Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sanar da ita, AB'ILAL ya xo gidan,, karasowa tayi tsakiyar falon ta zauna kn kujerar dake fuskantar kujerar da AB'ILAL ke zaune, se barin murmushi takeyi. AB'ILAL ya dawo da kwayoyin idaniarsa knta, hadi da rissinawa ya gaida hajiya karamar ta amsa cike da kaunarsa, ta rike haba se binsa takeyi da ido kmr taga sabon abu. "Abu na Allah wai budurwa da jika... Yau kaine a gidana na ta'ala, a lallai Shiyasa naga hadari ya hadu, koda yake ba abin mamaki bane, tinda kayanka ce, a gidan ita ka biyo, amma kiran duniar nan wanne ne bn maka ba...." AB'ILAL ya dago ya zuba mata ido, jin hjya krma tace kayansa, na nan sam ma be fahimci kn tushen zancen nata ba, data ambaci kayan nasa, har tasamu darajar ma ya dago ya kalleta sosai hadi da tsayar da tunanunnuknsa yana me sauraren kalamin hjya karama. "Kayana kuma?'' Ya maimaita hkn a zuciarsa. Alhaji bashir Dake zaune a kn kujerar 1ct kusa da hjya karama se murmushi yake yace "Ashe da dalilin zuwan nasa ruwa baya tsami bnza..." AB'ILAL ya dawo da dubansa kn alhaji bashir din, sam be fahimci inda suka dosa ba. Hjya karama ta amshe da ''A mna Alhaji, in bnda abinka yaushe rabon AB'ILAL da gidannan, nasan yau dinma da kyar ya iya gane gidan...ko makuwar kai yayi oho..." AB'ILAL yayi kasa da knsa kunya ta kara rufesa. Alhaji bashir yace "Ayyuka ne sukayi masa yawa..." Hjya karama tace "Kai de Alhaji ko dan yana danka ne..." Duk sukayi yar daria a tare bnda AB'ILAL daya dan kakalo murmushi kawai yayi, shi kaf tunaninsa ya koma kn bom-bom din dayayi tozali dashi a shigowarsa gidan, kaf hnklinsa ya kara tashi. Hjya karama ta kuresa da ido sosai dan kara karantarsa tin isowarta falon ta fahimci ramar da yayi kmr yy ciwo. "Baba wai ciwo kayi ne kayi wannan uwar ramar har haka?'' Hjya karama ta gaza daurewa ta fiddo da abnda ke cikinta. Alhaji bashir ya amshe da "Nima na hango hkn, se nyi tunanin ko dan mun juma ne bamu gansa ba,," hjya karama tace "Ah'a kam, wannan rama ce yayi sosai...ciwo ne kayi kou baba?" AB'ILAL yayi kasa da knsa sosai, alhaji bashir ya kuresa da ido shima. "zazzabi ne kawai Anty karama..." AB'ILAL ya fadi cikin daddad'ar muryarsa ya fadi hkn ne, danya samu su sassauta masa da kallo. Hjya karama ta shiga dmwa hk shima alhaji bashir sbda yana tsananin kaunar AB'ILAL , sannan shi mutum ne me yawan barkwanci, kwata kwata beda damuwa. "Zazzabi ai ba kawai bane Amma ita hajiya ai bata sanar damu ba balle muzo mu gaidaka...ko ta sanar dake ne Kurratul Aini?" Cewar Alhaji bashir Da yy mgnr cikin kulawa. Hjya karama tace "Aah wlhy bata sanar dani ba Alhaji haba ai dako yayane sena tambayeka izinin inje in gaidasa..." Alhaji bashir yace "Allah sarki, ni de ince, wlhy bamuji ba..amma jikin da sauki kou?'' AB'ILAL ya daga musu kai alamar Eh, ya sosa keya a zuciarsa yace "Ciwon *sone* da sha'awar nono...'' "Allah ya kara sauki...yasa kaffarace.." Cewar hjya karama, Alhaji bashir da AB'ILAL suka amsa da Ameen. Mikewa Hjya karama tayi zucia fal farin ciki, ta rasa ma ina zatasa AB'ILAL dan munar ganinsa yau a gidanta, ta nufa kiching ta barsu shida Alhaji bashir se hira sukeyi, ba jimawa ta dawo ita da ma'aikatan gidan su uku kowannensu da ita knta rike da tamfatsa tamfatsa din tray, suka ajiye a can table din dake gaban AB'ILAL, duk kayyaki ne na