Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

din a parlour fatuha ta aje jidda tana qoqari fita
"keee.. Yace da Ita.
Nan taja birki ta tsaye zuciyar ta na duka uku uku dan bata manta rashin kunyar da ta mai ba da safe ,"ba dake nake magana. ya fadi cikin daka tsawa. juyowa tayi tana zare ido , "kije kitchen ki hada min coffee ki kawo min.. zaro ido fatuha tayi waje um kwarankwatsi ban san me hakan ba. tsoki yaja mtss "yar kauyan banza toh burni nake nufi tea mara madara zaki hadu ki kawo min karki sa sugar a ciki.. ya ida zancan tare da balla mata harara abin ma dariya ya so ya ba fatuha wani lokaci sadiq in yana harara kamar qaramin yaro a zuciyar ta tace bema san idan yana fada wani qara kyau yakeba
ta dan ja tsaki ta fita.. saida ta gama hada mai ta kai mai yana zaune parlour yadda ta barshi jidda na saman cinyar shi da alama bacci ya dauke ta hannu ya miqa ze amshi coffee tana bashi ya saki cup din ya fadi gaba daya ruwan tea din ya zube mata a kafa wani irin ihu fatuha ta bude baki zatayi janyo ta yayi tare da to she mata baki yana kallan ta ido cikin ido idanuwanan tana sun ciko da kwalla hawaye daya nabin daya..
murmushi yayi komin banza ya sata kuka gashi matsar da yayi ma bakin bana wasa bane dan bakin sai radadi yake mata sai da tayi kuka san raita sannan ya sake ta tare da hankada ta ta fadi kasa sannan ya tashi ya kashe kayan kallo ya matso gaf da ita har tana jin saukar numfashinshi yace cikin cool voice na shi "wannan ka dan na maki akwai saura nan tafe.. ya ja saki tare da daukar jidda sai da ya kai bakin kofar bedroom ya juyo tare da yin killing smile din shi yacigaba da cewa. "kuma ki tabata kin gyara gurin kafin ki bar wajen.. Yana fad'in hakan ya shige bedroom ya barta tana matsar kwalla tare da jera mai Allah ya isa, kuma indai gyara gurine wallahi banyi mugu kawai sannan taja kafar ta wadda ta kone wajan har yayi ja bakin tama haka saboda ya ji matsar manya


Direct bedroom dinta ta wuce tare da rage kayan jikinta
bathroom ta shige tayi wanka ta fito daure da towel tana shafa mai tana jera wda cigaba da jera mishi Allah ya isan
A haka har ta gama shirin tafada saman bed se bacci



*Fan's kuyi hakuri da wannan page din yau bana jinyin typing din saboda ina wani dan aiki*


*taku har kullun mai qaunar ku Salma mas'ud nadabo*
*CAPTAIN SADIQ*
๐Ÿ‘ฎ๐Ÿผโ€โ™‚

*Writing by*
*Salma mas'ud nadabo*


*Edit by*
*Raheenat*


๐Ÿ“˜ *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*๐Ÿ„
โ˜…we are the bestโ˜…


http//mobile.Facebook.com/Real-Hausa-fulani-writers-forum RHFWF-173984973194167/?refid=52&red=opare_speed_dial_&_yn_=H-R


*Email*:[email protected]


