu aron kannen ku? Dan wallahi da gaske nakeyi Auren su muke soyin indai kun bamu dama, cikin wata d'aya ne za'a d'aura Auren".


Dariya Anisah ta sanya tace, "ikon Allah wallahi mu kam yau muna ganin abun dariya, to bari kuji nan duk da kuke ganin mu, muna da wanda zamu Aura nan da sati ukku, za'ayi wannan gagarumin bikin, muna gayyatar ku d'aurin Auren namu".


cikin samarin d'aya ya d'aure fuska ya ce, "wallahi baki da wani mijin bayan ni! ".


Husnah kuwa murmushi tayi bata ce uffan ba, Anisah tace, "Allah sarki to baban mu munji mun gode a sauka lafiya ".


Yaya Yusuf da Shaheed kuwa ido kawai suka sanya masu, kawai sai ganin Husain sukayi, yana magana cikin 'bacin rai yace, "Anisah Suhailah Safiya da ke duk na sallame ku, ku tashi Shaheed ya kaiku gida nagode! ".



Ganin yanayin fuskar Husain babu annuri ne ya saka kowa shiga tai tayin sa, Husnah kuwa ta basar dashi, tace, "kai kuma kai ne ke sona ko? To ka bani number wayar ka a rubuce, saboda bani da waya a hannu na, ko kuma ka bani wata wayar taka naje gida da ita, kaga ba zaka sha wata wahalar ba"



Haushin Husnah ne ya turnu'ke Husain kawai ya saka hannun sa da karfin gaske ya janye hannun Husnah da gudu kamar zata kife 'kasa, amman Husain bai ma kula taba, sai cikin motar Shaheed ya saka Husnah ya maida 'kofar ya rufe, juyo kawai sai Amaryar sa ya gani tsaye a bayan sa sai fuci take kamar wadda ta had'iye maciji, duk abokan Husain suka matso gurin Yaya Yusuf da Shaheed su Anisah duk suna gurin cikin zafin nama suka iso gurin.



Amaryar Husain cikin 'bacin rai ta ce, "wato yau ranar dinnier din mu shine zaka wani kama hannun mace a gaban ido na ko? To yau_yau d'in nan ko kuma ma nace yanzun _yanzun nan nake san sanin wace ce ita, miye alakar ka da ita! ? .


Husain yace, "wannan ba muhallin ki bane, babu abunda ya shafe ki da wannan maganar, kuma ma ke miye naki a ciki? "


Cikin fushi ta ce, "ni kuwa nake da muhallin son sani wace ce ita a gareka kuma miye alakar ka da ita, dan ko waye ya ganka a wannan lokacin sai ya zargi wani abun "


Share ta yayi, Husnah kuwa tana samu ta bud'e 'kofar ta fito kawai sai jin sukayi muryar ta kamar yanda take magana ta ce, "him ke malama daman bai sanar dake cewar kece matar sa ta biyu ba? Ai kuwa dai gaskiya hubby baka kyauta ba, kana nufin kamar yanda ka yi mani haka kayi mata, tab lallai ma, yarinya to bari kiji tun ina karama ta, aka d'aura muna Aure dashi, kuma yau shekarar mu ukku da tarewa, gida d'aya, a 'kasar da yayi karatu ya baro ni nima na 'karasa nawa karatun, to kin san wani abu ku? ".



Husnah tayi murmushi tace, "ya dawo ne nan ya ce, shi yana son ya auri tsohuwar mace wadda zatayi saurin haihuwa, wadda haihuwa d'aya zata tsufa shi kuma sai yafara yi mata wulakanci ya saketa ya d'auke muna dan ya kawo muna, kinga ba zamuyi saurin tsufa ba, shine yace nadawo gida ya samo matar da ta dace da aikin, nazo na gani za'ayi bikin cikin gaggawa, dan haka nazo bikin, to nikuma ina ganin ki sai naji tausayin ki shine nace zan sanar dake gaskiya amman shine yace ya rantse sai ya cika burin sa a kanki tunda har ya gano kin mutu a kansa shi kuma soyayyar 'karya ce yake yi maki dan haka babu wanda ya isa ya hana sa aikata hakan ".



Husnah ta fashe da kuka kamar da gaske ta durkushe 'kasa tana kukan karya.


Ba Husain ba hatta su Yaya Yusuf da Shaheed mutuwar tsaye sukayi, ganin Husnah harda hawaye a idon ta.


Mutane kuwa cike suke da mamakin cewar wai Husain ne da wannan hadaddiyar matar amman shine zai koma wa, wata guzumar mata haka.


