Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bashi key din motarshi dake hannunshi. Hade rai Alhasan yayi ganin haukar na AB'ILAL na gaske ne, ya gaji da lallabashi. "Bazan baka ba, kai mahaukacin ina ne dazaka dauki hanyar kano yanzu da tsakiyar daren nan,..." Alhasan yy mgnr shima a hasale. Ab'ilal ya kara hasala ya daga kafada cikin izza da mulki da kasaita yce ''ina ruwana da dare, in zaka bani key ka bani kawai ni kano zan tafi, bazan kara kwana a wannan garin naku ba na manya manyan karuwai da yan DANDI..." Karshen mgnr tashi ta bawa Alhasan dmr gano tabbas wani abu akawa AB'ILAL din daya harzuqashi har haka, maybe wata macece ta kawo masa kanta..." Zuciar Alhasan tayi wannan tunanin. Nan de ya shiga lallaba AB'ILAL wanda ya dage kan dole shi seya bar garin zuwa garin kaduna a wannan tsohon daren me furfura. Da kyar AB'ILAL yabi alhasan zuwa cikin gidan nasa madaidaici me madaidaicin kyau da Tsaruwa, a bedroom suka yada zango AB'ILAL ya haye kan bed din zuciarsa babu dadih, jinsa yakeyi tamkar bashi ba, daya lumshe idanuwansa surar hilwah ce kawai ke masa yawo a idanuwansa, dan hk bema son lumshe idanuwan nasa, . Zaunawa gefen bed din Alhasan yayi zucia fal damuwa ya zubawa AB'ILAL ido wanda idonshi ke kallon saman dakin, se ajiyar zucia kawai yake saukewa. "Frnd wai meke faruwa ne dakai plx?'' Alhasan ya jefowa AB'ILAL tambayar cikin sanyin muryarsa me cike da damuwa.


"Fans kuyita hkri dani plx...."






Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GiclAKDbf2h19M4nZIpDfl
BBM TRUSTED PRE ORDER. Muna yin order na kitchen item, shoes, bag, veils, abayas, bag to school, lace , atamfa .E.T.C
Muna kasuwanci cikin aminci da storon Allah duk wanda yayi business damu inshaallahu zaiji dadi πŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒ.Idan kuma kuna bukatar ayi maku order na wasu kayan wanda kuke bukata duk muna yi.A kaduna nike zaune unguwar rimi zaku iya zuwa gida ko shago ku same ni πŸ˜€πŸ˜€.Domin karin bayani ku tuntube ni a 08068655941 sai na jikuπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒ
08/01/2022 Γ  18:24 - SAADATU BINTU ABDULLAHI: πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯
*YAR DANDI CEH*
πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯πŸ”₯
(SHE'S A WORLDLY PERSON)

SAADATU BINTU ABDULLAHI✍🏽
*Writer of KYAUTAR ALLAH* ga masu bukatar books din marubuciar su tuntubi lmbr nan 08136349646.

πŸ…ΏοΈ13
AB'ILAL yayi banza dashi kmr be jishi ba nan ko yana jinsa kawai tsabar wulakanci ne, sannan bayason hayaniya kwata-kwata, Dan guntun tsuki AB'ILAL yaja,. Alhasan be daddara da reation din AB'ILAL ba ya kara tambayarsa meke damunsa. a matukar hasale hadi da harzuqa AB'ILAL ya tasowa Alhasan "karka dameni kaji na gaya maka, ina ruwanka da abinda ke damuna, nifa munafunci ne banaso, in kasan zaka damenine,,se in tashi in bar maka gidanka, tinda ba gidana bane!" Ya karashe mgnr a mugun hasale still kwayar idonshi na kallon saman rufin dakin irin na zamani,kai kace bada Alhasan yake mgnr ba. Ba karamin batawa Alhasan rai mgnr AB'ILAL ta karshe tayi ba Amma seya jure ya shanye ma ranshi kawai ya tashi ya fice ma a dakin, ya nufa dayan dakin da niyar a can ze kwana sbda yasan yau suka kwana a daki daya da AB'ILAL kwana zasuyi suna fitina iri iri. Nan ma daki ne wanda ya amsa sunansa daki yaji kayan furniture mahaukata irin na bugawa a mujallah, daman idanuwanshi cike suke da bacci dan hk ya yada zango a kan dankareriyar katifar data zagaye gadon, ya lumshe idanuwanshi da niyar yy bacci amma baccin ya gagareshi saboda tunanin halin da AB'ILAL yake ciki childhood friend dinsa, tabbas inda amana baze iya bacci ba. mikewa yayi jiki a sanyaye ya sauko daga kn bed din, ya saka slifas dinsa ya nufo dakin da AB'ILAL yake kwance yadda ya barshi hk ya sameshi still idanuwansa a rufe, duba time yy yaga wuraren 1:am mamaki ya cika masa zuciya , inda normal normal ne da ynzu yana sallarh ko kuma yana bacci zuwa 2:am ya tashi amma yau gashinan ya zama kmr bashi ba, kai kace mutum mutumine, duk yabi ya sukurkuce a ciki lokaci kankani ya zama kmr wani gunki.
