Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da kujerar motar ya lumshe idanuwan shi tare da ware su murfin motar ya bude tare da samata ki yana shigowa parlour haske ya kunna ya gwaraye parlour k'allan parlour yayi ba kowa, t kashe haskan yayi a hankali ya qarasa bakin kofar dakin fatuha har zai murda handle din kofar sai ya fasa tare da ja baya ya wuce part din shi, fatuha ko duk wani motsi da sadiq yake a kunnanta take jin shin lamo tayi kamar me bacci haka ta rinqa zare ido har barcci ya kwashe ta.

Yana shiga bedroom toilet ya shige ya sheqa wanka ya fito, tsane jikin shi kawai yayi tare da zura k'ayan bacci yabi lafiyar bed ya kwanta.


Kiran sallah ne ya tashi fatuha toilet ta shiga tare da yin wanka tare da dauro alwala daure da tawel tafito Dan karamin towel na hannunta tana tsane jikin ta dashi, shafe jikin tayi da lotion tana gamawa tabude wardrobe ta ta janyo wasu Riga da sket tasha stone's a jiki ta mai kyau tana gama sasu ta dauko aftadress ta aza bisa domin gabatar da sallah tana idawa ta k'oma saman bed ta ta kwanta bacci ya qara kwasheta ba ita ta tashi ba sai karfe bakwai kallan agogwan dake manne jikin daki tayi tare da yin miqa toilet ta shiga tayi brush ta fito tare da sharce sumarta ta kwanta a gadan bayan ta a hankali ta bude kofar daki ta zuro kai ta laleqa taga ba kowa fitowa tayi ta nufi dining area tana qaraso wa taga sadiq zaune cikin shirin shi na unform yasha kyau har ya gaji dago eye's ball's din yayi su kayi ido hudu kauda kai yayi ya cigaba da breakfast gaisheshi tayi ya amsa a taqaice qoqarin barin gun take har ta juya yace "Fatuha" waigowa tayi hakan yasa iska ta hura gashin kan ta har ya shifi fuskar sadiq lumshe ido yayi tare da ware su a kanta itama din shi take kallo kauda kai yayi yace "Ki dawo kici abincin ki" washe baki tayi tare da jan kujera ta zauna saving din kanta tayi tare da janyo plate din gaban ta Sadiq kallan ta yake ta qasan ido hannun hagunta tasa ta gyara gashinta da iska ke yawo da shi ta zura hannun ta, cikin plat ta fara cin abincin, chips ne da farfesun kifi wani irin dadi ya mata sai k'ada kai take tana ci sadiq mamaki qazantar fatuha yake, cin abinci da hannu ?ko wankesu batayi ba? kallan ta yake da gowar da zatayi ta kai wata lomar sukayi 4 eye's murmushin karfin hali ta mai tana qoqarin boye hannu ta dan kwata kwata ta manta yana wajan kauda kai yayi tare da daukar briefcase din shi kallan shi fatuha take tayi rau rau da ido ko kallan ta beyi ba yasa kai ya fice ture plate din tayi take nan taji abincin ya gundire ta, kwashe kwanikan tayi ta kai kitchen a nan ta ci karo da rabi'a na aiki gaisheta tayi ta amsa cikin fara'a taya ta aiki fatuha ta shiga yi tun tana hana ta har ta kyale ta, kusan tare sukayi komai na launch sannan suka jera a dining area bayan sun kamala fatuha ta shiga rokar rabi'a kar tatafi ta barta ita ka dai aiko taci sa'a rabi'a ta tsaya taji dadin hakan sosai, Dan haka ta wuce part din sadiq ta gyara shi tas ta dawo parlour suka cigaba da hira da rabi'a ko da aka kira sallah azahar tare sukayi sannan su kaci abinci sai kusan qafe hudu rabi'a tayima fatuha sallama fatuha bata ji dadi ba amma hakanan ta hakura ta zauna kiran sallah la'asar ne ya sata shiga bedroom ta shiga toilet tayi wanka tare da alwala saboda yau tasha aiki ba laifi wata hadadiyar Riga da isket ta kuma sawa hijabinta ta zura tayi sallah bayan ta gabatar da sallah ta cire hijabin ta dawo parlour, jin zaman parlour ya isheta ta yasa ta fita farfajiyar gida su ola da Sunday ne da sauran yaran sadiq suketa shawagi a gidan resting chair ta samu ta zauna tare da jin gina da kanta ta lumshe ido wani iska ke kadawa mai dadi da sanyi , Sunday ne ya zuguro imeka dake ta kallan fatuha har yana lashe baki hey imeka stop looking at her mind ur business this girl pass ur level na Oga consin sister be that I don't now fa amma this girl na beautiful ho u no go stop looking at her I will tell Oga sorry Sunday haba kar muyi haka da kai imeka ya fadi cikin hausar sa Mara dadi leave me alone Sunday ya fada , sorry lemme leave the place ma imeka tabirim bala mai gadi ya koma duk abun nan da sukeyi fatuha bata Sani ba.


