Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba, lumshe ido yayi tare da ware su a k'anta murmushi fatuha ta saki mai cike da sakwanni iri-iri, rufe idanuwan ki kiga wani abu cikin sauri da zakuwa ta lumshe idanuwan ta wani dan kit ya fido tare da bude kit din oya bud'e wata hadadiyar sarkar gold ce wani irin ihu fatuha tasaki tare da rungume sadiq ,shima rungume ta yayi tare da kai hannu saman gashin ta yawarware daurin data mai. cikin cool voice din shi yace "Gashin ki yafi kyau a h'aka" smile tayi tare da dagowa d'aga fafadan qirjin shi ta juya baya tana facing din dressing mirror tare da matsar da gashin ta gefe samata sarkar sadiq yayi ba qaramin kyau sarkar ta mata ba juyowa tayi tare da cewa "Uncle na gode" murmushi sadiq yayi nike da Godiya fatuha yau kusan shekarana uku bana tunanin, bana zuwa asibiti .murmushi ta saki tare da fita d'aga d'akin tana Isa parlour ta fad'a jikin mom, mom kin ga sarkar da uncle ya siya min? murmushi mom tayi irin nasu na manya amma dai gaskiya mun gode wannan kyau ta haka, lokacin yayi dai-dai da fito warshi d'aga bedroom din fatuha, angel ce ta turo baki tace "Daddy ni fa☹?" ja mata kumatu yayi tare da fido mata zube na gold ya sa mata murmushi ta saki love u daddy tare da yimai pack, lalai abin ma yar h'aka ce kenan? yaran ka kawai ka Sani ni Kuma ko oho mom ta fada, bayan mom yaje tare da zuro kanshi ta wuyan ta sorry mom next time ke zan siyawa kin ji Dan smile tayi sannan shima ya zagayu ya zauna sun dade suna hira sannan kowa ya wuce bedroom din shi.


Bangaran majeed ko cikin farin ciki ya koma gida, ko da umma ta tanbaye shi sai ce mata yayi ya kusa cika mata burin ta, murna ko har ba'a magana ko da ya koma d'akin shi da ya rintsa ido fatuha yake gani h'aka ya rinqa juyi saman bed har bacci barawo ya sace shi.


