Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shigo to ta ina ya shigo ya mata wannan cizon, Hilwah tayi shiru hadi da kara kasa da knta, hilwah ta bita da ido ganin bata da niyar bata amsa yasata ci gaba da mgna itana hawaye . "Ki gayamin meye ya hadaki da AB'ILAL ya miki duka, kuma ya akayi sauro ya cijeki plx ki gayin plx? " hilwah ta goge hawayen dake zubo mata itana, ta sassauta kukanta ganin Salwah duk tabi ta damu har lokacin se kuka takeyi tace "ni be min komi ba,..." Ta fadi da muryarta ta kuka, hadi da karyayyen harshenta. Salwah taji takaicinta ya rufeta zurfin cikinta haushi yake bata "to wannan kurajen sauron ina kk samesu? Tinda kinki gayamin meya hadaki da yah AB'ILAL ya dakeki dan wlhy nasan dukanki yayi ga mari nanma a kn fuskarki, inna gayawa amihh ita tazo ta tambayeki zaki gaya mata gaskia Tinda ni baxaki gayamimba..." Hilwah ta tsagaita da kukanta jin Salwah tace zata gayawa Amihh kuma dagani da gaske take bada wasa take ba, ta kara goge hawayenta dake kn fuskarta kwayar idonta na kn salwah ta fara mgna ''plx karki gayawa Amihh, ni be min komi ba.." Salwah ta hade rai tace "in kina cewa be miki komi ba bnjin ddh, infect ma haushi kk bani sbda ga abu ina gani a zahiri... Kawai ki gayamin gaskia tinda bakiso in gayawa Amihh dan Allah ki gayamin?'' Salwah ta karashe mgnr da sigar roko, hilwah ta tsaya a kn bakarta kan be mata komi ba, salwah tayi juyin dunia Amma hilwah tace mata ba komi, aiko tace seta gayawa Amihh nan hilwah ta shiga rokonta tana mata magiya, kan karta gayawa Amihh, salwah tace seta gaya tinda bata gaya mata me yah ab'ilal ta mata ba, hilwah ta fashe da kuka tana rokon Salwah kn karta gayawa Amihh, Salwah tace to kawai sbda hilwah ta tsagaita daga kukan nata, da kyar kuwa ta samu ta tsagaita daga kukan nata, zuwa lokacin ta fara jin axababben ciwon kai na gefe da gefe biyu na knta, dan hk ta amshi hakurin da Salwah ta bata tayi shiru ta dau na annabawa, Salwah ta zuba ma hilwah kunun gyada da kosai ta tura mata gabanta, zuba musu ido hilwah tayi bata taba cin kosai ba gaskia kwara ma kunun gyad'a ta taba sha da tana gidan dandi wata rana kankana ya taba siyo musu. Mikewa tayi da niyar taje toilet tayi brushi salwah tace ina zata je ta bata amsa da brushi zatayi, salwah tace okay, ta bita da ido harta shige bathroom din jiki babu kwab'i, se tausanta ya kara ratsata salwah, ta rafka uban tagumi a zucia tana me adduarh Allah ya sakawa hilwah ga AB'ILAL tama mnta cewar shidin wai dan uwanta ne. Hilwah ta fito tazo ta zauna ta fara shan kunun gyad'an Amma sam bata kai hannu ga kosan ba sbda bata iya cinsa, ko tace ma bata taba ganinsa ba se yau, ita inbama datazo gidanba bata cin Abincin ire ire hkn, nata fa ban kankana ke dafa mata amma a gidan Amihh ta koyi cin Abincin iri irin wad'annan..Salwah ta tambayeta meyasa bazataci kosanba, hilwah tace bata taba ma ganinsa ba balle taci. Salwah ta bita da ido da mamaki a ranta tace "baki taba ganin kosai ba? kosai ne fa? ko de baki taba ciba?'' Salwah ta tambaya hilwah. "Ban taba ganinshi ba se yau..." Mamaki ya kara cika salwah jin hilwah tace bata taba ganinsa ba, ita de bata taba ganin dan nigerian dayace be taba ganin kosaiba se hilwah. "Kici kinji dea akwai ddh...'' Hilwah ta girgizawa