Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zan iya gode maki my wife? kin sani farin ciki mara musaltuwa kin kore min duk wata damuwa my love? naji dadi da kika kilace min kan ki har wannan lokaci? nayi maki alqawarin zan baki farin cikin har qarshan rayuwa fatuha" wani irin dadine ya lulube fatuha tare da jin Son mijinta na qara narke mata a zuciya. lamo tayi a jikin shi tana sauke numfashi a hankali y d'ago da face nata yayi mata pack am sorry my wife, nasan na wahalar dak'e amma ai be ida zancan ba fatuha ta hada bakin su guri guda tana mai French kiss. take ta qara rikitashi da salon ta ganin zai zarce tasa mai kuka, dariya yayi tare da ja mata hanci yace "Matsoraciya kawai" naji din ba komai kuma gida zaka mai dani wallahi" lalai kam kwarankwatsi ba inda zaki ya fada yana kallan fatuha, dariya suka saki a tare yace "My love akwai drama?" ida zancan yana laka ce mata hanci qara matse ta yayi suka shige blanket suka koma bacci.


Basu tashi ba sai kusan shadaya. a hankali sadiq ya zame jikin shi tare da shiga toilet, ya qara hadawa fatuha ruwan dimi daukar ta yayi ya kaita toilet yana dire ta ta bude ido tare da lumshe su, da wani kunyar shi take ji a wannan lokaci. ruwan dadi ya mata taji dama dama, Sannan ya mai dota bedroom shima ya koma yayi wanka ko da ya fito ta shirya cikin riga da sket na atamfa dinkin ya mata kyau sosai ga make up tasha wani lalausan smile Sadiq ya saki tare da qarasuwa ya rungume ta baya ciki cool voice yace "My love kinyi kyau?" murmushi tayi tace "Thanks" lotion ta janyo tare da shafa mai ita da kanta ta zaba mai kaya wani hadadan yadi mai tsada ta curo mai milk da ratsin brown mara kauri ya sha diki'n da dark brown zare taimaka mai tayi yasa tuni suka fito sukayi kyau. knocking din kofar da ake ne ya sa sadiq qoqarin fita kusan a tare suka fito da fatuha parlour ta bi da kallo wani irin kyau ya mata gidan kamar ba'a qasar Nigeria ๐Ÿ‡ณ๐Ÿ‡ฌ take ba,

A hankali ya bude kofar baba jinmai ce riqe da kuloli ,murmushi sadiq ya saki tare da gaishe ta angel ce ta fada jikin shi tare da rungume shi tace "Daddy?" dariya sadiq ya saki ya cabe ta, qarasa shigowa baba jinmai tayi ta aje kuloli, fatuha qarasowa tayi ta gaida baba jinmai ta amsa angel sakowa tayi daga jikin daddy ta rungume fatuha smile fatuha tayi tace "I miss u angel tare da yi mata pack a kumatu"

Parlour angel ta dawo tace "Daddy ya kunna mata kallo" kunna mata yayi shima ya zauna kusa da ita baba jinmai ko jan fatuha daki tayi tare da bata sakwan mom na kayan tsimi da turaru ka masu kamshi da shegyan tsada. Godiya fatuha ta rinqa jera mata suka fita a tare, murmushi baba jinmai tayi tace "Jidda taso mu tafi ko? bata fuska fatuha da angel su kayi lokaci daya tace " A barta anan munyi missing nata ni da baban ta ko? ta fada tana kallan sadiq" murmushi yayi tare da daga mata gira yana jin dadi yadda fatuha ke gwada ma angel so da kauna. baba jinma saki'n baki tayi tace "Alalai ni zaku ma shaqiyanci to ai shikenan ni na wuce Allah ya bada zaman lafiya" har baki'n kofa fatuha ta rako ta Sannan ta dawo parlour hannu jidda ta janyo tace "Zo muje kiyi break nasan ba kiyi ba" tashi su kayi a tare taja mata kujera Sadiq yayi ta zauna shima ya zauna Sannan angel ta zauna, saving din su fatuha tayi a hankali sadiq ya fara feeding din fatuha itama tana feeding nashi da angel sai murna suke suna jin dadi cike da so da kauna ida sadiq ya zage yana gwada masu so".


