Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ne sannan tayi ma jidda wankan, tana mata tana zuba mata surutu dauke da ita ta fito sannan ta zauna da ita saman bed sadiq na zaune saman sofa yana kallansu shafe jikin jidda tayi da mai sannan ta dau uniform din jidda zata sa mata nan fa kar ku ga zare ido dan ta rasa ta inda zata samata rigar saboda gown ce irin mai kamar biri da wando dinan tayi tsuru tsuru, sadiq jan tsaki yayi tare da fisge rigar ya Shiga sama jidda fatuha duk tana kallan yadda ya ke samata sai da ya gama shirya jidda sannan ya mata pack, daddy good morning , morning too angel how was ur night, cool daddy. good, fatuha ko ta saki baki tana kallan su.


Sai da suka gama shiryawa tsaf sannan sadiq ya dau briefcase din shi ,fatuha kuma ta dauki jidda suka sauko downstairs mom da abba na zaune a dining area har sun fara breakfast cikin ladabi sadiq ya gaishe su haka ma fatuha da jidda mom ce ta kalli fatuha washe da baki ta ce "Ya kwanan baqunta?" murmushi fatuha tayi tare da jama jidda kujera ta zauna cikin natsuwa ta shiga saving din jidda abinci, da ta gama sai ta zauna shima cikin dari dari sannan ta sa hannu cikin plate din.. wata irin tsawa sadiq ya daka mata wadda tasa fatuha fara matsar kwalla, cikin kakausar murya yafara cewa "Wai bana ce maki ki daina feeding din angel da hannu ki bane eeh" Mom ce ta kalle shi tare da wurgamai harara , baby wai me yasa ka ke haka ne eeh fada ta mai sosai sannan shima Abba ya dara da ce mai "Kai haka ake a rayuwa? kai kullun cikin zafin rai sadiq wai me yasa baza gyara halin ka bane eh baby?", shiru sadiq yayi tare da aikawa fatuha harara ita ko tayi kamar bata gani ba sai ma gwalo da ta aika mai cikin na tsuwa suka gama breakfast.


Briefcase din shi sadiq ya dau ka fatuha na dauke da jidda suka fito harabar gidan, haka fatuha ta rinqa zare ido tana qarewa yaran sadiq kallo *ola* ne ya qaraso cikin sauri tare da amsar briefcase din sadiq ya kai mai mota fatuha na biye ta shi suna zuwa gaban mota fatuha ta aje jidda cikin mota ,zata juya sadiq ya fisgota ta fado jikinsa,da sauri ya ture ta tare da taka mata qafa da booth din kafar shi ya murzashi sosai, jin za tayi ihu yasa ya matse mata baki da hannun shi da karfi yana kallan ta ido cikin ido ,idanun fatuha sun cika da kwalla tap saboda ita ka dai tasan azabar da take ji ,ture ta yayi tare da nunata da yatsa ya shige motarsa har zai tada yajiyo muryarta tana magana da yake ahankali take magna shiyasa baiji abinda take fadi,kwafa yayi ya tada motar suka bar harabar gidan. fatuha ko Allah ya isa ta Shiga jeramai tare da shigewa gidan a guje.



*Taku har kullun Salma mas'ud nadabo*
*CAPTAIN SADIQ*
๐Ÿ‘ฎ๐Ÿผโ€โ™‚

*Writing by*
*Salma mas'ud nadabo*

*Edit by*
*Raheenat*

๐Ÿ“˜ *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*๐Ÿ„
โ˜…we are the bestโ˜…

http//,mobile. Facebook. Com/Real-Hausa-fulani-writers-forum-RHFWF-173973194167/?refid=52&red=opera_speed_dial_yn_=H-R


*Email*:[email protected]



*Facebook*:www.Facebook. com/REAL HAUSAFULANIWRITERSFORUM.com



*๐Ÿ‘๐ŸผGodiya ta musanman ga masoya na โคina jin dadi addu'ar ku ta fatan alheri๐Ÿ˜ nima ina san ku ana mugun tare*๐Ÿค๐Ÿฝ


