Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta bata iyawa dasu sai dai ji'ka_ji'ka.

'karaso mutanen biyu sukayi d'ayar tace, "bakwa bu'katar sallama da munyo maku, Am ba zamu 'bata lokaci ba, nasani sarai wannan gidan shine gidan Sa'idu kuma mijin mataciya da musaka, am batare da 'bata lokaci ba, munzo ne zamu d'auki "yar mataciya Husnah take ba? ".

Malka tace, "uban waye ya turo kune yace kuzo kuyi wa mutane fitsara 'kana nan yara daku?".

Kawai d'ayar tace, "ubanki ne ya turo mu kaji shegiyar mata ana magana da wanda yake matsayin uban yarinya shine zaki wani sakawa mutane baki? Kuma idan kika 'kara kwatantamu da 'kana nan yara sai mun nuna maki cewar munfi ma inda kike tuna nin kaimu".

Malam yace, "waye ya turo kune gidan nan? ".

Kai tsaye sukace, "Amina ce 'Kanwar ka ga photon ta, ansar photon yayi yace masu, "ga Husnah can ke kizo kibisu".

Malka tayi tsalle ta dire tace masu, "babu inda zata, sai dai su d'auki Indo ko Nafi".

Kallon inda takeyi masu nuni sukayi suka bushe da dariya, d'ayar wadda tun zuwan su batayi magana ba, tana dai kallon sune d'aya bayan d'aya tace, "Husnah muka zo d'auka kuma ita zamu d'auki dan haka kubamu Husnah ta bud'e jakar ta ta d'auko bandir din yan naira dari biyar biyar ta isa gaban Malka ta janyo hannun ta ta d'ora mata, ta wuce ta isa inda Husnah ta janyo hannun ta suka zo zasu fita Husnah da sauri ta kwace hannun ta tayi cikin d'akin su da gudu jakar da Zarah ta shirya mata jiya itace ta kama ta run gume, tayi zaune tana zabga kukan da tarasa na miye ma takeyi, saukar lafiyayyen mari taji wanda ya d'aga mata hankali ya rud'ata da sauri ta tashi tsaye Baban sune tsaye yana fuci kamar wani wanda yayi gamo da kumurcin maciji, ya janyo hannun ta da 'karfin gaske ya fito d'akin da ita ya dan kawa matan nan su biyu ita yace gata nan baiwar kuce duk irin hukunci da kuka ga damar yi mata kuyi mata shi saboda ta 'bata maku lokacin ku kuma ku sani ita din baiwar kuce duk irin hukunci da kuka ga damar yi mata koda laifi ko babu kuyi mata ai dai kun biya kud'in ta tunda kun bani dubu dari da goma kun baiwa Malka dubu hamsin yaran gidan nan kowa dubu ukku ukku".

Dariya sukayi suka ja hannun Husnah wadda maganar da Baban yayi taka ma yi mata yawo a 'kwa'kwalwa sai kawai ta saki jikin ta tabisu babu wanda yayi yun 'kurin biyar bayan su babu wanda ya tambayi sunan su kawai dai sun sayar da marainiya ne.

A cikin motar su suka saka ta suma suka shiga driver ne kejan taxi din, 'yan unguwar kuwa cike da mamaki yaran da suka labe lokacin da suka ga zuwan wannan mutanen duk sunji abunda ya faru ai kuwa suka sanar wa mutanen unguwar, ai kuwa mutanen na shiga motar har sun fara tafiya aka bisu da jifa.

Da gudu suka bar unguwar suka d'auki hanya sai wani dajin a bakin titi suka tsaya, suka fito suka sallami mai taxi din suka shiga tasu motar suka d'auki hanya tun sha biyun rana sai 'karfe shida suka tsaya suka sayi abinci a wani hotel suka baiwa Husnah baiwar Allah Leda d'aya suka d'auki nasu suna tafe sunaci ita kuwa Husnah ta 'kasa wani dogon motsi dan ta tabbatar da wannan mutanen masu yanka kan mutane ne.