Alhasan be daddaraba ya karaso bakin bed din ya zubawa AB'ILAL ido har wata rama yayi a wannan yan awannin, launin idanuwansa suka rikide zuwa kalar ja amma ba jawur ba. "Frnd Dan Allah ka gayamin meke damunka, ka sani a damuwa wlhy..." Alhasan yayi mgnr kai daji kasan da gaske yana cikin damuwa fiye da wadda ma ya fadi da bakinshi. AB'ILAL yayi shiru kawai a wannan karon ma yana jinsa, kansa yayi masa nauyi azabar ciwo kawai yake masa kmr ze fad'o kasa, amma dukda hkn tunanin yarinyar da tsanarta sun gaza barin zuciyarshi. Gabaki daya Alhasan ya shiga damuwa ya karasa ya zauna gefen bed din , kwayar idonshi ta gaza ko kyaftawa daga kan fuskar AB'ILAL wadda ta dan tasa ma se ynzu alhasan din ya kula da hakan, wato fuskarshi ta dan kumbura. "Dan ALLAH ka gaya min meke damunka plx...." Alhasan yayi mgnar still cikin damuwa yake kmr wanda uwasa da ubansa suka amsa kira. Mgnr da alhasan ke masa a saman kai ba karamin kara masa ciwo yakeyi ba, dan HK ya lumshe idanuwansa daya gaza lumshesu tin tini, sbda beso ya hasko surar hilwah, aiko yana lumshe kwayar idon nasa ta fado yanar gizo gizon idanuwamsa a gigice ya bude idanuwansa kmr wanda fatalwa ta masa gizo ya sauke nannauyar ajiyar zuciya ita kanta ajiyar zuciya inze sauketa, to da isah da izzarta take fitowa kai kace shi din sarki ne, danyafi karfin dan sarki. Alhasan ya kai hannu yana kokarin cirewa AB'ILAL hannun daya rufe fuskarshi dashi AB'ILAL ya kwace hannun a razane dan gani yakeyi kmr hilwah ce ta tabashi da hannunta mara tsarki, a razane ya juyo da kwayar idonshi ya kalli alhasan wanda ya firgita saboda yadda AB'ILAL ya razana daya taba masa hannu. Bude baki Alhasan yayi da niyar yayi mgna, AB'ILAL ya dakatar dashi da yatsun hannunsa guda biyu na hannunsa na hagu, a yadda kawai ya dagowa Alhasan yatsun guda biyu yasan beson ya kara mgna ne, kuma inya kara mgnr yasan zasu samu matsala dan haka yaja bakinsa yayi shiru kawai ya miqe ya fada bathroom din dakin ya dauro alwala, ya fito ya isa ga abin sallah ya hau nafifilin nema wa abokinsa sasaucin abinda ke damunsa zuwa ynzu Alhasan ya fara tunanin kila ko jinnun dake kan AB'ILAL ne zasu bayya kansu daman ya jima yana tunanin anya kuwa ba Aljana bace ta Auri AB'ILAL ashe kuwa hakan ne, aljanar ce, tinda gashinan yau zata bayyana kanta, a cewar alhasan daketa jero nafilfili se zancen zuci kawai yakeyi. Daya kai raka'ah biyu yayi sallahma yy addu'ur'insa, kana ya miqe ya nufa inda ab'ilal din yake yaga yadda ya barshi hkn yake har zuwa yanzu ajiyar zucia ya sauke shima ya kasara side drower ya dauki wata wayarshi kirar i phone me kyau ita anyita ne danjin abubuwa, shi kuma Alhasan ya maidata tajin karatun alqyr'ani me girma. Ya kunnata ya saka karatun alqur'ani me girma cikin suratul bakara nan da nan kira'arh ahamad sulaiman ta fara tashi cikin daddad'an sauti muryarsa, ta karade gaf dakin, alhasan ya saita volume din karatun dai-dai kana ya mayar da wayar ya ajiyeta a inda ya dauketa, still tana karatun alqur'anin. Wani irin sanyi