Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bakin ta ba suka shigo da gudu angel ta fada jikin daddy murmushi Sadiq ya saki daddy I miss u miss u more angel kissing di kumatunta yayi itama tayi mai hanan cikin fara'a ta nufi fatuha basma kuma na gefe tsaye tana satar kallan sadiq kasancewa ta zo Hutu gidan Anuty bilki, gaishe da sadiq sukayi ya amsa a takaice sannan hanan taja fatuha suka wuce dakin ta angel kuma na maqale da daddy

Suna shiga d'akin hanan basma ta cire mayafin kanta ta fada saman bed, itama hanan bed ta hau fatuha kuma ta zauna saman sofa, laa fatuha baki zama saman bed a'a bari a nan ma yayi wallahi basma kinga wadda nake fada maki mai gashin nan d'ago kai tayi ta kalli fatuha ta dan yi smile sannu ki fa yauwa inji fatuha hira suka shiga zubawa kasan Cewar duk sa'anin junane amma dai basma ta dan girme su dan yanzu ita SS2 zata hanan kuma SS1 kunsan a tare suke komai da hanan da basma duk da basma Anuty ce a wajan hanan sosai fatuha ta saki jikin ta amma sai dai tana dan dari dari da basma , kiran sallah magrib ne ya tashe su d'aga fira alwala suka dauro suka gabatar da sallah bayan sun idar angel ta shigo da gudu d'akin tace "Anuty fatuha daddy yace ki fito mu tafi?" to tace tare da yafa mayafin ta a tare suka fito d'asu hanan parlour a tsaye suka tada sadiq Anuty bilki ce ta bata rai tace haba baby kabari kuyi dinner mana sai ku tafi a'a gaskiya yau girkin baba jinmai zanci I miss her food ohni ba kayi missing din nawa ba ko ba haka bane sis so kike muyi barnan na gida ko toh shikenan a gaida gida dan ko rakiyar banyi langwabe kai sadiq yayi pls kar muyi haka mana harara wasa ta kaima sannan ta ja veil din ta dake saman kujera suka fito a tare hira suke sosai kamar karsu bari , bude murfin mota sadiq yayi angel ta shige gaba fatuha na b'aya sannan ya ja motar be zame dasu ko ina ba sai shop right shiga su kayi yayi masu siyaya sosai ice cream teddy's duk ya kwaso kayan wasa kamar be jin kudin ya cika boot da su sannan suka juyo gidan a gajiye likis.

Yana horn bala mai gadi ya bude mai geta yayi parking sannan yayi masu ola nuni da su kwaso kayan boot lokaci ma jidda tayi bacci, fatuha ce ta dauko ta suka shige gida upstairs sadiq ya haye fatuha ta shige bedroom kaya kawai ta cire ma jidda tasa mata na bacci, tana qoqarin cire nata akayi knocking din kofar zura hijabi tayi ta bude ola ne riqe da trolley din jidda da k'ayan wasan ta duk ya aje sannan ya mata sai da safe rufe kofar tayi ta rage kayan jikin ta ta wuce toilet tayi wanka ta fito daure da towel tsane jikin ta ta yi ta shafa mai sannan tasa rigar baccin ta gown dai dai gwiya white n brown mai zanan cartoons sannan ta saki gashin kanta tare da daukar jidda part din sadiq ta wuce da ita a parlour ta same shi yana k'allan news ,sanye da k'ayan baccin shi maroon riga da wando mai dogwan hannu bedroom ta shige ta shinfidar da jidda sannan ta fito har yadda ta barshi a parlour har yanzu haka yake qoqarin fita take yace fatuha ki kawo min dinner nan to ta ce mai sannan ta fita.