*Asuba ta gari*

Kasan Cewar yau weekend fatuha ta shiga kitchen tare da su baba jinmai suna aikin suna zuba hira kunsan a tare suka gama komai ,da misalin karfe 10:30 take tsaye gaban dining tana jera kayan abincin cikin natsuwa sallamar da kayi ne yasata dagowa tare da kallan kofar ta amsa a taqaice majeed ne ,sanye da shada ash tasha aiki sai kamshi yake zubawa dining area yanufo tare da yin smile fararan hakoran sa suka bayana. gyara murya yayi tare da cewa "Dama ashe kyawawa na aiki, gaskiya kamata yayi ace warhaka kina barcci ?" dagowa fatuha ta danyi a tunanin ta tuntuni ya shige ciki dan tasan kowaye a gidan saboda tasha ganin pics nashi dan murmushi ta saki cikin yauki tace "Suwaye kyawawa anan? naga dai ni kadai ce ta ida zancan tana wai gawa" murmushi ya Kuma saki a qaro na biyu fatuha kenan duk inda wata kyakyawa take kin kai ai, idanma b'aki sani bâ to y au zan fada miki."wallahi kin h'ada d'uk wani abun da ake nema wajen wata y'a mace, yar dariya ta saki wallahi yau uncle da tsoka ka zo gidan nan ko?yau dai ranar tsokana ce? b'ata ida rufe b'akin ta ba sadiq ya shigo sanye da kayan gym din shi da alama d'aga gym ya d'awo, tunda yaga fatuha da majeed tsaye gabaki daya anurin fuskar shi ya sauya kamar an aiko mai da mutuwa daurewa yayi ya qaqaro murmushi my man yaushe ka shigo? wallahi yanzu na shiga bama kowa parlour sai wannan kyakyawar d'ake ta zuba aiki, Ni fa ko kallan ta ma kake ya Isa ya kosar da mutun d'aga yunwa .wani irin kallo sadiq ya wurga ma fatuha tare da bin kayan jikin ta da kallo gown ce mai kyau sai dai ya matseta duk wata sura na jikin ta ana gani, ganin kallan da sadiq ya mata yasa ta barin parlour ba shiri ,majeed Kuma ya bita da kallo har yana cewa har zaki gudu? ko tanka mai ba tayi ba ta shige bedroom ,wai gowa yayi yana kallan sadiq ko lura da irin canjin da fuskar shi yayi bai lura ba ya haura upstairs, sadiq ya biyo bayan shi bayan sadiq yayi wanka ya shirya cikin kanana k'aya d'aya saba sawa suka fito tare da majeed dining area suka nufa, lokacin kowa ya halara gaishe da su mom sukayi a tare, tare da jan kojera suka zauna, a'a yau wanake gani a gidan ?dan murmushi majeed yayi yana sosa keya lalai ka kyauta, amma dai wuni ka zo yi? eh mana ki sha kurimin ki mom nama kusa kwaso kayana na dawo nan da zama ya ida zancan sa yana sunkuyar da kan sa kasa, dariya mom da abba sukayi sadiq ko ya cika fam kamar zai fashe. janyo plate fatuha tayi zatayi saving din sadiq kamar yadda ta saba, sai da ta gama samin nashi zatayi saving din majeed ya fakaici idanuwan su ya riqe hannu fatuha alamar kar ta zuba bata dau abin komai ba a tunanin hutar da ita yake son yi, ta zauna ta fara cin abincin ta sadiq ne yayi saving din majeed da kanshi sannan suka fara break duk wata loma da majeed zai kai sai ya kai kallan shi ga fatuha idan sukayi ido hudu ya aika mata killing smile din shi duk wannan abun a qwayar idanuwa sadiq, cikin bacin rai ya ture plate din shi cike da masifa da zafin rai ya bar dining, kallo su M'y suka bishi da shi, fatuha ce tayi qoqarin tashi mom tace "Kyale shi ki cigaba da cin abincin ki ,tunda kika ga h'aka ba qaramin bata mai rai a qayi ba d'aga kafada majeed yayi tare da cewa " Indai sadiq ne ai ba yau ya saba haka ba" tunda sadiq ya bar dining fatuha ta rasa natsuwar ta ,tunda safe ta lura yake d'acin rai ta rasa dalili...hmm!


Ko da ya shiga part din shi a parlour ya zauna tare da lumshe ido wani irin bacin rai na damun shi ,Kuma gashi ya rasa dalilin h'aka dafa shin da akayi ne yasashi ware eye's ball's din shi fatuha ce tsaye da plate a hannu ta cikin cool voice din tace "Uncle pls kayi break koma waye ya bata ma rai kayi hakuri ta ida zancan tare da zama tana miqa mika ma plate din" amsa yayi ya aje gefe yana kallan fatuha kamar me neman wani abu a fuskar ta can Kuma ya kauda kai tare da cewa zanci kin ji tashi ki je bana san magana ne ya fadi yana lumshe ido fita ta zo yi lokacin yayi dai-dai da shigowar majeed bigewa su kayi da junnan su, "ohshh majeed yace" haka ma fatuha tayi b'aya waigowa sadiq yayi yana kallan su wani miyau mai daci ya hadiya. dariya fatuha ta saki tare da cewa "Sorry , majeed" yace tunda nazo gidan nan kike bige ni, har saida kika bige zuciya ta. zaro ido waje fatuha tayi tana dan kule bakin ta tace "Kai uncle ba ruwana ta fadi zancan tana ida fita" ritse ido sadiq yayi tare da dunqule hannuwa shi yana mai da numfashi sama sama majeed ne ya dafa shi lumshe ido yayi a hankali yana janyo natsuwar shi zagayuwa yayi ya zauna , big man ina tunanin ka daina zafin ranan ashe har yanzu kana yi , wai ma waya bata ma rai haka big man?kawai am not in the mood shiyasa eyya sorry ko alura ce ta motso ya fadi yana dariyar shaqiyanci pillow kujera sadiq ya wurga wa majeed wallahi ka rainani kai naka bai tashi ba sai nawa, hhhh, kasan me ammi tace a'a tace wallahi next meeting in bamu fido mata ba wallahi auran dole zata mana. Ni dai nayi mata wallahi very soon zaku Santa ,amma kai ban sani ba kana nan kana ruwan idon nan naka, dan tab'e baki sadiq yayi tare da cewa "Ba wani ruwan ido har yanzu b'anga wadda ta d'ace d'ani bane shiyasa?ko za kayi bayani sanda ammi zata kwasoma yar kauye. Dariyar yake sadiq yayi tare da daukar remote control...


