Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hawayan ta, hanan dak'e baki'n kofar tace "Fatuha ki fito me make up ta zo har an gama ma basma ke ka dai ake jira?" to tace tare da yin sauri ta watsa ruwa ta fito,


Ko da ta fito shaharariyar me make up fandi ta zo fatuha kawai take zaman jira. tana daure da towel ta fito ta sauna tana shafe jikin ta da mai. Anuty bilki ce ta shigo da kayan da zasu sa washe da baki ta aje kayan, a'a fatuha dama ba'a gama make up din ba d'aga kai fatuha tayi , ya kamata kuyi sauri ku shirya kar ku bata lokaci saboda da kun dawo zaku dinner to tace sannan Anuty bilki tasa kai fa fice. a hankali fandi ta fara tsantsara mata make up kafi'n ka ce me fatuha ta fito wasu maroon materials tasa gown mai Stone's masha Allah tasha kyau har ta gaji, ga head tasha ita kanta me make up ta yaba da irin kyan da fatuha tayi . su fatsima ne suka shigo sanye da ashoben su ash atamfa mai ratsin maroon suma sun sha head kun san a tare suka fito da basma kusan kaya colours daya suka sa har yan mata amaryar anko daya su kayi. motoci ne masu numfashi da tsada suka faka amaran suka shige ba a zame ko ina ba sai meenah event hadadan hall na party iyakar haduwa hall din ya hadu. kuma ya qayatar kasancewar kamun na mata zala ne shiyasa ba ango ko daya sai yan'mata da iyaye yan asharale ne suka fara buga ganga tuni hall ya dau sauti amaran zama su kayi ma zaunin su aka fara gudanar da shagulgula. can na hango su fatsina da nana da Zara anshige fili anata kwaso shoki haka suma qawayan basma biki yayi biki sai dai muce alhamdulillah .


Fatuha ko duk wannan bidirin da ak'e zuciyar ta naga muradi'n ranta, ji take kamar ta rushe da kuka kallan kowa take da ke farin ciki da walwala angel ta hango itama ba laifi ta saki jikin ta tana warwasawa,

Anci ansha inda aka raba turaru kan wuta da atamfofi masu tsada sosai aka raba kaya kamar ba'a so, sai kunsan yama liqis taro ya watse suka dawo gida,


Ko da suka dawo wanka amaran suka qara tare da dauro alwala suka gabarta da sallah magrib da isha, sannan amaran aka fara shirya su cikin wani wanka ni kai na har mamaki nake irin shirin da akayi ma bikin. lace suka sa blue mai ratsin dark blue mai shegen tsada ga make up da aka qara zuba masu sai kamshi suke yan matan amaraya ko pink lace suka sa mai ratsin white kowa ce tasha make up fatuha ko saboda tsabar kyau kasa gane ta kake ,dan ba qaramin kyau tayi ba kuma ga anuri da y'a sauko mata na amare. basma ma ba'a barta a baya ba tayi kyau bâ l'ai fi,


Shiryawa angwayan suke cikin getzner shad'a blue tasha aiki da dark blue zare ,duk wannan shirin da sadiq keyi jin shi yake susuku dan kwata kwata baya tare da walwalar shi , links yasa ma hannun rigar shi sannan ya daura agogan shi hublot tare da zura takalmin shi black mesarath tuni ya fito yana sheqi da wani irin kyau sajan shi yayi lufluf ya kwantan can gashin shi ya leqo ta cikin wula .feshe jiki'n shi yayi da turare masu kamshi da sanyi dadi kusan shigar su iri daya da majeed shima ba'a barshi baya ba Dan yasha kyau har ya gaji, sai murmushi yake saki fararan haqoranshi na bayana , abokanan angwayan ma ba'a bar su abaya ba Dan suma sunsha kyau Khaleed sai rawar kai yake zuba wa haka shima Dr yakub ba'a bar shi a baya gayu su kayi na sosai ,


Cikin natsuwa suka fito suka shige moto cin su mais alfarma da tsada, dan a da'ko amaran ko da suka iso amaran sun shirya tsaf motoci aka fara shiga kowace amarya ta shige motar angwanta,


Murmushi majeed ya saki yana bin fatuha da wani irin kallo mai cike da so da kauna, a hankali ya kai hannu ya taba hannu ta tare da kallan lalan dake hannu ta yace, "My love lalan nan yayi kyau?" smile tayi wanda iya karshi laban ta tare da qara manewa karshan kofar tana tuna abin santa.


