Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Yana fita sadiq ya bude murfin motar cikin zafi, shigar fatuha bedroom ke da wuya taji an banka do kofar cikin zafin rai waigowa tayi a dan tsorace fisgota sadiq yayi tare da fizge wayar da dake hannu ta yayi wurgi da ita ta bigi Bango ta dawo a tarwatse ware ido fatuha tayi tare da sakin kuka, manna ta sadiq yayi da b'ango ya koma mata kamar zaki idanuwashi sunyi jawur kamar garwashi cikin kakausar murya yace "Waya baki izini fita gidan nan bada driver ba?" kuka fatuha ta kuma saki ko bakin magana ta rasa ganin bata da niyar bashi amsa yasa sadiq sakinta tare nufar kofar fita ya banka ta da karfi ya fita hata mom dake part din ta sai da taji bugun kofar da sadiq yayi. zame wa fatuha tayi awurin tare da sakin kuka, koda sadiq ya Shiga part nashi cili yayi da bribriefcase din shi saman three star ya zauna tare da lumshe ido yana maida numfashe sama sama. ware idanuwan shi yayi saboda d'aya rintse fatuha da majeed ya yake gani shafa ganshin kanshi yayi da hannu yace noooooooo! Cikin d'aga murya........



*Taku har kullun salma mas'ud nadabo*
[7/1, 10:09 AM] โ€ช+234 903 344 8176โ€ฌ: *CAPTAIN SADIQ*
๐Ÿ‘ฎ๐Ÿผโ€โ™‚


*Writing by*
*Salma mas'ud nadabo*

*Edit by*
*Raheenat*

๐Ÿ“˜ *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*๐Ÿ„
โ˜…We are the bestโ˜…

http/mobile.Facebook.co m/Real-Hausa-fulani-writers-forum RHFWF-173984973194167/?refid=52&red=opera_ speed_dial_&yn=H-R


*Email* [email protected]


*Facebook* www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERFORUM.COM

75_76

Sai da fatuha taci kuka ta gaji sannan taja jiki ta hau saman bed ,tarasa dalilin da yasa mai kyau yake yin irin haka. kuka ta kuma rushewa da shi data tuna a irin yana yin data ganshi, h'aka ta riqa raira kuka kiran sallah magrib yasata tashi jiki ba qwari ta dauro alwala tare da gabatar da sallah. zaune tayi bisa daduma abin tausayi ganin tunanin be fishe ta yasa ta janyo AlQur'ani tana karantawa har aka kira sallah ishi bayan ta idar da sallah ta ja jiki ta koma bed ta cigaba da raira kukanta abin tausayi turo kofar da akayi ne yasata miqewa tana kallan kofar, angel ce tsaye bakin kofar qarasowa tayi d'akin tare da hawa saman bed din tace "Anuty waya saki kuka?" murmushi fatuha ta qaqaro wanda iya karshi laban ta tace "Ido nane ke ciwo" sorry Anuty , ki fito parlour kuyi dinner naji shuru ne baki fito ba ke da daddy shiyasa na biyo ki. dadday dai yace ya koshi, ko kema kin koshine? ta fadi zancan tana kallan fatuha Dan smile tayi tace ban qoshi ba ina nan zuwa naci komin dare fita jidda tayi d'aga daki'n fatuha ta cigaba da raira kukan ta har sai da kanta ya fara ciwo, ganin bame lalashin ta yasa tayi shuru tana sauke ajiyar zuciya bacci barawo ya sace ta.


Bangaran sadiq in ban da juyi saman bed ba abinda yak'e da kyar ya samu ya rintsa.


*Asuba ta gar'i*

Ko da fatuha ta tashi jiki ba qwari tayi sallah sannan ta qara komawa ta kwanta saboda kanta dake mata ciwo. Kuma taci sa'a yau weekend ba ita ta tashi ba sai karfe 11:30pm ware ido tayi tare da kallan agogan d'ake makale a daki'n, cikin sauri ta mike tare da shiga toilet ta watsa ruwa. ko da ta fito mai kawai ta murza sai after dress d'ata zura parlour ta fito ba kowa dining area ta wuce tare da bude kulolin dak'e jere wanjan chpis ne da farfesun yan'ciki zuba wa tayi a plate tare da had'a ruwan tea sannan ta zauna. loma biyu zuwa uku tayi ta ture plate din dan kwata kwata bata jin d'adi abincin.

