Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hadasun zasufi shakuwa. Hajiya maryam taji ddhn hkan, sede tana zullumi kan kada gogan yayita zalintar hilwah, hakade tace bari tayi kasada in taga da zalinci seta dawo da ita side dinta. Ba tare datayi shawara da hilwah ba balle AB'ILAL, ta kira masu gyara gida, daga companyn turawa tasa aka canza kaf kayayyakin furniture din Side din AB'ILAL hatta da tsarin komi seda aka canza. da TV seda aka chanza aka zuba azababbu masu azabar kudi da kyau. Ranar Gogan benan ya fita zuwa office dinsa dake nan kd, zesa hannu a wata takadda daza a kaita zuwa kasar American, a can uban gidansa yake. be dawo gida da wuri ba,har seda yaga tafiyar takaddar kana ya dawo gidan 9:3pm, ya shigo falonshi a gajiye, se faman jan tsuki yakeyi, inda ace a kano ne bazeyi whlr nan ba. da yayi ba yau....tunaninshi ya tsaya cak yayin daya shiga karewa falon kallo yana me shakar kamshin dadin dake falon, Nan take ya fahimci an canza komi ne na falon, yasan Aikin Amihh ne, to meyasa tasa aka chnza masa kaya bayan shi bece a canza masa ba....yana nan tsaye yana wannan tunanin Amihh tayi sallahma ta shigo falon, ya amsa hadi da juyawa ya zuba ma AMIHH ido , tana gama shigowa falon hilwah ma ta shigo sanye da riga iya guiwa mara nauyi, sede fa ta amsheta ainun, komi ya fito ya bayyana real Aini, kallo daya AB'ILAL ya mata ya dauke knsa daga knta nan take yaji duk wani sauran annuri dake kn fuskarshi ya gushi. "Amihh meyasa aka chnza min furniture din falo?'' AB'ILAL yayi mgnr da Hajiya Maryam murya cike da jaraba. Ba tare da Amihh tabi ta knsa ba, ta karasa ta zauna kan kujerar 3ct. hilwah ta tsaya cak knta na kasa, se aikin sharar kwallah takeyi tinda Amihh tace mata zata dawo side din take kuka har ynzu amma kukan nata besa amihh fasa abinda tayi niya ba, shine ynzu ta taso ta gaba dataji shigowar AB'ILAL gidan, can suka bar salwah a falo itama tana kuka, sam bataso komawar hilwah side din AB'ILAL ba. "Taho nan ki zauna...."cewar Amihh datayi mgnr da hilwah tana me nuna mata kusa da ita, hilwah ta gaza motsi tanaji gabanta nata tsananta bugu.. AB'ILAL dake tsaye Yanaji kamar zuciarsa zata fashe dan takaicin ganin hilwah a side dinsa me tsarki. Dadin dadawa kuma yaji amihh tace wai ta zauna masa a kn kujera, cikin sanyin jiki yaga hilwah na kokarin karasawa ta zauna kmr yadda Amihh ta umarceta, ranshi ya harzuka cikin tsawa yace "Karki kuskura ki zauna min a kan kujera! Nan ba gidan karuwai bane!" ya fadi a matukar harzuke. Nan take hilwah taja ta tsaya tana mejin hantar cikinta na kad'awa jikinta ya hau kakkarwa ta gigice sbda tsawar daya mata ta firgitata Ainun, zata iya cewa tinda uwarta ta haifeta ba a taba mata irintaba, nan take hawayen dake kn fuskarta suka kara yawaitar gudu, hadda shashsheka.




