Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

samu ba, da sauri ta nemi after dress din ta nan ma babu, zanen da ta d'ora ne kawai a jikin ta, da sauri taja da baya zata koma cikin bayin kawai taji anyi sama da ita, ihu tazo yi, yayi saurin rufe mata baki ya ajiye ta a bakin gadon ya d'auke hannun sa a bakin ta, yace, "shiiiii Amaryar Husain yau dai Husain yayi niyar mayar da matar sa Husnah ainahin matar sa ta sunna kinga kuwa yau babu wanda zai ce sai na rabu da mata ta, ke anaki tunanin kina nufin dan ina kiran ki da karuwa, abun ya kai zuciya tane, eh tabbas ina kiran ki da karuwa ne dan nine nake son ki zamo mani haka kuma a gareni kawai, kuma dan baki da wayau ne, da zaki tuno ranar dana mari Mardiyya akan ta kiraki da sunan da nine kawai nake kiran ki dashi, kuma a gaban ki nace idan ta 'kara furta wannan kalmar sai na koreta daga gida na, sai dai taje ta auri wani, to yan zun mu dawo maganar hakki na dan yau kam babu d'aga 'kafa ni ango ne"


Husnah kam baki ya mutu, a take Husain ya...........



*COMMENT AND SHARE*



*UMMU IHSAN ce*๐ŸŒน:๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน
8/26/21, 12:41 PM - Ummu Ihsan ce ๐ŸŒนโœ๏ฟฝ?: ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ

*ยฐโ€ขยฐA GIDANTA NA GIRMAยฐโ€ข๏ฟฝ?*

๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ๐Ÿ”ฎ


*BY NANA: KHADEEJATU*

*_UMMU IHSAN_*


*SADAUKAR WA GA :- DUK KANNIN MASOYA NA NABOYE DANA BAYYANE INA SONKU SOSAI SON FISABILILLAH*


*YA ALLAH KAJIKAN BABA NA DA MAMA NA KAYI MASU RAHMA KA KYAUTATA MAKWANCIN SU KA SANYA SU A ALJANNAR KA TA FIRDAUSI BIGAIRI HISAB SU DA YAN UWA MUSULMI BAKI `DAYA.*

*AMIN YA ALLAH*


*To Alhdulillah Allah ya nufeni da dawowa gashi zamuci gaba daga inda muka tsaya*



*_Bismillahir Rahmanin Rahim_*

๐Ÿ”š๐Ÿ”š๐Ÿ”š๐Ÿ”š๐Ÿ”š๐Ÿ”š๐Ÿ”š


111~116

Yace, "malama kuma natsu kawai yau Misha soyayya, kai nima wannan hawaye da kikeyi tun zurani sukeyi dan bana jin tausayin ki yarinya, wai ma ni ina tsiwar taki take ita nake nema yau".

Husnah dai ido ya raina fata, sai ta dawo kalar tausayi, yau harda su kiran Husnah da Yaya Husain dan Allah kayi hakuri wallahi na tuba nabi Allah na bika, amman inaa Husain kam sai da ya maida Husnah cikkakkiyar mace, abunda yayi ta bashi mamaki, bayan shi har photon Husnah ankawo masa ita da wani hotel wanda sai da yayi ciwo akan ganin wannan abun, amman duk da hakan baiji zai iya rabuwa da ita ba, lallai Husnah anji jiki, sai yaji tausayin ta duk ya kama shi ".

Husnah kuwa tun da Asubahi take tsinewa Husain wanda ya yi zaune a kusa da ita ya aikin lallashin ta ita kuwa kukan ta kawai takeyi tana ja masa mugu wanda yake cutar marainiyar Allah, dariya yayi yace, "Allah Husnah idan kika sake koda furta kalma d'aya sai na kashe maki baki dan naga bai mutu ba, gashi ina na ganki d'auke da ciki na, kina tafiya daker".


