Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ke dibar ta, har ta isa cikin d'akin su, ta fad'a a saman gado ta d'ora hannu a kai tace, "yau ni Husnah na shiga d'ari da talatin ace kamar ni Husnah zan Auri Husain tazuru, kuma tsofo, bama wannan ba, wai harda 'katuwar kishiya, ni yau Husnah nice haka, Allah na tuba ka yafe ni, idan laifin da nayi maka ne, ka hukun tani da Auren Husain! ".


Su Anisah da Suhailah Safiya basu yin dariya ba, amman jin yanda Husnah ke shirme musam man ma yanda take kiran 'katuwar kishiya abun ya bala'in basu dariya wai Husnah ce yau da tsoron kishiya kishiyar ma wai matar Yaya Husain .


Aikin da Husnah keyi ke nan su Anisah tun basu d'auki abun da gaske ba, har suka dawo sukaji tana bala'in basu tausayi, sai suka dawo lallashin ta.


Husain kuwa cikin d'akin sa ya dawo ya rasa miye yake yi masa dad'i a rayuwa, shi dai kawai yasan ba zai iya sa'bawa umarnin su Daddy ba, amman ba zai iya Auren karuwa ba, da hankalin sa, kuma ma saboda tsabar an maida shi wani iri shine za'a ce karuwa itace uwar gidan sa, a gaskiya ba'a kyauta masa ba".


Haka Husain ya zauna aikin komai baiyi ba, har abokan sa, suka shigo suna yi masa, kirarin mijin mace biyu a rana d'aya abun yayi kyau ya 'kayatar.


Kyalesu ya yi, saboda duk haushin kowa yake ji, Daddy ne ya zo da kansa ya tasa shi a gaba sai da yaga Husain ya fito angon sa, tukuna kowa ya ga Husain a lokacin yaga ango sai dai matsalar d'aya ko kuma a abun ya zame masa ado wato rashin dariya, sai in ya lura da Daddy shi yake kallo sai yayi murmushi yayi yar fuska.


A cikin gidan aka d'aura Auren Husain da Amaryar sa Husnah akan sadaki dubu d'ari biyar


Ai kuwa gidan ya d'auki gud'a, da ihu su Anisah kawai suka saka kid'a sai dan cewa sukeyi harda kiran 'kawayen su a waya, Shaheed kuwa saboda murna sai ya tara nashi abokan yace a cikin ganin nasu ma zasuyi partyn su, na murnar Auren sa dana Husain da Husnah wannan shine ya 'kara cika gidan tako ina kabi mutane ne .


Husnah kuwa duk tabi ta takurawa kanta ko wankan da ta saba yin sa yau batayi ba, Ummey ce da 'kawayen ta, akan Husnah sai da Husnah taga Ummey tayi fushi sanan tayi wankan gurin saka kayan da Ummey ta kawo mata ma, sai da taji Ummey ta ce, "Husnah idan baki saka kayan nan ba, to ba zan 'kara kulaki ba! ".


Sannan Husnah ta saka materials d'in a gaskiya ya had'u iya had'uwa, gashi fari fes sai d'aukar hankali yakeyi makeup, aka ce ayi mata amman Husnah ta saka kuka dole Ummey ta ce, su kyaleta ita ce tayi mata da kanta, ai kuwa Husnah mamakin takeyi taya Ummey ma zatayi mata kwalliya, indai ba kwalliyar tsofafi ba? ".


Husain ne ya shigo cikin d'akin neman Ummey dan Daddy ne ya aiko sa gurin ta, a nan ne tadda ana rigimar kwalliya, tsaki ya yi, yayi tsaye yana kallon yanda Ummey ta dage akan sai Husnah ta tsaya tayi mata kwalliya, amman Husnah ta 'ki , sai doka kafa takeyi.


Duk takaicin Husnah ya 'kara kama shi, babu wanda ya kula da zuwan sa, sai Ummey amman tayi kamar bata san da zuwan sa ba.