Yau yasha aiki sosai wajan à office sai kusan yama likis sadiq ya nufo gida ,yana zuwa b'akin gate horn yayi bala mai gadi ya wangale mai gate ya kunno hanci motar shi hango fatuha yayi harabar gidan saman resting chair gashin ta ya bage kusan rabin qirjin ta duk waje suke domin Riga da isket ne ajinta Sun matse ta sosai d'omin da kyar take numshi, imeka da ke gefan bala mai gadi sai kallan ta yake ,lumshe ido sadiq yayi tare da ware su yaja motar da karfi dai dai parking space yayi parking ko dai daita parking din beyi ba ya fito cikin zafin rai fatuha dake kishingide ya nufa cikin zafi rai ya daka mata tsawa tare fisgota ta fada bisa fafadar kirjinsa ware ido tayi tare da saka mai kuka Janta yashiga ya cigaba da yi sai da ya zo parlour ya turata saman kujera har sai da kanta ya bigi kujera kuka ta qara saki tana kallan sadiq dan bata san laifin data mai ba, kallan ta yake ido cikin ido matsowa yayi daf da ita har tana jin saukar numfashishi matse mata fuska yayi cikin daka tsawa yace "Uban waye yace ki fita waje haka? ya fadi a tsawa ce" har cikin kanta sai da taji tsawar da sadiq ya mata runtse ido tayi tana girgiza kai tana kuka sakin fuskar yayi ya ja gashin kanta har saida ta saki qara tare da rushewa da wani saban kuka idan na qara ganin kin fita ba farfajiyar gidan nan baki sa hijabi ba sai na kona gashinan ya ida zancan taré da matse mata fuska da karfi kuka ta kuma saki tana kallan sadiq wani irin tsanar shi na fizgar ta, lumshe ido tayi tana jin zafi da radadin , wani wawan tsaki sadiq ya ja tare da tura ta ta bigi da kujera sannan ya dau briefcase din shi ya h'aura sama, kuka ta saki mai ban tausayi.

Yana shiga parlour shi ya wurgar da briefcase din shi ya zauna bisa kujera taré da lumshe ido, wata zuciyar ta ce mai "Kai sadiq ina ruwan ka da harkata? inma tsirara zata dinga yawo me ruwan ka ? runtse ido ya kuma yi" wata zuciyar tace masa "Ko Dan saboda tarbiyar diyar ka ka taka mata birki? saboda duk abinda tayi shi jidda zata kwaikwaya?" duk wannan zancan a zuci yake kiran sallah magrib ne ya tasheshi bedroom ya shige ya rage k'ayan jikin shi agurguje yayi wanka yana fitowa ko mai be shafa ba ya zura jalabiya a hankali yake sauko wa d'aga upstairs, inda ya bar fatuha har yanzu nan take kuka jin alamar tafiya ya sata dago jajayan idanuwanta ta kalli sadiq, sadiq ma k'allan ta yayi tare da aika mata harara mtss ya fice, kuka ta kuma saki sannan ta ja jiki ta shige daki tana alwala tana kuka har ta gama haka tafito ta zura abaya tana idar da sallah ta cigaba da lazumi har sai da aka kira isha'i ta tashi tayi sannan ta ja jiki ta k'oma bed ta cigaba da raira kukanta kanta har ciwo yake mata amma Dan jaraba takasa d'aina kukan.