motsa baki a ciki, shide AB'ILAL kaf hnklinsa be gun yana ga kofar dakin har zuwa ynzu se kallonsa yakeyi yana kara kalla, alhaji bashir na janshi da hira ne Amma baya fahimtar komi...ma'aikatan suka gaidasa byn sun gama ajiye tray din hannunsu, amsawa yayi a dakile, suka fice a falon se yabawa kowaccensu takeyi da kyaunsa a zuciyoyinsu. hjya karama ta dawo ta zauna akaci gaba da hirar da ita, ruwa kadai AB'ILAL ya iyasha a cikin jerin abubuwan da aka tara masa a gabansa na motsa baki, da more rayuwa, shima ruwan seda hjya karama da Alhaji baahir suka matsa masa, shine ya iya daukar ruwan yasha,, sunata hira yayinda rabin hirar hjya karama dame gidanta Alhaji bashir su kejan ragamar hirar, a bangaren AB'ILAL kam ta malam ce wadda bata wuce Ameen, shide da ido kawai yaketa binsu, har zuwa lokacin sallar isha'i, Alhaji bashir da AB'ILAL suka mike zuwa toilet guda biyu dake manne a falon ba jimawa suka fito zuwa masallaci, hjya karama kam tin shigarsu toilet din ta nufa kiching. Har suka fice a falon AB'ILAL na juyowa yana waiwayon kofar dakin da hilwah ta shiga, wadda besan ba wacece amma kawai bayanta ya tsaya masa a rai, kawai so yakeyi yaga fuskar me bayan... Bayan sun idar da sallar sun jima a masallacin sbda Alhaji bashir na daukar karatu a gun limamin masallacin, dan hk se 9:am suka dawo gidan, side din alhajin suka nufa sam ba hk AB'ILAL yaso ba, a ranshi kawai yaji yafison zama a side din Hjya karamar, sbda daddad'an kamshi me kama dana hilwah da yake shakah. Alhaji bashir ya kira hjya karama ya sanar da ita sun dawo suna side dinsa, ba jimawa tazo, ta hada abincin dare a nan side din nasa, da harta hada a side dinta tasha a can zasuci abincin daren. Hjya karama, Alhaji bashir, da yallabai gogan, nan side din Alhaji bashir sukaci abncin dare, Yayinda salwah da hilwah suna can side din hjya karama, sam su basu ma wani cin abncin dare sosai, se hjya karama ta matsa musu sukeci, dan hk yau basuma ci ba, sbda me takura musun bata bi ta knsu ba.

Suna cin abncin daren suna hira suna raha, har suka kammala,,AB'ILAL be wani ci ba sosai, se juya spoon din hannunsa kawai yakeyi yayinda hoton bayanta daya gani yaketa masa yawo a cikin kwakwalwar kai, gabaki daya ya hanashi sukuni. 10;30pm ya musu sallama ze tafi gida. Alhaji bashir yace "Aah alaji ka kwana a nan mna, mu Ai munsha kwana zakayi ..." Hjya karama ma ta amshe da "nima Nasha kwana zeyi, har inasa dan ladidi ya gyara side dincan .." AB'ILAL ya girgiza musu kai kawai alamar Ah'a. hjya karama da alhaji bashir suka sashi gaba kn ya kwana, su Son samunsu ne ma yy 1week, AB'ILAL daketa duba agogon hannunsa yaki amincewa da hkn badan sun so ba, suka rakoshi har motarsa hjya karama na shirin bude baki tace masa bari a kira maka m..." Ya katseta ta hnyar shigewa motarsa sam beson ta kara ma masa magiya kn ya kwana a gidan, danshi a zatonsa cewa zatayi bari a kira mahaifiyarsa, nan ko so takeyi tace bari a kira masa matarsa suyi sallahma, sam AB'ILAL be jira ta kara mgna ba, ya kunna motarsa, ya sauke glashin motarsa, ya kara musu sallahma,,suka masa fatan sauka lafia, ya fice da motar a gidan, se kallon side din hjya kadama yakeyi ji yakeyi a ransa kmr akwai wani abu na fannin rayuwarsa a side din nata.. Hjya karama da alaji bashir suka nufa side din Alhajin bayan ficewar AB'ILAL a gidan.

