Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

maganar Husain cikin 'bacin rai yace, "kan uban can uban waye tuzorun ne? ".

Husnah ta murguda masa baki tace, "duk wanda ya tsargu dashi nake ".

Duka Husain ya kawo mata Ummey tayi saurin tare sa, kafin Ummey ta dawo hannun ta tuni Husnah ta janyo ruwan sanyi ta bude robar zata zuba masa, wannan matar da mutanen gurin sukayi saurin anshe ruwan suka janyo hannun Husnah.

Husain cike da fushi ya ce, "ai da kun barta tayi gan gancin ai kata wannan d'an yen aikin da yau anyi gaggawar kama maki gado a asibiti ".


Husnah tace, "daman burin ka bai wuce kaga baya na ba, kuma ni nafi karfin ka wallah...


Kafin Husnah ta rufe baki kawai taji saukar mari, wanda tunda Husnah take rayuwar ta da girman ta a iya sanin ta, shine mari na ukku da aka ta'ba yi mata, ba Husnah ba, hatta Husain da su Ummey sai da sukaji saukar marin.

Daga ido sukayi suna kallon wanda yayi marin waye zasu gani?.


Anisah dake zuwan ta ke nan ta zaro ido waje tace kai, Anty Husnar ce kika mara har hakan! ? .


Ummey kuwa cewa tayi haba mi yasa kika aikata irin haka bayan kowa yasan ba halin ki ba ne?.


Husnah kuwa rufe idon ta tayi sai kawai ruwan hawaye ke zuba, a take gurin yayi ja, shatin hannu ya bayyana, a fuskar ta.


Kawai Husain ya ce, "haba Anty Z mi yasa kika aikata irin hakan bayan kin san kowa yana ganin girman ki da kawaicin ki, ga ilimin da Allah ya baki?.


Cikin takaici ta fara magana, "haba Husain taya zaka bar 'karamar yarinya irin wannan tazo tana sa'in sa da kai bayan yanzun da, da can ba d'aya ba, yan zun fa kai ne a gaba da ita, kuma abun da take shirin aikawa aikin yan wuta ne, ya kamata a taka mata burki dan zuwa gaba zata ce, zaku ri'ka yin danbe ne ko a gaban uban kowa, tunda bata da kunya, shi yasa tun farko ban yarda da ka amince ka Aure ta ba! "


Yaya Yusuf ne ya ce, "kin kyauta kamar yanda kike ganin Husain kane ne a gurin ki haka nima nake ta kamar cewar wannan yarinyar kanwata ce, kuma yanda baki son ganin an batawa wa Husain haka ita ma ta'ba ta tamkar ta'ba wani yanki ne na jiki na, dan haka, zaki iya zama anan gidan sai ranar da kanwata taji zata iya yafe maki ".


Hannun Husnah ya ja suka bar gurin ya fita da ita daga cikin gidan suka shiga cikin motar sa, yaja suka tafi.


Anty Z kuwa da su Husain da su Ummey zaman dirshan sukayi kowa sake da baki Husain ya ce, "Anty yau fa kin ta'bo wa kanki shi yasa ban so kika saka bakin ki ba tunda nasha sanar dake cewar nine kawai Yaya Yusuf yake iya d'aga wa 'kafa idan na ta'ba yarinyar nan, yan zun kin ga shedar ko? Kawai yan zun nasan yayi fushi dake dan haka kada ki yarda kuje tare dashi a gida d'aya wallahi zaiyi maki abunda bai ta'ba yi maki ba, amman yan zun nasan zai sauka idan Daddy yayi masa magana kinji Anty na? "



Gyad'a masa kai kawai tayi cike da mamakin abun ita fa ada yanda take jin Yaya Yusuf yana fad'ar yanda yake jin yarinyar nan kuma Husain yana 'kara sanar da ita sha'ku war su ta d'auka duk da wasa ne amman Yan zun ta tabbatar".