AB'ILAL ya faraji yana sauka a duk sassan jikinsa sanadiyar karatun alqur'anin, seda ya lumshe idanuwansa yana me bin karatun a zuciarsa, Alhasan ya juya ya koma kan daddumar yaci gaba da nafilfilinsa zuciarsa cike da tsoro kada de iskar dake kannasa ta tashi sbda karatun alqur'anin dayasa, a tunninshi in iskar dake kan AB'ILAL din ta tashi, ze figeshi ne yayi sama sama dashi ya dakashi da kasa, dan yasan aljanu karfi garesu, dan haka Alhasan daya kai raka'ah biyu yayi sallahma seya juyo ya kalli AB'ILAL seya ganshi yadda ya barshi still kwayar idonshi a rufe take gam. Alhasan seya juya yaci gaba da sallarhshi a hk har asubahi ta shigo dukkaninsu basuyi bacci ba, a bangaren AB'ILAL sam bejin ddn jikinsa ne, ji yakeyi kmr zazzabi ke neman rufesa tunanin yarinyar ne ya haifar masa da hkn, gashi ya gaza dena tunanin nata. Jefi jefi se aikin saukar ajiyar zucia kawai yakeyi kmr dan damben daya ci duka kuma ya fadi wasa. Jin ana kiran sallarh shiga masallaci sallarh asubah yasa Alhasan dakatawa daga nafilfilin da yakeyi yayi addu'ur'i ya shafa ya mike da counter a hannunshi yana istigfari ya nufo inda AB'ILAL ke kwance jiya eyau, daga dukkanin alamu bemasan an kira sallarh asubahin ba, har zuwa lokacin idanuwansa a rufe suke, se aikin sauke ajiyar zuciya kawai yakeyi, kur alhasan ya kureshi da ido nan take ya gano jikinshi na dan kakkarwa alamar zazzabi. "Subhanallahi!'' Cewar Alhasan ya karasa da hannunshi ya shafi goshin AB'ILAL nan take ya jishi ya dauki zafi rau rau, kmr an hura wuta, da hanzari ya kashe AC din dake dakin, ya dawo kan gadon ya zauna gefen gadon hadi da tambayarsa "Zazzabi ne ke damunka kou? Ka tashi ka daure kayi sallah kasha mgni plx...." Ya karashe mgnr muryarsa cike da rauni hadi da dmwa. AB'ILAL ya sauke ajiyar zucia kawai yana sauraron me Alhasan ke cewa, daman shima yanaso ya tashi kodan yayi sallarh asubahi dukda beji kiran sallarh ba amma jikinsa na basa lokacinta ya karato. A hnkli ya yunkura ya tashi zaune hadi da bude kwayar idonshi tar a kan hannayensa dake zaune bisa cinyoyinsa, ji yayi kaf jikinsa ya masa nauyi musammanma kanshi daya ke jinsa kmr ze fado kasa ya tarwatse, idanuwansa suka masa kmr an sa dank'areren dutse, wato sun masa nauyi. Alhasan ya zuba masa ido tabbas akwai abnda ya faru da abokinsa gagarumi, domin kuwa be taba ganinsa a irin wannan yanayinba , ko ciwo yakeyi baka isa ka gane ba sbda tsabar dauriyarsa amma a lokaci kankani duk yabi ya susuce ya rasa gane kansa. "Bari in temaka maka ka tashi frnd..." Yy mgnr yana kokarin temakawa AB'ILAL dake yunkurin tashi tsaye, dakatar dashi AB'ILAL yayi, Alhasan ya dakata hadi da zuba masa ido kawai, ya yunkura ya tashi jiki babu laka , se tangal tangal yakeyi kai kace faduwa zeyi, wanda be sanshi ba se yasha ko ciwo yasha wato kmr yayi jinyar sati biyunnan haka duk yabi ya saki daga jiya zuwa yau. Slifas din alhasan ya saka a hnkli ya fara takawa harya isa bathroom din dakin yayi tsarki, ya dauro alwala ya fito da kyar, a hnkli yake taka kafafuwansa. yana