Kallo sadiq yabi basma da shi ba laifi ta mai kyau. yau ce rana ta farko daya fara ganin kyan ta ayanawa yayi a ranshi, tunda ya ga basma haka to ya fatuha zata kasan ce? wani irin kishi ne ya lulube shi tare da qunar zuciya juyowar da yayi ne su kayi ido hudu da basma smile ya sakar mata tare da kauda kai,


A dai-dai affcent center motocin suka faka lokacin har wasu sun halara tun daga bakin hall din kana jiyo irin sautin dake tashi ,wajen y'a hadi bâ karya, ga wasu kujeru sa ak zagaye haldi'n farere Tass, jerawa yan'matan amarya su kayi shigar farrar matériel sulayi sa baki'gwagwaro sa a la d'aura mais a k'ai, Angwayen KO bakin Sweet suka sa y'a sa farar taklmi m'asha Allah shigar ta su yayi kya, amaran suka shiga tsakiya sadiq sai bin fatuha yake da kallo bugun zuciyar shi na daduwa, ita kanta fatuha ta qasan ido take kallan sadiq tare da jin kishin shi,


A natse suka shigo hall din, nan tale wajen y'a gwarare da shewa da ihu, tuni aka canza salan kida da sauti majeed hannu sa na maqale dana fatuha yadda ya shige mata kamar zai maida ta ciki .sadiq ya cika tap dan har ya fara ganin jiri riqe hannu basma yayi dan ba yadda zaiyi dan baya so ya bata ma qanshi rai .ko bai so basma so na aure ba yana sonta a matsayin ta na kanwar shi , ko da suka shigi gurin zama suka yi aka fara gudanar da shakali, can na hango su Anuty Raheenat anata kai kawo anzu shagali😜 ashe abin ba ita ka dai bace har da yan Real Hausa fulani writers. can na hango Fulani da Anuty Rahama nalele suna rab a ma mutane kayan motsa a baki, nima dai ba'a barni a baya ba Dan na Shiga a dama dani shoki kawai ake kwasowa.


A hankali majeed ya matso daf da kunan fatuha yace, "My love yanzu fa gobe kin zama tawa ko? yana magana yana wasa da yan yatsunta" sadiq dak'e gefe yana kallan su baki'n ciki na cin shi, dafe kirjin shi yayi domin yafara yi ma sa nauyi , a hankali ya miqe ya bar guri tunda ya fito d'aga hall din jiri ke di barshi, KO gaban sa baya gani. Sa kyar y'a isa inda yayi parking fin motarsa ya ya daura hannu shi kenan ya ji an riqe hannun. waigowa yayi su kayi 4 eye's da Dr yakub girgiza kai Dr yakub yayi yace sa...!! be ida rufe baki'n shinba sadiq ya fadi jikin shi sumame rudewa Dr yakub yayi yasa sadiq a mota ya bar harabar gurin da gudu.


MC yaba amarya da ango damar su yanka cake ,saukowa sukayi a hankali daga sama. majeed ya yanka yaba fatuha a baki hall din ya dau ihu sadiq aka kira da basma amma ba ango ba alama haka MC ya rinqa kira ango ganin abin kunyar dak'e shirin faruwa yasa Khaleed hawa a matsayin ango yaba basma cake a matsayin sadiq tuni hall ya dau tafi, basma iyakar cika ta cika bata taba jin bacin rai ba irin na yau, yaune ta tabatar da sadiq be Santa kuma ba zai taba Santa ba tunda har ya iya wulaqantata gaban bainar jama'a. idanuwan ta ne tap da qwalla, tana tausayawa kantada Irina rayuwar sa zatayi a gidan SadiQ. haka akayi turo kusan duk abinda ango zaima amarya Khaleed ne yayi ma basma.