Jin jikin ta na rawa, gashi har 'karfe tara na dare yayi ne ya sakata yin saduda ta bud'e ledar ta d'auko robar ciki ta lemo da naman kazar dake ciki ta soma ci, cin yuwa sai da ta 'koshi zuwa dare misalin 'karfe sha d'ayan dare suka 'karaso inda suka tsaya a bakin titi matar d'aya ta bud'e motar ta fito ta zago gurin Husnah ta bud'e motar ta janyo hannun ta daman Husnah ri'ke take da jakar ta, fitowa tayi sukayi sallama tace mata jirani na kawo maki naki kason, ai kuwa da murna matar ta sara mata, hannun Husnah ta ja suka tsallake titin a gurin wata 'katuwar mota fara suka tsaya ta janyo remote ta bud'e motar ta saka Husnah a kujerar mai zaman banza ta rufe, ita kuma ta zagayo ta bud'e motar ta d'auki wata jakar ta tsallaka titin ta kaiwa matar, aikuwa da farin ciki ta ansa ta bud'e jakar cike da kud'i, sukayi sallama suka rabu.

Tana bud'e motar ta shiga kawai ta tayar da motar suka d'auki hanya tana tu'kin motar tana kallon Husnah ganin duk ta takure guri d'aya sanyi yayi mata yawa sai tayi dariya tace.......


*Comment and share*


*GIDAN TA NA GIRMA*


*SADAUKAR WA GA :- DUK KANNIN MASOYA NA NABOYE DANA BAYYANE INA SONKU SOSAI SON FISABILILLAH*

*YA ALLAH KAJIKAN MAHAIFINA KAYI MASA RAHMA KA KYAUTATA MAKWANCIN SA SHIDA YAN UWA MUSULMI BAKI `DAYA.*

*Alhamdulillah Allah muna godiya a gareka daka nuna muna sallah lafiya ya Allah ka karbi ibadun mu ka yafe muna kura kuren mu amin*

*Ina yiwa kowa barka da sallah Allah ya mai_maita muna amin*


*_Bismillahir Rahmanin Rahim_*


11~15

Tayi dariya tace, "idan ma zaki saki jikin ki yarinya to ki saki jikin ki dan duk duniyar nan babu wanda yasan wace ce ni kuma daga Ina nake sai Allah dan ko wannan matar ko sati d'aya ba muyi da haduwa da ita ba, ke ko sunana na gaskiya bata sani ba, ballema wata Amina gwaggon ki dan haka yariya sai kiyi mani biyayyah kamar yanda tsohon ki yace, idan kuma ba haka nan ba him! ".


Ita dai Husnah da ido kawai take bin ta dan ba kowane irin zance take ganewa ba da manufar zancen saboda karancin shekarun ta da kuma uban baccin da takeji Amman kalmar ta da tafurta cewar, "gwaggo Amina bata santa ba ta bata tsoro matu'kar tsoro, tunanin ta ya bata saceta kawai akayi, sai kuka takeyi tana kiran Aunty Zarah.


Wata uwar tsawa ta daka mata a take kukan ya bacewa Husnah sai ta kara firgita kamar kace mata ar ta gudu sai zarar ido takeyi, Abu da kuruciya idan an natsu guri daya sai bacci ai kuwa bacci ne ya dauketa mai cike da tsoro sai firgita takeyi acikin bacci, ita kuwa matar duk abunda Husnah keyi akan idon tane kuma tsab tayi kamar bata sanda ita ba hankalin ta na akan titi sai gab da asubahi suka iso cikin gari tayi tafiya sosai a cikin garin kafin ta 'karasa a wata unguwar wani katon gidane ta nufa tayi horn aka bude mata ta shiga da motar a cikin gidan a gaskiya duk da duhun asuba gidan kyawun sa yana nan daram bud'e motar tayi ta dauko Husnah tayi cikin gidan da ita a kujerar falo tree star ta kwantadda Husnar ita kuma ta haye up.


