Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gyara daurin dankwalin ta tare da amsa mai ta qaraso parlour itama ta zauna, ohni mai gida ace min jiki yayi sauki da har na fara dakan gunba ance min kana can rai hannu Allah ka zama dan gurgu ta ida zancan tana dariya ,turo baki sadiq yayi yace "Haba ammi har so kike na bingire kenan ?dariya ammi tayi tare da janyo jidda jikin ta yar nema yau ba'a amin gwalangwatsin ba smile jidda tayi kawai tare da cewa "Ammi ina gorubar da kika ce zaki siyo min ni da jamal? yar nema ashe baki manta ba ai tuntuni na siya tana daki na cikin drowe, da gudu jidda ta shige dakin ammi ta dan juyo tana facing din sadiq gyara murya ammi tayi tace "Ni ko Sadiq ya kamata kayi aure? Yanzu fisabilillahi dubi yadda jidda tayi wayau sosai yarinya na shirin zaman yan'mata, amma kai baka ko maganar aure bale nuna sha'awar ka ko dai baka lafiya ne Abubakar sadiq?" sadiq dake zaune saman three star ya hada gira sama data qasa kamar be taba dariya ba, kai kullun baka so a fada ma gaskiya sai ka hau gunguni shi kuma Ibrahim ya zuba ma ido ko maganar aure bai ma, sadiq ko tunda ammi ta fara magana ya kai wuya dan shi be da tsarin yin wani aure yanzu, Alhaji ne ya qaraso parlour da alama yanzu ya dawo daga kasuwa ganin ammi nata fada yasa Alhaji qaraso dan yaji ba'a sin zancan, ganin sadiq tatasa gaba ya san maganar gizo bata wuce qoqi, haba ladingo ya za ai ki tasa yaro gaba kina mai maganar aure? eh koma me ake samu a auran nan ai ya taba yi inya gaji da zama haka ai dole yayi aure tunda shi ba qarfe bane, ammi tabe baki tayi tace "Malam kenan da yaranan na da wannan tunanin ta tuni yayi amma kwata kwata banga alamar yin hakan ba , koma dai meye ba kyau sasji gaba ba kina mai fada, ba ko abin motsa baki amma sai fada kike mai, shiko sadiq dadine ya mamaye mai zuciya sai murmushi yake, ammi tayi yake tace "Wallahi malam abin ya tsayamin araine?" Alhaji zama yayi kusa da sadiq tare da shafa gashin shi yi hakuri kaji Abubakar sadiq, qaqaro murmushi sadiq yayi Wanda iya qarshi lips din shi yauwa ko kai fa, ammi kuma asiya ta kwalawa kira ta kawowa Alhaji abinci da sadiq, sadiq sai fama daurewa ammi yake bayan asiya ta kawo komai ammi tace ya sauko ya ci, na koshi ya fadi a taqaice, bude baki ammi tayi ta fara fada yanzu ni sadiq ban isa nama magana ba ko na baka shawara sai ka nunamin ban isa ba ko Ibrahim ai bai isa yamin haka ba matsar kwalla ta fara Alhaji da ke gefe ta kaici ma ya hana shi magana sadiq ganin abun ammi da gaske ne ya sashi cin abincin tare da sakin rai sannan ammi ta ji dadi ba laifi ya dan saki jiki amma sai wani bangare na zuciyar shi ya ke ji kamar ta famamai inda ke mai qaiqayi tabas yasan yayi rashin kausar har abada bazai kuma samun wada zata maye gurbinta ba, amma wani bari na zuciyar shi yaqi yadda ya cusa san wata diya mace har ta samu gurbi a zuciyar shi numfashi ya sauke tare da miqewa tsaye yana kiran angel, mai gida kardai ka ce min tafiya za kayi ?ko har yanzu baka huce ba? murmushi sadiq yayi haba matar ni na isa nayi fushi dake nayi fushi dake gobe ina zan fake washe baki ammi tayi tace yauwa dan albarka , Allah yasa ma Albarka ameen ammi , bari na kirama yar neman nasan yanzu haka ta wargaza min daki dariya Alhaji yayi ya ce aiko data kyauta, malam har da kai masu biye ma ifiritan nan ko da yanzu Jamal zai zo su hade biyar baka siyan part din nan dariya Alhaji yayi tare da shigewa bedroom din shi, ammi kuma ta shige nata tana kwalawa jidda kira aiko tana isa dakin taci karo da abin goriba duk jidda ta watsar a tsakar dakin ohni ladingo ai dama na fadi nasan za'a rina tunda najiki shuru washe baki jidda tayi tace ammi, sadiq dake parlour ya qaraso yana dariya laa angel waya ce kiyi ma ammi baena turo baki tayi tace "Daddy ba bana nake ba" ammi tace gidan ku kikayi ko? dariya jidda tayi ta boye bayan baban ta , ammi bari mu qarasa part din Umma toh shikenan saura canma ki mata barnar haqora jidda ta washe sannan sadiq yayi ma ammi sallama suka wuce part din Umma.