Husain ne ya kira Daddy yayi masa bayanin wani d'an sa'bani ne ya shiga tsakanin Husnah da Maman Baby gashi Yaya Yusuf yaji haushin abunda ya faru har ya ce da Maman Baby ta zauna a nan gidan ko kuma tayi gidan su".


Daddy kuwa yace gashi nan zuwa.

Haka Daddy ya shigo duk da cewar mata sun cika gidan amman ya d'aure ya shigo yana kallon Maman Baby yayi murmushi yace, "kinyi wauta 'yata ai tsakanin Husnah da Husain to kawai ki saka masu ido idan suna abun su, amman idan kika yi wasa kika saka biki su da kansu su Husain d'in zasu baki kunya ne, amman yanzun zan kira wayar Husnah sai na lallaba ta nasan halin zuciyar Yusuf idan yayi fushi ".


Da sauri Husain ya ce, "Daddy bata da waya a hannu ta, wayar ta tana guri na tun kwanaki na anshe ta a gurin ta".


Cike da tsabar mamaki suke kallon sa, Ummey kuwa ta ce, "ja iran ban za, yan zun daman wayar Husnah tana hannun ka shine ita bata fad'a ba kaima baka fad'a ba kukayi shiru? ".


Murmushi Daddy ya yi ya ce, "ku jira zan kira wayar Yusuf d'in , ai kuwa Daddy na kiran wayar Husnah ce ta d'aga, Daddy ya saka hans free ya ce, "Husnah ya ya akayi kukayi fushi ne, kina son Yayan ki Yusuf ya rabu da matar sa, akan d'an wani abun? ".



Husnah kuwa tace, "Daddy kawai sai ta dake ni dan kawai bata sona, tafi son wannan guzumar matar tashi, ai ni wallahi ba bu ruwa na da ita, amman kuma na riga da nayi wa ya Yaya Yusuf magana yayi hakuri ya bar ta tayi zaman ta a tare dashi amman nikam ba zani gidan ta ba, ko da ta haihu ne? Yaya Yusuf ne kawai Yaya na, amman ita kuwa tayi ta zama Yayar tuzorun nan da guzumar matar sa".



Ba mutanen gurin ba hatta Daddy sai da yayi dariyar 'kuruciyar Husnah, tabbas daga jin yanda take maganar ta akwai yarinta a ciki.


Husain kuwa cikin jin haushin Husnah yace, "zan kama ki ne da hannu na, sai kinyi dana sanin wannan kalaman naki ".



Husnah kuwa tace, "kan ka akeji, wai mahaukaci ya fad'a rijiya".


Dariya suka sakar masu, Daddy yace, "Husnah ku dawo gida kiga wani abun kuma kiji wani labari mai dad'in gaske da zan baki".


Husnah najin hakan, cikin farin ciki tace wayyo Daddy daman mun dawo gamu nan a bakin kofar falon".


kashe wayar Daddy ya yi yace, "kujira su 'karaso daga ciki".


Husnah ce a gaba Yaya Yusuf na biye da ita d'aure da fuska, Maman Baby ce ta kafe Husnah da ido itama Husnah ta kafe Maman Baby da ido.


Tashi tsaye Maman Baby tayi da alamun mamaki da far gaba.

Husnah kuwa hawaye ta saki tana gir giza kai, ai kuwa kowa ya tashi tsaye yana kallon su, Maman Baby ta ce, "Huuuuuussssssnnnnnnaaaaashhhhhh.........




*Comment and share*



*A GIDANTA NA GIRMA*




*BY NANA: KHADEEJATU*

*_UMMU IHSAN_*


*SADAUKAR WA GA :- DUK KANNIN MASOYA NA NABOYE DANA BAYYANE INA SONKU SOSAI SON FISABILILLAH*


*YA ALLAH KAJIKAN MAHAIFINA KAYI MASA RAHMA KA KYAUTATA MAKWANCIN SA SHIDA YAN UWA MUSULMI BAKI `DAYA.*


*YA ALLAH KA BAIWA MAMANA LAFIYA KA BAIWA DUK KANNIN WANDA BAIDA LAFIYA NA GIDA DANA ASIBITI ALLAH KA BASHI LAFIYA AMIN YA ALLAH*




*_Bismillahir Rahmanin Rahim_*

81~85


Tace, "Huuuuusssssnaaaaah"? Ta d'aga hannu tana nuna Husnah.