Husnah kuwa duk sai tsalle_tsalle takeyi da doka 'kafafun ta a 'kasa, Ummey tace, "Husnah ki zo ayi maki kwalliyar ko nayi maki da kaina ko kuma ki zauna kiyi wa kanki ".


Husnah tace, "Ummey nifa wallahi ko d'aya kin san bana son 'bata fuska kuma tunda kin matsa mani nayi wanka na saka wannan kayan kibar ni haka mana".


Dariya mutanen keyi, ganin wautar Husnah, sai da Ummey tasake 'bata fuska san nan Husnah ta zauna a ka fara yi mata kwalliya Ummey na fad'ar kuyiwa 'yata kwalliya banda 'bata mata fuska dan ana gamawa zasu je gurin partyn da Shaheed ya shirya masu, ta murnar Auren Husain da Husnah ta".


A take Husnah ta 'kara d'aure fuska, tayi rau_rau da ido sai hawaye ai kuwa aka sanya mata gud'a ana yi mata kirarin Amaryar Husain ta soma kukan farin ciki kukan Allah ya nuna mata ta zama 'yar gatan ango Husain "


ai kuwa ta saki kukan dole aka sakar mata fuska saboda ruwan hawayen da takeyi.

Husain ya juya zai bar cikin d'akin Ummey ta ce dashi, "Husain angon Husnah ba gurin Amaryar taka ka zo bane? Kodai kunyar mutane kakeji shine ka juya, to ka jira ta a harabar gurin da ake taron".


Cike da mamakin maganar Ummey Husain ya rasa ma mi zai fad'a kawai ya fita ya bar cikin d'akin.


Da harara Husnah ta raka shi, Ummey dai tana kallon su tana dariya 'kasa_kasa, sai da aka dawo lallaba Husnah sannan ta yarda akayi mata makeup, d'in.


Husain na fita ya nemeni Daddy ya rasa, Yaya Yusuf ne da Shaheed suka zo suka saka shi a gaba sai da suka zaunar dashi akan kujera, anan ne aka kawo Amaryar Husain wato Mardiyya, taci wanka iya wanka, Husain na ganin ta ya saki murmushi itama ta mayar masa, a kujerar kusa da Husain aka bata masauki wato shine tsakiya, kujerar hannu damar sa, aka ajiye flower, da wasu abubuwa, a kujerar hagun sa kuwa aka zaunar da Mardiyya.



Shaheed da Amaryar sa su Anisah da 'kawayen su kai gurin dai ya cika masha Allah komai ya kammala amman ba a fara gaba tar da komai ba.


Mardiyya ce ta ce, "mijina ba za'a fara gabatar da komai bane? Duba fa tun d'azun aka gama shirya komai to zaman miye mukeyi? ".


Kallon ta kawai ya yi baice da ita uffan ba, kawai dai taga ya tsare guri d'aya da ido kuma ta juya haka taga kowa ya maida hankalin sa gurin, kawai itama ta juya, mi zata gani kawai sai ta tashi tsaye a firgice ta zaro ido waje ta daki kirji tana nuna inda mutane ke kallo......




*(Tofah shin miye Mardiyya ta gano??? kudai kawai ku biyo Ummu IHSAN )*



*Comment and share*




*A GIDANTA NA GIRMA*




*BY NANA: KHADEEJATU*

*_UMMU IHSAN_*


*SADAUKAR WA GA :- DUK KANNIN MASOYA NA NABOYE DANA BAYYANE INA SONKU SOSAI SON FISABILILLAH*


*YA ALLAH KAJIKAN MAHAIFINA KAYI MASA RAHMA KA KYAUTATA MAKWANCIN SA SHIDA YAN UWA MUSULMI BAKI `DAYA.*


*YA ALLAH KA BAIWA MAMANA LAFIYA KA BAIWA DUK KANNIN WANDA BAIDA LAFIYA NA GIDA DANA ASIBITI ALLAH KA BASHI LAFIYA AMIN YA ALLAH*