Tinda suka shiga dakin dazasuyi sallar magrib, basu fito falon ba a dakinsu suka ci gaba da kallon series dasukebi a Zee World din. Haka kawai hilwah taji yanayin jikinta ya sauya ta rasa dalilin hkn, ga bugun zuciarta dake tsananta time to time, se jan numfashinta takeyi sbda kamshinsa datakeji a hancinta, ta rasa daga ina kamshin nasa yake zuwa gareta, se tayi tunanin ko kamshin nasa ne ke mata gizo kmr yadda shidin yake mata gizon. A daddafe tayi sallar isha'i salwah na ankare da ita, da canzawar mood dinta, byn sun idar da isha'i salwah ta tasata da tambaya kn meya sameta, meyasa mood dinta ya canza, hilwah tace mata ciwon kaine kadan, ta fadi hkn ne sbda t huta da tambayoyin salwah, tasan inba hkn ta fada mata ba, bazata barta ba. Sannu salwah ta mata, itama ta shiga dmwa ta hada musu goldenmoon sukasha lokuta da dama shi suke sha basu cika cin abncin ba da daddare. Bayan sunsha goldenmoon din Salwah ta bawa hilwah magunguna na ciwon kai, ta amsa tasha sbda tabbas kn nata na mata ciwo, bayan tasha mgnin ba jimawa bacci me nauyi ya sureta, itama salwah ba jimawa bacci me nauyi ya sureta, nan kasan carpet ita ta kwanta, yayinda hilwah ke kn bed ta kudindine cikin duvet. 12:am ta farka a nannauyan baccin daya sureta, ta tashi da matsanancin k'ishi, ta sauko daga kn bed din, ta nufa frij ta duba taga ruwansu ya kare se uban drinks a cikin frij din, ta fice a dakin ta nufa falon gidan, wani irin mummunar faduwar gaba ta tsinci knta a ciki, sbda kamshin jikinsa daya cikata Ainun, Ji tayi kafafuwanta suna neman gagarar daukarta ta lumshe kwayar idonta ta zubawa kujerar 3ct ido, hk kawai take ganinsa a zaune kmr yanai mata gizo, jingina bynta tayi da bango mafi kusanci da ita, ta rintse kwayoyin idanuwanta hadi da sauke gwauron ajiyar zucia me dauke da numfashi,,,,tafi karfin 30mnt a wannan yanayin , kana ta iya jan kafafuwanta da kyar ta isa ga frij din falon ta budeshi ta dauko ruwa na gora, ta juya zata koma bedroom dinsu ta juyo ta kalli kn kujerar 3ct din, tabbas kamshin nasa dake falon yana neman zautar da ita, duk a tunaninta kamshin nasa ma gizau yake mata a hancinanta guda biyu, jiki a sanyaye ta nufa dakinsu ta isa ga gefen bed ta zauna ta bude ruwan ta kafa bakinsa a kn bakinta ta fara kwalkwala yayinda har zuwa ynzu kamshin jikinsa be bar hancinta ba, tasha ruwan kusan rabin gora kana ta mayar da murfin gorar tana rufewa tana tunaninnika a zuciarta, ji tayi ciwon kn dake knta ya dawo sabo dal, har wata juwwa taji tanaji, ta koma ta kwanta tana mejin kaf