Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nan tom na fad'a naku".


Kawai Ummey tayi tafiyar ta, suna jin tashin motar ta, kowa ya kama gaban sa yayi cikin d'akin sa, Husnah kuka kawai takeyi tana fad'ar, "wan nan wace irin rayuwa ce, ni to miye laifi na? Mutumen da ya za'bi Auren wata a kaina shine zan shigewa yazo yana wulakanta ni, wallahi ba zaiyuyu ba haka kawai da ajina a gari nazo nayiwa wan can mutanen bauta Allah ya tsare! "



Husain ma fad'ar yake, "haka kawai a shiga rayuwa ta dan anga nayi jihadin Auren karuwa kuma a zo ace sai abinda take so zanyi taji dad'in raina ni, ko dan anji nace ina son ta, ne to nayi ne kawai dan Anty Zarah kuma saboda farin cikin Anty Zarah amman badan haka ba da sai na wulakanta rayuwar ta, kuma wallahi sai na baiwa kowa mamaki dan ni kam ba zanyi zaman kunci ba, akan wata karuwa ba!.


(Ni kuwa nace toh fa wannan wane irin ma'aurata ne haka a duniya ?)

Abu kamar wasa Husnah da Husain ko kallon junan su basayi, Daddy, da Ummey sun hana kowa ziyar tar su kuma sun hana su zuwa gidan kowa, Husnah ba 'karamar takura take ciki ba, Husain kuwa daga gurin aiki sai hotel sa restored park shooping mail da dai sauran su amman Sam baya zuwa gidan kowa dan su Ummey sunyi rantsuwa akai, duk da haka yana cikin damuwa.


A cikin yawon sane ya had'u da wata budurwa wadda ta li'ke masa tun baya kulata har ya soma kulata, soyayya suka 'kulla shida ita, har take shaida masa a gidan su ance ya turo iyayen sa, ai kuwa yayi farin ciki da hakan sai dai kuma wani hanzari ba gudu ba koda ya sanar da Daddy abunda ke faruwa a waya Daddy ce masa yayi bada yawun sa ba, haka Ummey, Yaya Yusuf ma yana fara sanar dashi akan cewar yana neman Auren wata yarinya Zainab kuma ance ya turo manyan sa, Yaya Yusuf cewa yayi to ya tura manyan nasa mana dan shi yanada abun yi, Husain rikicewa yayi ya rasa waye zai saka baki har su Daddy su yarda? Kawai ya tuno da Anty Zarah, har ya fara farin ciki sai kuma ya tuno da cewar Husnah fa 'kanwar Anty Zarah ce, to amman kuma da kunya duk da Anty Zarah tafi kula da lamarin sa akan 'kanwar ta, kawai sai ya d'aure ya kira Anty Zarah cikin dabur cewa ya fara labar ta, mata, daga karshe yace su Daddy sunce babu ruwan su, Anty Zarah duk da taji babu dad'in amman kuma sani sakacin 'kanwar tane tunda tayi ta nuna mata illar abunda takeyi, ita ce mace ta zubar da komai ta rungume mijin ta, ta'ki jin magana yan zun sai ta Allah kam, lallashin sa tayi, kuma tayi masa alkawarin taimakon sa, yayi farin ciki sosai wanda ya kasa 'boyewa sai addu'a yake zuba mata, kashe wayar Anty Zarah tayi harda kukan ta.



Kamar yanda Anty Zarah tayi alkawarin shawo kan su Daddy tayi nasara amman Ummey fad'a sosai tayi mata tunda tana goyon bayan yiwa Husnah kishiya, ita kuwa tace, "Ummey mukam yaran mu muke son gani ga matar Shaheed nan ta tsufa da yawa haihuwa yau ko gobe, kuma kowa yasan Husain na haihuwa dan kawai ankashe masa mata da yaro ne, da yan zun yaron ya fara wayau ita kuwa Husnah waye yasan halin da take ciki? ".