*Ya Allahu ka yadda na sauke nauyin jama'arh lafia😍.....*
08/01/2022 à 18:24 - SAADATU BINTU ABDULLAHI: 30***
Amihh dake zaune ta zuba ma AB'ILAL ido, tana mejin zafin kalamansa ji takeyi kmr ta tashi ta rufeshi da duka sbda takaicin zafin ya kira hilwah karuwah, idanuwanta takai ga hilwah wadda keta kuka, hkn se ya karawa Amihh zafi a ranta harma ta gaza mgna sbda takai karshen bacin rai. "Get out of my side pls! Banason ganin marasa tsarki '' AB'ILAL ya dakawa hilwah tsawa, cikin tsanah, da kiyayyah , ko ganinta besonyi a side dinsa, ko yace ma a duniarshi. Jiki na rawa Hilwah ta juya tana kuka da niyar tabar falon Amihh tace "karki sake ki fita a falon nan, tinda shima kasar bata ubanshi bace!'' Amihh ta fadi cikin kunar zucia, mgnr tata ta karawa Ab'ilal takaici, da kunar rai. hilwah taja ta tsaya ba tare data juyo ba se faman sharar kwallah kawai takeyi, tana shashsheka. Yayinda shashshekar tata ke kara batawa Amihh rai, dawo da dubanta tayi kn AB'ILAL daketa faman huci kmr ze fashe. "Idan ka kara kiran yarinyarnan da karuwa Allah ya isa tsakanina dakai!'' Amihh ta fadi cikin matsifa murya babu alamar wasa, sbda tsabar takaici har idanuwanta sun kankance, matsifa na cinta. Jin kalaman Amihh AB'ILAL yayi kmr saukar aradu a cikin zuciarsa, wai yau a kn wata karuwah ne uwarsa ke masa ALLAH ya isa. "Amihh ni kikayi ma Allah ya isa?'' AB'ILAL ya maimaita zuciarsa cike da tsanar hilwah. Hajiya Maryam ta daura kafa kan daya irin na tijarar nan, ta kankance idanuwanta ta fara mgna tana numfashi sbda jaraba, ji takeyi a ranta AB'ILAL be taba bata Mata rai ba irin na yau, ashe duk iskncin baqsnta matan, daya rinkayi a baya ne. "Nan gaba tsine maka zanyi kuma duk a kan Dan hakin daka raina din!" Ab'ilal ya zaro ido zucia na kuna yana me maimajta kalaman amihh a zuciarsa Takaicinsa daya daya zamana sbda karuwah mara tushe Amihh ke neman tsine masa albarka, nan ya dankare a tsaye. Hilwah se aikin shashshekar kuka kawai takeyi zucia bb ddh, bata tabajin zafin kalami ba kmr yadda taji zafin kalamin AB'ILAL gareta a yau, tabbas ya bar tarihi a rayuwarta , kalmar karuwa daya jefeta dashi ita tafi komi bata mata rai ita ta sata kuka, ji takeyi kmr zuciarta zata fashe. Amihh taci gaba da mgna a harzuqe"Idan har bazaka zauna lafia da yarinyarnanba, nidakai bazamu zauna lafia ba har abadan! In kanaso kasan wacece ni dan ubanka kayi abinda kaga dama ga yarinyarnan! Baka sanni bane, bakasan wacece niba, se in har ka kuskureni a kan yarinyarnan a nan ne zaka gane wacece ni! Gatanan ta dawo nan side din naka har Abadan, dan ALLAH Muhammad ka kwad'ata ka cinye! Kaga in zaman nigeria zeyu gareka!'' Amihh na gama fadar hkn ta mike ta fice a falon cikin zafin zucia. Ajiyar zucia ya sauke rai babu dadih, ya zubawa bayan hilwah ido, wadda ke tsaye har lokacin kmr mutum mutumi, kallonta yakeyi amma tsanarta na yawaita a zuciarshi. kwata kwata hilwah bata yima Ab'ilal ba, se ynzu yake kara tabbatar da cewa ita din karuwa ce, duba da yanayin kayan jikinta, riga iya guiwa se mayafi data yane knta dashi, wai a hk ne take yawoh kuma Amihh na gani Amma a hk ace me Tarbiya ce, kuma wai matarsa, shi bega ma abinda yaja hnklin Amihh ba