Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wasu abubuwa da dai sauran su*


dafatan bazaku raina aduk sanda na turk maku kuma zaku anshe sa da hannun biyu,.

Bance dole mutum ya koya ba nayi ne dan wanda suke da ra'ayin koyon basu san yaya zasuyi ba.

Dan haka duk wanda yake son koyo nabashi damar koyon abun sa.

Bari dai mu fara abunda yake gaban mu.


*Yau zamu fara ne da koyon decoration na bottle empty da zare rumy*

_*kayan bukata*_

*1_Robar lemu Ko ruwa*

*2_Zare Rumy*

*3_Flower duk irin wadda mutum yake so*

*4_Scissors da gum*

Dafarko dai mutum zai samu kwalbar shi sai ya d'auko almakashi, ya yanke saman robar inda marfin, sai asamu gum ana shafawa ajikin rubar ana li'ka zaren Rumy har sai an zagaye ko ina, har a gama, sai ki saka fulawar ki duk irin wadda mutum yake so shike nan.


zanci gaba insha Allah idan har akwai tambaya ko neman 'karin bayani ga WhatsApp number :-
_08065348329_
Dan Allah banda kira.



*Addu'a Kasai nake nema a gurin ku, kuyiwa mahaifiyata addu'a Allah ya bata lafiya Allah ya jikan mahaifina amin nagode*


plc *Comment and share*


*A GIDANTA NA GIRMA*


*DAGA AL 'KALAMIN NANA: KHADEEJATU*

*_UMMU IHSAN_*


*SADAUKAR WA GA :- DUK KANNIN MASOYA NA NABOYE DANA BAYYANE INA SONKU SOSAI SON FISABILILLAH*


*YA ALLAH KAJIKAN MAHAIFINA KAYI MASA RAHMA KA KYAUTATA MAKWANCIN SA SHIDA YAN UWA MUSULMI BAKI `DAYA.*

*YA ALLAH KA BAIWA MAMANA LAFIYA KA BAIWA DUK KANNIN WANDA BAIDA LFY NA GIDA DANA ASIBITI LAFIYA AMIN YA ALLAH*


*_Bismillahir Rahmanin Rahim_*

41~45


"Kai inaaaa sam Mommy ba bu wani Aure a gaban ta Amman koma Auren waye zan gani da ido na dan sam ban yarda da wannan shirin na su Mommy ba, matar da ta tsani wani ya ce zaiyi Aure ballema ita tayi wani Auren!? Husnah" ke nan ta ke wannan zan cen cikin damuwa

Haka Husnah ta kwana da tunanin wannan lamarin har yaso ya hana ta bacci.


A can gidan su Husain kuwa.

Fitowa Husain ya yi da niyar rama abun da Husnah tayi masa amman kuma kash ya makara, yana fitowa Husnah na barin gidan.


Dafe goshin sa ya yi ya doko uban tsaki ya buga 'kafar sa ya juya a fusace ya dawo cikin d'akin sa, sai tsaki yake zubawa.


Haka "Husain ya ya kwana da fushi da kowa na gidan dan a ganin sa sune suka saka Husnah ta raina sa da ya wa".


Shirin biki kawai Zubaidah keyi ita da 'kawayenta amman Husnah ido ne na ta sai dai kuma wata sabuwar bidi'ar da Zubaidah ta zowa Husnah dashi wadda Husnah take kallon har "yan han jin Zubaidah shine kullum da safe sai ta kawo mata wasu kayan mata tana cewa sai Husnah tasha saboda sabon saurayin ta".

yau ma kamar kullum Zubaidah ce tsare da Husnah tana bata kayan mata, ita kuwa Husnah kallon ta kawai takeyi ko 'kyafta ido babu har Zubaidah ta so ma tsar guwa, Zubaidah tace, "wannan kallon fa Husnah?.


