Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Kara kasa tayi da knta tana shashshekar kuka kmr zata hadiye zucia ta mutu. "Bakiga komi ba..." Ya fadi cikin muryarsa dake cike da tsanarta, sam ko alamar tausanta bejiba, dukda kukan datakeyi kmr ranta ze fita, sema haushinta daya karaji. "Daga yau ke zaki rinka kaf Aiyukan dake gidannan, zan dakatar da ma"aikatan side dinnan , kece zaki rinka komi kama daga kn gyaran sama zuwa gyaran nan kasan, da wankin kayayyakina, da gyara dakin baccina, ke komi ke zaki rinka yi, kuma bnson kazanta dannan ba gidan karuwai bane!" AB'ILAL ya fadi babu alamar jin kanta a muryarsa, sema dumbin haushinta da tsanarta. Ajiyar zucia ta sauke yayinda kalamansa ke shigarta tako ina, ta rintse idonta ta bude dan gani takeyi kmr mafarki takeyi ba gaske bane zata fada wannan mummunar rayuwar, wani irin zazzabi me zafi taji ya kara rufeta na tsantsar damuwa da tunani me zurfi. AB'ILAL ya daka mata tsawa "Ko bakiji bane!?" Tsawar tasa seda ra gigitata har hkn yajawo ta zabura, ita dako hayania bataso, Gashi yanzu har tsawa ake mata, me karfi wadda in yayita se hantar cikinta ta kad'a sbda gigita. "Badake nake mgna ba! Yar iska kawai karuwah!'' Ya karashe da murya cike da tsanarta da bazata misaltuba a fili. Saurin daga masa Kai tayi, zuciarta cike da daci da zafin karuwah da yake kiranta dashi, ko yar iska daya ce bata mata zafi ba kmr kalmar karuwa daya kirata dashi. Wata iriyar kwafa yaja kawai zucia babu dadih shi da knshi yasan tsanar da yayiwa yarinyar tayi yawa, ci gaba yy da mgna murya cike da matsifa "Ashe ba kurma bace! Nasha iskncin gidan karuwai ya kurmantan dake yar iska kawai!'' Ya karashe mgnr ko a jikinsa se binta yakeyi da kallon kyama, ya juya da niyar ze fice a dakin har ya kai bakin kofar fita ya juyo ya kalleta Cikin tsana ya nunota da yatsa. "Ammm..bari in kara jaddada miki karki sake ki kuskura kiyi amfani da koda cokali a side dinnan, in zaki kwanta ki kwanta a kasan tiles shima da sassafe in kikatashi ki gogemin tile's dina ni bnson kazanta, nan ba gidan yan iska da kazamai bane...bade knce kin Aminta da Aure naba wlhy kadan kk fara gani, se knyi nadamar rayuwarkima baki daya! Kuma daga yau zaki fara aiyukan dana lissafa miki! " Yana gama fadar hkn ya fice a dakin yana haki ya nufa bedroom dinsa.... nan kasan dakin ta zauna zaman dirshan kawai ta kara fashewa da matsanancin kuka me tsuma zuciar me sauraro, kalamansa kawai keta aikin yawo a brain dinta, tayi kuka tayi kuka, ta tuna uwarta mahaifiyya duk a yau, kuma tayi nadamar zuwanta ma gidan dan tasan zata tsinta abinda batayi tsammani ba, gashinanma ta fara tsinta tin yanzu, zamanta gidan dandi yafi mata nan gidan sau dubu. Har akayi sallarh La'asar aka idar tana nan kasan tiles din tanata aikin kukan babu kakkautawa,,da kyar ta bawa knta hkri da knta sbda bame bata ta mike da kyar yayin da takejin knta ya kara mata nauyi kawai ta fada toilet tana dafe bngo, tayi tsarki ta dauro alwala ta dawo dakin ta fara jero sallarh azahar da la'asar, tana sallarh tana tunani tunani, se ynzu takeji a ranta anya ba barin gidansu datayi bane ALLAH ke nuna mata ishara a yanzu , duk da bataga isharaba se ynzu ne take gani, kalaman mahaifinta keta dawowa kwakwalwar knta, tana wannan yanayin amihh ta turo kofar dakin ta shigo dawowarta kenan daga aiki ko side dinta bataje ba ta nufo side din AB'ILAL dan taga hilwah. "Oh my sweery i miss you..."