Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

take salwah na zaune ta gurin knta se faman kuka takeyi tana jijjigata kmr zautacciya haka kawai ta tsinci knta dayin kuka bayan fitar maryam a dakin, kukan da salwah keyi seya kara kid'ima hajiya maryam, ya kasance idanuwanta a bude suke amma kuma sam bata gani dasu Sbda tsabar tsananin kid'imewa, jiki na rawa ta shiga bawa hilwah taikon daya dace, a farko seda ta fara mata allurar dazata farfado da ita daga doguwar sumar da tayi, ta farfad'o amma kuma bata bude idonta ba, numfashinta ya dawo yadda ya kamata, sede batasan inda knta yakeba, hajiya maryam ta mata allurar tsaida jinin daketa aikin zuba a kan nata, duk abinda hajiya maryam kema hilwah zuciarta na maqale da tausanta. Salwah ta koma gefe se sharar kwallah takeyi, duk ta gigice. Duba inda hilwah ta bugu hajiya maryam tayi, nan taga gurin ya fashe sosai har sema an mata dinki gashi kuma gurin akwai gashi, gashin ma ba dan kadanba, dole seda hajiya maryam tasa reza ta aske gashin dake gurin kadan, danta samu damar mata dinkin, seda ta mata allurar kashe zafi kana ta fara mata dinkin, this is the first time data taba jin tausai sosai da sosai da tanawa hilwah dinkin ji takeyi tamkar jikinta take d'inkewa. Bayan ta gama mata dinkin ta kara mata wata allurar a bom-bom ta gyara mara kwanciarta sosai kana ta koma ta zauna kasan carpect din dakin ta zubawa hilwah ido ta rafka uban tagumi hannu biyu biyu, kar kaso ka bincika kasan zuciarta, duk ta daburce gashi ynzu batasan ma ina zata samu number din yan uwan yarinyar ba ta sanar dasu abinda ke faruwa, ta ma rasa ya zatayi.. Salwah data tsagaita da kukanta ta dawo gefen hilwah ta zauna ta zuba mata ido, yayinda farar fuskarta tayi ja jawur sbda tasha wahala, sumar nan tata ta kwanto har zuwa kirjinta, idanuwanta a rufe ajiyar zucia kawai taketa saukewa a kai a kai. Salwah ta dawo da idanuwanta kan mahaifiyarta tana neman karin bayanin meya faru amma tasan bazata samu ba, saboda ta kula ma mahaifiyar tata kmr bata hayyacinta. Suna nan zaune jugum jugum har lokuta suka shude awanni suka tafi, yammaci ta gabato hilwah bata farfad'oba. Mikewa hajiya maryam tayi jiki babu lala ta nufa toilet. ba jimawa ta fito byn ta dauro alwala ta saka hijjabinta nayin sallah ta shimfida dadduma, ta tada sallarh la'asar.... Salwah ma mikewa tayi ta nufa toilet domin dauro alwala , ita duk ta mnta ma batayi sallarba sbda tsabar kidimewa seda taga Amihh na sallah shine ta tuna. Fitowa tayi daga toilet din byn tayi alwalar idanuwanta na kn hilwah ta juya ta fice a dakin ta nufa dakinta danyin Sallar la'asar din, duk tabi ta damu da lamarin hilwah dukda batasan wacece ita ba. Har tayi sallarh ta idar hilwah na ranta, ko hijjabin dake jikinta bata cire ba ta dawo dakin inda ta samu Amihh zaune gefen bed din, zuwa ynzu ta fara firgita da lmrin na har ynzu hilwah bata farfadoba , kuma yaci ace ta farfado bayan awa daya, Amma gashi awanni uku na neman shudewa bata farfadoba. Salwah ta karasa ta zauna a bedside drower ta zubawa hilwah ido,,,dukkaninsu su biyun ita suka zubawa idon... Har lokacin sallarh magrib yazo , suka mike suka gabatar da