Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yawancin su duk barayi ne mom ya ida zancan yana tsame hannu shi daga cikin plate din abinci...." Tare da dalla wa rabi'a harara ai saiki zo ki kwashe ragowar abinci ki cinye Maya mutunci kawai ya qara jan tsoki mtssss ya dawo parlour ya zauna tare da daura Jidda a cinyar shi..." Dadday please muje shan ice cream.."Ok angel bari na dako car key sai mu fita" aje Jidda yayi saman three star sannan ya haura sama....


Sai da suka kusan cinye rabi alawar sannan suka saurara mata sai dai muce Allah ya tsare kar ayi zawo.


Sai yama likis fatuha ta waiwayi gida shima din dan zata canza kaya dan ta je gada.... Washe da baki fatuha ta qaraso gida..Inna da baba jinmai sai labari suke saman tabarma ta zo ta wuce su...baba jinmai washe da baki tace... "Fatuha yan'mata" murmushi tayi tare da shigewa uwar daka...baba jinmai ce ta qare mata kallo tsab tace "Masha Allah fatuha kyakyawa sai dai rashin jita baya bari a gani" tana da dan tsohu dai dai gwargwado ita ba gajera ba kuma baza'a kirata doguwa ba, tana da karan hanci kamar biro, bakin ta dan qararami ne pink...ba laifi tana da hips saidai yanzu ne ta Fara kirgan dangi , wannan kenan...baba jinmai ce ta numfasa tace..."Ni ko ladingo ina so inzan koma zan tafi da fatuha" dama hajiya tace na nema mata wanda zata dinga taimakama yar jikarta saboda yarin ya ce shine da na yanke shawara in jauro ya dawo daga gona sai mu tattauna kan zancan..Tap baba jinmai bana jin malam zai yadda da batun ki, saboda baya bari taje ko ina iyakar ta cikin kauyan nan, baba jinmai da malam zai yadda da haka nima da zan so hakan, ko dan fatuha ta gyaru tunda nasan birni da kauye ba daya bane dole inta je can ta natsu... Nisawa baba jinmai tayi ta ce..." Bari jauran ya dawo ni na mai magana...toh Allah yasa ya amince..


Fatuha ce ta fito washe da baki daga uwar daka, tasha jan baki a dole yau itama gada zata..tace "Inna nayi kyau ?"murmushi inna tayi ita da baba jinmai suka hada baki suka ce..." Kinyi kyau fatuha..." Qara washe baki tayi sannan ta sa kai ta fice...


Riqe da car key ya dawo men parlour tare da daukar Jidda..yace "Mom zamu fita shan ice cream may be mu biya gidan Anuty bilkisu.... OK a dawo lafiya angel amin tsaraba fa.toh grandma Sannan suka fita.


Ko da suka fi anwanke mai motar shi CRB black.... Kaitsaye wanja motar suka wuce... *ola* ya bude mashi murfin motar dana Jidda tare dayi ma Jidda wasa...sannan suka sa kai suka fita, Sosai yayi yawo da Jidda... Daga nan suka wuce gidan Anuty bilki...


Cikin jin dadi ta tarbe su inda ta cika Sadiq da kayan fruit Jidda ko sai wasan su suke ita da jamal.. washe da baki Anuty bilki tace..."Ohni baby yanzu an fara zuminci tana fadin hakan ne cikin zollaya..."harara ya wurga mata....oh you mean da bana zuminci ko tunda haka kika ce bari na tashi na tafi....,hararar wasa ita ma ta mai' tap naga yadda zaka fita daga gidan kuwa...hira suka sha sosai daga nan suka wuce family house.


Part din ammi ya fara zuwa tana zaune saman one star tana kallan film din India wanda ko za'a kashe ta bata san me suke cewa Ba, washe da baki ta juyo tace "Ah'ah yau mai gidana da kanshi? ya fatima ita da Ibrahim din?" "lafiya lau ya ce tare da zama..." Ka ce min da sarkin surutu ka zomin yanzu ta fara min wannan yaran na yahudawa. Murmushi Sadiq yayi yace."Kisha kurimin ki ammi ai koya maki take..." Ah ni ina zan iya wannan gwalangwatsin wannan sai Ku, Asiya ta kwallawa kira, cikin sauri ta qaraso tare da gaishe da sadiq... Ciki ciki ya amsa kamar me koyan magana... Yauwa yan'nan kawo wa mai gida fura dana dama dazu tana cikin fridge , toh ammi ta mike ta wuce kicin.