Parlour ta kuma dawowa tare da kallan agogo ganin karfe 3:00pm yasa fatuha rau rau da ido, tasan za'a rina tunda aka bar amanar ta a hannu sangami a iya tunanin ta ko wanne gari suka kai su mom ya ci ace sun dawo gida, zama tayi saman one star can kuma sai ta tashi upstairs ta haura sama direct part din sadiq ta shige a hankali ta murda handle din cikin sa'a kofar ta bude saboda a tunanin ta ya kulle part din, tana shiga sanyi da kamshi suka mamaye mata hanci lumshe ido tayi tare da mai da kofar parlour ta rufe bedroom dinshi ta shige tana ta kalle kalle wani album ta hango ya leqo ta qarqashin gado duqawa tayi tajanyo shi da hannun ta washe da baki ta bude album din pics din sadiq ta fara cikin karo da shi ya saki murmushi a pic din gashi yasha kyau har ya gaji ,cigaba tayi da ganin pics din album din wani guri ta Ganshi da kausar wani gurin shi daya ganin yadda suke pics din yasa fatuha ta dade tana kallan pics din ko ba'a fada mata ba tasan maman jidda ce saboda suna kama da jidda ji tayi gaba ki daya sun birge ta haka ta lalace tana kallan albums din kiran sallah la'asar ne ya sata qoqarin mai da album din har ta turashi qarqashin gado sai ta ji wani album din janyo shi tayi tare da yin smile, bari na tafi da wannan inna idar da sallah ya debe min kewa, tunda ni ka dai suka bari wato sun barni a gida duk abinda zai cinye ni ya cinye ni downstairs ta dawo ta aje album din a parlour ita kuma ta koma bedroom din ta dauro alwala.


