Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

feshe jikin ta da turare masu kamshi sanna ta yafa veil din ta a hankali ta bude handle din kofar bedroom din parlour ta fito sadiq dake zaune saman two star ya lumshe ido, jidda na zaune gefe shi kamshin turaren fatuha ne yasa ta ware sexy eye's ball din shi ya sauke su kanta wani irin kyau ta mai tabe baki yayi yace ashe wannan yarin yar nada kyau duk yana wannan zancan ne a zuci miqewa yayi tare da daukar car key suka fita, gaba jidda ta shiga fatuha na baya jidda sai zuba mata surutu take.


Sun sha yawo kamar me ice cream ko har sai da suka ture, fatuha ko baki har kunne dan dadi duk inda suka wuce sai an kalle su saboda sun sha kyau sun gaji munjibir park sadiq ya kai su zama yayi a resting chair yana kallan su fatuha wasa ko ba wanda basuyi ba , basu suka bar munjibir park sai yamma likis a gajiye suka dawo gida, fatuha ko dadi fal a zuciyar ta jidda ko saboda tsabar gajiya tayi bacci cikin mota , sadiq ysa hancin motar shi cikin gida parking space yayi parking bala mai gadi sai washe mai hakura yake daga mai hannu sadiq yayi tare da dai daita parking din motar sannan ya kashe motar fatuha kamar jira take ta fito murfin motar gaba ta bude tana qoqarin daukar jidda shima sadiq ya turo kai da hannu yana qoqarin daukar jidda ji kake gwab sun qume kai wash sadiq yace fatuha ma haka yadda sadiq yayi da fuska shi yaba fatuha dariya sai kace baby ,dariya ta rinqayi har ana ganin fararan haqoran ta dariya da fatuha take sai ta qara mata kyau hakan yasa sadiq kallan ta kallan da yake mata ne yasa ta tsagaita dariyar tare da daga mai gira harara ya aika mata ,in kin gama dariyar ki dauko ta mu shiga gida dariyar da yake shirin zo mata ta guntse tare da daukar jidda.


*Taku har kullun Salma mas'ud nadabo*
*CAPTAIN SADIQ*
👮🏼‍♂

*Writing by*
*Salma mas'ud nadabo*

*Edit by*
*Salma mas'ud nadabo*


📘 *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*🐄
★we are the best★


http/mobile.Facebook.com/Real-Hausa-fulani-writers-forum
RHFWF-173984973194167/?refid=,52&red=opare_speed_dial_&yn=H-R

*Email*:[email protected]

*Facebook*:www.Facebook.com/REALHAUSFULANIWRITERSFORUM.com




53_54

*Ina farin cikin tayamu marnar zagayowar wata mai Albarka,wata mai falala,wata mai dubin nasarori da ni'imomi , yan uwa Dan Àllah kada mubari wanga babbar garabasar ta wuce bamu samu nasarori da yake ciki,mudinga istigfari da hailala neman gafara à wajen Allah,mu yawaita Adu'a da karatun Alkur'ani mai girma, mu dinga nafiloli da rokon Allah ya biya mana bukatun mu na Alheri,Allah Ubangigi ya bamu ikwan yin ibada a cikin wanga watan mai Albarka watan Ramadan Allah yasa muna da raban ganinshi Ameen Dan Alfarman anabinmu Muhammad Sallah'llahu allaihi wa'sallam*