bashi ya d'awo gida ba sai bayan sallah isha'i, yana shigowa parlour dining area ya wuce yana b'ude kulolin yaga alamar fatuha bata ci abinci ba d'ogwan tsaki yaja tare da rufe kulolin. K'wala mata k'ira yashiga yi shiru ba'a Amsa ba dan haka cikin natsuwa ya nufi dakin fatuha ya murda handle din kofar can saman g'ado ya hango fatuha cikin cool voice din shi yace mata " Yanzu Dan iskanci
kina jina kikayi banza dani?" Tayi shiru bata tanka masa ba, rashin yayi mugun bacci Dan haka ya daka mata wani uban tsawa w'adda ta sata zabura ta sauko d'aga bed tare da fashewa da wani sabon kuka😭, harara ya aika mata ya mata nuni d ta biyoshi, bin shi take har tana sarke kafa dining area ya isa itama taja ta tsaya oya wuce kici abinci ,à takaice tace masa ta koshi , wata tsawa ya kuma daka mata jiki na bari tana kuka ta fara zuba abincin dan kadan ta zuba wani irin kallo sadiq ya wurga mata tare da yin magana cikin daure fuska "Haka kike zuba abinci eeeh?" kuka tasa tare da cigaba da zuba abincin har ya kai bakin plate din tana qoqarin qara zuba wani sadiq ya matse hannunta da karfi har sai da ta saki qara, saboda ya lura bata da niyar daina zuba abincin juya abincin ta Shigayi ta qasa ci sai kuka , cikin murya mai sauti sadiq yace "Ko kiyi ma matune shuru! ko nasa alburushi na bula maki kai kowama ya huta, kuma abincin karki ci ki bari na tashi tsaye Allah danne ki zanyi na dura maki har da plate din" cikin hawaye fatuha tashiga dura abinci har tana jin kamar zatayi amai amma sai da ta cinye shi tana gama ci tayi qoqari tashi cikin sauri sadiq dake saman kujera dining area ya lumshe ido k'amar me jin barcci, har tayi nisa yace "Fatuha" juyowa tayi tana kallan shi hawaya da ke maqale a idanuwan ta suka gangaro bisa kumatunta, wani irin yerr sadiq yaji ajikinsa kallan ta yashiga yi kamar yauw yafara ganinta yakara Kiran ta akaro nabiyu "Fatuha!!!" gaban tane ya yanke ya fadi kuka ta kuma saki tare da dawowa ta durqusa g'aban shi tana rera wani saban kukan, a hankali sadiq ya kai lalausan hannun shi ya cigaba da gogema fatuha hawayan ta, lumshe ido tayi tare da ware su kan sadiq .yana gama goge mata hawayan ya mata alama ta tafi har tayi gaba ya ruqo hannun ta juyo da sauri domin ita yanzu yafara bata tsoro , Kangabar da kai yayi yace "Fatuha please kukan ya isa haka?" kallan shi take shima din haka, wasu Sabin hawayan ne suka qara zubowa wani irin kallo sadiq ke bin ta dashi ya koma abin tausayi kamar bashi ba hakan yasa fatuha hadiye wasu hawayen ,smile yayi tare da sakin ta cikin sauri ta shige daki tare da fada wa saman bed ,
shima sadiq upstairs ya haura cikin da farinciki dashi kansa mamakin haka yake..... Hmmm Kayi bayani Sadiq😘.


_*insha Allah bazan sake typing ba har sai bayan sallah wannan page din naku ne masoyan wannan littafin ga*_




_*Taku har kullun Salma mas'ud nadabo*_
[6/30, 9:43 AM] ‪+234 703 121 9749‬: *CAPTAIN SADIQ*
👮🏼‍♂

*_Writing by_*
*_salma mas'ud nadabo_*

*_Edit by_*
*_Raheenat_*


📘 *_REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM_*🐄
★we are the beat★


http/mobile.Facebook.com/Real-Hausa-fulani-writers-forum RHFWF-173984973194167/?refid=52&red=opare_speed_dial_&yn=H-R


*_Email_* [email protected]

*_Facebook_* www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERSFORUM.COM


_59_60_



*_Assalamu alaikum dibin masoya wannnan littafi ina mai yi maku B'arka da sallah kuma ina fatan kunyi sallah lafiyar Allah ya qarbi ibadun mu a yau ne zan cika alqawari nayi typing sai bayan azumin ga shi yau har Allah ya k'awo mu tabas duniya tana gudu Allah y'asa mu cika da imani_*


Tun ranar da fatuha tasha maqara ta shiga wasan boya da sadiq, kwata kwata b'ata bari su had'u dan ta lura aljanu ne gare shi, lol, ko gyaran part nashi za tayi sai ta b'ari ya tafi office haka shima bangaran sadiq bai wani damu da rashin ganin na ta ba, saboda yasan lafiyar ta lau of cos yana ganin part nashi fes .


