Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya sai ta Bindigar sa a kan Husnah, itama Husnah ta saita Bindigar ta akan Husain, sai zufa ke zubo masu kawai Husain ya ce da Husnah, " daman nace sai na kashe ki da hannu na yau ga dama ta samu, kinga babu mai yi maki magiya ballema a hana ni aikata hakan " ya bushe da dariya.


Husnah kuwa dariya ta bushe da ita, tace, "to kai ka manta yanda akayi har na yarda na zauna dakai? To ka sani daga yau sai nabar tarihi nice mace ta farko wadda ta fara kashe mijin da ya damu da ita"


'kara saita Bindigar sukayi a take suka halba, jin kake darammmmmmmmm_darammmmmmmmm.....



Dai dai saiti da shigowar su Anisah Tk Zubaidah Yaya Yusuf, wata irin 'kara suka fasa, suka dafe kai.......





*Comment and share*



*A GIDANTA NA GIRMA*




*BY NANA: KHADEEJATU*

*_UMMU IHSAN_*


*SADAUKAR WA GA :- DUK KANNIN MASOYA NA NABOYE DANA BAYYANE INA SONKU SOSAI SON FISABILILLAH*


*YA ALLAH KAJIKAN BABA NA DA MAMA NA KAYI MASU RAHMA KA KYAUTATA MAKWANCIN SU KA SANYA SU A ALJANNAR KA TA FIRDAUSI BIGAIRI HISAB SU DA YAN UWA MUSULMI BAKI `DAYA.*

*AMIN YA ALLAH*


*To Alhdulillah Allah ya nufeni da dawowa gashi zamuci gaba daga inda muka tsaya*



*_Bismillahir Rahmanin Rahim_*

95~100

Wani irin uban ihu duk mutanen gurin sukayi, babu kamar yallabai wanda ya fad'i kwance 'kasa cikin jini yana zabga uban ihu hannun sa d'aya dafe da ka fadar sa, d'aya hannun kuma dafe da cinyar sa, sai jini ke zuba, mutanen gurin cike da mugun mamaki suke kallon Husnah da Husain da yallabai wanda ya fita cikin hayyacin sa, abunda ya 'kara baiwa mutanen mamaki shine ganin Husain da Husnah a tsaye ri'ke da bindigogin suna a jere da junan su, sun 'kara saita Bindigar akan yalla'bai kuma Husnah itace ta saita zuciyar yalla'bai Husain kuwa ya saita Bindigar sa akan yalla'bai, duk cikin jin haushin abunda su Husain da Husnah suka aikata wa ogan su, kawai suma suka d'auki bindigogin su suka saita su Husnah da su.


Husain yace, "ashe dai ku duk kidahumai ne tunda har kukayi tunanin zamu iya kashe kan mu da kan mu mu aikata kusan kai, amman gaskiya na kara raina maku da wayau tunda har kukayi sakacin zama baku sha maganin bindiga ba, ai kuwa zamu 'karasa kashe mugun iri inyaso kuma sai ku kashe mu"


Husnah tace, "yalla'bai kaga yaran nan naka basu damu da abunda muka aikata maka ba, tunda ka gan su nan kowa ya nemi Bindigar sa dan ya kare kansa kai kuma indan ta sune mu 'karasa kashe ka, ko suma sun gaji da goyon bayan ba, saboda haka kasan nayi fa, daga yau kayi ban kwana da wannan izzar taka da mulkin zalluncin al'uma".

'kara saita har sashen su Husnah da Husain sukayi zasu sake halbawa, cikin tsawa da rad'ad'in aza yalla'bai yace, "ku... da... Kata... Dan.... Allah, kada ku kashe.... Ni..... , ku fad'i abunda..... Kuke da bu'katar sa.... koma miye koda duka dukiyar... Dana tara ne.... ".