Dariya Husnah tayi tace, "ni kuwa zan so sanin wannan sirrin da ake shirya wa, da alama dai wannan Amaryar ba kowa bace face maku san ciya ta ce dan ina ji a jiki na kamar ke ce uwar Amaryar ni kuma ta kusa da Amaryar Mommy amman yau ba zan sha maku wannan abun ba kamar kullum domin kuwa kin san idan na karya da safe bana iya bu'katar komai a gaba na amman za ki iya ajiyewa har zuwa gobe indai ba bu wata damuwar".


Mutuwar zaune Zubaidah tayi tun lokacin da Husnah ta soma baya nin ta, kawai Zubaidah tace, "Husnah waye ya sanar dake abun da muke shirin shirya wane?.


Husnah kuwa yi tayi kamar bata gurin.

Zubaidah ta ce, "Husnah zan yi maki Aure ne da wani mutum wanda baki ta'ba gani ba, kuma baki ta'ba jin labarin sa ba, shine ya za'bi Auren ki, fiye da kasan cewa dake na yan wasu shekaru, kuma Auren a can baya sati ukku na saka amman yanzun cikin wannan satin na biyu zamuyi bikin saboda zaku wuce America ne dan mafi yawan cin har kokin sa a can yake yin su mutamen bai da wata mata a tare dashi duk suna Kauyen su yaran sa sha biyar na Aure, bakwai wanda ya haifa ba tare da Aure ba kuma duk ana kular masa da su ba bu wanda yake cikin yunwa da talauci ".


Sai da Zubaidah takai aya Husnah dake tsare da ita da idon ta, kawai ta tashi tsaye ba tare da tace da ita uffan ba ya shige cikin d'akin ta, zaunawa tayi a bakin gadon ta, tunanin komai ya 'bace mata kawai dai zaman tayi batare da tasan mike damun ta ba.


Zubaidah kuwa wayar ta ta d'auka ta kira wata number ta ce, "hello Alhaji an yanka ta tashi domin kuwa Husnah ta gano komai, kuma naga alamar zata iya bijere muna badan komai ba sai dan naga bata ce dani komai ba, nafi kowa sanin halin Husnah domin Husnah 'yata ce".


Daga can 'ban garen a kace da Zubaidah, "ku fara hidimar bikin tun yau san nan kuma zan aiko maku da duk abunda ku ke da bukatar sa, kuma kada abar ta zuwa ko nan da bakin get san nan kuma yara na zan turo su domin suyi mani sa ido akan ta da duk wani abun da take aika tawa kuma ba na bu'katar a takura mata kuma duk abun da take bu'katar sa ayi gaggawar kawo mata shi, kwata_kwata ba na bu'katar ta nemi abu ta rasa shi ki turo mani account number na ta zan turo mata da ishesh shen kud'i ".

Cikin farin ciki Zubaidah ta ce, "to ranka ya dad'e angama".

Ket ya kashe wayar.

Husnah kam tashi tsaye tayi ta kama za ga yen cikin d'akin sai nazarin wannan shirmen ta ke yi har yan zun Husnah bata gamsu da wannan baya nin ba duk da ya fito ne daga bakin wadda bata yi mata 'karya.


Haka Husnah takwana cikin matsa nan ciyar damuwa.


"Zubaidah kuwa harkar gaban ta kawai takeyi ita da 'kawayen ta yau ma gidan kid'a ne kawai ke tashi har kamar kunnen mutum ya fashe, tsaki kawai Husnah keyi, wayar ta ce tayi alart kawai ta 'ki bi takan wayar dan yau ko karya wa bata yiba saboda Zubaidah hidimar gaban ta ta ishe ta, mutane maza da mata ne ke shar holiyar su, a gidan dan haka ne yasaka Zubaidah man tawa da Husnah bata ci abinci ba".


"Husnah kuwa jakar ta kawata d'auka da wayar ta, tabar sai makulin motar ta, ta fito cikin falon gidan kallon mutanen gurin tayi, amman jin takeyi kamar ta samu bindiga ta halbesu kowa ma ta fu ta, kawai tayi gaba abinta, su kuwa sai kirarin amarya "yar 'kamshi sukeyi mata, zuciyar Husnah kamar ta fashe haka takeji saboda tsabar yan da wannan Sunan yake ta'ba zuciyar ta"


Jikin motar ta ta 'karasa zata bud'e mota, kawai wasu gar dawa majiya 'karfi har su hud'u suka za gaye ta kowan nen su 'kirar yan rastalin ne dashi, duk sun had'e rai sun tur ni'ke fuska suna tambayar ta, d'ayan su yace, "Madam sai ina fa?.