_ itace kalmar data fito daga bakin Hajiya maryam ta karaso inda hilwah take zaune bisa dadduma ta zuba mata ido yayinda knta ke kasa, tin shigowar Amihh ta kalleta kallo daya ta dauke knta tayi hanzarin goge hawayen dake kn fuskarta. ganin Amihhn da hilwah tayi seya sama ma wani bangare na zuciarta kwanciar hnkli, hadi da sassaucin dmwarta. "Sannu da zuwa Amihh. " ita ce Kalmar data fito daga bakinta har lokacin knta na kasa, tayi controlling knta zuwa kmr bata cikin dmwa. Hajiya maryam ta zuba mata ido tana me naxarin muryarta, nan take ta fahimci tayi kuka sbda har muryarta ta dishe. "Yauwa sweery narh...plx dago min face dnki in gani kuka kikayi koh?'' Hilwah ta girgiza mata kai ba tare data dago kn nata ba, ta riga datama knta alqawarin insha ALLAH koda AB'ILAL ze kasheta ne bazata taba gayawa Amihh ba sbda karamcinta gareta kuma bataso tayi silar batawarta da danta. "Oya to dago min beauty face dnki in gani mana?'' Cewar Amihh. Hilwah ta dago knta a hnkli sbda batason jayayya da Amihh,. Hajiya maryam ta zubawa red face din tata ido. "Sweetheart kinyi kuka ne sosai ma kou?" Hilwah tayi saurin girgiza mata kai hadi dayin kasa da knta. Hajiya maryam tace "ban yadda ba, knyi kuka ne zaki girgiza min Kai, bansanki da karyaba ko wani abu wancan dan neman ya miki? Ki gayamin knji my love, karkimin hiding komi plx knsan ina sonki fiye da yadda nakeson yar ciki na kou?'' Hilwah ta daga mata kai domin kuwa ta aminta da amihh na sonta fiye da yadda takeson salwah, inma be fi ba to zexo diro diro, ballan tana ma tanada tabbacin yafi din kmr yadda ta fada din yau da bakinta. Amihh taci gaba da mgna fuska dauke da damuwa "To gayamin why are you Crying? Wayasa bbyn Amihh kuka?" Hilwah tayi shiru kawai tana me kara kasa da knta, hajiya maryam taci gaba da mgna " Ko de ba babyna bace ba?'' Hilwah tayi saurin grgiza mata kai, Amihh tace ''to yau ba bakin mgna ne?'' Hilwah tace "Akwai..." Cikin sanyin murya tayi mgnr amihh tayi murmushi harga wajen ubangiji tana kaunar yarinyarnan. "To tinda akwai baki gayamin meyasa bbyn Amihh kuka?'' Hilwah tace "ciwon Kaine..." Amihh tayi jim tana nazarin abinda hilwah tace da muryarta irin ta wadanda sukaci kuka suka koshi. "Ba ciwon Kai bane, kukan ne. kukan ne ma ya jawo ciwon kan...na cinka Kou?'' Amihh ta karashe mgnr tana zama nan kasa kasa kusa da hilwah ta jawota jikinta duk kunya ta rufeta na yadda Amihh ta gano cewa kukan datayi ne yasa mata ciwon kai. Rungumeta Amihh tayi jikinta, nan take taji jikinta yayi wani irin mugun zafi, daji zazzabi ne a jikinta, nan da nan Amihh ta gigice, "Kn gani kou zazzabi kkeyi kou? Kukannan da kkyi ne ya kawo miki zazzabi..kinci abinci?'' Hilwah ta daga mata kai alamar Ehh, Amihh tace "tin yaushe?'' Hilwah tace "tin kafin salwah ta fita tazo ta hadamin tea and egg, ta bani mgnin zazzabin ai..." Amihh ta kara shafo