Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tana rawar sanyi shine na kira mata Dr yakub ,good baby ka kyauta bari na dubata abba da ke haurawa upstairs ya ce kice ina mata sannu to mom ta ce tare da shiga ita da jidda, ko da suka shiga a lokacin fatuha tayi bacci cikin tausayawa Mmy take kallanta domin sakanita d Allah take son yarinyar d'aga karshe tayi mata Adu'a suka bar dakin.


yau ko sadiq shi da kanshi ya shirya jidda, sannan su kayi bacci jidda ko sai missing din Anuty fatuha take sadiq ko dadi ya ji komin banza ta saitu.



*taku har kullun Salma mas'ud nadabo*
*CAPTAIN SADIQ*
👮🏼‍♂

*Writing by*
*Salma mas'ud nadabo*

*Edit by*
*Raheenat*

📘 *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*🐄
★we are the best★


http//mobile.Facebook.com/Real-Hausa-fulani-writers-forum RHFWF-173984973194167/?refid=52&red=opare_speed_dial_&_yn=H-R


*Email*:[email protected]


*Facebook*:www.Facebook.com/REAlHAUSAFULANIWRITERSFORUM.com


45_46


*Yan uwa kuyi hakuri jiya nayi mstk maimakon nasa 43_44 sai nasa 43_45 ina fatan zaku min uzuri yauw zamu tashi d'aga 45_46 ina fatan kungane ni Salma ina Al'fahari d'aku Nagode sosai yanda k'uke son wanga littafin nawa Allah Ubangigi yabarmu taré Ameen....wanga pag din sadaukarwane gaduk mai bin labarin I love you ol my fan's😍😍🤸🏻‍♂*



Misalin karfe 6:00am na safe fatuha ta tashi Alhamdulillah jikin nata da sauki, à hankali ta sauko d'aga gadon ta shiga toilettes wanka tayi tare da yin arwala ,tana fitowa tasa doguwar Riga ta shimfida daduma domin gabatar da sallah ,kasan cewar yau juma'a tana gamawa ta cire rigar ta saka wata Riga da wando mai mai ruwan zumuwa Rigar ya tsaya mata har gwuwa ba qaramin kyau kayan suka mata sai suka fido da ship din ta sosai veil din kayan ta dauko se yar hoda data Murza se lipstick ta sama lips din ta , tayi kyau masha Allah direct part din sadiq ta wuce a dai dai bakin kofar ta ci birki ta zaro idanuwan ta har ga Allah yanzu Sadiq ya fara bata tsoro daure, fuska tayi à hankali ta murda handle din kofar, parlour ba kowa sai sanyi AC da ke tashi da kamshi a hankali ta qarasa kofar bedroom ta murda a hankali sadiq ta hango gaban dress mirror, sanye da bathrobe yana goge gashin kan shi cikin sallama ta qaraso bedroom din ciki ciki ya amsa kamar me koyan magana jidda dake zaune saman bed itama sanye da bathrobe da alamar da ya gama gyara kanshi ze gyarata washe da baki jidda tace Anuty tare da rugawa a rungume ta bata fuska tayi tace "Anuty ashe baki lafiya shine baki fada min ba? ta ida zancan tana bata fuska" murmushi fatuha tayi tace "Ai yanzu na warke sauki ranki Jidda ta" toh shikenan Anuty sadiq ko harkar gaban shi yake fatuha kuwa sai binshi take da ido a sace ohni mutun sai shegen kinibibi kamar mace dan gutun tsaki fatuha ta ja tare da daukar jidda suka fita.