Shiru Ummey tayi dan tasan Zarah akwai karamci ta bar yar uwar ta, ta goyi bayan kanen mijin ta, wanda sukafi sha'kuwa dashi tabar yar 'kanwar ta kuma jinin ta, wadda bata da ta biyun ta a duniya, Ummey taso butulcewa amman Anty Zarah ta dage har sai da suka yarda.


Kiran Husain su Daddy sukayi fad'a sosai sukayi masa, har suke kiran sa da marar tunani yasaka Zarah a cikin lamarin sa, dan kawai ya kun tata mata, ta goyi bayan sa tabar gudan jinin ta har take kiran sa da mahaihuwa 'kanwarta kuma juya, sosai kunyar Anty Zarah ta kamasa har yaji baya iya had'a ido da ita.


Haka aka tura aka kai sadaki da lefe koda aka saka biki wata biyu, Husnah duk bata san mike faruwa ba, har sai da Ummey tace tazo tana neman ta cikin d'oki Husnah taje gidan a lokacin bikin saura kwana biyar, Anty Zarah ce ta shirya haka.


Ummey tace maraba lale mar haban da zuwan ki 'yata, ita dai Husnah cike take da mamakin wannan maraban da kowa yake yi mata, bata 'kara sa mamakin ba Ummey ta ja hannun ta suka shiga d'akin ta a bakin gadon ta ta zaunar da ita, Zubaidah ce ta shigo ita da Anty Zarah Yaya Yusuf gaban Husnah ne ya soma dukan ukku_ukku a take jikin ta ya bata akwai wani abu a 'kasa.


Kusa da ita Ummey ta zauna su kuma duk suka zauna a 'kasa Ummey ce ta rasa ta ina zata fara, Anty Zarah kuwa tace, "Husnah! Husnah!! Husnah!!! Na kira sunan ki sau ukku dan ina son ki fahimci cewar ba mafalki ne kikeyi ba, Husain Auren sa yau saura kwana biyar, zaki zauna ne a nan gidan ayi himar biki dake matsayin ki na uwar gida, ga lefen ki nan saman gadon Ummey na fad'an kishiya duk da ni banga abun fad'a a nan ba, mijin da bakaso miye ma ba fad'a a kan sa?.

kuma idan Allah yasa anyi wata tara cif da Auren sai kiga mun samu karuwar yara kinga Auren yayi albarka, an samu yan bari_bari a gidan, dama gida babu yaro ai babu dad'in zama gaskiya amman yan zun Husain yayi dabara wallahi ya burge ni"



Husnah kallon bakin Anty Zarah kawai takeyi zuwa can tayi murmushi tace, Allah ya taimaka ai kuwa kunyi dubara kun kawo mafita, hakane Anty Zarah to ni miye zanyi da wasu kayan fad'an kishiya tunda ba ni akayi wa mutum kansa yayi wa, kuma ba akaina zata zauna ba, amman ku ri'ke kayan ku, ko kuma ku 'kara mata kawai zai fi".



Murmushi Zubaidah tayi tace, "Husnah ki kwantar da hankalin ki, ki rungume mijinki da abokiyar zaman ki, sai kiga komai na tafiya yanda kike so nima nakusa Aure insha Allah ".



Husnah tace, "kada ki damu mommy ni bani da wata matsala da Auren nan kuma bani da wata damuwa dashi, kinga sai dai ku baiwa wasu hakuri ba Husnah ba, Ummey na zan koma gida ina fatan kiran ke nan nazo na tayaku murna? "


Shiru kowa ya yi Anty Zarah kuwa tace, "Husnah nan fa zaki zauna sai an gama hidimar bikin nan dan yau saura kwana biyar biki gidan amare tun ana saura sati d'aya suka fara shagalin biki".


Tashi kawai Husnah tayi, tayi masu sallama ta baro d'akin, a falo ma bata kalli kowa ba, a harabar gidan ne ta had'u da Husain da abokan sa sun dawo gurin Amarya sai tsokanar sa, sukeyi, ta gefen su tabi zata wuce ke nan abokin Husain ya ce, "uwar gida sarautar mata an fito ke nan ko kina neman wani ne? ".



