Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kofar falon da karfi ya shigo babu ko sallahma. A razane Alhasan ya zubo masa ido sbda yadda ya turo kofar Falon ya shigo da karfi, seyaso ya razana Alhasan din. Kallo daya Alhasan ya masa ya gane babu lafia yau, an tabo zuciar mutumin, daman ya lafiar kura, balle tayi hauka. " aiko yau seta ALLAH," alhasan ya fadi a ranshi, yana me kara zubawa AB'ILAL ido se faman huci yakeyi. Karasowa AB'ILAL yayi ya zauna a kan kujerar 2ct se sauke ajiyar zucia yakeyi kmr wanda ya sha gudu ya gaji. "Wannan wace iriyar kofa ce mara kyau kasa a falon nan! Wannan ai iskanci ne! Da wulaknci, wannan kofar ta yan iska ce!’' AB'ILAL ya fadi a hasale, dagajin yadda yake mgnr alhasan yasan da matsifa cike da cikinsa. "Me kofar tayi?'' Alhasan ya tambayeshi cikin sanyin murya. "Au tambaya ma kakeyi me kofar tayi, ai dayake kasan kai makaho ne baka gani, ko kuma kai kuturu ne baka taba kofar kaji...mtws!" ya karashe mgnr yana tsuki, hadi da lafewa a kn kujerar, jaraba da tijara fal cikinsa. Alhasan be tanka masa ba, gudun kada abin ya wuce haka. "Allah ya temake ka, ya baka yawan rai M.A..." Alhasan ya fadi hkn kmr sarki da bafadensa. AB'ILAL ya masa bansa ya wani basar ji yakeyi kmr ma ya rufe Alhasan din da duka. Murmushin Alhasan ya sakar masa se wani faman karkada kafa yakeyi zallar mulki da tsantsar saurauta kawai, ke yawo a ruhinsa. "Ashe ka shigo kd..." Cewar Alhasan, dabe daddaraba, sbda ya riga ya saba, komi ze masa ze shanye. Ai kmr AB'ILAL na jira ya taso masa da cewa "dole mana gashi naxo, ja ganni kuma kana tambayata.., mtws hmm!'' Ya karashe mgnr yana jin zuciarsa kmr zata fashe. Alhasan ya bude baki yana kallon AB'ILAL wato de yau yana ganin ba alamar arzikima a tattare da mutumin. AB'ILAL yaci gaba da mgna a mugun hasale. " waini Amihh zatawa Auren dole, auren dole kmr wata mace, da wata tsinanniya wlhy bnsonta sena saketa tinda ba Tare mukazo dunia ba..." A hasale yake mgnr muryarsa me cike da tijara se tashi takeyi. Alhasam daya zuba masa ido, ya gane kn zancan nasa dukda ba a natse ya masa mgnr ba. "Aure kuma? Plx ka fahimtar dani sosai...wani irin Aure?" Alhasan ya jefowa AB'ILAL tambayar a matukar kid'eme. "Kasan kai kurma ne bakaji Ai,,to nace maka Aure wai Amihh tamin jiyannan, auren ma da karuwah..." Ya karashe mgnr yana me jin zuciarsa kmr zata fashe, sbda takaici da zallar baqar kiyayyar yarinyar. Alhasan duk yabi ya shiga dimauta shi kalmar karuwancin bata damesa ba, sbda yasan kowacce mace a gun AB'ILAL karuwa ce koda ma me mutumci ce. Ajiyar zucia ya sauke fuska dauke da mamaki hadi da damuwa yace "Aure? To da Hameedah ko?" a fusace ab'ilal ya amshe da cewa "inda ace mani ita ce da sauki, wannan fa karuwa ce na ce maka, ta gama gantalewarta a titi kuma wai Amihh ta rasa wadda zata hadani da ita se ita, kai wlhy ko za ayi menena sena saki yarinyarnan!'' Ya karshe mgnr Kmr zeyi kuka, ya dafe knsa dake masa azababben ciwo kamar ze tarwatse. Alhasan daya zuba masa ido yaji tausansa ya ratsa masa zucia, tabbas yasan yana cikin wani hali irin wanda be taba ganinshi a makamancinsa