gareta ta makala masa ita, in tarbia ce bega alamar taba a tattare da yarinyar, dauke kwayar idonshi yayi a kn jikinta dmn ba itan yake kallo ba, tsinanniyar rigar dake jikinta yake kallo, tsanarta ta kara yawaita a zuciarsa, juyawa yayi jiki babu laka zucia na juyayi, yayinda sbda bacin rai ko ganin gabansa ba yayi sosai...a hk har ya isa bedroom dinsa, a kn tamfatsetsen bed dinsa ya kwanta, yana me dafe knsa dake masa wani irin azababben ciwo, harga Allah yasan Amihh ta shiga hakkinsa , ta hadashi da abinda ranshi beso, Ta shiga hakkinsa ta kuma ta shiga hakkinsa, abin dunia ya hadu ya masa yawa, Gashi beda katafus tinda yaji mgnr tsinuwa jikinsa ya kara masa sanyi! Can cikin zuciarsa da ransa da jinin jikinsa ji yakeyi kmr ze maceh, zuciarsa se kuna takeyi yayinda yaketa maimaita kalaman Amihh a ransa wai wai yau shi take ikirarin zata tsine mawa a kn tsintacciyar mage, mara tsarki wadda ta rayu a cikin sab'on ubangiji! Takaici ya rufesa! Inside ji yakeyi kmr ya hadiye zucia ya mutu, ko ya samu sassaucin bala'in dake ransa.

Tanajin sadda ya bar falon har lokacin se hawaye takeyi tana shashsheka. Nan kasan tiles din falon ta zube ta fashe da wani matsanancin kukan da batasan dalilin dayata yinsa ba, ji takeyi kmr ranta ze fita, kukan takeyi hadda majina tasan de halin da take ciki beci ace tana wannan kukan ba kmr ranar fitar ranta, zata iya cewa bata tabayin kuka me cin zucia ba kmr na yau. Nan kasan tiles din dakin ta kwana tana kwallah sam bata rintsaba, ga sanyin kasan tiles din na ratsata ga sanyin AC amma sam hkn be dametaba... Kmr yadda ta kwana bata rintsaba hk ya kwana be rintsaba, kwana yy yana nafilfili, da asubahi ya fice zuwa masallaci ya gnta kwance a kn tiles din falon amma be bi ta knta ba ya fice a falon, zucia babu dadih, Da ace yanada yadda zeyi ya bar ganin yarinyarnan da yayi, ko ya samu farin cikinsa ya dawo rayuwarsa.. Tanaji yazo ya fice a falon, yana fita ta tashi zaune da kyar kmr me ciki zucia babu ddh, yayinda takejin knta ya mata mugun nauyi Kmr ze fashe, a daddafe ta iya tashi tsaye, idanuwanta sun kumbure, fuskarta fara sol seda tayi ja jawur, ji tayi jikinta ya mata nauyi sbda sanyin data kwasa a kasan tiles din falon. Da dafe bango ta karasa cikin dakin daya zama mallakinta, komi nata nan amihh tasa aka kawo mata, dakin ya hadu iya haduwa, bathroom ta fada ta hada ruwan dumi tayi wanka a,daddafe ta fito tayi alwala kana ta dawo dakin, tanajin jikinta ya mata dama dama sede dan zazzabi datakeji a jikinta, shiryawa tayi cikin doguwar riga irin ta yan hutu mara nauyi, tasa hijjabi ta nufa inda aka tanada danyin sallah, ta tada sallarh asubahi, ta idar ta jima tana lazimi da addu'ur'inta, bayan ta shafa nan kasan daddumar ta silale tanajin zazzabi na neman kamata sosai, rintse idonta tayi tana tunano kalmar da AB'ILAL ya jefeta dashi Na karuwah! Taji wani siririn hawaye na zirarowa daga kwayar idonta, se aikim sauke ajiyar zucia takeyi na kwanan da tayi tana kuka,,,tana nan kwance baccin whla yazo ya tafi da ita, baccin takeyi amma kuma bame dadih ba, again kuma ga zazzabi na nukurkusarta, se kudindine jikinta takeyi da hijjabin jikinta, datayi sallarh dashi bata cire ba.