Tsit Husnah tayi sai shash shekarar kukan ta ke tashi, kama ta yayi ta tashi tana cije baki, ya kaita tayo wanka tayi alwala, ya dawo da ita, ko sallah da ket tayi ta, tana gawa ya kawo mata tea ta sha ya bata magani ta sha, sai bacci, d'aukar ta yayi ya maida ita saman gado, shima ya kwanta sai sha biyu suka tashi shine ya fara falkawa yayo wanka ya saka kayan sa ya fito ai nahin Angon sa, yazo ya fesa turare ya tsare Husnah da ido duk ta rame, murmushi yayi, yayi mata kiss ya fita, sai da Husnah taji tashin motar sa, sannan itama ta bud'e ido, a gaskiya Husnah kam anji maza ba wasa, duk ta zama wata iri.

Daket ta tashi tayo wanka tana fitowa daga cikin bayin sai taga ya ajiye mata riga da siket mini, ba tare da damuwa ba Husnah ta saka kayan, sunyi mata cif rigar hannun d'aya na bireziya gareta, mai ta shafa ta sha powder da jan baki ta saka yan kunne da sarka, ta d'auki turare ta feshe jikin ta, sannan ta dawo bakin gadon ta zauna tace, "wash! Wallahi wannan mutanen mugu ne, 'karar waya taji a kusa da ita tana d'aukar wayar dake saman filo, Ummey ta gani kawai ta d'auka ta fashe da kuka, Ummey tace, "yi hakuri Husnah yan zun haka nace ya dawo mani dake gida, tunda sace ki, tun jiya ya kashe wayar sa, kuma taki wayar a kashe sai yanzu ya zo gidan ya bani wannan number yace wai ya sauya maki waya da layi haka ne Husnah? ".

Husnah kuka dai take Ummey ke tambayar ta kodai wani abun ne, Husnah ta kasa cewa da Ummey komai sai kukan da takeyi, Ummey tace, "Husnah dukan ki yayi ne, ko yunwa kike ji ne? ".


Husnah daket tace, "Ummey wallahi inda ma duka na yayi yafi mugun tar da yayi mani ".

Murmushi Ummey tayi tace, "Husnah kibar ni dashi zanyi maganin sa ki kwantadda hankalin ki ki natsu zan lallaba sa ya dawo dake amman sai ki daina kukan nan gudun ciwon kai".


Haka dai Ummey tayi ta lallashin Husnah ta daina kukan sukayi sallama, kwance Husnah take Husain ya shigo sai da gaban Husnah ya fad'i da sauri ta rufe idon ta dariya yayi yace, Husnah tashi kiji wani labari, kin tashi tayi, saman gadon ya hau da sauri Husnah ta tashi zaune, dariya yakeyi yace, wai Ummey na dawo mata dake gida nikam nace da ita ai kince ba zaki iya rayuwa babu niba".



Kuka Husnah ta sanya masa tace, "wallahi nikam sai ka maida ni gida, dan kaga ka cucheni shine zaka hanani zuwa gida dan kar na kafad'a? "


Dariya Husain yakeyi yace, "ke kina nufin zaki fallasa sirrin mijin kine da naki sirrin Allah ko tafiyar ki aka kalla ansan miye ya faru dan wallahi sai Ummey tafi kowa ganewa".


Husnah kam yan zun taji ba zata iya yarda Ummey ta ganta a wannan yanayin ba kawai sai ta koma ta kwanta taci gaba da kuka, Husain kuwa ansamu abunda ake so Husnah ta daina maganar gida sai yaci gaba lallaba ta da ker ya samu taci kazar Amarcin ta, haka suka yini har dare inda Husnah tace, lallai yau ba zai kwana d'akin ba, yayi ta mata wayau har ta yarda, suka kwana a tare.


Tun daga wannan ranar Husain bai sake yiwa Husnah komai ba sai da yaga ta soma sakin jiki dashi, Husnah kam tun ba'a saba ba har ta zama yar hannu, maganar komawa gida sai tasha kara, Husain yayi ta bata hakurin laifukan da yayi mata haka, ta hakura itama ta nemi yafiyar sa duk suka yafi juna, kawai suka dawo zallar masoya.