fitowa alhasan ya fada toilet din ba jimawa ya fito shima, bega AB'ILAL a dakin ba hkn ya bashi tabbacin ya fita ne domin zuwa masallaci dukda kuwa besan inda masallacin yake ba amma masallaci baya taba boyuwa. zuwa lokacin an tada raka'arh farko ta sallarh asubahi. Ficewa shima yayi da slifas a kafarshi ya nufa masallacin dake kusa da gidanshi daman basu da nisa da masallacin. Yana shiga yaga mutuminsa a sahun farko , karasawa yayi yabi sahun baya aka ci gaba da sallarh dashi amma ya rasa raka'arh farko dole seda in an idar shi kar yayi sallahma ya tashi ya kawo wadda ya rasa. Suna idar da sallarh ko adduarh beyi ba sbda azabar sanyi da yakeji ya mike yana ganin hanya na haduwar masa biyu biyu uku uku hudu hudu, ya fice a masallacin se ambaton sunayen ALLAH kawai yakeyi, ya koma gidan Alhasan. A bedroom ya yada zango a daddafe ya lullube da bargon dake kan gadon still se rawar sanyi yakeyi, yayinda haqoransa ke hadewa da junansu, sam shi bame yawan yin ciwo bane, zan iya cewa kafin yayi ciwo da woya, dan haka shi da knshi yy mamakin rikicewar jikn nasa. A haka alhasan ya dawo ya samesa dmn Allah Allah ya rinkayi ya idar sbda yazo yaga a wani hali yake ciki. Cikin hanzari ya karaso bakin bed din ya zauna ya zuba masa ido ta cikin bargon still jikinsa se rawa kawai yakeyi sbda tsabar zazzabi, a hnkli Alhasan ya zame bargom daga kansa yana fadin "subhanallahi! Frnd zazzabi ne me zafi halah ya kamaka... Plx ka daure ka tashi muje asibiti dan Allah...." Alhasan ya karashe mgnr a firgice saboda zafin zazzzabin Jikin AB'ILAL daya dakeshi tin kafin ma ya kaiga kai hannunsa jikinsa, da sauri ya maida hannun nasa baya saboda zafin zazzabin jikinsa yayi yawa. AB'ILAL yayi saurin jan bargon inda Alhasan ya yaye masa ya kara lullube kansa yanajin wani irin azababben sanyi, inda ze samu ma a kara masa barguna guda uku so yakeyi, se ynzu AB'ILAL ya fara tunanin anya kuwa hilwah ba Aljana bace ,ko kuma mayya masu lashe ma mutum kurwa, domin kuwa silar ganintane ya haifar masa da wannan mummynan yanayin a jikinsa. Alhasan da duk yabi ya damu best friend ba lafiya se cewa yakeyi "Ka tashi muje asibiti plx...." AB'ILAL yayi bnza dashi domin kuwa bejinma ze iya tashi vitamin A dinsa ya fara sauka. Hnklin Alhasan ya soma tashi domin be saba ganinsa a wannan halinba, gashi yy juyin duniya kan ya tashi su tafi asibiti amma ya masa bnza, karshema alhasan cewa yayi ze temaka masa ya tashin ko ya daukeshi amma ina AB'ILAL yaki amincewa,,jiki bb laka alhasan ya dauko wayarsa domin kiran doctor dinsa doctor Eesha, har yayi dealing number dinta ta shiga ta dauka ma yayi saurin katse wayar, tunawa da yayi da halin mutuminsa, dukda yana cikin Wannan halin amma be zama lallai in yaga doctor mace ba ya yadda ta dubashi. Dole ya chanza akalar kiran zuwa ga kiran abikinsa kuma likitansa doctor kabeer , bugu daya biyu dr kabeer ya dauka. Alhasan ya masa bayani kan cewa yazo gidansa yanada mara lafiya ya dubasa abokinsa ne ba lafiya, zazzabi me zafi,'' ba bata