sallarh magrib din, dukkaninsu hnklinsu na kan hilwah, a cikin sallarh suna aduarh suka rinka mata Allah ya tashi kafadunta. Suna idarwa suka dawo suka kara yin jugum jugum, hajiya maryam se aikin duba agogon dake daure da tsintsiyar hannunta takeyi, karin damuwarta dayace tasan iyayen hilwah suna can suna nemanta ruwah a jallo. A hnkli hilwah ta fara bude kwayar idonta a dai-dai kan fuskar salwah dake zaune a bedside, ji tayi kanta ya dan mata nauyi, nan ta shiga zagaye dakin da kwayar idonta, tana me kokarin tunano abinda ya faru.... Salwah ce ta ankare da farkawar tata kasancewar hajiya maryam ta lula duniar tunani. "Sannu..." Ita ce kalmar data iya fitowa daga bakin salwah, shiru hilwah tayi ba tare data amsaba ta bi salwah da ido. Sannun da Salwah tace ne ya dawo da hajiya maryam duniyar tunanin data afka, ta sauke kwayar idonta a kan Hilwah, ita ma dawo da kwayar idonta tayi kn hajiya maryam din se ynzu ne abnda ya faru ya dawo cikin knta. Nan hajiya maryam ta shiga jerowa hilwah sannu , ji takeyi kmr zata maidata ciki, ita de hilwah se bin hajiya maryam da salwah take da ido, tanajin wani irin sanyi a ranta. "Me ke miki ciwo yanzu?'' Hajiya maryam tayi tambaya hilwah cike da kula kwayar idonta na kanta, tana zaune gefen bed din. "Kaina...." hilwah ta fadi cikin sanyin murya, hajiya maryam ta matso ta kamo hannunta cikin nata kana tace "ze bari,,sannu knji baki ganin jiri?'' Hilwah ta daga mata kai hadi da cewa "Ina gani kadan kadan..." Hajiya maryam ta kara damqe hannunta cikin nata tanajin wani irin sanyi a ranta kasancewar hannunta dake cikin nata. "Sbda jinin da kika zubar ne....sorry knji , ngde da abinda kikayi min Allah ya jibanceki da lamarinki sbda annabi s.a.w..." Duk suma suka amshe da s.a.w. wani irin murmushi hilwah ta sakarwa Hajiya maryam, ita ma ta sakar mata murmushin. Salwah de ta zuba musu ido bata taba ganin annashuwa a kn fuskar Amihh ba tinda take da ita se yau, annashuwar data gani a tattare da itan me fidda annuri ce, tanaso tasan meyasa amihh ke ma hilwah godiya. "Me kikeso kici?'' Hajiya maryam ta tambayi hilwah har zuwa lokacin hannunta na cikin nata duka biyu. Girgiza kai hilwah tayi alamar bazataci komi ba. Hajiya Maryam ta dansha mur tace. "Se kinci fa...." Tayi mgnr hadi da mikewa da niyar ta fice a dakin, hartakai bakin kofar fita ta juyo ta kalli hilwah wadda itama, kwayar idonta ke kan hajiya maryam. "Ya sunanki ?'' Hajiya maryam tayi tambahar. "Hilwah..." ta bawa hajiya maryam amsar tambayarta tana lumsar idanuwa. Maimaita sunan nata hajiya maryam tayi a bayya ne. Salwah kuma ta maimaita a kasan ranta ba karamin dadih sunan ya mataba. Juyawa hajiya maryam tayi ta fice a dakin, salwah ta zubawa hilwah ido se sannu taketa mata, hilwah ta daga mata kai hadi da sakar mata dan guntun murmushi, salwah ta mayar mata da kayataccen murmushin itama kana tace "Sunanki dadih .." Hilwah ta kara sakar ma salwah murmushin gefen baki tace "thank you...ke ya sunanki..." "Sunana Salwah.." Ta bata amsa cike da jin dadin mgnrta harta. Salwah harta fahimci hilwah nada karyayyen harshe mgnrta seka natsu zaka ganeta sosai. "Rabin sunana..." Cewar hilwah, salwah