ba se yau. "Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un!" Ita ce kalmar data fito daga bakin alhasan ya kara sauke ajiyar zucia kana daga bisani yace "To ita ma yarinyar yar kano ce kou?'' AB'ILAL da idanuwansa sukayi jajawur bemason mgnar dande beda yadda zeyi ne mafita kawai yake nema koda da tsiya ne yace "yar kd ce,.. ni bnsanma ta yaya Amihh ta sameta ba ta mannamin, wlhy frnd duk dunia yarinyarnan nafi tsana, nifa daza a bani dama da zan iya kashe yarinyarna...ita kuma Amihh dagani sonta takeyi, tinda tana ikirarin tsinemin a kan yarinyar...hmm!" Ya karashe mgnr da mugun zafin zucia har fuskarshi na huci. Alhasan ya zaro ido jin mgnr kisa a bakin AB'ILAL tabbas yasan abun babba ne. Cikin sanyin murya hadi da kwantar da hnkli Alhasan ya fara mgna "Dan ya frnd kadena mgnr kisa,..tinda bakasonta kiyayyar har tayi zafi haka kawai ka sawwaqe mata..." AB'ILAL ya furzar da wata iska daga bakinsa me dauke da huci kai kace jarumin namijin zaki ne, ya fara mgna da muryarsa data fara dishewa dan bacin rai, yaci gaba da mgna rai bb ddh "Amihh tace inna saketa seta tsinemin albarka...na rasa ya zanyi..wlhy banason yarinyarnan, ni dama wata ce se in hkra amma bazan iya hkrin zaman Aure da wannan yarinyarba, wlhy sede ko Amihh ce ta aurota kawai amma ni bani ta Auro mawa itaba..." Alhasan yayi shiru yayi kasaqe yana sauraron kalaman AB'ILAL nan da nan ya fara jin zafi dukda kuwa sanyin AC dake falon. "wannan shi ake cewa an gudu ba a tsiraba... To yar qawar Amihh ce ko yaya ne?" AB'ILAL ya masa bnza a wannan karon se aikin cusa hannunshi yakeyi a cikin sumar kansa. Kwantar da murya Alhasan yayi kana ya fara masa mgna. "Plx aboki ka rinka daukar abu a sannu se yazo maka a sannu, in zaka karanta lamarinnan kaddara ce, kaga munsa Amihh ta dawo kd daga kano sbda Kada ta maka Aure, se gashi ashe a nan din zata maka Auren...dan ALLAH ka dauka da sanyi plx..." Ya karashe mgnr da sigar rarrashi. A hasale gogan ya kara Amshewa da "Ta yaya zan dauka da sanyi ? Karuwa ce fa, da mutuncina ka auramin mazinaciyya, me yafi wannan zafi dan ALLAH?'' AB'ILAL ya fadi cikin zafin rai, kai dajin yadda yake mgnr kasan abin na cinsa inside. "A ina ka tabbatar da ita karuwa ce plx? Ba kyau fa plx kabi a hnkli..." Alhasan ya fadi da sanyin murya shi knshi jikinsa yayi sanyi, sbda yadda yaga ikon ALLAH a zahiri. "Karuwa ce mana, in ba karuwa bace mecece, yama za ayi kace wai ta ina na tabbatar da ita karuwa ce, to kazafi na mata se kabi mata haqqinka tinda uwarku daya ubanku daya..." AB'ILAL ya fadi a matukar hasale kai kace ze tashi ne ya rufe Alhasan da duka, sbda tsabar tijara. Alhasan yayi shiru na wasu yan mintoci kawai dan yasan halin kayansa. After 5mt Alhasan yaci gaba da mgna "Ba haka nake nufi ba frnd, ynzu de shikenan kayi hkri... " "nifa sakin yarinyarnan zanyi Alhasan wlhy ALLAH bazan zauna da ita ba, dan ina iya mata lahanin dazan dauwama a gidan yari.." AB'ILAL ke mgnr cikin zafi da zuciarsa da babu sassauci ko a murya kasan babu sauki a lamarinsa. Alhasan ya zuba masa ido, ya kula duk natsihar daya masa ma a wannan halin da yake