*"Yan uwa barka da sallah da fatan kunyi sallah lafiya Allah ya mai_maita muna amin, Amman ni har yan zun banji wadda tace ta tuna da Ummu IHSAN ba ace Ummu IHSAN ga kafar gaba mai awaza da 'kafar baya ba, nidai nace kada ci ya rufe maku ido atoh* 😜


*_Bismillahir Rahmanin Rahim_*


76~80

Cike da tsabar rikicewa, take nuna gurin, hannun ta ta ri'ka d'aga wa tana dan dukan jikin Husain wanda ya kafe guri d'aya da ido, sai alokacin da Mardiyya ta dake sa ya sauke ajiyar zuciya a bayyane, san man kuma ya dawo da idon sa, gurin ta yace, "lafiya dai?

Mardiyya cikin kidemewa ta ce, "a ina muka had'u da dangin aljannu kuma, nidai nasan duk a cikin dangi na da shige_shige na ban ta'ba had'uwa da su ba! ".


Tsaki Husain ya doka ya ce, "dallah mallama ki zauna ki natsu, haka kawai kin wani dawo da hankalin mutane inda muke".

Mardiyya ta ce, "kaga fa nan gurin suke nufowa fa nikam zan gudu dan na tseratar da rayuwa ta".


Tsaki Husain ya 'kara dokawa,, ya saka hannun sa ya dawo da ita mazaunin ta ya ce, to ki saurari abunda dj yake fad'a a kan ki mana! " ya sake jan tsaki.

Zama Mardiyar tayi, kawai ta jiyo muryar dj na fad'ar, "kai masha Allah uwar gida sarautar mata anfito ke ce taro, danki kowa ya taru daga zuwan ki, hankalin kowa ya dawo kanki domin kece fasa taro, uwar gidan Alhaji Husain Allah dai ya 'kara dan kon soyayya, kice fitila mai haskawa a cikin wannan taron daga zuwan ki, kowa ya sara maki, kai hatta Amaryar Husain ta tashi dan baiwa uwar gidan Husain girma, kai amman wannan uwar gidan kim d'aga tuta, ga ki kyakykyawar gaske, dake da mai gidan ana go gagga gurin kyau, kowa ya kalleki ya san da cewar za'bi da Husain yayi baiyi tumun dare ba, lallai Husain ka d'aga tuta".


Wani irin 'kololon ba'kin ciki ne ya tukare wa Mardiyya zuciya har zuwa ma'koshin ta, sai huci takeyi, ta ce, da Husain cikin tsana nin 'bacin rai, "daman ka matsa mani nazo ne gidan ku gurin wannan tsi nannen partyn dan a wulakanta ni? To wallahi dana san cewar da gaske wannan ita ce za'bin rayuwar ka ba ni ba wallahi da tuni ban yarda da 'karyar da akayi mani ba, akan cewar babu Aure a tsanin ku, amman Yan zun iyayen ka sun had'a Auren na kune saboda wani alkawari tsohon ajiyewa to bari kaji tun daga yanda kake kallon ta na gane cewar duk 'karya ce, Auren so da kauna kukayi, kuma yan zun nan zan bar maku gidan ku, nafasa yin partyn! ".

Mardiyya masifa kawai take zubawa ido rufe bata ma san da su Husnah sun iso gurin ba, har an zaunar da ita a gefen daman Husain.


Husain kuwa haushin ganin irin yanda kowa yake kallon Husnah da irin yanda Dj yake ta kod'a irin kyaun ta, gashi idon kowa har yan zun akan Husnah ne, 'karin takaicin shi yanda Mardiyya take tayi masa hauka, a cikin mutane harda su 'kannen Ummey da Daddy da abokan Ummey wanda suka rako Husnah, abun haushi ma yan da Husnah keta yin murmushi kamar wata kyakykyawar gaske.


Duk abun da Mardiyya keyi akan kunnen su Husnah kuma duk sunji abun da take fad'a.