koda ya dawo daga masallacin be gntaba, ya nufa bedroom dinsa ya kwanta yana juyi, a ranshi yana kissima irin cin ubantan dazeyi ta yadda da knta zatace ma Amihh batason zama da shi, karshe Amihh tace ya saketa shima ya huta, wannan shawarar da zuciarsa ta basa tayi masa ddh , se kulla irin muguntar dazetayi mata kawai yakeyi a ranshi da hk bacci me nauyi ya daukesa sbda jia be rintsaba.

7:pm Amihh ta bar gidan, taso ta biya side din Ab'ilal taga Hilwah se taga yayi sassafe da yawa, hk ta fice a gidan zuciarta fal tunanin ko a wani hali hilwah take, jiya ma bata rintsaba sbda barinta datayi tana kuka, tsakar dare taji kmr taje ta dawo da ita side dinta sede ta daurewa ranta kawai, amma badan taso ba, ita knta tasan AB'ILAL ze whlr da yarinyarnan, amma bazata barshi ba hkn tama knta alqawari.

11:am salwah ta shirya zuwa scul kasancewawr tana da lecture 11:30am, fitowa tayi harabar gidan ta nufa side din AB'ILAL domin taga hilwah harga ALLAH bata iya barin gidan inhar bata ganta ba sbda kewarta bata wani rintsa ba sosai. Taba handle din falon tayi tajita a bude tinda ya dawo daga sallarh asubahihi ya mnta be rufe kofar ba, Turowa tayi ta shigo salaf salaf kmr munafuka, ta maida kofar falon ta rufe, ta shiga karewa falon kallo, bataga kowa hkn ya bata tabbacin duk suna bedroom dinsu, direct hnyar bedroom din hilwah ta nufa tana me adduarh Allah yasa kadasu hadu da yayah AB'ILAL. A hnkli take tafia kmr munafuka har ta isa bakin kofar bedroom din hilwah, da ita aka gyara komi a gidan shiyasa tasan bedroom din nata. Tura kofar tayi ta shigo bakinta dauke da sallahma, a kwance ta gnta a kasan dakin har zuwa ynzu bata ko motsa ba, ta takure ta kudindine a cikin hijjabin dake jikinta dagani salwah tasan sanyi takeji sbda yadda ta takure a cikin hijjabin jikinta, kuma ga sanyin AC karasawa tayi ta kashe AC dake dakin kana ta iso inda hilwah ke kwance, ta tsugunna ta ajiye hand bag din dake hannunta, ta kai hannu kan fuskarta dake a bude taji jikinta da zafi sosai, saurin dauke hannunta tayi daga jikin nata tana fadin . "innalillahi! Dea zazzabi kikeyi?'' Mgnr da tayi ya farkar da ita daga baccin whlar da takeyi daman bata da nauyin bacci sam, a hnkli ta bude kwayar idonta a kn fuskar salwah, nan da nan taji farin ciki ya rufeta, da tunaninta ta kwana a ranta. "I miss you salwah...'' Itace kalmar data fito daga bakinta cikin karfin hali. Nan take tausanta ya mamaye zuciar salwah tace "I miss you 2 me rabin suna ..zazzabi ne ke damunki kou?'' Salwah ta karashe mgnr hadi da kai hannu kn fuskarta ta kara tabawa taji zafi rau rau fiye da fari ma data tabatan, janye hannunta ta karayi zucia fal tausanta tace "knsha mgni?'' Hilwah ta girgiza mata kai, Salwah tace "Ai kamar ma bakiyi breakfast ba kou ?" Hilwah ta daga mata kai kawai cikin dakiya. Salwah ta zuba mata ido, se ynzu ta ankare fuskarta a kumbure take kuma tayi ja, seta dan firgita ita ga zatonta ko yah AB'ILAL ne ya mata wani abu. "Fuskarki ta kumbura why?'' Salwah ta tambayi hilwah. "Bkm..." Shine abinda ya fito daga bakin Hilwah. Salwah tace "Ba wani, ko