*Facebook*:www.Facebook.com/REALHAUSAFULANI WRITERSFORUM.com



41_42

Kiran sallah asuba ne ya tada fatuha, arwala ta dauro tare da yin wanka bayan ta idar da sallah ta shafe jikin ta da mai kamar kullun tare da fesa turare uniform ta zure sannan ta daure gashin kanta Wanda da kyar ta kama shi, ganin be kamuwa yasa ta sake shi haka kawai ta fita direct part din sadiq ta shiga tana karema parlour din kallo ,har yanzu glass din jiya nan zube a parlour baki ta tabe ta shige bedroom sadiq na kwance jidda na maqale a jkin shi da alama daga masallaci ya dawo bacci ya kwashe shi dan jalabiya ce a jikin shi ba night dress ba sajan nan nashi yayi lufluf kwance, qare mai kallo fatuha tayi sannan ta bala mai harara kamar idanuwan shi biyu a hankali ta sa hannu ta fara janye jidda daga jikin shi janyo jidda ya qara yi ya maqale ta, abin ma dariya ya ba fatuha qara jan jidda tayi shima ya qara jan jidda haka suka riqa ja inja qara leqa fuskar shi tayi taga dai bacci yake a hankali ta qara miqa hannu zata janye jidda cikin dubara ta janye jidda direct bathroom ta dire ta, kamar kullun ta shirya jidda murmushi tayi washe da baki tace Anuty I like u murmushi fatuha tayi tare da langwabe kai ta shafa kan jidda tare da cewa jidda kisan ban iya wannan yaran ba, murmushi jidda tayi ina nufi kina birge ni Anuty murmushi fatuha tayi wadda ya baya kyawawan hakuran ta tace nima haka Jidda pack jidda tayi mata itama fatuha pack tama jidda.

Janyo hannun jidda tayi cikin ni shadi suka qaraso dining area tea ta shiga hada ma jidda mai kauri, Wanda yaji ovaltine da madara tare bread n egg a hankali ta Shiga feeding din jidda tana amsa itama in taji dadi se ta gutsuro bread din taba fatuha, mom da abba ne suka qaraso cikin fara'a dining area cikin ladabi fatuha ta gaishe su ,cikin farinciki suka hada masu breakfast, washe da baki mom ta amsa jidda ce ta washe baki tare da cewa morning grandma n grandpa morning too angel suka amsa a tare bayan jidda ta gama hada masu ta aje masu cikin ni shadi suke breakfast.

Tsaye yake gaban dress mirror sanye da bathrobe hannu shi riqe da qaramin towel yana goge sumar kanshi da alama daga wanka ya fitu cikin tsuwa ya yake shirin lotion ya shafa tare da saka uniform din shi sannan ya feshe jikin da turaruka masu kamshi booth din shi ya curo ya saka black se sheqi yake tsaf ya fito sojan shi hula shi ya dauko ya sa sai agogwan shi silver na zurfa wani irin kyau yayi ba dan kadan ba sai dai fuskar nan daure briefcase din shi ya dauko tare da daukar wayar shi da ke bedside drowe a hankali ya bude kofar bedroom kallo daya yayi ma parlour tare da jan dogwan tsaki fatuha kin rainani wallahi sannan yasa qafa ya fitu daga part din a hankali yake saukowa daga upstairs tuni kamshi turaran shi ya mamaye parlour fatuha da ke feeding din jidda ta dago idanuwan tana qaremai kallo cikin isa ya qaraso wayar shi ya cure ya kara a kunne cikin natsuwa yake wayar , holle ole daga bangaran ola yace hello boss, ka zo ka amshi briefcase din , to ya ce mai tare da kashe wayar ya qaraso dinning area smile yayi tare da gaishe da su mom jidda washe da baki ta gaishe haka fatuha banza yayi da ita kamar be ji tare da qare mata kallo yau kuma wani saban iskanci yima mutane yawo a gida ba dankwalli duk yana yin maganar a cikin zuciyar shi a hankali ta janyo cup da niyar hada mai breakfast hannu ta ya rike ya wurga mata wani irin kallo ya aje hannu tare janye cup din mom ce ta aika mai harara sai yayi kamar be gani ya cigaba da aikin da ya ke ole ne ya shigo cikin sallama suka amsa sannan ya amshe briefcase din sadiq ya fice da ita abba ne ya katse shurun da cewa, ah ka ce min qafa ta warke murmushi sadiq yayi tare da cewa eh abba toh masha Allah , abba ya maganar kwangilar kunko samu a'a munan dai muna fama amma insha Allah this time around zamu samu abinda muke so murmushi sadiq yayi tare da cewa Allah yasa mom ta amsa da ameen tashi yayi tsaye tare da cewa oya angel mu fati , ah baby karka ce min ruwa tea din har ya isheka ba bread ba komai eh mom na koshi toh shikenan, hannu jidda ya kama har sun kai baki ko abba yace yawa baby ina san fadama ranar Sunday tare da mom din ku zamu tafi uk , OK sadiq ya ce tare da sa kai ya fita fatuha na biye da su da lunch box din jidda har gaban mota sannan ta miqa wa jidda lunch box din tare yi mata pack sadiq kallan su yayi tare da tabe baki sannan ya shige mota.