lokaci dr kabeer ya ce Gashi nan zuwa.." Kana ya katse kiran. Alhasan ya ajiye wayar a side drower din ya nufa kiching domin ya hadowa AB'ILAL koda ruwan tea ne ko coffee yasha kafin dr ya karaso, dukda de yasan halin kayansa da wuya yasha din. A gaggauce ya hado masa coffee kawai ya nufo dakin hannunsa riqe da dan karamin plt me dauke da glass cup me mugun kyau da tsaruwa, ya karaso bakin bed din ya zauna hadi da ajiye plt din dake dauke da cup din a gefensa, idonshi na kan AB'ILAL dake cikin bargo har zuwa lokacin jikinsa be bar kakkarwa ba. Nan Alhasan ya shiga lallaminsa kan ya tashi yasha coffe din, Amma AB'ILAL ma yaki tanka masa, kuma idonshi biyu yana jinsa, kawai de beda ra'ayin amsa masa ne kuma beda ra'ayin shan coffee din, se faman lumsar idanuwa yake tayi a cikin bargon ya juya ya koma ya kwanta rubda ciki, yana kara lumshe kwayar idonshi yana budewa a hnkli a hnkli duk sun kara masa nauyi sbda be rintsaba tin jia har zuwa yau, rabonshi da bacci tin shekaran jiya da daddare shima ba wani baccin kirki yayiba sbda ibadar dare da yakeyi. A haka dr kabeer yazo ya sameshi da kayan aikinsa, shi knshi dr kabeer din ya girgiza da ganin yadda zazzabin yy ma AB'ILAL mugun kamu, seda ya tambaya wai kwananshi nawa a wannan yanayin, Alhasan ya shaida masa daga jiya ne zuwa yau kawai. Dr kabeer da idanuwansa ke manne da glass yace "what! Jiya zuwa yau shine yayi laga laga haka?" Ya karashe mgnr da mamaki a ransa, Alhasan ya daga masa kai alamar tabbatarwa. Dr kabeer ya jinjina kai kawai shi da kanshi ya tausayawa AB'ILAL sbda yana jin jiki, "yaci abinci?" Dr kabeer ya tambayi Alhasan, jinjina masa kai Alhasan yy alamar ah'a ya nuna masa inda ya ajiye plt din dake dauke da cup me Coffee din daya hada masa yace "Ga coffee ma na hada masa be sha ba...'' dr kabeer yace "Okay ba damuwa..." Daga hk ya fara kokarin duba ab'ilal ba wani bata lokaci ya duba BP dinsa yaga yy kasa kuma damuwa ce tasa hkn, cikin hnzari ya bashi taimakon gaggawa yasa masa drib byn ya debi jininsa domin yaje ya masa gwaje gwaje, domin kuwa already yazo da komi nasa na bukatuwa, cikin drib din ya narka masa allurorin bacci domin alhasan ya sanar dashi beyi bacci ba jiya. Wasu magunnguna dr kabeer ya rubutawa Alhasan ya bashi yace ya nemo ynxu a ciki a bawa AB'ILAL guda daya in yayi bacci ya tashi. Alhasan yace to jiki na rawa suka fice daga dakin shida dr kabeer din , suka fito compound tare kowa ya hau motarsa suka fice a gidan bayan dr yace ze dawo bada jimawa ba. Direct Alhasan pharmacy ya nufa domin siyan magungunan, driving yakeyi amma tunanin AB'ILAL da halin daya barshi yana ranshi.A gaggauce ya isa dialogue pharmacy a nan ya siya magungunan ya juya ya koma gidansa. Yana yin packing ya fito cikin sassarfa hannunsa riqe da ledar magungunan daya siyo, ya karasa cikin Gidan nasa hannunsa riqe da ledar magungunan daya siyo. Koda ya shigo dakin yana tunanin zega AB'ILAL na bacci, nan fa ya ganshi idonshi tar a bude ya zubowa kofar dakin ido, ba karamin mamaki abin ya