de Yayah ab'ilal ya miki wani abu ne plx ki gayamin bazan gayawa kowa ba..." Hilwah ta girgiza mata kai, tana murmushin karfin hali. "Bakison zaman nan side din kou?'' Salwah ta kara tambayar hilwah zucia babu ddh. Shiru Hilwah tayi a wannan karan bata bata amsaba. Salwah taci gaba da mgna "Zan gayawa Amihh kawai ki dawo side dinmu Kou?'' Hilwah ta girgiza mata kai, salwah tace "Why? A nan waze rinka dafa miki abinci, kuma in baki lafia waze baki mgni?'' Hilwah ta nunawa salwah knta da hannu ba tare data ce komi ba, salwah tayi narai narai da kwayar ido, kmr zatayi kuka. Ta mike kawai ta ajiye bag dinta ta cire hijjabin dake jikinta ta fice a dakin ta nufa kiching, komi akwai a kiching din, ruwan zafi ta daura a kn gas na Lipton tasa kayan kamshi, kana ta dawo ta soya kwai guda biyu tasa kifin gwangwani, ta gama ta hado mata tea me kauri da kwan ta hada a trea ta nufa bedroom dinta, nan ta sameta inda ta batta, ajiye trea din tayi, ta karasa ta taimaka mata ta tashi tana me ganin jiri, Salwah ta kamata suka nufa toilet nan ma ta taimaka mata tayi brush , ta wanke fuskarta kna suka dawo dakin, ta tasata gaba tasha tea da kwan data soya nata kadan shima seda ta daure taci kadan, Salwah Ta bude bag dinta akwai magunguna na zazzabi hk dana ciwon ciki,, ta bawa hilwah mgnin zazzabin tasha ta koma ta kwanta a kn tamfatsetsen bed din dake dakin, salwah ta lullubeta, hilwah ta bita da ido, ta dauki trea din ta fice dashi zuwa kiching din duk abinda takeyi a hnkli takeyi inside kuma se adduarh takeyi Allah sa kada yah AB'ILAL ya fito ya gnta ita ko ganinsa tayi firgitata yakeyi. Bayan ta gama wanke kwanonin data bata ta ajiyesu a ma'ajinsu ta dawo dakin, har lokacin hilwah idonta biyu. Karasawa Salwah tayi ta taba jikinta taji zazzabin nata ma ya fara sauka. "Sannu love, zan kira Amihh in gaya mata baki lafia.. " hilwah ta girgiza mata kai alamar ah'a. Salwah ta turo baki tace "sena gaya din, maybe in ita tazo ki gaya mata daliln kumburin fuskarki inma yah AB'ILAL ne ya miki wani abun, zata masa mgna.." Hilwah tace "ah'a plx karki gaya mata..." Salwah tace "to sekin gayamin meyasa fuskarki da idanuwanki suka kumbura ko knyi kuka ne?'' Hilwah ta daga mata kai alamar Eh. Salwah tace "to meyasaki kuka? Yah AB'ILAL ne ya dakeki kou?'' Hilwah tayi saurin girgiza mata kai kana tace "kewarku ce tasani kuka..." Ta fadi da muryarta me ddh, da sarkaqiyya, 'karyayyen harshenta na nan har ynzu. Zucia cike da tausai Salwah tace "to zan gayawa Amihh ki dawo side dinmu, nima nyi missn dinki jiya bnyi bacci me ddh ba...plx dea karki fita falo, sbda karku hadu da yah AB'ILAL knji, kiyi zamanki bedroom enki plx?' Hilwah ta daga mata kai kawai zucia fall kaunar salwah. Taci gaba da mgna "Kiyi zamanki a nan bedroom plx yah AB'ILAL Matsifa gareshi, kuma bnso ya miki, inkika zauna a bedroom dinki knga baze gnki ba balle ya miki matsifa har zuwa ki dawo side din Amihh muci gaba da zamanmu Kou?'' Hilwah ta daga mata kai alamar Eh, karasawa tayi ta manna mata deep deep kiss a goshi ta mata sallahma tasa hijjabinta ta dauki hand bag dinta