Babban abinda ke daure mata kai ta rasa laifin da tayi ,yanke shawarar zuwa bama sadiq hakuri tayi duk da bata san laifin data mai ba dan bata iya jurewa wannan horan. tashi tayi tare da kwashe kwanikan ta kai kitchen sai da suka dan taba hira da su baba jinmai sannan ta fito.

Direct part din Sadiq ta wuce a hankali ta murda handle din kofar tare da shigowa cikin sallama zaune sadiq yake saman two star da laptop gaban shi kallo d'aya zaka mai kasan babu annuri a fuskar shi. dogo kai yayi ya kalli fatuha tare da lumshe ido ya kauda kai yace "Just leave me alone" sadiq ya fada a tsiwace tare da tatara takadun d'ake gaban shi da laptop din ya shige bedroom tare da buga kofar da karfi. kuka fatuha ta saki tare da fita d'aga part din da gudu jin ta fita yasa sadiq jinji Na da kofar bedroom ya lumshe ido.


Da gudu ta wuce mom a parlour ta shige daki saman bed ta fada tare da sakin kuka mai cinrai. kuka taci ta gaji, mom d'ake parlour bin fatuha tayi da kallo tana mamakin mai ya h'ada su, koma dai minene ai sun saba zasu shirya ne amma abin mamaki basa kai haka kauda zancan mom tayi tare da cigaba da kallan ta, duk yinin yau babu wanda yaci abinci cikin su fatuha inban da kuka ba abinda take shi ko sadiq sai baki'n rai dayake fama da shi,

Iskace mai sanyi da ke ta kadawa da alama ruwa za'ayi saboda damuna data fara shigowa. qara cida ce kawai ke tashi b'akin widow sadiq ya tsaya a hankali ruwa ke saukowa kallan ruwan yake yanda yake saukowa da karfi a wannan karan lumshe ido yayi tare da ware su, ya koma saman bed ya kwanta bangaran fatuha tunda aka fara ruwa tak'e lilibe cikin blanket


Gaba ki d'aya yini yau ba wanda yayi ma wani magana cikin fatuha da sadiq, horan dak'i sukayi wa kansu ba tare da sun nemi abin sama bakin sallatin su ba , har bacci ya kwashe su.


Shiryawa yake cikin manyan kayan shi kasan cewar yau zasu je family meeting, fatuha ce ta fado mai a rai kawar da tunanin yayi dan har yanzu be huce ba ko yana hucewa sai ya d'awo dag'a meeting cikin Isa yake saukowa d'aga upstairs ,lokacin har su mom sun shirya suna parlour zaune suna jiran fitowar sadiq da fatuha ganin sadiq ya sako yasa mom cewa angel, kira Anuty mu wuce , ko da angel ta shiga d'akin kwance ta samu fatuha qudindine cikin blanket , fitowa tayi da sauri d'aga bedroom din tace "Grandma Anuty bacci take" toh fa! amma ai fatuha bata kai haka tana bacci .shiga d'akin mom tayi tare da qarasawa wajan bed din fatuha tace a hankali, a hankali fatuha ware idanuwan ta da suka yi nauyi saboda tsabar kuka, kallanta mom tayi tace "Mike damun kin fatuha?" dafe kai tayi tare da cewa mom "Kai nane ke ciwo" eyya sorry dama meeting zamu tunda b'aki jin dad'i ki zauna kawai a gida to kawai tace tare da shigewa blanket, sannan mom ta fita ko da ta fita sadiq ta aika ma harara tare da ayana ma ranta in sun dawo zatayima abin tufkar hanci.


Katafarin parlour su da aka ware danyi meeting suke zaune, tunda sadiq ya shigo gaban shi ke yankewa yana faduwa yarasa dalilin h'akan addu'a da ke bakin shi ya furta dan samun na tsuwa. majeed ya shigo tare da zama gefen sadiq tare da miqa mai hannu suka gaisa da kyar sadiq ke danne zuciyar shi kan majeed tare da bata hakuri, Alhaji babba ne ya shugo sanye da babba riga tasha aiki sai sheqe kayan suke, cikin sallama ya shigo tare da zama a kujerar sa ta musanman wato kakan su sadiq, ammi na gefan shi ta dama sauran jikoki da iyaye na gefe da yan uwa .