Da sauri Husain ya ce, "dakata! An gaya maka cewar mu shasha sune da zaka bamu dukiyar haram mu ansa? To idan bacci ma kakeyi yanzun ka falka fansar a d'aya ce, ka basu umarnin su kawo bindigogin su anan su ajiye su a gaban mu kuma duk su durkusa 'kasa kai suma kwanta su rufe ido indai har suna bu'katar ganin ka a raye!,

Kuma wannan yan uwan nawa da suka shigo a yanzun nan ka bada umarnin a maida su gida lafiya ba tare da wata damuwa ba"



Cikin tsawa da a zabar da yalla'bai yake ji ya basu umarnin yanda Husain yake bukatar ai kuwa sukayi tsalle suka dire suka ce, "mufa sam bamu yarda da wannan maganar ta gamam min ha'kori ba kawai dai ka bar mu dasu mu kashe su dama kasan muna da haushin su a can baya lokacin da ka saka su goga gadin wannan masifar lokacin da suka suka saka muka rasa mutanen mu suka saka aka kaisu a gaban hukuma dan haka gara kabar mu mu kashe makiyan mu! "

Husnah tace, yalla'bai kaga sun nuna maka shedar sun fi kowa farin ciki da ganin bayan ka, tunda sukeyi maka fatan barin duniyar nan".
Cikin masifa yalla'bai yace, "idan kuka yarda suka sake aikata mani irin wannan raunin saboda gardamar ku, to ba kuba har dan ginku sai na 'karar dasu..."

Tunda suka fahimci da gaske yalla'bai zai iya aikata fiye da abunda ya fad'a duk sai suka saduda sukayi yanda su Husain suka bada umarni aka fita dasu Yaya Yusuf ta wata hanya wadda Zubaidah ta nuna masu tace, "indai da gaske ne gidan zasu kaimu to nan ne kawai hanya mafi sau'kin bi".

Anisah da Tk da Shaheed wanda suke cike da mamakin taya su Husain da Husnah suka koyi irin wannan aikin suda ba training din koyon halbi sukayi ba, daket suka ajiye tunanin suka ce, "kai gaskiya babu inda zamu saboda mutseratar da rayuwar mu, mubar ta yan uwan mu a cikin hatsari"

Husain da Husnah cikin masifa sukace dallah ku tafi so kukeyi ayi mutuwar kasko anan ne? Iye? ".

Tafiya sukayi badan sun soba sai dan ganin irin yanda su Husnah da Husain suka hasala, suna shiga hanyar kamar labule suka wuce zuwa wanda suka kaisu suka dawo suka nuna masu video sun kai su, murmushi su Husnah sukayi.


Husain yace, "to ranka ya dad'e sun aikata yanda muke so, amman kuma wani hanzari ba gudu ba, nasan halin ka gaba da baya zaka iya idan mun barka a raye zaka iya biyar mu da dangin mu ka kashe kaga kuwa mun kashe wutsiyar maciji mun bar kai da gan_gar jiki, kaga kuwa da sauran Rina a kaba ke nan ".

Husnah ta ce, "dan haka gara mu fara kashe ka kaida yaran ka, tun kafin ka kashe muna kowa namu, muma ka kashe mu".

Cikin zabura wani yazo tashi ya d'auki Bindigar sa, Husnah ta dawo da Bindigar akan sa, tace, wato kaine kake son zama farkon mutuwar ko? ".

Jin Bindiga a akan sane ya saka shi fasawa, cikin rawar jiki yaja baya Husnah tasa 'kafar ta, ta ri'ka tura bindigogin nesa dasu, sannan ta gyara tsayuwar ta ta ce, " yalla'bai ina da bukatar aron waya, dan ba zamu rabu da ku haka kawai kuji dad'in ganin bayan mu ba, dan haka gara musan nayi tun kafin lokaci ya 'kure muna ".