*Wannan safin nakune masoya na asha karatu lafiya*โค


33_34

Parlour ta qaraso tare da share yar qwallar da ya taru ร  idonta, Mom na zaune saman three star tana kallo juyowa tayi cikin murmushi tare da kallan fatuha, ita ma fatuha murmushi tayi tare da fara kwashe kayan abinci da ke dining area, ah fatuha da kin bari rabi'a ta zo ta kwashe, washe baki tayi tare da cewa barshi kawai hajiya, mom murmusawa tayi tare da cewa "Ni ko fatuha da kin daina ce min hajiya nan da yafi! Ki rinqa kira na da sunnan da sadiq ke kira na" murmushi fatuha tayi tare da cewa, toh, sannan ta kwashe kayan ta kai kitchen mom kuma ta cigaba da kallan ta tana ayana wasu abubuwa ร  ranta,tana fituwa direct part din sadiq ta wuce ta gyara part din sosai, tana gamawa ta shiga toilet shima toilet din sai daya sha wanki dan fatuha gyara tayi bana wasa ba, tana gamawa ta washe baki tare da zama saman sofa tana qarewa dakin kallo hotan sadiq ta hango manne jikin bango tangameme shi da kausar sunyi murmushi.


A hankali ta qaraso wajan hotan tare da washe baki tana kallan hotan, ohni ashe sangami na murmushi ah ji yadda ya washe hakura dan Allah ai da haka yake kullun daya fi kyan gani, murmushi tayi tare da daura hannu saman pic din ,um gaskaya kana da kyau Qur'an chan kuma sai ta bata fuska tare da cije lips dinta dariya tayi sannan tace, "Kwarankwatsi zaka zo ka same ni wallahi ba kasan *wacece fatuha ba yar gidan baffa jauro*" sannan ta bala wa pic din harara ta fita daga part din.


Tana sakowa downstairs ta shige bedroom dita wanka ta kumayi, tana fitowa ta shafe jikin ta da lotion tana shafa lotion din tana washe baki , Qur'an wanga mai sanyi garai ga kamshi tap wallahi birni tayi sai da ta gama shafe jikin da mai tas sannan ta sa wasu uniform din.



Cikin school yayi parking tare da fituwa ya budewa jidda murfin mota smile ya mata me sanyi, sannan ya ciro mata lunch box dita ya miqa mata, bata fuska jidda tayi tare da cewa "Daddy am going to miss u daddy" saman kanta ya shafa tare da cewa "Sorry angel soon za'a tashi aiko se inna dawo gida sai muje shan ice cream ko my angel" washe baki tayi tare da yi mashi pack sannan ta shige class yana kallanta har ta shige sannan ya sauke ajiyar zuciya ya shige mota yatafi.


Bayan ta gama shirin ta tafito parlour ba kowa sai kamshi da ke tashi na girki, kitchen din ta nufa tare da sallama baba jinmai ke girki sai rabi'a na gyara salat murmushi tayi tare da gaishe su washe da baki baba jinmai ta amsa tarรฉ da cewa "Yar albarka kin zo taya ni aiki ne?" daga kai tayi alamar Eh, can kuma fatuha ta bata fuska tare da cewa baba wai ina kike kwana jiya kika barni ni ka dai, washe baki baba jinmai tayi tare da cewa, ah aini fatuha banan nake kwana ba a gida na nake kwana se da safe na zo ,turo baki fatuha tayi tace gaskiya baba yau binki zanyi,ah ba za'ayi haka ba ki zauna nan nima ai gidan bacci ke kai ni baba jinmai ta shiga lalaba fatuha.


Taya su aiki tashiga yi sosai can baba jinmai ta miqawa fatuha kwano ta debo man da za'a soya kaji a stor, wani irin murmushi tayi tare da Shiga stor din nan ta zuba a kwano tare da qule wani a leda tasa a aljihun skrit din ta tafitu sannan tayi ma baba jinmai sallama ta koma parlour ta cigaba da kallo tayi tana washe baki, mom ce ke saukowa daga stairs sanye da mayafi da car key a hannu ta kallan gefan da fatuha take tayi tare da cewa "Oh na manta, nayi da ke jiya zan kai ki gyaran kai wallahi na manta gashi yanzu fita zanyi" murmushi fatuha tayi ta ce ba komai gobe maje , toh shikenan inna manta ki tuna min please toh ta ce mata tare da rakota har bakin kofa sannan ta koma parlour ta cigaba da kallo.