ta kara kureta da ido, yanzu ta kara fahimtar hilwah bata da R da S kwata kwata a bakinta. "ni da ke duk munada rabi rabin suna, ke hilwah ni kuma salwah..." Cewar salwah da farin ciki ya cika mata zuciya hk kawai takejin dadin mgnr hilwah, Dan haka ta hau janta da hira sama sama, wai a hk ma dan tana tausanta ne bata da lafia da lafiarta lau seta dameta da surutu sosai, sbda tanaso tayi ta jin muryarta me dadin nan. A hk hajiya maryam ta dawo dakin ta samesu hannunta dauke da trea.l, se taji dadin yadda tazo ta samesu suna hirar hkn ya bata tabbacin jiki yayi sauki. Krsowa Hajiya maryam tayi ta zauna gefen bed din ta ajiye trea din dake hannunta a kasa ta bude kular dake dauke da superghetti wadda taji kayan lambu da bushashshen kifi da nama da danyan kifin ma duka. ta zuba mata a plt Me kyau, da knta ta dagota ta jingina mata bayanta da fuskar bed din.. ta shiga bata jlp din superghetti din a bakinta, ta amsa zucia cike da farin ciki, seta tuna mahaifiyarta ita ke bata abinci safe rana da daddare a baki, sam batasan cin abinci da kntaba seda ya zamana ta baro gidan iyayenta, shine ta iya kai lomar abinci bakinta. Tsaf hajiya maryam tayi feeling dinta taci sosai ta koshi gashi bata taba cin abinci me dadinshi ba. Ta bata drinks din strawberry Wanda ta hada da hannunta, tasha taji wani irin ddh. Mikewa hajiya maryam tayi ta fice a dakin, ba jimawa ta dawo hannunta riqe da magunguna ta bawa hilwah tasha, ta koma ta kwanta tanajin damar jikin nata. Salwah se aikin sakarwa hilwah murmushi takeyi, itama tana mayar mata da adashen murmushin. "Ina ne gidanku? Se inje in sanar da mahaifiyarki halin da kike ciki, tazo ta ganki, nan da kwana biyu hk se ki koma gida...." Cewar hajiya maryam da tayi mgnr cikin natsuwa. Hilwah dake sauraronta ta lumshe ido, a ranta tace nida bnda gidan iyaye me zance?'' Shiru tayi ba tare da tace komi ba. Hajiya maryam ta zuba mata ido tana nazartarta yayinda hannunta ke kan kafafuwanta. "Ko gidan naku da nisa ne?" Hajiya maryam ta kara tambaya idonta na kn hilwah. A wannan karom Hilwah karayin shiru tayi, salwah ta zuba ma hilwah ido, hk hajiya maryam ma idon ta zuba mata, mamaki ya rufeta ta fara tunanin ko de basu da gida ne, ko bata da iyaye ne, to in bata da iyaye a gun wa take zaune?'' Ta tambayi knta, ta bawa knta amsa da oho. "Iyayenki zasu damu da rashin ganinki , gashi ba waya a hannunki balle a kirasu a sanar dasu?" Cewar hajiya maryam data gaza hkri hk kawai ta tsinci knta dason tasan wacece yarinyar su waye iyayenta. "Wayana na motana..."_ cewar hilwah. Se ynzu hajiya maryam ta tuna data amshi car key da ATM card a hannunta sadda zasu sata a mota. Mikewa tayi tana fadin bari insa a dauko miki motar taki, ai riskine a barta a can..." Ta karashe mgnr tana ficewa a dakin, ta nufa compound nan ta samu dan ustaz a baranda a kan dadduma yanata nafilfili zuwa lokacin anyi sallarh isha'i shine daya dawo daga masallacin ya dasa da nafilfili, yayi sallama nema yana zaune se Aikin zubo addu'ur'i yakeyi, gidan fayau haske kamar rana. hajiya maryam ta karaso inda yake ta tsaya, yana ganinta ya shafa addu'arhsa ya mike tsaye yana fadin, "Hajjaju