Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Tunda bikin ya matso kullun sadiq da fever yake kwana ,gashi yaqi zuwa Dr yakub ya duba shi. har yayi mita ya gaji,

Majeed ya shigo bedroom din sadiq, sadiq na zaune saman sofa ya jingina in ban da tunani ba abinda yake ,dafa shin da majeed yayi ne ya sasa ya dago murmushi ya sakar mai sannan ya zauna, yace "Ga katin ka nan tun dazu nake kiran wayar ka bata shiga?" na kashe wayar ne saboda bana san takura sadiq ya fada. to shikenan yanzu dai ga katin daurin auran anjima zan amso na dinner katin sadiq yabi da kallo sannan majeed ya sa kai ya fita yana fita sadiq janyo kati yayi wasu hawaye masu zafi suka zubo mai, a hankali ya fara dauka katin d'aya bayan d'aya yana yagawa yana kuka. h'aka ya rinqa bin kati yana cewa shikenan fatuha kin zama ba tawa ba. me yasa nayi nauyin baki na kasa fada maki abinda ke rai na? fatuha bana iya rayuwa bada ke ba ya qara rushewa da saban kuka😭.

Zaune suke a bedroom ,hannan ta shigo da katin bikin . ta mika ma fatuha nata da basma wani irin murmushi basma ta saki ta ce "Yanzu ni zan auri yaya sadiq?" ta rungume katin tana jin dadi. angel da shigowar ta yanzu amsar katin hannu fatuha tayi ganin ansa majeed baro baro a jikin kati kallan su angel ta shiga yi tana cewa dama anuty fatuha uncle majeed zaki aure bata ida zancan ba ta fita daga dakin da gudu tana kuka.

Bata zame ko ina ba sai part din sadiq . tun a parlour take kwallawa sadiq kira daddy!! daddy!! Sadiq da fitowar shi d'aga wanka kenan yaji irin kiran da angel ke mai da sauri ya fito parlour tsaye ganinta da kati rike a hannu watsar da katin tayi qasa tasa kuka. "Dama daddy ba kai zaka auri Anuty fatuha ?wallahi daddy ba zan taba zama da wata a matsayin uwa in ba fatuha ba ta ida zancan tare da zamewa a qasa tana kuka kamar ranta zai fita" mamaki ne ya lulube sadiq be taba tunanin angel bata san yadda abun yake ba. a hankali ya qaraso kusa da ita tare da d'aga ta ya rungume kuka take sosai tace "Daddy indai kana san farin cikina ka fasa auranka da Anuty basma ayi da fatuha idan ko baka so a daura da Anuty basma" angel me yasa baki san Anutyn ki basma? ya fada zai qara buda b'aki ya qara magana angel tace "Daddy baka so na? leave me alone" ta fita da gudu daga part di har ta bangaje fatuha da ta biyo ta lokacin da ta fita da gudu d'aga bedroom din su. Kallan sadiq tayi dak'e tsaye ya kame kanshi, hawaye ne suka cigaba da yima fatuha zarya itama juyawa tayi da gudu ta bar wurin. zamewa sadiq yayi a gurin ya zauna tari ne da yazo mai ya sasa miqewa ya shige toilet da gudu jini kawai ke fita yana tarin wanke face din shi yayi ya jinjina da bangwan toilet,

Angel na shiga dak'i ta fada saman bed ta saki kuka, fatuha ce ta shigo dak'i dagowa angel tayi cikin d'aga murya mai sauti tace "Just leave me alone? ta buga murfin kofar daki'n da karfi" zamewa fatuha tayi baki'n kofar ta saki kuka me cin rai da kyar ta iya jan jikii ta koma bedroom din ta bakin window fatuha ta tsaya tana raira kuka a hankali iska ke kadawa kasancewar hadari ke akwai. a hankali ruwa ya fara sakowa mai cike da sanyi da karfi rufe window fatuha ta yi ta zame gefen gado ta cigaba da kuka haka bangaran angel in banda kuka ba abinda take, tana tuna irin rayuwar da su kayi a baya cikin ji dadi, haka shima sadiq rayuwar su yake tunawa a baya mecike da so da kwanciyar hankali, kuka fatuha ta Kuma saki tare da janyo pic din sadiq tana kalla tana tuno lokutan da yake yi mata fada farkwan zuwan ta gidan. dariya take mai kuka kuka ta daura hannu ta saman pic din tace "Mai kyau ina sonka tun bansan me so ba! nake sanka amma sai gashi lokaci d'aya na rasaka. har abada zan zauna da wanda zan koyawa kaina son sa." wani saban kuka ne ya kubuce mata,