Husnah kuwa gir giza mata kai kawai takeyi, tana ja da baya, kawai ta juya da gudu zata bar gurin, cikin zafin nama Husain ya tare ta, Yaya Yusuf ma 'karasowa gurin yayi ya kama hannun Husnah wadda take ta 'ko'karin 'kwace wa daga ri'kon da Husain yayi mata, tana ganin Yaya Yusuf ta fad'a jikin sa ta fashe da kuka, Husain kuwa damuwa ce cike da fuskar sa, kawai ya juya zai bar gurin Yaya Yusuf ya ri'ko hannun sa, ya janyo su shida Husnah sai a kusa da Ummey ya ajiye su, shima ya zauna ya fara magana.


Ya ce Maman Baby zo nan ki zauna kema a kusa da Ummey ".


Matsowa tayi a kusa da 'kafar Daddy ta zauna, tana kallon Husnah ita kukan takeyi.


Bayan kowa yayi shiru ne sai shashshekar kukan Husnah da Anty Z kawai akeji, Daddy ne yayi gyaran murya ya ce, "Zarah da alama dai wannan ita ce, Husnar ki ko? ".


Gyad'a wa Daddy kai tayi, Husnah tace, "ni Husnar ta ba ce, ni ban ma san taba! ".

Murmushi kowa yakeyi dan gaskiya kam yan zun kowa yaga tsan_tsar kaman da sukeyi da junan su.


Aunty Z ta ce, "Husnah wallahi ko da kin'ki ko kiso nice Anty Zarar ki wadda baki da wadda ta kai ta a fad'in duniyar nan, kuma koda kin furta cewar baki ma san ni ba, zan yar da, domin halin ki ko kwayar zaira ba zan iya man tawa dashi ba"


Kallon ta Husnah tayi tace, "ni ban san ki ba na 'kara fad'a ni bani da kowa wanda zan kalla nace dashi nawa, sai Daddy da Ummey da Yaya Yusuf, amman duk wani wanda zan kalla daga bayan hakan to abokin had'uwa ne da rabuwa, dan haka kije can ki nemi "yar uwar ki ba ni ba ehe".


Murmushi Anty Zarah tayi ta ce, "Allah sarki goggo Marka da Baban mu dasu Indo ko suna wace duniyar ne a yanzun? ".


A take jikin Husnah ya d'auki rawa ta yi sauri ta tashi tsaye ta ce, "wallahi duk cikin wannan mutanen da kika ambata bana kaunar d'aya daga cikin su, kuma indai ina amsa Sunan Husnah wanda mahaifiya ta, ta za'bo ta rad'a mani wallahi sai na d'aukar wa mahaifiya ta fansa, kuma duk wanda yake da sa hannu a mutuwar ta, sai naga tashi mutuwar, kuma kamar yanda Baban su Indo ya nuna muna cewar baya son mu baya son mahaifiyar mu, nima bana son sa kuma bana kaunar sa, haka zalika Marka sai tayi mamakin abun da taso mu zama bamu zamo ba, sun sayar dani ita da mijin ta a gurin mutanen da basu san su waye su ba, dan kawai su halakar dani Allah bai soba, aka koyar dani miyagun dabi'u babu sallah babu salati babu ambaton Allah sai da nazo gidan nan, an kwashe duk wasu abubuwa nawa wanda zan ri'ka kallo ina tuna rayuwar da mukayi, ina kallon mahaifiya ta da yar uwa ta, wadda wani lokacin idan ina kallon photon nasu, nakan tuna da ibada nakayi duk da ban san ko mai ba, duk wannan Abubuwan sai na d'auki fansar su akan wanda yake da alhakin aikata hakan a kain! ".