Husnah ce kwance tasha ado, tana kallon series gidan 'kamshi kawai ke tashi hankalin ta ya tafi a film din, bata ji shigowar mutane ba sai dai kawai aka dafa ta, da sauri ta zabura, ai kuwa suka saka mata dariya.


Husnah ganin masu dariyar Anty Zarah Anisah Suhailah Safiya da matar Shaheed kawai sai ta saki ihu ta rungume Anisah, Husain da tun d'azun yana tsaye yana kallon su yayi dariya ya 'karasa gurin shima, duk aka zazzauna Husnah da Anisah sai firar yaushe gamo suke, su Anty Zarah ne suka katse masu firar da fad'ar, "A Husnah haka akayi ko? An biyo miji batare da sanin muba ana nan ana shan soyayya".




Dariya suka saka mata, Husnah tace, "kai Anty Zarah satoni fa yayi kuma ku ko kuzo nema na, ai babu komai, koda yake taya ma zaki zo nema ba bayan dan gaban goshin kine ya sato ni, gashi nasan baya laifi, gashi daga zuwan ki har kin nemo laifi na".



Dariya sukeyi, Husain ya ce, "yau Anty Zarah dan Allah dubeta ki gani ai itace ta ce na sato ta ta gaji da zama gidan Ummey kuma tana jin kunyar tace wa Ummey zata biyo ni, shine na taimaka mata, ai kin san ni da taimako ko? "


Da sauri Husnah ta ce, "wallahi mutum ya fad'i gaskiya ai dai naga yanda lokaci d'aya mutum ya dawo wani iri dashi ya rame yayi d'an wuya tunda na baro masa gidan sa, shine kullum cikin zama gidan Ummey ".



Husain ya ce, "yauwa dan Allah halan wane gurin kika tafi, kika sa ina ta wahalar neman ki, gashi Ummey ta'ki bani damar da zan tambaye ta ko na tambayi wani, Anty Zarah dai nasan bata sani ba tunda inda ta sani da ta sanar dani dan kar na wahala da yawa kamar yanda nasha ba'kar wahalar neman gurin da kike, har gidan Anty Zubaidah naje da sunan nazo gaishe ta".



Dariya duk aka sanya harda Husnah Anty Zarah ta ce, "wannan dariyar ta nuna muna cewar duk kun san inda take ko? ".


Anisah ta ce, "kai ne baka kwantadda hankalin ka ba, amman da ka kwan tadda hankalin ka da ka gano inda take".


Husnah tace, "nikam ina gidan Shaheed ina futawa ta".


Husain ya ce, "Shaheed munafuki ashe kina gidan sa, shine yake ce mani nabashi number ki ko na sanar dashi inda kike? ".


Dariya akeyi, Husain ya ce, "ina zuwa".


Tashi yayi ya nufi d'akin sa, yana d'an dad'e kafin ya dawo, da wani babban littafi ya dorashi a jikin Husnah ya ce, "Baby na ki duba wannan littafin yau zakiji abunda baki ta'ba jiba keda yan uwa na, nabaku wannan damar ".


Gefe ya koma Husnah sake da baki take kallon littafin wanda aka rubuta, sirrin zuciyar Husain, mijin Husnah.


Duk sai suka sauka 'kasa suka ajiye littafin a tsakiyar su, Husnah ce ta fara bud'e littafin, kawai photon Husnah wanda takai Daddy asibiti ya bayya na, cike da mamaki Husnah ta d'aga idon ta tana kallon Husain gashi tana d'aukar photon taga rubutu kamar haka:->


_Wannan itace wadda tayi zarra acikin matan duniya muryar ta kawai naji, sai naji zuciya ta, ta amince da ita sai naji cewar kawai itace mata bugun numfashi na_