Murmushi Husnah tayi ta ce, "iska na wahalar da mai kayan kara, indan ta Husnah ne yarinya kama mijin ki dan bai gaba na, nifa yan zun jin kaina nakeyi kamar wata wadda take rayuwar ta ita d'aya, dan bazan takura kaina ba, a gidan wasu bana su Ummey da Daddy ba, eh".


Cikin 'kara jin haushin Husnah Husain yace, "yarinya kin kawo kanki gidan yari, dan sai kin yabawa aya zakin ta" kallon su kawai akeyi ganin Husnah da Husain suna magana a tsanin su, ganin yanda kowa yake d'aukar su photo, waya da camera video, Kasai shims Husain sai ri'ka yin murmushi yana magana, "yarinya tun kafin aje ko ina kije ki cewa su Daddy kin fasa dan DUK kika yadda kika saka 'kafar ki cikin gida na sai nayi maganin ki".


Dariya Husnah tayi ta ce, "Allah ko? Ni wallahi ba irin butulu bace mai mancewa da alkhari ba, Amman kai da kake da ja, kaje gurin su Daddy ko ka anshi abun maganar a hannun Dj sai ka sanar da kowa cewar ka fasa yin biyayyar, kaga ka futa da kallon idon su Daddy ko? ".


Tsaki Husain ya ja ya ce, "to halan waye kike nufin kin fi sa son faran tawa su Daddy? Ke yarinya ni nan da kike gani indai akan farin cikin su, Ummey ne nafi kowa kaunar sa".


Dariya Husnah tayi ta ce, "Allah sarki ni a yar gidan Zubaidah, wannan maganar da ban dariya take".

Da sauri Husain ya ce, "wallahi idan kika sake kiran sunan wannan babbar karuwar a gaba na sai na sa'ba maki! ".


A take Husnah ta ce, "sannu uban Husnah ai dole ka hana ni fad'ar sunan mommy wadda ta raine ni, tab lallai ma mikam wallahi.... ".


Kasa 'karasa maganar Husnah tayi ganin abokiyar Ummey da kannen Daddy da Ummey, sai su Anisah wadda suke ta gimtse dariyar su.


Goggo Aina'u tace, "to kaji iyayen fad'a ana can anata kiran ku, ku fito ku yanka cake, kira kusan biyar amman duk ba kuji ba, saboda tsabar masifa irin taku, ka duba Husain matar ka har gurin zama ta sauya saboda ita a tunanin ta, fira ce kukeyi, bata san masifa bace kukeyi iyayen masifa kawai, ni ku tashi muje, kuma Husain kaje ka lallashi Amaryar ka, ku same mu gurin da za'a yanka cake din ".


Cikin fad'a da masifa take maganar ai kuwa da sauri suka dubi gurin da aka nuna masu Mardiyar ta koma, cike da mamaki suke kallon yanda take cika take batsewa sai hura hanci kawai takeyi.


Hannun Husnah aka ja suka nufi gurin da za'a yanka cake din, Husain kuwa da mamaki cike a fuskar sa ya isa gurin Mardiyya wadda take tare da 'kawayen ta, suna 'kara fure mata kunne.


Yana 'karasa wa, baiyi wa kowa magana ba, hannun ta kai ya janyo kawai ta ri'ke 'kawar ta, ta tirje, jiyowa Husain yayi, cike da mamaki, yake bin su da ido, Kawai ya tattare hannun rigar sa, kawai ya tallabe Mardiyya yayi sama da ita, ai kuwa mutanen gurin suka d'auki ihu da tafi, Husnah kuwa kallo d'aya tayi masu ta d'auke kanta gefe, tayi murmushin gefen baki, ta gyara tsayuwar ta, Husain na 'karasowa gurin ya ajiye Mardiyya wadda take kallon fuskar Husnah taga ko zata ga wani abun amman kuma Husnar sai murmushi takeyi, Husain ya tsaya a tsakiyar su Mardiyya jin takeyi kamar ta kashe Husnah, tunda ita har yan zun bata damuwa da abunda takeyi mata.