Husnah sai 'karfe shidda ta samu falkawa ahan kali ta soma biyar falon da ido a figice kawai idon ta na 'karasa sauka akan katowar plasma kawai ta zun duma uban ihu wanda sai da duk wanda yake gidan ya firgita a tamanin duk suka karaso cikin falon harda matar da tazo da Husnar ganin iri yanda duk ta rudene bataji bata gani sai ihun takeyi ne gashi su basuga komai ba kawai da sauri matar ta karaso gurin Husnar ta riketa tana girgizawa tana fadar, "kee Husnah lafiyar ki kuwa uban miye kika gani wanda ya tsorata ki da har kike rafka wa mutane irin wannan ihun iye!? "

A cikin masifa take zancen wanda ya kara firgita Husnah kawai tayi luuu ta some a take aikuwa duk mutanen dake gurin suka kara tsorata ganin karamar yariya a firgice gashi har ta kaita da somewa cikin zafin nama wasu maza masu uniform iri d'aya su biyu suka karaso da robar swan suka yayyafa mata ruwan a fuska da jiki atake ta sauke ajiyar zuciya ta dawo cikin hayyacin ta, ahankali ta soma bud'e idon ta.

Da kallo take biyar su har idon ta yadawo a kan matar da tazo da ita hara rar da matar takeyi matane yasaka ta sauke idon a 'kasa.


Matar tace, "zaku iya tafiya" tana nuna masu hanya, dukan su babu musu suka fita, kallon Husnah tayi tace, "bazan iya daukar maki kauyenci ba, kuma daga yau daga rana mai kamar ta yau kada na sake ganin kin tara mani mutane acikin falo kuma duk wani 'kauyenci naki ya 'kare daga yau saboda haka tashi ga kayanki nan ki dauka mushiga ciki na nuna maki masaukin ki koma nace muhallin ki, haka Husnah ta tashi jiki ba wani 'kwari suka shiga cikin d'a kunan dasuke acikin falon ta kaita wani d'akin mai dauke da gado madai_daici da way drop fentin d'akin purple ne da green akwai rowel na labulai ash color haka kayan d'akin ash color ne, nuna mata komai tayi da amfanin sa, sannan ta bud'e mata kofar toilet da take gurin ta 'karasa nuna mata da koyar da ita yanda zatayi amfani da komai dan bata son yawan tambaya, da gida danci tana gama koyar da Husnah komai sai ta fita tabarta a gurin wanka tayo da alwala cikin rashin iya amfani da komai sosai amman tayi 'kokari gaskiya, sauya kayan jikin ta tayi tayi sallah tayi zaune ta rafka uban tagumi kamar wata babbar mace, ahaka matar tashigo mata da abinci ta ajiye mata a gaban ta tace, "ga abinci nan kici idan kin 'karasa ki sameni a falo" bata jira amsar Husnah ba kawai tasaka kai ta fita.


Da sauri Husnah ta soma shan tea mai kaurin gaske sai kamshin kayan yaji yakeyi har tana kone baki amman taki ajiye wa har sai da ta shanye coffin duka san na ta lura da wainar kwai aikuwa kamar an aikota kawai ta soma ci kamar wani zai kwace mata haka tazo akan arish amman ta kasa iya cin sa, loma d'aya tayi ta ajiye sa a gefe tana fadar, "wannan abun babu dad'i gaskiya dama nasani da banci ba na 'bata bakina, kuma fa na 'koshi sosai kamar zanyi amai wai Allah inda ma anty nanan ko mamar mu wai da sunci wannan dad'in wallahi amman ko yanzu ai nasha lama dan nakusa cinye komai bari dai naje na kai masu sauran kilama shike nan ni take jira na kawo mata sauran itama taci, kilama duk kurine irin na wannan aljanar matar ai wallahi tunda aka fara kawo mani dole ne naci yanda nakeso na rama irin yanda su Gwaggo marka da Baba da yaran su suke yi muna nida Anty Zarah da mamar mu".