Haka suka suka wuni ranar ciki'n kunci. duk yadda su hanan suka tanbayi fatuha mike damun ta ?sai tace masu headache ke damun ta. angel ko fir taqi cin abinci dan ko kofar daki'n taki budewa, fatuha tayi magana tayi magana har ta gaji part din sadiq ta shiga yana zaune a parlour ya jingina DA ban go,a hankali fatuha ta qaraso gaban shi cikin muryar kuka tace "Mai kyau" bude ido yayi na kallan fatuha kamar wanda ya Dade be ganta ba mai kyau dan Allah kayi ma angel magana taci wani abu tun safe ta rufe dak'i taqi fitowa? sai faman kuka take please ka mata magana" lumshe ido sadiq yayi yace "Fatuha I don't now how to do angel bazata saurare ni ba sai dai in zanbi abinda take so" kuka fatuha ta Kuma sadiq d'ago ta sadiq yayi ya cigaba da lalashi .sun dauki mintin 30 yana rungume DA Ita ,kanta ya dago yana kallan kyakyawar fuskarta DA ya kumbura yace "Ina sonki Fatuha! Ina kaunar ki ! tun ranar DA kika shigo gidan ga Allah ya jarabce ni DA sonki, a DA Ina tunanin wasa ne a yanzu DA nake shirin rasaki Na gane cewa kece farincina ,kece abin alfabarina, kece anurin zuciyata ,ban taba tsamani Zan iya son wata diya mace bayan rasuwar matata sai gashi Allah ya hadani DA wacce idan Na rasata ba makawa mutuwa zanyi. wallahi fatuha Zan iya mutuwa idan kin zama malakin wanina ,wayyo Allah Na 😭 nayi zurfin ciki ta kin bayanar miki DA kece linzamin zuciyata ,DA ace wani ne ba majeed ba koda Zan ransa komai nawa bazan bar masa ke ba, saidai kash majeed ya wuce duk yanda kike tunani a wajena Ina son majeed sonda Zan iya sadaukar masa DA komai nawa ciki KO hard'a ke ,ya ida Zan can sa hawaye Na cikiba DA ambaliya a fuskar sa." Majeed DA tunda SadiQ yafara magana yake tsaye baki'n kofa basu Lura dashi ba domin sunyi nitsa a duniyar Su ta masoya, kamar gumki ya zama zufa ne ke fito masa a KO Ina, wani irin jirine yake daukarsa ji yayi kamar ya kurma ihu domin a tunanin sa mafarki yake. DA kyar DA taimako'n adu'a yabar wajen KO gabansa baya gani, yana zuwa falo ba kowa DA sauri yayi waje.

Fatuha KO wani irin farinciki ne ya kamata. takara shigewa a jikin SadiQ , A cikin zuciyar ta tace "Ya Allah Na gode maka, Ashe bani kadai nake haukana ba, kuka ta fashe dashi DA ta tuna cewa baki'n alkalami ya Riga ya bushe" daman SadiQ yasan bazata iya bashi amsa ba. Dan hak'a ya Kara rungume ta suka ci gaba DA kukan Su abin tausayi😢.

Majeed Na shiga motar sa ya jata DA karfin tsiya, DA Sauri Mai gadin ya bud'e Masa gyet saura kada'n ma yabi ta kansa , ikon Allah Mudi maigadi yace domin abun yayi matukar bashi mamaki Allah ya kyata yace yashiga dakin sa ya kuna redio yana saurare.

Kudu majeed yak'e saman titi k'amar zai tashi sama hawaye na bin fuska'r sa , kuka yak'e sosai gashi kuma yana tuki Na fitar h'ankali duk inda ya huce sai an bishi DA kallo , yana shan kwana wani babban mota yashiga gaban sa ji kake kuuuuuuuuuuuuu😭🙆‍♀Innalillahi wa'inna ilaihi raji'una.