A hankali ta juyo ta shige gida, kwashe kayan breakfast din tayi mom na zaune a parlour tana kallo fatuha ta zo ta wuce kitchen washe da baki ta gaida baba jinmai itama baba jinmai washe da baki ta amsa ,rabi'a na gefe tana gyara kayan miya tayata fatuha ta Shiga yi suka gyara tare sosai ta taya su baba jinmai aiki a kitchen saboda aiki na burge ta kusan tare da ita aka dafa lunch baba jinmai ko dadi take ji har qosawa take suje kauye jauro yaga yadda fatuha ta koma kamar balarabiya, bayan sun gama aikin fatuha ta wanke duk wani kwano da akayi anfani da shi rabi'a ko sai hanata take amma taqi bari sai da suka gama komai sannan fatuha ta dawo parlour, ko da ta dawo mom ta bar parlour bedroom ta shige tare da rage kayan jikin ta bathroom ta shige ta watsa ruwa daure da tawel tafito bayan ta gama komai sannan ta tuna ashe bata gyara part din sangamin ba, ko mai bata shafa ba ta zura kayan ta direct part din sadiq taje ta fara gyara sai da ta gyara shi tas sannan ta zauna a parlour saman three star tana maida numfashi lumshe idanunta tayi tare da ware su, fita tayi daga part din ta koma bedroom ta kuma watsa ruwa sannan ta shefe jikita da mai tare da fesa turare da maida uniform din ta.



Misalin karfe 2:00pm su jidda suka dawo ,kasan cewa yau sadiq be da wani aiki tare suka dawo part din shi ya nufa masha Allah gyaran part din ya mai yana jin dadi ganin part din shi a gyare, duk rashin jin fatuha tasan aikin ta shiyasa wata rana yake daga mata kafa bathroom ya shige ya watsa ruwa ya fito cikin wando da riga ya shirya, kayan sun mai kyau sosai. bangaran su fatuha kuwa jidda na dawowa yadda ta saba yi mata haka ta mata sannan tace taje parlour ko da ta fito parlour daddyn ta gani jikin shi ta fada tana zuba mai surutu shikuma yana saurareta yana jin dadi, mom da abba ne ke saukowa daga upstairs abba sanye da shada malinmalin brown mom na sanye da atanfa pink mai ratsin greed n bleu sanye da mayafinta ba qaramin kyau sukayi ba, parlour suka qaraso washe da baki jidda ta sauka daga jikin sadiq ta riqe hannun grandpa murmushi abba yayi yace "Sadiq yau da wuri ka d'awo daga wajen aiki kenan?" smile yayi tare da cewa eh to mu zamu wuce gidan ammi mu masu sallama to Allah ya tsare ameen jidda ce tace grandpa zan biku toh shikenan yima fatuha magana inji mom sai muje tare ko, rugawa tayi bedroom fatuha kuwa tunda jidda ta fita wani irin bacci ne ya sure ta ko da jidda ta shigo taga fatuha na bacci veil din ta ta dauka tare da fita ,grandma Anuty bacci ta take toh shikenan tunda bacci take mu tafi kawai ta samu hutu ne washe da baki jidda ta bi su abba, sadiq ya rako su har parking space sannan ya koma gida ko da ya koma wani irin killing smile yayi upstairs ya haura sannan ya fito kitchen ya shiga ya dauko ruwa a fridge me sanyi Wanda har qanqara ya fara saboda tsabar sanyi a hankali ya murda handle din dakin fatuha ya shiga hangota yayi saman bed tana sharar bacci gashin ta ya baje saman gadon, cije lips yayi sannan ya qaraso sai da yazo dai dai face din ta ya bude murfin rubar ruwan ya juye mata shi, fatuha da ke bacci wani irin razana tayi ta tashi cikin gigice wa ta yunkura zata fita saboda tsoro, sadiq ya janyo gashin ta tare da dauke ta da lafiyeyan mari ,wani irin kuka fatuha ta saki tare da zama saman bed jajayan eye's din ta ta dago tana kalla sadiq wani irin murmushi yayi yace "Fatuha yau zan koya maki hankali, bani kika so ki nakasa ba ? toni yau kona maki gashi zanyi ya ida zancan tare ya matse mata fuskarta, idanuwan fatuha sunyi jawur sai kuka take tana bama sadiq hakuri ashana ya Ciro a aljihun shi ya kunna tare da fusgo gashin ta wani irin kuka fatuha tasa dan Allah me kyau kayi hakuri wallahi bazan sake ba ta ida zancan tana qara rushewa da saban kuka, shhhh yimin shiru fitsarariyar banza nufo gashin ta yayi da wutar take fatuha ta fashe da wani sabon kukan tare da tafiya luuuu ta sume, murmushi sadiq yayi ganin suma tayi marar kunyar qarya kitchen ya koma ya dauko wani saban ruwan sanyi ya dawo bedroom ya qara juye mata shi wata irin ajiyar zuciya ta saki tare da fashe wa da kuka tana bama sadiq hakuri, cije lips yayi na qare mata kallo yarin ya ce sosai amma sai rashin kunya duk ร  zuci yake wanga zancan , bindiga ya ciro ya daura mata akai tuni fatuha ta saki fitsari ta sauke numfashi agwagwame cikin sarkewar murya tace dan Allah me kyau kayi hakuri bazan sake ba, tsaki yaja tare da cewa fitsari ma kikayi ko? a'a wallahi ruwa ne haka wallahi, murmushi yayi dan yasan qarya take sannan yace daga yau se yau kika qara min rashin kunya sai na b'ula maki kai da wannan abar , girgiza kai tayi alamar baza ta sake ba, sannan ya hankada ta kanta ya bigi gado ta qara sakin wani saban kukan sannan sadiq ya sa kai ya fita.