Yalla'bai ya ce, "dan Allah kada ku had'a mu da hukuma d'an sun dad'e suna nema na basu ganni ba, amman ni ina ganin su, kuma koda sun ganni a lokacin ba zasu iya aikata komai a kaina ba, yau ita ce rana mafi muni a gareni domin kuwa tun kafin hakan ta faru masu yi mani duba sun sheda mani wata rana sai na d'auko wa kaina wanda zasu ga baya na, kuma duk tsafina baya aiki akan su, ni kuma shine na na saka akayi mani duba ga duk yara na, amman sam ba su bane wasu ne can na daban mace da namiji kuma babu wanda yake ganin fuskar su, shi yasa nake ta kashe duk wanda na d'auko koda kuwa a ce mace mai tsohon ciki ce, da mijin ta sai na kashe su, gudu ni su kashe ni".


Kuka Husnah ta saka ta ce, "shi.. Ke.. Nan ka yarda da tsafin ka sabawa Allah kake kashe mutanen da baine ka kawo su duniyar nan ba, kuma shine kaso ka 'bata mani rayuwar ka Aure ni, ka kashe ni da raina..! "

Kuka kawai Husnah keyi, "Husain cikin tsan_tsar tsana ya dubi mutanen gurin a wulance, yace, "tir da rayuwa irin wannan, wallahi kun daukar wa kanku kaya, kuma tunda har masu tsafin ku sun sheda maku cewar mune zamu kashe ku, mun fasa, idan kun so mu ku kashe mu, amman mu bamu yarda da tsafi ba, ballema mu zamo masu cika umarnin matsafa, kawai Husain ya jefawa yalla'bai Bindigar, ya juya gurin Husnah ya anshi Bindigar hannun ta ya ajiye sukayi zaune a 'kasa suna dafe da kai Husnah na kuka harda hawaye da majina Husain kuwa kukan zucci yakeyi idon sa yayi mugun ja, jijiyoyin kansa duk sun tashi saboda tsabar shiga cikin tashin hankalin.

Su kuwa yaran yalla'bai suna ganin haka da sauri suka d'auki bindigogin su suka sai ta su Husain dasu, yalla'bai ne ya basu umarnin da su rabu dasu su kai sa d'akin sa, ayi masa aiki.

Ya bada umarnin a fita dasu Husnah daga cikin gidan.

Cika umarnin sa sukayi suka tasa Husnah da Husain a gaba suka fitar dasu daga gidan su Husnah na fita mutanen ya koma tanga menen gidan dan baiwa ogan su kulawa, sauran kattin dake harabar gidan ko kallon su Husnah basuyi ba, saboda suna lokacin da aka fito dasu duk da cike suke da mamakin wannan shine karon farkon da aka ta'ba shiga gidan da mutane kuma suka fito da ransu da kafafuwan su, har suka isa bakin get maigadin gidan suka bud'e masu get din cike da mamaki, su Husnah da Husain ba fita daga cikin gidan aka rufe get din kawai suka ga ashe ma cikin uban jeji suke kallon_kallo aka shiga yi, tsakanin Husnah da Husain, sai duba gurin da suke sukeyi.

Rasa ma wace hanyar ce zasu kama, sukayi tunda gurin duk itace ne da shikko ki babu alamar gurin da mota ko mashin suke bi.

Tsaye suke sun ri'ke 'kugu suna dube_dube, wata murya sukaji marar dad'in saurare daga bayan su ana fad'ar, tunda kuka ki kashe sa, to kusani ba zaku iya fita cikin jejin nan ba, idan kuma kuka dawo zaku shiga cikin gidan ku kashe shi da hannun su, to zaku sami hanyar fita daga cikin jejin nan cikin sau'ki".

Husain ya ce, "mu ba jahillai bane kuma ba zamu cika umarnin wani banza ba, sha katafi, kuma mun dogara ga Allah shine zaiyi muna mafita! ".


Husnah tace, "idan su kun samu damar batar dasu, to mu munyi imani da Allah kuma munyi imani da kaddara mai kyau ko marar kyau dan haka insha Allah yau a gida zamu kwana".