Salwah kai kawai alamar ah'a, salwah ta bita da ido har lokacin se mamaki takeyi a ranta. Hilwah ta dansha kunun gyad'an da salwah ta zuba mata Rabi ta ajiye cup din tace ta koshi salwah tace ta dan kara mna ta girgiza mata kai, Salwah ta mike hadi da cewa bari inje in kawo miki magani naga alamar kinada zazzabi na maleria ne da ciwon kai, duk fuskarki tayi wani kubul kubul, bnsan ina kk samu sauro ba ya cijeki ba..., bari in kawo miki magunguna, har na ciwon jiki ma..." Hilwah ta daga mata kai alamar to, salwah ta fice a dakin hilwah na kallonta harta fice ta koma ta kwanta, nan kn carpet din jiki a sanyaye, ko ina nata ciwo yake mata,...abubuwan da AB'ILAL ya mata tin zuwanta gidan har zuwa ynzu suka shiga tariyowa a cikin kwakwalwar kanta, hk kawai takeji a zuciarta ta tsaneshi kmr yadda ta tsani mutuwarta, tasan itama ya tsaneta dan hk ta kara tsanarsa bisa kn tsana, bata taba tsanar wata halittaba a rayuwarta kmr yadda ta tsani AB'ILAL.

A bangaren gogan tinda ya shiga bedroom dinsa ya kwanta akan bed dinsa me laushi, ya riqe knsa kawai ya tsinci zuciarsa da kunci ya rasa dalilin hkn, yasan dan marin daya mata ne, to meyasa ya tsinci kn nasa da kunci? Bayan shi ba tausanta yaji ba shide kawai yaji zuciarsa cike da kunci...juyi ya shigayi a kn bed din, daya rintse ido kawai tunano yadda ya daga hannu ya sharara mata marin yakeyi. Dago hannunsa na hagun yayi ya zuba masa ido, har ynzu laushin fuskarta be bar jinsa ba a tafin hannun nasa Ba, rintse idanuwansa yayi yana me aikin tunano lauahi da tsantsin fuskarta a zuciarshi, qoqarin kauda hkm yy a ransa amma abu fa yaci tura kuma ya gagarah, bacci yakeso yayi amma baccin yaki zuwa har kusan ya shafi 1h se aikin juyi kawai yakeyi a kn tamfatsetse lallausar bed din nasa Zuciarsa se aikin jeka dawo takeyi a kn tunani abinda besan dalilinsaba, tsabar takaici, ji ya farayi kmr ya cire zuciar tasa daga jikinsa, sbda ta mugun bata masa rai, shi da knshi haushin kansa yaso ya fara ji, duk yadda fa yaso yayi bacci gazawa yayi sede yy shiru kawai hadi dayin likimu, Amma idanuwansa a bude...

Tana shiga side din Amihh Ta nufa bedroom din Amihhn ta dauko magunguna masu inganci na maleria dana ciwon kai da zazzabi, dana ciwok jiki, dukda de tasan mgnin maleriar zeyi aiki ga zazzabi da Ciwon kan amma ta dauko de na ciwon kn da zazzabin dana ciwon jikin, in case, ta nufo hanyar ficewa a falon ta kai hannu zata bude handle din kofar fita falon, Amihh ta rigata shigowa cikin falon, salwah ta bita da ido, itama Amihh ido ta zuba mata, duk a gaggauce take, dan hk bata ankare da magungunan dake hannun salwah ba . "Sannu da zuwa!'' Itace kalmar data fito daga baki salwah zuwa ga Amihh amsawa tayi dagani tana dan sauri ne, ta rabe salwah zata wuce tana me fadin "kin kaiwa hilwah breakfast?'' Salwah ta amsa da Eh..amihh tace okay kawai ta nufa hanyar shiga bedroom dinta Salwah ta juyo ta zubo mata ido ta gaza tafia so takeyi ta gayawa Amihh halin data samu hilwah a ciki kuma tana tsoro a ranta. "Am...ihh!'' Salwah ta cire tsoro a ranta ta kira sunan Amihh, hajiya maryam data kai Hannunta kn kofar dakinta tana shirin budewa ta dakata jin salwah ta kira sunan nata, ta juyo ta zubawa salwah ido tace "meya faru?'' Fuska babu alamar wasa tayi tambayar.