Bedroom ta dire jidda ta shirya ta cikin uniform din ta, sannan ta raba mata gashin ta gida biyu taja hannun ta suka wuce dining area ,mom da abba na zaune a dining area cikin natsuwa ta qaraso ita da jidda ta gaishe su mom cikin ladabi a tare suka amsa tare da yimata ya jikin, washe da baki tace da sauki jidda ta jama kujera ta zauna sannan ta fara saving nata tana cikin saving nata sadiq ya qaraso dining area gaishe da su mom yayi tare da yi masu pack sannan ya samu kujera ya zauna masha Allah ya sha kyau har ya gaji, kallo daya fatuha ta masa ta kauda kai cikin tsanar sa Amma duk da haka sai da ta yaba kyau irin na sadiq har mamaki take anya akwai wanda ya fishi kyau kuwa musanman yau da yake sanye da manyan kaya, tunda ta zo gidan yau ce rana ta farko data fara ganin me kyau da manyan kaya shada ce sky blue yasa tasha dinki da dark blue zare anmai irin dinkinnan na sarauta se hula blue mai ratsin dark blue , hannu ya kai ya dau cup ya fara hada tea dan shi mutun ne ba mai san yawan cin abinci , bayan ya gama hada tea ya fara sha a hankali mom ce ta kalle shi tare da cewa baby karka ce min yau ma tea kadai zaka sha lagwabe kai yayi yace eh, haba baby wai me yasa baka san cin abinci ne eh abba da ke gefe yace "Sai kace ba soja ba sojoji da aka sani da cin abinci , shagwabe fuska yayi ya cigaba da shan tea din ganin mom nata magana yasa shi cin chips din kadan fatuha sai da tabatar jidda taci ta koshi sannan ta kyale ta bayan sun kamala cin abincin sadiq ya dau jidda fatuha na biye da su da lunch box har bakin mota , sannan jidda ta mata pack ta shige mota juyowa tayi ta shigo gida da abba ta ci karo mom ta rako shi riqe da briefcase din shi wuce su tayi ta koma dining area chips ta Zumaba da farfesun kifi bata wani ci da yawa ba saboda har yau bakin ta ba dadi bayan ta kamala ta fara kokarin kwashe kwanikan ,mom ce shigo washe da baki tace "Haba fatuha ke da baki da lafiya ina ke ina aiki ki ?zauna ki hutu" washe baki fatuha tayi tana qoqarin yin magana mom ta hanata kwalawa rabi'a kira tayi cikin ladabi rabi'a ta qaraso tayi ta d'urkusa har kasa ta gaishe da mom , yawa rabi'a kwanikanan zaki kwashe sannan yau ki je ki gyara part din sadiq saboda fatuha bata jin dadi har cikin zuciyar rabi'a bata so mom ta ce ta gyara part din sadiq ba saboda basa wani shan inuwa daya jiki ba qwari ta kwashe kayan dining area din fatuha kuwa daki ta koma tasha magani bata wani dadi ba bacci ya kwasheta.


A cikin school yayi parking din motar shi tare da zagayowa ya budewa jidda murfin mota ,ta fito lunch box din ya miqa mata tare da yi mata pack ,daddy am going to miss u , I now angel karki damu anjima in an tashi ni zanzo daukar ki kin ji angel murmushi tayi tare da yi mai pack ta shige class yana kallan ta har ta shige ,shi kuma ya wuce wajan aiki taré da kaunar diyar tashi.