Ko da fatuha ta juya bata ga sadiq ba tuni idanuwan ta suka kawo ruwa. dama shi take gani tana jin sanyi a ranta .

Ko da Dr yakub yaja mota basu zame ko ina ba sai asibitin shi ,suna shiga aka turo gadan daukar marasa lafiya sadiq da yanzu idanuwan shi sun fara budewa haka yake ganin asibitin na juyamai oxygen ne manne a hanci shi numfashin shi sai sama sama yake Dr yakub ko har ya fara matsar kwalla. emergency aka wuce da shi doctor sun Dade a kanshi Dr yakub ma kasa shiga yayi sai zarya da yake a baki'n kofar kusan 1 hour suka dauka sannan aka fito da sadiq sanye da oxygen a hancin shi daki aka bashi tare da samai life sport machine sai qarin jini da ake mai a hankali Dr yakub ya qaraso gaban shi tare da yin kneel down gaban gadan sadiq, hawaye ne kemai zarya a hankali ya kai hannu ya shafa sumar kan sadiq yace "Friend why me yasa kake bama kanka punishment haka? why sadiq ya ida zancan hawaye masu zafi na gangaro mai wayar shi ce dake ringing ciki aljihu ya tsuro tare da kallan suna dake maqale a screen din majeed kashe wayar yayi gabaki daya tare da janyo wayar sadiq ya kashe sannan ya dau kayan sadiq da aka cire mai yaba daya daga cikin ma'aikatan asubitin su wanke.

Bayan ankamala dinner kowa ya dau hanyar zuwa masaukin shi majeed sai kiran Layin sadiq yake baya Shiga dana Dr yakub. hakura yayi da Kiran tare da maida wayar aljihu.


Bangaran basma ko kuka take sosai tare da taqaicin amincewa da auran sadiq ,Khaleed sai bata hakuri yake tare da ganin rashin kyautawar sadiq ya rasa dalilin da zai mata irin wannan cin fuskar bayan tana qanwar shi kuma matar da zai aura, shi a ganin duk wanda yasa mu basma a matsayin mata ya mure ya rasa me yasa sadiq ke nuna rashin ko in kulla a kanta da wannan tunanin suka qaraso gida ko Godiya bata mai ba ta shige gida da sauri tare da tsananta kukanta.


Motar su fatuha na fakawa majeed ya fara jero mata kalaman soyayya tare da jan ta a jiki, ganin zai wuce Gona da iri yasa fatuha saki'n kuka lalashin ta majeed ya Shiga yi tare da yimata pack ko saurara shi ba tayi ba ta bale murfin motar ta fita da sauri.


Bangaran sadiq ko bashi ya tashi ba sai wajan 2:00am na dare a hankali yake ware sexy eye's ball's din shi da wani irin ishin ruwa ya tashi. Dr yakub da ko rintsawa baiyi ba ya miqe da sauri ya qaraso wajan shi cikin cool voice sadiq yace "Ruwa" da sauri Dr yakub ya bude fridge ya dauko rubar ruwa ya bashi ko da ya sha ruwan miqewa yayi yana qoqarin cire jini da ake qaramai riqe, hannu Dr yakub yayi yace, "Captain me kake shirin aika tawa? ya fada bakin shi na rawa" kallan shi sadiq yayi yace so nake na tafi gida bana so majeed ya gane bani da lafiya ya ida zancan yana cire Karin jinin wasu hawaye ne masu zafi suka zubu ma Dr yakub yace, "Sadiq wai me yasa kake so ka raya rayuwar wani ka bata taka? why sadiq Dr yakub ya fada yana jijiga sadiq" kuka sadiq ya Saki tare da cewa "Bazan taba bari majeed ya mutu saboda bakin ciki na ba nafi san farin cikin majeed a kan na kowa a duniya bani da dan uwa sama da majeed saboda haka ban taba bari saboda ni ya rasa rayuwar shi sadiq ya ida zancan yana kuka mai tsuma zuciyar mai saurare" a hankali ya ida cire kayan asibiti tare da zura kayan shi wayar shi ya dauka tare da kunna ta Dr yakub mutuwar tsaye yayi yana bin sadiq da kallo tabas yanzu yasan me sadiq yake nufi so yake ya rasa rayuwar shi ya zamamar dole ya kawo karshan abunan ko saurarashi sadiq beyi ba saima car key daya dauka tare da fita yana ingisawa.....