Tana kallo har bacci ya kwashe ta a parlour, cikin bacci taji ana sallama tashi tayi tare da ware idanuwan ta ta sauke su kan Anuty bilki, ware ido ta kuma yi tana qarewa Anuty bilki kallo dan tabas tayi mata kama da sadiq sai dai sadiq ya fita kyau sosai qaqaro murmushi tayi bakin ta na rawa ta gaida Anuty bilki zama tayi tare da amsawa tayi ma fatuha murmushi, um hajiyar ba ta nan ta fita, murmushi Anuty bilki tayi tace ai na sani munyi waya yanzu zata dawo ba dadewa zatayi ba, fatuha kitchen ta shige ta fada ma baba jinmai anyi baquwa lemo ta zuba mata a tray da kyan motsa baki tare da ce mata gata nan zuwa taga baquwar , Anuty bilki ko kayan jikin ta ta rage tare da haurawa upstairs dan ta watsa ruwan , fatuha na zuwa parlour taga ba baquwa sai afra da ke bacci saman kujera baba jinmai ta qwalawa kira ta fitu a rude ita ma Anuty bilki da shigar ta bedroom kenan ta sauko turus baba jinmai tayi a parlour lafiya fatuha me ya faru baba wallahi baquwar ce ban gani ba gashi ta bar yar ta a nan Anuty bilki ce ta qaraso, washe baki baba jinmai tayi tace, ah wai Bilkisu kike nufi ai yar gidan ce amma tayi aure ganin gida tazo yi murmushi fatuha tayi tace, "Aiyo aini ban sani ba shiyasa" itama Anuty bilki dariya tayi sannan ta haura sama tare da ba fatuha afra ta kula da ita kafin ta fito.


Misalin karfe 12:00pm jidda ta dawo school ita da Jamal, kasan cewar school daya suke da yan'yan Anuty bilki cikin murna fatuha ta tare su , kasancewar fatuha me san yara ce shiyasa ta ja jidda da Jamal bathroom ta masu wanka suka fita tas sannan ta sa masu kaya ta zo da su dining area suka ci abinci sannan ta dawo parlour da su suna dan taba hira sama sama, can sai ga hannan ita ma ta dawo daga school washe da baki ta qaraso ta fada jikin Anuty bilki wash mom I am tied sorry sweet je kiyi wanka ki canza kaya fatuha ko washe baki tayi tana qarewa su hanan kallo, tsakanin hanan da fatuha kunsan sa'anin ne shiyasa tunda ta shigo fatuha ke kallan ta hakan sai yasa ta tuna da fatsima kwalla taji ta zo mata gaskiya ta San tayi kewar su inna da fatsima daki ta shige tayi kwanciyar Hanan ce ta shigo ta shige toilet tayi wanka sannan ta fito daure da towel suna hada ido da fatuha tayi murmushi.. sannu ki ,yauwa fatuha tace mata, nan hanan ta fara janta da hira sama sama, hanan dama kawa take so gashi ta samu aiko nan hira ta barke tsakanin su in fatuha ta fadi wani abu hanan tayi dariya sosai har cikin ta ya kule.


Sai yama likis su hanan suka tafi, har bakin mota fatuha ta rako su ita da jidda kamar kar su tafi saboda fatuha taji dadi hirarsu da hanan.


Bayan sun tafi suka koma bedroom din jidda, taci gaba da zubama fatuha surutu can kamar kamar aj mintsi neta ta tashi ta koma parlour kadan kadan ta leqa waje.


Motar sadiq ce ta kunno kai cikin gidan, wani irin murmushi fatuha tayi tare da yin Sauri da haura sawa, upstairs part din sadiq ta shige direct toilet din shi ta shiga ta fido da man da ta kule a leda ta juye shi qasan toilet din sannan ta fito tana dariya tana waigen part din ji tayi ta fada jikin mutun, idanunta ta zaro cikin tsoro da fargaba ,tayi lamo tana jiran aradu, wata irin tsawa sadiq ya daka mata tare da ture ta ta tafi tagalgal zata fadi ya fisgota tare da qanqance idanu yana kallonta , fatuha kuwa har ta fara matsar kwalla, cikin kakausar murya yace "Ke wace irin mahaukaciya ce ? ya karasa zancan da murya mai sauti" Wanda yasa fatuha sakin kuka saboda a iya rayuwar ta ba Wanda ya taba mata irin wannan ihu, kuka take sosai tana girgiza mai kai janta ya cigaba dayi har sai da ya kai last stairs sannan ya ban kada ta ta fadi qasa tayi zaman yan bori nunata yayi da yatsa tare da cije lips din shi ya dau briefcase din shi ya shige part nashi fatuha ko kuka tayi san ranta da kyar ta tashi saboda qugun ta ya riqe bedroom ta Shiga shiga ร  toilettes dan watsa ruwa, bata jima sosai ta fito daure da tawel yashirya cikin Riga da skt na yan kanti sosai tayu kyau masha Allah ta fito parlour can kuma sai tayi murmushi ta haura sama.