Haka dai Husnah tayi ta zabga shirme har sai da matar ta gaji da jiran ta tazo ta sakota a gaba tare da kwaso kayan da taci abincin, har kitchen ta raka Husnah takai kayan suka dawo cikin falon ta zaunar da Husnah a 'kasa ita kuma tana akan kujera ta d'ora 'kafa d'aya akan d'aya tana girgizawa tace, "Husnah ki bud'e kunnen ki, ki saurari abunda zan sanar maki, da kyau"


"Husnah ban dauko ki dan narasa yar aiki ba, ban dauko ki dan bani da kanwa ba ko yan uwa ba aa kuma ban dauko kiba dan bazan iya haifuwa aa, kawai dai na d'auki kine, saboda wani dalili wanda bazan iya sanar dake ba ko wane irin dalili ne, amman zan iya sanar dake sunana da wasu abubuwa wanda babu wani mahalukin da yasan haka, tun bayan sauyuwar da nayi, Husnah Sunana Zubaidah Ashir mu hudu ne a gurin iyayen mu duk kannin mu matane nice ta ukku Asma'u ce babba sai Ruma sai ni sai kanwata Zulai, kowa daga cikin yan uwana yanada kamun kai nice kawai daban dasu, inada shekara sha hud'u na bata rayuwa ta iyayena sunyi kukan bakin ciki sunyi mani nasiha da lurar dani akan illar abun amman ni ban wani damu ba, sai itayen nawa suka rika sanya mani ido sam sun hanani fita, ko nan da kofar gida atakaice dai sun sanya ni kulle, nikuwa cikin dare nake tserewa tun basu gane ba har suka gane sunyi sunyi amman abun yacitura sai dai suka sanya mani ido tare da addu'ar shirya a lokacin inada girman jiki sosai babu wanda zai iya yarda da cewar Asma'u yayata ce, duk ganin akeyi nice babba, inada shekara sha biyar nasoma zubar da ciki tunda iyaye na suka fuskaci haka suka fara neman su auraddani ni kuwa na shammace su na gudu, akikacin inada shekara sha bakwai a gaskiya bariki tayi babu mai hanani babu mai takurani, bariki ta karbeni da bariki nayi kud'i natara manyan gidaje da motoci da manyan kadarori dan haka kema zan d'ora ki a wannan harkar idan kinason kiyi kud'i ki rama abunda matar Baban ku da Baban ku sukayi maku keda mamar ku da Antyn ki zan wayar dake fiye da tunanin mai tunani".

"Nabaki wannan labarin ne Husnah dan nasan bakida wayau ballema 'kwa'kwal warki ta rike wannan sirrin nawa, ballema kisan duk abun da na aikata yanada kyau ko baida kyau dan bana bukatar zuwa gaba kiyi mani wata tambayar kwatan kwacin hakan".


Ita dai Husnah kallon ta kawai takeyi amman sam bazara iya fahimtar miye jigon labarin nata ba itafa kawai kallon Zubaidah takeyi amman duk abunda take fad'a bata gane ba sai kud'in kawai da motoci sune kawai taji sun burgeta a labarin cikin farin cikin da an nushuwa Husnah tace, "dan Allah nima ina son nayi kud'i masu yawa da gani sai Anty Zarah kawai bada kowa ba".

A cikin kuriciya Husnah take maganar ta amman kuma ita Zubaidah ta yarda har cikin zuciyar ta.