ciki da wuya yajisa saurarensanma baya tunanin yanayi, ya kula ko hkri ya basa ma se ya kwaso wani bala'in ya kara laftowa, be daddaraba ya ci gaba da masa mgna da laushin murya. ''Dan Allah frnd kada kayi kuskuren sakin yarinyarnan, tinda kasan halin Amihh, kamar yadda ka fadi tace inka saki yarinyarnan tsine maka zatayi, wlhy tsinemakan zatayi, plx mubi a hankali a rabu salin Alin, duk ci gaban da kake ganin muna samu a dunia sbda munabin Allah ne kuma munbin iyayenmu, dan ALLAH kabi a hnkli ka gama da Amihh lafia fushin iyayenmu a kn mu beda dadih frnd babbar matsifa ce, 9month ba 9days bane, kayi hakuri plx dan Allah..." Ajiyar zucia AB'ILAL ya sauke yana me jin dan sassuci a zuciarsa sbda kalaman Alhasan sun d'an shigeshi kadan ko ince wasu sun shigeshi. "Bani ruwa..." Ita ce kalmar data fito daga bakin AB'ILAL uban yan mulki se huci kawai yakeyi kmr wanda yaci gindi ya kawo ya sauka yana hutawa, kafin ya daura daga inda ya tsaya (wannan ba hucin cin gindi bane hucin jaraba ne da zallar matsifa😂) mikewa alhasan yayi ba bata lokaci ya nuda frij din dake falon, ya dauko bottle water me sanyi normal one, ya dawo inda AB'ILAL yake , ya bude ruwan ya bar murfin a kai kana ya mikawa AB'ILAL din. Ya dago kwayar idonsa da knsa dake masa nauyi ya zubawa ruwan da alhasan ke miko masa ido, seda ya dauki 5mnt yana kallon ruwan, shi kuma alhasan na tsaye beda yadda zeyi. AB'ILAL ya amshi ruwan Alhasan ya koma ya zauna kujerar dake facing AB'ILAL din ya zuba masa ido, se kallon bottle water din dake hannunsa kawai yakeyi. Yakai baki da niyar yasha, ya tuno yadda yaga yarinyar a falon uwarsa, kawai ya fasa shan ruwan dukda uwar kishin ruwan da yakeji, yayi wata irin jifa da bottle water din, ya isa ga tamfatsetsen TV dake falon ya dakeshi kana ya dawo ya fadi kasan falon ya fara zuba... Alhasan ya zuba masa ido, be taba ganin mutum me muguwar zuciaba irin ta AB'ILAL ba. kwata kwata babu sauki a lamarinsa, baqar zucia gareshi me bakin tsiya, hadi da farar matsifa, duk duniya alhasan be taba ganin tijararre me wuyar kai ba kmr AB'ILAL. Tinda ya wurgar da bottle water din ya koma ya kwanta a kn kujerar yana hadiyar mugun yawu, me mugun zafi xuciarshi se harbawa takeyi kmr ze zauce. "Plx ka rinka cewa innalillahi wa'inna ilaihirraju'un!'' Cewar Alhasan da kwayar idonshi ke kn AB'ILAL har zuwa lokacin, shifa alhasan tsoronshi Allah, tsoronci kada baqar zuciar AB'ILAL ta buga ya shiga uku ya bani ya lalace, a garin kaduna. Ajiyar zuciar kawai AB'ILAL keta faman saukewa time to time, se faman zufa kawai yakeyi, yayi amfani da abinda Alhasan yace masa, se aikin maimaitawa innalillahi wa'inna ilaihirraju'un yakeyi a zuciarsa... Alhasan ya masa kuri da ido, shima a tasa zuciar se masa fatan sassauci yakeyi, a gaskia da ace Amihh tayi shawara dashi da bata yima wannan me baqar zuciarba Aure ba, shi ba kowa ma yake tausayamawa ba, bace wadda aka hadata aure da AB'ILAL din, yasan ta shiga uku ta bani ta lalace, tabbas zeci ubanta la'ada waje..." Alhasan ya fadi a ranshi yana me ci gaba da ma abokinnasa adduarh ALLAH ya sassauta masa baqar zuciarsa.