mutanen makka, wato nace Ainifin ya jikin ita me tarar aradu?'' Hajiya maryam ta hade rai ta kula shi besanma ba ason abu ba, kai kace ma zigashi akeyi. "Bana ce maka banason rashin kamun kai ba wai.." Cewar hajiya maryam da tayi mgnr babu alamar wasa a tattare da ita. Da hanzari dan ustaz ya kai hannayensa duka biyu ya dafe kansa wanda keta faman shining yace "latagadab!" Wato kada tayi fushi. Girgiza kai kawai hajiya maryam tayi, tace yaje cikin motar dasuka fita da ita dazu, zega atm card da key din motar. Dan ustaz yace toh ya juya a guje ya nufa packing space se waqar larabawa yakeyi.. hajiya maryam ta koma cikin gidan ba jimawa ta dawo hannunta riqe da yan dari biyar biyar sababbi guda goma, ta mikawa dan ustaz dake tsaye hannunshi riqe da Atm card din da mukullin motar, ya mikawa hajiya maryam ta amshi ATm din kawai, kana tace yaje ya dauko motar hilwah a sidi And song, ta bashi 5k din dake hannunta tace ya hau abin hawa, dan ustaz ya amshe yanata godia ya fice a gidan, se kara kirga 5k din yakeyi ya mnta yaushe rabonshi dayaga 5k a rayuwarshi. Juyowa hajiya maryam tayi ta dawo cikin gidan. Direct dakinta ta shigo nan ta samu salwah a zaune a gefen bed din, Hilwah kuma tana kan dadduma tanata jero sallarh la'asar da magrib da isha'i, seda ta watsa ruwan dumi salwah ta bata kaya ta canza kana tayi sallah. hajiya maryam ta zuba mata ido, kana ta juya ta fice a dakin ta nufa kicking dan kara sama mata abinda zata karaci kafin tasha mgninta na dare. Ita sam bata tunanin knta dukda kuwa tanajin yunwa. Jlp din Cuscus ta hada mata irin na larabawa wanda rabinshi duk ganyayyaki ne, a ranta se kokwanto takeyi anya ma hilwab zata iya cin cuscus din.... Dawowa dakin tayi hannunta riqe da trea a tsaye ta samu hilwah salwah ma na tsayen,... "Amihh wai hilwah zata tafi gida...." Salwah ta tareta da mgnr, hajiya maryam ta karaso cikin hanzari tana fadin "gida kuma? Wani irin gida!? Haba yatah.. Koma ki zauna plx..." Ta karashe mgnr kwayar idonta na kn hilwah, wadda ta tsaya ita wai so takeyi ta tafi gida, komawa tayi ta zauna gefen bed din har zuwa ynzu jiri take gani. Hajiya maryam ta ajiye trea din dake hannunta a kasan dakin, ta zauna gefen bed din kusa da ita cikin sanyin murya ta fara mgna "Yarinyata gida zakije,? Why plx? baki gama warkewa ba fa, ta yaya zakije gida, ki bani address din gidanku knji se inje in snr dasu halin da kk ciki ... amma ke bazan iya barinki ki tafi gida ba gaskia, se an kwana biyu naga yanayin jikin naki..." Hilwah tayi shiru kunnuwanta na sauraron daddad'an kalaman hajiya maryam. "Kin hakura zuwa gobe kou?'' Hajiya maryam tayi mgnr da sigar rarrashi, hilwah ta daga mata kai kawai. Murmushi hajiya maryam tayi, tana kokarin zuba Cuscus din a plt dan Ustaz ya hau doko sallahma a falon , hajiya maryam tace salwah taje, ba bata lokaci salwah ta mike ta fice a dakin... Hajiya maryam taci gaba da zuwa cuscus din a plt din, hilwah ta zubawa cuscus din ido, irin wanda mahaifiyarta ke dafa mata, tana sonshi sosai, dan haka duk ta kagu ta fara ci. Ba bata lokaci hajiya maryam ta fara feeding hilwah,..abinda ya bata mamaki shine ganin yadda hilwah Kecin cuscus