ta nufa kofar fita hilwah Tace mata ''thank you darling..." Salwah ta juyo ta sakar mata Murmushi tace "Kinfi hkn...bye tace care of ur safe, kiyi bacci plx..." Hilwah ta daga mata Kai Alamar to, tana gani Salwah ta fice a dakin, ta batta da kewarta ta, rintse kwayar idonta tayi tanajin zuciarta na beating da karfi da karfi tabbas tasan tana cikin jarabawar ubangijinta Alhamdulillahi! Shine abinda ya fito daga bakinta, yayinda hawaye masu zafi suka shiga bin kuncinta, nan ta shiga aikin tunanin farkon rayuwarta har zuwa ynzu, datake kwance bisa kn gadon, a fari tasan dadin dunia babu wanda bataji ba, amma sam dadin be jima ba ta fara tsintar knta a jarabawa, ta shiga hadarirrika da dama kuma ta haye tana fatan taci gaba da hayewa dunia da kiyamarta, da wannan tunani tunanin bacci me karfi ya dauketa a wannan karon bacci me ddh takeyi zucia cike da jin dadin karamcin salwah da Amihh gareta, tana jinsu a rayuwarta kmr jini da hantarta.


A bangaren Alhajin ALLAH wato goganku be farka a baccinba se wajajen sallarh azahar ya tashi yayi wanka yayi alwala ya fice a gidan sanye da jallabia se zuba kamshi yakeyi ya nufa masallaci dai-dai ana kokarin tada axahar,...dasuka idar da sallarh seda ya jima yana maraji'arh alqur'ani me girma kana yayi addua'ur'insa ya shafa. Da counter dinsa a hannunsa yana lazimi ya fice a masallacin ya dawo cikin gidan, yanajin cikinsa na kiran ciroma, tsit yaji gidan kamar ba kowa se yayi tunanin ko yarinyar ta koma side din Amihh ne tabe baki yayi yace "dakin raba kanki ds izayar dunia..." Juyawa yayi Ya nufa kiching, dan hadawa knsa abinda zesa a bakin salati, tinda yake a side din be taba shiga kiching dinba se yau, ya karasa ya shige kichng din yana me binsa da ido tsarinsa yy kyau harda AC a kiching din, rasa ma ta ina ze fara yayi sbda shi be iya ko kunna gass ba, koda yayi karatu a waje a restaurant sukecin abinci, Dan hk be iya komi ba a fannin girki. tea kawai yake iya hadawa knsa da knsa, Gashi amihh duk tabi ta tsangwanmesa ko abincin nata be samu yaci kmr ba ita ta haifesa da cikintaba. Dawowa falon yayi byn ya hado tea din da bread me yanka yanka ya zauna a kn 2ct ya dansha tea din yana yatsina fuska ko tea dinma be iya hadawa ba ji yy be masa ddh ba, Haka de ya tuttura da bread din yanaci yana tsuki, yau yasawa ranshi insha Allah se yaje side din amihh yaci abincin ko zeji ddh, zuciarshi na cike da kewar abincinta. Bayan ya gama ya dauki cup da bread din ya maidasu kiching ya wanke cup din ya maidasa ma'ajinsa sbda shi mutum ne da beson kazanta, zagaye gidan ya shigayi yana tsukin haushin canza masa tsarin gidanshi da Amihh tayi, hannunshi yakai kan handle din kofar dakinta besanma ko dakin waye ba, be taba shiga dakin ba se yau, dakunan dake side din nasa sunkai 8 a kasa akwai hudu, haka ma a saman akwai dakuna hudu, amma be taba shiga ko daki dayaba a gidan, inba dakinshi ba se yau yaji yanaso yaga dakunan dake gidan.... Tura kofar dakin yayi ya shigo, kwayar idonshi ya sauka a knta, tana kwance har lokacin bacci takeyi batasanma inda knta yake ba, batasanma anyi sallah