Direct dining area ta wuce ta zubo mai tuwan shinkafa miryar taushe tasha naman rago sai kamshi ke tashi ,sannan ta wuce part nashi saman stool ta aje mai plate din zata fice riqo hannu ta Sadiq yayi tare da cewa "Fatuha, waya bata makin rai tunda muka dawo naga baki farin ciki? ko bros ya maki laifine?" laa Allah ba abinda kamin kawai na gajine yau munsha hira da su hanan toh naji amma ai ba kiyi dinner ba bana jin yunwa ice cream din dana sha ya cika min ciki wallahi ok tunda hakane na fasa kai ki school din zaro ido waje fatuha tayi dan Allah kayi hakuri Allah zanci tam oya zo zauna muci zame hannu ta tayi daga ruqwan da sadiq ya mata ta zauna a qasa tare da janyo plate din gaban ta shima sadiq din zama qasa yayi cikin natsuwa ta fara kai loma daya sannan ta debo ta kaima sadiq amsa yayi wata lomar ta debo ta kai mai baki hadawa yayi da yatsanta ya ciza yar qarasa ta saki tana yar fe hannu ta dariya sadiq ya saki ,kuka ta fara mai tana kaimai bugun wasa riqe hannu yayi yana dariya ya rungume ta sorry sis yana magana yana shafa bayan ta lamo tayi a fadandan qirjin sa tana maida numfashi dago da fuskar ta yayi yace sis yau baki surutu kamar ankule maki baki gashi kin bata min night dress da miya gaskiya ba zan yadda ba ya fadi a dan shagwabe, kallan shi fatuha tayi ta lumshe ido tare da cewa yi hakuri mai kyau bazan sake ba good girl to fada min Fushin nan name to um um dama ina so naje kauye ne kwana biyu wajan inna kafin na fara zuwa makaranta wannan shine damuwar eh ok karki damu insha Allah zan kai ki zame jikin ta fatuha tayi daga na sadiq riqe habar ta Sadiq yayi yace fatuha ki dauke ni kamar yayan ki duk abinda ke damun ki ki fada Mani na maki alqawarin samamaki farin ciki kamar yadda kika samamin fatuha murmushi ta saki wanda ya bayana fararan hakuran ta daukar plate din abinci tayi zata fita sadiq ya rako ta har kitchen ta aje plate din ta wanke hannu ta.


sai da ta zo b'akin kofar Shiga bedroom sadiq ya mata pack a goshi itama ta mashi a kumatu sannan ta shige bedroom shima ya haura upstairs.


B'ayan kwana biyu h'aka rayuwa ta cigaba da tafiya inda sadiq ke b'awa fatuha da jidda kulawa sosai haka suma suna faran tamai rai duk wanda yaga sadiq a yanzu yasan b'aya fama da wata matsala ,sai wani kyau da yake ta qarawa bangaran karatun adini kuwa fatuha tayi nisa sosai tana mai da hankali yadda ya kamata kuma a yanzu duk duniya bata da aboki ko qawa sama da captain shine uwar ta shine uban b'ata bari yayi fushi da ita ko kadan baba jinmai ko duk yadda ta bigi cikin fatuha ta fada mata wani abu na daban sai ta gane abinda take tunanin ba haka bane zala shaquwace kawai tsakin sadiq da fatuha.


Dr yakub yafi kowa farinciki da canji irin na sadiq har mamaki yake da hamdala da sadiq yaji shawarar shi.

Kwana biyu ko d'aya je wajan ammi ma taji d'adi ganin canjin shi h'aka majid da kwana shi biyu da dawowa d'aga Lego's anmai transfer ya d'awo kano da aikin sosai sadiq yaji d'adi hak'a ko ba komai dan uwan shi ya d'awo kusa da shi.


Kasancewa yau ta k'ama friday shiye shiye ake sosai na tarbar su mom ,yau zasu d'awo Nigeria tare da yaya jawad h'aka Anuty bilki ta kwaso duka yaranta tazo dasu anata aiki , fatuha na h'ango sanye da uniform din ta na yan'aiki wanda ta Dade raban data sasu sun mata kyau sosai part din sadiq ta wuce riqe da cup ganin b'aya parlour yasa ta tura qofar d'akin yana tsaye gaban dressing mirror sanye da shada blue ta sha aiki da dark blue zare yana combing din gashi kan shi, murmushi ya saki tare da qarasowa wajan fatuha amshe cup din yayi ya aje saman stool kallo tabi shi da shi dan yau ba qaramin kyau ya mata ba har mamakin kanta take har yau ta kasa ganin wanda yafi sadiq kyau da komai gashi kullun qara kyau yake ,hura mata iskar da akayi ya sata ware manyan idanuwan ta tana kallan sadiq, smile yayi yace "Tunanin fa? kin hanani tunani amma ke gashi kinayi yanzu" ah bafa tunani nake ba to mikikeyi bayan gashi na gani um kayi kyau thanks ke ma kinyi kyau a haka din eh mana cup din ya dauka ya kai bakin shi hmmm ya lumshe ido lalai fatuha ta iya hada coffee gaskiya zani da ke dariya tayi tace "Allah idan na biye ma sai mu kwana anan muna surutu hehe" ko tam shikenan tafi tunda tafiya zakiyi ni bana so kiyi aikin shiyasa nace akiramin ke amma tunda kin fi so ki wahala shikenan tafi munma bata, langwabe kai fatuha tayi tace "Kayi hakuri ka ga su mom ne zasu d'awo kaji" ok amma sai kin min pack ko kina tafiya to tace tare da yimai pack a goshi sannan ta fice d'aga d'akin sadiq ya bita da k'allo.