D'aga mata gira yayi, sai ta sake bud'e wani shafin shi kuma an rubuta,

_ceton mahaifina tayi amman nikam nasan wannan ni aka aikowa da ita, domin na Aure ta, tabbas nikam Allah yayi mani gata, da ya had'a ni da wannan kyakykyawar yarinyar ajin farko, lallai nasamu babban rabo_


Wani shafin ta duba taga an rubuta,


_"ya ilahi na shiga cikin mawuyacin halin 'batan masoyiya ta, na rasa mike damuna, farin ciki na ya gushe, Allah ya kawo mani wannan yar baiwa, wadda duk taku d'aya nata yake bugawa tare da zuciya ta!"_



Haka ta sake duba wani fejin, taga an rubuta,

_Ciwon son wadda bata ma san dani ba a rayuwar ta zai kashe ni, ya Allah koda sau d'aya ne ka bayyana mani ita, damuwa ta Aure ni, nikam ya ya zanyi da rayuwa ta ne!?_



Haka dai sukayi ta dubawa duk na damuwa suke gani, suna zuwa tsakiyar sukaci karo da:-


_Alhamdulillah Alhamdulillah yau Allah ya amshi addu'a ta, Baby Husnah 'yata ta kawo muna shawara munbi kuma gashi nayi nasarar samun jin muryar da ko a cikin mafalki na ba zata 'bace mani ba, ni Husain ina daga cikin masu rabo, abar kauna ta zata kawo kanta guri na.. Ina cikin farin ciki"_


Photon Husnah ne wanda take cikin motar ta tana driving ta sako kan motar ta a gidan su, da wanda ta bud'e motar da wanda ta zuro 'kafar ta, tana murmushi da wanda ta fito a jikin motar da wanda ta rungume Daddy da Ummey da wanda ta fara takawa kai har cikin falon gidan nasu da wanda tazo dai 'kofar d'akin su Anisah taji suna maganar ta, ta tsaya tana murmushi da wanda sukayi fad'a gurin cin abinci da wanda ta fito zata tafi gida har bayan motar sai da akayi masa photo.


D'ago idon ta ta sakeyi tace, "amman taya duk ka d'auki wannan photon haka kuma duk ban san anyi su ba, kuma lokacin da zani koma gida baka nan".


Murmushi yayi yace, "ki bari ki 'karasa mana".


Murmushi Husnah tayi taci gaba da dubawa, photon da tagani ne wanda yafi bata mamaki shine ta fito 'kofar gidan Zubaidah da niyar zata 'boye trolley d'in ta, kafin ta gudo shine ta gani da sauri tace, "wannan ya bani tabbacin cewar kai ne ka sauya wa trolley d'ina gurin ajiya ko? ".


Dariya ya yi babu amsa, tana duba wani shafin taga an rubuta,

_guduwa guduwa guduwa, yan mata na ai guduwa indai ba a gida na ba ban ga gurin da zaki jeba, kiji dad'in sa, dole gida na ne mafakar ki domin nine suturar ki sirrin ki, kuma duk wan nan shirmen na had'in wannan Auren ba zaiyi amfani ba, saboda an ginawa zuciyar ki da tawa mafaka d'aya wato gidan Husain da Husnah zuciya d'aya"_



_Alhamdulillah ga Husain ga Husnah a gida d'aya zuciyoyi biyu a guri d'aya, a gaskiya ina jin dad'in yanda Husnah take biye mani muna fafata soyayya a dabai baye, ni ina nuna mata soyayya ba tare da sanin wani ba itama tana amsa, ba tare da sanin yanayi da girman soyayyar ba, kuma ina gamsu wa da yanda naga sa'kon yana isa a gareki masoyiya ta_




_"Tabbas soyayya tana dad'i musamman ma akanki Husnah, saboda akan kine nasan mine ne farin ciki mine ne ba'kin ciki_