Husnah kuwa ta wuce war ta, Tk ne da Anisah suna fira rabi fira rabi fad'a, Husnah tazo wuce wa Anisah tace, "haba yar uwa koda kowa yayi maki laifi ina ganin banda ni kuma laifin wani ba zai shafe ni ba".



Kallo d'aya Husnah tayi masu ta d'auke kai tace Husnah fa bata da uwa a duniyar nan kunga kuwa Husnah rayuwar kadaici takeyi dan haka ni ban san ina da wani d'an uwa ba a duniyar nan Husnah juya a cewar wasu da kallon wasu mutanen ".




Tk yace, Husnah ni nasan cewar jaruma ce a can da amman ban sanar wa yan zun ba".


Husnah tace, "yan zun Husnah tasan maraici ba kamar can da ba, kawai ta wuce su ta kama tafiya da 'kafa har ta fita gidan, Husain kuwa idon sa na akan ta da duk wani motsin ta, kawai yabi bayan ta shima ya fita da 'kafar sa, da dan gudun sa ya cimmata ya jera da ita yace, "miya sa kika fito kika baro driver wanda zai kaiki gida? ".



ko kallon sa Husnah batayi ba taci gaba da tafiya har suka isa bakin get d'in gidan su bata yi magana kwan_kwasa kofar tayi masu suka le'ko ganin masu gidan ne ya saka su bud'e masu suna basu girma, wuce su sukeyi har cikin falon ya rakota, kawai ta wuce cikin d'akin ta, shi kuma sai ya zauna a gurin ya kusan awa d'aya sai da abokan sa sukayi ta kiran sa, sannan ya tafi.


Husnah kuwa jefar da mayafin ta tayi da jakar hannun ta, tayi kwance ta saki kuka, babu mai lallashin ta har ta gaji dan kanta Husnah tun daga wannan ranar bata sake d'aga kiran kowa ba kashe wayar ta tayi zaman d'akin ya dawo mata sabo ba dare ba rana ruwa kawai take sha duk tabi ta rame ta fita hayyacin ta.


Koda aka kawo Amarya Husnah bata fito ba d'akin ta ma a kulle yake, Husain ma ya so ta fito ya had'a su yayi masu nasiha amman shuru_shuru kake ji ko ranar dasu Anty Zarah suka zo gidan Husnah na jin su suna doka mata 'kofa amman taki fitowa dole suka 'hakura.




Tunda aka kawo Amarya sai da tayi sati d'aya Husnah ta bud'e d'akin ta, tadawo tayi kwanciyar ta, Husain ne ya shigo d'aure fuskar sa ya zauna a bakin gadon nata, ita kuwa daga ita sai yar shimi da wadon best d'in ta rufe rabin jikin ta da zanen gado tayi rub da ciki ta d'ora filo ta d'ora hannun ta duka a kai tana saka jan farce, ja.


Husnah tana jin sa, shi kuwa ya bud'e bakin sa yace.........



*Comment and share*



*A GIDANTA NA GIRMA*




*BY NANA: KHADEEJATU*

*_UMMU IHSAN_*


*SADAUKAR WA GA :- DUK KANNIN MASOYA NA NABOYE DANA BAYYANE INA SONKU SOSAI SON FISABILILLAH*


*YA ALLAH KAJIKAN BABA NA DA MAMA NA KAYI MASU RAHMA KA KYAUTATA MAKWANCIN SU KA SANYA SU A ALJANNAR KA TA FIRDAUSI BIGAIRI HISAB SU DA YAN UWA MUSULMI BAKI `DAYA.*

*AMIN YA ALLAH*


*To Alhdulillah Allah ya nufeni da dawowa gashi zamuci gaba daga inda muka tsaya*



*_Bismillahir Rahmanin Rahim_*


1001~105


Cikin d'aure fuska yace, "Husnah kina nufin cewar haka da kika aika ta shine mafi ta? Ummey da kanta tazo gidan nan ta nemi alfarmar ki fito tayi mata dake amman kika ki fitowa kin kusan wace ce Ummey a guri na da matsayin ta kuwa?".