*_Muje zuwa fan's_*🤪

*Kuyi hakuyi Sa wannan bâ yawa*


*_taku har kullun salma mas'ud nadabo_*
[7/5, 7:04 AM] ‪+234 814 314 2333‬: *CAPTAIN SADIQ*
👮🏼‍♂

*Writing by*
*Salma mas'ud nadabo*

*Edit by*
*Raheenat*

📘 *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*🐄
★We are the best★


http/mobile.Facebook.com/Real-Hausa-fulani-writers-forum RHFWF-173984973194167/?refid=52red=opera_speed_dial_&yn=H-R


*Email* [email protected]

*Facebook* www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERSFORUM.COM


91_92


A hankali yayi parking motar shi tare da yi mata key. harabar gidan tsif ba motsin kowa sai motoci birjik kamar wanjan saida mota. a hankali ya cigaba da takawa duk da yana jin jikin shi kuka kuka ya fara ji sama sama hakan ne ya sasa tsayawa tare da kallan agogo hannu shi mamaki ne ya lulube sadiq a hankali ya fara bin inda kukan ke fita fatuha ce zaune sama resting chair tana rai ra kuka. qarasowa yayi gaban ta firgigit ta daga a dan tsorace ganin sadiq ne yasa ta fada jikin shi tare da sakin wani kukan, daurewa yayi tare da zamewa ya janyo ta suka zauna a hankali yake shafa mata bayanta ba wanda yace ma dan uwan shi komai ,sun dau kusan 5 minutes a haka fatuha ce ta dako tana kallan sadiq ciki'n sanyin murya tace 'Uncle" ya naji jikin ka zafi? dan smile sadiq yayi yace "Nima haka naji jikin nawa" kallan shi take cike da tanbayoyi amma sai ta kasa tare da komawa tayi lamo a fafadan qirjin shi kunsan a haka suka zauna har bacci ya dauke fatuha idanuwan sadiq biyu yana kallan fatuha har sai da ya fara jin kiran sallah asuba sannan ya tashe ta. sannan yace "Dear tashi asuba tayi?" qarayin lamo tayi a jikin shi shafa gashin kanta yayi yace "Fatuha" a hankali ta ware eye's ball's din ta, tace "Na'am" tashi mu shiga gida jiki ba qwari ta tashi har tayi gaba ta tsaya tare da cewa "Yau ne zan rasa farin ciki na! yaune mafarki na zai rushe" wasu hawaye ne masu zafi suka sulalo mata tace, "Yanzu duk wani rayuwa da mukayi zata zama tarihi mai kyau? ina ma fatan alheri Allah ya baku zaman lafiya da basma tana ida zancan ta fashe da kuka mai ban tausayi" a hankali sadiq ya janyo ta jikin shi ya rungume shima hawaye na mai anbaliya cikin sanyi murya sadiq yace "Fatuha ki kasance mai biyaya a daki'n mijin ki? majeed na sonki please karki bari majeed yayi kuka dake dai-dai da rana daya? duk wanda yayi hakuri a rayuwa zai ga ribar haka ya ida zancan yana share hawayan shi tare da sakar ma fatuha lalausan murmushi" itama shi ta mai tare da shigewa cikin gida.


Duk inda ka wuce had'a had'a ake na shagali abinci ke ta yawo da kayan motsa baki, kaji ko har ture su ake da naman rago yan'matan amarya na zaune a dak'i sai shirya fatuha ake saboda wudil za'a wuce da ita sai an daura aure aje dako ta. tunda ake mata make up take kallan agogo tana irga mintinan da suka rage ta zama malaqi majeed. hawaye ne tap da idanuwan ta bayan angama make up din ta zura kayan ta atamfa mai ratsin green pink brown masha Allah kayan sun mata kyau tasha danqareriyar sarqa ta gold da yan hannu sai sheqi take. Anuty bilki ce ta leqo tace, "Fatuha ku fito ga moto cin da zasu kai mu wudil?" gaban tane ya yanke ya Fadi dan har wani jiri take gani a haka su fatsima suka sata tsakiya aka lulube ta anata zuba guda, mota suka shige driver ya jasu suka har ba kan titi.