Cike da mamaki Husnah take kallon mutanen harda su ri'ke baki, tace, "to ko an saka kune ku hanani rawar hantsin gaba nane?.


Duk suka zaro ido suna kallon ta, cike da mamaki ganin ko tsoron su ba ta ji ba, d'aya daga cikin su ya ce, "tabbas an saka mu duk inda kika saka 'kafar ki mu ma mu saka tamu 'kafar saboda tsaro, dan a yan zun haka kina da masu harin da suke da burin sace ki saboda wanda zaki Aura mutane da yawa ne suke neman sa cikin su kuwa harda jami'an tsaro ".


Dariya Husnah tayi ta ce, "yo ni ina ruwa na a cikin lamarin sa, kai nifa ba bu uban da ya isa ya takurawa rayuwa ta, domin kuwa ni bance ina son sa ba, ballema nayi burin Auren sa, wai ma anya mutum ne ko aljani dan nifa nafa zargin sa?.


Zaro ido sukayi waje suna kallon 'karamar yarinya marar tsoro amman suna ganin dan bata san waye zata Aura ba ne da ta shiga tai tayin ta da shi kuma ta kame bakin ta, da furta masa mummunar magana, amman zasuyi mata uzuri na rashin sani".

Muryar Zubaidah ce ta jiyo tana fad'ar, "Husnah gidan uban waye zaki, baki ji nace kada ki yarda ki bar gidan nan ba ne!?.


Ko kallon ta Husnah bata yi ba, tace, "yo da yunwar zan zauna ne, har 'karfe biyu da rabi ban karya ba, salon yunwa ta kashe ni, ni kam zan je neman abinci ne".

Dafe kai Zubaidah tayi ta ce, "kiyi hakuri shaf na man tane, amman kije tare da wannan nasan zasu baki kulawa ta musamman".


Husnah ta ce, "wallahi kowa ya kama gaban sa, kin dai san tun akan Tk halina bai sauya ba".


Zubaidah ta ce, "wannan ya shafe Tk ya wuce sa kawai dai kiyi hakuri kuje tare".

Husnah kuwa tsayuwar ta ta gyara a jikin motar alamar sai dai suyi ta tsayi a gurin, wayar Zubaidah ce tayi 'kara kawai ta d'auka cikin rawar jikin da kaud'in murya tace, "hello yallabai kayi hakuri Husnah rigimar ta tayi yawa, kabar ta, ta fita zata ciyo abinci ne kawai".


Ta yi shiru, zuwa can ta ajiye wayar tace, "minti talatin na baki idan ki ka wuce hakan ni da ke ne".


Murmushi Husnah tayi kawai taja motar ta tabar gidan sai da Zubaidah tayi ta kiran ta san nan ta koma gidan.


Tun da safe Husnah kejin fad'uwar gaba amman bata san mike faruwa ba, kawai dai ta tashi jikin ta duk ba bu 'karfi, zuwa 'karfe ukku na rana Zubaidah ta shigo cikin d'akin wasu matan wanda Husnah bata san su ba biye da ita, hannun su cike da kaya har su biyar, kallon su kawai Husnah keyi, ajiye kayan sukayi a gaban Husnah duk sukayi tsaye suka run gume hannun su.


Husnah kuwa kallon Ikon Allah kawai takeyi, Zubaidah cikin d'aure fuskar ta babu alamar wasa tace, da Husnah "Husnah yau kam nice uwar babu wani alamar d'aukar raini kuma yau ne ake kamun Amarya dan haka, ga masu shirya Amarya nan mijin da kansa ya turo su, sai ki tashi tsaye su shirya ki, idan an gama ku fito ga motoci can suna jiran Amarya".