Haka akayi ta kawo mai fura ya sha sosai, Saboda shi Sadiq mutun ne mai san fura sai da ya sha ya koshi sannan suka wuce part din Umma,


Suna shiga part din da basma suka ci karo, sanye take da riga da wando riga mai dan gajeran hannu pink mai manya flowers tayi kyau sosai duk da yarin yace,hakan yasa sheep din ta fitowa.... Kallo daya Sadiq ya mata ya watsar Gaishe shi tayi tare da jan hannun Jidda tana mata wasa,tace "Basma ina umma?Umma na bedroom OK kira min ita, Sannan ya samu guri ya zauna.


Umma washe da baki ta fito sun dade suna hira,Inda tasa talatu ta cika mai tray da kayan motsa baki ,suna cikin hira majid ya dawo suka dasa sabuwar hira.


Sosai suke jin dadi gadar inda yau sai da su fatuha suka taka, duk da ba wani abu suka iya ba..." Sosai sun burge mutane ita da fatsima saboda cikin tsari suke rawar su kamar manyan yan'mata.....





*Taku har kullun Salma mas'ud nadabo*
*CAPTAIN SADIQ*
๐Ÿ‘ฎ๐Ÿผโ€โ™‚

*Writing by*
*Salma mas'ud nadabo*

*Edit by*
*Blood sister deeja*


๐Ÿ“˜ *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*๐Ÿ„


*๐Ÿ‘๐ŸผGodiya da jinjina๐Ÿ‘๐Ÿผ gare ku masoya na โค Ina matuqar jin dadi yadda kuke bani qwaringwiwa wajan suburbudu maku wannan novel din*๐Ÿ’ƒ๐Ÿผ๐Ÿ’ƒ๐Ÿผ

*This page is for u amal*


21_22

Basu suka dawo daga family house ba sai 9:00pm Anuty bilki ta wuce gidan ta

A gajiye likis ya dawo direct toilet ya shiga yayi wanka yana fitowa ya dau jidda ya mata wanka sai rigima take mai ....sai daya gama shirya ta tsaf ya samata night dress pink wando da riga ya raba mata gashin ta gida biyu sannan ya kwatar da ita... Oya yanzu ayi bacci.... Bana jin bacci daddy please ka bani story... Ok angel bari daddy ya shirya... Toh daddy am waiting... Sai daya shirya sannan ya qarewa dakin kallo ba laifi ta gyara dakin amma dai shi gyaran bai mai ba..... riqe da story book din jidda ya dawo saman bed lokacin har tayi bacci smile yayi tare da yi mata pack ya janyo laptop din shi ya cigaba da aiki bashi ya gama aikin ba sai 12:00 sannan ya kwata tare da janyo Jidda kamar za'a kwace mai ita



Sosai suke kallan gad'a washe da baki kasan cewar yau suka fara zuwa...tap Alqawalin Allah kallo na wuce mu... "Sosai ma inji fatsima...ke ni daga yau ban qara fashi wallahi kullun sai na zo...nima haka Qur'an haka suka sha kallan gada daga nan kuma suka fara tsokana dan wannan ya zamar masu jiki sannan suka dawo gida



Tunda safe ya tashi kasan cewar yau Monday cikin shirin shi na uniform ya ke shiryawa ba qaramin kyau yayi ba gafen da Jidda ke kwance ya kalla da alama baccin ya Mata dadi so be so ya tashe ta shiyasa beyi Mata wanka ba briefcase nashi ya dauka tare da yi Mata pack ya fitu...a parlou shi ya ci Karo da rabi'a na shara.. kallan tsana ya bita da shi har yayi gaba ya dawo... Keeee!!!cikin tsoro ta dago qara murtike fuska yayi yace... Angel na bedroom tana bacci so kibi hankali karki tashe ta kuma in tatashi ki Mata wanka kina jina..Eh" ya watsa mata harara ya ce saura na dawo naga kin min sata ya ja tsoki ya fice...