Sadiq na Shiga daki saman bed ya fada tare da lumshe ido, yana maida numfashi a hankali wata irin tsanar fatuha na ratsashi ware sexy eye's dinshi yayi tare da tashi tsaye, ya je gaban fridge ya bude ya curo fresh milk ya sha sannan ya fara jin zuciyar shi ta daina kuna, ya tashi ya cire uniform dinshi yashiga toilettes .



*Taku har kullun Salma mas'ud nadabo*
*CAPTAIN SADIQ*
๐Ÿ‘ฎ๐Ÿผโ€โ™‚

*Writing by*
*Salma mas'ud nadabo*


*Edit by*
*Raheenat*


๐Ÿ“˜ *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*๐Ÿ„
โ˜…we are the bestโ˜…


http//,mobile. Facebook. Com/Real-Hausa-fulani-writers-forum-RHFWF-173973194167/?refid=52&red opare-speed_dial_yn_=H-R


*Email*:[email protected]


*Facebook*:www.Facebook. com/REALHAUSAFULANIWRITERFORUM.com


*hehe qawalliya roman jaba wannan page naki ne amal*


35_36

A hankali ya murda handle din kofar toilet ya zura kafar shi ji kake suuuu gwajaf yayi faduwar yan bori, fatuha da ke maqale bakin kofa ta kasa kunne jin faduwar sadiq ya sata bushewa da dariya har da rawar tanbola dan shauqi bude kofar tayi ta shigo bedroom din tana shigowa ta qara fashewa da dariya, saboda zaman da sadiq yayi a qasan toilet qarasowa tayi bakin toilet din, a hankali sadiq ya dago sexy eye's ball's din shi ya sauke su kan fatuha wani irin kallo ya wurga mata dariya ta kumayi tare da bala mai harara, ah me kyau ansha qasa dariya ta kumayi tare da gyara tsayuwa toh me kyau bari na kirama hajiya ta kirama mai dauri saboda nasan ka goce koka kare ta qara bushewa da dariya ,sadiq ko cije lips yayi yana jin wani irin radadi da tsanar fatuha na ratsa shi kallan banza ya wurga mata yana qoqarin tashi amma ya kasa wani irin radadi qugunshi ke mai, cije lips yayi ya zauna dan baya iya tashi dariya fatuha tayi tace, "Kwarankwatsi baka iya tashi Qur'an ka bugu ba kadan ba qila ma ka kare ko ka goce", dariya ta kumayi ta nuna idanuwan ta da yatsu biyu sannan ta nuna idan sadiq Wanda ke binta da kallan tsana, daure fuska tayi tace ka tuna turani da kayi dazu a matatakala na fadi? toh Allah ya isa ba kasan wacece fatuha ba ko? kaje kauyan wudil ka tanbayi *wacece fatuha diyar baffa jauro qawar fatsima*, sannan ta qara fashewa da dariya ta ce "Kuma daga yau zan fara nuna ma irin kallan haukar fatuha ,kuma wallahi kasani fatuha ba'a mata abu ta hakura ko ta dangana, a lokaci ba hakuri nayi ba shi yasa na rama, ta bala mai harara tana qoqarin fita, sadiq ko wani miyan bakin ciki ya hadiye yana jin wani irin bakin ciki ,ji yake kamar ya tashi ya shaqe fatuha har sai numfashin ta ya kusa daukewa ya sake ta lumshe idanuwan shi yayi.