Da daddare bayan sunci abincin dare, amihh ce tayi feeding hilwah harta koshi...dukkaninsu zuciyoyi babu dadih, Salwah kanta ma ke mata ciwoh tasha mgni Amma yaki sauka, Hilwah kam komi na rayuwarta ciwoh yake mata, ji takeyi tamkar zata kamu ne da ciwon zucia. Baysn sun gama, Suka nufa bedroom din salwah , sukabar Amihh a falon, tanata tunani tunani. suna shiga dakin suka kwanta Amma duk cikinsu babu mejin bacci Amihh tazo ta musu adduarh ta musu seda safe kana ta nufa nata bedroom din, zucia babu dadih se tunani takeyi a kan a wani hali AB'ILAL yake ciki, da ace lafia lafia ce tasan da dashi zasu ci abincin daren yau. Koda ta shiga bedroom dinta ba bacci ta kwantaba Alwala ta dauro ta dawo ta ci gaba da nafilfili ta riga data sawa ranta Bacci be gantaba a halin ynzu,....

Koda Amihh ta fice a dakin gaxa baccin duk sukayi, kawai suna kwance ne Amma kiwannensu da abinda ke ranshi. Ita de Salwah tausan hilwah takeyi, sbda tasan waye AB'ILAL ballan tana ma dataji kalamansa shida Amihh, se salwah taji ta kara tausayama Hilwah, kwata-kwata babu ma Alamar sauki ko sassauci a lamarinsa, ita kanta salwah kalmar karuwar da yace ma hilwah ya tsaya mata a rai. A bangaren hilwah kam abubuwan sun hadun mata ne goma da ashirin, ga dmwar tunanin halin da take ciki again ga damuwar aurenta da wannan guy din, a zahirin gaskia bata bakin ciki, a farko da batasan wayeba shi ne ta damu, amma a ynzu data ganshi kuma ta gane shin din ashe abinda gangar jikinta ke tunani ne a kullum, se taji sauki ga ranta ta rasa dalilin dayasan taji hakan. Kalma daya ce ta tsaya mata a zucia itace kalmar karuwar daya kirata dashi Amma tasan ta cancanci ya kirata da hakan ne ko fiye da hakan ma, sbda ya ganta a hotel maybe shiyasa yake kiranta da karuwa, ita abinda tunaninta ya bata kenan. Karin tashin hnklinta kuma ga kasanta nata ruwa, anbaliya kawai, shi ba ruwanshi da tana cikin damuwa ko wani hali take ciki shide kullum cikin zuba yake babu kakkautawa zallar tsiyaya kawai yaketayi, jefi jefe sha'awarta ta jini na tsungularta, nanma dauriar takeyi, ba Tablet kuma babu pad duk a takure take, duk bayan wasu awanni se tayi wanka, seta canza pant, amihh ta bata sabbin panties masu kyau dozing ashirin, hadda pad ta bata Amma ba irin pad din da take sawa ba sbda tsane ruwan ni'imar dake jikinta, wannan inta sashi ze takura mata sbda na tsane jinin al'ada ne shi kuma wancan be kai wannan girma ba kuma ya fishi soft sosai, abubuwan sunma hilwah yawa ga tunanin mahaifiyarta dake maqale da ranta a kullum, again ga kewar su kankana da,Amal dake ranta, har Alhaji sunusi ma tana kewarshi, uwa uba kuma cocaine da codeine dinta da wiwi ma duk tana kewarsu tasan da tanashansu da dmwar bata mata yawaba har haka ba. Ajiyar zucia hilwah ta sauke tanajin ruwan dake zuba a kasanta yana yawaita. ''Tashi muyi sallah tinda duk mun kasa bacci...'' Cewar Salwah. Ba musu hilwah ta tashi, kusan a