A men parlou ya ga mom zaune tana karanta azkar.. Har qasa ya gaishe ta tare da yimata pack...baby" na'am ....Jidda fa ...mom Jidda na bacci.. Ok.. So nake ma na samama Jidda school da malamin islamiyya ya rinqa Mata a gida... Ai hakan na da kyau kamar kasan magana dana ke San yimaka kenan ka rigani..smile yayi tare da wucewa dining area a tsaitsaye yayi break din ya fita ...


Tana tashi tayi wanke wanke sannan ta share gidan su qwal ba laifi yanzu fatuha anfara yin aiki shima din sai tasa kanta inna ta fito washe da baki...Ah'ah fatuha an Fara zama yan'mata....rufe fuskarta tayi ala dole kunyar inna take ji .....ohni fatuha kunya na ake ji to madalla Allah ya shirye ki.. Ameen inna tare suka shiga madafi yau dai ba laifi fatuha tayi aiki sosai dan yau ko damar zuwa gantali bata samu Ba


Baba jinmai ce cikin daki sai harhada kayan ta take cikin ganamasgo washe da baki...mom ce ta leko dakin..Ah baba sai sauri kike ki tafi.. Washe baki tayi tace.. wallahi na matsu na ganni a wudil dinan na dade banga dan uwana jauro ba..."gaskiya ko" Yauwa maganar samomin yar aiki fa dan Allah baba jinmai ki samomin natsatsa Wanda zata iya aikin nan kisan halin baby da shegiyar tsurfa... Insha Allah Zan duba maki.. Sannan mom ta ciro maqudan kudi tabawa baba jinmai tayi tsaraba tare da hadata da driver ya kaita tasha murna wajan baba jinmai ba'a magana


Ana kaita ko tasha ta samu motar zuwa wudil dama mutun daya ake jira tana shiga mota tatashi

Baffa ne tsaye bakin uwar daka..ladingo ni zan wuce yau da wuri Zan dawo karki aiko min da abinci...toh malam ..fatuha da ke zaune bisa tabarma tace...baffa zanbi ka....kinga zafi ake ga rana idan mu kaje tare wuya zaki sha fatuha.....baki ta turo gaba ta fara matsar kwalla...toh shikenan dako hijabin ki muje washe baki tayi tare da shigewa akurkin dakin ta ta dauko hijabinta suka fita


Misalin karfe 2:00pm motar su baba jinmai ta tsaya a tasha wani irin dadi ne ya lulube ta yau ta zo mahaifarta zata ga dan uwanta da iyalan shi mashin tatare kasan cewa mota bata shiga cikin garin sai dai mashin ko amalanke


Direct gidan baffa aka sauke ta tare da biyan maimashin sannan ta sauke yan kayan ta da tsaraba washe da baki ta shiga gidan tare da sallama inna dake qoqarin fitowa daga madafi chak ta tsaya...saboda tsabar murya ta rasa Ina zata tsoma kanta..Ah'ah mutan birni sannu da zuwa tare da shifida mata tabarma da debo Mata ruwa a kwano na randa mai sanyi.....ah ladingo sai hidama kike kya bari mu gaisako... Washe baki tayi ace mutun ya sha tafiya ruwan sha ya gagare" toh ya hanya.... Hanya lafiya lau" ina fatuha yan'mata nasan yanzu dai samari sun fara yi mata layi Masha Allah indai kyau ne fatuha akwai shi..."Hmm inna ce ta marairaice tace..sun fita da Malam zuwa gona maganar samari kuwa fatuha babu su" fatuhar da bata ganin kowa da gashi a kauyan nan wani uba ne zai yadda dan shi ya auri fatuha bayan ta masu rashin kunya


baffa ko koda nayi Mata magana zai fara sababi.....alalai jauro haka ya bar fatuha ta zama abinda ta zama ohni jinmai!!! bari shi jauran ya dawo ya same ni... Haka inna ta rinqa lalaba ta dan bata so tayi ma baffa magana saboda kan fatuha be jin kunyar maida magana haka baba jinmai ta gama kunfan baki


Jidda koda tatashi bata ga daddy din ta ba..da kyar ta yadda rabi'a ta Mata wanka shima sai da mom tasa baki Ana gama Mata wanka ta sauko downstair wajan mom...grandma Ina baba jinmai yau bata min wanka ba ita da dad ta Ina zancan tana matsar kwalla...sorry angel tare da goge Mata kwalla sannan ta jata jikin ta..baba jinmai ta je kauye lokacin da zata tafi kina bacci shiyasa angel... Grandma shi kuma daddy fa ya tafi ya bar little princess din shi at home...sorry angel ai zai dawo kin ji....um grandma please call him... Ok angel amma sai kinyi breakfast sannan... ok " oya muje nayi feeding naki