bashi ba, sbda an masa alluran bacci, shi ga tunaninsa tini ma yayi nisa a baccin, karasowa yayi bakin bed din ya tsaya tsaye ya zubo masa ido, yana fadin "kayi bacci ne ka tashi frnd? Ko bakayi baccin bane?'' Yayi masa tambayar fuskarshi dauke da mamaki, shuru AB'ILAL yayi ba tare daya ce masa komi ba, alhasan ya zuba masa ido yanada tabbacin be rintsaba sbda ga idanuwansa nan jajur kmr garwashin wuta, a bangaren AB'ILAL kuwa gaza baccin yayi, kwata kwata dukda ga baccin yanaji a idanuwansa amma ya gaza yinsa saboda tunaninta, ya gaza ficewa a kahon zuciyarsa. Rabawa Alhasan yayi ya zauna gefen bed din ta wurin kanshi, har ynzu cike yake da mamaki, ya ajiye ledar hannunsa a side drower ya cire wayarsa a aljihu ya danna wa dr kabeer kira, bugu daya ya daga, nan alhasan ya Roqeshi kan ya dawo da wuri, dr kabeer yace insha Allah nan da 30mnt ze dawo, alhasan yace okay daga hkn sukayi sallahma. Alhasan ya dawo da kwayar idonsa kan AB'ILAL byn ya gama wayar. Ya fara tunanin wani abu ne ke damun AB'ILAL abun ma gagarumi domin kuwa ruwa baya tsami banza, nan da nan Alhasan shima ya kara shiga dmwa. "Frnd Dan Allah meke damunka plx?'' Alhasan yy tambyar muryarsa cike da zaquwar yaji meke damun abokinsa. AB'ILAL ya lumshe idanuwansa kawai ya budesu ba tare daya ce komiba, kwata kwata ko mgna baya so a masa, saboda knshi kamar ze fashe yake jinsa, juyar da fuskarshi yy gefe guda, ji ykeyi kmr ana buga masa kacau kacau a tsakiyar Kansa, har wani dil-dil gefen da kwakwalwarsa take yakeyi masa, dafe kn nashi yayi zucia cike da damuwa, ya rintse idanuwansa. Sannu Alhasan ya bishi dashi domin kuwa ko ba a gaya masa ba yasan yana mugun jin jiki. Maganin da dr yace a bashi Alhasan ya dauko ya shiga kokarin bashi, amma fir Ab'ilal yaki amsa, karshe ma yace baze shaba, alhasan yy juyin duniya amma yakisha, gashi yaki cin komi, se abin ya kara damun Alhasan ya shiga dmwa Ainun, yace "Bari kawai in kira Alhaji babba in gaya masa bka da lafiya, ni ciwon nan naka tsoro yake bani, an baka mgni kaki sha again kaki cin abnci, an maka allurar bacci kakiyin baccin, ko tantama babu wani abu ke damunka a ranka, kwara in kira Auwal hubb, ko Alhaji babba in gaya musu kawai..." Yy mgnr cikin dmwa, idanuwansa na kan AB'ILAL , wanda yy shiru yana sauraronsa, harya dauka ya dire, cikin muryarsa ta marasa lafiar dake jin jiki ya fara mgna "Plx karka kirasu frnd.. , na fara jin sauki..." A hasale Alhasan ya amshe da "Sauki? a ina ? Kaki cin abinci, kakishan ruwa, kaki shan mgni, ta ina zaka samu sauki? Zakace kar in gaya musu? Ah'a kwara in gaya musu gaskia karkazo ka mutum min a gida, ka barni da gwaramar katsinawa da larabawa..." Ya karashe mgnr yana latsa karamar wayarsa dake hannunsa. AB'ILAL ya juyo da fuskarshi garesa ya zuba masa ido, cikin dakiya yace "plx wazaka kira?" Alhasan ya bashi amsa a takaice. "Alhaji babba..." Ab'ilal ya girgiza masa kai cikin karfin hali, yace " karka kirashi pls,..." Alhasan yace "why?" AB'ILAL ya cije lefe kansa na kara masa nauyi, kasa