*_taku har kullun salma mas'ud nadabo_*
http://www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERSFORUM.COMCOM
*CAPTAIN SADIQ*
👮🏼‍♂

*Writing by*
*Salma mas'ud nadabo*

*Edit by*
*Raheenat*


📘 *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*🐄
★We are the best★

http/mobile.Facebook.com/Real-Hausa-fulani-writers-forum RHFWF-173984973194167/?refid=52&red=opera_speed_dial_&yn=H-R


*Email* [email protected]



*Facebook* www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERSFORUM.CM


*69_70*



*_👏🏽Godiya gare ku mosayan ❤wannan novell din, ina jin d'adin y'adda kuk'e comments😍 ana mugun tare irin sosai din nan._*🤸🏽‍♀🤸🏽‍♀


*_wannan shafin naki ne Maimuna Lawal Allah ya bar zuminci har ya'ya da jikoki Ameen🤝._*


*F* atuha na shig'a bedroom din ta, ta aje ice cream din saman bedside drowe d'an gabaki d'aya ice cream din yafita ran ta, a duniya ba abinda ta tsana kamar mai kyau yayi nisa da ita, ita kanta har mamakin h'akan take jiki ba qwari ta ida cire school uniform din ta tare da shigewa bathroom ta sheqa wanka ta fito, b'ayan ta tsane jikin ta tabi da lotion mai kamshi tare da sanya black after dress din ta mai Stone's d'aure gashin kanta tayi kamar ganmo tare da Murza yar hod'a da lipstick masha Allah fatuha ba qaramin kyau tayi ba, fitowa tayi d'aga bedroom din ta wuce na mom cikin sallama ta shiga mom Na tsaye gaban dress Mirror tana shirin da alama fita za tayi cikin fara'a ta amsa,tace "Mom fita zakiyi ne?", eh wallahi zani gidan ammi ne, d'ama yanzu nake cewa ko zaki raka ni ?dan murmushi fatuha tayi itama tana san zuwa wajan ammi din nan amma tunda ta zo sau biyu ta taba zuwa g'ashi tana san ganin basma, amma Assignment ba zai bari ba gashi malam anjima zaizo , mom kin manta yau Wednesday, oh haka fa na manta fa shafa next time munje kuma wallahi mom ina san zuwa basma har ce min take bani da kirki bana zuwa, ai ta fada duk zaryar da suke maki b'aki zuwa masu kema kin fara k'oyan h'alin uncle din naki, dan smile fatuha ta saki mai cike da jin d'adi ita dai duk abinda za'a ce d'aga mai kyau yake so take ,mom ai baya san yawo uncle shiyasa. ke kuma sai biye mai kike ko? zuminci fa abin wasa bane mom ta ida zancan tana daukar handbag din ta kusan a tare suka fito, angel na zaune a parlour tana k'allan cartoon ganin grandma zata fita yasa ta tashi grandma zan biki please nop yau malam zaizo zuburo b'aki tayi gab'a tana sanyin kuka please grandma ki je dani,angel kiyi h'akuri grandma ta je kin ji? muma ranar Friday mun tafi kinji? d'aga kai jidda tayi b'adan taso, ba har b'akin mota suka raka ta suka juyo.