Sadiq na gaba tana biye dashi à baya, bakin bedroom din ta taci birki tana qoqarin bude kofar sadiq ya juyo fuskarsa ba yabo ba falasa yace"Iina kuma zaki da ita bayan tayi bacci? um dama wanka zan mata shafa sumar jidda yayi tare da cewa "Ki samata night dress kawai saboda tayi nisan bacci" Allah ya taimake ta jidda ta taba fadin Kalmar shiyasa ta gane mai yake nufi,haurawa sama yayi ita kuma ta shige daki tare da kunna haskyan dakin shin fide jidda tayi sannan ta soma rage kaya jikinta ,sai da ta shiga toilet tayi wanka sannan ta fito daure da qaramin towel cikin natsuwa ta shafe jikin ta da mai tare da zura night dress din ta riga ce pink mai zanan cartons jikin rigar, rigar dai dai gwiwa ta tsaya sai dan siririn hannun kamar na vest gashin ta ta sharce ya baje a gadan bayan ta bayan ta gama shirya kanta ta shirya jidda cikin kayan bacci, sanna ta dauke ta a hankali take taka upstairs din saboda yau jidda ta qara nauyi cikin natsuwa ta murda handle din kofar part din sadiq parlour ba kowa sai sanyi AC dake tashi da kamshi direct kofar bedroom ta bude tsaye ta hango sadiq gaban dressing mirror yana goge sumar shi da qaramin towel sanye yake da bathrobe white hakan yasa ana ganin lalausan gashinshi na qafa kauda kai fatuha tayi, tare da yin sallama juyowa yayi ya qare mata kallo , mamaki gashin fatuha ke ba shi gashin har yaso ya mata yauwa juyowa yayi ya cigaba da abin da yake shin fide jidda tayi tana qoqarin fita,lumshe ido sadiq yayi tare da ware su yace "Fatuha" juyowa tayi tana kallan shi can sai tayi qasa da eye's ball's din ta, ki hada min coffee toh tace tare da fita downstairs ta dawo tare da shiga kitchen ta hada mai coffee ta dawo, ko da ta dawo yana zaune a parlour yana kallan news aje mai tayi saman stool tare da ficewa cikin natsuwa ya shiga shan coffee yana kallan news amma sai dai ku san kallan news din kawai yake ba wai dan yana fahimta ba kashe kayan kallan yayi ya koma bedroom saman bed ya kwanta tare da janyo jidda jikin shi lumshe ido yayi ba wai dan yana jin baccin ba ,saboda gaba ki daya kwanakin nan da tunanin kausar yake kwana.



Tana shiga bedroom ta fada saman bed tare da yin addu'a bacci ko minut 10 ba tayi ba bacci ya kwashe ta.


Kiran sallah asuba ne ya tashe ta wanka tayi tare da dauro arwala tana fitowa uniform tasa tare da gabatar da sallah, sannan ta shafa mai da fesa turare parlour ta fito ko ina share kwal hakan ya tabatar mata da rabi'a ta zo kitchen ta shiga washe da baki ta gaishe ta cikin fara'a ta amsa kasan cewar yau Saturday shiyasa fatuha bata je part din sadiq da wuri ba , rabi'a ta shiga tayawa aiki doya suka fere suka dafa sannan suka yanka fatuha ta gyara albasa rabi'a ta fasa kwai ta kade tare dasa albasa da percil da tonka santé da tafarnuwa da sauransu.. fatuha na kallo soya doyar da take , rabi'a da taga fatuha ta iya suyar sai ta sakar mata ta shiga gyara fruit saboda za'ayi ma sadiq juices da su bayan ta gyara ta markada ta juyo a jug ta saka qanqara ta kai dining area kafin ta dawo fatuha ta kamala soya doyar ta juye a kula rabi'a shigowa tayi da murmushi tace ,"Ah sannu da qoqari" murmushi fatuha tayi ki kai kula dining ni bara na soya kwai to fatuha tace tare da wanke hannu ta a zing ta dau kula ta wuce dining area, bayan ta aje kulla ta dawo parlour ta kunna kallo arewa24 tana kallan gari ya waye washe da baki take kallan dan tana jin dadin shirin ganin goma ta gota yasa ta haura upstairs tana bude parlour zaune taga sadiq saman three star, idanuwan shi lumshe abin ya so ya dan bata mamaki saboda be saba bacci a parlour ba sallama tayi sadiq da ke jingine kamar me bacci ya ware sexy eye's ball's din shi kan fatuha tare da amsawa kalla shi tayi ta tabe baki tare da gaishe shi amsawa yayi kamar be san magana fatuha ko shiga daki tayi amma sai dai yau tana ganin suku suku da sadiq yayi, yayi yawa sai taga yayi kamar wadda be samu bacci ba tabe baki ta yi tace ke "Fatuha ina ruwan ki?" duk wannan zancan a zuci takeyin shi tada jidda tayi washe da baki jidda ta tashe tana cewa,Anuty good morning? murmushi fatuha tayi tare da daukar ta ta kaita toilet ta mata kwanka suka fito suna dariya tsane mata jiki tayi sannan ta shafa mata lotion kasan Cewar akwai wasu kayan ta a dakin shiyasa anan fatuha ta shirya ta, jeans n t-shirt tasa mata rigar white sai jeans blue masha Allah tayi kyau sosai fita tayi daga dakin tabar fatuha na gyara daki.