Zubaidah tace, "Yauwa Husnah yanzun dai tunda kin yarda daman haka nake sonji ina son ki yarda da bariki dan bariki uwace, shiyasa na daukeki keda kike karamar yarinya kuma marainiya wadda batada uwa nasan bazan sha wata wahalar ba sosai, shiyasa na nafi yarda da na daukeki gaki kuma naga kwata_kwata bakida wayau koda zuwa girman kine sai na mayar dake babbar yar dana haifa da cikina".

Dariya kawai Husnah keyi harda tsallen murna zatayi kud'i.

Yinin ranar hidima kawai takeyiwa Husnah wanka ne kawai batayi mata, sai dai tace jiki kiyo wanka.

Cikin wata biyu sosai Husnah ta sha'ku da Zubaidah wadda ta d'auki burin duniya ta d'ora akan Husnah kuma itama kullum cikin yawon ta takeyi.


Kwanci tashi babu wahala a gurin Allah gashi Husnah ta shekara ukku gidan Zubaidah yanzun tana yar shekara sha ukku kenan sam idan kaga Husnah bazaka ta'ba gane taba dan ta zama kamar d'iyar turawa tayi fari da kiba abun sai sam barka kuma tana zuwa school tsadaddiyar gaske Husnah bata wasa da karatu turanci kuwa kamar wata baturiya ya zauna mata akan halshen ta, amman kuma sallah sai abun ya bugo mata takeyi idan tanayin sallar ma Zubaidah fad'a takeyi amman ita Husnah takasa dainawa saboda kullum tana kallon hoton su itada Anty Zarah, kuma tana mafalkin tada mamar su gashi kuma ta kasa sanar da Zubaidah.


Husnah ce kwance tanayin Assignment Zubaidah ce ta shigo itada wani mutum saurayi sam Husnah bataga wani abun kallo a garesa ba amman shi kallon ta kawai yakeyi, kamar wani tsohon maye, hasala Husnah tayi, kawai tayi tsaki ta tashi ta kwashe kayan karatun ta, ai kuwa zata wuce, aka daka mata uban tsawa wadda sai da yan hanjin cikin Husnah suka katsa da sauri ta saki kayan hannun ta ta zaro ido waje, kawai......


To mizai samu Husnah?

Kuma waye ya dakawa Husnah tsawa Zubaidah ko wannan mutumen?


Shin Husnah zata biyewa yan bariki tayi bariki ko kuwa?


Shin ina labarin Anty Zarah da kuma su baban su Husnah?


Duk wannan amsar tana gurin Ummu ihsan, kudai kudai biyoni dan jin wannan amso shin, dan labarin ba'a fara komai ba daga cikin sa.




*GIDANTA NA GIRMA*



*BY NANA: KHADEEJATU*

*_UMMU IHSAN_*


*SADAUKAR WA GA :- DUK KANNIN MASOYA NA NABOYE DANA BAYYANE INA SONKU SOSAI SON FISABILILLAH*


*YA ALLAH KAJIKAN MAHAIFINA KAYI MASA RAHMA KA KYAUTATA MAKWANCIN SA SHIDA YAN UWA MUSULMI BAKI `DAYA.*


*Alhamdulillah Allah muna godiya a gareka daka nuna muna sallah lafiya ya Allah ka karbi ibadun mu ka yafe muna kura kuren mu amin*


*Ina yiwa kowa barka da sallah Allah ya mai_maita muna amin*


*_Bismillahir Rahmanin Rahim_*


16~20

"Zaki rufewa mutane wannan shegun idon naki ko kuwa sai nayi maganin ki a gurin shegiya?"


Wan nan gayen yace, "Him baby shiyasa nake tambayar ki wace ce ita wannan fitsa rarriyar yarinyar kika ki sanar dani ita din wace ce gashi raini 'karara a fuskar ta ya bayyana a kaina da alama idan ta 'kara girma sai tace ita d'in wata aba ce ni dama zaki bani ita na koya mata hankalin".


Yana maganar yana lasar baki kamar wani tsohon maye.