Ba ita ta tashi daga bacci sai karfe 11:30pm ita kanta tayi mamaki baccin da tasha, toilet ta shiga tayi wanka ta fito tare da shafe jikin ta da lotion wardrobe ta bude ta ciro atamfa brown me ratsin black n white atamfar ta hadu riga da skirt dinkin ya mata kyau qarewa kanta kallo tayi ta cikin dressing mirror murmushi ta saki tare da cewa gaskiya birni tayi dubin yanda na koma kamar ba fatuha inna ba duk wannan zancan tana yinshi ne a zuciyarta, murmushi takara yi tana qoqarin kama gashin kanta bude kofar da akayi ne yasa ta saurin waigowa a tunanin ta Jidda ce sai taga hanan washe baki tayi tare da cewa "Hanan cikin fara'a" hanan ta qaraso dakin sanye take da lace sky green mai ratsin black se veil din ta white ba qaramin kyau tayi ba ta fito yan'matan sak, zama tayi saman bed tare da cire veil din wash na gaji wallahi dariya fatuha tayi wai kin gaji, aiki me kikayi da kika gaji? murmushi hanan tayi tare da cewa "Kai fatuha karki ce min wannan uban gashin naki ne?" fari da ido fatuha tayi tace na hanan ne bugu hanan ta kai mata cikin wasa kai Amma fa kin ji dadi murmushi fatuha tayi tace "Ina Jamal da afra?" suna parlour tare da grandma nima tanbayar ki nayi sai grandma ke ce min baki ji dadi ba shine fa na shigo na maki sannu toh ashe har kin warke kin fara make up ta ida zancan cikin tsokana, dariya fatuha tayi ta ce "Wallahi naji sauki danma mom bata barni nayi aiki ba" ai ta kyauta wallahi amma yau baki je school ba eh exam muke na JSCE shiyasa ban je ba yau bani da paper Jamal kuma fever yake shiyasa, murmushi fatuha tayi ni wallahi ina san makarantar nan se ma na shirya jidda zata tafi sai naji kamar na bita, ai karutu akwai dadi akwai wahala kiyi ma mom magana mana smile fatuha tayi tare da cewa toh jidda ce ta shigo bedroom din ta fada jikin fatuha murmushi tayi tace "Yan makaranta har andawo kenan?" daga mata kai jidda tayi ta eh Anuty kin ga daddy ya siyo min ice cream da zamu dawo har da chocolate da yawa kuma fa naba daddy naki ya aje mana murmushi fatuha tayi ta ce toh ,a zuciyar ta kuwa cewa tayi tap wannan daddy naki ai sai ke hanan ce ta katse mata tunanin da cewa bari naje wajan uncle nima na amshi nawa tana fadin tana qoqarin daukar veil din ta zata fita , fatuha inkin gama shirya jidda ki same ni a parlour muyi lunch toh tace mata to bawai dan tasan me hanan ke nufi da kalmarta na qarshe ba daukar jidda tayi ta shige da ita bathroom ta wanke ta tas sannan suka fito ta shafeta da mai tare da Samata gwon pink me qaramin hannu se gashinta da ta gyara mata tayi kyau sosai masha Allah.


Direct parlour suka fito Anuty bilki na saman two star zaune, mom na zaune saman three star suna kallo gaishe su tayi mom tayi mata ya jiki ita da Anuty bilki da gudu jidda ta koma wajan Jamal da ke zaune saman daya daga cikin kujerin dining area itama ta zauna cikin fara'a fatuha ta qaraso ta fara saving din su , hanan dake saukowa daga upstairs tana zunburo baki gaba cikin bacin rai ta qaraso dining area din fatuha ta kalle ta tace, "Lafiya naga kamar an bata maki rai ?"dan guntun tsaki taja wallahi uncle ne ya bata min rai shi kullun cikin bakin rai maganar arziqi ba taba hada ku dashi, murmushi fatuha tayi tace "Yi hakuri kinji zauna mu ci abincin mu in mungama mu fita farfajiya shan iska" yawa tawa abinci suka ci cikin nishadi bayan sun gama fatuha da hanan suka kwashe kwanikan sunka kai kitchen sannan suka fita farfashi jiyar gidan domin shan iska.

Saman resting chair suka zauna ,suna dan taba hira fatuha ba qaramin jin dadi gurin take ba saboda har da yan shuke shuke lumshe ido tayi ta ware su, kai fatuha karki ce min wai bacci kike ji ah ba bacci nake jiba kawai wajan yamin ne ina san guri kamar haka, shiyasa sanda nake akauye kullun muna bakin rafi ni da fatsima murmushi hanan tayi sun dade sosai a filin gida suna hira kiran sallah magrib ne ya tashe su a wajan suna tafe suna hira ,sadiq da ke qaqorin fitowa zai je masallaci sanye da jalabiya milk fatuha bata lura ba ta fada mai dan ita bata gani tana rike da hanan wata iri tsawa sadiq ya daka mata Wanda yasa yan hajin ta katsawa hanan ko take ta kama gefe jikin fatuha ta rabe, harara ya aika masu su duka stupid girl's kuna tafiya kuna kalle kalle baku kallan gaban ku mtss sannan ya sa kai ya fita. sauke ajiyar zuciya hanan tayi ta ce ba dai jaraba ba mtss sannu indai uncle ne haka yake kullun cikin bakin rai da hargowa, murmushi fatuha tayi tace ni zan fada maki haka sannan suka shige cikin gida.