Cikin sallama su ka shiga part din umma, Umma na zaune tana kallo tana shan fruit a hankali da alama zaman ya mata dadi ,cikin fara'a ta amsa sallamar su sadiq zaunawa yayi tare da gaishe ta ta amsa jidda ko saman ciyar Umma tayi masauki, yan'mata baba fari da ido jidda tayi tace "Na'am grandma" a'a waya koya maki fari da ido haka? dariya tayi tace "Anuty mana" wace Anutyn? Ta bata Amsa da cewa "Anuty fatuha mana" ah ni ban santa ba kam aiko Anuty fatuha na da kirki sosai yanzu haka tana gida murmushi Umma tayi tare da yi masu tayi fruits qasa sadiq ya sauko ya sha fruits din shi ya qoshi sannan ya haura upstairs cikin natsuwa ya murda handle din kofar daki kwance ya hango majid yana ta sharar bacci dan gutun tsaki ya ja tare da shiga daki fridge ya bude ya dau ruwa mai dan sanyi sanyi sai da yazo saitin face din majid ya zuba a hannun sa ya shiga yayafa mai, firgigit majid ya miqe yana qoqarin tashi ganin sadiq yasashi komawa ya zauna tare da zabga tsaki , kai dai wallahi mugune ,in banda mugunta ina bacci zaka sheqa min ruwa? harara sadiq ya aika mai yanzu lokacin bacci ne kana ganin la'asar ta wuce, mtss toh ina ruwan ka? da ruwa na sannan ya zauna saman sofa, wallahi big man baka kyauta min ba wallahi mafarkin wata hot baby nake kawai ka zo ka katse wa mutane jin dadi mtss tashi ka ban guri Dan iska kawai, dariya sadiq ya fashe da ita sakin baki majid yayi yana mai kallan rainin wayau me haka wai , kaga kyale ni je kayi wanka first munyi magana, ya ida zancan cikin dariyar shaqiyanci tsaki majid ya kuma ja sannan ya yaye blanket din jikin shi ya wuce bathroom ko 50 minutes beyi ba ya fito sanye da bathrobe dressing mirror ya nufa ya shafe jikin shi da mai da sunyi 4 eye's da sadiq sai ya aika mai harara shiko sadiq fuska yayi tare da janyo newspaper yana qarantawa sai da ya gama shirin shi tsaf sannan shima ya zauna saman sofa tare da qanqace ido yana kallan sadiq kamar zai mai masifa, dariya sadiq yayi tare da kuma daurewa duka majid ya shiga kai mai dan iskan banza sai wani kallo kake kana dariya munafuki Allah kadai kasani, mafarkin uwar me kake to? Maji da yace "Dadin abun ba kai na farau ba, ya ida zancan yana harara sadiq" smile sadiq yayi yace nina ce ma wani abun ne? wanka fa kawai na ce kayi? ko nace wani abu ya ida zancan yana kare fuskar shi da newspaper yana dariya, sun dade sosai a family house ba su suka fara tunanin dawowa gida ba sai kusan 9:00pm lokacin jidda ma tayi bacci har farfajiyar gida suka rako su sannan sadiq ya ja mota suka bar gidan.




fatuha ko tana idar da sallah parlour ta dawo, ta cigaba ta kallan album tun bata jin tsoro har ta fara ji saboda duhu ya kunnu kai kuka ta ci ta gaji tare da rakubewa jikin kojera rungume da album har bacci wahala ya kwashe ta, a dai dai parking space yayi parking dauke da jidda ya fito tare da yima motar key a hankali ya bude kofar parlour, ya qarewa parlour kallo tare da kunna haske parlour ya gwaraye ko ina cikin natsuwa ya qaraso kallo daya yayi ma kujera da fatuha take kwance sannan ya wuce upstairs bedroom ya shin fide jidda sannan ya shiga bathroom ya watsa ruwa yana fitowa jalabiya white yasa ya fita daga part din, saboda yana son shan coffee ya dawo downstairs inda ya bar fatuha nan take kwance ware mata kallo ya shiga yi duka gashin kanta ya baje akan kujera , cinyarta bude yake kasan cewar qaramar riga ce a jikin ta fuskar ta Sadiq ya qarewa kallo masha Allah yauce rana ta farko da ya fara kallan fuskar fatuha da kyau eyes lash din ta sunyi gadar gadar kamar ansa mascara, tabe baki yayi yana qoqari shiga kitchen har ya kai bakin kofa ya dawo saboda album din da ya ganta rungume dashi cikin zafi rai ya juyo yace fatuha cikin daka tsawa cikin razana ta tashi tsaye tare da sakin album din qasa, dab da ita sadiq ya qaraso cikin zafin rai yace "Uban me kike min da album? Dan iskanci shine kika sakeshi kasa ko ? a tsawace yayi maganar" kuka fatuha ta saki saboda gabaki daya ya ruda ta mari ya wanke ta da shi lafiyayan open your month and talk to me , kuka fatuha ta saki mai tsuma zuciya tare da yin magana cikin shashakar muryar tace "Dan girman Allah kayi hakuri me nayi maka ne mai kyau? koko amanar da mom ta baka tun yau zaka fara cinta ta ida zancan tare da fashewa da kuka, bayan horan da kamin na barina a cikin makekyan gidanan be ishe ka ba shine Dan karfin hali harda mari na😭 kuka ta kuma saki tare rugawa da gudu bedroom.

Sadiq ko amanar mom da yaji fatuha tace ne yasa jikin shi yin sanyi tare da daukar album din jiki ba qwari ya haura upstairs.