*Agurguje*

Haka rayuwa ta cigaba da tafiya cikin jin dadi, fatuha ce tsaye gaban dressing mirror sanye da uniform kasancewar yanzu ta koma school, yanzu haka tana SS3 kuma ita ce Head girl tana shirya sadiq cikin uniform nashi smile yayi tare da yi mata pack yace "I love u" "love u more habibina" briefcase din sadiq ta dauka tare da school bag din ta suna fitowa angel suka samu zaune saman dining area ta fara break gaishe su tayi tare da yi masu pack suma kujera suka ja suka fara break. bayan sun kamala fatuha ta kira yar tsohuwar me aikinta tace ta kulla da gidan Sannan karta dafa abinci sai ta dawo zata daura to tace mata tare da yi masu Allah ya kiyaye hanya. ta koma gida mota suka shige sadiq ya ja su be sauke su ko ina ba sai harabar makaranta yana parking angel ta bude kofa ta fita fatuha na qoqarin fita ya riqe ta, murmushi ta saki a hankali ya janyo ta jikin shi yayi kissing na ta lumshe ido tayi tare da ware su a kan sadiq tace "Habibina zanyi missing naka?" nima haka my love, Sannan fatuha ta bale murfin motar ta fita,


Tana Shiga class su Zara suka dau shewa kai Head girl kina wuta wallahi, harara ta aika masu wallahi na kusa maganin ku hehe lalaima wata dariyar shaqiyanci Zara tayi tace "kwanan naga wani sheqi kike me sirin?" littafin hannu ta fatuha ta gefa ma Zara dariya suka sa zakiyi bayani wallahi ganin uncle ya shigo yasa su natsuwa aka cigaba da gabatar da darasi, kasancewa yau juma'a karfe 12:30pm suka tashi drive ne ya zo daukar su direct gida ya dire su


Wanka suka yi sannan fatuha ta shirya cikin 3 quarter pink tasa t-shirt milk ba qaramin kyau fatuha tayi ba ,sai gashinta da ta sharce ya kwanto har gadan bayan ta fitowa tayi tare da shiga kitchen, tuwon shinkafa ta daura miyar agushi taji naman rago kamshi sai tashi yake Sannan ta ahada juice din mangworo dan ba qaramin dadi yake mata ba. kwana biyu nan bayan ta kamala ta dawo dining ta jera Sannan ta koma bed ta qara sheqa wanka ta fita ta shirya cikin gown din ta maroon mai Stone's diki'n ya hauta sosai parking din gashi ta tayi jin a shigone ya sata waigowa angel ce tsaye baki'n kofa, murmushi tayi tace "Mom kinyi kyau" murmushi fatuha tayi langwabe kai angel tayi tace mom ina so naje gidan mami yau ne birthday din Jamal smile fatuha tayi tace "To shikenan amma sai kin fara lunch" dan shagwabe fuska tayi tace "Please mom kin san fa nice best friend tare zamuyi komai" ok naji ina zuwa wata hadadiyar gown ta curo daga wardrobe tare da gift tace gashi wannan gown din taki ce ita zaki sa ki tafi wani irin tsale angel tayi ta rungume fatuha tana mata pack thanks mom, Sannan ta zame jikin ta dariya fatuha tayi tare da lakace mata hanci tace "Wannan gift din kuma na Jamal ne Godiya ta mata tare da rugawa daki ta shirya girgiza kai fatuha tayi ta cigaba da abinda take. rungume ta baya akayi lumshe ido tayi tace " Habibina" ajiyar zuciya sadiq ya saki yace "My love" gabaki daya make up din ta gigitani kinyi kyau smile tayi tare da juyowa suna facing juna a hankali ya kai hannu ya warware parking din....