Cikin d'aure fuska itama Husnah ta tashi zaune tace, "ban sani ba kasan ni ba'kuwa ce a gidan nakun ko? "

Cike da jin haushin rainin da Husnah tayi masa ya d'auke ta da mari kuma ya 'kara d'auke ta da mari sai huci yakeyi wani irin uban ihu Husnah ta saka masa, sai da ya saka hannun sa duka biyun ya rufe kunnen sa, jan farcen Husnah zubewa yayi a jikin ta ihu kawai take rafkawa, da guda Amaryar sa ta shigo cikin d'akin babu ko sallama fuska taci bilicin sai uban atach da ta zubo, tana tafa hannu tana fad'ar, lafiya my honey? Mike faruwa ne? ".


Husnah kuwa kukan ta kawai takeyi Husain kuma kukan Husnah ya damesa har cikin zuciyar sa yake jin sa, ita kuwa ta dage iya kar gaskiyar ta hawaye kawai take ambaliya, Amaryar Husain kuwa jikin Husain ta shige tana shafa shi sorry my honey kayi hakuri zo muje ka daina damuwa da rigimar mace bare masifaffen mutum wanda baya son mutane mai wulakanta kowa, kasan ni bana son fushinka dan ka zamo sadauki, oya muje na baka farin ciki kaji masoyina? "

Shi bama kallon ta yakeyi ba, Husnah ce kawai ya kafe da ido wadda har fuskar ta tayi ja idon ta ya fara kum bura ga shatin hannun sa duk sun fito lafiya lau, kawai Husnah ta sauka a 'kasa ta soma tsalle daga nan taje ta janyo trolley d'in ta har biyu, ta nufi bakin koda dasu cikin zafin nama Husain ya tury Amaryar sa, yayi kan Husnah yasaka hannun sa biyu ya tallabe ta saboda tsoro dan bata sarar ba taji anyi sama da ita, sai ta saki trolley d'in shi kuma yayi kan gadon da ita ya kwatar, ai kuwa tayi wani zillo zata tashi ya danne ta, Amaryar Husain kuwa zuciyar ta kamar ta fashe ta saki uban tsaki tabar cikin d'akin harda bugo masu 'kofar da 'karfin gaske".

Husnah kuwa duk da tana jin zafin marin sai da taji sanyi_sanyi a zuciyar ta, amman kuka kam yin sa takeyi ganin ya'ki barin ta, ta tashi tsaye ko zaune kawai tayi kamar ta ha'kura yana ganin ta saki jikin ta, sai ya koma gefe ya dafe kai, Ummey ce ta shigo cikin d'akin da saurin ta kamar zata tashi sama Husain da sauri kowa ya maida hankalin sa gurin Ummey, Husnah na ganin Ummey kawai ta saki wani uban kukan Anty Zarah da itama ta shigo cikin d'akin da saurin ta, sakin baki tayi tana kallon Husnah ta ta'be tace, "Husnah tace uban waye kike yiwa wannan iskan cin? Husain shine ka saka mata ido tana irin wannan iskan cin a gidan ka, bayan ta daki Amaryar ka, dan ka rama mata shine take wannan iskan cin kazo kana lallashin ta? ".

Cike da takaicin abun da Anty Zarah takeyi mata, cikin kuka tace, "wallahi na fasa Auren dole mutum ya sakeni naje neman dan gina wallahi kuma na Auri wanda nake so, yake sona".

Aikuwa da sauri Anty Zarah ta buge mata baki Husain kuwa jijiyoyin kansa har tashi sukeyi idon sa ya rufe cike da masifa yace, "sai mi dan na rabu dake ke kai ce mace ko kuwa ce maki akayi zama na karuwa son rai nane, dan kinga kowa yana goyon bayan ki, sai aka ce maki no sonki nakeyi ne!? ".