Amaryar kuwa tace, "anyi walkiya Husain na gano ka kuma kowa ya gano ka, daga ganin yanda kake mazurai kowa yasan baka da gaskiya dan kowa yaga yanda idon ka ya rufe a lokacin da tazo gurin nan, dan haka malam na fasa Auren ka koda kuwa kaina kawai ka zama dan Autan maza a cikin duniyar nan".


Kawai Husain sakin baki yayi ya kafe Husnah da ido ko kiftawa babu, su Yaya Yusuf da Shaheed kuwa cike suke da tsoron anya Husnar suce kuwa?.



Anisah ce ta dawo gurin Husnah ta dafa ta ta shi tsaye suka bar gurin, suka shiga cikin motar su, babu wanda yace uffan har su Yaya Yusuf da Shaheed kuwa sai da suka je gida.


Su Daddy ne suka riska a gidan Husnah na zuwa tayi ribas ta juya zata gudu cikin fushi Daddy yace, idan kika yarda kika bar gidan nan sai kin had'u da fushi na, zo muyi magana dake ".


Dawo wa Husnah tayi cikin d'ari_d'ari ta dawo ta zauna gurin cike da mutane harda Husain da abokan sa, da yan uwan Daddy da abokan sa, da Ummey da yan uwan ta, da abokan ta.


Su Anisah da kowa dai an zauna anyi shiru .


Daddy yace, "miya sa husnah ta ta aikata wan nan dan yen aikin? ".


Husnah ta fashe da kuka kamar wadda aka daka tace, "Daddy har wai kun manta da abunda ya yi mani a cikin taron mutane maka mantan haka wanda suka kasan ce, ba mutanen kwarai ba, ya wanke ni da mari abunda babu wani mahalukin da ya taba kwa tan ta hakan a a gareni, irin wannan to zarcin da yayi mani yana nufin zan iya kyalesa ke nan!? "


Daddy tun kafin na aikata nasan miye zai biyo baya amman Daddy tunda rama irin yanda yayi mani to Alhamdulillah yaji abunda naji a rayuwa ta, dan haka duk hukuncin da kuka yanke a kaina zan rungume sa, hannu biyu, koda kuwa ya kasan ce zan bar maku gidan nan ne, nadai rama zuciya ta tayi fari fes, Daddy wasu saboda dariyar marin da yayi mani harda d'aukar photon abun sukayi, kuma harda gori a gaban idon kowa hakan ta faru".



Shiru tayi sai shashshekar kukan ta kowa yakeji, shiru gurin yayi zuwa can Daddy yace, "Husnah tashi ki shiga ciki ki kwanta sai da safe zamuyi magana dake, san nan kuma kada na sake jin zan cen barin gidan ku, dan baki da gidan da yafi wannan".


Tashi Husnah tayi cikin daddy ya yi murmushi ya dubi Husain ya ce, "Husain abun da naja maka kunne ke nan a kan sa, insha Allah yan zun ka fahimci abunda mukayi maka hange tun wancan lokacin, Husain Husnah ai kowa ma yasan a tsakanin ku, Sam babu ji ruwa, yan zun sai ka sami amaryar taka, ka bata hakuri ayi Auren kawai gone a futa, ni zan san mata kin da zan d'aukar wa wannan rashin jituwar naku"


Daddy yace, to kowa dai yaji duk abunda ya faru dan haka sai kuyi masu fad'a su duka, sannan ku bani shawarar matakin da zan d'aukar masu zuwa da safe, ku tashi ku tafi ".


Duk kowa fita yayi, Hajiyar kuma murmushi tayi kawai.


Husnah tun da ta shiga cikin d'akin take farin ciki su Anisah dai kallon ta kawai suke yi.


Haka suka kwana, Husain kuwa sai cizon baki yakeyi shi a dai haka ta kwana.


Tun da safe su Yaya Yusuf da Shaheed abokan su dasu Anisah da yan uwan Daddy da Hajiya aka zazzauna a take kowa ya kawo tasa shawarar, ai kuwa Ummey da Daddy sai farin ciki sukeyi.....