*Taku har kullun salma mas'ud nadabo*
[7/7, 9:01 PM] ๐Ÿ˜ƒ๐Ÿ˜€SmileR๐Ÿ˜€๐Ÿ˜€: *CAPTAIN SADIQ*
๐Ÿ‘ฎ๐Ÿผโ€โ™‚

*Writing by*
*Salma mas'ud nadabo*


*Edit by*
*Raheenat*


http/mobile.Facebook.com/Real-Hausa-fulani-writers-forum RHFWF-173984973194167/?refid=52red=opare_speed_dial_&yn=H-R


*Email* [email protected]


*Facebook* www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERFORUM.COM



99_100


1 *Month letter*

Rayuwa ta cigaba da tafiya ciki'n jin dadi, inda sadiq ya samu qarin girma dan yanzu h'aka abuja ya koma da aiki sai weekend yake dawowa kano. fatuha kuwa shirye shirye SSCE suke angel kuma JSSCE, sosai suke samu kulawa wajan sadiq inda yake fifita son su dana kowa, ya ware masu guri na musanman a zuciyar shi h'aka ita fatuha sosai take bashi kulawa da nunamai tsantsa soyayya.

Bangaran su fatima majeed ya sama mata makaranta su fatuha ta fara tun daga jss1 sosai tak'e maida hankali dan ganin taci ma burin ta,

Basma kuwa Khaleed ya sama mata admission a BUK tana karanta english, sosai take samun kulawa wajan Khaleed.


Dr yakub kuwa sai soyayya suke zubawa shi da hanan har manya sun shiga maganar.


Yauma kamar kullun wainar flower tak'e soyawa wadda kwana biyun nan ta zamar mata jiki, dan ko yini bata iyayi bata ci ba, har wata yar kiba tayi da haske komai na jikin ta ya ciko da ka ganta kasan tana jin dadi. rungume ta da akayi ne yasata saki'n murmushi tare da waigowa sadiq ne sanye da kaki'n shi hannu sa na riqe da qugunta, kallan shi tak'e cike da so tace, "Habibina yaushe ka dawo?" pack sadiq ya mata yace "Yanzu nan ji nayi bana iya hakuri rashin ganin ki har sati? gaskayi sweetheart daukarki zanyi mu koma tare?" smile fatuha tayi tare da cewa "Bari na kashe gas din nan to" kallan wainar yayi tare da cewa "Miqiqe da wannan abun?" ci tace ataqaice tana qoqarin tura wani cikin baki'n ta dan bata iya hakuri. bin ta da kallo sadiq yayi tare da cewa "Yaushe kika fara cin wannan dear?" d'aga kai sama tayi tace um na dan kwana biyu" ok yace tare da daukar ta suka haura upstairs cakulkuli ya shiga yi mata sai dariya tak'e zubawa dan tsagaitawa yayi yana kallan face nata yace "Ina Angel?" shafa gefen face nashi Fatuha tayi tace "Tana wanjan grandma dazu da baba jinmai ta zo shine ta bita suka tafi" ok yace tare da fara kiss nata ko ta ko ina French kiss ya fara mata yana aika mata da sakwanin shi masu zafi h'aka ita fatuha ganin zasu lola duniyar ma aurata naja masu kofa na fece.


A tare suka shige toilet sukayi wanka, dauk'e da ita sadiq ya fito yana mata cakulkuli tana dariya tace "Habibina sokake ciki na ya qule ko? ta ida zancan tana mai da numfashi" lakace mata hanci sadiq yayi tare da dire ta saman sofa ya janyo lotion yana shafa mata itama tana shafa mai Sannan suka shirya cikin jeans n t-shirts iri daya jeans blue rigar red da ratsin dark blue n white wani irin kyau suka zuba masha Allah,