Taro ya fara budewa da addu'a sannan ya fara jawabin cikin natsuwa kamar yadda kuka Sani Inayi maku murna da zuwa wannan taro na qara dankwan zuminci. tare da yi maku albishir da abubuwa da yawa na farin cikin a wannan shekara mun samu kimani naira billion dari cikin riba kasuwancin mu sannan mun talafawa gidan marayu tare da asibitoci sannan anbiyawa mutun 30 kujera maka , kabara wajan ya dauka tare da hamdala, sannan Kuma ga muhimiyar sanawa ita ce majeed ya samu matar da zai aura, sadiq dake zaune saman kujera gaban shi ya qara yankewa ya fadi, muryar Alhaji babba ce ta dawo mai dodan kunne, ba kowa bace sai yar gidan ibrahim wanda yake ruqu fatuha Kuma har gidan iyayan ta muje munyi bin cike ashe ma akwai sanaya a tsakanin mu Kuma sun aminci sun bada. wani irin gumi ne ya karyo ma sadiq mai matsanan cin zafi take nan ya fara ji wutar shi na dauke wa ba sadiq ba hata mom sai da ta girgiza da wannan furin cin, wata kalmar ya qara jefowa a karo na biyu sadiq Kuma mun yanke shawarar bashi kanwar sa basma tare da sharadi idan har ya kawo wadda yake so nan da sati daya kamin asa biki to za'a basa dama ya auri wadda yake so basma ma kuma ta hakura zabin shi wannan shine hukuncin dana yanke. sannan ya kalli baban basma Alhaji khabiru cika mana taro da addu'a.

Gabaki d'aya parlour juyawa sadiq yake da kyar ya samu ya miqe, majeed in ban da washe baki da yake ba abunda yake dan ko ta kan sadiq bai bi ba haka basma baki har kunne sadiq ne ka dai da mom basu farin ciki sai hanan. yana fitowa d'aga parlour parking space ya nufa cikin sauri ya bale murfin motar ya shiga da gudu ya fisgi motar ya harba kan titi gudu yake tsulawa kamar zai tashi sama yana isowa gida ya danna horn bala mai gadi na bude mai geta yace "Subhanalal " saboda yadda sadiq ya shigo da motar yana shigowa ko dai-daita parking ya kasa ya bale murfin motar ya fito cikin sauri ya wuce part din shi yana shiga ya zame bakin kofa tare da dafe kanshi๐Ÿคฆโ€โ™€ maganar Alhaji babba na dawo mai. mikewa yayi ya shige bedroom saboda har yanzu bai dai na ganin jiri ba, wani irin kuka sadiq ya saki mai tsuma zuciyar mai saurare kneel down yayi a wurin can Kuma ya mike yashiga fatali da kayan d'akin kamar saban kamu. sai da yayima d'akin fata fata ya shiga toilet da kayan jikin shi sakar ma kanshi shower yayi, maganganun Alhaji babba namai yawo a brain wata zuciyar tace "Wato jiya fatuha tabama majeed izinin turawa gidan su?" hadeye kukan da yake yayi tare da fitowa sharkaf ya zauna kasan carpet be damu da kayan dake jikin shi ba.

Bangaran fatuhu ko tunda su mom suka fita gabanta ke faduwa, ta rasa dalilin haka ta rasa suku nin ta jin an bude kofar d'akin ya sata waigowa mom ce tsaye bakin kofa murmushi fatuha ta saki wanda iya karshi laban ta, mom har kun dawo da wuri haka? eh tace tana qoqarin danne damuwar ta tare da qarasa shigowa zama tayi kusa da fatuha cikin sanyi murya tace "Fatuha gobe da safe ki shirya zaki je wudil baffa nasan ganin ki?" sannan ta tashi ta fita kallo fatuha tabi mom da shi take nan jikin ta ya haubari da tsoro tsoro ko dai uncle ya kai qarata kauda zancan tayi tasan ma ba zanyi hak'a ba ,amma zuciyar ta na cike da tanbayoyi, ganin bata da amsa ta hakura.