*Taku har kullun Salma masu'd Nada no*
*CAPTAIN SADIQ*
👮🏼‍♂

*Writing by*
*salma mas'ud nadabo*

*Edit by*
*Raheenat*

http/mobile.Facebook.com/Real-Hausa-fulani-writers-forum RHFWF-173984973194167/?refid=52red=opera_speed_dial_&yn=H-R

*Email* [email protected]

*Facebook* www. Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERSFORUM.CM


87_88

*_this page is for u Anuty Raheenat ina jin dadi yadda kike bani goyan baya tare da min good editing and every single person that always comment on this novel, I am in love with ur comments_*



Firgigit sadiq yamike yana sauke ajiyar zuciya, ya jiqe sharkaf da zufa da kyar ya iya miqewa ya bude fridge ya tsiyayo ruwa yana sha . tarine ya zomai lokaci guda da gudu ya shige toilet yana yi jini na fita da kyar ya saita kanshi ya dawo saman bed yana furta duk addu'ar da ta zo bakin shi. bai taba mumunar mafarki irin h'aka ba, kuka ne ya kubuce mai dan baya fatan ranar da majeed zai rasa rayuwar sa saboda furicin shi a kan fatuha, wayar shi yayi sauri rarimowa ya fara kiran layin majeed kira biyu zuwa uku majeed ya dauka da alamama yayi nisan bacci, hello baby, hamdala sadiq yayi tare da sauke ajiyar zuciya, dama wani abu zan tanbaye ka tunda bacci kake shikenan sannan sadiq ya katse wayar tare da komawa toilet ya dauro alwala yana rokwan Allah ya rage mai san fatuha a rai shi.

Kiran sallah asuba ne ya tashi fatuha alwala kawai ta daura tare da gabatar da sallah .bayan ta idar ne ta wuce daki'n angel a hankali ta murda kofar taci sa'a ta bude cikin natsuwa ta shigo angel da fitowar ta d'aga toilet ke nan daure fuska tayi tare da janyo hijabin ta tada sallah. baki'n gado fatuha ta samu ta zauna tana jiran jidda ta idar da sallah, ko da ta idar bata kalli inda fatuha take ba sai qoqarin barmata daki'n da take. riqe hannun ta fatuha tayi cikin sanyi murya tace "Angel fushi kike dani ko?" shuru tayi kamar ba da ita fatuha take ba sai ma qoqari zame hannuta jin ta kasa zamewa ya sata saki'n kuka tana cewa, "Ni ki kyale ni tunda baki san babana? kin zabi ki zauna da wani ba daddy na ba" hawaye ne suk'a fara yima fatuha zarya tana girgiza ma jidda kai, tace "Angel ya za ayi nace bana san abban ki? please ki daina fushi dani fatuha ta fada tana shafa fuskar angel" cire hannu angel tayi tace "Idan har kuna so ku ga farin cikina to ku fasa auran da zakuyi d'aga ke har daddy ta fada cikin d'aga murya sannan ta fita ta barma fatuha daki'n" kuka fatuha ta saki na shiga uku wannan wani irin abune gabaki d:aya duniya ta mana kunci. ya Allah ka kawo mana mafita fatuha ta fada tare da tashi ta bar daki'n.


Haka angel ta rinqa fushi da su fatuha Dan ko saurarasu ba tayi .duk abin yabi ya dame su idan kun angel na magana to da mom tak'e gashi ta daurawa basma karan tsana dan ko bari batayi ta taba abu itama ta taba. abin duk yabi ya damu Sadiq tun basma bata dauka abinda zafi har abin ya fara bata mata rai ga uban na mata diyar na mata,


Yauma kamar kullun mai gyaran jikin ta zo. kurkur tayi masu tabi ko ina na jikin su dashi da saqoqo sannan ta had'a masu Zuma cokali 3 madara peak ta ruwa rabin gwangwani da white egg 3 da lemon tsami d'aya ta had'a ta buga su ta murje amaran dasu ga wasu turaru ka masu kamshi da suke wanka da su a tsimin lale. tuni fatar su ta fara canza launi ga wani sheqi da suke abunka da fararen mata ko kaya suka cire kamshi suke.