Washe da baki ta fada jikin sadiq daddy morning, morning too angel, how was ur night angel, cool daddy n Ur's daddy same ya ida zancan yana mata pack, daddy yes sweet, um me ya sami eye's din ka sunyi ja, lumshe ido yayi yace angel daddy ciwo ido yake, sorry daddy ,a kira uncle yakub ya duba ka please daddy, na warke ai har ma nasa magani ,sure daddy? yes angle pack ta mai tare da cewa daddy am Hungary, ok ina Anuty ? Anuty na busy now, OK muje nayi feeding naki ko sweet, OK daddy daukar jidda yayi yana mata wasa tana dariya sai da suka qaraso dining area ya ja kujera ya zauna sannan ya d'aura jidda saman cinyar shi ya shiga saving din su sai da ya kamala ya fara feeding din jidda yana bata tana bashi cikin jin dadi.


Bayan ta gama share bedroom din tas ta dawo parlour ta kwalwale shi tas, ta kunna Burne a socket tare dasa turaran wuta tuni part din ya dau kamshi mai sanyi gudun AC ta qara lumshe ido tayi tare da zama saman three star tana qarema dakin kallo, ita kanta part din ya mata kyau yadda ta gyara shi ji tayi kamar tayi bacci tashi tayi ta fita daga part din.


A hankali take sakowa daga upstairs jidda dake saman cinyar daddy ta kwalawa fatuha kira, cikin jin dadi Anuty juyowa fatuha tayi har sai da gashin ta iska ta kada shi fari tayi da ido tace "À" dariya jidda tayi tace "Daddy ka ga yadda gashin Anuty yayi lumshe ido yayi ya ware su kan fatuha yana qare mata kallo gani yake kamar idannuwan shi ke mai gizo kwanan kullun qara canza mai take kawar da zancan yayi ya cigaba da abinda yake, saukowa jidda tayi daga cinyar shi riqe da doya a hannun ta fada jikin fatuha Anuty na'am bude bakin ki na baki yam toh fatuha tace tare da bude dan qaramin bakinta ji tayi jidda ta bata ragowar doyar hannunta sadiq da ke zaune saman kujera dining yana kallan su ta qasan ido har mamakin yadda jidda ta saba da fatuha haka yake, tabe baki yayi ya shanye ragowar tea din da yake sha ya miqe ya wuce su ya haura upstairs fatuha ko dining tazo ta cika tunbin ta sannan taja jidda suka koma parlour suna cikin kallo rabi'a ta fito tare da yi masu sallama, har bakin gate suka rakata bala mai gadi sai tsiya yake ma jidda ita kuma sai turo baki take fatuha ko dariya abin ya bata janyo jidda tayi suka dawo cikin gida suka cigaba da kallo.


Wani irin sanyi da kamshi ya doki hancin shi part din kwal kamar ba'a kwana ciki wani irin sanyayan ajiyar zuciya ya saki tare da sakin handle din kofar, bedroom ya shiga nan ma wani irin lalausan smile ya saki komai ya mai yadda yake so take ya ji wani irin bacci na fizgarsa saman bed ya fada tare da sauke ajiyar zuciya bacci da baiyi jiya ba shi ya kwasheshi.