jikinta tajishi zafi rau rau, murya cike da tausayawa tace "sorry my love, tashi ki hau bed in hado miki abinci kici in miki allura kou?'' Nan take jikin Hilwah ya hau kakkarwa jin Amihh ta ambaci allura, abinda tafi tsoro kenan ba a taba mata ba tin zuwanta dunia har rana me kmr ta yau. Amihh ta ankare da hkn tayi Murmushi tace "kina tsoron Allura ne?'' Hilwah tayi saurin daga mata kai, Amihh ta riqe baki tace "to wannan rnr haihuwa yazakiyi?'' Hilwah tayi shiru kawai tana me kara lafewa jikin Amihh, har lokacin zuciarta bata bar bugu ba dajin sunan allura. "Kwantar da hnklinki anma fasa allurar...tashi ki hau bed inje in hado miki abinda zakici kisha mgni kou?'' Jin amihh ta ambaci ta tashi ta hau bed yasata tunanowa da irin uban warning din da AB'ILAL ya mata, nan take taji a ranta ko zata mutu bazata kara hawa bed din ba, yau kawai ya dasa mata tsoronshi a ranta, amma fa har gobe bata bar tunaninsa ba.amihh ta tashi ta kamota da niyar tasata ta hau kn bed din hilwah taki tacema Amihh nan din yafi mata, tayi mgbr hadi da karasawa kn carpet ta kwanta. ba tare da Amihh tayi tunanin wani abu ba tace ok tana zuwa ta fice ta bar dakin, tana fita hilwah ta daure ta tashi ta dauro alwala a daddafe ta dawo ta hau dadduma ta fara jero sallar azahar da la'asar, tanajin knta na sarawa yayinda kalaman AB'ILAL keta mata yawo a kwakwalwar knta. Amihh Ta na fitowa falon sukayi kicibus dai-dai ya fito daga bedroom dinsa yana sanye da jallabiya peach color me mugun kyau, shima yana mugun son peach dande color din na mata ne. Ido ya zuba mata itama ta zuba masa nata kwayar idon. "Ina wuni Amihh.." Ya gaisheta cikin ladabi yana kokarin Karasowa inda take tsaye duk iskncinsa yana respecting dinta sbda yasan beda kowa a halin yanzu inba ita ba. Ba tare data amsa gaisuwar tasa ba ta kalleshi ta basar, se jikinsa ya basa ko de yarinyar ta sanar da Amihh irin abubuwan daya gaya mata ne, daya shiga bedroom dinta, dan hk seyasha jikin jikinsa, Ya karaso ya rissina mata, cikinb ladabi Ya kara gaisheta taki amsawa sema ta jefo masa tambaya"Meyasa yarinyar nan kuka?'' Ita ce kalmar data fito daga bakin Amihh, yayinda tadawo da kwayar idonta a knsa, kasa yy da knsa, dayake bashi da kunya yace "kmrya Amihh, ni meye nawa a kukanta, ko wani abun tace na mata?'' Amihh ta girgiza kai kana Tace "nasani abu a duhu..ai dayake nasan halinka, ba mutumci ne dakai ba, inma ka mata Ai ba fadi zatayi ba, tinda ita tanada tarbia alkunya , ba fadar mugun halinka zatayi ba gareta,.." AB'ILAL ya dago ya tabe baki jin Amihh ta ambaci tarbia wai hilwah ce me tarbia, gani yakeyi kmr Amihh batasanma me take fadaba. Ciki rashin kunya ya fara mgna "Gaskia ni Amihh, dande ba yadda zanyi ne, amma abinda kikeyimin ya isheni a kn yarinyarnan, wlhy bna kaunarta Amihh, daza kice in sawaqe mata daya fi min Alheri..." Amihh tayi murmushi irin Murmushin nan me taken yaro besan wuta ba seya taka, ta fara mgna cikin natsuwwa amma fa me mugun zafi. "You are free Muhammad, ka saketa in har kai ka haihu da ruwan katsinawa ka saketa, inajin kana ganin turirin wuta ne, Amma bakasan zafin ta ba, zanso ka gwada kai hannunka