idanuwanta ma babu bacci a ciki, kawai ta kwanta ne ta lumshe kwayoyin idanuwanta har wani kara jawo numfashinta takeyi sbda kamshinsa dake cikin hacinayensa har zuwa ynzu,,,wad'ansu tunaninnika suka shiga zirya a cikin kwakwalwa me aykin dake cikin knta, ta kai hannunta na hagu ta dafe knta tana jero salatuttuka ga shugaba Annabi muhammadu S.A.W, kana daga bisani ta daura da istigfari, ta rufe da hailala, hk kawai taji wani irin dadih a ranta, zuciarta ta mata wasai da wasu tunaninnikan sede har ynzu babu bacci a kwayoyin idaniarta , amma zuciarta ta watsake,,ada ta cushe da abubuwa da dama, ta gyara kwanciarta, ta koma ga hannunta na dama, kawai surar guy din keta yawo a duniar tunaninta, "Handsome!'' Ta fadi hkn a bayyane tana wani sakin shu'umin murmushi, da surarsa tazo tunaninta seta tsinci knta a faffad'an murmushi... Mikewa tayi still tana sakin murmushi me tattare da Annuri ta nufa bathroom, ruwa me dumi ta hada tayi wanka da abubuwanta na kamshi, ta gama wankan ta dauro alwala ta fito sanye da bathrobe, dai-dai salwah tazo juyi idanuwanta suka sauka a knta, tarr ta bude idanuwanta a knta masu cike da bacci, duba tamfatsetsen agogon dake ajiye a bed side tayi, taga ya nuna 1:39am, ta dawo da kwayoyin idaniarta kn hilwah dan kara tabbatar da wankan ta fito kmr yadda taga tana d'iga. "Me rabin suna wanka kkyi?'' Hilwah data karasa ga drawer din kayansu ta juyo ta kalli salwah dmn ta kula ta tashi a baccin tin fitowarta daga toilet. "Yeah wanka nyi .." Hilwah ta bata amsa tana kokarin zumbula doguwar riga ta bacci me mugun kyau, kalar milk me ratsin peach. "Meya sameki na wanka by this time.?" salwah tayi tambayar se faman zabgo hamma takeyi. Hilwah ta gama saka rigar ta dauko hijjabi ta saka tana fuskantar Salwa tace " Au se abu ya sameka kake wanka da daddare....'' Cewar hilwah. Salwah tace "A mana, ko yah AB'ILAL yazo ne..." Hilwah ta gallara mata harara tana mejin wani kala a jikinta, har alwalarta ma na kokarin karyewa, amma tayi control tace "bani da time dinki..." Ta karasa kn dadduma ta tayar da sallarh nafilah, salwah ta bita da ido hadi dayin daria tace "Ni inada naki time din Ai..." Ta fadi hkn hadi da yunkurawa ta tashi ta nufa toilet tana fadin. "Nima bari in dauro Alwala inzo mu kwashi ladar nan tare karki barni da baccin asara....'' Ta karasa shigewa toilet din ba jimawa ta dawo daure da alwala ta nufa ma'ajin hijjabansu na sallah ta dauko ta saka, ta isa ga hilwah daf da ita ta shimfida daddumarta itama ta fara jero tata kiyamul lail din.