_ya ilaihi wai nine za'a had'a Aure na da Husnah kuma harda su fad'ar sai kayi muna biyyaya dole, lallai ne nayi fice, Husnah ta yarda har zuciyar ta, amman kishi ya hanata bayyana, hakan, abun farin cikin anan kuwa shine, ta yanda Husnah taje gurin dinner din biki na ta soke abun tun alokacin ne na yarda da cewar komai 'boye soyayya wata rana sai ta bayyana tun da gashi, soyayya ta ta bayana akan idon ki Husnah da kuma gan_, gar jikin ki, tabbas ni mai nasara ne, Husnah saboda ki 'kara sona na yarda da cewar zan Auri Mardiyya amman sam ni ko son ganin fuskar ta bana yi_



_zaman Aure na da Husnah nine kawai nasan amfanin hakan kuma ni ba gangar jikin Husnah nake muradi ba ita kanta Husnah da zuciyar ta nake muradi banyi Auren sha'awa da Husnah ba, kuma nayi alkawarin sai idan ita ce naga tana bu'katar hakan amman ni kam nasan soyayyar Husnah halitta tace a hakan, ba zan takura mata ba duk kuwa da yanda nake bu'katar mata ta tabbas sai na tabbar da Husnah ta cika da sona ta yanda bani da wani aibu a gurin ta, sai soyayya zallar ta_


_Haa kashe ni aka zoyi Husnah ta kawo jikin ta, aka halbe ta, tun a wannan lokacin na fahimci cewar soyayya ta tayi tsiro a zuciyar ki Husnah, kasan cewar zuciyar mu d'aya shi yasa aka had'a dani dake aka d'auke wai har abamu bindiga ace na kashe kaina, toh idan na kashe Husnah ai kaina na kashe, haka Husnah idan ta kashe ni kanta ta kashe, to kasan cewar da zuciya d'aya muke amfani, da ido muka tsara komai da zuciyar mu sai gashi lokaci d'aya, mun kaiwa abokin tabar mu bari, kai amman yayan gata ne a soyayya ta da Husnah_


_Daddy kuci gaba da bamu hakuri amman duk da gan hanci muke abun mu, kasan cewar ina son na 'kara tan tance ya zurfin soyayya ta yake a yan zun a gurin Husnah shine na Auri Zee na Aura kuma nayi nadamar Auren nata dan taso ta kashe ni, ta rabani da ruhi na_



_Husnah ina son ki ina kaunar ki ina jiran ranar da kema zaki ce dani mijin ki soyayya ta har abada Allah ya azurta mu da zuri'a ta gari_


ajiye littafin Husnah tayi tace, "muna son 'karin baya nin ka"

Husain ya ce, "Sai kuma abunda nine kawai nasan sirrin sa da fassarar sa shine wanda yake ci maku tuwo a kwarya Husnah shine ina kiranki da Karuwa ".


Husnah tsakani da Allah ni dai wallahi tun lokacin da nafa ganin ki komai naki yana burgeni, amman dalilin da yasa nake cewa haka, shine idan na kiraki da wannan sunan idon ki na nuna mani wanni sirrin wanda na barwa kaina sani, kuma ba zan iya sanar da kowa ba, Husnah ke sheda ce ranar da naji Mardiyya ta ambaci sunan da nine kawai nake kiran ki dashi, na dake ta har na korata gidan su, Husnah wallahi ni har a zuciya ta bana zar gin ki da komai dan haka ni ban 'bata Aure na ba"


"Husnah ina sonki ina sonki ina sonki ina sonki bana son ganin kukan ki ina kaunar ganin farin cikin ki ha 'karshen rayuwa ta dan Allah Husnah ki soni kada ki bani na rasa ki kada ki barni nayi kuka akan rasa soyayyar ki".



Da gudu Husnah taje ta rungume mijin ta, tace, "ina sonka mijina".


Tafi aka sanya masu kowa dad'i yake ji ganin yau su Husnah da Husain sun shirya a gaban su.