kaji yaya yanayin zafinta yake, a ranar zakayi nadamar zuwanka dunia, a lokacin nadamarka bnza take gareni, abinda zucia da ruhinka ke ingizaka ka aikatasu wlhy ni na maka alqawari ubangiji baya bacci se kayi nadamar abinda ka aikata a lokacin da nadamar ka bata da amfani... I wish ka kuskureni nima kuma zan kuskureka da mummunan abinda ke raina, garin kaduna zuwa katsina da kewayenta ta mna kadan ni da Kai Muhammad!'' Ta karashe mgnr tana nunasa da yatsa kawai ta juya ta fice a falon, isa yayi ga kujerar dake kusa dashi ya zauna, kalaman Amihh sun masa nauyi a kai gashi de cikin natsuwa tayisu amma sun shegeshi da gangar jikinsa, Wai a hk ma danya kula yarinyar bata gayawa Amihh irin abinda ya mata dazu ba, abin ya masa dadih, duk wannan abubuwan da Amihh ke masa a knta ze huce, ita ma se na lahira yafita jin dadin dunia, kadanma ta gani!" Ya fadi hkn a ransa yana me murmushin mugunta a bayyane se faman aikin girgiza kafa yakeyi... Yana nan zaune bisa kujerar yana dafe da knsa Amihh ta dawo falon hannunta riqe da trea tinda ya juyo ya kalleta ya dauke knsa, ita kam ko kallon inda yake batayi ba, yana gani ta nufa bedroom din hilwah da trea din a hannunsa wanda yakeda tabbacin abinci ne a ciki, zuciarsa ta cika da mamakin irin bautar da Amihh kewa yarinyar , ko su yayan cikinta bata musu hkn koda kuwa suma ciwo ne, nan AB'ILAL ya kara nitso cikin duniar tunani ko a nan kawai yanada tabbacin amihh na son yarinyar nan fiye da tunaninsa, kashh!!, se aka samu akasin shi be kaunarta fiye da tunanin me karatu.

A kn daddumar Amihh ta sameta data idar da sallarh seta koma ta kwanta, a hk Amihh tazo ta sameta. da knta ta tasota zuwa toilet ta kara mata brush suka dawo dakin ta jawota jikinta a hk tayi feeding dinta da superghetti Jlp wadda taji kayan lambu da kifi bushshe da namah, ta danci ba lefi, sbda Amihh ta matsa mata, a karshe ta bata magunguna na zazzabi dade wanda zesa taji dadih a jikinta. Hilwah ta mata godia yana daya daga cikin abubuwan dakesa Amihh karason hilwah komi aka mata seta nuna halin Katsina wa dukda ita ba bakatsiniar bace, wato karamci, bakatsinen mutum be manta alheri, kuma akwai raya alheri da alheri. Komawa hilwah tayi ta kwanta kan daddumar ta kudind'ine da hijjabin jikinta , Amihh tayi juyin dunia kn ta hau bed, hilwah taki hawa ta kara ce mata nan yafi mata ddh, nanko ta ciki na ciki bata da yadda zatayi ne kawai amma ita ason samunta ne ta koma kn bed din sam bata saba da kwancia a kasa ba, ballantana ma ynzu datakejin jikinta duk babu dadih kawai tana manage ne. Badan Amihh taso ba ta batta nan kasan sbda ta kula hkn takeso ta lullubeta da duvet din gadon data gnshi a kasa inda AB'ILAL ya wurgardashi, amihh ta mata sannu kana ta juya ta fice a dakin ta nufa side dinta da trea din a hannunta, dazata wuce falon ko kallon inda yake bata kara yiba tayi ficewarta. Amihh na ficewa ta cire duvet din data lulllube mata jikinta dashi ta jefashi can kasa kusa da bed din, zuciarta cike da tunanin warning din AB'ILAL gareta, sam bata mantaba, tasan har abadan bazata taba mantawa ba, domin ita akwaita da riqon Abubuwan Alheri dana sharri.