Koda ya bar gidan be nufa ko ina ba se babban club din garin, sbda dazu ance masa se zuwa dare suke taruwa su yan shagakin duniar, a zuciarsa yakejin tana kusantosa sede matsalar besan a ina take ba, kawai de a jikinsa yakejin tana kusa dashi, Sbda zuciarsa dake tsananta bugu. Bayan ya isa clube din yaga yammata iri daban daban, lungo da sako seda ya duba be gnta ba, ya fice a Club din zuwa ga hotel din dasuka fara haduwa shida ita, nanma zagayensa ya shigayi tako ina lungu da sako, amma sam be gnta ba, yafi karfin 2h a hotel din sbda a nan yakesa ran ze gnta amma be gnta ba, ya juya ya fice a hotel din, ya nufa zuwa wani club din nanma be sameta ba, dukda dare ya tsala amma sam shi ba hkn bane ke damunsa, babbar damuwarsa ya samu ya gnta ko a ina ne, ko a wani hali ne, shide yanasonta ko yaya ta zama, ko ita ce uwar kaf karuwan dunia shide yana santa a haka, ALLAH ne ya jarabcesa,,,rnr be dawo gida ba se 4:44am, amihh tayi tsumayensa hatta gaji tayi dubansa a side dinsa, har 12;am tana ziryar side dinsa, amma babushi babu dalilinsa gashi ta kira wayarsa yaki dagawa, abnda yafi ma Amihh ciwo kenan a gami da AB'ILAL in ta kirashi be daga ba, rnr zuciarta ji takeyi tafi ta uban kowa cunkushewa a dunia. Dole ta koma side dinta tana me tunani da tsammanin ko ya tafi garin kano ne, sbda in ze tafi baya sallama wasu lokutan shiyasa ta barshi a yana garin kanon, koda ta isa side dinta ta kwanta , gaza bacci tayi, ita ce har wuraren asubahin bata rintsaba, tana jikin window tana wasu tunani tunani, a hk har taga shigowar motarsa cikin gidan, da mamaki tabi motar tasa da ido, tin tini takeji a jinin jikinta ba lafia ba, shiyasa ta gaza rintsawa,. "Daga ina yake a wannan tsohon daren?'' Take tambayar knta da knta, hadi da dumbin mamaki a tattare da zuciarta da fuskarta. Tana nan tsaye jikin window din tana tunani har taga fitowarsa daga motar ya nufa side dinsa duk tana tsaye bakin window din, ba jimawa taga fitowarsa daga side din nasa daure da Alwala sbda yalwar hasken dake compound din gidan kmr rana, dan hk ta hango ruwan Alwala a kn fuskarsa, Tana kallonsa ya fice a gidan zuwa masallaci, dai-dai ana kokarin tayar da sallarh asubahin, jiki ba laka Amihh ta juya ta nufa toilet ta dauro alwala itama, ta fito ba jimawa, ta saka hijjabi ta nufa kn dadduma ta tayar da sallar asubahain, sam ko natsuwa bata dashi, sbda tunanin daga ina AB'ILAL yake a wannan lokacin, dan sam bata da full kwanciar hnkli hk ta idar da sallar, ko adduarh batayi ba ta tashi ta fice a dakin, ta fito falo, ta fice a side din gabaki daya, sanye da hijjabin data idar da sallar asubahin dashi, ta nufa side dinsa, ta isa har bedroom dinsa bata gnshi ba, hkn ya bata tabbacin be dawo daga masallacin ba, ta dawo falon ta shiga zirya a tsakar falon idanuwanta se lumshewa sukeyi jikinta duk tako ina a mace yake, burinta ya dawo daga masallacin taji daga ina yake, abnda yasa abin ya dameta, sam be taba fita ba ya shigo gida a wannan lokacin, ita kawai a yanayin jikinta takeji wani abu na damunsa,,duba da la'akari datayi da irin gagarumar ramar da yayi, itama ta kara firgitata, hnklinta sam be kwanta ba tako ina, zuciarta na rawa. "Allah ka jarabcemu da abnda zamu iya...." Abinda ya fito daga bakinta kenan, se kara zirya takeyi a falon, zuciarta sam ba natsuwa, da tayi wannan tunanin ta dawo tayi