Tun lokacin da Husnah ta soma magana cikin tsana nin fushi da yanda take sakin magana wadda ya kama ta, a kwatse ta, sai Anty Zarah ta kama ri'kon a barta, tayi dan haka ne zai saka ta iya sauraren ta, ai kuwa kowa ya yi shiru, har ta gama.


Anty Zarah ce ta tashi tsaye ta 'karasa gurin Husnah ta rungume ta ita ma Husnar run gume Antyn ta tayi, suka saki kuka a tare sai da sukeyi mai isar su, sannan Antyn Z ta ce, "Husnah daman kina a raye a kusa dani, aka sanar damu cewar masu satar mutane sun sace muna ke, Husnah kin san irin shiga tashin hankalin da nayi, a kan haka, ko Aure na ce ba zan yi ba, har sai ranar da na ganki, Husnah dan Allah kiyi hakuri ki saurare ni, nasan kanwata tayi farin cikin had'uwa dani sai dai fushin zuciya ne da kuma dukan da nayi maki wanda nasan ba zanyi nadamar sa ba, sai dai naci gaba da lallashin ki, Husnah ki zauna miyi magana ta fahimta kinji "yar kanwata? ".



Sakin ta Husnah tayi ta dawo kusa da Yaya Yusuf ta jin gina da jikin sa tace Anty Zarah nayi farin cikin ganin ki amman kuma yan zun haushi kike bani, kin ma tuno mani ashe ke "yar adawa tace, kije can da naki kannen nima ga nawa Babban Yayan, ko Yaya na, yauwa Daddy gani wane albishir ne zaka bani? ".


Kowa dariyar Husnah yakeyi ga hawaye tanayi, tana gogewa na farin ciki amman ita ala dole fushi takeyi.


Daddy yace, Husnah ta, sun ta'ba mani "yatako? Rabu da su zan yi maki maganin su, yan zun dai mu dawo maganar farin cikin ganin yar uwar ki, Husnah kiyi hakuri kinji ko?, kuma Antyn ki duk abunda ta sanar dake gaskiya ne, nine da baffan ku muka matsa mata ta yarda ta Auri Yusuf amman tace ita fa sai ranar da kika dawo hannun ta, duk yan uwan ta sunyi Auren harda kannen ta, amman ita bata sa ranar Auren ba, ganin haka ne kuma na yaba da hankalin ta, shi yasa na matsa wa Baffan ku, shima yaatsa mata, duk da hakan sai da Husain ya baro 'kasar da yake karatu ya zauna da ita har ta yarda ta Aure sa, kuma koda akayi Auren kullum da photon ki take kwana dashi take tashi, kuma kullum cikin kuka take, sai da Yusuf ya d'auke photon ya 'boye san nan ta rage yawan kukan, kuma tun lokacin da na samu accident din nan na ganki Allah ya d'ora mani sonki, kuma lokacin da Yusuf ya ganki shida Shaheed tuni suka fahimci lallai akwai wata alakar dake tsakanin ki keda Zarah, kuma cikin ikon Allah har kika dawo gidan nan da zama baku ta'ba had'uwa da ita ba, mu kanmu muna mamakin irin wannan tsabanin had'uwar da kuke samu, dan haka Husnah ina taya ku murnar ganin junan ku".


Sai kuma magana ta biyu shine Husnah ke da Husain mun gaji da ganin ku a cikin gidan nan yau d'in na zaki bi mijin ki, ku tafi gidan ku, kuma ni da kaina zan bi bayan ku dan naganar wa ido na, sashen da kika zaba, dan ko d'akin Husain ne kika ga kin fi so to a can zaki zauna, kunji ko? Kece uwar gidan sa sai gurin da kike da bu'katar zama zaki zauna, kuma akwai wasu kayan d'akin da na siya maki da wanda Yayan ku Yusuf ya siya maki, duk zamu saka a kawo maki abun ki a cikin sashen ki, masu d'aura wa zasu d'aura maki abun ki, zuwa da safe dan haka Husain idan gurin bai isa ba zaka 'kara mata da naka sashen ".