*bazan dena baku hkri ba a kan rashin editing.....*




*Ku bar AB'ILAL yayi iskncinsa plx time dinsa ne....hmmmm😂*
08/01/2022 à 18:24 - SAADATU BINTU ABDULLAHI: 34***
Salwah tayi kasa da knta ta rasa ma ta ina zata farawa Amihh mgnr dukan da AB'ILAL yama hilwah ita da bata tabbatarba hasashe takeyi, sbda hilwah bata gaya mata da bakinta ba... Ganin tayi shirun yasa Amihh jan guntun tsuki ta fara fad'a "banason isknci kinajina kou? Ni sa'arh dangin ubanki ce? Ko ni sa'arki ce daxaki kira sunana ki barni tsaye!'' Ta karashe mgnr cikin muryarta me cike da tsiwah da tsawa seda Salwah ta Dan firgita taja baya, dukda basa kusa da Amihh sunada nisa Amma gani takeyi kmr zata karaso ne ta tsinketa da mari... "Yi hkri Amihh..." Itace kalmar data fito daga bakin Salwah ba tare data ankare ba, sbda kallon da Amihh ta kuma jifanta dashi. Kwafa Amihh tayi ta nufa bedroom dinta kawai, salwah ta karasa ta dauki wayarta dake kn kujerar 3ct cikin hanzari ta fice a falon hannunta riqe da wayarta da magungunan. Dan ustaz dake zaune a kusa dame gadi a dan bencinsa dake kusa da bakin get din fita, ganin salwah ta fito daga falon Amihh yasashi tasowa a guje ya nufo inda salwah take tahowa tsantsin takalminsa se kwasarshi yakeyi. Salwah ta zubawa dan ustaz ido dan ganin yanata sauri ya karaso inda take, rana na haskashi yanata shining din man da yake shafawa, sanye yake da wata tsohuwar kod'addiyyar jallabia maroon amma ta koma kalar ash ash pink pink sbda tsabar kodewa. . "Dan Ustaz lafia kaketa gudu kmr agwagwar larabawa?'' Cewar Salwah dataja ta tsaya ita yanayin gudun dan ustaz dinma daria yaso ya bata. Gyara tsayuwa dan ustaz yayi bayan ya matso daf da salwah sbda tsabar gajartarsa salwah na ganin kwanyar knsa shi kuma se ya daga kwayar idonsa sama yake kallonta, ya kai hannu ya shafi gemunsa wanda keta maiqo, se faman washe green teeth dinda yakeyi yace "wato ainifin hajiya yar karama, ni nan da kk gani na a kasa me tsarki aka haife, ainifin shiyasa kika ganni na biyo wata halitta a kasar saudia , Amma se akayi rashin sa'arh na biyo agwagwarsu..." Salwah ta kwashe da daria hadi da girgiza kai kawai, tace "Amma ko bakaji ddhba Dan Ustaz a memakon ka biyo larabawa kayi kyau, Amma seka biyo agwagwa!'' Dan Ustaz ya kara fad'ad'a fara'arsa still hannunsa na kn gemunsa yace "Ainifin ni nan, ai matan aljanu sun mace a kaina yafi a kirga! Aiko knga ni din kyakyawa ne, knsan agwagwar larabawa Akwai kyau. '' Salwah ta zaro ido jin dan Ustaz ya ambato aljanu tace "wai! Aljanu fa kace dan ustaz?'' Daga mata kai yy alamar tabbatarwa ya hada da cewa "kwarai ma kuwwa hajiya