Sun sha kallo har sun gaji ba su suka bar parlour ba sai 1:30pm shima kiran sallah ne ya tashe su, arwala suka dauro sannan suka gabatar da sallah suna idarwa suka dawo parlour, ola ne yayi knocking din kofa fatuha ta tashi ta bude mai washe da baki ya kalle ta, cikin hausarsa mara fita yace madam sannu ,yawa fatuha tace , dama wannan malam min ne da ke koya maku karatu ne ya zo yanzu, murmushi fatuha tayi ta ce malam ai ba da rana yake zuwa ba ta fadi tana leqa waje bari ina zuwa daki ta shiga ta janyo hijabin ta tare da daura zani saboda mini skrt ne jikin ta sannan ta fito lokacin har ola ya koma bakin aikin shi malam na zaune saman tabirin mai gadi suna dan taba hira cikin natsuwa fatuha ta qaraso tare da gaishe shi, murmushi yayi ya amsa, ah malama fatuha murmushi kawai tayi kinga yau na zo tun 2:00pm wallahi ina da wata safga anjima shine nace da naki zuwa qara na zo yanzu tunda kwana biyo ba muyi karatun ba murmushi fatuha ta yi ta ce aiko dai malam mun gode bari na kira jidda toh yace mata tare da tashi daga tebirin bala mai gadi ya koma inda suke gabatar da darasin, fatuha na shiga gida tasa mata hijabin ta suka fita.

Cikin jin dadi suka gabarta da darasin su inda malam yayi masu qari tare da yi masu yan tanbayoyi suka bashi amsa sai da ya tabatar sun gane misalin karfe hudu ya sallame su, ya wuce akan cewa gobe karfe hudu zai zo insha Allah littafan su suka kwashe suka shiga gida dama daure da arwala fatuha take sallah ta gabatar sannan ta cire zanin ta shiga wanka tana fitowa daure da towel ta tsane jikin ta tare da shafa jikin ta da lotion har ta dauko uniform din ta zata maida ta tabe baki, tunda na gama aiki ai sai na sa na gida dan ni na fara gajiya da su ta fadi tana turo baki wardrobe ta bude ta curo wata pink gwon mai dogwan hannu rigar simple ce mai kyau tayi shap sosai tayi mata kyau rigar ita kanta sai da ta yaba rigar parlour ta dawo ta zauna, jidda na zaune tana kallan carton itama ta zauna tana kallon.


Ring din wayar shi dake bedside drowe ne ya tasheshi dan guntun tsaki yaja tare da kai hannu ya dau wayar ,ba tare da ya duba suna ba,hello yace cikin alamar gajia ta daya bangaran a kayi dariya , sadiq tashi yayi zaune tare da saki guntun murmushi, wallahi sadiq baka da kirki Allah yasa ma ka gane mai magana yar dariya yayi tare da shafa sanjan shi ba Khaleed bane dariya Khaleed yayi yace ashe dai kana gane mutane dan guntun tsaki sadiq ya ja ya za'ai na kasa gane muryar childhood friend dina, ah ka kyauta ina majid ai ya fika zuminci, haka dai kace toh yau na leko Kano insha Allah zan shigo toh shikenan sai ka zo indan ka zo ka kira ni toh yace tare da yanke wayar agogwan dake manne a bangwan daki ya kalla ware sexy eye's ball's din shi yayi ohno na kwanta ina ta bacci har 4 ya gota tashi yayi tare da yaye blanket din jikin shi toilettes ya shige ya sheqa wanka yafito daure da karami'n tawel à kugunsa, sanye hannun shi riqe da qaramin towel yana tsane sumar kan shi yana cikin shafa lotion wayar shi ta fara ruri hannu ya sa ya dauka tare da karawa a kunne, hello big man ganin a filin gidan ku, smile sadiq yayi yace are u serious, yea angayama kowa irin kane Mara zuminci dariya sadiq yayi kai friend nine fa koma yane , toh shikenan ganin zuwa katse wayar yayi tare da zura jalabiya white ya fito daga part din shi ya wuce su fatuha a parlour suna ta karatun dan fatuha ta dake sai jidda ta koya mata karatun boko yanzu haka har ta iya ABCD.