Parlour suka fito a tare, suka wuce dining area lafiyayan chicken and begetable stew tayi tare da cuscus da miyar kwai , tun kafi sadiq ya fara ci ya lumshe ido saboda kamshi dadi dama gashi fatuha ba baya ba wajan iya abinci saving nashi ta gama yi Sannan ta fara feeding din shi yana ci yana jin dadi gefe ga natural lemun kankana amsar cokalin yayi tare da kai mata abinci baki ta amsa tana ci zuciyar ta na tashi da gudu ta haura sama tana kakarin amai. binta sadiq yayi a baya toilet ta shige ta rinqa kwara amai kamar zata amayo yan cikin ta gabaki d'aya sadiq ya rude sai tanbayar ta yake lafiya? wanke mata fuska yayi tare da kuskure mata bak'i ya d'auke ta lamo tayi a jikin shi tana sauke ajiyar zuciya ba abinda ke mata dadi kamar turaran d'ake jikin shi kamar karya sauke ta. saman bed ya dire ta tare da komawa toilet ya wanke inda tayi aman tare da wanke toilet din ya fito gefan bed ya dawo ya zauna yana taba goshin ta. sweetheart sannu mirginuwa tayi ta lafe jikin shi tana shinshinar kamshin turaran shi tayi lamo, haka ya rinqa zuba mata sannu tare da ciro wayar shi ya kira Dr yakub ko mintin 10 ba'ayi ba yazo, sadiq yamai iso har bedroom din tana kwance sai sanyi take ji tana qudidine cikin blanket, sannu Dr yakub ya mata tare da yan gwaje gwaje tanbayar ta yayi yace me dame ke damun ki kamar mai dame kike ji, cikin sanyin murya Fatuha tace Zazabi ciwo kai da yawan tashin zuciya" rubuce rubuce Dr yakub yayi tare da bata wata yar gwal yace "Ta shiga toilet tayi fitsari a cikin ta" ta kawo mai a hankali ta tashi da shiga toilet sadiq dai na gefe sai sannu yake mata, ko 5 minutes batayi ba ta fito amsar gwalbar yayi tare da sata cikin jakar aikin shi ita kuma Fatuha ta koma ta kwanta smile yayi yana kallan sadiq yace Insha Allah zata Samu sauki indai abinda nake tunani ne sai dai muce Allah ya raba lafiya, amma for now sai mun fara yin test din tukun na" murmushi ne ya subuce ma sadiq tare da fatan Allah yasa abinda shima yake tunanine .

Har baki'n mota ya raka Dr yakub Sannan ya juyo gida, ko da ya dawo kwance ya same ta yadda ya barta. saman bed din shima ya hau tare da taba goshin ta cikin shagwaba tace "Habibina?" na'am sweetheart lumshe ido tayi tace "Zanci irin wannan abincin dana fara ci randa na zo birni?" kallan ta sadiq ya shiga yi yau kusan shekara nawa shi yanzu aka tare shi da mindiga be iya tuna me akayi ranar. cikin sanyin murya sadiq yace "Sweetheart kiyi hakuri ki fadi wani abun amma wannan bana iya tuna wa ko min akayi? ko kina iya tunawa sai a maki?" d'aga kai tayi yace "To fadi min" shinkafa da miya da kosulo da farfesun yan'ciki to sadiq ya ce mata tare da yi mata pack ya fita,