Husnah harda su Murgud'a baki kamar irin taga mai maganar nan.

Tafiya suka fara yi a jere duk sun gaji har suka bar kofar gidan kawai sukaji wani uban ihu da gir_giza sai kuma sukaji wani irin dammm kamar bom ya tashi sai hasken wuta suka gani ga iska mai 'karfi gaske ya taso da 'kura itacen gurin kamar su karye da wani irin 'karfin gaske Husain ya janyo Husnah ya rungume suka kama wani icce suka ri'ke sai addu'a sukeyi duk wadda tazo bakin su, aikuwa sannu a hankali har iskan ya daina jan su, kawai ma suka daina jin iskan a jikin su iskan yayi gaba, kawai sai zafin wuta ga hasken ta, kafin su Husnah su 'karasa mamaki sai kawai sukaga itace sun 'bace, gidan da suka baro ne keci da wuta bal_bal_bal cike da mamaki su Husnah da Husain suka saki baki da hanci suna kallon gidan wuta kawai yakeci da ita, juyawa Husnah tayi tace, "ikon Allah, Husain yace Allah mai iko da buwaya.

Kawai suka fara jin motsin motoci a bayan su suna juyawa kawai suka gan su a kusa da titi, da sauri Husain yace, "mi hakan ke nufi!?.

Husnah tace, "titin kusa da gidan da na girma ne, lallai kuwa nadawo gida" da gudu Husnah ta nufi gidan Zuby har ta kai bakin get Husain ya rigata ya tsare hanyar shiga cikin gidan yace, "kee! Kina nufin wannan kazamin gidan zaki shiga? To bari kiji bada umarni na ba, kuma na haram ta maki shigar sa, wannan karuwar matar zaki je gurin ta, wata kilama da saka hannun ta gurin kashe mani mata, kema taso kashe ki, to ba zaki shiga ba ciki ba".

D'aure fuskar da Husnah taga Husain yayi ne ya sakata sakin uban kuka, tace, "haba haba wannan wane irin rashin adalci ne, ni wallahi uwata ce ita dan ni *A GIDANTA NA GIRMA*.

Husain ya ce, koda kuwa *A GIDAN TA kika GIRMA* bata baki tarbiyya ba haka ilimin addini, dan haka wuce muje gida malama".


Husnah kuwa kafewa tayi sai kuka takeyi zuwa can sukaji muryar Shaheed yana fad'ar, "haba Yaya Husain nifa a gani na tunda Allah ya kubutar daku kamata yayi ku samu gurin da zaku zauna ku futa, kuci abinci kuyi wanka, kuyi sallolin da ake biyar ku, sai sanar damu taya kuka ku"buto daga tarkon azzalumai ba wai fad'a ba".

Cike da mamaki Husnah da Husain suke kallon Shaheed wanda yake tsaye da alama gidan Zubaidah ya fito, Anisah kuwa da gudu ta rungume Husnah harda kukan ta.

Husain murza idon sa yakeyi cike da takaici yace, "mi kukeyi a nan gidan kema Anisah karuwancin ne kika soma? Shaheed dan kunga bana nan sai ku d'auki d'amarar zubar da mutumcin mu? "

Yaya Yusuf ne ya dafa Husain ya ce, "zo muje cikin gidan zanyi maka bayanin komai" hannun Husain yaja wanda Husain a yan zun kam ya zama wani calendar dashi sai bin su yakeyi da ido.

Husnah da gudu tayi cikin gidan itada Anisah a jikin Zubaidah Husnah ta fad'a ta fashe da kuka itama Zubaidah kukan ne takeyi ta ri'ke Husnah da kyau.

Husain takaici ne ya kamasa ganin duk yan gidan su a cikin gidan Zubaidah jin yakeyi kamar yayi ta dukan kansa.