Alhaji ne yayi gyaran murya ya ce..um kina shan fama babanta ya maki rigima ita ma ta maki...murmushi tayi tare da shafa sumar Jidda Wanda tasha gyara.... a hanakali tayi feeding Jidda sai da suka gama tsaf sannan shima Alhaji ya wuce office


After sun gama cin abincin mom ta Kira sadiq...yana zaune saman kujerar shi ta office idanun shi a lumshe kamar meyin bacci wayar shi ta fara ruri a hankali ya bude sexy eye's ball din shi ya sauke su kan screem din wayar....sweet mom ne rubuce hannu ya Kai ya dauka ....



daga dayan bangaran ...hello baby ya kake ya aiki ...lafiya lau mom.... Dama wannan ja'ira ce ta matsamin ka tafi aiki baka tashe ta ba sai rigima take...murmushi yayi daga bangaran shi hakan sai ya qara fituwa da zala kyan shi numfasawa yayi yace mom bata wayar...ok ...Jidda dake zaune saman cinyar mom ta washe baki tare da amsar wayar...daddy.. yes angel bata fuska tayi kamar yana ganin ta"tace shine daddy ka tafi work baka tada little princess din kaba..."sorry angel lokacin kina bacci bana so na tada little princess na bacci that is why my angel ...ok daddy inka dawo zamuyi wasa ko...yes mana ...washe hakura tayi....sannan ta ce um daddy ta qara bata fuska daddy baba jinmai tatafi kauye ban dani bayan tamin promise tare zamu...sorry angel next time tare zamu kinji...."Yeeee love u dady..."Love u more angel bye sannan ya katse wayar tare da binta da kallo.


Yanzu tunda kinyi wayar da daddy naki sai ki huce ko dariya tayi ta cigaba da zuba ma mom surutu





Aiki baffa yake sosai fatuha na gefe tana taya shi tare da bashi labari in ta fadin abin dariya ya dara haka har suka gama


Cikin sallama suka shigo inna na zaune saman kujerar tayani gulma tana dama hura saboda baba jinmai nasan hura musanman damun inna..washe da baki suka qaraso fatuha ko jikin baba jinmai ta fada tana Mata oyoyo..Ah'Ah wanake gani kamar mutanan birni sannu da zuwa sannan baffa ya samu guri ya zauna ...inna ce tace...ohni fatuha yaushe zaki girma kin fada mata jiki salan ki karya ta baki ta turo gaba Kai inna har wani nauyi ke gareni tare da matse yar kwalla ..baba jinmai ko dariya abin ya ba




*Taku har kullun Salma mas'ud nadabo*
*CAPTAIN SADIQ*
๐Ÿ‘ฎ๐Ÿผโ€โ™‚

*Writing by*
*Salma mas'ud nadabo*

*Edit by*
*Raheenat*


๐Ÿ“˜ *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*๐Ÿ„
โ˜… we are the bestโ˜…

https://mobile.Facebook.com/Real-Hausa-fulani-writers-forum,-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&_tn_=H-R


*Email*:[email protected]

*Facebook*:www.Facebook. com/REALHAUSAFULANIWRITERSFORUM.com



25_26


Basu suka dawo gida ba sai bayan isha lokacin har jidda tayi bacci, dauke yake da ita har suka qaraso parlour, lokacin rabi'a tana qoqari fitowa daga kitchen' wani irin kallo ya wurga mata Jiki ba qwari ta gaishe shi har tayi gaba yace" Keeee!!" Tsayawa tayi cikin tsoro da fargaba , Harara ya qara wurga mata cikin ktsawa yace mata "Sai ki zo ki amshe ta ko?" Jiki a sabule ta amshi jidda ,Kiyi mata wanka sannan ki Samata night dress ki kawo min ita daki na dan ban yadda ta rinqa kwana da ke ba ki koya mata halin bera tsaki yaja Mtsss, sannan ya wuce part din Abba.

Abba ne zaune saman two star fuskar shi manne da glass, sanye yake da fara jalabiya blue remote ne a hannu yana kallan news, Mom na gefen sa tana yanka fruit.