Amihh na ficewa a falon ya taso ya isa yayima falon key luck , ya koma ya zauba bisa kushin din daya tashi ya daura kafarsa daya kan daya yanata aikin karkadata kmr dan sarki, jefi jefi seya juya ya kalli kofar dakin yarinyar jira yakeyi yaga fitowarta dan Aiwatar da aiyukan daya bata, amma yaji shiru har kusan mintuna talatin suka shude, mikewa yayi rai a matukar bace, ya nufa bedroom din nata, ya turo kofa ya shigo yana haki, idanuwansa suka sauka a knta tana kwance kan daddumar duk tabi ta kara kudindine knta a cikin hijjabin dake jikinta, idonta biyu sam bata ko rintsesu ba sbda tunanukan dake ranta bata tunanin zasu batta ta rintsa, yana shigowa dakin taji gabanta ya yanke yayi wani irin MUMMUNAR faduwa, seda takai hannu ta dafe kirjinta tana me jin zuciarta kmr zata fashe. Wani irin mugun kallo AB'ILAL yabita dashi wadda yafi na dazu zafi, kallo daya ta masa ta dauke knta tin shigowarsa sbda tsoro da firgicinsa daya dasa mata su ranta. "Ubanwa ya baki izinin kwancia a kn daddumar nan? Damar yin sallah kke dashi a knta itama sallar bana tunanin kinayi dan hk karki kara kunsantar inda aka tanada dan sallah kinajina kou!?'' Ya karshe mgnr hadi da daka mata tsawarsa me firgitata, nan da nan ko ta firgice bugun zuciarta ya karu, ji kkeyi fat! Fat ! Fat! Sbda kawai zallar tsoronshi dake ranta, hkn ke firgitar sa zuciarta. A matukar hasale ya iso daf da ita kmr ze takata yaci gaba da mgna muryarsa cikin matsifa da jaraba "Ina mgna dake still kina kwance, Zaki tashi ko sena Kai ciki duka, in karairayaki, in karairaya banza da hofi!'' Ya karashe mgnr cikin tartsatsi babu alamar wasa a tattare da muryarsa dashi dinma baki daya, daji tasan ze aikata abinda ya fadi. Mikewa tayi jiki na rawa tana me jin wani zazzabin yana neman kara rufeta bacin na dazu daya sauka sbda mgnin da Amihh ta bata, ynzu ga wani sabo ya bayyana sbda firgicin daya haddasa mata, kasancewar bata saba da wannan yanayin ba. Kallon tsana yaci gaba da binta tashi, yayin datayi saurin sauka daga gun sallarh ta dawo kn tiles din ta rakube gu daya , kuka takeso tayi amma hawayenta sunki zuwa, duk tabi ta takure gu daya. Ko kadan AB'ILAL beji tausantaba sema tsanarta daya karaji ta bayyanar masa. "Ke bazaki tashi ba ! ki fito ki fara aikinki ba ko sena shiga jikinki, sannan zaki fi gane yaren nawa! Yar iska kawai!'' Yayi mgnr tasa cikin tsawa, se ynzu hilwah ta tuna da aiyukan daya lissafo mata kuma yace ta farasu yau, gashi bata da lafia, jiki balle ta zucia, jiki babu laka ta fara kokarin mikewa tana ganin jiri a idanuwanta, ta wuceshi tana kokarin barin dakin taje ta fara aiwatar da abubuwan daya satan. Taba kokarin bude handle din dakin ya daka mata tawa, cikin tsana da kiyayya. " ke karuwah!'' Hilwah ta rintse kwayar idonta hadi da jingina bayanta da kofar dakin sbda jirin dataji yana neman kwasarta na zafin kalamarsa wato karuwah dayake kiranta