Cike da ba'kin ciki Ummey ta fashe da kukan takaici duk sai iskan cin kowa ya tsaya tsab kamar anyi ruwa an d'auke babu wani mai magana kukan Ummey kawai ke tashi, tana fad'ar innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, allhuma afjirni fi musibati, wahalafni khairin min ha, kawai ta tashi buuuu kamar guguwa tabar d'akin kowa yana kiran Ummey Ummey amman inaaa Ummey tasa kai kuka kawai takeyi, tashi duk sukayi suka mara mata baya, Husnah kuwa kasa tashi tsaye tayi dan jiri ke d'ibar ta, kuka kawai takeyi, kanta jin takeyi kamar ya tarwatse saboda ciwo, Husnah daurewa tayi ta tashi a hankali ta nufi why drop dinta ta d'auki doguwar riga ta saka juwar da zatayi ta dawo bakin gado kawai jiri ya kwashe ta sai 'kasa wan wars, kwance Husnah take numfashin ta ya d'auke d'iba.



Ummey kuwa haka tabi hanya tana kuka su Anty Zarah da Husain suna biye da ita suna kuka, basu tsaya ko ina ba sai cikin gidan duk wanda ya ga Ummey a lokacin sai tabbar da babu lafiya, a gidan mutane duk sun rud'e shi kan shi Daddy ya shiga cikin tashin hankalin dan yau shine farkon ganin kukan Ummey har tabiyo hanya a hakan yasan mummunan abune ya faru.


Hannun Ummey Daddy yaja, suka zauna yace akawo mashi ruwa, da gudu Anisah ta kawo ruwan sanyi coffi ansa yayi ya zuba ruwan da hannun sa ya bata tasha, ya kawo mafefeci yanata fifita mata, yanayi yana tofa mata addu'a cikin Ikon Allah ta soma sauke ajiyar zuciya sai da yaga alamar natsuwa a tattare da ita ya kama hannun ta duka biyun yana murzawa yana kallon ta, zuwa can yace, "kin gano wa idon ki mugun zaman da sukeyi ko?"



Naso na dakatar dake, amman kuma naga ya dace ki tabbar wa idon ki gaskiyar lamarin, Hajiya maganar gaskiya ita ce, Husnah da Husain ido ne kawai maganin su, duk ranar da suka ga damar gyara rayuwar Auren su, su gyara, ai idan ita Husnar shirme yayi mata yawa, shifa Husain baga matar Auren sa nan a gaban sa ba, miyasa ita ya d'auke ta a matsayin matar sa, kuma ita ma margayiya Mardiyya fa haka yake zaune da ita ne? ,



To dan Allah ki rabu dasu da iskan cin su, gir_giza kai Ummey tayi hawaye na zuba a idon ta, tace, "Alhaji na ri'keka da kasa baki a kawo karshe Auren nan da suke ikirarin ba zasu zauna da juna ba kowane a gaban idona ya bukaci a kashe Auren tunda basu kaunar junan su, Husnah da Husain Auren su zunubi ne kawai suke kwasa su dukan su biyun! "



Gir_giza mata kai Daddy yayi yace, "ya ilahi tabbas kuwa zan d'auki mataki akan wannan kukan da suka saka mani mata tanayin sa, idan su basu san darajar Auren suba to ni nasan darajar nawa Auren, duk kuje ku bamu guri dukan ku bana bu'katar ganin mutum ko d'aya a gurin nan! ".



Tashi kowa yayi kowa da kukan sa, Husain gida ya koma direct d'akin Husnah ya shiga halin da tsinci Husnah a cikin sa shine ya 'kara d'aga masa hankali koda ya ta'ba ta sam bata motsi, gaban sane ya fad'i cikin sauri ya kira Anty Zarah yasan ita ce kawai zata iya daukar wayar sa, cikin razana, yace "Anty Zarah Husnah ta mutu bata motsi".