tare suka tashi da salwah, hilwah ta diro daga kan gadon jiki babu laka Salwah tabita da ido Harta shige toilet din. salwah bayanta kawai take kallo, harta shige toilet din, ta daga duvet din dake gefen inda hilwah ta tashi, nan taga inda ta tashi ya jige, sau biyu kenan tana gani ta rasa meyasa take ganin hakan, ta fara tunanin kode fitsari ne hilwah takeyi. "Wani irin fitsari ne dan kadan?'' Salwah ta tambayi knta, shiru tayi hadi da yin jim tanajin kunya dase ta tambayi hilwah meyasa take zuba, kuma ba jinin period ba. Tana nan zaune tanata tunanin hilwah ta fito daga toilet din daure da alwala, salwah ta mike ta nufa toilet din itama dan dauro alwalar. Hilwah ta nufa Wardrobe dan canza kayan dake jikinta, ta sauyasu zuwa wata doguwar riga mara nauyi ta dauki hijjabi zumbulele ta saja ta tada sallarh nafilar, Salwah ta fito itama tasa hijjabi tabi sahunta ta tayar da tata sallar. Duk bayan sallarmar raka'ah biyu se hilwah ta shiga toilet ta kara dauro alwala kana ta dawo taci gaba da yin sallarh duk salwah na Ankare da ita, tin tana tunanin neman lada ne harde yau ta fara tunanin akwaide abinda ke faruwa.... Da asubahi amihh tazo dan ta tashesu suyi sallarh asubahin ta taddasu suna kn dadduma ne ma suna nafilfili, juyawa tayi ta koma dakinta zucia fal farin ciki, ada kullum seta tashi Salwah danyin sallarh asubahin amma ynzu Alhamdulillahi zuwan hilwah yasa har sallarh dare sukeyi. Seda sukayi sallarh asubahi gari ya fara haske kana suka koma suka kwanta, bacci ya daukesu ba wani me ddh ba, se mafarke mafarke sukeyi a kan abinda ke zuciyoyinsu. A bangaren Amihh ma hkn ta kasance.


A bangaren Ab'ilal ma sam be rintsaba. Hk alhasan shima be rintsaba. 1:am alhasan ya bawa AB'ILAL shawarar su tashi suyi sallar nafilah, ba musu AB'ILAL ya tashi suka dauro alwala a nan falon suka tada sallarh nafilar, sunatayi hadi da adddu'ur'i har asubahi.. suka kara Alwala suka nufa masallaci dan samun sallarh asubahin a jam'i. Da aka idar basu baro masallacinba seda alfijir ya fara bayyana kana suka dawo gidan. AB'ILAL ya zube a falo, yana dan jin sassuci a zuciarsa ba kmr jiyannan ba. Alhasan ya dubeshi yace "mushiga bedroom mna.." AB'ILAL ya masa bnza. Alhasan be kara mgna ba sbda yasan ko ya kara ba tanka masa AB'ILAL din zeyi ba. Yabar falon ya nufa bedroom danya samu ya kwanta yayi bacci, yana kwancia kuwa bacci me nauyi ya kwasheshi....A bangaren AB'ILAL kam gaza baccin yayi ga damuwa na cinsa duk silar yarinyar ne, ga yunwa na kwakular cikinsa beci ba, be sha ba har ynzu. Jiyama da Alhasan ya masa tayin cin abinci saura kadan AB'ILAL din ya zagesa dole ya barshi. A zahirin gaskia sam shi yunwarma bata damesaba kmr yadda tunani da tsanar yarinyar suka hadu suka ma zuciarsa rubdugu har Amihh ma dan beda yadda zeyi ne Amma da haushin abinda ta masa yakeji. Se 8:am ya samu bacci barawo a wahalce ya daukesa, baccin yakeyi amma bayajin dadinsa kwata-kwata.