*Fan's kuyi hakuri da wannan page din am to busy shiyasa nayi shi ba yawa*

*Taku har kullun Salma mas'ud nadabo*
*CAPTAIN SADIQ*
👮🏼‍♂

*Writing by*
*Salma mas'ud nadabo*


*Edit by*
*Raheenat*


http//mobile.Facebook.com/Real-Hausa-fulani-writers-forum RHFWF-173984973194167/?refid=52&red=opare_speed_dial_&yn=H-R


*Email*:[email protected]

*Facebook*:www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERSFORUM.com



47_48

Bayan su idar da sallah parlour suka dawo suna kallo , kitchen fatuha ta shiga anan ta iske baba jinmai tana farfesun yan'ciki gaishe ta tayi cikin sakin fuska ta amsa mata tare da yimata ya jiki ,da sauki ta bata amsa tana qoqarin bude fridge fruits ta debo ta zuba a ball na glass tare da wankewa sanna ta dauko wuka parlour ta koma hanan da ke zaune saman one star ta duro qasan carpet tare amshe wuqar,t ace "Bari ni na yanka fruit din? kinga ke bakida lafiya" harara fatuha ta aika mata waya ce maki bani lafiya? lafiya ta lau inda za'a auna mu qilama na fiki lafiya dariya hanan tayi ta ce "Wasa kenan" tare da cigaba da yanka fruit din sai da ta gama yanka fruits din sannan ta maida wuqar ta dawo parlour suka fara cikin fruit din cikin jin dadi suna kallo suna taba hira.