Ola sadiq ya kira a waya bugu d'aya zuwa biyu ya dauka ina san ganin ka sadiq ya fada a taqaice ,ko da ola ya zo ganin Watsin da akayima dakin tsoro ya bashi kallan sadiq yayi da magana a bakin shi ganin fuskar sadiq ba annuri yaja baki ya tsuke. nuni ya mai d'aya gyara d'akin shi Kuma ya shigida saman sofa hawaye daya na bin daya kamar ba soja ba,


Gabaki d'aya gidan Alhaji Ibrahim ba wanda ya rintsa, d'aga angel sai abba ne kawai suka samu bacci bangaran sadiq inban da kukan zuci ba abinda yake, fatuha tunanin me yasa baffa ke neman ta? take ko dai inna ce ta rasu? ba'a San fada mata girgiza kai kawai tayi.

Tunda safe fatuha ta tashi ta shirya cikin riga da sket din ta na atamfa yellow mai ratsin white a jiki masha Allah kayan sun hauta sai fuskar fayau, bayan ta kamala ta fito parlour cikin natsuwa ta gaida mom da abba d'ake ta break angel na gefe itama ganin bata ga sadiq ba yasa gaban ta ya qara faduwa a karo na biyar jiki ba qwari ta zo ta hada tea kurba biyu zuwa uku ta aje , mom ce tace "Fatuha har kin koshi?" eh mom dama in zan yi tafiya bana wani cin abinci to mom tace , sannan ta qara da cewa ga driver nan zan h'ada ku da shi in ya kai ki yau zai maido ki ki gaida mutun gida sannan inkin Isa ki kira ni ki fada min. lagwabe kai fatuha tayi tace "Wallahi mom jiya wayar ta lalace" garin yaya? fadowa tayi d'aga dressing mirror ta dauke, eyya to bari na baki baby Nokia in kin dawo a sake wata to fatuha tace tare da shi ga daki ta dauko sim din ta miqa mata wayar .mom tayi ta zura sim din ciki har ta kai bakin kofa ta dawo tare da haurawa sama part din sadiq ta nufa a hankali ta murda handle din kofar taji Kule gam tsoro ne ya kamata amma ba yadda ta iya haka ta dawo tare da yima mom sallama angel ko sai rigama take sai tabi fatuha mom ta hana.

Shigewa mota tayi driver ya harba da su kan titi cikin dan qanqanin lokaci suka Isa wudil. cikin kwatan can fatuha har driver ya kawo ta gidan fitowa tayi a hankali tana qare ma gidan su kallo gabaki daya gidan ya canza a yadda ta San sa mamaki ne ya bayana a fuskar ta qarasa Shiga tayi cikin sallamah inna d'ake parlour ce ta fito tare da yima fatuha maraba da zuwa duk da fatuha ba'a cikin jin dadi take ba bata yadda inna ta gane ba, parlour ta janta suka Shiga har yanzu mamaki ne shifide a fuskar ta tace cikin sanyin murya "inna waya gyara gidan nan?" murmushi inna ta saki ina yaran nan sadiq wallahi shi ya mana abin arzikin nan murmushi fatuha ta saki mai cike da jin dadi baffa ne ya yaye labilan ya shigo har qasa fatuha ta tsugunna ta gaisheshi amsa mata yayi a taqaice sannan ya samu wuri ya zauna. itama fatuha qasa tayima kanta mazauni tana jiran jawabin baffa gyaran murya baffa yayi tare da cewa "Fatuha nasan cewa na maki laifi amma kiyi hakuri ina fatan bazaki watsamin qasa a ido ba? ina fata bazaki bani kunya ba ?duk wannan jawabin da baffa keyi kan fatuha na qasa ,d'ago kai tayi tace "insha Allah baffa bazan baka kunya ba" yauwa diyar albarka, dama dan uwan sadiq ne ya zo neman auran ki tare da iyayan shi jiya da dare, mukanmu munyi mamaki da wannan zuwa fatuha ganin halacin da zura'a suka mana gashi nasan baban yaran hakan yasa na amince dan na lura yaran mai natsuwa ne Kuma dama neman auran budurwan anso iyayanta su zaba mata miji Na gari da wannan nayi la'akari na zaba maki majeed a matsayin miji. dagowa fatuha tayi a razane dan sai yanzu ta fahimci inda aka dosa idanuwan ta tap da kwalla suka ciko nan take hawaye suka fara anbaliya a fuskar ta me yasa mai kyau zai mata irin wannan horan me yasa fita tayi d'aga parlour da gudu ta fada dakin inna ta saki kuka mai tsanani mai ban tausayi, inna ce ta dafa bayan ta tana lalashin ta, haba fatuha bai kamata ki watsawa muta nan qasa a ido ba Kuma kowani mutun da qadarar dake zuwa mashi .fatuha idan dai majeed alkairi ne a gare ki Allah ya tabatar haka inna ta riqa bitana tausar fatuha har ta samu tayi shuru tana sakin ajiyar zuciya ko ruwa kasa sha fatuha tayi sai bayan sallah la'asar suka dau hanyar kano wayar tace dake cikin jaka taji qara message sai a lokacin ta tuna da mom tace ta kira ta curo wayar tayi ta karanta message din kamar haka,