Wata uwar harar ce Husnah ke binsa da ita hawaye duk sun wanke mata fuska, sai shashshekar kukan ta kawai ake ji.


Zubaidah cikin takaici da nuna bacin ranta a fili tace da Husnah "daga yau daga rana mai kamar ta yau na kashe wasa dake Husnah kuma na kashe maki kirana da Aunty sai dai mommy Ina ganin wannan shine 'karshen ranin da kike son yi mani tare da ba'ki na, kuma daga yau ko kallon banza dana arziki ban yarda su had'aki da duk wani bakona ba namiji ne ko mace, kuma yan zun nan nake son ki kwashe tarkacen ki kibar gurin nan kafin nafito maki ai nahin kala ta".


Da hannu take nunawa Husnah ta bar gurin ai kuwa cikin hanzari Husnah ta kwashe kayan ta tabar gurin tana kuka.
Bayan su Zubaidah sun zauna ne take baiwa mutumen hakuri take sanar masa da cewar Husnah yar Yayan tace aka bata halak malak.


Acan cikin d'akin kuwa Husnah kuka kamar ranta zai fita, sai da tayi mai isar ta har bacci ya d'auke ta fuskar ta duk ta kumbura saboda kuka.


Tun daga wannan ranar Zubaidah take d'aure wa Husnah fuska kuma Husnah girma sosai take bata mommy sama mommy 'kasa sam babu raini kamar wadda ta haifeta haka take baiwa Husnah umarni.


Haka rayuwa take tafiya wata rana farin ciki wata rana akasin hakan gashi Husnah girma takeyi kyawun ta nafita amman sam Husnah bata san kimar kyawun taba ita dai gata macce har macce domin Husnah kam akwai daukar hankalin mai kallon ta mace ko namiji ita kanta Husnah kyawun nata har tsoro yake bata, sam Husnah bata san wani abu ba wai saka mayafi ajikin ta, kai ko dan kwali da hula Husnah tun da take a gurin Zubaidah bata ta'ba siya mata ba, duk cikin kayan Husnah daga riga da wando sai riga da skict na kanti kuma duk mafi aka sarin kayan Husnah mini ne takalmi kuwa hell sai mai tudu.


Husnah ce tafe daga ita sai riga iyakar ta zuwa cibiyar ta sai wandon ta crazy kanta kuwa twisting ne a kanta kamar wata 'yar Baby ga wani no respect glass dake idon ta fuskar ta babu makeup sai with lips da ta d'an shafa, tafe take tana taku a hankali kamar mai tausayin 'kasa key ne a hannun ta tana kad'awa da d'aya hannun ta d'aya hannun kuwa littafai ne ta rugume, hara bar gidan ta nufo har ta iso a bakin wata jar mota tabud'e ta saka littafan zata shiga kawai daga bayan ta taji ance, "sannun ki Husnah wato kedai kullum cikin yin sakko zuwa makaran ta bayan ko karyawa bakiyi ba, duka_duka yanzun fa bakwai tayi na safiya, to nidai yanzun kam bazan lamunce maki ba muje maza ki karya kuma akwai maganar da zamuyi dake duk yanzun nake da wannan lokacin".


Dan bata rai Husnah tayi tana doka kafa kamar wata karamar yarinya cikin shagwaba wadda bata san tanada ita ba, tace, " I'm so sorry mommy Wallahi bana son na makara ne, sabido akwai wanda suke da burin ganin nayi latti suyi mani fonishiment gashi mun kusa fara WAEC da NECO kin ga kuwa bazan so na fits da tabo ko d'aya baby dan ba girma na bane kuma ba ajina bane".


Dariya marar tayi tace, "nikam dai yau sai kin bani lokaci dan wallahi idan kika tafi ba tare da munyi wannan maganar ba bazaki sameni a gidan nan ba dan zani dubai ne yau guy kawai nake jira, dan ma nice na dakatar da tafiyar da tun da asuba muka bar 'kasar nan".