Anuty bilki ce zaune saman sofa mom na saman bed zaune, mom yanzu sai yaushe zaku dawo? wallahi ban sani ba amma nasan sai mun kai 2week tunda shi wancan zuwan da yayi se da yayi kusan 3week, shagwabe fuska Anuty bilki tayi amma fa gaskiya mom zamuyi missing naki wallahi, murmushi mom tayi tare da cewa ah kanku bazan zauna ba naqi bin tsohon mijina ba akan Wanne dalili zan barshi kullun yana zuwa uk ni ina Nigeria ni mai ya'ya, ya'yan da suna gidan miji, dariya Anuty bilki tayi kai Mom harar ta wurga mata kinga in ta kuramin zakiya tashi ki ban gu kona samu na cigaba da hada shirgi na, ah Mom wato kaya zaki kwasa da yawa kenan? laaaa yau Allah ya kawo mu ya' na tirtse uwar ta Dan zatayi tafiya da uban ta , toh kaya zan diba da yawa kika bata min rai wallahi har wata sai muyi ta ida zancan tana bude bedside drowe baqar leda ta curo ,yauwa ga wannan tun wancan satin na so na aiko baby ya kawo maki, to ban samu dama ba washe baki Anuty bilki tayi kai Amma fa mom naji dadi Allah yasa wannan maganin irin wancan ne gaskiya wancan naji dadin shi murmushi Mom tayi tace "Ai ina tunanin wannan yafi wancan, dan wannan dan sudan ne" amma fa na gode Mom kamar kinsan gobe zai dawo toh ai shikenan daya garin da madara ake sha duk dare shi kuma dayan da zuma ga turaruka nan masu kamshi in kina anfani da su ko cup kika riqe sai yayi kamshi, washe baki Anuty bilki tayi mom thanks kamar kin san abban hanan nasan kamshi sosai wallahi , ah daughter waye baya san kamshi ?sai dai in Mutum bai samu ba kamshi na da muhinmanci sosai daughter ko kamshi kika riqe to wallahi kin riqe mijinki à wannunki, haka Anuty bilki ta riqa jerawa mom godiya agogo ta kalla kusan 8:30pm Mom bari muzo mu lalaba mu tafi gida dare ya fara yi, bada'n gobe abban hanan zai dawo ba da mun kwana wallahi, ai ko ba bazai d'awo gobe ba ban zan bari ki kwanar min gida ba, ke kullun kika zo yini sai ki bige da kwana ?ai hakuri ake a zauna har miji ya dawo ya same ka ba wai ka kwaso kafa kazo gida ba, mayafinta ta janyo da handbag dinta ta tura bakar ledar ciki fitowa sukayi daga bedroom din Anuty bilki na gaba mom na bayan ta suka sauko daga upstairs sai da ta iso parlour ta yafa mayafin ta ,su hanan da ke zaune parlour suna shan fruit Anuty bilki ta qaraso hanan ku tashi mu tafi dare nayi ,bata fuska hanan tayi tace "Momi na fa dauka sai 9:00pm zamu tafi "ai kin san bana san driven din dare ko ?kuma ba da driver nazo ba hanan bata so su tafi yanzu ba da ba exam suke ba da nan zata kwana fatuha ma haka bata ji dadi ba saboda in hanan ta zo tana dibe mata kewa Anuty bilki ce ta katse masu tunani da cewa "Hanan yima baba jinmai magana zamu tafi ta baki afra "bata ida rufe bakin ta ba sai ga baba jinmai riqe da hijabin ta a hannu afra na goye a bayan ta washe da baki tace ah kuma har kun fito yanzu na ke cewa bari na kawo maki Afra yau nama yi daran tafiya da yake na tsaya yima mai gida farfesu, mom ce ta ce ku dai baku ji baby ya sata farfesu ke kuma kin miqa mata diya tana ta fama ga afra da shegen kuka ,ba komai ai kuma ko kukan ba tayi ba Allah ya taimake ki shi kuma baby bayan yasan baki wuce magrib shine zai daura maki wahala, murmushi baba jinmai tayi tana qoqarin miqawa hanan afra ,dariya Anuty bilki tayi tace mom da kin bar shiga tsakanin baba jinmai da baby ko ka shiga kai zaka sha kunya murmushi mom tayi ,to ai sai mu wuce tare sai na sauke ki gida baba toh shikenan tare suka fito fatuha na kusa da hanan sunata zuba surutu jidda na riqe da hannu Jamal duk suka rako su filin gida , Anuty bilki na qoqarin bude murfin mota sadiq ya shigo tsayawa tayi tana sakin Murmushi qarasowa yayi yace "Sister har zaki tafi ?na dauka kwana zakiyi ai ya fadi cikin zolaya, harara ta maka mai baby ka rainani wallahi dariya yayi baba har dake zasu tafi da niyata na kai ki, ah ba komai Hanan dake kusa da fatuha sai turo baki take sadiq ne ya kalle ta tare da aika mata harara sister na kusa fara cima hanan naga kwanan wani rashin ji ke damun ta, ni ba ruwana wannan tsakanin ku ne, toh shikenan raurau da ido hanan tayi tare da cewa uncle sorry harara ya kuma aika mata ganin be da niyar hakura yasa ta tabe baki ta shige mota tana yima fatuha bye bye su duka suka shige motar Anuty bilki tace "In anyi hutu this time around jidda a gida zatazo" toh ya ce mata ai sun kusa fara exam I think this Monday zasu fara eh Anuty bilki tace mai tare da ja su suka bar harabar gidan sannan su fatuha suka jiyo riqe take da hannu jidda.



Direct bedroom suka wuce sadiq kuma ya wuce dining area , ko da suka shiga bedroom fatuha ta dire jidda tayi mata wanka sannan itama tayi kusan tare suka shirya saboda itama yau ta gaji tasha surutu har da godema Allah, night dress suka sa sannan ta dau jidda tana mata surutu suna haurawa upstairs a hankali ta murda handle din kofar part din sadiq, a parlour suka iske shi zaune yana kallan news da gudu jidda ta fada jikin shi ,daddy yes angel ,um daddy ina ice cream din Anuty da chocolate din ta? laqace mata hanci yayi yace "Yana bedroom da gudu jidda ta shige bedroom fatuha kuma na qoqarin fita har ta bude kofar, jidda ta qaraso riqe da ledar shopping Anuty ga naki , angel har dani a tsarabar washe baki jidda tayi ta ce eh toh na gode ta amsa ta fita.


Direct bedroom din ta ta shige tare da kunna haske, saman bed ta zauna tare da bude ledar shopping din tun kan ta fara shan ice cream din miyan ta ya tsinke ,tana sha tana kada kai Amma fa wannan abu akwai dadi sosai gaskiya me kyau yasan kan kwadai, sai da ta cika cikin ta da ice cream sannan ta kwanta bacci yayi awan gaba da ita.