A dai-dai b'akin kofa suka ci qaro da sadiq sanye da 3 quarter black da white t-shirts da alama gym zashi, k'auda kai fatuha ta yi ala dole fushi take da sadiq, smile yayi tare da d'aga angel sama yana mata wasa tana d'ariya ko k'allan inda fatuha take beyi ba saboda ya lura yau rigima take ji, rabawa tayi ta gefan shi zata wuce ta cika tap qiris take jira ta fashe, ruqo hannu ta yayi h'akan yasa ta tsaya chak a wajan, ta kasa kwace hannu ta sai binshi da take da kallo, aje jidda yayi qasa yana aje ta kamar jira take tayi cikin gida da gudu, fisko fatuha yayi ta fado fafadan qirjin shi har tana jin bugun zuciyar shi lamo tayi a qirjin nashi, a hankali ya d'ago da habar ta yana kallan ta lumshe ido yayi tare da ware su kan fatuha cikin cool voice din shi yace "Fushin na menene?" um dan b'ata rai tayi tana qoqarin zamewa d'aga jikin shi tunda be san fushin me take ba, dan matse ta yayi da karfi ta saki yar qara, ta fara matsar kwalla, d'aga nace zanyi tafiya sai fushi fatuha 3 days fa kawai zanyi kin ji dear, turo b'aki tayi gaba ni ba fushi nake ba. to me kike? ba komai, ok tunda ba fushi kike ba please ki h'ada min k'ayana na rasa k'ayan da zansaka ki riga kin shagwaba uncle da yawa, dan zunburo b'aki ta kuma yi maicike da shagwaba, please karki ce bakiyi, zanyi mana promise ,promise good girl sannan ya mata pack a goshi ya fita.

B'ayan ta kamala h'ada mai k'ayan sannan ta kalli agogon d'ake mane a d'aki kusan karfe 4:30 sauri fitowa tayi d'aga part din ta wuce bedroom, d'auro alwala tayi tare da gabatar da sallah tana gamawa ta d'auko alQur'anin ta saboda yau laraba, alqur'ani kawai suke yi tare da janyo hijab din jidda tun a parlour ta zura mata suka fita a tare, lokacin har malam ya zo karatu suka yi sosai INSA malam y'a masu qarin bayin akan hadisi, sai gab da magrib suka shigo cikin gida, alwala k'awai suka gabatar tare da yin sallah b'ayan ta idar ta tsaya yin lazimi sannan tayima jidda assignment tayi nata kiran sallah isha ne ya tashe su bayan sun gabatar suka fito parlour sukayi dinner sannan kowa ya wuce bedroom din shi saboda sun gaji likis.


*Asuba ta gari*

Sallah asuba fatuha tayi tare da yin wanka, mai kawai ta shafa tare da sa yar gown iya karta gwiwa sannan ta fito bedroom din jidda ta shiga tayi mata wanka tare da shirya ta cikin unform sannan ta bar d'akin, kitchen ta shiga cikin sallama baba jinmai nata jefa bafanke gaishe ta fatuha tayi cikin fara'a ta amsa sannan suka gaisa da rabi'a, bude fridge tayi tare da fido yan cikin rago ta gyara ta d'aura kan wuta tare da zama tana taya su baba jinmai aiki ,sai hanata suke amma taqi sai da farfesun yayi ta juye a kola tare da h'ada coffee tasa a tray direct part din sadiq ta wuce ,a hankali ta murda k'ofar parlour ba kowa aje tray din tayi saman stool ta nufi bedroom din tsaye ta h'ango sadiq yana qoqarin sa necktie sallama tayi tare da gaisheshi cikin fara'a ya amsa sannan ta qaraso ta amshi necktie din tana samai bayan ta samai ta kalle shi uncle u looking so handsome tare da mai pack shima pack ya mata tare da daukar suit din shi black ya riqe a hannu ta ,janyo trolley din tayi suka fito parlour lokacin angel ta turo kofar tare da cewa "Daddy ta fada jikin sadiq" hug nata yayi d'an shagwabe fuska angel tayi daddy am going to miss u daddy, me to angel, amma daddy zaka min tsaraba teddys yes angel washe b'aki tayi tace "Anuty fatuha k'ema ki fadama daddy tsarabar da zaimaki" smile tayi tare da cewa "Duk abinda daddy yake so shi nake so yamin tsaraba" kallan ta sadiq yake me cike da so sannan ya zauna saman one star tray ta janyo ta zuba mai farfesun a ball saboda sadiq mutun ne mai san farfesu shiyasa fatuha kullun sai ta mai dan ta faran ta mai, feeding din shi farfesun ta fara yana sha angel itama tana bashi haka suka rinqa feeding din juna su cikin jin d'adi happy family sannan suka fito tray din fatuha ta kai kitchen ta wuce bedroom tasa uniform tare da d'auko school bag din ta.