azahar ba sbda mgnin da salwah ra bata na zazzabin yana dansa bacci. Karasowa yayi cikin dakin ya maida kofar ya rufe yanajin zuciarsa na masa kuna da zafi sbda ganinta da yg kwance, karasowa yy bakin bed din datake kwance kmr gadon gidan ubanta, ko gadon gidan karuwai, ya fadi hkn a ranshi ganin yadda taketa bacci, takaici ya rufeshi wato bacci ma takeyi tsanarta ta kara yawaita a zuciarsa, ji yayi kmr ya rufeta da duka sbda kiyayya, gata de da fari da kyau amma shi ganin bakinta yakeyi, sam ko kyaun nata ma be gani ynzu, jiya zuwa yau ya kara tsanarta sbda kalaman Amihh garesa. Duvet din dake lullube a jikinta ya yayeshi ya jefoshi kasa, cikin kyama ya bita da ido, har lokacin bacci takeyi, batasanma anayi ba, sanye take da riga mara nauyi, red se hijjabin jikinta golden. Wata iriyar uwar wawiyar tsawa ya daka mata. "Keehhhh!!!!''' Ya fadi da karfin tsiya kmr ze fasa dakin, muryarsa cike sa karad'i. A matukar gigice ta farka, batasanma sadda ta diro kasan gadonba jikinta na rawa duk tabi ta firgice ta tsure jin tsawar tasa, har tsakiyar knta... Ido ya bita dashi zuciarsa babu alamar tausanta...dago kwayar idonta tayi ta zuba masa su, jikinta na rawa nan da nan ta fara hawaye ita daman akwai saurin kuka, zuciarta se up up takeyi kmr zata fashe, data diro daga bed din bata ankare dashi ba se ynzu . "Ubanwa ya baki danar yin bacci? Nan gidan ubanki ne, ko an gaya miki gidan karuwai ne, na ...." Ya fadi kwayar idonshi na knta cikin tsantsar tsagwaron tsanar yake mgnr, ko a kwayar ido ya isa ya tabbatar maka da AB'ILAL be kaunar hilwah.




*Akwai mutane masu min karamci ngde sosai, Hajiya Saadia na'aman (momyna) bazan iya miki godia ba ngde sosai Allah ya rabaki da bakin cikin dunia da lahira baki daya, Allah ya kara lafia. Ameen*
08/01/2022 à 18:24 - SAADATU BINTU ABDULLAHI: 31***
Kasa tayi da knta, yayinda hawaye masu zafi keta aikin zirya a kn kuncinta, zuciarta na kuna sbda kalmar karuwa daya jefeta dashi. ko karuwar asali bataso a kirata da wanannan kalmar balle ita da bata taba sanin hanyar karuwancinba. Wani irin kallo yake binta dashi me cike da tsana hadi da takaici, ji yakeyi kmr yayi ball da ita yadda take tsugunne a kn guiwowintannan, murya cike da tsanarta yaci gaba da mgna yana motsi da yatsunsa irin alamar warning dinnan. "Daga rana me kamar ta yau ya zamana na farko kuma karshe, karki kara koda zama ne a kn bed din dake gaf side dinnan! Bama bed ba, hatta da kushin din dake side dinnan karki kuskura ki zauna a kai, nan ba gidan karuwai bane, gida ne na masu tsarki, so banason marasa tsarki su rinka zamar min a kn abubuwana masu tsafta kin gane kou? Nan ba hotel bane!'' Ya karashe mgnr yana tunawa da farkon inda ya fara ganinta, hawayen dake zubowa daga kwayar idonta suka yawaita, bata taba tsammanin rashin mutumcinsa yakai har haka ba se yau, a kalamansa tasan babu alamar wasa. "Ina me kara tabbatar miki da cewa duk wani abu dake side dinnan ya haramta gareki har abadan! Kinjini kou?'' Ya karashe mgnr yana me jan kunnensa alamar gargadi.

Please Login or Register in order to submit comment