Akwana a tashi ba wuya wajan Allah sadiq ne janye da trolley din mom dana abba sai da ya zo bakin kofa ya ba ola da Sunday yayi musu umarnin da su sa kayan bayan boot, ok boss fatuha ko na parlour zaune sai tsoro take yanzu idan su mom suka tafi Allah ka dai yasan muguntar da sadiq zai mata ranan unguwa ka dai suka je amma sai da ta dandana kudar ta, bale kuma kwanaki duka wannan zancan a zuci take tare da kukan zuci dan tasan watan cin uban tane ya tsaya, su mom ne suka qaraso parlour tana riqe da hannu jidda sai lisafa mata tsaraba da zata mata take washe da baki fatuha ta tashi tana yi masu Allah ya kiyaye hanya , mom har ta kai bakin kofa ta juyo da kalli sadiq tace toh ga amanar fatuha sauran kuma inna dawo naji ka mata wani abu dan nasan halin, bata fuska yayi kamar qaramin yaro yana bin fatuha da harara tuni yan hanjin ta suka fara kadawa dan tasan kashin ta ya bushe daurewa kawai take amma ji take kamar ta daura hannu aka ta sa ihu gashi baba jinmai taje biki kauye daga ita sai rabi'a kuma rabi'a data gama aikin ta take tafiya ,jidda ce ta katse mata tunanin datake taré da janta tm har suka qarasa farfajiyar gidan, sadiq ne ya shiga wajan zaman driver da alama shi zai kaisu airport tuni jidda itama ta shige motar mom ce ta juyo tace fatuha duk abinda kike buqata kiyiwa baby magana kinji toh tace mata tana raraba ido tana daga masu hannu har motar su ta fita daga harabar gidan.


*Taku har kullun Salma mas'ud nadabo*
*CAPTAIN SADIQ*
👮🏼‍♂

*Writing by*
*Salma mas'ud nadabo*

*Edit by*
*Raheenat*

📘 *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*🐄
★we are the best★

http//mobile.Facebook.com/Real-Hausa-fulani-writers-forum RHFWF-173984973194167/?refid=52&red=opare_speed_dial_&yn=H-R


*Email*:[email protected]

*Facebook*www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERFORUM.com



49_50

Su sadiq na fita harabar gidan, fatuha ta juyo gida cike da tsoro raurau tayi da ido kamar tayi kuka saboda tuntuni rabi'a ta tafi sai ita kadan kwal a gidan sai su ola, parlour ta zauna tayi tagumi kamar munafuka tana ta raraba ido kamar wadda tayima sarki qarya, ganin tsoran ba zai fishe ta da komai ba yasa ta kuna kallo washe da baki ta dau remote control tana canza tashoshi Bollywood ta kai tayi shiru tana kallan film gaba ki daya imanin ta naga TV jin cikin ta ya fara kukan yunwa yasa ta tashi dining area taje ta zubo macaroni da miya yaji kifi sosai kasan cewa fatuha ba mai san macaroni ba ce yasa ta zuba kadan, ta dawo parlour saman three star ta zauna ta Fara ci bayan ta kamala ta kai plate din kitchen tare da wanke wa bedroom ta koma tare da rage kayan jikin ta ta shiga wanka bata wani dade ba ta fito ko da ta fito lotion ta shafa tare da feshe jikin ta da turare white t-shirt din ta na aiki tasa kasan cewa rigar ta kawo mata gwiwa sai taji bata sha'awar sa skirt din gashin ta ta baza ta sharce masha Allah fatuha ba qaramin kyau tayi ba ,qarewa kanta kallo tayi a dressing mirror dariya tayi tace "Kai dan Allah dubi yadda nayi kamar ta cikin film din dana gama kalla hhhh lol" ta kumayin dariya tana godéma Allah da yawadata ta da gashi à haka tasa kafa tafita daga bedroom din.


Bangaran su sadiq har yana kai su mom airport , ya wuce da jidda family house dan shi yama manta da wata fatuha part din ammi ya shiga riqe da hannu jidda , a'a wana ke gani , murmushi sadiq yayi tare da zama saman kujera yana gaisheta sannan yace, "Matar yanaga kin qara kyau?" washe baki ammi tayi tana

Please Login or Register in order to submit comment