*taku har kullun Salma mas'ud nadabo*
*CAPTAIN SADIQ*
👮🏼‍♂

*Writing by*
*Salma mas'ud nadabo*

*Edit by*
*Raheenat*


📘 *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*🐄
★we are the best★

http//mobile.Facebook.com./Real-Hausa-fulani-writers-forum RHFWF-173984973194167/?refid=52&red=opare_speed_dial_&yn=H-R

*Email*:[email protected]

*Facebook*:www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERSFORUM.com


51_52

Fatuha na shiga bedroom saman bed ta fada tare da sakin saban kuka tana cigaba da jerawa sadiq Allah ya isa da ace Allah ya isan na fitowa a jiki to da daran yau ba abinda zai hana shi fitowa ajikin sadiq, kuka ta ke mai tsuma zuciya har da shesheqa tana a jiyar zuciya ita babban abinda ke damun ta koda ta zo mai muguntar sai ta kasa kuma ko tayi mai ramawa ya ke, lumshe idanuwanta tayi tare da sauke numfashi a hankali ta cigaba da jerawa sadiq alkaba'i haka har bacci barawo ya sace ta.


Bangaran sadiq ko saman sofa ya zauna tare da ganin be kyauta ma fatuha ba, lumshe ido yayi tare da ware su koma mai yayi mata ita ke san shiga gonar shi shiyasa shi kuma baya saurara mata da tasan yadda yake ji in yaga albums dinan da ko fada mata akayi ta dauko su inda ya aje ba zatayi ba, iska ya busar mai zafi daga bakin shi bayan ammi ta gama hada mai zafi ita kuma ta da gulamai lusafi album din ya bude a hankali kamar mejin tsoran wani abu ya shiga kallan pics din ya dade yana kallo inda yake ganin mutuwar kausar ta dawo mai sabuwa har hawaye sai da ya zubar kamar ba soja ba, anan saman sofa bacci ya kwasheshi.


*Asuba ta gari*

Ko da ya tashi da asuba wanka ya sheqa sannan yasa jalabiya ya wuce masallaci ,yana dawowa ya samu bacci mai cike da natsuwa amma duk da haka qirjin shi namai zafi saboda tsabar damuwa lumshe ido yayi tare da jan jidda jikin shi bacci ya kwashesu.

Fatuha ko da kuka ta tashi fuskar ta har tsami ta mata, saboda ba qaramin mari tasha hannun sadiq fuskar nan ta kunbura tayi sumtum kallan mirror tayi tare da fashewa da kuka fuskar tayi jawur har idanta sai da ya qara girma saboda tsabar kuka ,toilet ta shiga tayi wanka tare da dauro arwala tana fitowa after dress tasa black tare da gabatar da sallah ko da ta idar da sallah kuka ta cigaba da rerawa sannan ta tashi jiki ba qwari ta murda handle din kofar tare da ficewa daga bedroom din direct part din sadiq ta shiga, duk da tana jin tsoro haka ta lalaba ta murda handle din kofar bedroom zaune ta hango sadiq saman sofa yana danna laptop yana shan coffee cikin dari dari ta qarasa shiguwa tare da yin sallama, dago kai sadiq yayi ya qare mata kallo shi kan shi yasan be kyauta ma fatuha ba ya bata mata baby face din ta, rabewa ta shiga yi dan tak take jira ta arce sunan ta ya kira cikin cool voice din shi gaban ta ne ya yanke ya fadi duk da yauce rana ta farko da me kyau ya fara kiran sunan ta, sai taji duk duniya ba wanda ya iya fadi fatuha qara kiran suna ta yayi hakan yasa ta fara matsar kwalla tana yarfe hannu ta qarasa kusa da shi tare da tsugunnawa tana wasa da yantsun hannu ta idanuwanta taf da kwalla hannu yasa ya dago da habar ta lumshi ido yayi tare da waresu gaskiya be kyauta ma fatuha ba ji yadda ya mai da fuskarta, tausayi ta bashi sosai kuka ta shiga reramai a tunanin ta wani mari zai qara zabga mata shhhh ya ce mata cikin cool voice nashi shiru tayi tana matsar kwalla bedside drowe ya bude ya ciro magani a dan top sannan ya dawo sofe ya zauna tare da talabo mata fuskar matsar maganin yayi a hannu ya shiga shafa mata a face din ta kuka fatuha ta saka sai kace ya watsa mata ruwan zafi iskar bakin shi ya shiga hura mata mai sanyi nan fatuha ta lumshe idanuwan ta wani irin dadi taji dan tunda ta tashi da safe fuskar ke mata radadi sai yanzu da taji dama dama, ware eye's ball din ta tayi kan sadiq, sadiq da ke qoqari dagowa goshin su ya hade ushhh , shagwabe fuska fatuha tayi tare da fara kuka sorry yace mata sannan ya sa hannu ya murza mata wajan dan karya kunbura sannan ya kyaleta tare da yi mata lalausan smile tashi tayi tana qoqarin daukar jidda su fita, fatuha yace juyowa tayi tana kallan shi, shiga da ita toilet dina ki mata wankan to ta ce mai sannan ta shige da jidda bathroom bin ta yayi da kallo tare da daukar newspaper.