din cike da kwarewa kai dagani kasan ba yau ta fara ciba, tabbas akwai tambayoyi cike da zuciar hajiya maryam amma ba damar yi sbda batason ta takura mata ganin halin da take ciki. Salwah ce ta dawo dakin ta bawa Amihh car key din Hilwah da dan ustaz ya bata tana fadin "gashi inji dan ustaz wai ya dauko motar ..'' Hajiya maryam tasa hannu ta amsa tace okay, ta ajiye drower din bedside. Ta ci gaba da bawa hilwah cuscus din. Salwah ta zauna gefen gadon itama, ta zubawa mahaifiyarta ido Mamaki fal ranta na yadda amihh keta tarairayar hilwah,... Amihh ta gama bata cuscus din ta bata magungunan dare ta sha, ta mike ta nufa bathroom ta hada mata ruwan dumi tace tayi wanka, ba musu hilwah ta shiga bathroom din tayi wankan ta fito kirjinta daure da bathrobe, Amihh da salwah suka zubo mata ido, tabbas ALLAH yayi halitta. Kallo daya biyu Hajiya maryam tama hilwah ta dauke kwayar idonta a knta tana me wani irin tunani a ranta, tabbas tanason wannan irin na hilwah. Hajiya maryam ta temaka mata ta shirya cikin kayan bacci sabbi kalar purple riga da wando ne, masu kyau da laushi. Hilwah taga tarairaya sosai se bin Hajiya maryam takeyi da ido, tana jinta a rnta kmr mahaifiyarta kwantawa hilwah tayi tanajin jikinta ya mata dadih sosai sbda wankan da tayi Amihh se sannu taketa jero mata....dan Ustaz ne ya kara sallahma da karfi a tsakiyar falon, salwah ta tashi ta fice a dakin ta nufa falon, Dan ustaz ta gani a tsakiyar falon hannunshi riqe da hand bag din Amihh da phone dinta. "Sannu hajiya karama,..wato ainifin hajiya karama kar de kiga kamar na dameki ne... Ga wannan jakar ta hajiya ce mutanen makka da wayarta se kira akeyi,..." Salwah tasa hannu ta amsa, haka kawai ta tsinci knta dason tambayar dan ustaz meya faru dazu. Tana tambayarsa kuwa kmr yana jira ya kwashe lbrin komi ya sanar da salwah shiru tayi, tayi jim tana me karajin soyayyar hilwah a rantan lallai dole Amihh tayita nan nan da ita ashe ta ceci rayuwarta ne. Salwah ta koma dakin zucia fal kaunar Hilwah. Ta samu Amihh na lullubeta da duvet tana mata adduarh, nanma seda kn salwah ya kara daurewa. Karasawa tayi ta mikawa Amihh bag din da phone dinta data kara daukar wani sabon ringing din. Seda ta gama ma hilwah adduarh kana ta dago ta amshi wayar da bag din zuciarta cike da mamaki, ita fa tama mnta dasu tadesan dasuka fadi da hilwah duka abubuwan dake hannunta seda suka zube, tashama tayi missn dinsu har abadan., kila shine dan ustaz ya gani ya dauko mata. Duba screen din wayar tayi yayinda kiran ma tini ya jima da katsewa nan ta budeta a luck taga number din hajiya Juwairriyya ne. Kallon salwah dake tsaye tayi tace "ki kwana da ita..." Salwah tace toh amihh ta juyo ta kalli hilwah kana ta fice a dakin, tana dealing number din hajiya juwairiyya. Hilwah tabi bayan Amihh da ido taso ace su kwana tare, salwah ta shige bathroom danyin wanka ta fito kirjinta daure da bathrobe Ta kai idanuwanta ga hilwah, wadda zuwa lokacin baccima ya dauketa cikin magungunan da Amihh ta bata akwai mesa baccu. Ficewa salwah tayi a dakin ta nufa bed room dinta ta shirya cikin kayan bacci kana ta fito ta nufa kiching dan samawa knta abinda zataci.