Cikin sallama ya shigo tare da gaishe da abba, Cikin fara'a Abba ya amsa yace "Ah har kun dawo daga zuminci?" Eh abba, to masha Allah ina jidda ? jidda tayi bacci, OK" sun dade suna hira sama sama daga nan Sadiq ya wuce part nashi ,ko da ya shiga dakinshi ya iske ankwantar da jidda shima bathroom ya shiga ya watsa ruwa ya fito sai da ya gama shirin shi na bacci sannan ya hada coffee yana sha yana dana laptop din shi ,ya dade a haka sannan ya ture laptop din tare da janyo jidda jikin shi bacci ya dauke shi.



Bayan an gama gada kowace ta wuce gidan su, Cikin sallama fatuha ta shigo gida lokaci baffa ya dawo gida yana zaune bisa tabarma inna na kusa da shi baba jinmai na gefe su, gefan baba jinmai ta je ta dauna washe da baki itama baba jinmai murmusawa tayi sun danyi hira sama sama da fatuha daga nan bacci ya sureta.


Baba jinmai ce tayi gyaran murya tace "Dama jauro ina so muyi wata magana da kai."inna da ke kusa da baffa tayi qoqari tashi baba jinmai tace "Kema zauna"haka ko akayi inna ta samu guri ta zauna.


Dama so nake nama magana kan fatuha ina so in zan koma birni sai mu koma tare, Zaro ido baffa yayi waje yana kallan yar uwar tashi ร  zuciyarsa yace "Anya ko baba jinmai tasan me take fada kuwa?"qara murmusawa tayi ta ce jauro ina fatan ba za ka watsamin qasa ido ba a ganina fatuha nima diya tace jauro, Baffa tsale yayi ya dare ya ce be san zancan ba babu inda fatuha zata tanan kauyen nan tare da shi baze lamunci hakan ba, baba jinmai ce ta fara matsr kwalla tana cewa "Ba komai jauro dan ka ga Allah be bani haihuwa ba shine zaka wulaqanta ni kan diyar ka, jauro da Allah ya bani haihuwa da yau ba zanji zafin abinda kayi min ba, tana maganar tana ta kuka inna sai lalashin take, Ganin kukan da take yasa jikin baffa yayi sanyi dan shi a ganin babu abinda baba jinmai zata nema a rayuwar shi ya hana ta.

Bayan da ya iya haka ya hakura ya amince tatafi da fatuha, aiko washe da baki tamai godiya tare da yimai alqawarin zata riqe amanar fatuha sosai daga nan kowa ya wuce dakin shin.



Ko da ya tashi ya gama shirin shi ciki uniform masha Allah yayi kyau sosai, Ze dau briefcase din shi shikenan jidda ta tashi washe da baki tace "Daddy morning" morning too angel , hum yau ma daddy guduwa zakayi ka bar little princess din ka a gida? langwabe kai yayi ya ce "Sorry angel daddy work ze je kinji kuma yara basa zuwa kema very soon zaki fara zuwa school ai kinaso ko angel" washe baki tayi tace "Yes daddy zan fara zuwa school kamar yadda su yaya hannan ke zuwa da Anuty basma ko?" Eh mana angel' tsale tayi ta kai mai hug thanks my daddy ,smile yayi tare da yimata pack please angel ki tsaya rabi'a ta maki wanka kin ji? naji grandma na cewa kullun se kin rigima, Bata fuska tayi tace
"Daddy..." shhhh tare da yi mata pack ร  kumatu ya fice.


A dining area ya hadu da abba shima yana breakfast, mom na gefen shi ahankali ya qarasa yayi masu pack sannan ya samu waje ya zauna ya fara breakfast lafiyayan chips ne da plantain and egg sai tea mai kauri Wanda ya sha ovaltine, cikin natsuwa suka gama break din su abba da Sadiq tare suka fito inda yaran Sadiq ke ta kwasar gaisuwa wajan abba tare da qamema Sadiq din cikin natsuwa moto cinsu suka fita daga harabar gidan.