Kit ya kashe wayar.

Anty Zarah kuwa wata uwar kalmata buga tace shike nan Husnah ta mutu, na shiga ukku ni Zarah da wani uban hanzari Yaya Yusuf yake kiran Husain Amman Husain ya kasa d'auka, kawai suka ja mota dan sai sunfi sauri suna isa 'kofar gidan suka taka burki suka fito da gudu Shaheed da Yaya Yusuf da Anty Zarah Anisah suka shiga cikin gidan d'akin Husnah suka nufa turus sukayi, suna murza ido, da ket su Yaya Yusuf da Shaheed suka 'karasa gurin Husnah suka fara dubawa Anisah tace shike nan Husnah ba'kin ciki ya kashe ki, wayyo Allah ni Anisah".


Bin ciken Husnah sukeyi har suka gano cewar somewa tayi, ai kuwa d'aukar jin jira sukayi mata suka fita da ita sai mota suka nufi asibiti da ita, da sauri aka anshe ta taimakon gaggawa aka bata, bata falka ba har akayi awa ukku dole Yaya Yusuf ya kira Daddy ya sheda masa halin da ake ciki, da sauri Daddy ya sanar wa Ummey, ai kuwa ta 'kara rud'ewa, haka sukaje asibiti amman har zuwa lokacin bata falka ba, sosai suka shiga cikin tashin hankali, Husnah sai da cikin dare ta falka daga suman da tayi, kanta takejin yana sara mata kamar ya cire.



Dafe goshi tayi a hankali ta juya sai akan idon Anisah wadda aka bari ita da Anty Zarah su Yaya Yusuf da Shaheed da Husain suna waje, da sauri Anisah tace, "Husnah sannu kin falka ne? "


gyad'a mata kai Husnah tayi tana rufe da ido ta, haushin kowa takeji, Anty Zarah kuwa tun lokacin da taji Anisah ta ce Husnah ta falka ta soma ajiyar zuciya da godiyar ta kafe Husnah da ido.


Fita Anisah tayi sai gata ta dawo dasu Yaya Yusuf da Doctor, sannu suke yiwa Husnah amman bata kalli kowa ba kuma bata amsa ba, Doctor ne ya ce, "ina fatan ba wata matsalar bace ta hanaki bud'e ido ba"


Kai Husnah ta nuna masa wanda take jin kamar ya tarwatse saboda ciwo, sannu suke jero mata, Doctor yace, "ku bata koda ruwan tea ne ina son nayi mata allura ne da ruwa"


Da sauri Anisah taje ta had'a mata ruwan tea sai da ya rage zafi sannan ta kawo mata, Anty Zarah ce tace, "Husnah bari na kamaki kisha tea ko? "


Da sauri Husnah tace, "wallahi yau sai dai nayi ta zama da yunwa ta dana yarda ki bani wani abu da hannun ki! "


Cikin muryar masa lafiya Husnah take wannan maganar, ai kuwa Anty Zarah taji babu dadi duk da tasan hakan zai iya faruwa, daman, Anisah ce ta kama Husnah ta tashi ta bata ruwan tea idon ta har yanzun a rufe suke, sai da ta dan sha san nan ta kauda kai gefe, dan lokaci Doctor ya bata kafin ya dubata, ya fita.


Yaya Yusuf ne ya ce, "Husnah dan Allah ki ajiye komai ki samu lafiya sai muje gida muyi magana kinji? ".


Ba tare da Husnah ta kalli inda yake ba kuma bata gyad'a masa kai ba, shiru tayi abun ta, kowa cike yake yau da mamakin irin wannan fushin na Husnah wanda ya shafi kowa.


Allurar da Doctor yayi mata ne ta soma aiki, bacci har ya fara d'aukar ta Anisah ta tashi ta gyara mata kwanciya gudun wuyan ta yayi ciwo.