Yana fita farfajiyar gida ya hango Khaleed jingine jikin motar shi mai tsada kallo daya zaka mai kasan shima dan hutu ne, kuma gaye ne sanye yake da shada tasha diki mai kyau Khaleed chocolate colour ne yana da saje da yakara bayanar da kyawunsa, yana da manyan ido murmushi ya saki ganin sadiq ya qara so fararan haqoran shi suka bayana cikin jin dadi sadiq ya qaraso tare da miqa mai hannu suka gaisa, Ashe dama zan kara ganinka a duniyar nan? murmushi Sadiq yayi bagashi ba ai kai ma baka zama shiyasa haka kuma dan last week ma na dawo daga London har muka hade da yaya jawad wajan shopping shi da matar shi har ya ke ce min sun kusa zuwa gida jira kawai yake Anuty shukara da haihu su zo, murmushi Sadiq yayi ya ce haka ya fada min suna tattaunawa har suka qaraso kofar parlour cikin parlour suka shigo har yanzu su fatuha na nan inda ya bar su ,Sadiq yace "Fatuha" dagowa tayi ita da jidda tare da gaishe da Khaleed murmushi Khaleed yayi tare da amsawa yana bin fatuha da kallo Sadiq ya katse mai tunanin da cewa "Fatuha ki kawo mana glass cup?" tace mai toh tare da shigewa kitchen ,jidda ga uncle Khaleed smile jidda tayi Khaleed murmushi yayi ya ce karka ce min angel ce ta girma haka ,ita ce mana zaro ido waje Khaleed yayi yace kai amma gaskiya mun yadda zuminci, come here angel kusa da shi jidda ta matso kallan ta yayi tare da daukar ta suka haura upstairs sai tanbayar ta ya ke tana zuba mai surutu suna shi ga part din Sadiq saman two star Khaleed ya zauna tare da daura jidda a cinyar shi ,sadiq fridge din bedroom ya bude ya curo lemu ka masu sanyi ya kawo ma Khaleed lokacin yayi dai dai da shigowar fatuha dauke da tray da cup's amsa tray din Sadiq yayi tare da yi mata nuni da ta dau jidda, Khaleed sai bin fatuha da kallo ya ke kiran jidda tayi suka fita a tare tana fita Khaleed ya sauke ajiyar zuciya, yana kallan Sadiq, Sadiq din ma kallan shi yake ,big man ina kuka samo beautifully girl, wake nan ya fadi a taqaice wadda ta dau angel yanzu murmushi Sadiq yayi yace "Fatuha she is my sister baka ga muna kama ba ya fadi zancan yana cigaba da zuba ma Khaleed juice" amma ai nasan kai ne dan auta baka da wata sister bashi glass cup yayi na lemo yana qara saki wani murmushin Wanda iya karshi lips din shi, she is my consin sister yanzu ka gane ko murmushi Khaleed yayi yace amma fa tana da kyau karka ce min basma ce ta zama mai kyau haka tanbayar Khaleed ta kusa fara kai Sadiq wuya amma sai ya maze yace ba ita ba ce wannan diyar sister mom ce eyya shi kan Sadiq yana mamaki karyar da ya zauna yana shunfuda ma Khaleed toh me inya ce me aiki ce dan guntun saki ya ja a zuciyar shi ,Sadiq mom fa , mom ba ta nan sun tafi uk da abba OK hira suke sha sosai suna kallo.




*Taku har kullun Salma mas'ud nadabo*
*CAPTAIN SADIQ*
👮🏼‍♂


*Writing by*
*Salma mas'ud nadabo*

*Edit by*
*Raheenat*

📘 *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*🐄
★we are the best★

http/mobile.Facebook.com/Real-Hausa-fulani-writers-forum RHFWF-173984973194167/?refid=52&red=opare_speed_dial_&yn=H-R

*Email*:[email protected]

*Facebook*:www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERFORUM.com


57_58


_*Godiya ta musanman gare ku mosayan ❤ wannan novel ina jin dadi 💃🏼yadda kuke comments🤓 a kan wannan littafi hakan ya nuna min ana mugun tare 🤝🏽 wannan shafin naku ne ,Dan Allah duk wadda nayima laifi ta yafe mini ni nafe ma kowa Alfarman wanga wata mai Albarka mai falak mai dumbin nasrori watan Ramdan ,yan Dan Allah mu yawaita Adu'a da neman tafiyar Allah mudinga tashi cikin dare domin yawaita nafiloli da neman bukatunmu na Alheri à wajen Allah Allah yakaimu Farawar azumi lafiya Ameen Dan Alfarman anabinmu Muhammad Sallah'llahu allaihi wa'sallam Allah yasa muyi idaunmu cikin kociyar hankali da farinciki idan bamu ganshi ba Allah yayi mana rahma Ameen ni salma mas'ud nasani nake ma duk wani masoyina happy Ramadan Kareem*_



*S* ai da fatuha taci kuka ta gaji sannan ta tashi ta shige kitchen, ta bude fridge ta ciro fruit ta wanke ta dawo parlour tana ci tana kallo har bacci barawo ya kwashe ta.