Da sauri Husain da Husnah suka d'aga ido suna kallon Daddy wanda ya d'aure fuskar sa babu wata alamar wasa a cikin maganar sa, kawai Husnah taci gaba da kukan ta, Husain kuwa cewa yayi, "Daddy akwai kayan d'akin da na zuba a kowa ne sashen kuma kasan ni ba tarkace nake so ba, shi yasa na saka irin wanda nake so, kuma, ma Daddy ai bada ita na siya ba, amman kuma tunda gashi tayi shishshigi sai ta d'auki na can baya kawai, basai an kawo wasu kayan d'akin ba".


Hararar sa Husnah takeyi ta ce, "kai Daddy dan Allah ku barni nayi zama na anan gidan dan ni ya fiye mani ko wane a kulki ne, irin na tuzoru Allah Daddy ".


Anty Zarah ta ce, "Husnah wai ke miye yasaka kwata_kwata baki da hankali ne, mijin naki ne, kike kira da wannan Sunan? "


Yaya Yusuf ne ya ce, "kin ga malama kibar su, mana suyi fad'an ban kwana dan nasan daga nan gidan an ajiye fad'a sai kuma soyayya da zasu 'kulla".


Ummey kuwa cewa tayi, "Zarah dan Allah kibi komai a sannu indai Husnah da Husain ne sai dai ido kawai, ni kam zan raka "yata har gidan ta, yauwa Husnah ga goggo ki Hajiya Turai Matar baffah ki Isah ".


Husnah kuwa 'bata fuska tayi tayi shiru bata kalle su ba, har sai da Ummey ta sake mai_maitawa , Husnah ta ce, "Ummey nifa bani da kowa kuma duk wanda yake fa alaka da rabani da Anty Zarah babu ruwa na dashi, kuma ni fa Ummey ki baiwa Daddy hakuri ya bar ni a yi zama na a kusa da ku ".


Dariya Hajiyar tayi ta ce, "ni kuwa Husnah tun lokacin da na ganki nake da tabbacin cewar ke yar muce, ni nayi ma mamakin yanda akayi Husnah bata gane cewar ke kanwar ta bace, gaku a gida d'aya sai da naji wannan maganar na fahimci cewar ashe baku ta'ba had'uwa da juna ba, gashi kuma Husnah har nasanar da su baffan ki dasu goggon ki Amina nasan duk suna kan hanyar zuwa su ga "yarsu Husnah ".


Husnah ture baki tayi, gaba, Ummey kuwa dariyar Husnah takeyi, zuwa can kuma Daddy yace, "Husain Husnah 'korafin ku bai 'karbu ba yan zun zaku tashi mu tafi, kuma tashin kawai ".


Yaya Yusuf ne ya ri'ko hannun Husnah da Husain suka tashi tsaye yace, "to goggo dan Allah idan sun iso suyi hakuri bayan sati biyu zuwa ukku sai su ziyar cesu a gidan su ".


Cikin dariya tace dashi, "ko kuma muje raka yar mu gidan mijin ta ba".


Haka kuwa a kayi su baffah na zuwa aka shiga cikin motoci dan ko Husnar basu gani ba, suna zuwa duk an shiga motoci Husnah Anty Zarah Ummey Daddy motar su d'aya Anisah Suhailah Safiya Husain Yaya Yusuf Shaheed motar su d'aya .


Yan rakiya ma sun shiga naso motocin suka d'auki hanya sai gidan Husain.


Tun daga farkon unguwar, ake hango wani had'add'en gida, a gaskiya tsayawa fad'ar had'uwar gidan 'bata lokaci ne.