karama..." Salwah ta jinjina kai tana me daria kasa kasa tace "kai dan Ustaz a rage na gobe...'' Dan ustaz ya hade rai ya wani sha murr, ya fara jawowa salwah ayoyi kn shi wai a dole malami ne baya karya, salwah se uban daria takeyi Dan Ustaz na mugun burgeta shi din akwai sani ne kuma akwai shagala. "Uhm dan ustaz inna biye maka semu kwana a nan bari in wuce kafin amihh ta fito...'' Cewar Salwah data karashe mgnr tana waiwayon kofar fitowa daga falon Amihh dan ganin ko zata fito, nan taga kofar ko motsi batayi, juyawa tayi cikin hanzari ta fara tafia da niyar tabar gurin, dan ustaz ya dakatar da ita ta hanyar cewa ''Dan dakata hajita keremarh wato ainifin inada mgna ne me muhimmanci dake...." Salwah ta dakata jin dan Ustaz yace mgna me muhimmanci tace "maza ka gayamin, bnso Amihh tazo ta ganni a nan..." Dan Ustaz yayi murmushi kana ya ci gaba da mgna "Ainifin nace dama, ina ita wannan yarinya me dankaran kyau?'' Salwah ta zubawa dan ustaz ido ta gano hilwah yake nufi amma tayi kmr bata gane ba tace ''wa kake mgna?'' Dan ustaz ya kara murmusawa yace ''Ainifin ina nufin wannan bakuwa taku me mugun kyaunnan, Wato anifin Wannan me kama da larabawar.." Salwah tace "ok Hilwah?'' Dan ustaz yayi jim yana me jinjina sunan hilwah a ranshi shi bema taba jin sunanta ba se yau, maimaita sunan ya shigayi a fili yana me kara jan gemun nasa, ysna murmushin jin ddh yaci gaba dacewa ''Hilwah! Hilwah ! Hilwah! Tebbas wannan suna nata ya dace da addinin musulinci kuma Ainifin ya dace da ita, Hilwah! Me kyau kenan a kalmar larabci aka masa kwaskwarima! Wayyo Allah na kaga zuciata, na kamu da kaunar wannan yarinya me Tsananin kyau irin na jinnul mahya..." Dan ustaz ys karashe mgnr yana daga knsa sama, ya hada hannayensa biyu alamar yana rokon ALLAH. Salwah data zubawa dan ustaz ido yanata hauka dan ita a ganinta hauka yakeyi. "Allah rabamu da jinnu, wannan fa mutum ce dan ustaz ba jinnu bace...." Dan Ustaz yayi murmushi harda farfar da kwayar ido yaci gaba dacewa ''Wato ainifin nasani, nasan ita mutum ce, kyauntane ya gigitani Masha Allah! ni de ina sonta Ainifin so na tsakani da ALLAH, wato ainifin nan Aurenta ma zanyi in kaita can kauyenmu mu raya sunnarh ma'aiki salallahu alayhi wasallam..." Salwah ta kara zaro ido waje tana kallon dan ustaz bata tabbatar beda hnkli ba se yau gaskia tama fara tunanin yanada takadda a gidan mahaukata. "Kai dan Ustaz ka kiyayi knka wlhy, hilwah kakeso,..'' Dan ustaz ya daga mata gira hadi da kama kugu kmr mace, damanshi d'abi'arsa kenan yace. " kwarai ma kuwwa, wato ainifin ni nan ba sonta nake ba kaunarta nakeyi....'' Salwah ta Kara zaro