Su Shaheed ne suka 'karasa gurin a kusa da Husnah ya tsaya ya dan matsa a kusa da ita kad'an ya ce, "gimbiyar Husain Daddy ya ce, a sanar dake kada ki basu kunya, ki nuna masa cewar ke yar sace, kinji kanwata?.


Murmushi Husnah tayi ta ce, "ada nayi niyar bata wannan taron amman yan zun na fasa, wai nikam matar Yaya Yusuf har yan zun bamu ta'ba had'uwa da ita ba, duk da na fahimci cewar tafi kaunar Husain da wata ba niba, saboda ranar naji su Anisah suna maganar cewar duk abunda Husain yake so shi take so, wanda Husain baya kauna kuwa, tafi sa rashin kaunar abun nan, dan haka nasan ta tsaneni fiye da tunanin mai tunani! ".


Kallon ta kawai Shaheed yake yi, Anisah tayi saurin fad'ar ai kema kin tsane ta ko? ".


Kallon Anisah Husnah tayi tace,"taya zan tsani matar Yaya Yusuf bayan na d'auke sa kamar Yaya na wanda muka fito ciki d'aya dashi? "


Shiru duk sukayi Suhailah ce ta ce, "Husnah kada ki damu tunda muna tare dake, ke tamuce, kuma Insha Allah komai zai zo maki da sau'ki nasan da cewar Husnah kina tunanin zamu iya juya maki baya kamar yanda kike tunanin Maman Baby tayi maki, aa mukam kece tamu kuma ba halin Maman Baby bane abunda kike tunani dan haka ki natsu guri d'aya kinji ko? Ki fitar da mu wannan kunyar ta mutanen dake gurin nan, kada ki yarda suje dake a bakin su, na wani mugun hali, kibar su, suyi ta ganin mutum cinki kinji yar uwar mu? ".


Murmushi Husnah tayi ta ce, "kada ku damu ni kuma sai na baku mamaki sai kun san da cewar ni takuce Insha Allah ".


Dariya duk sukayi suka gyara mata tsayuwar ta, Husain na had'a ido da su Shaheed ya watsa masu harara, su kuwa suka sanya masa dariya harda tafi, ai kuwa kowa ya d'auki tafi, ana kidaya daga d'aya zuwa ukku, aka basu umarnin su ri'ke wukar d'aya su yanka cake din.


Kowa zuru_zuru kawai Husain yad'ora hannun sa a tsakiyar wu'kar kawai Mardiyya tayi saurin d'aura hannun ta a saman nasa, saura Husnah kowa ita yake kallo, kawai ta kalli su Anisah sukayi murmushi, suka 'kyafta mata ido kawai sai ta d'ora hannun ta akan tsin_tsiyar hannun Husain, ai kuwa aka d'auki ihu, Husain kuwa mutuwar tsaye yayi, ya jiyo yana kallon Husnah wadda tayi kamar ba ita ce tayi ba.


Mardiyya kuwa ada tana murnar tayi wa Husnah tsiyar, kawai sai taga Husnah tayi fiye da mamakin ta.

Ita fa hannun tane taga ta d'ora a wu'kar saman hannun Husain , haushin Husnah Kawai taji ya 'kara shigar ta taji ina ma zata samu damar kashe Husnah da babu wanda ya isa ya hana ta aikata hakan, amman ta lura da babu yanda zatayi da Husnah.


Ana yanka cake din Husnah tayi saurin d'aukar cake din ta dur'kusa 'kasa ta d'aga hannu zata sakawa Husain a cikin bakin sa, amman bata kaiwa, aka d'auki ihu da tafi su Shaheed sai sara mata sukeyi, Amaryar Shaheed kuwa da sauri ta 'karasa gurin Husnah ta ri'ko hannun Husnah, Shaheed da Yaya Yusuf da abokan Husain sukayi saurin yiwa Husain rad'a a kunnen sa, kawai ya tsare Yaya Yusuf da ido, Yaya Yusuf kuwa yasha mur, kawai Husain yasaka hannun sa, ya d'ago Husnah ya kama hannun ta, ya saka cake din a cikin bakin sa har da had'awa, da hannun Husnah ya d'an ciza da sauri Husnah ta yi saurin kallon sa, ta janyo hannun ta, ta d'an cije baki, sakin Husnar yayi, itama Mardiyya cikin jin haushin Husnah ta d'auko ta saka masa a bakin sa, shima ya saka mata abaki sai ihu akeyi.