Bayan ta wanke jidda tas suka fito washe da baki jidda ta gaisheshi, amsa mata yayi tare da yi mata pack, Anuty me ya sami fuskar ki jidda ta fada a tsora ce kallan sadiq fatuha tayi shima ita yake kallo sannan ya kauda kai murmushi fatuha ta qaqaro tace "Bigewa fa nayi jiya, aini fushi nake dake Jidda kika tafi kika barni ni ka dai a gida to shine fa na bige gashi ba kyanan" raurau jidda tayi da ido tace "Sorry Anuty ba laifina bane laifin daddy ne ta ida zancan tana nuna daddy da hannu" daddy tace cikin shagwaba yes yace a taqaice yana kallan newspaper, daddy please kar a qara barin Anuty a gida ita kadai daddy kalli face din Anuty fa?" tana fadi tana ware ido juyowa sadiq yayi ya kalli jidda tare da lumshe ido angel kin fiye surutu please ki tsaya Anuty ta shirya ki kinga mun kusa maqara ,sai da fatuha ta gama shafe jidda da mai sannan suka fita kai tsaye bedroom din ta ta dire jidda ta shirya ta cikin uniform din ta sannan ta ruqo hannu ta suka fito parlour dînner area suka zauna ta shiga bama jidda abinci tana feeding din ta sadiq ya qaraso dining area riqe da briefcase din shi kujera ya ja ya zauna ,plate fatuha ta janyo ta fara saving din sadiq yau anci sa'a be hana ta ba sai da ta gama zuba mai ta tura mai gaba sannan ta hada mai tea a cup ya amsa ya fara sha zai kai chips din baki ya kalli fatuha da ke feeding din jidda, yace
"Ke Baazakiyi break din ba?" kallan shi fatuha tayi ta hadiye wani yawo dan bata san me yake nufi da hakan ba murmushi sadiq yayi ya ce yar kauye kawai kalaci nake nufi washe baki fatuha tayi tace "Aiyo zanci to" fara cin yanzu murmushi tayi tana ci tana feeding din jidda a zuciyar ta ko mamakin canji sadiq take, shiko sadiq amanar mom yake riqewa ba wai wani abun ba.


Bayan sun gama break har filin gida fatuha ta rako su da lunch box din jidda pack jidda ta mata tare da yi mata bye bye, fatuha na tsaye har suka fita daga harabar gida ta juyo ta dawo cikin gida kayan breakfast ta kwashe ta kai kitchen, a kitchen taga rabi'a na girki murmushi tayi tare da gaisheta amsa mata tayi cikin fara'a sannan ta aje kwanikan cikin zing ta wanke su tas rabi'a sai hannata take amma taki kusan tare sukayi komai na kitchen din sannan suka jera a dining area ,washe baki rabi'a tayi tace kai amma fa fatuha na gode dan ba dan ke ba da yanzu ina ta aiki wallahi murmushi fatuha tayi tare da cewa ba komai wallahi, bari na zo na lalaba na wuce gida ,kallan tausayi fatuha tayi tace "Wai har zaki tafi ne?" eh wallahi ,yanzu ni ka dai za'a bari a gida nan kamar maya ta ida zancan tana matsar kwalla, yi hakuri kin ji fatuha akwai inda zani da ba inda zani dana taya ki hira amma akwai inda zani, murmushi fatuha tayi tace "Ba komai bakin kofa ta raqo ta sannan ta koma parlour ta zauna tare da kunna kallo kitchen ta shiga ta gyara fruit sannan ta dawo parlour tana ci tana kallo har bacci ya kwashe ta.