Kawai Zubaidah tabar d'akin, Husnah kuwa kallon Ikon Allah kawai takeyi sai da suka ce da ita, "tashi kiyo wanka "


Husnah kuwa ta ce, "ni ba na wanka ku shirya ni a hakan ".


Kallon_kallo aka shiga yi kowa cike da mamaki amman tunda Zubaidah ta sanar dasu halin Husnah kuma tace dasu duk abunda tace kada su biye mata sudai bita a sannu har su samu ta yarda ayi komai cikin sa'a da nasara"

Haka dai suka dare sukayi yanda Husnah tace, suka gyara ta, Husnah sai dariya takeyi, su kuwa sun rasa dariyar miye takeyi, sai ma ta dawo tana burge su, kwalliya sosai sukayi mata ta Amarya Husnah tafito Amaryar ta tsab lallale ne kawai babu a ciki.


Fito da Husnah sukayi kowa sai mamaki irin yanda Husnah ke takun ta suke gashi dai fuskar ta cike da annuri ita kanta Zubaidah sai da tayi mugun mamaki cikin ranta har wasi_wasi takeyi anya Husnar tace kuwa? Kodai_kodai a kwai abun da take shirya wa ne!?.


"Kai ina sam Husnah bazata iya shirya komai ba dan Husnah rainon tace, kuma tasan daman Husnah ba za ta kunya tar da ita ba".


Husnah kuwa ita ce a gaba gurin shiga motar Amarya wannan abun da Husnah tayi ya 'kara baiwa kowa tabbacin yar gidan Zubaidah ce.


Husnah kuwa wani kallo take biyar duk mutane dake cikin motar ba kamar Zubaidah, wanda sai da Zubaidah ta tambaye ta, "Husnah ya ya dai? .


Husnah ta ce, "zanyi kewar ki ne mommy shi yasa nake ta kallon ki".


Wani irin dad'in gaske ne ya kama Zubaidah, wanda har sai da run gume Husnah a jikin ta, a haka suka 'karasa gurin kamun.


A gaskiya gurin kam ya had'u iya had'uwa, kuma komai cikin tsari akayi sa, sai kusan 'karfe tara aka dawo gida ba bu sallah ba bu salati, Husnah kuwa tsaki kawai takeyi.


Su na shigowa cikin gidan Husnah tayi cikin d'akin ta, tayo wanka tayi alwala, tayi sallah kamar yanda ta saba, cikin rashin iya wa.


'karfe goma na dare Husnah ce ta fito da wayar ta a hannun ta, tana waya, har ta bar cikin falon gidan tayo hara bar gidan, turus tayi ta fara zaro ido waje tana nuna wani gurin, cikin rawar baki ta ce.........




_*Yau akan ta'ba ka lashe wato dai zamuyi girki ne yau.*_


*IRISH DA CHIKEN STRIPS*


_*Abubuwan bu'kata*_

1_Tattasai ja
2_Tattasai tsanwa
3_Albasa
4_Albasa Carrot
5_Thyme & Curry
6_mangyad'a ko man zaitun
7_Magi &Gishiri
8_Dankali Arish


_*Yadda Ake Had'awa*_

"Yar uwa ki wanke naman ki na kazar ki mai kyau, sai ki d'ora a kan wuta, ki ta fasa shi, ki zuba gishirin ki kad'an da Magi star ki zuba curry da thyme da Albasa irin yan da kike so kid'an zuba ruwa kad'an ki barshi ya tana na idan ya fidda main sao ki kwashe kibar ruwan tafasar naman a cikin tukunya.

Kidan Kara ruwa kadan sai kizuba Dankalin ki kika yanka yarda kike so sai ki zuba acikin tukunyar taki inda ruwan naman ki suke ki zuba magi da Gishiri ki bar Dankalin har ya kusa dafuwa sai a sauke tukunyar.

"Yar uwa kisamu tasar suyar ki zuba man ki, ki saka Tattasan ki wanda kika yanka ja da tsanwa ki saka carrot da magi da Gishiri kad'an, ki barshi har na tsayin mintoci ki sauke tukunyar ki, ki maida tukunyar Dankalin ki ki juye soyayyen kayan miyan ki da naman ki wanda Kika kwashe, ki saka ludayi kijuya shi ya cure guri d'aya.