Karasawa Amihh tayi cikin daya daga cikin dakunan gidan ta yada zango a gefen bed din dake mamaye da dakin, wanda ya hadu harma ya gaji da haduwa. still wayar na kunnenta, inda take kiran lmbr hajiya juwairiyya har ta kusan katsewa kana hajiya Juwairriyya ta amsa kiran cikin tsananin tashin hnkli ko sallamah batayi ba ta fara mgna da muryarta ta tashin hnkli "hajiya maryam meke faruwa ne?'' Dazu koda wayar ta fadi daga hannun hajiya maryam bata mutuba yawancin hayaniyar da akayi a gurin duk hajiya juwairiyya ta jiyo meke faruwa, sede bazata iya tantance meneneba, seda dan ustaz ya dauki wayar shine ya katse kiran ta dena jiyo komi, tin a lokacin taketa neman number din ta gaza samu se after mgnrib shine number din ya fara shiga iyakar tashin hnkli hajiya Juwairriyya ta shiga yau. Jin yadda hajiya Juwairriyya tayi mgnr ya tabbatrwa da maryam ta shiga tashin hnkli, nan de hajiya maryam ta kwashe labarin abinda ya faru A to Z ta shaidawa hajiya juwairiyya nan take hajiyar ta hau sauke ajiyar zucia kamar wadda tayi tsere. "Ynzu ya jikin ita yarinyar?'' Itace kalmar data fito daga bakin Juwairriyya Hajiya maryam ta amsa da "Da sauki hajiya.... Kinga yarinyar kuwa masha ALLAH me kyau ga hnkli..." Murmushi me fidda sauti hajiya maryam tayi tace ''Hmmm,,,kede hajiya? Ki raba kanki wlhy...." Hajiya maryam itama murmushin tayi tace "To ynzu me nace hajiya..." Hajiya Juwairriyya tayi yar daria tace "Ai bnso ma ki ce pls..." Murmushi kawai hajiya maryam tayi tace "Hmm...hajiya Juwairriyya ina muka kwana da mgnr Auren alhaji..." Hajiya Juwairriyya tayi yar Dariya, "an fasa ne?'' Hajiya maryam ta tambaya cikin zaquwa . Hajiya Juwairriyya ta karayin Murmushi me sauti kana tace "kede bari Maryam, mazan nan namu se a hnkli, su de basu da abin kunya...wai ashe sbda ya siyomin mgnin mata ne bnsha ba shine yazo jiya ya firgitani da mgnr ze karo Aure, shi nan fa ganina yakeyi ban tsufa ba shi de insha mgnin mata insa kananan kaya shine abinda yakeso, beso yana ganina cikin kayanmu na gargajiya ni kam naga Ai na tsufa hajiya me zanwa ado a nan?'' Hajiya maryam ta kwashe da dariya "kai Alhajinki ko se a hnkli..amma ai gaskia ya fada hajiya inkin tsufa ai shi be gani, sannan can din Ai baya tsufa... " hajiya maryam ta karashe mgnr still tana Dariya. Hajiya Juwairriyya tace "Rabani da mazan nan inka biyesu se suja mka abin kunya su kuma basu da abin kunya sam a dunia wlhy..." Hajiya maryam ta juya akalar dariarta zuwa Murmushi me sauti. "Hajiya kenan, to meye a ciki dan kinsha mgnin mata kinsa English wears, mijinki nefa..." Hajiya Juwairriyya tayi yar daria irin tasu ta mnya tace "Rabani da mgnr nan hajiya..." Hajiya maryam tace "au baza kisha ba ki tsuke,,, abinda maza sukeso kwara a musu dan a zauna lafia..." Hajiya Juwairriyya tace "shikenan zanyi insha ALLAH..." Daga hk sukayi sallahma. Kwanan hilwah biyu a gidan ta matsa kan seta bar gidan kwata kwata batajin ddn rayuwarta sbda ba charger dazata jonawa knta, ga tsuliya nata zubda ruwah