Bangaran kayan ni'ima ba'a magana dan wasu mom da kanta take h'ada masu ,na kaza dana tantabara gashi kullun sai an basu madara da zuma sun sha kayan fruit ko har turewa suke su Kansu sun san tsumu nayi masu, mom ta saki murmushi tace "Kai amma wannan gyaran yana yi sosai? ji yadda suka murje yaran nan ku ni da nake mace ina taba fatar su biyo ni take ina jin dadi bale kuma angwayan" rufe fuskar su suka dan mom ba qaramar kunya ta basu ba. bayan a kama gyaran jikin mom ta raka batul mai gyaran jikin har baki'n motar ta sannan ta juyo ko da ta dawo cewa tayi su fatuha su h'ada duk abinda suke buqata dan jibi za'a koma family housa a fara gudanar da biki,


Jikin fatuha ne yayi sanyi ,dan yanzu har ta fara fidda tsamani ya zamar mata dole ta koyawa kanta son majeed. Ko da ta shiga bedroom dinta kayan ta ta shiga hadawa tana hadawa tana sana'ar wato kuka sannan ta aje trolley din a gefe,


Baki'n wani hadadan gida naga sadiq ya tsaya da motar shi horn yayi mai gad'i ya bude gate. gaishe shi mai gadi'n yayi a taqaice sannan yayi parking din motar suka fito tare da majeed kallan gidan majeed yayi yace "Big man gaskiya gidan nan na da kyau?" murmushi sadiq yayi yace "Taho mu Shiga" babu abinda ba'a zubaba na mure rayuwa ciki'n gidan .iyakar haduwa ya hadu, sai dai kash ba muradin ranshi bace zata kasan ce da shi ba a wannan gidan hak'a suka gama zagaya gidan sannan suka wuce gidan majeed masha Allah shima gidan iyakar haduwa ya hadu dan sun kashewa gida jan kudi bana wasa ba. bayan duk sun gama dubawa sadiq ya aje majeed a gida sannan shima ya nufo gidan Su,


Cikin sallama ya shigo angel na parlour zaune tana kallo ,ciki ciki ta amsa sallamar tana qoqarin barin parlour janyo ta sadiq yayi tare da langwabe kai yace, "Angel nasan sarai kin san ba kyau fushi da iyaye ?me yasa kike fushi da daddy kin ?um nasan nayi laifi amma ya kamata by now an yafe min" kuka ta samai tana cewa "Ni daddy Anuty fatuha nake so?idan ka aure ta ma hama min komai" d'ago da fuskar ta sadiq yayi yace "Me yasa bak'i san Anuty basma? tana fa sonki angel ?tana maki'n duk abinda kike so?" bata rai tayi tace "Ni bana son ka aure ta that is all ,ni Anuty fatuha nake so fuuuu ta wuce sadiq tayi dak'i" tsaye sadiq yayi yana mamakin irin kafewar jidda .fatuha dak'e qoqarin fitowa d'aga kitchen tayi lamo tana jin duk abinda suke. haurawa sama yayi ya wuce part din shi fatuha tana ganin haka sai ta bi bayan shi a hankali ta bude kofar daki'n. tsaye ta ganshi a hankali ta Isa ta rungume shi ta baya wani irin yar sadiq ya ji har itama fatuha di'n, juyo da ita yayi yana smile dan ja mata hanci yayi yana binta da wani irin kallo ba qaramin kyau tayi mashi ba. a hankali ya kai mata pack a goshi itama pack ta mai tare da zame jikin ta ta zauna zaman sofa, biyota sadiq yayi tare da yin kneel down a wajan yana kallan kyakyawar fuskar ta, yace "Fatuha kinyi kyau?" yar dariya tayi tare da rufe fuskar ta. murmushi sadiq yayi a hankali yasa hannu ya cire hannu ta dak'e fuskar ta. hawaye ya gani suna mata zarya, langwabe kai sadiq yayi dan shima da zai samu dama da kukan zaiyi. tashi yayi ya zauna saman sofa tare da janyo ta jikin shi yana lalashi'n ta, "Please fatuha ki daina kukan please bana so?" lamo tayi a fafadan qirjin shi tana jin bugun zuciyar shi tare da wani irin feeling na da ban wanda bata taba jin shi ba sai akan Sadiq, hak'a yake ji a hankali take sauke ajiyar zuciyar. d'ago da fuskar ta sadiq yayi yana bin ta da kallo mai cike da so. zuciyar shi sai bijuro mai da wasu abubuwa tak'e zame jikin shi yayi tare da komawa saman bed ya zauna yana kallan fatuha, itama di'n shi take kallan. kauda kai tayi tana wasa da yan yatsun hannun ta. miqewa tayi tana qoqari tashi sadiq ya ruqo hannu ta tare da janyo ta ta fada jikin shi, murmushi ta saki tana kallan shi a hankali ya daura lips din shi saman nata ya fara kissing nata kasan cewa fatuha tasha tsimi har ta gaji hakan yasa ta kasa hana shi. sai da yayi kissing nata san rai shi sannan ya sake ta, yana bin ta da kallo yana sauke numfashi cikin cool voice sadiq yace "Fatuha!" lamo tayi tana jin shi dan har bata san abinda zai sa ta matsa kusa dashi. shafa gashin kanta ya Shiga yi a hankali hakan ba qaramin dad'i yake ma fatuha ba can kamar an mitsine sadiq ya miqe yana tari da sauri ya shige toilet fatuha ta biyo bayan shi tun kafi ta iso ya kule toilet din da key dan baya so taga halin da yake ciki ,tari yake mai jini ya Dade a toilet din yana abu d'aya. fatuha ko duk ta rude sai faman kiran suna shi take yana bude toilet tace "Mai kyau me ke damun ka please ka fada min?" ta fada ta shafa mai gefen fuska ,saman bed ya hau tare da cewa b)"Ba komai kawai na kware ne haka fatuha ta rinqa mai sannu sannan tasa kai ta fita.