Zuwa can Zubaidah tace, Husnah ki yafe mani nasan nice silar lalata rayuwar ki, dan Allah ki yafe mani nasan ko hakkin ki kawai ba zai bar ni ba, Husnah kiyi mani uzuri a lokacin ina cikin giyar 'bata ne da jahilci amman yanzun na dawo hanya madai_dai ciya Husnah yan zun ina jin ciwon lalata rayuwata da taki rayuwar da nayi da rayuwar wasu ma yayan mutane Husnah, yan zun na ajiye komai sai tuba da nakeyi da neman ya fiyar Allah makadaici, tabbas a yan zun haka ina jin kunyar yanda zan kalli cikin idon iyayen ki da nawa iyayen da iyayen mutane da dama, Husnah na tuba nabi Allah har nafa biyar iyayen yara ina neman yafiyar su wasu sun yafe wasu basu yafe ba, gashi nawa iyayen ban ma san duniyar da suke ciki ba, ko suna raye ko basa raye Allah shine mafi sani, amman wallahi ban san inda suke ba, sai a yan zun ne nake nadamar wulakanta iyaye na gashi na bari damar ta ku'buce mani, nayi wasa da dama! ".


Kuka kawai Husnah da Zubaidah sukeyi Anisah cikin shashshekar kuka tace, "insha Allah suma duk inda suke suna nan suna yi maki fatan shiriya kuma da ace zasuga yanda kika shiryun nasani fushin su zai gushe ne su rungume yarsu, Anty Zubaidah har yanzun kina da sauran dama, da Allah yasoki da rahamar sa, shiyasa ya baki ikon tuba, fatan mu dai Allah ya kar'bi tubar ki".

Anty Zarah ta ce, " Anty Zubaidah ba zan gushe ba nima ina taya ki addu'ar neman yafiya a gurin mahaliccin mu kuma Husnah ta yafe maki, dan Husnah bata da fatan da ya wuce ki shiryu tayi farin ciki ".

Jin muryar Anty Zarah kawai Husnah ta koma jikin ta ta kwanta tana kuka tace Anty Zarah kece kikafi kowa sanin manufata ki 'kara sanar da ita cewar na yafe mata kuma burina ya cika wadda ta raine ne na *GIRMA A GIDANTA* yau ita ce zanyi alfari da ita, Alhamdulillah Allah kaine abun godiya ".

Rungume ta Anty Zarah tayi, tace, Husnah kin san idan har zanyi farin ciki tofa lallai ne na fara ganin naki farin cikin dan haka Husnah ina godiya ga sarki Allah wanda ya bamu Ikon ganin wannan ranar ta farin cikin ki Husnah dan haka lokacin kuka ya 'kare yan zun lokacin dariya ne".

Husnah gogoge hawayen ta , tayi tace, "bari nayo wanka na dawo zan baku labarin abunda ya faru "

Da gudu Husnah ta haye sama ta shiga tsohon dakin ta, mamaki ne cike da Husnah ganin d'akin fes dashi babu alamar datti murmushi Husnah tayi, tayi shirin wanka ta shiga bayin ta rufe.


Husain kuwa 'kara hasala yayi ya'ki cewa da kowa uffan Anty Zarah ce ta dawo a kusa dashi taja hannun su ya tashi sukayi waje can hara bar gidan suka nemi guri suka zauna Anty Zarah ta ce, "nafi kowa sanin halin Husain nasan Husain ya tsani gidan nan da matar gidan amman Husain kayi 'ko'karin yin afuwa da uzuri a gurin yan uwa musulmi baki d'aya,

Husain Zubaidah ta tabka babban kuskure amman ta gane kuren ta, sai ka yafe mata, nasani zaka iya yafe mata dan haka Husain ka sassauta fushin ka a kan ta, dan tun kafin ka dawo tace, ba zata iya tun karar ka ba da sunan neman yafiya dan tasan da ta riga da tayi maka illa babba, Husain mu taru mu 'karfafa mata gwiwar ta dan kada ta sare, alhaki ya hau kanmu tunda ta tuba kuma muna yi mata fatan tubar gaskiya ".