Fatuha da rabi'a sun wani qara shaquwa musanman yanzu rabi'a bata tafiya gida sai 4, shiyasa fatuha ke dan jin d'adi gidan ita dai burin ta bai wuce ace su mom sun d'awo ba ko Jidda d'an ta gaji da zaman ka dai ci ku san tare suke aikin ma yanzu dan fatuha yanzu ta fara gogewa da girke girke dan yanzu kusan abinci gidan ita ke yin shi duk da rabi'a na h'ana ta.


Misalin karfe goma na d'are ya shigo gidan tsit ba motsin k'owa, inda sabo ya saba d'ama shi mutun ne ba mai san hayani ya b'ane part nashi ya wuce tare da shigewa bathroom ya sheqa wanka,y ana fitowa ko mai bai shafa ba ya zura jalabiya white ba qaramin kyau ta mai ba , fitowa yayi d'aga part din na shi ya wuce men parlour direct dinning area ya wuce abinci ya zuba dan ka dan shinkafa da miya ce tasha k'ayan had'i loma biyu zuwa uku yayi ya ture plate din dan kwata kwata b'aya jin d'adin jikin shi gaba ki daya ,yayi missing din jidda b'ama ya ganewa yayi missing nata sai ya je bacci zai ji bed din wayam sai dai yayata juyi har ya samu bacci ya dauke shi, gashi b'aya so ya je gidan Anuty bilki yasan yana zuwa zata ce Jidda ta kawo shi shiyasa yake h'akura bangaran su mom ko duk san da ya tanbayi ranar dawowar su sai mom ta ce sai sun gama abinda suke.


Jiki ba kwari ya k'oma part din shi, wata irin fever yake ji sama sama ga qirjin shi na mai zafi, magani ya cura d'aga bedside drowe ya sha sannnan kwata ta tare da rufe jikin shi da blanket.



Asuba ta gari fatuha na tashi ta tsala wanka tare da gabatar da sallah, Sannan ta koma bacci cike da kewar su inna dan g'abaki d'aya yanzu kauye take so ta koma, zama gidan yanzu ya fara hawar mata kai abu d'aya ke mata dadi yanzu shine in malam ya zo k'oya mata karatu shima da sun g'ama ya tafi zata shigo gida kamar maya gaskiya ta gaji da irin wannan rayuwar gashi kwanan ta lura mai kyau ko abinci baya ci, anya yana gidan ma kuwa ba ita ka dai suka bari ba Sannan ta ja dan guntun tsaki tare da gyara kwaciyar ta.