*_Fan's ku d'anyi h'akuri da page din nan am to busy wallahi hakanan nayi page din dan farin cikin ku A na tare🤝_*



*Taku har kullun Salma mas'ud nadabo*
[7/1, 10:09 AM] ‪+234 903 344 8176‬: *CAPTAIN SADIQ*
👮🏼‍♂

*Writing by*
*Salma mas'ud nadabo*

*Edit by*
*Raheenat*

📘 *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*🐄


http/mobile.Facebook.com/Real-Hausa-fulani-writers-forum RHFWF-173984973194167/?refid=52&red=opare_speed_dial_&yn=H-R


*Email* [email protected]


*Facebook* www. Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERFORUM.COM


73_74


*_this page is for you ummin mama_*


Sai baya'n sallah isha majeed ya bar gidan su sadiq, bayan sadiq ya d'awo party din shi ya wuce yana shiga yaci qaro da angel na kallo cartoon, murmushi ya saki tare da cewa, "Angel? ya qaraso kusa da ita ya zauna pack ya mata a goshi" daddy yes dear please gobe muje shan ice cream please, sweetheart gobe ba time kin ga akwai work amma inna dawo da wuri zamu je kijin angel ok daddy, daddy yau a nan zan kwana? ta ida zancan ta cikin shagwaba ." dan ja mata h'anci sadiq yayi tare da cewa "Yanzu kin zama big girlfa? ko baki gani yanzu fa u are 9 year old ko baki Sani baby?" smile tayi ta ce "Haka kuma nima daddy zan zama kamar Anuty fatuha ko idan na girma?" yes mana smile ta saki tare da yimai pack a goshi, good night daddy, night angel.



Fatuha ce tsaye g'aban dressing mirror tana feshe jikin ta da turare da alama shirin bacci take, dan kayan bacci ne a jikin ta pink da ratsin green riga ce dai-dai gwiwa mai dan siririn hannu bayan ta kamala shirin ta, ta baza gashin ta har gadan bayanta. tsurawa dressing mirror din ido tayi tana tuna lokaci da sadiq yasa mata sarka lumshi ido tayi tare da daurasu a wuyan ta saurin ware ido tayi tare da cewa "U are very stupid fatuha tare da fita d'aga daki'n" bedroom din angel ta shiga lokacin har ta shirya cikin night dress din ta, tana kwace cikin blanket a hankali fatuha qaraso kusa da ita ware ido angel tayi kasan cewa bacci be dauke ta ba shafa gashin kanta fatuha tayi tace "Angel bakiyi bacci ba?" um yanzu na d'awo d'aga party din daddy, ok pack fatuha tayi mata tare da gyara mata blanket din ta kashe haskyan daki'n tare da rage gudun AC dakin ta fita.