ido tace ''kai anya kuwa dan Ustaz kanka daya? Matar yah AB'ILAL dince kakeso?'' Dan Ustaz ya yatsina fuska jin ta kira sunan wani namiji wai AB'ILAL yace "Ainifin wa'izubillahi! Salamun salamun! Astagfurillahi! Wato nace waye kuma wannan gajan, ainifin da kk fad'a, to ko ya aureta seya saketa ya barmin ita ni in aureta, ainifin nake gaya miki sonta a raina ya hayayyafa yayi jikoki ya koma kaunah..." Salwah ta riqe baki, tana kallon Dan Ustaz yanata raftago zance na bnza da hofi, girgiza kai tayi, ta bude baki zatayi mgna taji an bude kofar falon Amihh, tasan Amihh ce ba tare data waiwayaba ta ruga a guje ta bar gun ta nufa side din AB'ILAL. Dan ustaz ya bita da ido yana yatsina baki, shifa harga Allah da gaske yake son yarinyarnan yakeyi. Hajiya maryam data turo kofar falon ta fito cikin sauri sauri take tafia, dan Ustaz ya rugo a guje inda take, ya tsugunna ya fara jero mata gaisuwa "Ainifin nace ina wuni hajajju mutanen mekkah ya aiyukan naki ainifin ya asibitin naku ya fama da marasa lafia na gida dana waje, ya dangi kuma ya yan uwa, ya qawayenki ya zirga zirga , ya hkri da hidima damu ma'aikata, ya kuma ita wannan yarinya me kyau, Wato ainifin hilwah, Ainifin nace hajiya ya danginku na can kasar saudi arebia..." Hajiya maryam ta saki baki tana saurarom gaishe gaishen dan ustaz ke mata na hauka, girgiza kai kawai tayi ta wulla masa car key dake hannuta tace "bnsn hauka wuce muje, magajin gari..." Tana fadar hkn ne tana tafia, da wasu files a hannunta dayawa, ta nufa motarta dan Ustaz ya tashi daga tsugunnen ya biyota a guje yana gudun yana faduwa yana tashi sbda tsantsin takalmin dake kafarsa Kafin ya karaso yayi faduwa tafi goma amma kuma yana tashi, ya karaso ya nufa dreva seat ya shiga hajiya maryam kam tini ta dade a cikin motar a gidan gaba, dan Ustaz yaja motar suka fice a gidan....

Koda salwah ta karasa dakin kwance ta samu hilwah a kasan carpet din tini ma bacci ya dauketa, se sauke ajiyar zucia takeyi dagani a wahalce take ajiyar zuciar. ajiye mata mgnin salwah tayi ta dauko duvet din dake kan bed din, ta lullubeta dashi, ajiyar zucia hilwah ta sauke ta kara kudindinewa a cikin duvet din tana me kara sauke ajiyar zucia, hadi da shashsheka. Salwah ta tsaya ta zuba ma fuskar hilwah ido, kasancewar bata lullube fuskar tata ba. Zucia cike da tausan hilwah salwah ta ta tsugunna ta dauki trea din data kawowa hilwah breakfast din ta juya ta fice a dakin, ta nufa side din Amihh, direct kiching ta nufa dan hada abincin rana sbda yau zataje scul tanada lecture 2:am, kiching din ta isa ita da Ma'aikatan gidan suka shiga hidimar abincin ranar....