Masu gadin gidan ne har mutum ukku suka bud'e 'katon get d'in shiga cikin gidan sukayi sunyi tafiya sosai suka 'kara riskar wani get din mutum biyu ne suka bud'e masu get din suka shiga sai harabar gidan flowers masu kyau da sheki da d'aukar ido wasu kuma masu fidda wuta, gida ne hadden gaske yanayin gidajen turawa, part ukku ne a gidan a jere, kuwa duk irin d'aya, gidan amman kuma duka 'kofar shiga cikin gidan d'aya ce, haka suka shiga ko ina glub glub ne masu haske wani babban falo ne suka tsaya suna kallon 'kofofi guda ukku, Daddy ne ya ce, "Husnah ki za'bi wanda kike, so a cikin ukkun nan".



Husnah ta saka hannun ta ta nuna masa 'kofar dama, Daddy kawai ya kalli Husain kuwa cewa yayi, "Daddy ta dai shiga wan can na 'karshen ".


Husnah kuwa tace yauwa Daddy duka biyun nake so, na tsakiyar da wan nan din na damar sa".


Wani irin zabura Husain yayi ya ce, "a gaskiya Daddy ba zan yarda ba, sai dai ta d'auki wannan din na yarda amman banda wannan na tsakiyar nawa ne, kuma kasan na dad'e ina gyaran sa".


Daddy yace, "bani keys din su biyun duka na d'aukar wa 'yata sai dai ka ro'keta ko aro ne ta baka.


Ganin yanayin Daddy kawai sai Husain ya bada makullin yana harar Husnah ita kuwa murmushi ta sakar masa, Daddy ne ya bata makullin, ta bud'e na gefen damar suka shiga sudai yan rakiya dariyar su kawai suke kwasa, wannan Amaryar da angon sai kallon kawai a cikin lamarin su.


Falone babba sai d'aki ukku acikin SA KO wane da bayi a cikin sa, gashi sunji gadajen alfarma da zannen gado GA labulai purple wani d'akin kuma lemon green d'aya d'akin shine mai red, a gaskiya abun sai sam barka.



Kujerun ma abun kallo ne dan zaka rantse ba'a najeria kake ba, a yurai kake kai gidan dai komai yaji.


Yan ganin d'akin na fita Ummey da Daddy suka zauna suka fara yi masu nasihar su zauna lafiya yan zun da da can ba d'aya bane Aure sukeyi a yanzun zo mu zauna zo mu sa'ba.



Fad'an zaman Aure sosai akayi masu harda su Yaya Yusuf haka su baffah sunyi masu nasiha sannan aka kira wayar Daddy yace, "zan fita ansa kira idan kun gama ku jira ni, Hajiya zo kuga d'aya d'akin na Husnah ".


Ummey tayi murmushi ita da su goggo kawai suka fita aka bar su Anisah dasu Yaya Yusuf.

Yaya Yusuf ne yace kai kuje ku gano kuma kada a baku labari amman Husnah ki jira muyo maki video camera ki gani, haka su Anisah suka fita aka bar Anty Zarah da Shaheed da Yaya Yusuf da Husain.


Wayar Yaya Yusuf ce tayi ringing kawai ya ce "ina ga sun kasa bud'e 'kofar ne Shaheed jeka ka bud'e masu" tashi Shaheed yayi ita ma Anty Zarah tace ni ba zani na gano ba, ai dole ne naje naga gidan 'kane na"


Mere baki Husnah tayi ta d'auke kanta gefe Yaya Yusuf dariya kawai sukeyi shida su Shaheed lallai Husnah bata da wayo 'kuruciya ce zallar ta a kan ta, aka bar Yaya Yusuf kawai, Yaya Yusuf ya ce, "Husnah kin ga har yanzun basu dawo ba ko?, bari naje na gano miye ya tsayar da su? ".



Husnah bata kawo komai a ranta ba tace, "ok".