Ko da fatuha ta fita kitchen ta shige ta had'a coffee sannan ta daura cup din a dan qaramin plate na glass ta haura saman, a hankali tayi knocking din part din come in aka ce hakan yasa fatuha bude kofar a hankali ta shigo. sanyi AC ke tashi da kamshi na musanman cikin fara'a ta qarasa shigowa sadiq na zaune saman three star sanye da night dress din shi maroon wando da riga, cikin natsuwa ta samu guri ta zauna saman one star, miqa mai glass cup din tayi amsa yayi yana smile kurba biyu zuwa uku yayi tare da kallan fatuha yace kamar akwai magana a bakin ki dan murmushi tayi tana wasa da yatsun hannu ta, ina jin ki! uncle dama dama um gobe ina so naje family house ne ni da hanan wani irin miyau sadiq ya h'ade take nan coffee din ya fara fita ranshi ,waza taje gani family house ?ya fada cikin zuciyar sa qara h'ada rai yayi kamar an aiko mai da saqwan mutuwa majeed ne ya fado mai a rai qara tsuke fuska yayi yace "Ban shirya ma zuwan ki family house ba" ya fadi a taqaice, uncle... d'aga mata hannu yayi yace "Yawon yayi yawa ina laifin kije gidan Anuty bilki, next time kin je can din ?ya fadi a taqaice dan murmushi tayi wanda iya karshi laban ta, saboda bata san gardama da sadiq ko dan karya bata rain shi, qoqarin fita ta take jiki ba qwari janyo ta sadiq yayi ta fado saman fafadan qirjin shi dariya fatuha ta saki tare da dan dukan qirjin shi cikin wasa, murmushi ya saki tare da d'ago da habarta yace " Na dauka kinyi fushi da uncle ne" dan bata fuska tayi tare da taba gefan fuskar shi tace ba " Ba Komai uncle, Kuma dama can gidan Mami nayi niyar zuwa hanan ce tace na tanbaye ka muje can" qarewa lips din ta kallo sadiq yake har ta kai aya, sannan yace "Ok!" zame jikin ta d'aga na Sadiq tayi tace "Uncle bari na tafi" ok har kin fara jin bacci ne na dauka hira kika zo taya ni dan smile tayi wanda ya bayana fararan hakoran ta tace "Ba bacci nake ji ba kawai zan tafi ne saboda bana san dare yamin a nan ina jin tsora fita ni ka dai" d'aga gira sadiq yayi ok good night, har ta kai bakin kofa ta jiyu tace "Oncle zaka taya ni hira kafin bacci ya dauke ni?" yap ok zan kira ka video call ina je bedroom dawowa tayi ta mai pack a goshi sannan ta fice d'aga part din.

Ko da ta koma bedroom laptop din ta ta kuna, a bangaran sadiq ma haka kiran fatuha ya shigo laptop din sadiq dauk'a yayi yana kallan ta kamar tana gaban shi surutu ta cigaba da zuba mai yana dariya har cikin shi na kulewa haka itama sosai sukayi hira inda sadiq yake jin bacin rain d'ake damun shi ya sauka har tayi bacci suna video call smile sadiq yayi ganin fatuha tayi bacci sannan shima ya kwanta, amma duk da haka ya kasa kashe laptop din kuma ya kasa kauda idanuwashi d'aga kanta yarasa dalilin da yasa inda yana tare da fatuha yake bata guri na musanman a zuciyar shi ita ka dai ce macan d'ake ganin murmushin shi fara'a shi da halin da wannan tunanin bacci ya dauke sadiq ba tare da ya kashe laptop din ba.


*Asuba ta gari*

Addu'a cike a bakin ta tashi tana miqa d'auke, laptop din ta dake saman bed take qoqarin sadiq ta hango kwance yana bacci , murmushi tayi tana qare ma kyakyawar face din shi kallo hannu ta kai kan screen din laptop din can kuma ta janye hannu ta daukar laptop din tayi ta aje saman sofa yadda zata riqa hango shi duk abinda take, toilet ta shige ta watsa ruwa tare da dauro alwala daure da towel ta fito ko da ta fito lokacin sadiq shima ya tashi dan ba alamar shi ta cikin laptop din bed ba kowa sama ,cikin Sauri ta shirya tare da gabatar da sallah sket din makarantar ta ta janyo tasa tana gama sawa ta zura rigata tana bale ma balin riga ta, ta hango sadiq tsaye shima yana bale nashi dariya suka saki a tare morning uncle, morning too dear kin rigani tashi na riga ki shiryawa baki da sauri dan turo baki fatuha tayi dama can ka tashi idan ba hhhhh, kwarankwatsi ban tashi ba fashe wa fatuha tayi da dariya saboda tasan tsokanar ta yake kashe laptop din yayi domin ta qarasa shirya wa.


Kusan a tare suka fito lokacin angel har ta shirya cikin uniform din ta tana dining area ita da mom da abba cikn natsuwa suka qaraso, gaishe da su mom su kayi suka amsa a tare sannan suka ja kujera suka zauna saving din su fatuha tayi sannan suka fara break cikin jin dadi bayan sun kamala pack sukayi ma mom, abba ne yace lalai gidan nan ana gwada min banbanci jiya ina kallo mom dinku kukayi ma pack ni kuma ko oho ba komai zan rama dariya sukayi su duka tare da ba abba hakuri kusan a tare suka fito mom ta rako su har bakin kofa yaran sadiq sai qamewa suke, shigewa motoci sukayi abba ya shige nashi suka bar harabar gidan.