Kitchen ya shiga ya sami baba asabe na ta goge shi, gaishe ta yayi a taqaice tare da fada mata abinda zata ma fatuha to tace mai jiki na bari ta fara aiki ,shi kuma ya koma bedroom din sai zuba mashi shagwaba take, ko da baba asabe ta gama ta kai dining area ta jera, dauko Fatuha sadiq yayi ya kawota tare da daura saman cinyar shi ya fara saving nata a hankali ya nufo da cokalin bakin ta tunkan ya kai bakin ta zuciyar ta fara tashi da sauri ta miqe riqe ta sadiq yayi yana kuma tanbayar ta kafin ya ida magana ta wanke shi da amai langwabe kai sadiq yayi yace "Sorry my wife" kuka ta saka mai lalashita ya shiga yi tare da daukar ta suka koma bedroom be dire ta ko ina ba sai cikin toilet, wanka su kayi a tare Sannan yasa bathrobe tare da nadu Fatuha ciki'n towel sai kuka tak'e mai yana lalashin ta kwantar da ita yayi yana qoqari dako lotion wayar shi ta hau ruri a hankali ya kai hannu ya dauka suna Dr yakub ne ya baya na a jikin scream din cikin sauri ya dauka tare da karawa kunne, hello Dr yakub tare da cewa albishirin ka dan tsaki sadiq yaja tare da cewa me kuma hakan ina fama da Mara lafiya kana kirana ka min irin wannan kidding din toh shikenan tunda baka San sanin maganin dan. smile sadiq yayi yace "Goro" yauwa ko kai fa amma fa sai ka bani Goran albishir to sadiq yace tare da qaguwa yaji mi Dr yakub zaice dariyar shaqiyanci Dr yayi yace angwan qauri kasha kamshi Dr ya fada yana dariyar shaqiyanci ina fama congrat madam nada juna biyu na wata 1, wani irin lalausan murmushi sadiq ya zaki yace "Wai da gaske kake?" yace eh mana, gaskiya naji dadi wannan albishiri, toh nima a bani goran albishir dariya sadiq ya saki tare da cewa na dau nauyin tafiyar ku zuwa honeymoon kowace qasa kuke so a duniya tare da Baku kudin kashe wa .wata irin dariya Dr yakub ya fashe da ita yace "Wai da gaske kake?" yace eh mana ana daura maku aure da hanan zaka ji alat sallama su kayi tare da kashe wayar juyowa sadiq yayi tare da sakar wa fatuha da lalausan murmushi itama smile tayi lotion ya shafa mata tare da samata kaya Sannan shima ya shirya kallan ta yake cike da so tare da daura hannu shi saman cikin ta yace "My love yanzu nan akwai baby na ko," kallan sa Fatuha take tace "Wanne baby kuma?" yace ko baki so ki haihune um ya fada yana kallan ta kuka ta saki tare da tashi tace Allah bana so yanzu ya zanyi da exam da ciki tun yanzu yana bani wahala bale kuma inna fara exam kuka ta saki tana cewa Allah ban so a kai kasuwa janyo ta sadiq yayi jikin shi yace "Fatuha yanzu jinane baki so? ya fada yana kallan ta" ni ban ce bana son jinin ka ba? amma ai matsamin zeyi shikenan haka zan rinqa shiga cikin su Nana da ciki ta ida zancan tana kuka kalli ka gani ko fa yau cikin ya hanani cin abinci, yi hakuri Fatuha ai duk wannan abun na dan lokaci ne. tsale tayi ta dire ita bata so sai dai a zubar har ta kai ga ran sadiq ya fara baci qoqarin fita yayi d'aga dak'i tare da cewa gobe zai auro wanda zata iya zama da cikin shi koma a inane kuka fatuha tasa tana cewa Allah ba mai shigo min gida ni ka dai ke da kai wallahi, ta ida zancan tana qara sakin kuka. abinma dariya yaso ba sadiq ganin duk tabi ta rude yasa sadiq yace mata ya fasa amma sai in zata zauna da cikin shi? amincewa tayi tare da juya mai baya tana qara sautin kukan ta,

Janyo ta sadiq yayi yana lalashin ta lamo tayi a jikin shi, cikin cool voice yace "My love mi zaki ci?" cikin shagwaba tace "Danwake" bata fuska sadiq yayi yace gaskiya babyna ba zaici mai da yaji ba, kuka ta fara shirin samai ganin ba yadda zaiyi haka ya fada ma baba asabe tayi mata dan wake ba laifi taci dan wakyan sosai da akayi har da side plate.


Haka rayuwa ta cigaba da tafiya inda fatuha ke samun kulawa sai dai cikin mai laulayi ne sosai .kusan a tare suke laulayi da su fatima amma sai dai duk ta fiso ga wani shegyan kwadayi da ya samata angel ko da taji mom na da ciki murna ba'a magana mom za tayi mata qani ko qanwa ta samu abokiyar fira.


Shirye shirye ake sosai na biki'n hanan dan yau duk kusan sun halara family house saboda yau ne za'ayi kamu, bayan sun gama exam din maths a school driver ya zo daukar fatuha be zame da ita ko ina ba sai family house. a gajiye likis ta dawo yana sauke ta tashigo gida umma ce ta tare ta, tare da hada mata ruwan wanka ta shiga toilet ta fito kasan cewar ansan yadda cikin ta yake farfesun kifi mom ta mata mai dadi tana fitowa ta iske kayanta saman bed after dress ce ta zura Sannan ta fito parlour tana fitowa ta samu su fatima suna ta kwasar suma nasu farfesun, kwabe fuska tayi tana kallan mom da itama kallan ta take dariya daki'n ya dauka mom ta janyo ta tare da bude mata kola ta fara feeding nata tana amsa sai janta suke ta fiye raki harara da rinqa aika masu mom tace taje tayi din kuma din ai kawai shuru kukayi da bakwa rakin kuma raki ba'a Sani sai ranar juyewa ammi dariya tayi tace kai hauwa kina fama da surikan nan naki wallahi, ya zanyi ammi ,komai cikin walwala da jin dadi da soyayya suke samu inda gidan maza jan nasu ya zama kamar gidan iyayan su dan yanzu sunfi mazan ma samun qugun zama har qorafi mazan keyi saboda banbanci da ake masu anfifita Matan a Kansu musanman yanzu da suke da juna biyu..