_Sister ina matukar farin cikin Sanar d'ake yau buri na ya cika, tun jiya nake qoqarin kiran ki wayar takin Shiga ba wani albishir bane ila yaya sadiq ya kusa zama miji a gare ni ,sannan ina taya ki murnar zama inlow a gidan mu cikin family din mu d'aga basma._

Wani irin kuka fatuha ta saki mai cinrai ko ida karanta sakwan ba tayi ba wayar ta fadi jikinta in banda bari ba abin da yake. ashuru driver ya juyo haba fatuha komai yayi zafi maganin shi Allah bai kamata kina kuka irin h'aka ba ,duk wannan magana da ashuru yake fatuha ba jin shi take ba kalmar sadiq yazama miji Na kawai qwawalwarta ke fada mata har suka iso garin kano fatuha na sheka kuka kamar ranta zaifi ta, ko da ashuru yayi horn aka bude geta kafin ya tsada motar ta bale murfin motar ta fita da gudu sadiq da yanzu ya ji Qarar shigowar mota d'aga labila yayi tare da koma ya cigaba da zarya a bedroom din.

Da gudu fatuha ta haura sama ko kallan muta nan parlour batayi ba part din sadiq ta wuce Allah ya bata sa'a tana bude kofar ya bude, ganin bata gashin a parlour ba yasa ta shigewa bedroom da gudu . fadawa tayi jikin sadiq tare da sakin kuka mai cinrai ,rintse ido sadiq yayi yana jin yadda fatuha ke sheqa kuka cikin sarkewar murya tace "Uncle dan Allah karkamin wannan horan wallah bazan iya dauka ba, dama ace mafarki nake abin da nake ji ba gaske bane ta ida zancan tare da sakin saban kuka ta zame kasa.......



*Taku har kullun salma mas'ud nadabo*
[7/1, 10:09 AM] โ€ช+234 903 344 8176โ€ฌ: *CAPTAIN SADIQ*
๐Ÿ‘ฎ๐Ÿผโ€โ™‚

*Writing by*
*Salma mas'ud nadabo*


*Edit by*
*Raheenat*


๐Ÿ“˜ *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*๐Ÿ„
โ˜…We are the bestโ˜…

http/mobile.Facebook.com/Real-Hausa-fulani-writers-forum RHFWF-173984973194167/?refid=52&red=opera_speed_dial_&yn= H-R

*Email* [email protected]