dashi!, wlhy tanajin zafi fiye da tunanin zuciar me imani da mara imanin ma baki daya. Ci gaba yayi da mgna kwayar idonsa na knta, sam baya bari ya kalleta sosai, sede sama sama, sbda tsabar tsananin kiyayyar da yaje mata kuma yau gashi a inuwa daya dashi da karuwah ta gidan karuwai ma. "bari in gaya miki wani abu daya! Ki bude kunnenki kiji ni nan Bana mgn biyu a rayuwata! So ke baki isa ki sani ba in fara a knki ,wlhy daga rana me kmr ta yau na miki mgna daya bakizo kin aiwar da abinda nasaki ba se na lahira ya fiki jin dadih! Stupid!'' Ya karashe kmr ze karasa ya watsa mata mari, jin ya gama mgnrsa ya sata daga masa kai kawai zucia bb ddh ta fice a dakin ganin yana da niyar kmr ze mareta, ta fice da sauri ta nufa saman upstairs din side din nasa, matakala daya ta taka taji ta gaji ta tsaya ta huta tana me ganin jiri, a hk a hk da kyar da kyar harta samu ta gama hayewa, ta iso babban falon dake saman, taganshi tsaf tsaf ba alamar ko da tsinke a kasa, ta nufa aikin zagaye bedrooms din dake saman, duk ta gansu tsaf sbda ba a taba shigarsu ba, duk da kyar take komi, ta dauki tsintsiya ta shiga aikin share falon dukda taga babu ko da tsinke, amma tayi sbda cika umarninsa, tana cikin sharar ya hayo saman upstairs din dan ganin wani iskncin take masa ya riga yayima knsa alqawarin uzzura mata koda ta halin qaqane. Tsayawa yayi ya harde hannusav a kirji ya zuba mata ido, ba tare data dago ta kalleshi ba taci gaba da sharar da hannun hagu Kai dagani kasan bata saba da ko da riqe tsinin tsinken tsintsiyaba balle ta iya sharar. Kallon takaici AB'ILAL ya bita dashi a zucia yace ashe bata iya komi ba sede ta bude kafa ta bawa maza wawakeken gindinta suci su bar bnza inda yake. Daka mata tsawa yayi "a gidan karuwan haka ake shara!!!'' Tsabar firgici da tsoro batasan sadda ta wurgar da tsintsiyar Dake hannunta ba ta mike tsaye jiki na rawa, sbda mgnr tasa. "Baza ki ci gaba ba sena kusa karyaki! yau ko zaki mutu sekin gyara ko ina a gidannan, yanzu ma kk fara ganin whlar rayuwa bade kn yadda an hadaki dani ba, to tabbas ni ne naqasar rayuwarki!'' Ya karashe mgnr ko gezau beji ba a ransa na girman kalmar daya gaya mata. Dago kwayar idonta tayi ta zuba masa, kawai se taji hawaye takai hannu ta share ta tsugunna ta dauki tsintsiyar taci gaba da sharar tana haki, daman ga jiki bb ddh ga zazzabi ga rashin sabo da whla, gashi tanayi yana daga nan yana daka mata tsawar dake gigita mata lissafi. A whlce ta gama share falon, suka nufa daya daga bedrooms din, inda yake tsaf tsaf amma seda ya hargitsashi yace kuma ta gyarashi dole, nan ta hau aikin gyarashi tana haki wani tayi dai-dai wani tayi mistake ya daka mata tsawar dake hargitsa mata lissafi, dole ma ta gyarashi yadda yake sbda tsurewa, koda ta gama gyara dakin ana kiran magrib, a gurguje ya karasa ya b'ata dukkanin sauran dakunan kana ya sauka kasa, domin zuwa masallacin sallarh