wancan tunanin, gabaki daya knta ya kwance, babbar adduarhta Allah yasa ba mummunar harka ab'ilal ya jefa knsa a ciki ba... Ta sauke ajiyar zucia me cike da zallar tashin hnklin da take ciki, ita de kawai hnklinta be kwanta ba, taji a jikinta yana cikin wani hali ne, sam ma bataga alamar natsuwa ba a tattare dashi... Tana nan tana zirya a falon ya shigo wuraren 7:am kasancewar ya tsaya yayi askar din safe hadi da zikiri da salatuttuka ga ma'aiki S.A.W. yana shigowa idanuwansa suka sauka a kn Amihh se zirya takeyi a falon tana ganinshi ta kureshi da ido nan take ta hango Ainihin matukar ramar da yayi se taji zuciarta ta amsa da tausayin d'anta, Ainihi Amihh tana jarabar son AB'ILAL kmr k'ashi da tsoka daya a miya. "Hubbul ruhh!" Amihh ta kirashi da sunan datake kiranshi dashi da yana karamin yaro, karasowa yayi ya fada jikinta daman kmr yana jira ya sakar mata nauyinsa ya fashe da kuka, amihh ta rungumeshi a jikinta sosai nan ta kara tabbatar da ramar da yayi ta shahara, duk jikinsa yabi ya canza. "Hubbul ruhh, meye na kuka? Waya tabamin kai? Ciwo kayi ne kayi wannan ramar?'' Amihh ta jero masa wadannan tambayoyin duk ta shiga d'imauta da dmwa, AB'ILAL be tankataba yaci gaba da kukansa yayin da hawayensa keta sauka a kafadarta inda yasa knsa, sam ko nauyinsa Amihh bataji hnklinta kaf ya riga ya gama tashi kawai de tana danne zuciarta ne, amma ji takeyi kmr ta fashe da matsanancin kuka. "Tell me plz, meya sameka Abii na? Daga ina ka dawo da Asubah?'' Amihh ta kara tambayarsa muryarta na kokarin bayyana tashin hnklinta amma tanata daurewa hadi da kokarin control. Cikin kuka ya fara mgna "Amihh san yarinyarnan wlhy kasheni zeyi!, na rasa sukuni a rayuwata, amihh pls kimin adduarh , Amma ba adduarh dazan rabu da santa ba,,amihh ina santa wlhy, ko a ina take ina santa, koda bata da kowa a dunia Amihh ina santa, Allah ne ya jarabceni, a knta ban iya bacci ban iya sukuni rayuwata ba dadih, pls amihh me nayi ALLAH ya jarabceni da Tsananin santa har haka!? Pls ki tayani neman gafara ga ubangijina, ya yafemin abnda nayi ya jarabceni da soyayyar yarinyarnan me kashe zucia da gangar jiki!'' Ya karashe yana me kara fashewa da kuka daman ya jima yana neman inda ze samu ya kwanta yayi kuka, ko ze samu sassauci a zuciarsa. Tabbas kukansa na tabata, bata taba ganin kukansa ba se a yn kwanakinnan kuma duk a kn yarinyar, Abin ya daurewa Amihh kai, bata taba ganin so irin wannan ba Ace mutum marabarshi d mahaukaci shine sitirar dake jikinsa,. "Pls kayi shiru ny boy..Kana cin abnci ma kuwa babana?" Amihh ta tambaya tana kara rungumosa jikinta, duk taji ma nauyin nasa babu wani na kirki ynzu. Kwace jikinsa yayi daga jikinta, fuskarsa shabe shabe da ruwan hawaye, ya tsugunna a kasan guiwowinsa idaniarsa na zubda kwallah, , ya dago ya zuba mata sexy yum-yums idaniarsa, wadanda suka koma kalar jajjawur sbda kuka a yn mintunan kukan da yayi yafi karfin a kirgashi a mintoci ko awanni, sbda da zuciarsa yake kukan, zucia kuwa tafi Second ko mintoci da awanni gudu, ko bature be isa ya kiyasta gudun zucia ba. Cikin hawayen ya fara mgna idaniarsa na kn Amihh itama idanuwanta na kn dannata da duk take ma masa kallon full mahaukaci. "Amihh bana ta Abinci a halin da nake ciki ynzu,, pls ki gayamin ina yarinyarnan take, dan Allah Amihh ki gayamin! Ki dawomin da ita tinda akwai Aure na a