Ba ita ta tashi ba sai kusan karfe 10:30 brush kawai tayi tare da gyara gashin kanta ya kwanta har gadan baya, Sannan ta fito parlour sanye da gwon black mai kyau masha Allah fatuha tayi kyau ga wani haske da ta qara, gashi kullun yan matan ci bayana yake a jikin
ta. Jin bata ji kamshi bane yasa gaban ta ya fadi leqawa kitchen tayi taga wayam ba rabi'a ba alama d'an bata rai tayi ta d'awo parlour tare da wucewa dining area bule kulolin jiya ta fara yi jiya ma k'usan ita ka dai ta ci abincin dan guntun tsaki ta kuma ja tare da kwashe kayan ta wuce kitchen, gyara kitchen d'in ta shiga yi sai da kitchen din ya fita tas Sannan ta d'aura ruwan zafi k'an wuta ta fita sai da ta gama gyara k'o ina Sannan ta dawo kitchen ,ta juye ruwan zafin cikin Plack's sannan ta soya kwai ta juye a plate ta rufe yan ciki ta fido a fridge suma ta wanke ta gyara ta d'aura a tukunya t'are da gyara k'ayan miya ta zuba da k'ayan kamshi tuni kitchen din ya gwaraye da k'amshi d'adi, parlour ta fito tare da haurawa up stair's a hankali ta murda handle din kofar part din sadiq wani irin sanyi da kamshi dadi suka doki hanci ta, lumshe id'o tayi tare da ware su tare da qarewa parlour k,allo tsit parlour ba k'owa, h'akan ya tabatar mata da mai kyau ya tafi wajan aiki kofar bedroom ta nufa tare da bude ta a hankali ta shiga d'akin k'amar yand'a ta saba, sanyi AC ne kawai ke tashi sai kamshi k'ayan d'akin ta fara tatarewa duk da d'akin ba wani dati yayi ba blanket ta janyo zata linke sai taji anja, ware ido tayi waje tare da fara jin tsoro ko lafiya qara jan blanket din tayi taji anja dawowa tayi gaban bed din tayi ta tsaya a hankali ta kai hannu duk da zuciyar na dukan uku uku saboda tasan yau Tuesday sadiq na zuwa office kuma b'aya kai wannan lokacin bai fita ba, a h'ankali ta sa hannu ta fara yaye blanket din dai dai fuskar sadiq taja ta tsaya Chak, saboda ba abinda sadiq yake sai rawar dari .cikin rudewa fatuha ta ce "Mai kyau me ya same ka?" ta fadi bakin ta na rawa inbada rawar dari ba abinda ya ke sai hawayan fever d'ake bimai fuska dan ko magana be iyawa sai ma rintsa ido da yayi yana qoqari janyo blanket ya rufe jikin shi, riqe blanket din fatuha tayi har da yar kwalata mai kyau dan Allah me ke damu ka hannu ta kai ta taba goshin shin wani irin zafi taji rau take nan ta hau reramai kuka duk fever da ke jikin sadiq sai da fatuha ta dan bashi dariya, saboda yadda ta rude sai ka ce yau ta fara ganin ana fever amma sai ya guntse dariyar tare da qara lumshe ido dan bai San ganin wannan kukan ko mutuwa yayi ai sai h'aka fita tayi d'aga d'aki ganin zaman be fishe ta, tana zuwa bakin k'ofar fita suka ci qaro da ola shima zai shigo ya ji ko lafiya Oga bai fito ba ganin fatuha na kuka yasa shi tsayawa tanbayar ta lafiya kora mai bayani kawai tayi sannan. Shima ya haura sama part din sadiq wayar shi dake aljihu ya Ciro ya kira doctor yakub Sannan ya zauna saman sofa fatuha kuma na zaune kusa da sadiq tasa ruwan a ruba da towel tana dadana mai akai saboda jikin nashi ba qaramin zafi yayi ba cikin 15 minutes doctor ya qaraso gaishe shi fatuha tayi tare da matsa mai ya zauna, shi kuma ola ya fice , duba sadiq ya Shiga yi yan rubuce rubuce yayi tare da gwada BF din shi ya hau sosai kallan sa doctor yakub yayi tare da gwada kai ya curo allura ya mai fatuha dake gefe sai ka ce ance ita za ayima wa hada su rutse ido dan ba abinda ta tsana k'amar allura, bayan ya kamala duk abinda yake Dr yakub ya juyo cikin fara'a yace insha Allah anjima zai tashi kuma insha Allah fever zata sauka k'arki d'amu anjima zanzo, mai da magunguna dan Allah inya tashi ya samu yaci abinci dan babu alamar ya ci abinci idan zan d'awo zan dawo da ledar ruwa to fatuha ta ce mai tare da mai Godiya ta rakoshi har b'akin kofa ta koma ciki. Ko da ta koma ciki ,kitchen ta shige ta qarawa farfe Sun da take ruwa Sannan ta koma part din Sadiq leqa fuskar shi tayi ganin yana bacci yasata sakin ajiyar azuciya tare da taba goshin shi Alhamdulillah zazzabin ya sauka Sannan ta rage gudun AC d'aki ta fara gyara part din.