magrib byn ya buga mata warning kn kada ta yadda ya dawo ya sameta bata gama gyara ko ina ba a gidan. Barinaikin tayi ta nifa toilet tayi alwala tayi sallah a gurguje ta idar, ta koma dayan dakin ta fara gyaransa tanayi tana hutawa, har de ta gama da kyar be dawo ba, ta koma dayan dakin tana cikin gyaransa ya dawo bayan anyi sallarh isha'i harma ya jima a masallacin ya dawo ya ga bata gama ba, aiko nan ya rufeta da balbalin bala'i da matsifa kmr ze daketa, a wannan Karon hkri ta rinka basa amma ina ai kace zugashi akeyi, se kara dagewa yakeyi yana mata tijara dacin zarafi, da hk har suka gama da gyara nan saman tayi mopping lokacin ana neman 10:30am ne, a matukar gajiye take ga matsifarsa ga tijararsa ga uban aikin, wai a hk ma danba datti da ace da datti batasanma yazatayi ba, sam ita bata saba whlr nan ba, yau ce rana ta farko data taba aiki a rayuwarta tin zuwanta dunia, ko tsinke bata taba kaudawa ba se yau, aiko ta whla zakasha ko ita tayi gaf aikin dunia. Yasata gaba suka dawo nan kasan, seda ya hargitsashi sosai kana yace ta gyara, a gajiye ta shiga gyara falon, hatta da kujeru seda yace ta matsar ta share falon, ai duk tijararsa seda ya batta, sbda bazata iya ba, a yadda y fahimta ko ledar pure water akace ta dauka da wuya ta iya dauka, tanayi tana ganin jiri harta gama kimtsa nan falon, suka nufa bedrooms nanma seda ya yamutsasu kana yace ta gyara komi a mazauninsa, ta shiga aikin gyaran tanayi tana haki, harta gama gyara dakuna ukun, suka koma dakinsa nanma tsaf yake amma seda ya hargitsashi yasata gyarashi tana gyarawa yana cewa be masa ba, seya taso mata da matsifa, rnr fa tsaye suka kwana sbda azabar fada da matsifarsa, se 4:30am ta gama gyaran ko ina har kicking da store seda ta gyara, Kana ya barta ta nufa bedroom dinta nan ta tadda trea me dauke da kulolin abinci, nan take zuciarta ta bata Amihh ce ta kawo mata ko salwah, ilai kuwa salwah ce tazo ta ajiye mata Amihh ta aikota tin 7;am taga bata gnta ba se tayi tsammanin ko tana bedroom din AB'ILAL ne, amma kuma batasan meya kaita bedroom din nasa ba, da wannan tunanin ta bar side din koda ta isa seta gayawa Amihh ta kai kawai bata tambayeta komi ba ita ma bata gaya mata kominba. Tana karasowa dakin ta zube kasan tiles tana sauke ajiyar zucia a matukar whlce har numfashin ya ya chnza zuwa na whla, kwanci kawai tayi tanajin wata iriyar matacciyar whla a tattare da duk sassan jikinta, rintse idanuwanta tayi bayan ta kwnta rub da ciki, se ynzu ta tuna batayi isha'i ba ta yunkura zata mike amma ta Gaza mikewa kawai ta koma ta kwanta tanaji ana kiran asubahi amma ta gaza tashi tayi sallarh bayanta ya riqe ya k'age se faman aikin mata ciwo yakeyi infect ma tanajinsa kmr ba nata ba, ba bata lokaci baccin whla yazo ya sureta ya tafi da ita garin whla daman da whlar ya sameta a tattare da ita dan hka

Please Login or Register in order to submit comment