A bangaren AB'ILAL Be samu bacci ba kwata kwata sede ya gaji da juyi ya tashi dan knsa wuraren 10:30am ya sauko daga kn bed din , yana me jin knsa na juya masa na rashin baccin da beyi ba, fadawa bathroom yayi, seda ya kwashe 1h a bathroom yana wanka, kana ya fito bayan ya dauro alwala, ya goge jikinsa sosai, kana ya shafa kyakyawan lotion dinsa ya shirya cikin danyar shadda mint color dinkin kaftani, dinkin ya matukar amarshi ainun, kasancewar yau juma'arh ce shirin zuwa masallacin yakeyi. ya feshe ko ina da ko ina na jikinsa da perfume , ya dauki hula ya kafa wadda ta dace da tsarin shaddar dake jikinsa, fuskarnan tasa ta fito das, sajensa ya kwanta luf se shining yakeyi yana walwali, ya hadu iya haduwa! Nan take ya fito a zallar asalinsa na me kyau, kallo daya zaka masa ka fahimci cewa shi din ruwa biyu ne Wato de ba zallar nigeria bane shi, sbda kyaun nasa ya shahara, ya fito sosai zanensa ya zanu tako ina cif cif das das, shu'umin kyau garesa hadi da makirin kyau tako ina ya cika taf, yanada cikar haiba, kyaunshi na bugawa ne a mujallah , ya hadu iya haduwa, ko a indian film ban taba ganin me kyaunshi ba. dauko makirin watch dinsa yayi ya daura a tsintsiyar hannunsa, ya kara fashe jikinsa da turarensa, ya zira takalminsa me mugun tsada, ya kara fashe jikinsa da perfume dinsa, again and again sbda shi din ma'abocin kamshi blne, baya gajia da kamshi. ya dauki counter dinsa dake kn mirorr da car key ya fito falon se zuba kamshi yakeyi, dai dai agogon bangon falon ya buga karfe shabiyun rana dai-dai. tsayawa yayi ya zubawa inda ya bar yarinyar dazu tana kuka da ido , kawai se yaji jikinsa ya masa wani iri se hasko yarinyar yakeyi a durkushe a gun, rintse kwayar idonsa yayi na wasu yan daqiqu kana ya budesu jiki a sanyaye ya juya ya fice a Falon, fitowa compound yayi, yana takunsa na isa tamkar dawisu ma'aikatan gidan nata miko masa gaisuwa amma sam be bi ta knsu ba, tafiyarsa kawai yaci gaba dayi, shaddar nan tasa se faman walwali takeyi tana daukar kwayar idon me kallo. Direct ya nufa packing space karasawa yayi cikin gareji ya fito da motar daya sewa hilwah daman key dinta ne a hannunsa, yasa me wankin mota ya wanke masa ita yana daga nan zaune a kn wata kyakyawar kujera ta hutawa dan Ustaz ne ya dauko masa kujerar ganin da yana tsaye. yana daga zaunen yana danna wayarsa har aka gama wanke motar aka gogeta dmn batayi wani datti ba sbda ko a garejin an lullubeta da rigar mota. shiga motar AB'ILAL yayi ya figeta ya fice a gidan ya nufa babban masallacin santan bello, daman a nan yake juma'arh inhar yana nan kaduna....bayan sun idar da sallarh ya fito suka hadu da Alhaji babba, kasancewar shima a nan masallacin yake sallarh juma'arh. Karasawa AB'ILAL yayi ya gaidashi dukda haushinshi yakeji sbda yasan hadda sa hannunshi a auren da Amihh ta masa, bayan sun gaisa Alhaji Murtala ke tambayar AB'ILAL ya iyalin tasa, AB'ILAL yayi kmr be gane me yake cewa ba, ya canza akalar hirar zuwa ga tambayarshi yaushe ze koma kasar USA sbda a can ake duba masa lafiar jikinsa..'' Alhaji babba yace yana tunanin se Nan da 2 month ab'ilal ya jinjina kai kawai dmn ya kawo mgnr ne dan ya canza akalar bnzar tambayar da alhaji babba ya masa. Daga bisani yama Alhajin sallamah ya nufa motarshi ya shiga yaja ya bar masallacin , shima Alhaji babba ya shiga tashi motar dreva yajashii subaka bar masallacin. Ab'ilal na isowa gidan direct side din Amihh ya nufa dan samawa knsa abinda