"Yar uwa idan kin sauke a zuba wa mai gida da yaran albarka aci dad'i lafiya.


*Daga Alkalamin Ummu Ihsan*

_*Shawara ko karin bayani*_
08065348329


*Comment and share*



*A GIDANTA NA GIRMA*

*BY NANA: KHADEEJATU*

*_UMMU IHSAN_*


*SADAUKAR WA GA :- DUK KANNIN MASOYA NA NABOYE DANA BAYYANE INA SONKU SOSAI SON FISABILILLAH*


*YA ALLAH KAJIKAN MAHAIFINA KAYI MASA RAHMA KA KYAUTATA MAKWANCIN SA SHIDA YAN UWA MUSULMI BAKI `DAYA.*


*YA ALLAH KA BAIWA MAMANA LAFIYA KA BAIWA DUK KANNIN WANDA BAIDA LAFIYA NA GIDA DANA ASIBITI ALLAH KA BASHI LAFIYA AMIN YA ALLAH*




*_Bismillahir Rahma Nin Rahim_*



. 46~50


A cikin rawar jiki take nu na gurin da yatsan ta, ta saki wayar ta dad'i 'kasa ta ce, " Mo... Mommy.. Lafiyar ki kuwa.. Su.. Waye wannan suke shi... Shirin kashe mu... ta... ne... Ha.. Lam...!?.

Dariyar 'keta Zubaidah ta sanya ta ce, "oh Husnah wai baki gane ko su waye bane? Duba da kyau dai ko zaki gane su! "

Da sauri Husnah cike fa mamaki take kallon Zubaidah yau cike da mamaki ganin bindiga a hannun ta, kuma ta sai ta kan wani mutum wanda sam bata fahimci waye shi ba, su kuma wannan 'kat tin masu 'kirar "yan rastalin sun sai ta d'ayan da bindigogin hannun su, da alama sun kusa kashe ko su waye.

Husnah kuwa ta ce, "Mommy yaushe ne kika zama yar bindiga ban sani ba halan? Duk zama na dake ban ta'ba koda jin zan ce maka mancin haka ba, Amman duk wani abun da kike aika tawa nasan dashi koma miye! ".

Zubaidah ta ce, "Husnah ke nan ke a tunanin ki zan haife kine kizo kifini wayau, to bari kiji tun kina cikin zanen goyo nake wannan har kallar, kawai dai ina taka tsan tsan ne kawai dan bana son yawan surutu, kuma gashi ke duk abun da kika gani sai kinyi magana akai Husnah, ki sani koda nake karuwa ban 'boye maki ba dan nasan ka ruwanci shine cinki suturar ki kai komai ma naki kuma kema shine sana'ar dana d'ora ki akai, dan haka ba bu wani 'boyon da zanyi maki, yan zun dai ki duba wannan mutanen dan yan zun ne zan gwada maki ni kwarar riyya ce a gurin dan a gaban idon ki zan kashe su".


Da sauri Husnah ta ce, "Mommy na ro'keki da kada ki aikata hakan duk da ban san ko su waye ba, bazan so ki aikata hakan akan su ba".

Zubaidah ta ce," Husnah kidai duba da kyau kamar naga saboda ke suka zo gidan nan namu, da 'kararren kwana ".

A hankali da sanyi jiki Husnah ta 'karasa gurin wanda tafi kusa dashi waye Husnah zata gani? Murza idon tane ta soma yi, cike da matu'kar mamaki, ta ce, "Shaheed kai ne kuwa!? Miye ya kawo ka gidan nan kuma waye ya sanar dakai wannan gidan nake? Kuma kai da waye!?.

Bindigar dake sai ce a kan sa kusan biyar, taga ya kafe gurin Zubaidah da ido itama ta mayar da ido ta a gurin, turus ta yi, ta saka hannun ta, tana nu na wa, ta ce, "Yaya Husain harda kai, tana zarar ido, cikin tsoro da far gaba! ".