*Taku har kullun Salma mas'ud nadabo*
*CAPTAIN SADIQ*
๐Ÿ‘ฎ๐Ÿผโ€โ™‚

*Writing by*
*Salma mas'ud nadabo*

*Edit by*
*Raheenat*

๐Ÿ“˜ *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*๐Ÿ„
โ˜…we are the bestโ˜…


http//mobile.Facebook.com/Real-Hausa-fulani-writers-forum RHFWF-173984973194167/?refid=52&red=opare_speed_dial_dial_&_yn=H-R


*Email*:[email protected]


*Facebook*:www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERSFORUM.com



43_45

Sai da fatuha ta ci kuka sosai tare da jerawa sadiq Allah ya isa, sannan ta tashi jiki ba qwari ta nade zanin bed din Allah ya taimake ta katifar akwai leda dan haka ruwan da fitsarin be shige cikin katifar ba iya karshi saman bedsheet tatare shi tayi ta aje ta shiga toilet ta watsa ruwa, tana gamawa ta fito ta dauki bedsheet din ta wanke shi tas sannan ta fito da bokitin ta aje agefe sai da ta shirya tsaf sannan ta dau bokitin ta fita ko da tafi dasu ola taci karo da Sunday yaran sadiq suna ta shawagi a tsakar farfajiyar gidan, kai tsaye wajan shanya ta nufa ta shayan bedsheet din sannan ta dawo ta zauna saman wata resting chair da ke a farfajiyar gidan lumshe ido tayi tana jin wani tsoro sadiq na ratsa ta, wasu hawaye masu zafi na zubo mata, dan yau ba qaramar wahala tasha a hannun shi ba take nan wani zazabi mai zafi ya lulube ta sakamakon ruwan sanyin da sadiq ya sheqa mata, ganin masasarar taci qarfin ta yasa ta ja jiki ta koma parlour saman three star ta zauna ta qudindine waje daya tana kyarma abin gwanin ban tausayi๐Ÿ˜ฐ.