A bangaren su kankana kam, shida Amal sun shiga tsananin damuwar Rashin hilwah har wata rama sukayi a kwana daya, inka gansu kasha ko uwarsu da ubansu ne suka mace, saboda iyakar damuwa sun shiga. Kankana ya kira alhaji sunusi yana kuka ya sanar dashi abinda ke faruwa, seda ya fadi ya suma a rnr hawan jininsa ya tashi aka kwasheshi a can kasar da yake se asibiti, washe gari dayaji sauki ya baro kasar yabi jirgi ya dawo kasar nigerian direct gidan dandi ya nufa,..nan ya tadda sun kankana da Amal a tashin hnkli, kankana ya kara kwashe lbrin komi ya gayawa alhaji sunusi iyakar dmwa alhaji sunusi ya kara shiga. Kawai ya fashe da kuka yana tambayar su kankama da Amal suna kiranta kuma yana shiga? kankana ya tabbatar masa da kullum se sun kirata amma bata dagawa washe garin rnr da tazo gidan Amihh ta amshe wayar dake hannunta. Iyakar tashin hnkli alhaji sunusi ya kara shiga, a zahiri daxesan inda hilwah take da har can ze bita ga iyayenta ya Aureta , sbda ita ce farin cikinsa. A nan garinma seda Alhajin ya kara kwancia asibitin, sbda damuwar rashin hilwah dukda kuwa alhajin naji a ransa ze kara ganin Hilwah, kwananshi uku a asibitin aka sallamesa Kankana da Amal sukayi jinyarsa be sanarma da iyalinsa ma yana Nigerian ba. Ita knta magajiyar karuwai ta shiga dmwar rashin hilwah sbda zamanta a gidan ba karamin alheri take samu ba dukda kuwa hilwah ba bada gindinta takeyiba anaci, amma mnyan maxa naso kuma ko basu ciba suna bada kudi,..aiko jin uwar hilwah taxo ra tafi da hilwah seda hajiya magajiyar karuwai tayi zazzabi wannan qibar tata ta asara duk seda ta sab'eta ta zaizaye ta rame... Khamilah kanta data samu labari ta dan damu kadan, shima sbda ganin Amal ta damu ne. Amma a zahirin gaskia khamilah dadih taji, sede kuma ta gaza gano kan Amal... D&D su qamas su Anty kwalba, dasu hadin sigag duk sun shiga dmwa, sbda suna mugunyin hilwah sam basa son wanda ze bata mata rai, to a yau Gashi babu ita kilama ta bar gidan dandi ne na har abadan, Baraka da dan taure ma sun shiga dmwa da suka samu lbri, suma suna mugun missn hilwah, amma basu kai zallar D&D missn din hilwah ba...kankana kam har gobe yanaji a jikinsa Wata Rana uwar dakinsa zata dawo garesa, motarta da gidan data bari Alhaji sunusi ya mallakawa kankana, da niyar ko yau hilwah ta dawo ze sake mata wasu abubuwan duniar da sukafi Wannan, seda bata nan ne ya tabbatar da yana sonta tamkar yadda me rai ke son ran dake jikinsa. Kankana yama Alhaji sunusi godia da kyautarsa garesa, amma sam be wani farin ciki iskncinma duk sun rage shida Amal sede shaye shayensu ne ya karu, shike rage musu wata damuwar. Amal da kankana a yan kwanakin nan kullum cikin zagaye garin kaduna suke ko ALLAH zesa suga Hilwah Amma ko me kama da siffartama basa gani sede su karata da yawonsu su dawo gidan jiki bb laka, zucia babu dadih, kullum se kankana ya dauko kayan hilwah ya rungume seya fashe da kuka amal ce ke bashi hkri kafin daga bisani itama ta fashe da kukan. Satin Alhaji sunusi daya a garin kaduna yama Amal da kankana sha tara ta arziki kana ya juya ya koma kasar daya fito domin ci gaba da aikinsa, amma fa zuciarsa babu ddh, kuma ya ce kankana yaci gaba da neman hilwah in Allah yasa ya gano inda take, ko ya gnta ya gaya masa shi kuma a rnr zezo gidan su Hilwah ayi mgnr Aurensu Ko rnr ne a daura musu aure ya mallaki wannan kayan dadin ya killaceta a tamfatsetsen gida yayita more rayuwarsa da arzikin da Allah ya mallaka mata... Hilwah ta tafi tabar zuciyoyi da kewarta hadi da dumbin kaunarta na har abadan da'iman. Amal da kankana suka sa aka wanke musu hotunan hilwah dake wayoyinsu suka zo suka manna tako ina a dakin suna kalla kuma sunajin ddh, ALLAH sarki rayuwa kenan basu taba zaton zasu rabu da hilwah ba a rayuwarsa, a kullum suna tuna alherin hilwah ne da kyakyawan halinta, zuwa ynzu Amal da kankana har sallah suka farayi sunata adduarh Allah ya bayyana musu hilwah koda sau daya ne su kara ganinta a rayuwarsu, tin number dinta na shiga gashi zuwa ynzu ma bata shiga hajiya maryam ra kashe wayar gabaki daya ta jefata a drower. Se hnkulansu ya kara tashi jin suna kiranta basa samunta, amma dukda hkn basu bar sa ran kara ganintaba.....