Sosai yau sun sha karatu har da test sai da sukayi na history sosai fatuha ke maida hankalin ita da kawayan ta, Nana da Zara sune kawayan ta na makaranta kuma yan'yan masu kudi ne masu ji da Wayewa da yan matanci, fatuha ko tun tana jss2 ta zana JSSCE saboda qoqarin da hazaqa yanzu haka SS2 take hanan na SS3 Basma kuma ta gama, Nana ce ta kalle ta bayan uncle ya fita daga class tace "Niko fatuha ina wannan uncle din nan naki mai kyau?" kallan ta fatuha tayi tare da aika mata harara ina ruwan ki da uncle dina, laaa fatuha yaushe kika zama haka? inji Nana, Zara d'ake gafe tace "Karki ga laifin ta wallahi ai dani ce fatuha da tuni na canza zani wallahi, hmmm ku wai me kuke nufi ban fa gane wannan hausar taku fatuha ta fada, hehe Zara da Nana sukayi lokaci daya, wallahi rainin hankalin nan namin dadi serious, to bari kiji ki zauna nan kwado ya maki kafa wallahi dani na sami damar ki da tuni na dama wallahi inji nana, ku dai Baku da aikin yi ni ina da . uncle kuma nifa a matsayin wana na d'auke shi ba komai ba Allahu Akbar bugu fatuha ta kaima Nana da Zara da littafin dake hannu ta.



Basma ce zaune ita da umma tana taya ta kwalema a d'akin ta, pic din sadiq ne ya fado hannu ta kai ta dauka ta kurawa pic din ido umma ce ta taba ta firgigit ta dawo d'aga duniyar tunani tare da qoqarin aje pic. din murmushi umma ta saki yar auta me ke damun kine kwana biyu naga duk kin rame kin zabge kamar mara lafiya hawayan d'ake maqale a idanuwan tane suka zubu tare da riqe hannu umma, tace " Umma na rasa me ke damuna tun zuwan da yaya sadiq yayi kwanaki na rasa meke damuna wallahi umma😭 ina son yaya sadiq ta ida zancan tare da rushewa da kuka" lalashin ta umma ta shigayi haba auta me abin kuka? share mata hawaye umma tayi duk wata mace mai lafiya dole taso sadiq saboda ya tare duk abinda mata ke so basma insha Allah zan taya ki da addu'a, idan sadiq alheri ne a gare ki Allah ya baki shi inko haka ta faru sai nafi kowa farin ciki da kinga sai a h'ada da naki dana majeed tunda shima jiya yake fada min ya samu wadda yake dai-dai tawa da ita , murmushi basma ta saki tare da fita d'aga dakin da gudu umma ta bita da kallo tayi murmushi irin nasu Na Manya.


Misalin karfe 12:30pm suka tashi dag'a makaranta kasan cewa yau friday angel na gefan ta suna jiran drive, hadadiyar motace baka ta faka gaban su fatuha kauda kai fatuha tayi kamar motar ba gaban su ta tsaya ba ,saboda glass din motar tinted ne ko na ciki ba'a gani zuge glass din akayi hakan yasa angel washe baki tare da cewa "Second daddy?" majeed sanye cikin uniform din shi na aiki murmushi ya saki bale murfin motar angel tayi kamar tana jira ta shige gaishe shi fatuha tayi a taqaice tare da cewa angel fito kin san driver ne zai zo daukar mu ta fada, murmushi majeed yayi yace "To ni zan d'auki kyankyawa yau na kai ta har gida dan tun dazu na kori driven" dan zaro ido waje fatuha tayi tace "Sokake uncle ya Mani fada KO?" ah uncle ba zai maki fada ba ai yasan ni zan dauke ku dan smile fatuha tayi wanda iyakar shi laban ta ta bude murfin motar ta shiga cikin natsuwa ya ja motar inda yana driven yana kallan fatuha ta cikin mirror .sai da ya zo dai dai b'akin geta yayi horn bala mai gadi ya bude mai geta parking yayi su fatuha suka fito tare da mai Godiya sai da suka shige cikin gida yayi ribas ya fita.