duk bayan mintoci se tayi wanka gudun kada a dagota gashi a koda yaushe hajiya maryam na kusa da ita hk ita ma salwah bata koma gidan hajiya karama ba sbda a week dinnan bata da lecture a school. Badan hajiya maryam taso ba ta bar hilwah zata tafi gida, ta hada mata sha tara na arziki hilwah taki amsa dole Amihh ta matsa mata kan dole ta amsa ta mata godia. Tana sanye da doguwar riga abaya me kyau kalar green dark tasha flowers peach masu dan karen walwali, abinka da farin mutum seya amsheta Ainu. Amihh ce ta bata jallabiyoyi kusan kala goma sabbi hadda kayan indians masu kyau, arabians perfume's da Indians perfume's. Har bakin car amihh da salwah suka rako hilwah, hajiya Maryam taso tabi hilwah gidansu amma hilwah taki amincewa da hakan, ta hau mata kwana kwana, dole Hajiya maryam ta hakura tace to dan Ustaz yayi driving dinta zuwa gidansu, nanma taki tace zata iya driving knta hkn da tayi se tasawa hajiya maryam kwad'ayin son sanin abinda take boye mata, tanada tabbacin hilwah na boye mata wani abu. Salwah dake riqe da dan karamin akwati blue me kyau a nan amihh tasawa hilwah kyaututtukan data bata, akwatin dan madaidaicine medium size, bude gidan baya salwah tayi ta saka akwatin , sannan ta amshi wata yar jaka me kyau a hannun hajiya maryam itama dauke take da tarkacen ado, ta sakasu duk a bayan motar hilwah, kana ta mayar da murfin motar ta rufe. Hilwah na tsaye tana kallon Ainihin zallar karamci. Hajiya maryam da knta ta bude ma hilwah handle din dreva seat ta shiga ta zauna Ta dago kwayar idonta ta saukewa hajiya maryam cikin harshen larabci tayima hajiya maryam godiya. Jiya ta jita tana waya da larabci a nan ta gano balarabia ce, ko kuma de ta jibance larabawa. hajiya Maryam ta bi hilwah da ido jin tana larabci daji kuma ta kware a larabcin sbda yafi amsar harshenta, daga mata kai kawai hajiya maryam tayi baki sake ta gaza mgna. Salwah dake gefe tayi kicin kicin da fuska kmr zatayi kuka batason tafiyar hilwah a kwana biyun nan sun saba sosai, sun shaqu da junansu sosai sam salwah batason ta matsa daga inda hilwah take a kwanaki biyun sbda tanada kyakyawar dabi'arh. "Tafiya zakiyi ki barni ko me rabin suna?'' Salwah ta fadi muryarta cike da shagwaba. Hilwah ta sakar mata murmushi tace "Am sorry plx me rabin suna zan dawo nan da 2 days..." Salwah ta fasa ihun murna tace "yaushe plx?'' Hilwah tace "Nan da 2 days insha ALLAH..." Murna ta kara rufe salwah tace ALLAH ya kaimu. Hajiya maryam ta zuba musu ido kawai. Hilwah taja murfin motar ta rufe jiki babu laka ita knta batason barin Gidan Amma bazata jure ba rashin chargin kai ga tsuliya na motsi. Tada motar tayi ta dannewa zuciarta tana satar kallon Amihh ta fice da motar tata daga gidan. Amihh ta bi byn motar tata da ido, ta kalli Dan ustaz dake tsaye ya zuba musu ido shifa son hilwah yakeyi dande beda yadda zeyi ne, inji bahaushe yace bakin rijiya ba gurin wasan yaro bane. Get man na kokarin maida kofar get

Please Login or Register in order to submit comment