(Nima dai farin ciki nakeyi duk da ban san wace irin sharar bace)



*Duk wanda ban amsawa Comment ba yayi hakuri ina godiya da soyayyar ku a gareni, na gode sosai Allah ya bar zumunci*


*A GIDANTA NA GIRMA*

*BY NANA: KHADEEJATU*

*_UMMU IHSAN_*


*SADAUKAR WA GA :- DUK KANNIN MASOYA NA NABOYE DANA BAYYANE INA SONKU SOSAI SON FISABILILLAH*


*YA ALLAH KAJIKAN MAHAIFINA KAYI MASA RAHMA KA KYAUTATA MAKWANCIN SA SHIDA YAN UWA MUSULMI BAKI `DAYA.*


*YA ALLAH KA BAIWA MAMANA LAFIYA KA BAIWA DUK KANNIN WANDA BAIDA LAFIYA NA GIDA DANA ASIBITI ALLAH KA BASHI LAFIYA AMIN YA ALLAH*




*_Bismillahir Rahmanin Rahim_*


71~75
Cikin farin ciki Daddy ya ce, "Shaheed kira mani Husain kace masa ina jiran sa da gaggawa yan zun nan, am kema Anisah nemo mani Husnah kice mata ina neman ta da gaggawa yan zun nan ".



Ai kuwa cikin sauri su Shaheed suka cika umarnin Daddy, Husain ya ce, "wannan kiran na gaggawa Shaheed cikin fushi Daddy yake ko kuwa?".


Shaheed ya ce, "to nima dai ban sa ni ba, amman dai kayi sauri gudun yin laifin".

Jin abun da Shaheed ya fad'a ne, yasaka Husain tashi tsaye cikin sanyin jiki ya tafi kamar wani marar lafiya.


Itama Husnah koda Anisah ta sanar da ita kiran Daddy ruwan da take sha ne ta fur zar kamar wata 'karamar yarinya ta zaro ido waje tace, "Anisah na shiga ukku na ni Husnah wane laifin ne kuma na sake ai katawa, ni shugabar marasa jin magana ta duniya! ?.



Anisah ta ce, "kije da kanki kijiwa kunnen ki, dan nima ban sa ni ba amman dai kiyi saurin amsa sa'kon Daddy ".


Tashi Husnah tayi cikin damuwa da rashin sanin laifin ta, tabi bayan Anisah kamar wadda 'kwai ya fashe wa a ciki haka take tafiya, a bakin kofar falon suka had'u wani ban zan kallo Husain ya aika wa Husnah, itama tayi saurin mayar masa harda mur gud'a masa baki, su Anisah kuwa wuce su sukayi suna dariya 'kasa_'kasa Husain yace, "yarinya kin taro wa kanki masifa dan yanda kina tozar tani a cikin taron mutane harda su kiran cewar ke mata ta ce ke a tunanin ki zan iya Auren karuwa ne? Yarinya kin yi 'karya ni nan Husain nafi karfin ki wallahi! "



Tabe baki Husnah tayi ta ce, "ho ho shegiya 'karya, oh da kai har tunanin ka ya baka cewar ni Husnah zan iya Auren mum munan mutum kuma tsofo wanda ya zama tuzoru? Lallai tsohon nan kayi kus kure dan ni Husnah ta yaro ce mai jini a jiki, kuma kasani, ni ko mai sunan ka bana bu'katar hanya ta had'a ni dashi guri d'aya ballema ace Aure, kai tub da wannan yawun naka ma, ni idan aka bani damar tsayar da wanda nake son Aura ai Tk ne yafi kowa dace dana Aura ".



Cikin zafin rai Husain zafin zuciya ya d'aga hannu zai kaiwa Husnah duka, Husnah tayi saurin fad'ar Allah ya baka ikon ai katawa, wallahi zan yi maka fiye da abun da ka aikata a gare ni!.


Daddy ne ya matsa dab dasu yana kallon su, Husain ya d'aga hannu zai daki Husnah, ita kuma Husnah tana sakar masa magana ya ce, "wannan shine amsar kiran dana yi maku ko? Ashe dai har kun iso to ina godiya sosai da wannan amsa gayyatar da kukayi tawa".


Juyawa ya yi ya dawo inda yake zaune su Yaya Yusuf da Shaheed dariya kawai sukeyi 'kasa_'kasa, kai gurin mamakin halin Husnah da Husain akeyi wannan rashin jituwa nasu yayi yawa.


Da sauri suka dai na fad'an har suna rige_rigen zuwa, a gaban su Daddy suka dur'kusa kowa kai a 'kasa.


Hajiya dariyar ta kasa 'boyewa tayi kawai ta ce, "Ikon Allah Husain kai da Husnah yau wani sabon kicihi kuka tsiro na jin kunyar had'a ido damu to kodai kun sa santa kan ku ne naga duk fuskar ku da annurin fuskar ku ya nuna hakan, to Alhaji Alhamdulillah tunda har su sasan ta kansu kawai sai ayi gaggawar d'aura Auren nasu yau ko? Ko ya ya kuka gani ne jama'a? ".