Fitowar ta parlour yayi dai dai da fitowar su mom da abba cikin natsuwa ta gaishe su pack sadiq ya masu shida angel itama fatuha pack tayi ma mom suka fice a tare mota d'aya suka shiga da sadiq driver na ja sai da aka zo school din su yayi parking, gaba ki daya idanunta sukayi rau rau alamun zatayi kuka, suka bama sadiq hug suka fice yana kallan su har suka shige classes sannan driver ya ja mota sai airport.


Tunda sadiq ya tafi su angel suke missing nashi mom har mamaki suke, bata ko yar rahanan sun daina inkaga suna raha to sadiq ne ya kira waya haka shima can cike yake da kewar su inda yake jin kamar wata yayi ba kwana uku ba.

Akwana a tashi ba wuya wajan Allah yau kwana sadiq biyar kuma yaune ranar dawowar shi, zo ku ga murna wajan su fatuha sai zuba rawar kai ake mom sai janta take dan yanzu fatuha ta tashi d'aga yar aiki dan tuni sadiq ya yan'tata duk wani abinci da sadiq ke so fatuha ita da kanta ta mai sannan ta jera a dining area.

Bedroom ta shige tare da yin wanka, k'aya ta fido ta rasa wanda zata sa duk wanda ta fido sai ta maida can ta h'ango wata red gown me Stone's, aje ta tayi a gefe ta tsantsara kawalliya ba qaramin kyau tayi ba sannan ta zura riga masha Allah indai maganar kyau ake fatuha ta kai, angel ce ta shigo da gudu itama sanye da gown pink tace "Anuty daddy ya dawo?" waigowa tayi tare da yin fari da ido suka fito a tare shigowar sadiq parlour kenan su fatuha suka fito, k'allo sadiq ya bisu da shi mai cike da so rugawa su kayi a tare suka rungume sadiq d'ariya ya saki zaku ka dani ya fadi mom dake saukowa d'aga upstairs dariya ta saki tace "Sadiq kai da yaran ka kuna dirama wallahi" smile yayi tare da hug din mom in taqaice maku duk wani girki da fatuha tayi sai da sadiq ya ci inda yake ta binta da k'allo.

B'ayan ya hutu ya fido tsaraba yabama fatuha I phone 6 waya dadi da murna wajan fatuha ba'a magana jidda kuma Tap Apple mai shegyan kyau tare da new Teddy's h'aka suka dinqa zuba murna baki har kunne.


*2years letter*

Wata kyakyawar matashiyar budurwace da baza ta wuce 16 years ba ta rugu da gudu d'aga upstairs gudu take amma komai na jikin ta amsawa yake sanye take da 3 quarter pink sai riga white mai gajeran hannu ban gaje mutun da tayi ne ya sata tsayawa chak, cikin cool voice din ta tace "Sorry tare da rabawa ta gefan shi ta wuce" mutuwa tsaye majeed yayi yana binta da k'allo kafadar shi ya d'aga tare da sakin killing smile yabi stair's din da k'allo ,wai gowa ya kuma yi ko zai ga yarinyar amma ba alamar mutun. sama ya hau direct part din sadiq ya wuce a hankali ya murda handle din kofar ya shigo sadiq na zaune saman three star yana kallan news cikin sallama ya qaraso amsa mai sallamar yayi tare da aika mai harara wasa, sai yau zaka nemeni dan raini senses? dariya majeed ya saki tare da cewa "Sorry " ya zauna ni dai yanzu ba wannan zancan ba wacece na gani yanzu kamar d'aga part din nan ta fito? gaban sadiq ne ya yanke ya fadi qaqaro murmushi k'arfin h'ali yayi yace "Fatuha ce" *(Ohni salma🤦‍♀ yaushe fatuha ta waye haka🙄lol)* ok majeed yace tare da cije lips dinsa yana ayana wasu abubuwa a ransa......hmmmm