Bangaran sadiq yana sauke jidda ya wuce office, ko da ya je office yayi aiki sosai karfe 2:00pm nayi ya fito yaje school din su Jidda ya dauko ta suka dawo office tare sai zuba mai surutu take kowa na office din ji yake da jidda daka ganta hannun wannan sai ka ganta hannun wancan sai la'asar sadiq ya amshe ta suka wuce gida.


Fatuha ko kiran sallar la'asar ne ya tashe ta, wanka tayi tare da dauro arwala tana gama sallah parlour ta dawo tana lunch cuscus ne da miyar kwai take ci tana jin dadin abincin har wani lumshe ido take, sallamar su sadiq ce ta qatse mata cin abinci washe da baki ta kalli jidda rugowa jidda tayi ta fada jikin fatuha tana dariya itama fatuha dariya tayi tare da gaishe da sadiq ciki ciki ya amsa kamar me koyan magana sannan ya haura upstairs ,fatuha ko saida ta cikawa jidda cikin ta da abinci sannan ta kai ta bedroom ta rage mata kaya sannan ta kaita toilette ta mata wanka sai da ta wanke ta tas sannan suka fito suna daririku lotion ta shafa mata sannan ta sa mata gwon brown mai kyau tare da jan hannun ta suka dawo parlour ,Hango sadiq sukayi yana zaune a dining area yana lunch guri fatuha ta samu ta zauna jidda ko wajan daddy ta nufa tare da haye mai cinya tana mai surutu, daddy yes angel ,daddy please muje shan ice cream please ta fadi tana lagwabe kai ja mata hanci sadiq yayi ya ce "Wannan bakin naki kullun san zaqi yake" dariya tayi mai nuni tana cikin farinciki, ture plate din gaban shi yayi tare da aje jidda qasa qafa ta shiga bubuga mai ita aladule sai sun je shan ice cream yau , yace mata "Ok Angel is ok daina kukan kije Aunty ta Tashirya ki ko" sannan ya haura sama yana last stairs jidda tace amma har da Anuty zamu tafi dan kar dodo ya ji mata ciwo toh, yace tare da bude kofar part din shi.

Shirya jidda tayi tsaf amma ita ta rasa kayan da zatasa, duk gwon din data janyo sai ta maida jidda rugawa ta yi parlour zaune ta sami sadiq cikin shirin shi na qananan kaya yasa red riga mai ratsin black mai dogwon hannu sai wando black da takalmi yasha kyau har ya gaji sajan shi ya kwanta luf sai sumar kan shi da tasha gyara, daddy jidda tace ,a dan shagwabe sadiq ya juyo alamar gajiya menene angel lagwabe kai tayi tace daddy zo ka zaba ma Anuty dress ta rasa Wanda zatasa ,dan guntun tsaki sadiq ya ja yace "Angel me yasa kika fiye rigima?" um bata fuska tayi tana shirin yin kuka hakan yasa sadiq tashi ba dan ya so ba bedroom din fatuha ya shiga tsaye ya ganta gaban drower ta riqe qugu ga kaya baje a saman bed bakin kofa ya tsaya yana qarewa bayan ta kallo juyowa fatuha ta yi su kayi 4 eye's kauda kai tayi ta cigaba da abinda take a hankali ya qaraso wata gwon ya gani kawai ya janyo ba wai da ya lura da ita ba miqa mata yayi , kisa wannan mu tafi sannan yasa kai ya fice cikin 5 minute fatuha ta shirya cikin red gwon me Stone's sai black veil tasa tare da murza hoda ta shafa lipstick wani irin kyau fatuha tayi komai na ship din ta ya bayana duk da ba wasu shekaru gare ta ba kallo daya zaka mata Kasan ta hadu takalmi tasa tare da

Please Login or Register in order to submit comment