*Washe gari*


Bayan fatuha tayi wanka ta shirya cikin lace dinta maroon mai kyau masha Allah tayi kyau har ta gaji. ko da ta fito parlour ba kowa bedroom din angel ta shiga kwance ta hango ta dan girgiza kai fatuha tayi tare da bud'e wardrobe din ta tafido trolley din ta ta fara zuba mata kayan ta sai da ta gama zuba kayan tsaf ta aje trolley din tana qoqarin fita angel ta tashi "Anuty?" tace cikin sanyin murya juyowa fatuha tayi tana kallan jidda idanuwan ta tap da kwalla da gudu jidda ta rugu ta rungume fatuha tare sakin kuka itama fatuha kamar jira take ta fara nata kukan ba mai lalashin wani sai da suka ci kuka san ransu sannan suka yi shuru suna sauke ajiyar zuciya a tare, angel ce ta dago tace "Anuty shikenan yanzu bazaki auri daddy ba?" dan smile fatuha tayi tare da cewa "Angel bai kamata kina damun kanki ba kinji? idan kina san bina sai ki bini mu zauna tare". bata fuska angel tayi tace " Aini nafi so na ganki da daddy bada kowa ba" haka dai fatuha ta rinqa lalashin angel sannan ta tafi ,

Direct part din Sadiq ta wuce a hankali ta bude kofar part din ta shiga. parlour ba kowa sai kamshi dak'e tashi bedroom ta shiga kwance ta hango shi qudidine cikin blanket a hankali ta qarasa zama tayi gefen bed din. a hankali ta fara janye blanket din tana kallan face din sadiq a hankali ta kai mai pack a goshi , ya ware sexy eye's ball's din shi ya sauke su kan fatuha smile ya saki tare da juyawa ya gyara kwanciya dai dai saitin kunan shi tace cikin cool voice din ta "Uncle ka tashi kowa ya gama shiryawa kai ka dai ake jira?" ware idanuwa yayi yana Kallan ta janyo ta yayi ta fad'a saman fafadan qirjin shi yace "Fatuha me yasa kike so ki katsemin bacci?" um lamo tayi a qirjin shi tace "Saboda na rinqa kallan ka kafin muyi nisa da juna ta fada idanuwan ta tap da kwalla" tashi zaune sadiq yayi yana facing nata shima ji yake kamar yasa kuka, langwabe kai fatuha tayi tace "Ka h'ada kayan ka ne?" no, ok bari na h'ada ma,