Washe da baki fatuha ta fito daga part din sadiq sai da ta dai daita kanta sannan ta fara matsar kwallar gulma, bedroom din mom ta nufa tana yarfe hannu a hankali ta bude kofar mom ta hango kwance saman bed tana karanta azkar, cikin na tsuwa ta shigo tana matser kwalla mom ce ta dago su kayi 4eye's da fatuha murmushi ta saki tana qoqarin tashi ta ce, fatuha qaraso mana jikin kofa ta qara maqalewa tana matsar kwallar gulma da kyar ta iya furta mom dama baban jidda ne ya ce na kawo mai ruwa ina shiga dakin na ganshi ya fadi a kewaye kuma ya kasa tashi tana ida zancan ta fashe da kukan munafurci mom tashi tsaye tayi cikin rudani muje bedroom din nashi naga ko lafiyar baby, mom na gaba fatuha na baya tana aika gwalo suka shige part din direct bedroom din sadiq ta shige yanan zaune inda fatuha ta barshi yayi yayi ya tashi amma ya kasa mom ce ta qaraso tare da kiran sunan shi cikin damuwa ya juyo yana kallan fatuha na bayan mom tana matsar kwalla da sun hada ido da sadiq ta aika mai gwallo shikuma ya aika mata harara, sannu baby kaji bari mu taimaka ma ka tashi, no mom ba ku iyawa a miqomin phone din tana saman stool na kira *ola* da *Sunday* cikin sauri mom ta miqa mai wayar fatuha na gefe rabe zuciyar ta fes.


Bugu daya biyu *ola* ya daga kiran sadiq, sadiq ya sheda mashi yana neman shi, shi da *Sunday* cikin Sauri suka qaraso bedroom din, ganin su mom tsaitsaye yasa jikin su *ola* yin sanyi hango sadiq su kayi zaune a toilet yayi zaman yan'bori a hankali *ola* ya qaraso tare da gaida mom cikin hausar su wadda bata fita amsa mai tayi sadiq a hankali ya ce *ola* taimaka min na tashi kai da *sunday* OK boss Sunday d ola suka taimaka ma sadiq ya miqe suka daurashi saman bed mom sai sannu take mai itama fatuha sannu tamai wani irin mugun kallo ya mata, ya kauda kai mom ce tace baka ji fatuha na ma sannu bane lumshe ido yayi tare da ware su yace ban ji ba ya qara maida idanuwan shi ya rufe, wayar shi mom ta Curo ta kira doctor yakub ba ayi minti 39ba sai ga doctor yakub riqe da briefcase din shi ya shigo, fatuha ta mai isowa har bedroom din sadiq gaida mom yayi sannan ya shiga duba sadiq tare da tataba inda ya bige sannan yayi yan rubuce rubuce, gyaran murya yayi ya ce Alhamdulillah buguwa ce amma be goce ba kuma be kare ba abin ya zo da sauki mom murmushi tayi tare da hamdala, sannan doctor ya bashi magani da ze shafa da kuma na ciwan jiki sannan yayi ma su mom sallama ya tafi, mom da fatuha kuma suka fita cikin cool voice nashi sadiq yace da ola ya taimaka ya kai shi bathroom ya watsa ruwa amma ya fara goge man da ke zube a toilet sai da ola ya wanke toilet din tas sannan ya taimakawa sadiq ya shiga toilet, ola na bakin kofa yana jiran sadiq yana gama wanka ya kira ola ya taimakamai ya fito ko da ya fito ola ya fito mai da jalabiya milk bayan ya gama shafe jikin shi da mai sannan ola ya taimakamai ya shafa mai magani sannan yasa jalabiya ya koma saman bed ya lumshe ido ,ola ne ya bare maganin da ruwa ya bashi ya sha yana gama sha ya lumshe ido bacci mai nauyi ya dauke shi, ola ya koma saman sofa ya zauna Sunday kuma ya kwashe kayan da suka baci da mai ya fita.



Wash Qur'an yau nayi aiki inama a ce fatsima na kusa ta qara bushewa da dariya, ta kalli bed jidda na kwance tana sharar bacci dariya tayi tace "Allah sarki angal wato(angel) yau na naqasa baban ki se hakuri angal na san in zafi yayi zafi har sunnan ki sai ya fada ta kara fashewa da dariya tare da rausayar da kai ,Amma fa gaskiya ban duba mai ba ta ida zancan tana cire kayanta ta shige toilet tayi wanka daure da towel ta fito lokacin jidda tatashi, murmushi tayi ma jidda tare da daukarta dan lokaci 4:00pm saura malamin jidda ya kusa zuwa wanka ta mata a tare suka fito suka shirya sallah su kayi saboda anata kiraye kirayan sallah bayan sun gama sallah fatuha ta rako jidda har waje lokaci har malam ya zo ji tayi itama tana sha'awar karatun, cikin gida ta juya tare da Shiga bedroom din mom, mom na zaune saman daduma karasowa tayi tare da murmushi ta tanbayi mom itama tana so ta fara zuwa malam na qara mata karatu mom ta ce babu komai washe da baki ta fita ,taje wajan malam itama ba laifi fatuha ta Dan san sururi da yawa sai karatun nata ba tajiweed shine ka dai ya dan bata karatun ba laifi sunyi karatu sosai inda fatuha ta natsu tana ta karatu, dan wannan malamin ba karamar malami bane.