Tun lokacin da Zubaidah ta ambaci guy a cikin maganar ta, Husnah ta d'aure fuska ta rufe motar tabi bayan Zubaidah batare da kowace daga cikin su tasake cewa uffan ba, a babban falon gidan suka zauna inda aka jere abinci a cikin kuloli iri daban_daban tea kawai Husnah ta had'a tasha batare da kowa yayi wata magana ba, bayan Husnah ta ajiye coffi ne ta dawo da hankalin ta akan Zubaidah tace, "mommy na 'karasa".


Zubaidah tace, "ok Husnah akwai kud'i masu yawa na tura maki ta account dan zanyi tafiya wannan lokacin mai dad'ewa kuma ni kaina ban san lokacin da zan dawo ba saboda tafiyar ba tawa bace, ta guy ce, so bana bukatar ki kawo kowa a gidan nan haka zalika ban yarda kije gidan uban kowa ba saboda akwai wani alkawarin a kaina kuma kin ga ni nasaba harka da manya masu kud'i dan haka bana harka da talauci kuma duk uban da kika baiwa kanki batare da sani naba sai na hallakar dake a 'kasar nan san nan kuma komai kudin mutum kada ki yarda suga damar ki har mutum yasamu kanki ba tare da yasha bakar wahala ba, kina ganin yanda mazaje masu naira suke gwaggori yon zuwa gidan nan dan haka idan kunne yaji jiki ya tsira".

Tana kai aya Husnah data kafe ta da ido tun lokacin da Zubaidah tasoma maganar ta, ta nisa tace, "shike nan ko mommy? ".


Zubaidah tace, "mai hali dai baya fasa halin sa kekam Husnah zan so naga naki mazajen".


Tashi kawai Husnah tayi batare da tabata amsa ba ta saka kai zata fita har sai da ta kusa fita a bakin kofar sannan ta juyo ta kalli Zubaidah tace, "mommy sai kin dawo zanyi kewar ki duk da nasaba da hakan tun ba yau ba".

Juyawa tayi, tayi tafiyar ta, taja mota ta fita da karfi kamar wadda zata tashi sama tana tafe tana duban a gogo karfe 7:30 har tayi ai kuwa ta karawa mota wuta.

A can gidan kuwa tun lokacin da Husnah tayi wa Zubaidah magana ta fita kawai sai tayi murmushi tace, "nakusa zama miloniya nida nake da zan ka d'ed'iyar budurwa irin wannan gashi dai a zahirin ido idan ka ganta zaka dauka batajin hausa bama zakayi zaton cewar tasan kalma d'aya daga cikin hausa ba, Husnah ke nan yarinyar da zatayi gado na koma fiye dani da abunda nakeyi, Husnah kece jarina, yarinya 'yar shekara sha tara takwas yarinya mai lokaci ga natsuwa da aji a gaskiya dole ne na 'kara saka ido akan Husnah dan saura wata hud'u ta cike shekara sha tara, kuma a wannan ranar ne zan cika nufi na akanta".

Wani makirin murmushi tayi kai da taga abun baiyi mata ba kawai ta tashi tafara taka rawa sai da tayi rawa mai isar ta sannan ta zauna ta d'auko waya takira wata number ta kara a kunne tayi wata magana ta kashe wayar, horn akayi mata kawai ta d'auki jakar ta da akwatin ta taja tayi waje, a dai_dai bakin get tasamu wata bakar mota tana zuwa aka bud'e mata tashiga suka tafi.


Husnah kuwa a bakin get din wata makaranta, ta danna horn aka bud'e mata tashiga wow masha Allah wannan school din kamar ba a wannan 'kasar take ba, saboda tsabar girman ta da tsarin ta, a wani symbol aka, rubuta M.G. D. S. S millions

Please Login or Register in order to submit comment