Fita yayi yana dariyar wautar Husnah, Husain kuwa cewa yayi "wallahi shi yaro duk inda yake sai anyi masa na babba da yaro, wai ke 'katuwar mace dake ace kamar ki za'ayi wa wayau a tafi a barki wallahi nikam dai an had'a nida jinjirar yariya shi yasa kika cika rashin kunya ko kuwa dai dan kin saba yawon karuwan cin naki shine zaki zo kiyi wa mutane shiru kamar baki fahimci miye suke nufi ba?.


Husnah kuwa tana jin abunda Husain ya fad'a kawai ta fasa uban ihu ta tashi da gudu zata fita, kawai Husain ya riga ta a bakin kofar ya rufe ya yi tsaye yana dariyar 'keta, Husnah kuma jikin 'kofar tazo tana dokawa, shiko sai dariya yake yi, yace, "yarinya taya zaki zo kiyi wa mutane wasar kway_kwayo? Ni riga da na gano nufin ki yarinya dai na ma wahalar da hawayen ki"


Husnah kuwa cikin kuka ta ce, "mugu kawai wallahi yau sai ka maidani gida ".

Dariya kawai yakeyi tun lokacin da ya gano cewar Husnah kukan gaskiya takeyi bana wasa ba.


Zauna tayi tun tana kuka ana jin muryar ta har takai ga muryar ta bata fita, Husain kuwa tun yana yi mata dariya har yazo ya zauna ya d'auko handkerchief ya ri'ke sa a hannun sa shima ya zauna yana kallon ta, har sai da yaga fuskar tayi ja, yace, dan sun tafi sun barki a gidan kine kika zo keda ma naji kin zabi har part biyu saboda tsabar zari irin naki".



Husnah dai bata ce dashi komai ba har ya gaji da surutun sa yayi shiru abun sa yasaka handkerchief din yana goge mata hawayen idon ta yana dariyar yau fa abun yazo kamar Husnah mai shegen baki wadda bata barin ta kwana ita ce yau ta kyalesa yake cin karen sa babu babba ka.


Suna nan zaune sunyi shiru har 'karfe sha d'aya na dare, yace, "yarinya kima tashi ki kwanta ko kuma kiyo wanka ki sauya kayan jikin ki, kuma kiyi sallar magriba da Isha'i nasan duk bakiyi su ba, saboda tun kayan da mukaje dinner ne a jikin ki, da alama ma rabon ki da kici abinci tun safe yarinya idan olsa ta kama ki ke kika sani, nikam bari ma ki gani".


Tashi yayi ya bud'e 'kofar ya fita Husnah kuwa da harara take bin sa.


Tashi tsaye tayi tana tan gad'i kamar wadda tayi shaye_shaye, a kan gado kawai ta fad'a tayi kwanciyar ta "


Koda Husain ya shigo cike yake da mamakin Husnah, dan kwanciyar da tayi har tayi bacci.


Ajiye kayan hannun sa yayi, ya dawo jikin gadon ya kama dukan filo har sai da Husnah ta tashi cikin jin haushin dariyar da Husain yakeyi mata yace, "bakiyi sallar ba ko? ".


Kyalesa tayi ta tashi zaune cikin muryar ta wadda ta sha'ke tace, "wai miye ruwan ka dani ne, ka kyaleni mana".


Ai wallahi ba zan kyaleki ba, haka kawai kizo ki saka Daddy da Ummey suyi fushi dani suce na barki da yunwa kuma ban kula da addinin ki ba?.


cike da jin haushin sa Husnah ta tashi tsaye ta ce, "ina bayin yake ne saura kuma mutum yaci gaba da yi mani dariyar ".


Dariya ya sakeyi yace, "ke jiki yarinyar nan wallahi dole ne kiyi sallah ".

Nuna mata bayin yayi da hannun sa, kawai Husnah ta nufi bayin, har ta isa bakin kofar bayin ta jiyo tace, "sai shegen shishshigi kawai mutum ya iya".

Ta shige warta cikin bayin ta rufe harda keys,.


Dariya Husain yayi ya d'auki abunda ya

Please Login or Register in order to submit comment