Haka fatuha ta shiga hada ma sadiq kayan shi yana kallan ta saida ta gama hada kayan tsaf tabi daki'n da kallo. kuka ya kubuce mata saboda tunowa da rayuwa da sukayi yanzu rayuwar ta zama tarihi kuka take sosai, janyo ta sadiq yayi jikin shi yana lalashi a hankali ta fara magana, "Mai kyau me yasa mutum baya samun abinda ya ke so a lokaci da yake so? ta fada tana qara rushewa da kuka" a hankali sadiq ya lalubo lips din ta ya fara mata hot kiss wanda shi kanshi bai san yana hakan ba, bai kyle ta ba har sai da ta tsaigai ta kuka. sannan ya sake ta yana maida numfashi. h'ada face nasu yayi guri guda yace "Fatuha please ki dai kuka? , dama shi rayuwa bai zama dole ma same duk a bind a make so, muyi hakuri jarabawa Che saga Allah ,insha Allah zai Bamu Sak'a mak'o Mai kyau , Dan h'aka muyi adu'a Allah yasa h'akan shine Mafi alheri a garemu , kuma ki Daina kukan h'aka domin Hana ta Dan min da hankali a duk sanda naji. d'aga kai tayi tare da kauda kanta dan gabaki daya kunya ta lulube ta. tashi tayi ta fita da sauri daga bedroom din, ko da ta fita jingina tayi da kofar tana maida numfashi a hankali ta daura hannuta saman lips din ta. ji tayi kamar an yaye mata baki'n cikin dake damun ta sannan ta fito da gudu d'aga part din haka shima bangaran sadiq h'aka yaji.



Bayan kowa ya gama h'ada kayan shi su ola suka wuce da su boot. ga baki d'aya fatuha jiki'n ta yayi susuku, h'aka sukayi mota 5 fatuha ta dade tana kallan gidan sannan suka bar harabar gidan tare da harbawa kan titi,


Bayan sun Isa family house dangi har sun fara cika, take jikin fatuha yayi sanyi dan tasan tabas ta rabu da sadiq har abada, h'aka shima bangaran sadiq hakan yake ji a Randa,


Bayan sun dan huta kowa ya aje kayan shi inda ake ajewa, aka kira mai lale ta fara yima amaran lale kafin ka ce mai qawayan amaran sun fara halara Zara da Nana har sun zo sai rawar kai suke zubawa. sallamar da akayi ne yasa fatuha juyowa cikin fara'a ,waza ta gani inba fatsima ba. da gudu ta ruga ta rungume ta na murna h'aka itama tuni daki'n ya dau shewa duk da fatuha ba jin dad'i take ba amma ganin fatsima ba qaramin dadi ya mata ba, hakan yasa ta fara walwala.


Bangaran basma ma haka qawayan ta duk sun hada yan gayu masu ji da aji sai shewa suke suna taya basma murnar samun handsome kamar captain sadiq .sai pics suke kamar ba gobe kowa ce ka duba face nata kasan cikin farin ciki take,


Angwayan ma friends nasu da suke qasashan waje har sun fara sauka, haka part din nasu ya cika tap duk wannan abunda ake sadiq na gefe ya zuba masu Na mujiya kamar ba abinda ke damon shi. sun san halin miskilan cin shi shiyasa ba kowa ya damu da h'aka ba sai Dr yakub dak'e ta faman lura da shi dan yasan sarai ciwo ne ke cin shi kowane lokaci zai iya ta shi..





*_fan's kuyi h'akuri da wannan page din ba yawa, saboda ina schl shiyasa. amma insha Allah gobe zan maku page mai yawa_*


*Taku har kullun Salma mas'ud Nadabo*
[7/4, 9:54 PM] ‪+234 814 314 2333‬: *CAPTAIN SADIQ*
👮🏼‍♂

*Writing by*
*Salma mas'ud nadabo*

*Edit by*
*Raheenat*

http/mobile.Facebook.com/Real-Hausa-fulani-writers-forum RHFWF-173984973194167/?refid=52red=opera_speed_dial_&yn=yn=H-R


*Email* [email protected]


*Facebook* www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERSFORUM.COM



89_90


Shirye shirye suke sosai kasancewar yau ake kamu. da misalin karfe 4:00pm kowace ka gani shiryawa tak'e ciki'n ashobe. Fatuha da ke zaune cikin toilet tana sana'ar kuka knocking din kofar da akayi ne ya sata miqewa tana share

Please Login or Register in order to submit comment