kasa ya fara mgna. "Karka kirashi plx ynzu inka kirashi, hnklinshi ze dawo nan ne, Kaga kuma gobe zeje kano, a kn maganar dawowar Auwal hubb nan garin..." Ya karashe mgnr da kyar, seda alhasan ya matso da Kunnenshi kusa dashi kana ya iya jin me yake ce masa. Jim alhasan yy kana yace "to shikenan, ynzu me kkeso kaci kasha mgni plx, kasan de banason ganinka a wannan yanayin wlhy? Ciwonka kafiya ba wanda ya isa ya saka kayi, a haka zaka samu sauki plx?" AB'ILAL yayi shiru hadi da maida fuskarshi gefe guda kawai, se ganin surar hilwah yakeyi a jikin bangon. "Na tsaneki..'' AB'ILAL ya fadi a bayyane cikin fitar hayyaci,sam be ankare da cewar mgnr da yayi ta fito fili ba, Alhasan dake saurarensa ya zubo masa ido Fuskarshi ta cika da mamaki, hadi da dumbin tambayoyi a zuciarsa , tunani yakeyi shin menene AB'ILAL ya tsana?" Wato kmr de yadda tunaninsa ya basa akwai wata a kasa. "Wacece ka tsana frnd?'' Alhasan Ya jefowa AB'ILAL tambaya. Ajiyar zucia AB'ILAL ya sauke me mugun ddh, yaja gwauron numfashi, yayi jim jim, ya sauke ajiyar zucia ya lumshe idanuwansa. Alhasan ya kara jefo masa tambayar daya masa a baya,cewa wacece ya tsana, shiru AB'ILAL ya masa danshi a zahirin gaskia besanma mgnr tasa ta fito ba. Alhasan yaja bakinshi yayi shiru kawai, yana nazarin rayuwar AB'ILAL daga jiya zuwa yau, kunna krtun alqur'ani yayi, shi har ynzu tunani yakeyi iskokaine. Da kyar ya samu ya lallaba AB'ILAL ya dansha tea kadan shima seda yace ze gayawa Alhaji babba, sannan ya samu yasha dan kadan, wanda ko yaron goye baze isheshi ba, alhasan ya bashi mgnin da dr yace a bashi ya koma ya kwanta ynajin jikinsa kmr ba nasa ba. Alhasan ya jona burner din turaren wuta domin yasan mutumin da mugun son kamshi kmr jinnu, lumshe ido AB'ILAL yayi ba karamin jin ddn kamshin yayi ba, hadda hkn yasa yake Nacewa gidan auwal hubb, a ko da yaushe kamshi yakeyi kmr gidan shuwa arab, koda yake shuwa su biyu bayan indians da larabawa a son kamshi da bakatsinen mutum. Kimtsa dakin Alhasan ya shigayi saboda mutumin uban yan son tsafta ne, karya ne kaga ko tsinke a bedroom dinsa ko bathroom dinsa, shi din yafi mace tsafta da kwaskwas...yana gama kimtsa dakin ya karaso inda gwaskan yaje, yayi masa tayin wanka ko ze karajin dadin jikinsa, banza AB'ILAL ya masa a zucia alhasan yace "uban yan izzah..." Yana gama fadar hkn ya fada bathroom yayi wanka, ya fito ya shirya cikin kananan kaya irin na yan hutu, sun amshi jikinsa Ainun. A hk dr kabeer ya shigo dakin hannunshi riqe da wata kyakyawar jaka me dauke da kyn aiyukansa, tinda ya shigo dakin idonshi ke kan AB'ILAL wanda idonsa ke bude, shima ya zuba masa ido kallo daya biyu ya dauke kwayar idonsa a kn dr kabeer din , karasowa yy cikin dakin bakinsa dauke da sallahma a karo na biyu, Alhasan ya amsa. "abokina har yayi baccin ya tashi ne?" Dr kabeer ya tambaya dai-dai yana karasowa bakin bed din da AB'ILAL ke kwance. Alhasan dake tsaye gaban dressing mirror ya gama fesa perfume kenan,

Please Login or Register in order to submit comment