Shiga office din majeed sadiq yayi amma wayam ba majeed dan tabe baki yayi tare da fitowa d'aga office din ,da khaleed ya ci karo wanda shigowar shi yanzu kenan cikin fara'a sadiq ya tarbe shi, "Ah wai har yanzu majeed be dawo ba?" oh kama san da fita kenan eh munyi waya nace mai zanzo shine yace min yaje daukar baby shin d'aga school, baby sadiq ya maimai ta wallahi bansan sanda majeed zaiyi hankali ba wallahi mtww yaja Khaleed suka wuce office din shin.


Bayan sunyi lunch fatuha ta shirya tsaf cikin lace din ta maroon anmata dinkin bubu da lace din sosai kayan sun fido ta ,dan kwalin ta ta daura shi hawan hawan daurin ya zauna kamar gwagwaro janbaki ta shafa maroon da yar hod'a kwalliya sosai ta zauna ta tsantsara veil din ta ta dauk'o white ta yafa masha Allah fatuha ba qaramin kyau ta zuba ba,

Tana fitowa parlour ta sami mom da majeed sunata zuba hira yana sanye da blue shad'a tasha aiki, cikin zazakar muryata fatuha tace "Mom zan je gidan mami, to, shikenan ki gaishe min da su zasu ji, majeed ne yayi karaf yace " Tunda tafiya nima zanyi bari na aje ki a can?" to! fatuha tace tare da yin gaba majeed yabi bayan ta shida kanshi ya bude mata murfin mota ta zauna sannan ya bude ma kanshi ya shiga,

Ko 20 minutes basu dauka ba suka Isa gidan Anuty bilki, inda majeed keta janta da surutu har ta dan saki jiki da shi yana yin horn mai gadi ya bude ya shigo da motar tare da yin parking qoqarin fita d'aga motar take majeed yace "Baki ji ba, waigowa tayi sannan yace karfe nawa zaki koma gida?" da yama ta fada a taqaice. toh! shikenan zanzo daukar ki Godiya ta mai tare da shigewa cikin gidan.


Da gudu hanan ta rugo ta rungume ta kai amma naji dad'i wallahi, gaishe da mami tayi dake zaune parlour tana kallo sannan hanan ta ja ta bedroom suka baje suna ta zuba hira cikin jin dadi kai ka ce yan'uwane yadda suke nuna ma juna so sai kusan yama likis majeed ya zo gidan Anuty bilki inda ta rinqa zuba mai shaqiyanci shida sadiq sun raina ta basu san zuwa gidan ta sai da dalili shi dai Sosa keya kawai yake sannan suka bar gidan suka nufo gidan,


Tunda sadiq ya kunno kai da motar sa driven na ja shi kuma yana b'aya, gyaran murya yayi yace "Wancan motar kamar ta majeed? yallabai ita ce ai dazu dana zo daukar fatuha, Hajiya tace min ai majeed ya kaita to qila sun dawo ne, wani qulolin bakin ciki ya tsayawa sadiq har yana jin ya qasa hadiye miyau kusan a tare suka shigo gidan sai da fatuha ta fito majeed shima ya fito murmushi fatuha ta saki tana ma majeed godiya, qoqarin bude kofar motar driver keyi yi sadiq yayi magana a tsawace karka bude ya fadi, shi kan shi driver terere yayi da mamakin canji sadiq lokaci d'aya .zaunawa sukayi a motar sadiq na hango fatuha da majeed, har tayi gaba ta dawo ,oh na manta wayana a motar smile majeed yayi tare da bude motar ya curo wayar ya bata, tare da cewa gaskiya yadda na dako wayar nan ya kamata ki bani number ki dan murmushi tayi tace uncle number ta eh mana ya fada ko baza'a bani ba zan baka mana curo wayar shi yayi d'ake gaban aljihu ya bama fatuha ta rubuta mai number ta sannan ya shige mota ya bar harabar gidan.




Please Login or Register in order to submit comment