Wanka angwayan kawai suke suna shiryawa Khaleed ne ya kalli sadiq tare da aika mai harara tare da cewa "Wai ina kaje jiya?" bala mai harara sadiq yayi yace "Ina ruwan ka da inda naje? kai dai wallahi ka fiye sa ido? irin kune ana ruwa kuna irgawa" dariya majeed yayi yace "Kai dai tashi kayi wanka kaji baby ga kayan ka can tun dazu na aje ma ina so yau ka kasance cikin farin ciki kamar yadda kowane ango keyi majeed ya ida zancan yana zura kayan shi" a hankali sadiq ya miqe ya shiga toilet majeed .ya bishi da kallo tare da ida shiryawa tunda sadiq ya shiga toilet yake kuka kamar qaramin yaro sai da yayi san ransa sannan yayi wanka ya fito. ko da ya fito Dr yakub ne ka dai daki'n kallan shi sadiq yayi tare da kauda kai ya cigaba goge jikin shi da qaramin towel, sai da ya gama shafe jikin shi da lotion mai kamshi da sanyi dadi sannan Dr yakub ya balo magani ya miqawa sadiq dan bata fuska sadiq yayi yace "Wannan fa?" daure fuska Dr yakub yayi yace "Magani mana" bai ida rufe baki'n shi ba akq turo kofa aka shigo .murmushi sadiq ya saki tare da qarasawa ya rungume jawad zame jiki yayi tare da bata fuska yace, "Sai yauma zaka zo?" smile jawad yayi yace "Sorry baby tun jiya na zo kuma na zo nemanka aka ce ba kanan" dan lagwabe kai yayi tare da cewa "Toh shikenan, ina Anuty shukura?" tana wajan mom ok hadadiyar fara shada ya janyo white getzner tasha aiki ta gaji malin malin su jawad ne suka taimaka mai ya shirya tuni ya fito yayi kyau bayan sun gama shiryawa suka fita,

Zaunawa sadiq yayi tare da kallan agogo dak'e manne a bago'n daki'n. kusan karfe 1:30pm saura minti talatin a daura auran su. hak'a ya rinqa dane zuciyar shi yana bata hakuri.


Suna Isa wudil gida ya dau gud'a baba jinmai ta fito da sauri tana cewa "Ladingo amaryar fa ta iso ?" inna washe da bak'i ta bude masauki da su fatuha zasu sauka kusan tare suka shigo. Anuty bilki na riqe da ita masaukin suka sauka nan aka fara jera masu kayan motsa baki, yan'matan amaryar ko alwala suka fara daurawa suna sallah kasancewa azahar tayi haka itama fatuha ta gabatar da sallah sannan suka zauna aka fara gudanar da biki. gwago ce ta aiko a kira fatsima tashi tayi ta fita har Nana zata bita sai kuma ta dawo ta zauna ko da fatsima ta Isa gidan su shima cike yake da baqi ,babban abinda ya daura mata kai har da dangin baban ta, to ko suma biki'n fatuha suka zo? watsar da zancan tayi tare da shigewa daki inda gwago take washe da baki gwago ta tarbi fatsima ta fara mata magana duk yadda naso naji me ake cewa na kasa ji. hakan yasa ni da Anuty Raheenat muka bar gun jiki a sabule lol.


Duk inda ka waiga a cikin masallaci Sheikh Isyaka Rabi'u mosque ya cika da manyan mutune. saboda daurin auren, sadiq na hango ciki'n din bin jama'a, a Nata mai Allah ya sanya alheri duk wannan abu Dr yakub na lura da yanayin shi majeed ma sai murmushi yake saki daka ganshi kasan yana cikin farin ciki. haka shima Khaleed dan yasha kyau har ya gaji kamar ango gyara lasfika da kayine yasa gaban sadiq ya yanke ya Fadi .take wani irin zufa ta fara karyo mai da bugun zuciya, tabas yasan ana daurawa ya zama gawa wani irin jiri ya fara gani da kyar ya fara barin cikin taro ga wani irin tari da yake don tado masa. A hankali yake takawa dan yanzu ya fara yin nisa da masallacin,