*Taku har kullun Salma mas'ud nadabo*
*CAPTAIN SADIQ*
๐Ÿ‘ฎ๐Ÿผโ€โ™‚

*Writing by*
*Salma mas'ud nadabo*


*Edit by*
*Raheenat*


http/mobile.Facebook.com/Real-Hausa-fulani-writers-forum RHFWF-173984973194167/?refid=52red=opera_speed_dial_&yn=H-R


*Email* [email protected]

*Facebook* www. Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERFORUM.COM


101_102

*_Godiya ta musanman gare ku REAL-HAUSA-FULANI-WRITERS-FORUM wannan shafin naku ne, ana mugun tare irin sosai din anan Allah ya bar zuminci da qarin hada kanmu._*


Qoqari'n sa rigar ashoben tak'e da mami ta dinka masu, amma sket din ya kasa shiga saboda hips din ta da ya qaru. lagwabe kai tayi ji take kamar tayi kuka jin an bude kofa ya sata waigowa ganin sadiq ne tsaye, kuka ta fara reramai qarasowa yayi da sauri tare da dagowa da face nata "My wife me ya saki kuka?" um, wani kukan ta qara saki tace, "Habibina ashobe na ya kasa shiga? ta tun dazu nake jan sket din yaki shiga ta ida zan tana samai kuka" janyo ta jiki'n shi yayi tare da zaunar da ita saman bed yace "Wannan ne matsala?" d'aga kai tayi alama eh, toh shikenan bani kayan na gani amsar kayan sadiq yayi ya duba Allah ya taimake ta akwai space zaunawa yayi ya warware skeet din da rigar Sannan ya miqa mata tasa maqale qafa tayi ita bata iya sa kayan hannu ta nauyi yake mata, lakace mata hanci sadiq yayi yace, "My love yau baby na rigima ya saki ko?" turo baki tayi gaba cike da shagwaba kiss nata sadiq ya fara ko ta ko ina ganin ze zarce yasata samai kuka. smile yayi tare da cewa sorry Sannan ya samata kayan shima shiryawa yayi cikin manya kaya Sannan ya jata suka fito ko da suka fito lokaci su fatima sun shirya ita ka dai suke jira ta fito, tana fitowa fatima tace "Sai muje ko? ta ida zancan tana aika mata harar wasa" murguda mata bak'i tayi Sannan suka fice sadiq kuma ya wuce wajan angwayan saboda kamun ba maza.


Suna shigewa mota fatima tace "Ke h'aka ake? d'aga shiga sa kaya saiki maqale da miji" kam mikika daukan to nayi din ta fada tana aika fatima hararar wasa. dariya suka kwashe da ita a tare suka ce kin tuna san da muke zuwa gonar mai gari? dariya suka kuma saki tare da kallan juna suka yi tare da cewa Allah mun gode maka bamu taba tunanin ganin a haka ba rungeme juna sukayi tare da hade bakin su suka ce Allah ya bar mana zumincin mu har ya'ya da jikoki ameen. Fatsima harara ta aika mata ke mijina ya hana fadi wannan suna, dariya sukayi tare da cewa sannu mai miji a h'aka suka Isa wajan kamun kasancewar sune Maya Mayan qawayan amarya hada hada kawai suke biki yayi biki su Zara da Nana ma sai da suka zo ansha biki sosai sai kusan yama likis suka dawo, gidan mami suka wuce direct.


Cikin sallama suka shigo angel d'ake zaune da friends nata ta qaraso tare da rungume fatuha tace "Mom a I miss u?" miss u more dear, kin manta da mamanki tunda biki ya kama ko? to ai gashi nan ni na biyo ki bana iya hakuri kimin nisa fatuha ta fada tana shafa kanta smile tayi sannan ta koma cikin friends din ta.



Shirye-shirye ake na zuwa dinner ,ciki'n wata material lace green

Please Login or Register in order to submit comment