Ajiyar zuciya Husain ya saki yace, "nifa ba wai na ki yafe mata bane ni na dad'e da yafe mata kawai dai bana son ganin wan nan gidan ko kadan be, kuma itama idan ina kallon ta ada sai naji kamar na kashe ta amman yanzun yanda naga tana zubar da hawaye sai naji tana bani tausayi".

Murmushi Anty Zarah tayi tace, to Alhamdulillah Husnah tazo mu koma gida, suna nan zaune har su Husnah suka fito aka shiga motoci suka nufi gida, suna isa a bakin get suka sami mutanen gidan suna jiran iso war su, cikin farin ciki Daddy ya rungume Husnah da Husain haka Hajiya su baffah ma cikin farin ciki suke a babban falon gidan suka yada zango Husnah na jikin Hajiya Husain kuma jikin Daddy, baffah ne ya bud'e taro da addu'a da nuna farin cikin sa ga Allah subhanahu wata ala da ya kubuto masu da yaran su, baiyi wani dogon bayani ba saboda ya sanar da cewar yaran na bu'katar yin salloli da cin abinci da futawa, haka aka tashi taron.


Husnah d'akin su ta shiga Husain ma ya nufi tsohon d'akin sa, haka kowane daga cikin su ya gabatar da komai nasa, gashi magriba tayi basu fito ba abinci ma a d'akin aka kaiwa kowa, suna gama sallar isha'i suka kwana bacci sai sallar asuba kawai sukayi suka koma, sai 'karfe goma da rabi Husnah ta fito a cikin falon ta samu kowa a gurin harda Husain da fito 'karfe goma dai_dai.

Gaisawa tayi dasu Daddy da Ummey da Yaya Yusuf da Anty Zarah da Yaya Shaheed da matar sa, sai su Anisah da suka tafa Amman ko kallon Husain batayi ba.


Abinci aka bata taci ta koshi duk Husnah da rashin cin abincinta yau taci Indomie sosai, sai da ta 'koshi sannan kowa ya 'kara gyara zama nan Daddy yayi gyaran murya yake tambayar su abunda ya faru kuma taya aka zo aka d'auke Husain a asibiti, bayani dallah_dallah sukayi kowa sai da ya tsorata ga tsoron Allah daya 'kara ka masu, Husnah kuwa yan zun kuka takeyi sosai tace, "Daddy sai yanzun nake 'kara jin tashin hakali ace da hannu na ne na halbi mutum a 'kafar sa kai inaa!?.



Share mata hawaye Ummey tayi tace, shida ya kashe mutanen da bai san adadin su ba fa ciki kuwa harda matar Husain wato Mardiyya da dan cikin ta da suka halbe a ciki, bayan sun dawo da ita d'akin futu sun cire mata d'an itama ta birkice tace ga garin ku nan".


Tun daga Husnah har Husain tsaye suka tashi jikin su na rawa, Husnah wani uban kuka ta fasa, Husain kuwa fad'uwa yayi da'bas yayi zaman "yan bori, hakuri aka hau basu, da ket sukayi shiru yinin ranar basu da wani kuzari Husnah sai dramar su take tunowa, Husain kuwa ba'a cewa komai.


Daddy ne yace su tashi suje suyi gaisuwa, haka suka tafi gidan su Mardiyya sai dare suka dawo gida.