Husain ya ce, "bindigar nan bata wani tsoratar dani ba, amman ke kam kin tso ratar dani, daman tun daga lokacin dana ganki na fahimci cewar ke ba mutuniyar kir_ki bace, dan haka ne yasaka na umarci Shaheed ya bin ciko muna wace ce ke?, sai gashi har ni na gane wa ido na komai ".


Kuka Husnah ta sanya ta dur'kusa ta kama 'kafar Zubaidah ta ce, "mommy na ro'keki dan Allah kada ki aikata abun da kikayi niyar ai katawa, Mommy ki duba yanda na shirya yarda da umarnin ki, na Auren wanda ban sani ba, ban san waye shi ba, amman saboda naga hankalin ki yafi kar kata akan hakan, haka na jure ban musa maki ba, Mommy ki dubi wannan halarcin, ki kyalesu kada ki kashe su ! ".

Zubaidah ta wani bushewa da kafurar dariya ta ce, "Husnah na fahimci kun sha'ku dasu fiye dani da nake Maman ki, tunda gashi yau kece kike kama 'kafar ta, harda kukan ki dan naji tausayin ki kada na kashe su, amman inaa! Tunda nafa himci shakuwar ku tafi tawa, ni kuma zan kashe su a yan zun nan".


Da sauri Shaheed ya ce, "Husnah daman wannan ita ce, Maman ki? Daman kema karuwa ce? Daman gidan karuwai kike shine har kika shiga jikin mahaifin mu, ki ka zama kamar wata mutuniyar kwarai? Amman mi yasa kika shiga jikin mahaifin mu ko dan ku kashe shi ku kwashe dukiyar sa!? ".

Husnah kuwa kallon Shaheed kawai takeyi cike da damuwa, ta ce, "Shaheed ba wan nan zan cen ba, ayi zancen ku'butar ku a hannun Mommy da wannan azzaluman mutanen! ".

Husain ya ce, "ya Isah haka nan, na tsane ki tun kafin nasan ke wace ce , kuma ki sani idan na ku'buta sai na kashe ki da hannu na, muguwa azzaluma kuma mahaifin mu yafi karfin ki wallahi ta Allah ba taki ba, kuma sai na wulakanta rayuwar ki matsawar kika yarda na ku'buta sai kinyi dana sanin, sani "yan gidan mu! ".


Matsanan cin kuka ne Husnah ta fashe dashi ta ce, "Mommy idan har kika yarda kika kashe su ko kuma kika illatar dasu, kisani kin rasa ni ke nan duk wani burin ki a kaina ya watse dan nima kashe kaina zanyi, sai na barki kiyi rayuwar ki yanda kike bu'katar ta! ".


Dariya Zubaidah tayi ta ce, "Husnah dan na kashe su shine kema zaki kashe kanki, ai kuwa idan kika kashe kanki kinyi wa kanki, dan ko kin mutu kece kika mutu, baki ji wanda kike ya'kin a kan su ba, sunce zasu kashe ki, ba, ai gara kibar ni ni na fara gamawa dasu" kawai Zubaidah ta kira wayar ta ta ce, kuzo ina jiran ku".


Ai kuwa sai ga 'kawayen Zubaidah ta basu umarnin su d'auke mata "yarta suyi cikin gidan da ita.

Ai kuwa Husnah ta zille, ta janyo 'kafar Zubaidah da 'karfin da bata san ta dashi ba, ta wufce Bindigar dake hannun Zubaidah tayi saurin, ta'kawa duk wanda ya matso gurin ta da niyar ri'ke ta, Husain kuwa cikin zafin nama ya wafce Bindigar da Husnah ta fige, dan Husnah bata iya ri'kon Bindigar ba, kawai ya ta'ka Bindigar akan Husnah yace, "zan kashe wannan babbar karuwar, kowa ma ya futa, cikin rawar jiki Zubaidah da 'kawayen ta suka d'ora hannun su akai kamar zasu fasa ihu,.


Husain ya ce, "ku d'auke Bindigar ku a kan dan uwana ko na kashe wannan annobar da naga kuna tsoron a kashe ta, cikin rawar jiki duk wannan gardawan suka, d'auke Bindigar su akan Shaheed.