*_kuyi h'akuri da wannan page din nayi typing na shi sabod'a masoya masu san ji d'aga gare ni insha Allah gobe zan maku sweetest page_*



*_taku har kullun salma mas'ud nadabo_*
[6/30, 9:45 AM] ‪+234 703 121 9749‬: *CAPTAIN SADIQ*
👮🏼‍♂

*_Writing by_*
*_salma mas'ud nadabo_*


*_Edit by_*
*_Raheenat_*


📘 *_REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM_*
★We are the best★


http/mobile.Facebook.com-Real-Hausa-fulani-writers-forumRHFWF-173984973194167/?refid=52&red=opare_speed_dial_&yn=H-R

*_Email_*
realhausafulaniwritersforum@gmail. com


*_Facebook_* www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERSFORUM.COM



61_62



Sai da ta g'ama gyara part din tsaf sannan ta koma kitchen, lokacin har farfesun yayi ta juye a kula tare da plate ta zuba a tray tare da bread a hankali take taka upstairs saboda ta cika tray din da kayan abinci, baki kofa ta aje tray din Sannan ta bude k'ofar ta shi har cikin bedroom ta aje a stool qar'a leka fuskar sadiq tayi a qaro na biyu murmushi ta saki tare da zama gefan shi tana kallan yadda sajan shi ya kwanta luf har mamakin kyau irin na sadiq take ,sai dai yayi yar rama sannna fuskar tayi fayau dariya tayi tace "Ohni sangami ciwo yayi k'amu k'ayi bulun buqwi tunda likita ya tsulama allura kaji zafi sai bacci k'ake qila ma suma kayi saboda zafi, yadda kayi bacci kamar ba masifafe ba amma da ka warke zaka fara cika mana gida da tsuwa na huta da masifar ka ko ta kwana biyu ce wallahi um bari na lalaba naje nayi wanka a toilet din ka tunda kai ka zama gawar shanu dan tashin ka ba yanzu.


Tashi fatuha tayi ta bude wardrobe ta Ciro qaramin towel ta tare da rage k'ayan cikin tasa towel, duk wannan abinda fatuha keyi duk a kunnan sadiq dan ya d'ade da tashi kawai dai yayi lamo ne toilet din ta shige ta sheqa wanka ta fito ko da fito cikin sanda take tafiyar har ta qaraso gefe bed leqa fuskar sadiq tayi tana riqe da qaramin towel tana goge gashin kanta, Allah sarki ba wan Allah sai bacci kake b'aka san wainar d'ana ke toyawa ba wai da zaka tashi d'ana sha masifa, yarfe gashin k'anta tayi wanda hakan yasa ruwan gashin ya watso ma sadiq a fuska dan motsa ido yayi hakan yasa fatuha zaro ido tare da yin lamo tana zare ido tana yar fe hannu ganin ya juya ya gyara kwaciyar shi ya sata sakin a jiyar zuciya baki dressing mirror din shi ta tsaya tana k'allan mayu kan d'ake baje akan dressing mirror tsuru tsuru tayi tana tunanin man da zata shafa can ta kai hannu kan wani mai na gashi k'asan cewa fatuha ba boko yasa ta d'auka ta fara shafawa sadiq dake k'allan ta ta qasan ido sai dariya yake guntsewa in taqaice maku duk wani mai d'ake saman dressing mirror sai da ta shafa dan taji ya mai kyau ya ke ji Sannan ta fita d'aga d'akin, tana zuwa bedroom din kaya tasa sadiq d'ake d'akin d'ariya yayi sosai har da riqe ciki dan guntun saki ya ja tare da cewa "Yar kauye kawai Sannan ya tashi a hankali duk da har yanzu b'aya jin karfin jikin shi" waka yayi Sannan ya fito yasa jalabiya ash mai kyau Sannan ya gabatar da sallolin shi, yana idawa ya qara koma wa ya kwanta dan karfin hali kawai yake.


Sket da riga tasa na atamfa mai ratsin dark green da coffee sai gyara gashin kanta da tayi tare da yin ture ka ga tsiya, Sannan ta qara fesa turare rufe bedroom din tayi ta fito Sannan ta haura upstairs direct bedroom din sadiq ta shige kwance ta gan shi amma sai dai wannan lokacin idanuwan shi biyu murmushi ta

Please Login or Register in order to submit comment