Haka suka zauna a gidan su Daddy kullum cikin damuwa har sai da sukayi sati d'aya sannan suka fara dawowa hayyacin su, sai da sukayi wata biyu sun murmuje Daddy ya tarasu yace, su dawo gidan kusa dashi cikin mutane dan ya gama gyara masu gidan ya saka masu komai dan haka zuwa dare zasu koma gidan su, idan yaso su dai_dai ta zaman Auren su ko kuma ya d'auki mataki akan su, tun da ya fahimci basu da hankali suna mata da miji ace ko magana basu ta'ba yi ba duk zaman su a gidan kuma a gaban idon su ma ke nan ina ga suna gidan su, cikin fushi Daddy da Ummey sukayi masu kaca_kaca, kuma suka 'kara jaddada masu ko su gyara ko kuma suga 'bacin ran su.



Hakuri kawai suke badawa, Daddy ya ce, "ku tashi ku baiwa mutane guri sha_sha_shu kawai mutanen banza yofi! ".

Tashi sukayi sum_sum suka bar gurin dare nayi Ummey tace, "kuzo ku tafi mun sallameku! "


Cikin d'aure fuska Ummey ke magana dan haka suka bar gidan jikin su a sanyaye, driver ne ya jasu da mota ya kaisu gidan, ai kuwa gidan ba karya ya had'u kamar ma yaso yafi wanda suka baro had'uwa.



Husnah na shiga cikin gidan kawai ta wuce d'aki d'aya haka Husain.

Tunda suka shiga babu wanda ya fito Husnah fad'uwar d'akin ne ya saka ra kin fitowa Husain kuwa tsaki yakeyi an rabosa da gidan sa wanda yafi so da kauna.


Babu wanda ya fito sai da safiya gidan har da masu girka masu abinci suke dasu kuma Kafin su fito angama gyara ko ina a gidan, Husain koda ya fito ya ga abinci a danie table kawai yaje ya duba tsaki yayi ya fita ba tare dayaci komai ba, Husnah najin fitar sa itama ta fito abincin ta duba, tace kan uban can uban waye ya da umarnin cewar adafa mani sakwara da miyar dage_dage, kai wai ma su waye a kitchen din? "



Da sauri Husnah ta nufin hanyar da take jin kamshin girki a gurin.

Yammata ne guda biyu sa'anta sai tsohuwa d'aya sai wata wadda zata kai sa an Zubaidah, kallon su kawai Husnah keyi, cike da mamaki a fuskar ta a hasale tace kai waye ya d'auke ku yin aiki a gidan nan kuma wai harda girk! ?.



Duk shiru sukayi mata kawai Husnah ta juya a hasale zata fita, Husain ne suka ci Karl dashi kowa ya janye d'an uwan sa a hanya, cikin fushin Husain yace, "tunda kune kuka d'auki kanku aiki kuzo kubar gidan nan wallahi tunda ba gidan ku bane! ".


Hanya Husain ya nuna masu, cirko_cirko sukayi suka tsare su da ido, Husnah tace, "kamar ana magana da ita ce? Dallah malamai kowa ce ta san inda dare yayi mata, bama bu'katar wasu yan aiki anan uwa uba wai masu abinci".



Husain yace, "ko ku fita da arziki ko kuma ku fita da tsiya mayun mutane kawai ".


Husnah ta bude baki zatayi magana sukaji magana daga bayan su, uban waye kuke kora ne? To nice na kawo maku su suyi maku aiki tunda ku bazaku iya tsara komai ba da kanku, shine nakawo maku masu kula da gidan dan gudun kada shima gidan ku koyar dashi ba'kin halin ku, kuma nice na sanar dasu indai ba nice na bada umarnin subar gidan nan ba, ko suyi wani aiki a gidan nan ba, to kada subi umarnin kowa ko waye a gidan nan kuma na basu wayar da zasu ri'ka kira na idan wani abun ya faru koda wata bakar magana kukayi masu! ".



Jiki a sanyaye suke bin Ummey da kallo kawai ta juya tabar kichin d'in suma fita sukayi daga kichin d'in suna biye da Ummey kawai ta tace, "zan 'kara jan kunnen ku Husnah da Husain masu kunnen kashi, babu ku babu shiga sabgar masu aikin gidan

Please Login or Register in order to submit comment