*Facebook* www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERS FORUM.COM



77_78

Kuka fatuha ke rairawa Kamar ranta zai futa. gabaki d'aya jikin ta rawa yake qafafuwan sadiq ta riqe cikin shashekar kuka tace, "Please uncle I beg u in the of name of God a janye maganar auran nan wallahi ban shirya yin aure yanzu ba taqara rushewa da wani saban kuka" har yanzu jikin fatuha bar'i yake ,uncle ya zanyi da karatu na? bayan duk duniya ba abinda nake so sama da shi, wallahi uncle ba abinda ke tsakanina da majeed kaji ta qara sakin kuka mai cin rai ( *ko ni salma sai da na matse kwalla*๐Ÿ˜ฅ) da kyar sadiq ya sai ta kanshi tare da hade hawayan d'ake maqale a kwayar idanuwan shi ya juya, d'ago fatuha yayi d'aga zaune da take ya zaunar da ita zaman bed amma duk da h'aka ba daina kukan tayi ba .fridge ya bude ya curo robar ruwa ya tsiyaya a cup ya miqa mata .kuka kawai take baji ba gani, aje cup din yayi bedside drowe ciki cool voice din shi sadiq yace "Fatuha!" tsagaita kukan tayi tana kallan sadiq , lalashin ta sadiq ya shigayi cikin sanyi murya yace, "Fatuha ina so ki sani ko kadan bani na maki haka dan na hora ki" daura hannu shi yayi a fuskarta, h'aka itama fatuha ta daura nata saman hannu shi tana sauke ajiyar zuciya. ya cigaba da cewa "Bayan na dau alqawarin samamaki farin ciki har qarshan rayuwar ki fatuha? dan meyasa zan rusa maki mafarkin ki? ina so ki kasan ce mai daukar qadara mai kyau da mara kyau, da anyi shawara dani fatuha ba abinda zai sa na amince a katse maki karatun ki? ko yanzu nasan majeed zai barki kiyi karatu kinji, ki kasan ce me yima iyayan ki biyaya zaki ga riba haka, kuma insha Allah zaki so majeed saboda majeed nada kyawawan hali kuma yana sanki zai b'aki duk wata kulawa .ba zai bari ki taba zubar da hawayan ki a kanshi ba, ki daure ko so d'aya ne ki sama ranki son majeed ko dan yana dan uwa na" wasu zafafan hawaye ne suka gangarowa fatuha tana bin sadiq da kallo, dan ko bakin magana ta rasa, sadiq ko in ban da daurewa ba abinda yake dan numfashin shi neman yankewa yake ,sai ya numfasa yake cigaba da maganar saboda zafi da quna da qirjin shi ke mai, glass cup din sadiq ya miqa ma fatuha ta kafa kai ta shanye ruwan a hankali taji sanyin ruwan na ratsata, shiru suka dauka na mintina ba wanda ya tanka, can sadiq yace "Fatuha kimin promise baza ki tada hankalin ki ba, da kyar fatuha ta iya furta to wasu hawayan suka sulalo, jiki ba qwari ta tashi tana qoqarin fita sadiq ya bita da kallo dan bejin zai iya tsaida ta saboda ganin tama qara famamai ciwo a ransa".



Tana fita sadiq ya kafa rubar ruwan ya shanye yana maida numfashi tare da ganin wasu taurari namai yawo,

Tsayawa tayi b'akin stairs ta share hawayan ta dan bata san mom ta gani cikin natsuwa ta sako, mom da fitowar daga kitchen kenan ita da baba jinmai murmushi ta saki ah fatuha har kin dawo eh tace tana qoqarin hadiye hawayan idanuwan ta, masha Allah ya su inna? lafiya lau tace, sannan mom tace ina fata baffa bai maki dole ba d'aga kai kawai tayi alamar a'a, baba jinmai ce ta shafa fuskarta tace "Alhamdulillah hajiya ni dai bani da abin cewa kun gama min komai a rayuwa ta ida zancan tana matsar kwalla" d'aga kawo fatuha aiki sai gashi ta zama yar gida har zaku aura da ita hajiya na gode na gode Allah ya bar zuminci baba jinmai ta fada tana share kwalla idanuwan ta, haba baba ai duk mun zama d'aya ai fatuha ta cancanci abinda yafi haka, haka baba jinmai ta rinqa zuba Godiya sannan tasa kai ta fita, fatuha kuma ta shige bed ko da shiga d'akin sana'ar ta fara wato kuka dan ya zamar mata jiki d'aga shekaran jiya zuwa yau. bedside drowe ta bude ta Ciro sarkar da sadiq ya bata tana kuka sai ta ci kuka ta gaji sannan bacci ya dauke ta


Bangaran basma in ban da murna ba abinda take take, duk wasu qawayan ta ta fesawawa zata auri handsome, har wani jin ta take a sama yanzu, majeed ko ya kira layin fatuha har ya gaji yanke shawarar zuwa gidan gobe yaga sanyin idaniyan shi, sannan ya juya ya gyara kwanciyar shi .


Kiran sallah ne ya tashi fatuha jiki ba qwari ta shiga toilet tare da sheqa waka ta dauro alwala wani irin jiri ke dibar ta saboda kukan da tasha jiya ,da kyar ta iya gabatar da sallah ta zura uniform dinta tare da daukar school bag din ta ta fito,

Ko da ta qaraso dining area mom ce da abba sai angel dake gefe cikin natsuwa ta gaishe su kamar kullun

Please Login or Register in order to submit comment