Bayan sun gama karatu misalin karfe 6:00pm suka shigo gida cikin farinciki, mom na zaune saman three star tana kallo abba na gafenta gaishe su tayi cikin na tsuwa sannan ta shige daki jidda kuma ta fada jikin abba tana zuba mai surutu kiran sallar magrib ne ya sa abba tashi ya wuce masallaci ,jidda kuma ta shige bedroom lokacin fatuha ta fito daga toilet daure da tawel tayi arwalarta ร  toilettes din, murmushi fatuha tayi tace, "Jidda yi maza kiyi alwala kiyi sallah kiyi ma baban ki addu'a, be lafiya kinji" waro ido jidda tayi tace Anuty me ya samu daddy tareda ruga wajen kofa zata fita, janyo ta fatuha tayi tace, yi hakuri mu fara yin sallah sai na kai ki kinji jidda toh tace mata tana matsar kwalla fatuha kuma na lalashin ta.


Bayan sun gama sallah fatuha ta shirya jidda cikin night dress din ta blue n white wando da Riga ba qaramin kyau su kayi mata ba ,ta ja hannu ta suka wuce part din sadiq.

Suna Shiga suka samu ola zaune saman sofa, sadiq ma zaune saman bed ,yana shan coffee da gudu jidda ta fadi jikin shi tana kuka, daddy lalashin ta ya shigayi angel menene yake damun ki ,bata fuska tayi tace "Daddy ashe baka da lafiya shine baka fada min ba? ta ida zancan tana matsar kwalla" sorry angel lafiyar daddy qlau, waya fada maki daddy be lafiya? fatuha ta nuna da ke manne jiki kofa kamar ka ce tak ta arce wani irin kallan tsana ya gefa mata tare da qaqaro murmushi yayi wa jidda yana kallan fatuha , angel na rasa yadda akayi grandma ta samomaki new Anuty mahaukaciya ya ida zancan yana kallan fatuha ido cikin ido, kauda kai tayi tare da turo baki gaba, daddy new Anuty ba mahaukaciya bace ba injiwa ya ce maki ba mahaukaciya ba ce fatuha ko wani irin tsoki ta ja tare da jan kofar bedroom da karfi ta fita lumshe ido sadiq yayi yana tunanin irin hukuncin da zaiyi ma fatuha in ya tashi.


*Taku har kullun mai qaunar ku Salma mas'ud nadabo*
*CAPTAIN SADIQ*
๐Ÿ‘ฎ๐Ÿผโ€โ™‚

*writing by*
*Salma mas'ud nadabo*

*Edit by*
*Raheenat*

๐Ÿ“˜ *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*๐Ÿ„
โ˜…we are the bestโ˜…

http//,mobile. Facebook. Com/Real-Hausa-fulani-writers-forum-RHFWF-173973194167refid-52&red opare-speed_dial_yn_=H-R


*Email*:realhausafulaniwritersforum@gmail. com


*Facebook*:www.Facebook. com/REALHAUSAFULANIWRITERFORUM.com


37_38


Fatuha bedroom ta shigo tare da yin sallah isha'i saboda tana da arwalata, bayan ta gama sallah ta rage kayan jikin ta yar rigar bacci tasa wadda yanzu ta zamar mata jiki, in batasa ba ko bacci bata iyawa kanta ta qarewa kallo ta cikin mirror ita kanta mamaki kanta take saboda ta wani qara haske da kyau sannan komai na jikin ta ya ciciko rufe idanuwan tayi tare da ware su, ta sauke su kan qirjinta Wanda yanzu ya fara cikowa sosai, murmushi tayi tare da jin kunya ta bar gaban dress mirror din ta fada gado tare da yin addu'a lumshe idanuwan tayi sadiq ne ya fadu mata a rai tayi sauri ware idanuwan ta tare da sakin dariya saboda duk lokaci da

Please Login or Register in order to submit comment