Ko da fatuha ta tashi wanke wanke tayi, sannan ta dau tulun ta gidan su fatsima ta biya tare suka fito suna tafe suna hirar su, kandala suka hango dauke da tray gyadar ta qarasowa su kayi wajan ta, Kallan su take jiki ba kwari Harara suka wurga mata tarรฉ da cewa "Bamu gyada ta murtala jikinta baqwari ta fara zuba masu gyadar tasan ko zata mutu baza su bata kudin gyadar ba, kuma ta matsa masu su tona mata asiri " sai da ta gama zuba masu sannan fatuha ta amsa tace "Cikin Murtala da dan mai gari ya mana alqawari ne muka amshi gyadar, Sannan kice mai ko ya bamu murtalar mu ko kuma murtala ta rinqa haihuwa sannan suka wuce suka barta tsaye tana matsar kwalla.


Suna isa rafi suka aje tulu na su gefen rafi suka wuce gonar mai gari suka fara tsinkar mangwaro da gwaba sai da suka diba san ransu sannan suka zo zasu fita mai gadi ya kama su, kai kai uban wa ya baku ikwan shigowa gonar mai gari? har ku tsinke mai mangwaro, Fatuha ce ta turo baki gaba tace bala ne ya bani izinin shigowa ,shegiya mai kama da mayu, shi bala din sa'an kine inama kika san bala din?harara fatsima ta wurga mai in baka yadda ba sai ka kai mu wajan shi ka ji da kunnan ka ta ida zancan tana gyara Daurin zaninta.


Aiko haka akayi mai gadi jan su fatuha yayi har gaban bala, sai yan' harare harare suke su daya ,kaisu yayi suma bala ba yani sai ya ce shi ya ce su dinba dan yasan in bai ce ba tuna mai asari zasuyi, sannan yasa mai gadi ya sake su wani irin dadi suka ji suna ta shewa suka isa rafi suka debo ruwa.


Bai zame ko ina ba sai *Yandutse college* dan samoma jidda admission be sha wani wahalla ba ya samama ta inda duk angama abinda za'ayi, ranar Monday sai ta fara zuwa school sannan ya wuce office, a cewar shi inya dawo gida da yama zai samamata malamin adini.


Kwanci tashi asarar mai rai yau sati baba jinmai daya a wudil inda take ta hada kayanta dana fatuha, Fatuha sai kuka take har da majina dan ita a ganin baba jinmai bata mata adalci ba ita tace mata tana san birni da zata kwashe ta su tafi toh Wallahi sai nayi rashin mutunci idan munje sunje kenan, baba jinmai ce ta juyo haba fatuha sai ka ce za'a cinye ki sai kuka kike haba fatuha kinsan muna tare kuma zan kula da ke kamar yadda inna zata kula da ke, fatuha dan Allah kiyi shuru kinji, Inna da ke gefe duk da tana jin wani irin amma tasan baba jinmai ba zata tayi abinda zai cutar da fatuha ba amma ko yaya tana jin zafin rabuwa da fatuha saboda fatuha yarinya ce mai shiga rai, a hankali inna ke lalashi fatuha har tayi shuru haka shima baffa da ke gefe haka baba jinmai ta gama hada kayan fatuha cikin yar leda gari yayi zafi ta miqa mata ta rungume.


Baffa kuma yaje taro masu mashin, Sallama fatsima tayi ta shigo falon kallo daya zaka mata kasan itama ta ci kuka har ta gaji, wani saban kuka suka dasa ita da fatsima da kyar aka lalashe su sannan baffa ya shigo ya sheda masu gamai mashi din.


Suna kallan su har suka bile baffa ya goge yar kwallar shi dan shi ka dai yasan yadda yake ji, suna isa tasha suka samu motar Kano basu wani dade ba motar ta tashi.



Idanuwan shi lumshe kamar wanda ke bacci, zaune yake saman resting chair yayi crossing leg's nashi Taba shin da akayi ne ya sasa ware sexy eye's ball's din shi ba kowa bane sai majid murmushi yayi yace "Yaushe ka zo ban sani ba?" yanzu na shigo mom ta ce min kana nan sannan ya zauna daya daga cikin chairs din ,OK ya aiki? Alhamdulliha soma nake na dawo nan da aiki, kai Allah ya taimake ka har yau basu ma transfer din ba? Aiko dai ai bana fatan hakan wallahi murmushi sukayi su duka suka cigaba da magana ร  matsayin su na abokai kuma yan'uwa.




*Tah ku har kullun

Please Login or Register in order to submit comment