knta, Auren sunnah kikasa aka mana da ita, Amihh Wlhy yarinyar ba irin sauran mata bace Allah subhanahu shiya jarabceni da soyayyarta hadi da tsananin sha'awarta dan Allah Amihh ki temakeni!'' Ya karashe zuciarsa na beating da karfi ji yakeyi kmr zata fito daga kirjinsa ta fito fili, ya fashe da kuka me tsananta zuciarta me sauraro a zurfin tausansa. Lumshe ido Amihh tayi klmnsa na dukanta, ji takeyi kmr ta maidashi ciki, a lokaci knkani kamanninta suka sauya zuwa zallar damuwarta data fi ta da. "Tashi muje kayi wanka heart beat, kaci abnci, se in gaya maka inda take..." Amihh ta fadi da karyayyiyar zuciarta, dukda batajin zata iya gaya masa inda take, sbda zalincin da yayima yarinyar kmr sabo take jinsa a cikin zuciarta, amma tana tsananin tausansa, a jini da tsokarta tasan ya azabtu. Farin ciki ya rufe AB'ILAL jin tace zata gaya masa inda hilwah take, nan take farin ciki me bayyanar da annuri hadi da annashuwa me tsananin haske ya bayyana a kn kyakyawar fuskarsa, kmr bashi ke kuka ba, duk yabi ya shige halarar farin ciki. Amihh ta zuba masa ido, hadi da lumsar kyawawan idaniarta a knsa, ta kara budesu a kn nasa. AB'ILAL ya kamo hannayenta ya rike cikin nasa, still yana tsugunne bisa guiwowinsa ya fara mgna cikin zallar farin ciki "Auwal hubb da gaske xaki gayamin inda take?'' Amihh ta daga masa kai alamar Eh, kana ta fara mgna "Amma seka gayamin daga ina kake tin safe, ka dawo gidannan da asubahi?'' AB'ILAL ya lumshe idanunsa, komi Amihh tace masa ze iya yi sbda kawai tace zata gaya masa inda hilwah dinsa take. "Naje neman hilwah ne..." Ya bata amsa nan take. Amihh ta tsiresa da ido tace "Ina kaje nemanta?'' Ab'ilal ya bata amsa "Duk inda nasan akwai jama'arh a garin nan Amihh, inna ci gaba da zama ba tare da ita ba zan iya mutuwa Amihh...taba kiji zuciata kullum cewa takeyi zata fashe wlhy Amihh ni inaji a jikina inada ciwon zucia, mutuwa zanyi Amihh..." Ya karashe yana me dafe kirjinsa dake masa barazanar tarwatsewa. Amihh ta zuba masa ido tana sauraron kalamansa, wad'anda take jinsu har a kasan zuciarta. "Babana ka sassautawa knka pl..." AB'ILAL yayi hanzari katseta ta hanyar cewa "Amihh ai bani na daura wa kaina ba, balle in sassautawa kaina,,ki temakeni ki roki ALLAH subhanahu ya sassautamin plz!" Amihh ta sauke ajiar zucia sam zuciar tata bata cikin ddh tace "ALLAH ya sassauta maka hubbul ruhh..." AB'ILAL ya amsa da Ameen, still hannayensa na cikin nata. "Hubb ki gayamin inda take plz?'' Amihh tace "Seka tashi munje kayi wanka, kaci abnci sosai, ka saki sannan zan gaya maka..."" Jiki a sanyaye ya mike tsaye yana tangal tangal kmr ze fadi kasa,.. matsowa Amihh tayi ta rungumo abinta jikinta, a hk suka karasa har bakin toilet din bedroom dinsa, ya shige toilet din jiki babu vitamin A, Amihh ta juya ta fice Zuwa side dinta, ta nufa kiching domin ta hada masa abinci mara nauyi me sauki,,ba bata lokaci ta gama hada masa dafadukan superghetti me Irish wanda ta cikashi da kayayyakin ganye na gina jiki, ta gama ta juye a kulah, ta hada masa farfesun cow leg, ta juyeshi a cikin kular shima,, ta hada masa drink me sauki hadi da gina jiki, ta hada duk kulolin a kn tray, hadi da jug din drink din, ta hada plate da bowl da cup din jug din, data zuba drink din a ciki, ta dauko bottle water me sanyi ta ajiye

Please Login or Register in order to submit comment