*for more information 08136349646...*
08/01/2022 à 18:24 - SAADATU BINTU ABDULLAHI: *YAR DANDI CEH...* 🅿️23
SAADATU BINTU ABDULLAHI✍🏽

Yau kimanin kwana biyu kenan da zuwan AB'ILAL gidan, tinda ya fita Amihh bata sake ganinshi ba dukda tana damuwa Amma hkn besa ta nemeshi ba ko da ta waya ne, a wannan karon so takeyi ta nuna masa tabbas ita ta haifeshi bashi ya haifeta ba. Bayan tayi sallar azahar tana zaune nan kan dadduma, ta tashi ta karasa bakin bed dinta ta zauna, ta dauki wayarta dake kan gadon, ta shiga dealing number din hajiya Juwairriyya bugu daya ta daga, daga bngarenta ta fara mgna cike da kewar hajiya maryam. "Hajiya wainshin kina kasar nan?'' Hajiya maryam tayi murmushi da iyakarshi yaqe ne, kana tace "Assallamu Alayki..." Hajiya Juwairriyya tayi yar dariya kana ta amsa "Wa'alaykissalam, na mnta ashe bamu nemawa juna aminci ba,,to ya kike aminiata? Kwana biyu kin boye nima kuma na boye..." Hajiya maryam tayi yar daria ita ma kana tace "yauwa ynzu kikayi mgna, amma da kince ina kasar ne, bayan nida ke duk bama kasar...." Dariya sosai hajiya Juwairriyya tayi Tana nazarin dariyar maryam da klmnta tasan basu kai kai ciki ba. "Bari hajiya Ai alhaji ne ke gida yana hutu wlhy bani da katafus, ..." Cewar Hajiya Juwairriyya. Hajiya maryam ta kara Murmushi tace "masha ALLAH, Allah de ya Kara dankon soyayya da nisan kwana..." Hajiya Juwairriyya ta amsa da Ameen..." Duk sukayi jim na wasu yan daqiqu, kana hajiya Juwairriyya taci gaba da mgna. "Ashe Alhaji karami na nan kd kou? " Hajiya maryam ta sauke ajiyar zucia tace "eh yana nan kd hajiya Juwairriyya, lamarin yaron nan yana damuna hajiya, abin nasa se adduarh , kwata kwata yaronnan beda mutumci,.." Hajiya Juwairriyya ta sauke ajiyar zucia dmn tasan a can damuwar hjya maryam take,
tace "Ai ni nasan dajin wannan murya taki da abinda ke damunki hajiya, meya faru?" Hajiya maryam ta sauke numfashi kana ta fara mgna "Hajiya yaronnan kwata-kwata beda ladabi beda biyayya, Gashi nan de a tsaye ko rankwafawa beyi! ALLAH wadaran halin wannan yaron,.." Ta karashe mgnr da muryar takaici. Hajiya Juwairriyya tayi shiru tana sauraren hajiya maryam dajin hkn se tayi tunanin AB'ILAL ya kara wata tsiyar ne. tayi gyaran murya kana ta dauka da cewa "me yayi na rashin Ladabi hajiya?" Hajiya Maryam ta kwashe lbrin komi na auren data ma AB'ILAL A,to,Z ta shaidawa hajiya Juwairriyya, amna bnda na inda taga hilwah, wato gidan karuwai, sam bata gaya mata wannanba, tadece mata hilwah marainiya ce daga gidan marayu. Hajiya juwairiyya dake a zaune Amma seda ta

Please Login or Register in order to submit comment