Bangaran sadiq ko zuciyar shi fes bathroom ma ya shige ya sheqa wanka bai jima sosai ya fito daure da tawel da Dan karami yana sane gashin kansa, gaban dress mirror ya tsaya yana gyara kanshi da ya tuno da yanda fatuha tayi se ya saki murmushi jin dadi bayan ya gama shiryawa cikin 3quarte da armless t-shirt din shi cikin shirin shi na zuwa gym , sannan ya feshe jikin da turare masu sanyi kamshi a hankali ya bude handle din kofar tare da barin part din cikin isa yake sakowa daga upstairs fatuha ya hango saman three star qudindine kauda kansa yayi yana qoqarin fita har yayi gaba sai kuma ya dawo saboda barin da yaga jikinta nayi yasa yaji tausayinta kadan azuciyarsa, a hankali ya qaraso gaban three star din ya leqa fuskar ta Wanda tayi jawur ga shatin hannu shi kwace a fuskar ta lumshe ido yayi tare da waresu a kanta a hankali ya kai hannu ya taba goshin ta ji yayi goshi zafi rau kamar wuta, a hankali fatuha ta ware idanuwan ta ta fara rera mai kuka a tunanin ta wani muguntar ya zo yi mata, daurewa yayi tare da cewa yima muta ne shuru kafi na kife ki da wani sabon Marin tsuru tsuru tayi tana kallan shi ga wani irin zazabi da take ji ,lumshe ido tayi ta juya mai baya wayar shi ya ciro dake aljihunshi bugu daya biyu Dr yakub ya dauka sannan ya sheda mai yana buqatar ganin shi , OK ya ce mai tare qatse wayar sannan ya kalli inda fatuha take kwance hata gashin kanta jiqe yake a hankali ya kai hannu ya dauki fatuha ita ko sai matsar kwalla take tana bashi hakuri banza yayi da ita be dire ta ko ina sai bedroom din ta, saman bed ya direta sannan ya dau ko hand dryer daya ke anfani da ita ya busar mata da kan ta fatuha ko sai bin shi take da ido AC din ya rage ma gudu tare da rufe ta da blanket ya koma gefe ya zauna fatuha ko lumshe indo tayi kamar me bacci.


Ba'a fi 50 minutes ba sai ga Dr yakub sadiq ne ya mai iso har bedroom dinta, dudubata yayi sannan ya fito da alura da magunguna ya aje a gefe sai da ya gama zuko alura sannan yayi ma fatuha magana, hajiya ki juya zan maki alura ko dan fever ta sauka ,waro ido fatuha tayi ta fara kuka dan Allah kayi hakuri wallahi bana san alura kuka take sosai sadiq ta shiga ba hakuri, banza yayi da ita kamar bai jinta, ohni fatuha yau na shiga 3 ban taba tunanin muguntar me kyau ta kai haka ba duk wannan zancan tana yin shine a zuciyar ta ,Dr ne ya katse shurun da cewa please ki tsaya na maki alura kin ji ba zafi ba kuma ko dan ki samu sauki masasarar da kike yi kinji ,Dr ya ida zancan yana smile wallahi bana san alura dan Allah kayi hakuri ka kyale ni Dr yakub ne ya juyo ya kalli sadiq dake ta latsa wayar shi kamar ba mutun a wajan ka ji mara lafiyar ka bata san alura kuma irin wannan fever se da alura yake sauka ,dago sexy eye's ball's din shi yayi yana qarewa bed din kallo da fatuha take kwance saman bed din cikin isa ya qaraso yace fatuha shuri tayi kamar bata ji shi sarai yasan tana jinshi ,wani saban rainin ne haka ji yayi dama be kira Dr din ba ya barta ciwo ya kashe ta inya tashi daf da ita ya zo ya zauna tare janyo ta kuka tasa tana cewa ni ka kyale ni bana so banza yayi da ita ya riqe ta gam Dr ya zunkuda mata alura wani irin kuka ta saki tare da rungume sadiq gam tana kuka se da tayi kuka san ran ta sannan ta fara sauke a jiyar zuciya dan guntun tsaki sadiq ya ja tare da zame ta daga jikin shi fatuha ko yana zame ta ta koma ta kwanta saman bed tana sauke ajiyar zuciya, sannu Dr yakub ya mata sannan ya dau briefcase din shi tare da yima sadiq bayanin yadda zata sha maganin Godiya ya mashi sannan ya rako shi har bakin kofa yashiga motarsa ya tafi. shi kuma ya koma bedroom din fatuha ja mata blanket din yayi sannan ya fita ita kuma bacci ya sure ta.