Haka gidan ya kasan ce masu cikin farin ciki sai dare suka tafi, haka su Anisah suka sanar da Ummey sosai Ummey tayi farin cikin haka daddy, su Yaya Yusuf da Shaheed ma sunyi farin ciki sosai.
Haka rayuwar su Husnah da Husain ta kasan ce cikin so da kaunar junan su da kulawa ta soyayya.


Sai da sukayi wata ukku suka koma gidan su, Zee na ganin yanda suka dawo kawai ta tattara kayan ta tace ya zalunce ta ya muna funceta ashe dama yana can tare da Husnah yayi mata maganar wayau ya bata kud'i yaci gaba da zama da Husnah wallahi sai ya sake ta, Husnah tace, hubby kada ka yarda ka sake ta share ta kawa, ita ta manta cewar ita da kanta, tace ita tagaji da zaman ka kai da ita, kawai ka bata kud'i kayi tafiya mai nisa itama ta futa, to kanki kika yiwa".


Cikin zafin nama ta kawo wa Husnah mari, amman kafin hannun ta ya sauka a kan fuskar Husnah tuni Husain ya ri'ke hannun yayi mata mari biyu masu kyau.


Ya ce, "ban za kawai ke har kin isa ki mari mata ta bugun numfashi na a gaba na? "


Hannun Husnah yaja sukayi d'akin Husnah, da 'kamshi kawai ke tashi, cikin mamaki Husnah tace, waye yayi wannan aikin? "


Dariya Husain yayi yace, Suhailah ce, kuma idan kin futa kwana biyu, sai kije gidan Ummey kiyi sati biyu saboda bikin Anisah da Tk Suhailah da Muktar sai Safiya da Ahmad"



Sosai Husnah taji dad'in wannan maganar.

Haka kuwa kwanan su biyu da wowa suka nufi gidan Ummey, sosai Ummey tayi farin cikin ganin Husnah da Husain da sauyin da aka samu, jin takeyi kamar ta maida Husnah da Husain cikin ta, Daddy ma wani irin farin ciki yakeji, ganin wannan sauyin su Anty Zarah dasu Yaya Yusuf Shaheed matar Shaheed su Anisah kowa cikin farin ciki yake, tabbas Husnah da Husain sun dace da juna.


Daddy ne yace su shirya yau zasuje ziya gidan baffah daga nan zasu je gurin baban su Husnah a take Husnah da Anty Zarah sukace su ba zasu ba, Husnah ma harda fad'ar, ai Baban mu ya dade da rasuwa ni ban ma san shi ba".


Lallashin duniya sunce ba zasu ba, gidan baffah ma da akayi maganar cewa sukayi ba zasu ba, har sai da Daddy yace Yusuf Husain wannan aikin kune, dole a ranar aka fasa tafiyar.


Husain ne ya zainar da Husnah yana lallaba ta amman ta'ki yarda, tun yana lallashin har ya hasala yayi fushi ya daina kulata ya koma gurin matar sa, har sati d'aya, ai kuwa Husnah ta 'kara hasala, tana fitowa daga cikin d'akin ta zata shiga kichen kawai Zee ta saka wa Husnah 'kafa dan ita sam saboda abunda Husain yayi mata tana cikin zafi ta share su shida matar sa ta daina shiga lamarin su, to bata kula da suna zaune a gurin ba kawai taji an tadiyeta, a take tayi luu zata fad'i cikin zafi nama Husain ya janyo ta, suka fad'a akan kujerar da yake zaune a kan ta, shine a 'kasa Husnah a saman sa, a take Husnah ta bud'e ido ganin ta kwance a jikin mutum kawai tayi yun kurin tashi, da sauri ya ri'ke ta, yace, "ina fatan baki samu rauni ba"


D'aure fuskar ta tayi tace, "zan tashi ka kyaleni malam nayi abunda yake gaba na, kuma miye naka aciki koda raunin ne na samu ai dai naga ba jikin ka ba ko? "


Dariya yayi yace, "Husnah nine fa kika yiwa laifi kamata yayi Husnah kizo ki bani hakuri ki lallasheni ko".