Husnah kuwa tana kallon hannun Husain taga ya nufo inda take cikin sauri ta d'auki wayar Anisah da take hannun ta, ta kara a kunnen ta tana fad'ar, hello, hello zata bar gurin da sauri Husain ya ri'ko hannun Husnah wanda ba bu wayar a garesa, a take Husnah ta cije burki cike da mamaki Husain jiyowa yayi yana fuskan tar Husnah Kawai ya saka mata cake din babba a bakin ta, cikin jin haushin abunda Husain yayi mata tunda shi 'keta ce yayi mata, ai kuwa ta had'a da hannun sa ta girtsa masa uban cizo wanda sai da yace, "wash! "


Dariya Husnah tayi bayan ta turo cake d'in dan yayi mata yawa sosai a bakin ta.


Tafi kawai mutane ke yi har da ihun su, sudai Husnah tana bala'in burge su.


Husnah kuwa gurin su Anisah ta nufa, cikin masifa tace, "wallahi nifa, na gaji da mugun tar da Husain yake yi mani ko ya daina ko nayi maganin sa"



Dariya suka sakar mata Amaryar Shaheed ta ce, "kai Anty Husnah wallahi wannan dramar taku tana burge ni, ina ma ace zan ri'ka kasan cewa a tare da ku, wallahi da bani tare da hawan jinin dake damu na! "


Duk sai suka juyo suna kallon Amaryar Shaheed wadda tayi magana cikin yanayin damuwa wadda har fuskar ta sai da ts nuna hakan.


Cikin sauri Husnah ta ce, "ke kinga matar d'an uwa na kada ki 'bata muna wannan kwalliyar taki, kuma ma nida wan can tuzorun ai ba comedy bane mukeyi, rai na ni ne yayi da yawa, kin ga kuwa ba zan kyalesa ya ga da mata ba "


Dariya suka sakar mata Anisah tace, "wallahi Husnah kin bani dariya wai tazuru? Dan Allah kuji fa, yo koda ace Yaya Husain tazuru ne, yau ai ya shafe wanda yake da mata, d'aya tun da gashi da mata biyu a rana d'aya kuma kece uwar gidan sa ko? ".


Tsaki Husnah tayi, ta d'auke kanta, Amaryar Shaheed ta ce,"Anti Husnah dan Allah ki dai na kiran sa da wannan Sunan ba bu dad'in saurare".


Ta'be baki Husnah tayi ta ce, "shida yake kira na da karuwa bakuga laifin sa ba, sai nida nake bare a cikin ku ko? ".


A tare suka had'a baki gurin fad'ar, "Allah dai ya huci zuciyar ki Allah ya baki hakuri lallai duk kuna da laifi Husnah Husain ta bakin Ummey tace sai Allah ".


Tashi taron akayi Husnah basu san ma lokacin da tabar gurin ba, tayi cikin gida mutane ta gani a cikin falon, ta raba su ta wuce gurin Ummey akan hannun kujerar da Ummey take ta zauna tare da fad'ar, "wash! Ummey nagaji sosai dan Allah gobe ki bar ni naje naga mommy na! ".


Idon kowa akan su yake, Ummey tayi dariya ta ce, "Husnah manya keda kike da Auren wani a kanki shine kike zaton nice zan bar ki fita wani gurin, gashi naji Daddyn ku yana fad'ar yau ba zaki kwana a gidan nan ba sai d'akin ki, nida naso ya barki har mu shirya, amman shi yace, baya bu'katar hakan halin kune ya janyo maku".


Zaro ido waje Husnah tayi cikin rawar murya tace, "yau ni... Husnah.. Na shiga d'ari da talatin ace kamar ni Husnah... Nice.. Nice.. wai zan... Zan... dawo gidan wan... Wan can tuzorun da zama , shike nan kuma hawan jinin sa zai 'karasa ni...".