Suna ganin ta koma bacci su Yaya Yusuf suka sauke ajiyar zuciya suka fita daga cikin d'akin suka nufi massallaci, su Anty Zarah kuwa a haka suka kwana, sai lokacin sallar asuba sukayi sallah da gari ya soma haske san nan sukayi shirin zuwa gida dai_dai lokacin ne su Ummey suka shigo bayan sun gaisa ne, Anisah take basu labarin farka war Husnah, hamdala Ummey ta sauke, ita da Daddy da Suhailah, Ummey kuwa tace, "kuje gida ku futa Zarah sai zuwa anjima sai ku dawo amman fa kuyi bacci kunji ko?".



Amsawa sukayi suka tafi, tare dasu Yaya Yusuf suka tafi gida, Husnah kuwa tun lokacin zuwan su Ummey ta falka, ganin su Husain ne ya nata bud'e ido, sai fa da ta tabbar sun tafi sannan ta bud'e ido, murmushi Ummey tayi batare da ce Husnah uffan ba, rikata tayi, ta tashi zaune Suhailah ce ta, rikata suka nufi bayi, tayi brush, ta bata guri tayi lalurar ta sannan ta fito a bakin 'kofa suka had'u da Suhailah kawai ta ri'ko ta suka, dawo saman sallaya ta zauna, tayi sallolin da ake biyar ta, bayan ta gama ne Ummey ta bata breakfast da kanta, har sai da ta tabbatar da ta 'koshi Kawai doctor ya shigo koda ya duba ta yaga jikan ta yayi kyau yayi mata tambayar mike damun ta yanzun, ta sheda masa ciwon kai ne da ciwon ciki, allurai ya rubuta mata da magani ya basu sallama tare da sharuddan shan magani da cin abinci.


Doctor na fita suka fara tattara komai nasu, Daddy ne ya shigo cikin farin ciki ya anshi takardar sallama da ta maganin yace, "ku fito mu tafi gida ko? ".


Haka dai suka fito Husnah tana tafiya zaka fahimci cewar batada lafiya, saboda tanayi tana cije baki, har suka isa jikin motar Daddy suka shiga sai gidan Daddy, suna zuwa su Anty Zarah dasu Shaheed Yaya Yusuf suka fara murmushi tare da godiyar Allah, sannu suka hauwa Husnah amman kamar bada ita suke ba, d'aki kawai ta wuce abin ta.



Dariya Daddy yayi yace, "Ikon Allah ni wannan fushin na Husnah dariya yake bani, ace kowa ya shiga ciki, To wai mukam miye laifin mu a ciki ne, Bayan abun a tsanin ta da mijin tane Husain?".



Dariya duk sukayi Ummey tace, "yo ni wannan tam bayoyin naka a jere Alhaji ai duk bamu da amsar su, sai dai mu jira har ta samu sau'ki mu zaunar dasu zama na 'karshe akan wannan Auren nasu na jaraba".


Haka dai akayi ta tattaunawa, Husnah kuwa bacci kawai takeyi bata magana da kowa, har aka kwana biyu ta samu sau'ki Alhamdulillah, Daddy ne ya tara kowa a gurin Ummey Yaya Yusuf Anty Zarah dasu Shaheed Anisah Suhailah Safiya sai iyayen gayyar wato Husain da Husnah, Daddy ne ya fara bud'e taro da addu'a fuskar shi sam babu wata walwala, ba dariya fuskar sa a d'aure.



Yace, "duk kowa yasan abun da ya taramu anan to ba zanyi wani dogon bayani ba, Husnah Husain, miye kuka aikata a ranar da kuka saka Hajiya kuka abunda ya zo ya d'aga hankalin mu saboda munga ba'kon lamari a gurin wadda bama zaka iya fusata taba, sai gashi harda kukan ta da hawaye a idon ta, kuma ta biyo hanya a haka har gidan nan, ku muke saurare!? .




Duk shiru gurin ya d'auka sai sautin

Please Login or Register in order to submit comment