Shiru tayi masa shi kuwa gyara mata kwanciya yayi a jikin sa, ita kuma ta daura kanta a jikin sa,.


Wani wawan tsaki, Zee ta saka, tace bariki kawai, Husain ya daga idon sa, yace, oh tunda burin ki bai cika ba, ai ina kallon yanda kika saka mata kafa ni kuma kin san abunda ba zan d'auka ba ke nan, akan yar karuw... Da sauri Husnah ta rufe masa baki tace, "um umm nidai bana son wannan Sunan Allah".



Cizon wasa yayi mata, ihu ta saka, cikin takaici Zee tabar gurin, anan gurin ya lallashi Husnah har ta yarda, da sauri yace to tashi muje gida tun yanzun dan da zafi_zafi akan daki 'karfe "



Shiryawa sukayi suka bar gidan suna zuwa ashe daman su ake jira daman yayi niyar yau kam dole ya shawo kan Husnah.

Hanya suka d'auka tare dasu baffah, shine ma ke nuna masu hanya cikin ikon Allah koda tara ba dare yayi sun kusa isa garin hotel suka kama suka kwana tun da safe suka d'auki hanyar shiga garin, zuwa 'karfe biyu na rana suka isa, ita dai Husnah da Anty Zarah cike suke da mamakin ganin gidajen guri duk sauya masu hanyar da suka sani ma taso 'bace masu, ko baffah sai da yayi tambayar gidan su Marka wanda aka tambaya yace, "kuce gidan barayin kauyen nan" ai kuwa a take aka nuna masu, hanyar tafe suke da mamakin barayin Kauyen, taro suka gani ana ta rafka bala'i mutane ne suka taru ko wane da makamin sa, a hannun ana dukan wasu mutane a gurin, Husnah kuwa bud'e motar tayi, ba tare da wata wata ba, a take Husain ya biyo ta yana kiran ta amman sai ture mutane takeyi tana shiga itama Anty Zarah da sauri ta shigo gurin, Husnah turus tayi ganin ana dukan matar da har ta mutu ba zata iya mantawa da ita ba,


Anty Zarah ce ta dafa Husnah tace, "Husnah kin ga kuwa abun da nake gani da ido na kuwa? ".


Husnah ce, tace Alhamdulillah duk sai mutane suka jiyo suna kallon baki duk sai aka matsa masu, akayi shiru Husnah tace, " *HAJIYA MARKA*!! ke nan to Alhamdulillah gamu da ran mu Allah ta nufa bamu mutu ba kuma bamu wukanta ba kamar yanda kikayi muna fatan gani, ki dubemu da kyau ki gani".


Tun lokacin da Husnah ta ambaci sunan Marka kawai sa Marka ta saki ido da baki ita da wanda suke gurin suka zubawa su Husnah ido.


Anty Zarah ta ce, "Marka ki duba da kyau ki gani ko idon ki daya zai iya gane mu, amman koda yake, bari abaki amsa, ta dubi Husnah.


Husnah tace, "Anty Zarah ce da Husnah makinyanki mune nan a gaban ki, lafiya lau cikin kwanciyar hankalin amman ke dibeki keda "ya'yan ki "ya'yan so, kun dawo abun tausayi, yan mune zamu taima ke ku, Marka nazo da niyar d'aukar fansa amman Allah ya bi muna hakkin mu dan haka mun barki da halin da kike ciki".



Anty Zarah ta ce, "hum Marka mune kikayi wa farar kasan cewa haka, a yanda kike a yanzun sai gashi kin ga, Ikon Allah wanda babu wani mahalukin da ya isa ya chanza kaddarar Allah da hukunci sa, dube ki dubi yanda wani mummunan wari yake fita daga jikin ki dubi yanda kika maiyar da yaran ki wata da ciki wani an toye masa rabin fuskar wata kuwa da Alama ba zata sake amfani da hauren bakin ta ba ko d'aya, Marka ina bokayen

Please Login or Register in order to submit comment