Kawai Husnah ta fashe da kuka iya 'karfin ta, tana fad'ar, "wallahi Ummey bazan iya zama dashi ba, dan Allah kada ki yarda a kaini gidan sa! ".


Ai kuwa kowa sakin baki da hanci yayi yana kallon shirmen Husnah, ita kuwa Husnah kukan ta kawai takeyi tana doka kafa, sai aka sanya mata dariya da gud'a, ana yi mata kirarin Amaryar Husain wato ke kina nufin kishiyar ki kike son ta fara zuwa gidan nasa ta ri'ka juya ki kamar ra'kumi da akala? ".


Husnah bata bi takan su ba, wata mata Ummey ne suka kama hannun ta suna lallashin ta Ummey ta ce, "Husnah share hawayen ki kinji ko? Zanyi masa magana nasan yanda yake ji dake zai iya ha'kurin d'aga maki 'kafa kinji Husnar Daddy? ".


Gyad'a wa Ummey kai tayi matar cikin sanyin jiki ta ce, "Hajiya naji kin ce da ita Husnah daman kuna ri'kon yar d'an uwan kune? ".


Kallon ta kawai Ummey tayi tace da ita, "Hajiya wannan yar muce, kuma yan zun matar d'an mu Husain ".


Matar ta ce, "Allah sarki sannu Husnah ke kuwa kama ta ya yi kiyi farin ciki kin samu miji wanda yan mata suke rububin Auren sa, amman basu samu wannan damar ba sai ke, a gaskiya kinyi dace da mijin gogawa tsara".


Cikin jin haushi Husnah ta ce, "yo ni ina ruwa na dashi ma kowa yayi mai fidda shi ni kuma ce maki akayi ba manyan mutane ne ba suka zo neman Aure na ba harda baiko na sai da akayi amman na'ki sa, shine zaki wani ce dani wai nayi dace, to wannan maganar taki ta wanda basu da masoya ne, ba ni Husnah ba! ".


Kama baki matar tayi ta na kallon Husnah, cike da mamaki da al'ajab.


Ummey kuwa dariya tayi ta ce, "Husnah ke nan iyayen rigima Hajiya ai sai dai kiyi hakuri bari kiga mutumen, naki wato Husain d'in "


Ummey ta d'auki wayar ta ta kira Husain ta ce, "Husain kazo da hanzari ina jiran ka".


Ummey na ajiye wayar tace, "sa ido kiyi kallo Hajiya ".

Gyad'a wa Ummey kai kawai matar tayi.

Husnah kuwa bata dai na kukan ba, kamar ma 'kara mata kaimin kukan akeyi.


Husain ne ya shigo cikin d'akin da sauri yana kallon Ummey ya sauke ajiyar zuciya, matsowa yayi gurin Ummey ya ce, "Ummey gani ina fatan ba laifi nayi ba".


Ummey tayi dariya ta ce "ga dai matar ka nan ka lallashi abar ka, wai ba zata yarda akaita gidan ka a yau ba, kuma gobe zata je gurin mommyn ta ".


Husain kuwa ya kwa'be ya ce, "Ummey nifa bana son ganin mutum kullum baida hankali, shi yasa na ce bana son Auren yara, gashi antashi an had'a ni da jin jira, ni wallahi dama zaku barta gidan nan sai ranar da tayi hankali, kai Ummey wannan yarinyar kwata_kwata babu ranar da zatayi hankali, kuma ki rufewa mutane wannan bakin naki ko kuma yan zun nan na zane ki, dan bana son rashin kunya irin taki".


D'aure fuska ya yi.


Husnah kuwa cikin jin haushin sa, tace, "nifa Ummey ki daina saka tuzorun nan cikin lamari na, in dai ba son kikeyi ba mu sai da halin mu cikin ba'kin ki".


Husnah na ajiye

Please Login or Register in order to submit comment