Bangaran su mom ko sun isa family house lafiya,d irect part din ammi suka fara shiga cikin fara'a ta tarbe su da jin dadi asiya mai aiki ta kira ta kawo masu fura mai sanyi da kayan motsa baki, aiko sakin jiki sukayi suka sha dan ammi ba irin iyayan mijin nan ba ce me takurawa surukanta daukar su take kamar ya'ya ta Jidda ta janyo tana mata wasa ,yan'mata baba ina baban naki kwana biyu shuru murmushi jidda tayi tace "Daddy nanan lafiya lau "to madala kwana ki nake ji majid na cewa sadiq be ji dadi ba mom ce ta ce wallahi ko faduwa yayi a toilet Allah sarki ai abun ya zo da sauki, masha Allah ai yanzu ya warware sosai da tare zamu zo ma Eyya sun sha hira sosai da ammi daga nan suka wuce part din Umma lokaci baba be dade da dawowa daga kasuwa ba, baba jan abba yayi suka shige part nashi suka dasa sabuwar hira abin ka da yan'uwa haka Umma da mom suka bude saban shafi na hira basma ce ta fito sanye da gown ta zo har parlour ta gaida mom ,tare da kawo masu kayan motsa baki sannan ta ja jidda bedroom din tana mata wasa tare da tanbayar ina daddy washe da baki jidda tace yanan lafiya lau ok good ,idan kun koma gida ki ce mai anuty basma na gaisheshi to jidda tace mata, chocolate ta dauko a bedside drowe taba jidda sannan ta cigaba da assignment din ta da datake yi sun dade sosai dan kusan a can su kayi dinner sai kusan 9:00pm sannan suka fito, se da abba ya qara leqawa part din ammi ya gaishe da alhaji sannan suka fito har bakin mota Umma da baba da basma suka rako su sannan suka juya cikin gida.


Fatuha kuwa sadiq na lulube ta bacci ya kwashe ta ,ba ita ta tashi ba sai da ake Kiran sallar isha'i ko da ta tashi zazabin ya sauka sai dai jikin ta ba qwari, a hankali ta yaye blanket din jikinta ta shige toilet arwala ta dauro bayan ta gabatar da sallah ta koma saman bed ta kwanta, sadiq bashi ya fito daga gym ba sai magrib wanka yayi ya tafi masallaci bashi ya dawo ba sai bayan sallah isha'i ko da ya shigo gida yaji ba motsin kowa hakan tabatar mai da su mom basu dawo ba, bedroom din fatuha ya leqa kwance ya hango ta jin shigowar shi yasa fatuha qara yin lamo haskyan dakin ya kunna tuni dakin ya gwaraye da haske ,a hankali ya qaraso ya leqa fuskar ta tare da cewa fatuha banza tayi kamar me bacci tsaki ya ja yace "Nasan kina jina ko? ki tashi ki sha magani kona qarasa ki da bindiga, tunda dai mutuwar kike so" tuni fatuha ta tashi zaune tana zarar ido maganin ya shiga bale mata ya bata sai da ta sha sannan ya miqa mata fresh milk tace ta koshi wani irin kallo ya wurga mata ba arziqi ta kafa kai ta sanye, sannan ya fita daga daki yana fita ta ce ah ashe su sangami ana da kirki har da hada ni da madara mai dadi sannan ta ja dan guntun tsaki ta koma ta kwanta.


Bayan ya fito daga dakin fatuha parlour ya dawo ya zauna tare da lumshe idanuwan shi kamar me bacci cikin sallama su mom suka shigo wani irin smile yayi tare da tashi zaune, ya qaraso wajan su jidda ce ta rungume shi tana cewa daddy I miss u miss u more angel kin tafi kin bar daddy shi ka dai a gida, turo baki tayi tace "Daddy Anuty nan bata taya Kuyi hira ko? ta ida zancan ta bata fuska" eyya angel Anuty ba lafiya fever take, mom da zaman ta kenan saman three star tace me ya sameta sadiq yace mom fever take dazu na ganta a parlour zaune

Please Login or Register in order to submit comment