zeci, yana shiga dai-dai salwah na riqe da trea tana shirin barin side din zuwa side din AB'ILAL din domin ta kaiwa hilwah abincin rana. AB'ILAL Yayi kmr ma be gnta ba. ta gaidashi yaki amsawa kawai ya nufa dinning ya zauna, salwah na nan tsaye tsakiyar falon kmr an dasata, ta daga kafa da kyar ta fara tafiya da niyar ta fice a falon, ta tsinkayi muryar AB'ILAL na cewa "Ke zo kiyi serving dina...'' Jiki na rawa Salwah tace to ta dawo ta ajiye trea din dake dauke da abincin hilwah a kn dinning table din, ta fara bubbudewa AB'ILAL kulolin dake kan table din, abinci Kala biyar ne amma AB'ILAL yace duk basu masa ba. Ya umurce salwah data shiga kiching ynzu ta dafa masa tuwan shinkafa miyar kubewa danya. Takaici kmr ze kashe salwah gashi tanaso ta kaiwa hilwah abincinta a hk ma tasan ta batta da yunwa, gashi tanaso taje scul tanada lecture 2:am gashi ynzu ma 2:am din ta kusa befi 15mnt ba 2:am din tayi. Zucia babu ddh kuma ba damar ta nuna ta juya da niyar ta shiga kiching yace ta fara hado masa coffee tace toh kawai ta juya ta nufa kiching din, a gaggauce salwah ta hado masa coffee din ta kawo masa yanata aikin shafar wayarsa kirar Samsung, ta ajiye masa ta shiga kiching din ta fara kokarin daura masa tuwan xucia babu dadih, tasan de yau tayi missn lecture dinta. Se faman jin haushi takeyi tana aikin tuwon ma'aikatan gidan suka temaka mata gun hada masa tuwon, ta samu ta gama takai masa taga ko coffee dinma besha ba, se faman shafar wayarsa yake har lokacin, ta zauna tana jiran sadda ze gama yace tayi serving dinsa tasan bata isa ba ta bar falon batayi serving dinsa ba. Seda ya mula ya mulmule kana yace tayi serving dinsa, tana gama serving din nasa AB'ILAL ya fara cin tuwon a yangance Salwah nata satar kallonsa se yatsina fuska yakeyi, ya dauki cup din coffee din ya Kai bakinsa yaji ba ddh sbda sanyin da yy, ya kalli salwah yace taje ta kara hado masa wani, Jiki na rawa Salwah ta juya ta koma kiching din ta kara hado masa wani coffee din, ya amsa ya fara sha, ya kalleta yace taje ta masa farfesun kayan ciki yanzunnan..a zucia salwah tace ta shiga uku, kana ta juya ta nufa kiching ta shiga aikin hada masa farfesun Hilwah ce kawai a ranta tasan yunwa nacan tana kwakularta, mkrntarta ta yau kam tini ta hkra da ita...


A bangaren hilwah Ba karamin jin dadin baccin tayi ba at the end, amma a fari baccin be mata ddh ba. se juyi kawai takeyi a tsakiyar carpet din, bata tashi ba se karfe daya saura. ta tashi tana miqar gajiya da ciwon jiki dake addabarta, ta sauke ajiyar zucia hadi da miqewa tsaye ta nufa toilet a daddafe mazaunanta se ciwo suke mata sbda kwanan zaunen datayi se yanzu abun ke tambayarta. Wanka ta karayi da ruwan dumi sosai ta sake gasa jikinta, ta fito daure da alwala azahar kirjinta daure da bathrobe peach , ta karaso bakin mirror ta shafa versiline shi take shafawa dukda ga wasu creams sunfi kala ashirin amma bata shafasu sbda babu wanda take using a ciki shiyasa take shafa normal verselin kawai. Shiryawa tayi cikin wata riga dark green me stone a saman wuyanta sosai rigar ta dameta daf tako ina ta cika taf taf, kasannan nata kmr ze fashe a cikn rigar dake jikinta, ta feshe jikinta da turarrukan dake gaban mirror din wanda sukafi Kala hamsin, duk abinda takeyi cikin dauria takeyi amma batajin ddhn jikinta, side din inda ya maretanma ya kumbura. karasa tayi ta nufa inda aka tanada danyin sallah,

Please Login or Register in order to submit comment