*Muje zuwa fan's😘*


*Taku har kullun Salma mas'ud nadabo*
[7/1, 10:09 AM] ‪+234 903 344 8176‬: *CAPTAIN SADIQ*
👮🏼‍♂

*Writing by*
*Salma mas'ud nadabo*


*Edit by*
*Raheenat*

📘 *REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*🐄
★We are the best ★


http/mobile.Facebook.com/Real-Hausa-fulani-writers-forum RHFWF-173984973194167/?refid=52&red=opera_speed_dial_&yn=H-R


*Email* [email protected]


*Facebook* www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITERSFORUM.COM



71_72

*_Ina matukar Godiya ga masoyan wannan novel, ina jin d'adin yadd'a kuke bani goyan b'aya wannan shafin naku ne duk masoyin CAPTAIN SADIQ._*



Ko da fatuha ta shig'a bedroom wayar tace ta hau ruri d'ake bedside drowe, cikin fara'a ta d'auka saboda sunan dak'e maqale a screen din wato hanan, daukar wayar tayi tare da kallan screen din kasancewar video call ne saman bed ta haye, "Hey yan'mata ya kike?" lafiya lau, wai yaushe zaki zo gida ne? ina so muje gidan ammi birthday din basma ya kusa, a ina za'ayi birthday din? inji fatuha kema kin san ba'a gida za'ayi ba, tap aikin san h'alin uncle wallahi ba ze barni naje ba, nifa matsala ta d'ake kenan wallahi, ke komai uncle komai . Eh naji din, yanzu dai ki mai dubara sai muje , gaskiya ina tsoran fushin shin kin manta randa muka je birthday din haoula kenan, wallahi ban manta ba ina sane ras, toh yayi kyau , amma fa zan shigo insha Allah .to shikenan ki gaishe min da angel tam ta katse wayar tare da kwaciyar ta.


Kamar yadd'a suka saba in suka h'adu haka suka rinqa zuba hira tare da yin musu, d'ama sun saba baza su taba rabuwa ba tare da sunyi musu ba, amma duk wannan hirar da su majeed suke tunanin fatuha na maqale a ransa, kiran sallah magrib ne ya tashe suka d'auro alwala suka wuce masallaci. basu suka dawo ba sai bayan sallah isha, ko da suka dawo majeed bai shiga gidan ba d'aga waje ya tsaya tare da jan motar shi yana tunanin ta inda zai bulo ma fatuha dan a gaskiya a shirye yake da ya aure ta kota halin kaka.......hmmm tofa🤭


Ko da sadiq ya shigo gidan mom na zaune a parlour ita da angel suna kallo, kallan parlour sadiq yayi tare da cewa "Angel ina Anuty?" tana bedroom Ddy. ok yace sannan ya haura sama ko minutes 5 bai yi ba ya dawo parlour tare da wuce wa bedroom din fatuha, zaune take saman bed tana assignment da laptop din ta sanye take da rigar bacci dai-dai gwiwa sai gashin k'anta data nanade shi k'amar ganmo,

Bud'e kofar da akayi ne yasa ta d'aga eye's ball's din ta ture laptop din tayi tana qoqarin tashi, harara sadiq ya aika mata, tare da cewa "Ina car Key's dina?" zuburo baki tayi gaba, wato kin rai nani ko? shine zan fita kika d'auke min car Key's kika boye . sorry uncle wallahi bana so ka fita ne ka sha rana, Kuma da ka fita ai da bakwan ka be same ka ba am sorry tasa hannuwata biyu a kunne Allah yaba ka hakuri. matsowa sadiq yayi kusa da ita har tana jin saukar numfashin shi ja mata baki yayi har sai da ta saki yar qara, tabe baki tayi tana shirin yin kuka kul kika min kuka wallahi yau sai kin kwana kina kneel down kuma kin san zan iya, bani Key's din, bedside drowe ta bude tare da zaro Key's din ta miqa mai tana qoqarin komawa saman bed janyo hannu ta yayi yana qare mata kallo ba qaramin kyau ta mai

Please Login or Register in order to submit comment