A dai-dai bakin gate ya tsaya tare da yin horn shitu mai gadi ya taso ya bude mai gate, washe da baki yashiga gaisheda sadi , sannan sadiq ya sako hancin motar shi cikin gida Jamal dake filin gida yana ball ya saki murmushi ya biyo motar yana murna dai dai ta parking din motar yayi a parking space tare da bude murfin motar tunkan ya budewa jidda motar, tayi sauri fitowa ta washe ma Jamal baki small dad Jamal yace tare da fadawa jikin sadiq murmushi Sadiq yayi tare da d'aga shi sama yana mashi wasa dauke da shi ya shigo parlour tare da yin sallama Anuty bilki na saman three star zaune Hanan na saman one star cikin sallama sadiq yayi washe da baki Anuty bilki ta amsa tare wurga mai harara, sosa keya yayi tare da zama hanan da ke ,zaune a kujera ta gaisheshi a taqaice ya amsa mata tare da k'allan Anuty bilki cikin wasa tace dashi bl"Bari kallona!, ta fadi tana qara aika mai harara "dariya yayi yace "Kai sister tunda na kawo ta ai sai ki huce ban hucewa abinda sai da na rinqa binka sannan ka kawo ta, to ayi min hakuri plsss, toh tace tana kwallawa baba larai kira ta kawowa sadiq kayan motsa baki dauke da tray ta fito cike da kayan motsa baki ta aje mai a gaba tare da mai sannu da zuwa sannan ta juya ta koma bakin aikin ta, hira suka rinqa zubawa shida yar uwar shi suna cikin yin hirar Aliyu min jin Anuty bilki ya dawo shima zama yayi aka dasa sabuwar hira da shi, basu suka tashi ba saida suka fara jin kiran sallah magrib, alwala suka dauro sadiq da Aliyu suka wuce masallaci Kasan cewa Anuty bilki hutu take shiyasa ta cigaba da kallan ta.

Sai da aka gabatar da sallah sannan suka d'awo gida lokacin Anuty bilki ta shirya masu abinci a dining area ,aiko direct can suka wuce dining area Anuty bilki ta shiga saving nasu lafiyayan jallof taji naman rago da kosulo cikin jin dadi suka cin abinci tare da taba hira bayan sun kamala cin abinci suka dawo parlour suna hira suna kallan news sai wajan karfe 10:00pm sadiq ya baro gidan Anuty bilki.


Kiran sallah magrib ne ya tashe ta d'aga barcci bedroom ta shiga tare da shigewa toilet ta d'auro alwala ta gabatar da sallah bayan ta idar tayi zaune saman daduma tayi tsuru tsuru wani irin tsoran gida take ji da wani fargaba, duk ji take gidan ya isheta tunanin rayuwar ta a kauye ita da fatsima ta shiga yi har da yan hawayan ta ji take k'amar ta rufe idanuwan ta ta ganta a kauyan wudil gaba ki d'aya kewar su inna ta dame ta, jan jiki tayi ta hau saman bed bawai dan tana jin bacci ba blanket taja tayi lamo tana matsar kwalla.

Bala mai gadi dake gyangyandi qara horn yasasa tashi firgigit wangale gate din yayi, yana washe baki qaraso da motar shi yayi dai dai saitin bala mai gadi tare da zuge glass din mota , murmushi yayi yace malm bala hala har ka fara bacci murmushi bala mai gadi yayi yace "Wallahi ko shi ke san dauke ni? saboda yar isakar da ake tana kadawa mai dadi sai kaji bacci na fizgar ka" murmushi Sadiq yayi tare da da ciro inda yake ajewa acikin motar yan' dubu dubu ko irgawa beyi ba ya damkawa bala mai gadi tare jan motar, bala mai gadi jerawa sadiq Albarka ya shiga yi da fatan alheri sannan ya soke kudin shi aljihu yana yin parking ya kashe motar tare da jingi

Please Login or Register in order to submit comment