Wata irin zabura sukayi su duka, Husain sai murza kunnen sa yakeyi da alama kamar kunnen nasa bai jiyo abunda Ummey ta fad'a ba sosai.


Husnah kuwa zarar ido take yi kamar wadda tayi 'karya sai bin duk mutanen falon takeyi da ido d'aya bayan d'aya.



Yaya Yusuf ya ce, "oh! Ikon Allah ashe dai shirya war tasu ba wani abu bane mai d'aukar lokaci da yawa ba, kai amman nikam nafi kowa farin cikin wannan sauyin da muka samu a gurin Husain da Husnah ".


Dan uwan Daddy Alhaji Haruna ya ce, "to ai kuwa nine waliyin ango kai kuma Yaya nasan kaine uban Amarya sai muyi wa Annabi salati, Sallalahu alaihi wasallam".


Duk aka amsa da, "Sallalahu alaihi wasallam ".


Husnah fashewa tayi da kuka, zatayi magana ke nan wata dattijiya, tace, "ikon Allah Amaryar har ta fara kukan rabuwa da iyayen ta, zata je gidan abun son ta".


'kara fashe wa da kuka Husnah tayi, gashi tana son yin magana babu damar yi saboda mutane sun'ki su barta tayi magana, sai ta kaicin hakan ya 'kara yi mata yawa.


Husain kuwa hankalin sa yayi munmunan tashi, Sai zufa ce ke karyo masa ta ko wane sa'ko da lungu na jikin sa, da ket ya bud'e bakin sa ya ce, "dan Allah Daddy kayi...... ".



Da sauri Daddy ya dakatar dashi yace, "haba Husain miye na godiya kuwa ai Husnah kanwar kace kuyi zaman ku na gir ma ma junan ku ku ji ni ko?.


Wani abokin Daddy Alhaji Isma'il ya ce, " a a ba haka yake nufi ba, nikam na fahimci abunda yake son fad'a ko Husain? .


Da sauri Husain ya d'aga masa kai kamar wani dan 'kadan gare, ya ce, "eh Abba eh Abba ba hakan nake nufi ba".


Cikin sauri sai Alhaji Isma'il ya ce, "yauwa Alhaji kun dai ji da kunnen ku ko? To abun da yake son fad'a shine yace dan Allah Daddy kayi hakuri ko Husain? " ya dubi Husain wanda har da murmushi ya saki da sauri ya ce, "eh eh Abba hakane kuma zan ce ".


'kara dakatar dashi Alhaji Isma'il yayi yace, "zan 'karasa maka mana yaro na".


Da sauri Husain ya ce, "nagode Abba kai ne kawai ka fahimci nufi na".


Dariya Alhaji Isma'il yayi yace, "to Husain dai yana mai baku hakuri ne akan irin yanda suke yawan fad'a a tsanin sa da kanwar sa Husnah amman ya dau alkawarin hakan ba zai sake faruwa ba matsawar kuka Aura masa ita, to kunji nufin yaro na dan albarka ".


Ga baki d'aya gurin ya d'auki kai masha Allah abu ya yi kyau.


Husain da Husnah kuwa hankalin su a tashe yake, Husnah kuka kawai takeyi babu 'ka'kkautawa, ganin take duk basa son ta, Husain kuwa saboda tsabar shiga cikin mamakin Abba, kawai ya kafe Daddy da ido, Daddy ya ce, "Husain kud'in da kake ajiyewa kace zakayi abu mai mahimmaci dasu, to na raba su hud'u na d'auki sadakin 'yata Husnah a cikin su kaga naira dubu dari biyar ke nan tunda baka dad'e da fara ajiyar ba, kuma cikin gida jen da ka kammala na d'aukar wa Husnah wannan gidan da ka gama kammala wa, a cikin shekarar nan gidan da yafi kowa ne gida bur geka da soyuwa ba zan hana ka kawo wannan matar taka ba, dan munje mun baiwa iyayen ta, hakuri sun janye maganar fasawar da aka ce a baya, amman kuma ka sani Auren Husnah zamu fara d'aura wa, kafin muje can a d'aura Auren ka da mardiyar, dan haka Auren mata biyu ya hau kanka a wannan ranar, kuma Husnah itace uwar gidan ka Husain, ku tashi nagama magana sai naga wanda bamu isa dashi ba a cikin ku, kuma sai naga wanda bai d'auke mu matsayin iyayen sa ba daga cikin ku".


Daddy na gama magana ya sallami kowa, daga cikin yara amman banda abokan sa da yan uwan sa.


Husnah har jiri

Please Login or Register in order to submit comment