Shaheed kuwa yasan halin Husain zai iya halbe Husnah, saboda yanda yaga zallar kiyayyar Husnah a idon sa, da sauri Shaheed ya ce, "dan Allah kada ka aikata hakan akan Husnah wallahi bata da alaka da wannan aikin ".


Husain ya ce, "mutuwar ta, ta zama wajibi yau sai na kashe ta da hannu na mun rage mugun iri a duniyar nan! ".


Husnah kuwa kallon Husain kawai takeyi tasan yau mutuwar ta, tazo, tunda Husain daman ya tsane ta, yau kuma babu wanda ya isa ya hana shi kashe ta, zuwa can Husnah ta ce, "mutuwa kaine kake tsoron yin ta, ni kuwa daman na dad'e da mutuwa, dan haka barazana bata sakani wani tsoron mutuwa ka halbe ni kawai na futa da wannan 'kuncin rayuwar ! ".

kawai Husain ya 'kara saita Bindigar sa akan Husnah Kawai sai sukaji ta lau anyi halbi, jin kake damm.......!


*A GIDANTA NA GIRMA*


*BY NANA: KHADEEJATU*

*_UMMU IHSAN_*


*SADAUKAR WA GA :- DUK KANNIN MASOYA NA NABOYE DANA BAYYANE INA SONKU SOSAI SON FISABILILLAH*


*YA ALLAH KAJIKAN MAHAIFINA KAYI MASA RAHMA KA KYAUTATA MAKWANCIN SA SHIDA YAN UWA MUSULMI BAKI `DAYA.*


*YA ALLAH KA BAIWA MAMANA LAFIYA KA BAIWA DUK KANNIN WANDA BAIDA LAFIYA NA GIDA DANA ASIBITI ALLAH KA BASHI LAFIYA AMIN YA ALLAH*




*_Bismillahir Rahmanin Rahim_*

51~55

Ga baki d'aya gurin duk sukayi mutuwar tsaye sai kallon_kallo a keyi Husnah kuwa tuni ka kame guri d'aya idon ta a rufe .

Su Shaheed kuwa juyowar da zasuyi cike da mamaki sai ganin Alhajin su sukayi da su Hajiyar su dasu Anisah tare da jami'an tsaro harda Yayan su a ciki.

Husnah na jiyowa idon ta ya sauka akan wani mutum kwance cikin jini ga Bindigar sa ta fad'i a 'kasa, ashe cikin duhu ya boye ya saita kan Husain zai halbe shi, wannan CID suka gansa suka halbe sa.

Zubaidah kuwa ita a tunanin ta, Husnah ce, aka halbe, shine ta shiga cikin wani mugun shorct dan ita tunanin ta yanda zata sanar da yallabai.

Husnah kuwa tana kallon su Shaheed da Husain taga babu abunda ya same su, kawai tabar gurin da gudun ta ta shige cikin gidan ta fad'a cikin d'akin ta, ta rufe, zaman dir shan tayi zaman yan bori, tana zubar da wasu uban hawaye masu a zabar zafin gaake.


Ita kuwa Zubaidah ita da jama'ar ta suna ganin Husnah ta shige cikin gidan da gudu suma suka mara mata, baya.

Jami'an tsaron kuwa kama wannan mutanen sukayi Suka anshi Bindigar dake hannun Husain suka bar gidan dasu, Hajiyar kuwa fad'ar takeyi, "ina fatan duk kuna lafiya, babu abun da ya same ku ko?.

Duk suka rungume iyayen nasu, Shaheed ne kawai yake magana amman banda Husain.

Alhajin kuwa cewa yakeyi, "Husain ka ri'ka aiki da hankalin ka, fiye da aiki da izgilanci, Husain dan Allah idan kasan fushin zuciya baya barin ka, aiki da ilimin da Allah ya baka to ka daina yin kutse a cikin lamarin da bai shafeka ba".

Shiru Husain yayi Amman zuciyar sa jin ta takeyi kamar ta

Please Login or Register in order to submit comment