Cikin masallaci ko *_MALAM JAURO YA BADA DIYAR SHI KAN SADAKI NAIRA DUBU DARI GA DAN ALHAJI IBRAHIM WATO SADIQ IBRAHIM, MALAM ALIYU YA MIQA DIYAR shi KAN NAIRA DUBU DARI WATO FATIMA ALIYU GA DAN ALHAJI KHABIR WATO ABDULMAJEED KHABIR, TARE DIYAR shi BASMA YA MIQA TA GA DAN ALHAJI SANI WATO KHALEED KAN SADAKI NAIRA DUBU DARI -* kowa na masallaci mamaki ne ya lulube shi. sadiq wanda fitowar shikenan majeed ya biyo shi tare da cewa "Baby?" waigowa yayi tare da buda baki zai ce majeed jiri ya debe shi ya fadi qasa sumame" da sauri majeed ya qaraso tare da sakin kuka yana cewa "Duk laifi nane hawaye namai zarya" Dr yakub da kusan tare suka iso wurin yace "Ba kuka za kayi ba? muyi sauri mu kai shi asibiti" jikin majeed na rawa ya bud'e murfin mota yana kuka ganin ba zai iya tuqinba yasa doctor yakub ya amsa. car key din suka bar harabar masallaci da gudu kuka majeed yake yana cewa "Ban taba tunanin abin ya kai haka ba? am so sorry sadiq ka yafemin sai sanbatu yake a haka suka iso asibitin" sai da aka wuce dashi emergency sannan majeed ya zame jikin bango tare da sakin kuka. wayar shi ya curo cikin aljihu ya danna number umma bugu daya zuwa biyu ta dauka kuka majeed ya saki yana cewa "Umma saboda ni ina ji ina gani baby zai rasa ransa? Ya fadi hakan tare da sakin kuka" ita kanta umma ta tausayawa sadiq.

Kafin ka ce me, asibitin ya cika da yan'uwa. majeed na ganin abba ya fada jikin shi yana kuka kamar qaramin yaro yace "Shikenan abba baki'n ciki na zai kashe baby,?" a hankali abba ke shafa bayan shi tare da zaunar da shi d'aya d'aga ciki'n kujerin dak'e gurin. ajiyar zuciya kawai majeed ke saki ciki'n sanyi murya abba yace "Ba laifin ka bane majeed kaji? har da laifin sadiq da yayi nauyin baki ya kasa fad'a? ko yanzu da ku kayi saurin aka sauya daurin auran? indai fatuha tace bata san sa dole ya sake ta" kuka majeed ya saki tare da cewa a?"Abba wallahi da kunne na naji irin son da suke ma juna su? abba dan Allah a taimaki rayuwar baby ? ya ida zancan yana qara saki'n kuka" haka abba ya rinqa lalashin shi har yayi shuru, ammi sai da ta matse kwalla saboda tausayi , sai yanzu suka san abinda ke damun sadiq.


Abba biza yasa aka mai dan a fitar da shi waje saboda a wannan qaran ciwon yayi tsanani. dan yafi buqatar amai aiki gagawa tare da samun qwararin likito ci.


Su baffa na Isa wudil ya sanar da su an daura auran, fatuha wani irin kuka fatuha ta saki dan yanzu ta tabatar da ta zama malaqin majeed kuka take kamar ranta zai fita. lalashin ta su Anuty bilki suka shigayi da kyar aka samu fatuha ta shirya. ko da ta shirya daki'n baffa aka kaita ya mata nasiha sosai duk wannan nasihar da baffa ke ma fatuha kuka take har da shesheqa abun gwanin ban tausayi. a haka aka tataro ta aka sata mota taci kuka sosai sai anjiyar zuciya da take ta saki ,dan ko fatsima bata nema ba.

Bangaran fatsima ko su gwago sun gyara ta sosai duk da bata jin Son majeed amma a yadda ya mata bayani da yadda

Please Login or Register in order to submit comment